Advertisements
Chapter 32 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 39

93K to 96K   out of 116.5K words

Marwar ba ya wuce shi da Liyanar da taƙi Sam ta haɗa ido da kowa na wajen.




Suna shiga cikin motarsa ta haɗe kanta da gwiwa ta fara wani kalar kukan da ba ta san dalilinsa ba.



Har cikin ƙwaƙwalwarsa yake jin kukan na ta wanda hakan ya sanya shi samun gefen titi ya yi parking ɗin
motar.



''Fatima what's wrong.?" Ya yi maganar ya na ɗan kallonta, ganin ba ta ba shi amsa ba ya sanya shi ɗan
kai hannunsa da niyar taɓa ta.



Da sauri ta ɗago tare da buge hannunsa tare da faɗin ''Don't touch me.'' sannan ta jinginar da kanta
wajen sit belt ta ci gaba da kukanta.



Ganin sanyin da yake ƙoƙarin fara ma ta ba son sanya raini a tsakaninsu ne ''ya sanya shi juyo da kanta a
fusace ya na mai kallon cikin idanunta.
Ƙoƙarin cire hannunsa take a jikinta amma ta kasa, hakan ya sanyata sadaƙarwa tare da ƙafesa da
manyan idanunta.



Haɗe bakinsa ya yi da nata ya bata wani light kiss tare da mayar da ita baya kaɗan, kana ya ce ''Tell me
what's going on, why are you frowning, kin san fushi ba ya miki kyau, you look like gorilla, idan kika yi
kuka kuma, kama kike da ostrich, sai wuyan ki ya yi dogo.'' ya yi maganar yana gesturing da hannunsa.

Ƙara fashewa ta yi da kuka sannan ta ce ''After the cin mutumci of that hug har da zagina kake, a gabana
yarinyar nan ta rungumeka and you're even enjoying the hug, ''Ahhh Marwa kar ki karya ni'', haba Yaya
Aliih wannan ba girmanka bane sam sam.'' ta ƙarashe maganar tare da ɗaukan tissue ta na goge
hawayenta.

''Ahh okay, sakar miki fuskan da na yi har ya kai da za ki ɗinga ga ya min magana son ranki kenan, ya yi
kyau.'' ya na faɗin hakan ya yiwa motarsa key tare da barin wajen.



Bai ma ta magana ba ita ma ba ta masa ba har yaje ya yi shopping ɗinsa ma ba ta fito daga cikin motar
ba, a cewarta kar ta ga abin da ya fi ƙarfinta a wannan karon.




Sai da yamma sannan suka dawo gidan shi ma ko abincin da aka jera a dinning ba ta ci ba ta wuce saman
ɗakinta duk da yunwar da yake nuƙurƙusanta.

Ya na kwance a ɗakinsa ya na kallon duk wasu moves ɗinta.

Seeing her naked body always turns him on, kamar magnet haka ya yi ta jan ƙafa har ya ƙaraso cikin
ɗakin nata.




Tsaye take a gaban madubi jikinta ɗaure da towel light color, ta na shafe jikinta da tsadaddan manta.



Jin an fisge towel ɗin jikinta ne ya sanyata ɗagowa a razane tare da kallon yadda yake binta da wani
kalar mayen kallo.
A fusace ta fisge towel din na ta daga hannunsa haɗe da dalla ma sa harara sannan ta yi hanyar restroom
ɗinta.



Saurin fizgota ya yi ta faɗo jikinsa, sannan a hankali ya fara massaging jikinta.



''Ni ka daina taɓa ni, just go away, go and make your stupid love to her.'' Liyana ta yi maganar a hasale
tare da ƙoƙarin fizge jikinta daga nasa wasu hawaye na zubo ma ta.




''Sorry i can explain.'' Hydar ɗin ya faɗa tare da stretching hannayensa a kan kafaɗarta ya na kallon cikin
idanunta.



''Explain what?, the hug?, or that stupid Marwa.'' ta yi maganar ta na nuni da hannunta kamar Marwa na
wajen.



Wani kalar numfashi ya furzar wanda a take idanunsa suka yi wani kalar jaa, sosai ta tsorata da ganin
yanayinsa yadda yake wani kalar huci kamar mayunwacin zaki, sannan a hankali ya soma magana '' Can
you just give me a chance to talk, I can explain na faɗa miki, Marwa......... Marwa is the girl that I
intended to marry few years back, na sota a lokacin, amma ta watsa min ƙasa a ido, ta zaɓi wani a
maimakon ni, kuma har yanzu ina jin sonta a raina, amma ki yarda dani sam ban yi tunanin za ta yi
hugging na wa ba, i didn't even see her, why am I even telling you this bayan ba yarda za ki yi ba.'' ya
ƙarashe maganar ya na ƙoƙarin zama a cushion ɗin ɗakin.



''Karka zauna min a ɗaki, tun da Marwa ce wadda kake so sai ka nufi wajenta, thank God da ban ma yi
accepting ɗin stupid friendship ɗinka ba.'' ta yi maganar hawaye na ɗan zuba daga idanunta.



''My Lord, ke nake so yanzu ba ita ba just understand.......
Jiya banda data Wallahi kuyi haƙuri 😂




Manage please 💎🥀

I'm missing something precious 😭




''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂



*THE REGRET*
*PENDING AMARYA CE *🫧💕🥰




*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*✌️




*Page 55*




Respect that lady that wants nothing from you but your loyalty and real love ❤️
Respect her bro 😎😔
Note edited ✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻




><><<><><><>



My Lord, ke nake so yanzu ba ita ba just understand.” Ya yi maganar ba tare da ya san ya faďe ta ba.




Jin maganar da ya faďa ne ya sanya ta ďagowa da sauri, Wanda hakan ya sanya shi saurin ďago da wani
zancen daban tare da tashi daga zaunen da yake ya na mai tallab’o hab’arta tare da faďin “Liyana , idan
kika natsu za ki fahimci duk abin da nake son fahimtar dake, for my pass life I make some mistakes that
ni kaina idan na tuna su I feel like dying…’’ bai kai ga ķarasa maganar ba ta yi sauri ta cab’e haďe da
faďin “ You make love with her right?, daman na san za’a rina, you cheated on me tun kafin ka sanni.” Ta
ķarashe maganar tana mai zama a kan edge ďin gadon, hawaye na silala a kan fuskarta.




“ Noo wallahi Liyana is not what you’re thinking.” Ya yi maganar tare da ķara janyota jikinsa.




“ Let go of me, ni wallahi ka daina tab’a ni tun da Marwa kake so, sai ka je ka aureta daman akwai parts
da dama a gidan sai ka ajiyeta.’’ Ta ķarashe maganar ta na gyara zaman towel ďinta.




“ Liyana ki gane mana, wallahi she’s just a friend.” Ya yi maganar trying to get her lips on his lips.
“ Incredible, first ka ce min she’s the girl da kake son aura, amma yanzu you’re telling me she’s just a
friend, are you okay?.” Ta yi maganar a hasale.



“ Are you insulting me?, ko kin fara shaye shaye ne?, tun da har Ina lallab’a ki kin ķi ganewa sai mu zuba
dake, spoiled brat, oya hau kan gadon nan kafin na kwashe ki da maruka a wajen nan.” Ya ķarasa
maganar a zafafe.




Fashewa ta yi da kuka sosai sannan a hankali ta ce “ Daman na san ba sona kake ba, since from day one
a haďuwar mu ba sona kake ba, Allah ka zama gatana a gidan Aliyu, daga wannan sai wancan , ni na
gaji.” Ta yi maganar ta na mai goge ďan ķwallan da ya zo ma ta.




Saurin jawota ya yi jikinsa tare da rungumeta sannan a hankali ya fara sakar mata kiss a goshi sannan
salon labarin ya sauya.




Washe garin ranar ma da mugun kwaďayin abaćha ta tashi.



Ko da ta farka ba ta gansa ba cikin ďakin jiki ba ķwari ta nufi toilet tare da yin duk abin da ya dace sannan
ta fara harraman sallah.




Bayan ta idar da sallar ma direct kitchen ta nufa tare da kamawa Salimah aikin da ya dace sannan ta
koma samanta shirya cikin wani silky gown da ya mannewa shape ďin jikinta.
A hankali take saukowa daga saman stairs ďin hannunta ďaya na dafe da ķasan cikinta ya yin da ďayan
hannun ke riķe da mariķin benen.




A dai-dai lokacin kuma Hydar ya buďe ķofar parlourn hannunsa riķe da bottle water da hanky ya na goge
gumin jikinsa.




Kallon second biyar ta ma sa sannan ta ďauke kanta ta cigaba da taunan chewing gum ďinta, sannan ta
tako a hankali ta zauna a kan three sitter tare da ďaura ķafafunta a saman center table.



Da kallon mamaki kawai ya bita da shi tare da fara ķoķarin wucewa domin ya shirya, dan daga yau zai
fara shirye - shiryen su na tafiya china.




Har ya wuceta ya jiyo siririyar muryarta a kunnensa na faďin “Yaya Alih dan miķo min Apple.” Ta yi
maganar ta na ďan shafa cikinta.




Bai tanka ma ta ba ya wuce har zuwa inda take ya ďauki basket ďin apple ďin gabaďaya ya miķa ma ta.
Har ya tafi ta kuma kiransa, ķanķance idanunsa ya yi tare da miķo ma ta remote ďin da za ta iya
stretching hannunta ta ďauka, sannan ya ďauka ya miķa ma ta.




Daga haka ya wuce stairs da ďan sauri ba tare da ya ķara ko kallon inda take ba.




Ko da ya ķarasa ďakinsa ma banďaki ya shiga direct tare da yin wanka.




Zaune take a yadda ya barta hannunta riķe da plate ďin abinci, ďayan hannunta na kan cikinta ta na
shafa shi kamar jikin kyanwa.




Ķarasowa ya yi cikin shigarsa na wani sky blue ďin _Senate wears_ hannunsa na sanye cikin aljihun
wandonsa, sai ķafafunsa dake sanye da wasu takalma masu kyau da tsada black color, kansa kam na
sanye da hula black kalar na yoruba people ďin nan.




Kallonsa ta kai garesa ta ga yadda shigarsa ya masa wani kalar mugun kyau, ga wani haska shi da kayan
suka yi.
Take taji wani kalar wutan kishinsa na wuruwa a cikin zuciyarta.




Bai bi ta kanta ba ya wuce dinning ya na mai zama, coffee kawai ya sha mai madara sannan ya ďauki car
key ďinsa.

“Ina za ka je.?” Ya tsinci muryarta a cikin kunnensa.



A fusace ya juyo tare da faďin “ Wallahi daraja ďaya kike ci a gidan nan you better behave yourself, just
because ina ďan ďaga miki ķafa kar ki saki ki ďauko hanyar raina ni, c’mon wuce ki ďauko himar ďinki ki
same ni a cikin a mota.” Ya ķarasa maganar tare da ficewa daga cikin gidan.




Sai da ta saki wani tsaki sannan ta wuce ďakinta tare da ďaura wani zunbulelen hijab a kan kayan jikinta.




Sai da ta bawa Salimah sallahun lunch ďin da za a yi sannan ta bar living room ďin.”




Tsaye yake jingine da motarsa ķirar Lexus hannunsa riķe da wayarsa Wanda alamu sun nuna chatting
yake.




Bai ji alamun tahowarta ba sai Jin ķwace masa waya da a ka yi.
Da sauri ya ďago kansa tare da kai dubansa wajen da take tsaye, ta na kallon screen ďin wayar ta na
kuma kallon inda yake tsaye.



Ji take kamar ta buga wayar da ķasa ko za ta ji sanyin abin da take gani a ciki.



Kamar wata mai asthma haka numfashinta ya yi ta mata barazanar ďaukewa, ganin hakan ne ya sanya
Hydar saurin tallab’ota amma ta ķwace jikinta daga cikin nasa hawaye na ķoķarin fita daga idanunta.



Miķa ma sa wayarsa ta yi tare da shigewa cikin motar tare da mayar da kujerarta baya ta na mai ďan
kishingiďa.




Fashewa ta kuma yi da kuka tare da juyar da fuskarta ta na kallon window ďin b’angarenta.



Ko da ya shigo ma sai da ya ďan saci kallonta sannan ya fara tuķin motar.




Sun ďan yi nisa da fara tafiyar sannan yaji saukar muryarta kamar saukar aradu.



“Explain it Aliyu.” Ta faďa tare da karkato da jikinta ta na kallonsa.



Bai ma ta magana ba ya cigaba da tuķinsa.
Cikin wani kalar murya ta ķara faďin “ Aliyu explain what I just saw, ko na kashe abin da yake cikina tun
da ka na da wani .” Ta ķarashe maganar ta na shafa cikinta hawaye na ďiga daga idanunta.



Saurin take birki ya yi tare da parker motar a lokaci ďaya ya na mai juyowa tare da fuskantar Liyanar.




“Please Liya zan miki bayani idan kika ba ni dama stop this childdish okay!.” Ya yi maganar tare da dafa
hannunta.




D’ago jajayen idanunta ta yi tare da sauke su akan kyakkyawar fuskarsa.




Wani kalar ajiyar zuciya ya sauke tare da matso da kansa ya sakar ma ta wani kalar kiss a goshi sannan a
hankali ya ja baya tare da fara faďin.




“ Amir is my favorite Cousin, he has one sister which is Marwa, Maman Amir da Mami are sisters, and
Abbha and Abbhu are also brothers from the same mom and dad.



A gidansu Amir na yi kusan rabin rayuwata, hakan ya saka ni sabawa da Marwa sosai.
Na so Marwa sosai ba wai soyayyar yan uwantaka ba, soyayya na aure, dan har feelings namu bamu iya
b’oyewa musamman da muka fara zama teenagers.



Marwa is 28 years old a yanzu, na girmeta da shekaru 5, lokacin da na gama secondary school da zan tafi
China a lokacin ita kuma ta na ss one a lokacin ne muka fara sexing each other. That’s the first time that I
noticed what women really feels like.




Ko da naje Beijing bayan na yi one year itama tayi waec and neco ta ce dole sai an dawo da university
ďinta a can Beijing.




Shi kuma daman Amir Germany is his best country dan nan ya saka a first choice ďinsa.




Bayan dawowan Marwa babu abin da muka maida hankali a kai sai kasancewa da junanmu.



Ina level 300 a time ďin ta na level one ta samu ciki bamu lura da cikin ba sam har sai da ya bayyana.




A lokacin mun shiga tashin hankali sosai mara misaltuwa.



And we have no option sai dai ta haifeshi.



Bayan ta haifi yarinyar da kwana ďaya yarinyar ta mutu that was 2011 .
Na barta ta huta for good three months sannan muka cigaba daga inda muka tsaya.



Ko da nayi final year ďina ban dawo gida ba na cigaba da masters.




2015 ne muka dawo gida gaba ďaya then muka faďawa iyayenmu muna son juna har aka fara shirye
shiryen aure a tsakaninmu.




Still mukan haďu da Marwa a hotel ko wani ďan ķaramin gida da Abbhu ya siya min, we always made
love there.



Bayan results dinmu ya fito ma I suggest na dubo mata, a lokacin aure na da ita saura one week.



Ko da na dawo ban nemi naje gida ba sai gidana da yake a nasarawa.



Ko da na Isa gidan Marwa na tare da wani namiji wannan shine dalilin da yasa na fasa aurenta.



Ita kuma ta koma North Korea ta cigaba da karatunta, Amma dan Allah Liyana I’m very sorry I don’t
know that akwai ranar da zan faďawa wani all this, yanzu hoton jaririyar ta turo min wai we have to
remake our little angel again.” Ya ķarashe maganar hawaye na zuba a idanunsa.




“Innalillahi wa inna ilaihir raji‘un, Hydar you’re once stucked into Haram relationships and calling me yar
iska all this years, ni yanzu ya’ya’na kar wani ya zo ya musu abin da ubansu ya yiwa ya’ya’n wasu.” Ta yi
maganar hawaye na zuba a idanunta.
Janyota jikinsa ya yi ya na shafa bayanta tare da faďin “ Babu abin da zai faru da su please, don’t say
those words again kin ji , kowa ya na da mistake a rayuwa nawa mistake ďin kenan and I’m still
REGRETTING.” Sannan ya janyeta a jikinsa tare da tayar da motar suka nufi gidan Neneh dan har ķarfe
shabiyu na rana ya yi.




Jiki a sanyaye ya yi horn a gaban gate ďin gidan Nenehn, da ďan sauri gate man ya zo ya buďe ya na
musu waving ďin hannu at same time kuma ya na miķa gaisuwarsa zuwa ga Aliyun.




Aliyu just nodded his head countinue to search for inda zai parker ride ďinsa.




Bayan ya parker motar ma jikinsu a sanyaye ya riķo hannunta suka ķarasa shigowa gidan Nenehn.




A zaune take kamar yadda ta saba zama ta na hira da yan aikin gidanta, idanunta sanye da eyeglasses
cikin shigarta na lifaya butter color da ya mata kyau sosai.




Ķarasa shigowa suka yi bakinsu ďauke da sallama ko da Neneh ta ďago ta ga way’anda ke tafe sai da
zuciyarta ta yi wani irin faďuwa sannan ta dake ta cigaba da magana da Fadila sannan a hankali ta ďan
kallo su Liyanan tare da faďin “Baķin lahira maso gabas an iso kenan.” Ta faďa tare da cire eye glasses
ďinta ta na mai dallawa Hydar harara.




Shi kam bai wani kulata ba ya ďa rage tsayinsa tare da gaisheta.




“ Wallahi da wannan ya’r iskar gaisuwar mai sifirin da barina ka yi a hakan ba ka gaishe ni ba, Aa toh dan
da safe ake kalar wannan gaisuwar.” Neneh ta faďi hakan tare da ďan saci kallon Liyana.




Tsaki Hydar ya ja tare da zama a kusa da Nenehn ya na kallon Liyana da ta kasa ďago idanunta ta kalli ko
wannensu.




Ganin ta yi hanyar ďakinta na gidan Nenehn ne ya sanya sa ďago kansa tare da ďan kallon Nenehn.



“ Nifa yarinyar nan yanzu tsoro take bani, ooh ni Ajiddeh.” Ta ķarashe maganar ta na ďan kakkab’e
rigarta.




“ Neneh daman abin da ya kawo mu yau ďin ranar litinin zamu bar ķasar soo a saka mu a addua dan
Allah.” Ya yi maganar ya na ďan wasa da mayafin Nenehn.
“Idan ka yi wani abin kamar mai hankali, toh Allah ya tsare bara na zuba maka wani pepe soup ďin Abaji
da nayi.” Ta yi maganar tare da fara ķoķarin tashi.




“Nooo Neneh bar shi yanzu haka muna kan hanya ne zamu je gidan Mami Sannan mu biya gidan Ammi.”
Ya yi maganar ya na mai kallon diamond wristwatch ďin dake hannunsa.




Sannan ya ķara da faďin “ Neneh ki ce ta same ni a waje.”




“ Kai malam shiga ka tafi da ita, haka kawai na yi ta zabura cikin dare , wallahi ko bacci take kinkimarta
ka tafi da ita, hanyar lafiya a bita da shekara.” Ta yi maganar ta na mai pointing ķofar ďakin Liyanar.




Cikin takunsa na isa ya ķaraso har cikin ďakinta tare da kullo ķofar.



Zaune take a kan gadon ta jinginar da bayanta a fuskar gadon hannunta na rungume da pillow.




Ķarasa shigowa ya yi a hankali tare da ķarasowa inda take zaune ya na mai tallab’o fuskarta.



“What’s it for ?, mai sa kike saka kanki a damuwa bayan kin san mai ciki baya shiga kalar yanayin da kike
ķoķarin tursasawa kanki shigarsa?.” Ya yi maganar ya na mai shafa kanta.
“ Yaya Aliih .” Ta faďa a sanyaye.

“ Naam.”

“Did you love me.?” Ta yi maganar ta na kallon fuskarsa.




Shiru ya yi yana kokwanton amsar da zai ba ta sannan a hankali ta ķara faďin

32 / 39