Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
ki iya taran napep
su kawo ki gida ba, za ki gani a kwanon ki ai.''
Sannan ta kuma harar su Reedah tare da faɗin ''ku gafara min na wuce abeg.''
Unaisha ce ta gyara zaman glasses ɗinta sannan ta ce ''Calm down kina da baƙi a waje, You better
respect your self Hajiyata.''
Furzar da iska Liya ta yi sannan cikin sassanyar muryarta ta ce ''ya ce na yi wa Mamin abokinsa girki buh
I don't know how to do it.'' ta ƙarashe maganar kamar za ta yi hawaye.
Murmusawa Ily ta yi tare da faɗin ''Time.''
''What do you mean?." Liya ta faɗa haɗe da ɗage girarta guda ɗaya.
''Nothing much, kije ki ta ya matar hira i will handle it.''
''Salimar fa?."
''Itama yau ta huta.''
''Ki tabbatar kin yi mai daɗi please.''
''Allah sai na bar ki da kayan ki.''
''Sorry little sis.''
Daga haka suka bar Ily suka fito daga cikin kitchen ɗin.
Ko da ta fito ma matar har ta fara harraman tafiyya, cikin muryarta mai sanyi ta ce ''Ummi ba dai tafiya
ba na ɗaura miki girki.''
''Noo daughter na gode da karramawa, ai abin sha ɗin ma kaɗai ya yi, and besides am in a hurry
Abbanku ya dawo, kar ya ga na daɗe.''
''Toh Ummi yaushe za ki zo ki kwanar min?."
Murmushi Ummin ta yi tare da kallon zallar yarintar Liyanar, sannan kuma cikin muryarta mai nuna
ƙaunar Liyanar ta ce ''Don't worry daughter ai sai dai ki zo ki kwanar min, zan sa shi ya kawo min ke
okay.''
Murmushi Liyana ta yi mai kyau sannan ta ce ''Okay Maa my regards to Abba.''
''In shaa Allah dear.''
Daga haka Hydar da tun ɗazu ya sauko ya ɗauki jakarta.
Jakar dake ƙasa Ummin ta bata haɗe da faɗin ''Ga wannan ba yawa.''
''Mai yawan kenan Ummi, na gode sosai.''
Bai kallesu ba ya yi gaba haɗe da riƙe jakar na ta.
Sai da ta rako Ummi bakin mota sannan ta koma cikin gidan.
Ummu ce ta yi murmushi mai faɗi sannan ta ce ''Aliyyu.''
''Yes Maa.''
''Ka yi sa'ar mace wallahi, ka riƙe ta hannu bibbiyu, she's very socialize, I think you have won the trophy,
ba ka da wani damuwa a yanzu.
Ga sanin ya kamata, ga kyau ga sura mai kyau ga hali mai kyau.''
Aliyyu ji yake kamar ya nutse a ƙasa dan kunya, dan sura mai kyau ɗin nan ji yayi kamar ya koma gida.
Daman kuwa bai yi nisa da Gidansa ba ya yi parking motar tare da faɗin ''Ummi Amir ya ja ki i forgot
something at home, gobe sai na zo wurin Abban.''
''Is Okay Son je ka wurin matar ka duk da naga ta yi baƙin dare.''
Amir kam banda dariya babu abin da yake.
Bai kula sa ba ya fice a motar tare da sosa ƙeyarsa, Amir ya dawo wajen mazaunin driver, sai da ya yi wa
Amir kallon warning sannan ya wuce ya kama hanyar gidansa.
Bayan Liyana ta dawo ma sa wa tayi Ily ta kashe gas sannan suka fara hira har da Salimah.
Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ita wanda zai iso wurin, hakan ya saka ta ɗan lumshe idanunta na
y'an daƙiƙu tare da sauke su akan kyakkyawar fuskar sa.
Wani kalar murmushi ne ya suɓuce mata wanda ba ta yi aune ba.
Gaisuwan da yake amsawa ne ya dawo da ita daga duniyar da ta lula.
Kallon wadda ya sanya aiki zaune ta na hira da ya'n uwanta yayi.
Wani kallo ya watsa mata haɗe da faɗin ''Ina abin da na sanya ki?.''
Turo lips ɗinta ta yi tare da kai dubanta wurin da yake tsaye tare da faɗin ''Ai Ummin ta tafi.''
Sai da ya kalli fuskan ya'n falon sannan ya ce ''Biyo ni."
''Ina ɗin zan biyo ka?."
Bai kulata ba ya cigaba da tafiyarsa.
Kallon su Reedah ta yi tare da faɗin ''Wai ƙarfe nawa za ku tafi ne?."
''Anan za mu kwana.'' Rashidat ta faɗa ta na kallon fuskan ya'n uwanta.
''Cabɓ, tun da kuka zo ya ƙafe ku da idanuwa, wallahi ku taso ku kama hanyar zuwa gidan Abbhi, haka
kawai, akwai fa aure tsakanin ku.''
''Kaji Liyana da wani zance, Allah na tuba, gaskiya wannan maganar ta ki ta ɓata min rai ainun.''
Unaisah ta faɗi hakan tare da cire glasses ɗinta.
''Ai wallahi sai mun kwana, Ilham kunna mana TV abeg.'' Faridat ta faɗa haɗe da shingiɗewa akan kujerar
parlourn.
Tsaki ta ja tare da barin wurin.
Tsaye yake a wajen corridor ɗin ɗakinsa tsawon minti biyar ya na ta jiranta, cikin muryarta da yake jinsa
har brain ɗinsa ta ce ''Gani.''
''Saboda iskanci kin wani shanya mutum kamar mai jiran zuwan sarki, ko kin fara hauka ne.''
''Ni ka daina kira na mahaukaciya tun da ba a bola ka tsince ni ba.''
''Are you talking to me.''
''Allah ni ba da kai nake ba.'' ta faɗa tare da niyyar arcewa aguje.
Fizgota ya yi tare da haɗe ta da jikin bango, hannunsa ɗaya ya dafa a bangon da'yan kuma ya na mai riƙe
haɓarta da shi.
Mutsu - mutsu ta shiga yi da bakinta da har lokacin lipstick ɗin bai goge ba.
Tsirawa bakin ido ya yi tare da matsowa da fuskarsa gab da nata lumshe idanunta ta yi sosai ta na Allah
Allah ya sa sumbatar ta zai yi.
Hydar da mutsu - mutsun da take da bakinta ke ƙara birgesa hakan ya sa ya ƙara matso da face na sa.
Hannunsa na tsakiya da kuma na ƙarshe ya haɗe tare da balle mata lips ɗin har sau biyu.
Liyana dake tsammanin jin lips ɗinsa ne taji wani kalar azaba ba ta san time ɗin da ta buɗe ido ba ta
ware su akansa haɗe da riƙe bakin nata.
Ranƙwashi ya ƙara sakar mata haɗe da faɗin ''You're expecting me to kiss you right?, toh Allah ya tsare
bakina.''
Liyana saboda zugin da bakinta ke yi har ta fara ƙwalla.
Tsaki ya yi tare da faɗin ''Spoiled brat.'' sannan ya shige ɗakinsa haɗe da kulle ƙofar da ƙarfin tsiya.
Fashewa ta yi da kuka haɗe da durƙushewa a wurin.
Su Ily kam da suka gaji da zama tashi suka yi suka fita a gidan tare da tafiya gidan Ammi.
Daga ƙarshe dai Liyana sai da ta kusa hour ɗaya a wajen ta na gunjin kuka, sai da ta ji alamun kamar zai
buɗe ƙofa sannan ta shige corridor ɗin ɗakinta tare da shigewa ɗakin gaba ɗaya.
Can ɓangaren Hydar hakan nan yake jin wani kalar mix feelings a tattare da yarinyar. He dislikes her
habits, not her, amama wani ɓangare na zuciyarsa gaba ɗaya yake ƙinta.
Safa da marwa ya shiga yi tsakanin falo da master room ɗinsa, shi haka kurum yake son ya yi punishing
ɗinta.
Ace matar da ya aura babu kalar club da gidan nanaye da ba ta sani ba.
He always wants kamilalliyyar mace for his self, the one with Deen, ƙarshen zance kuma wacca idan ba
Hijab ta saka ba she will feel that the whole world ita suke kallo.
Saɓanin wannan da su Mami suka zaɓa masa, wadda ko da lingerie za ta iya zuwa duk wata duniya da ta
ga dama ba tare da ta ji ko ɗar ba, ba ya jin ta iya karatun Alkur'ani mai girma, kullum cikin waƙa take
kamar jiƙar Bob Marley.
Idan ya ce an cuce sa a wannan haɗin bai yi ƙarya ba.
Dubi mahaifiyyarta mutuniyyar arziƙi he can remember ranar da ta basu 5, 5k shi da Amir.
Very cheerful giver, uwa uba hankali, shi ma Dad ɗinta is something similar with the girl.
Wani kalar tsaki ya ja tare da shigewa toilet ya ɗauro alwala tare da gabatar da shafa'i da wuturi haɗe
da kwanciyarsa amma still baccin is no where to be found tunanin Liyana ya masa kane - kane a rai.
Ɓangaren Liyana kam tun da ta shiga ɗaki recalling ɗin haɗuwarsu da shi take tun lokacin da suke 100lvl.
Da akwai ranar da suka fita da Ily da aurensu ya na jingine da jikin mota ta sheƙar da ruwa a jikinsa da
gangan, and that day ma a maimakon ta ba shi haƙuri sai ma gwalo da ta masa tare da faɗa masa ta ga
uban da ya tsaya masa.
Haka tai ta tariyo duk wani abubuwan da ta ɗinga masa wanda sai da suka saka ta kuka.
Duk da yanzu almost 2 Weeks da saninsa a matsayin mijinta, buh that guy is very dangerous, he can
squeeze her a lokaci ɗaya a manta da babin ta ''Ya rabb have mercy upon me.''
Ta faɗa haɗe ƙanƙame jikinta, sannan a hankali ta shige toilet haɗe da yin wanka ta fito ɗaure da wani
white towel.
Drying ɗin gashinta ta yi tare da zira kayanka da take Sallah da shi, bayan ta idar da sallar ma sai da ta
ɗan roƙawa kanta tsari sannan ta kwanta bacci dan gobe za ta fita school.
Su Ilham kuwa tun da suka baro gidan Liya kowa ransa yake a ɓace, barimma Unaisah da Rashanda.
Ammi dai tun ta na tambayar na su har ta daina, Rufaidhat kuwa daman ko gidan rasuwa ba ta je ba , a
cewar ta da iyayenta suka mutu Ikimat ɗin ba ta zo ma ta ba.
Ɓangaren gidan rasuwa kam bayan fitar Liyanar da Hydar Abbhi sai da ya tayar da maganar, haɗe da
ƙoƙarin kiran police, amma da Jiddah ya tsawatar masa sai ya bawa police ɗin haƙuri haɗe da faɗa musu
is a family issue.
Mama Fatuh da Yusrah kan sun gama ƙullace - ƙullacensu sannan suka koma can gida Niger, Maraɗi inda
acan Mama Fatuhn ke da aure.
A taƙaice dai gidan ya watse daga Mama Maimu sai Mama Lantana mahaifiyarsu Mama Fatuh.
Sai dai mu ce Allah ya jiƙan Ummaru da gafara.
Washegari da sassafe kafin ta tashi har Salimah ta tanadar mata emergency ɗinta dan wani kalar ciwo da
jikinta ke yi saboda aikin da ta sha jiya.
Zaune take akan dinning table ta na cin milky donut ɗinta da strawberry hollandia ɗinta hankali kwance
ta na ci ta na lumshe idanunta haɗe da chatting da Lily.
Ƙamshin turarensa ne ya fara ziyartarta haɗe da dagule lissafinta ta dabarbarce lokaci ɗaya.
Cikin shigarsa na gym ya shigo hannunsa ɗauke da bottle water da kuma hanky.
Kallonsa ya kai wajen dinning ɗin take zaune cikin wani faux fur v neck jacket black color sai wani crystal
jeens palazzo trousers shima black color kanta ɗaure da wannan ɗan kwalin nata na martar minista.
Ƙafafunta sanye da wani classy crystal boots white color designers mai shegen kyau da tsada.
Sai kuma wani gucci bag white color akan table ɗin dinning ɗin.
Sai idanunta dake sanye da wani glasses mai form ɗin medical glasses Wanda ta saba sawa.
Tun da ya shigo kanta yake a tsugunne, jin idanunsa na yawo akanta hakan ya sanya ta fara ɗagowa a
hankali tare da sauke idanun ta akan nasa for the second time.
A dabarce ta ce ''Goo.... Good.....mor.....ning.....Yaya Alih.''
''Morning.'' ya amsa a taƙaice tare da shigewa cikin kitchen ɗin dake bayan ta.
Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da shigewa kitchen ɗin itama dan ta ɗauki package ɗinta ta
wuce school.......
*Durrah Hydar.*✍️
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."
*THE REGRET*
(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎
This page is dedicated to you my favorite brother.
Yaya Sa'id dinaa 💎
Allah ya shiga lamarin ka Alhajina.🦋🎊
Burin kowace y'a mace.👥🌕
May Allah's blessings always be with you Fav miii 👥
Iganya miii🫢💪
_ Pending Amarya 37_
Tun da ya shigo kanta yake a tsugunne, jin idanunsa na yawo akanta hakan ya sanya ta fara ɗagowa a
hankali tare da sauke idanun ta akan nasa for the second time.
A dabarce ta ce ''Goo.... Good.....mor.....ning.....Yaya Alih.''
''Morning.'' ya amsa a taƙaice tare da shigewa cikin kitchen ɗin dake bayan ta.
Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da shigewa kitchen ɗin itama dan ta ɗauki package ɗinta ta
wuce school.
★_______________________★
Ko da ta shigo kitchen ɗin ya na tsaye a gaban coffee maker ya na ƙoƙarin juye coffee ɗin a cikin mug, a
hankali ta iddasa shigowa haɗe da nufar kan kitchen island ɗin ta ɗauki abin da Salimah ta mata
packaging, ''Where did you think za ki je by this time.'' ya ƙarashe maganar ya na mai juya milk a cikin
coffee ɗin, kallonsa ta yi da kyau sannan kuma ta juya da niyyar ficewa daga kitchen ɗin.
''One step kika ƙara sai kin gane shayi ruwa ne.''
''Toh ni dan Allah mai na maka?." Ta yi maganar kamar za ta fashe da kuka.
''Ba za ki fita daga gidannan da wannan kayan ba, find something better to wear, otherwise babu inda za
kije.''
''Amma ai a haka nake fita daga cikin gidan nan for almost 4-5 months, and besides wannan shigar nake
tun ina gidanmu har a gidan kakanni na.''
''Ba na magana biyu, find something else to put on, leave my presence.''
''Yaya Alih.''
''Ba ni da ƙanwa irinki.'' daga haka ya zo zai wuce ta gabanta, da sauri ta riƙe rigarsa tare da faɗin
''Pleaseee.''
''Ƙyale min riga na ko na zuba miki ragowan abin da ke hannuna.''
''Dan Allah ka yi haƙuri, ai kayan ma a lefe aka saka min wallahi.''
''Cika min riga ta na wuce, wai yaushe ma na fara wasa dake to this extent.''
''Allah ni ba zan cika maka rigar ba , You have to say yes, an.....''
Bai bar ta ta ƙarasa maganar ba ya watsa mata ragowan coffee ɗin ba ki ɗaya haɗe da sakar mata
ranƙwashi a kai.
Ba zato ba tsammani Liyana ta ji saukar coffee mai zafin gaske a fuskarta, a gigice ta saki ihu haɗe da riƙe
fuskan na ta.
''You think that ba zan iya ba right?." Ya na faɗin hakan ya ja tsaki haɗe da ficewa a kitchen ɗin.
School ɗin da bata je ba kenan.
Da ƙyar ta lalubo hanya ta wanke fuskarta a sink ɗin dake kitchen, jacket ɗinta duk ya ɓace da coffee ɗin,
ji ta yi kawai kuka ta zo mata babu zato babu tsammani kawai ta haura sama da gudu.
Ɗauraye jikinta ta yi sannan ta ƙara saka wani polo shirt da kuma palazzo trousers, wani ƙaramin akwati
mai kyau ta ɗauka tare da zuba kayanta aciki.
Har ta gama loda kayan ta na ta hawayenta sai kuma ta koma a hankali ta zauna haɗe da fashewa da
kuka ta na faɗin ''Ba abin ka je gida ba Ammi ta ce ba haka ba, ka kama hanya kaje gidan Neneh kuma
gorin duniya ta haɗa ta yi maka shi.''
Goge hawayenta ta yi tare da ɗaukan wayarta ta na mai kiran Abbhi amma bai ɗaga ba.
Cilli ta yi da wayar akan gadon bacci ɓarawo ya sace ta.
Arround ƙarfe biyun rana Salimah ta shigo kawo mata lunch, ko kallonta ba ta yi ba ta shige toilet haɗe
da yin alwala.
Bayan ta gabatar da sallar ma kiran Abbhi ne ya shigo wayarta haka suka cigaba da hira har sai wajen
uku sannan ta shige toilet ta yi wanka haɗe da alwala domin miƙa sallar Asr. Hakan nan ta tsinci kanta da
yin shiru akan abin da Aliyu ya mata ya da safe.
Bayan ƙarfe shida na yamma ta sauko cikin shigarta na boomb short da kuma wani polo da ta ɗan ɗage
shi kunnen ta sanye da ear pods ta na jin waƙar _Ayra Starr_, kan ta ba ɗan kwali amma gashinta a tufke
yake, sai wani lipstick mai kyau dake ƙyalli a leɓenta.
Zaune yake akan kujerar parlourn ya na kallon tashar Spotlight ya na kallon wani wasan Madrid, sai
tapping ya ke da hannu ya na faɗin ''Mbappe pass the ball.''duk da she's a fan of Madrid amma Allah,
Allah take ƴan Liverpool su cinye wannan ball ɗin.
Wani kalar dribbling M Salah ya kai wa Belingum da Mbappe ya yi wa passing ball ɗin wan da atake
ƙwalon ya shige cikin ragar Madrid.
Wani kalar tsaki Hydar ya ja ya na faɗin ''Ohh God, damn it, ci biyar at thesame time.'' dariyar da yake ji
ana yi ne ƙasa- ƙasa ya sa shi juyawa ya na kallon side ɗin da yake jin dariyar na futowa, dan shi har ga
Allah bai ga shigowarta ba.
Haɗa idon da suka yi da shi ne ya sanya ta ƙwarewa ta fara tari sosai, nufuto ya fara yi hakan ya sa ta fara
janye jikinta ta na matsawa baya.
Daman tun da can a jogane yake zaune a falon tun cin farko da aka musu, Amir ya kira shi yake ta masa
dariya.
A zafafe ya ƙaraso wurin tare da faɗin ''You're laughing saboda an ci mu wasa right?."
''Noo wallahi am coughing ba dariya nake ba.''
''Za ki gane kurenki ne yanzu.''
''Dan Allah kayi haƙuri wallahi, fuskata kaɗan ya rage fatar wajen bai ɗaye ba dan zafi, please Yaya Alih.''
''Stop calling me with that stupid name da kike ƙoƙarin kakaɓa min.''
Sosai Liyana ta tsorata da lamarin Hydar.
Wani kalar ɓaci ransa ke ƙara yi, yadda take ba shi haƙuri at the same time take wani kalar murmushi,
abin da ya tsani Sultana ta yi.
Zuciya ce ta ɗibe shi hakan nan kawai ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga lafta ma ta kamar an aiko shi.
Dukanta kawai yake babu ji babu gani, Salimah da ta ji ihunta ta fito bawa Hydaar ɗin haƙuri, guda ɗaya
da Ya shauɗa mata a baya ba ta san time ɗin da ta shige ɗakinta ba haɗe da saka key.
Ga shi jikinta daman babu kayan arziƙi duk cinyarta sai da ya yi masa dukan lilis.
''Frog jump.'' ya faɗa a zafafe haɗe da cillar da belt ɗin hannunsa tare da shafa gemunsa.
''Ba ki ji abin da na faɗa bane!." Ya faɗa a tsawace.
Ta na layi ta tashi haɗe da faɗin '' Ni ban san yadda ake frog jump ba.'' ta ƙarashe maganar tare da
fashewa da kuka.
''Kin ga already Sallah ake kira, kafin na dawo daga masjid ki tabbatar kin fara frog jump ɗinnan, if not za
ki ga the worst side of me.''
Ya ƙarashe maganar tare da yin ƙwafa ya wuce masallaci da kayan jikin nasa.
Liyana cinyoyinta kawai take bi da kallo haɗe da yin da na sanin fitowar da ta yi, indai wannan ne aure
wallahi da ba ta yi ba, sanin miji ko iftila'i'.
Fashewa ta ƙarayi da kuka mai tsuma zuciya.
Ƙarar buɗe ƙofar falon da ta ji ne ya sanyata tashi da sauri ta na sharɓar majina haɗe da yin frog jump
ɗin.
Shigowa ya ƙarasa yi cikin takunsa na ƙasaita haɗe da faɗin ''Make sure kin zagaye falon nan sau uku.''
A tunaninta ko wucewa sama zai yi sai ta ga ya ma jawo ragowan fresh milk ɗinsa ya na sha.
Sai da ta zagaye falon sau biyu sannan ta ji ƙarar buɗe ƙofar ɗakin Salimah.
''Salimah ina za kije?." ''Yaya Hydar girki zan yi na ga dare ya fara yi.''
''Je ki huta yau ita za ta yi girkin, You over there."
Juyowa ta yi ta ƙafe shi da manyan idanunta.
''Ma za ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abatcha, Salimah akwai fresh cassava da na kawo yau a ina
kika ajiye?."
''Store ɗin ajiye potatoes yaya.''
''Mai kuma abatcha