Advertisements
Chapter 19 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 39

54K to 57K   out of 116.5K words

aiki, su kuma su Reeda da Sandy sun tafi siyayyan komawarsu.

Umma Mansura kuma da Ammi na tsaye cirko -cirko yayin da Neneh ta tafi raka su Mami domin tafiya
dan bata san wainar da ake toyawa ba.
Wani kalar mari Mama Fatuhn ta ɗauke ta da shi haɗe da faɗa mata suna ɓarauniya da kuma baƙaƙen
maganganu ita ma Yusrah suka haɗe suna ta zagin Liyanar, har Umma Mansura zata shigo Ammi ta yi
saurin girgiza mata kai.



Wani kalar mari Neneh da shigowarta kenan ta wankawa Mama Fatuhn tare da faɗin ''Ke kinsan waye
mahaifinta wurin kuɗi, kin san kakanta wurin kuɗi, haka zalika kin san mijin da ta aura ba kaɗan bane ba
a wurin kuɗi kowa anan zai shaida Alhaji Ahmed Qasim Kyari, ke da kallo ɗaya za'a miki a gane talauci
gaba da baya sha ³ , so so so mai kama da biri.''




Baƙin ciki ma ya hana Liyanar magana sannan a hankali kuma ta cire himar ɗinta haɗe da jacking ɗin
Mama Fatuhn ta kanainayeta kamar macijiya.

Kowa sai dukan hannun Liyana yake amma taƙi sakin Mama Fatuhn ta wani kalar shaƙe mata wuya.



Idanun Liyanar ya yi wani kalar ja.



Jikin Neneh wani kalar rawa yake dan ita a tunaninta Liyana jinnu ta tayar.




Duk da hammatan Mama Fatuhn ta hana ta sakat amma haka ta cigaba da naniƙe mata.



Hydar da zuwan sa gida kenan daga mayar da su Abbuh gida ya ji wayarsa na ringing wani kalar tsaki yaja
dan atunaninsa Amir ne ko Sultan hakan ya sa shi yaƙi ɗagawa, sai da ya ga wayan na ƙara sosai hakan ya
sa shi ɗaukan wayan amma sai kuma ya ga sunan Neneh ajiki.



Bayan ya ɗaga a kiɗime ta fara magana ''maza ka juyo ka dawo gidan nan, fitinar matarka zai sa ta yi
kisa.''
Kalmar kisan da yaji ne ya sa shi ajiye wayar haɗe da ɗaukan key ɗin motarsa ya fara tuƙi a million.



Ko lokacin da ya iso har an samu nasarar ɓanɓareta daga jikinta dan Mama Fatuh sai da ta suma dan
wahala.

Liyana na zaune sai huci take.

Abbhi ne ya zo ya zauna a kusa da ita wanda hakan yasa hawaye zuba daga cikin idanunta haɗe da
rungumesa.



''Abbhinaaa ni ka kira min lawyer na, wallahi sai na kai wannan maganar ƙara, mai zan yi da 250k, let her
check my account balance kuɗina 2 million za'a ƙara ya zama 20 million, Abbhi 250k is a chicken change
a wurina wallahi."



''Is Okay, duk wanda ya taɓa min ke nayi alƙawarin bi miki haƙƙin ki daman ko waye shi, i don't care
about the closeness, zata fuskanci hukunci, dai-dai gwargwadon abin da ta aikata miki kinji.''



Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta kalli wa'yanda ke wurin ba.......




To be countinue on Monday in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩
*Durrah Hydar.*✍️




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



Pending Amarya 34




''Abbhinaaa ni ka kira min lawyer na, wallahi sai na kai wannan maganar ƙara, mai zan yi da 250k, let her
check my account balance kuɗina 200k (last page na samu typing error ban lura ba). za'a ƙara ya zama
20 million, Abbhi 250k is a chicken change a wurina wallahi."



''Is Okay, duk wanda ya taɓa min ke nayi alƙawarin bi miki haƙƙin ki daman ko waye shi, i don't care
about the closeness, zata fuskanci hukunci, dai-dai gwargwadon abin da ta aikata miki kinji.''



Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta kalli wa'yanda ke wurin ba..........
Neneh da sai yanzu jininta ya ɗan sauko ce ta ce ''Alhamdulillah ga Hydar ɗin ma ya ƙaraso, sai ka zo ka
ɗauki wannan fitinanniyyar matar ta ka, wallahi tun da Ummaru ya mutu, Liyana ba ta bar shi ya ji daɗin
mutuwarsa ba kullum cikin fitina take, ai wannan ba Fatima ba ce ba fitina ce wallahi.'' ta ƙarashe
maganar tare da direwa Hydar ɗin trolly ɗinta.



Murmushi kawai ya yi sannan ya durƙusa ya na mai gaishar da Abbhi dake kusa da Liyanar.

Babu yabo babu fallasa ya amsa haɗe da tambayarsa ya aikin.



Bayan sun gama gaisawar ya ɗauki trolly ɗin haɗe da sawa acikin booth, ko da ya dawo cikin gidan
Neneh na ce mata ta tashi ta bi mijinta ƙi tayi, wai ita alankatafir ba zata bi shi ba.




Sai da Abbhi ya lallashe ta haɗe da tura mata 5 million a account ɗinta sannan ta tashi jiki a saɓule, haɗe
da bangaje Mama Fatuhn da ta miƙe daga sumanta da ta farfaɗo, duk a gaban Hydar ɗin.




Bayan motar Hydar ɗin taje ta zaga ta zauna duk su Abbhi da Neneh suna kallonta, shi ma Hydar ɗin bai
yi magana ba ya shige gaban motar haɗe da yi masa key.



Sai da suka fita daga unguwar sannan ya juyo da fuskarsa zuwa inda take zaune ta na hawaye.




Parker motar ya yi cikin muryarsa mai amo ya ce ''Uban waye driver ɗin ki?."

Ko kallonsa ba ta yi ba ta cigaba da goge hawayenta da hanky ɗin da Abbhi ya bata.



''Ba kya ji ne?."



''Leave me alone tun da dai da na shigo motar nan ban maka magana ba.''
''Zan bubbuge miki baki idan ki ƙara min magana without a bit of respect, dawo front sit kafin na ba ki
correct slaps.''

Tsaki ta daka sannan ta buɗe motar haɗe da shigewa front sit ɗin.



Shiru ne ya ratsa cikin motar sannan a hankali ya juyo da kansa ya kai duban sa gareta tare da faɗin
''Amma wallahi ba ki da kunya, yanzu saboda rashin ɗan ido da mahaifiyyar ki kike faɗa harda bangaza?,
see the way she's shouting time ɗin da muka shigo, wallahi ina ganinta na san ita ce mamanki, ashe dai
tsotsa ki kayi a nono.'' ya ƙarashe maganar haɗe da fuskewa kamar ba shi ya yi ba.




Juyowa ta yi ta kallesa haɗe da haɗiye miyau sannan ta ƙara mayar da kanta gefe.



''Mai sa ba za kiyi magana ba?, sosai that lady deserve to be your Mom, gaskiya aje ayi DNA TEST
because albasa ba tayo halin ruwa ba, Dan dai kar nayi saɓo da nace samun ki a matsayin ya' da Ammi ta
yi shi ne jarabtar ta.''



''Ya kuma ishe ka haka."



''Shut up while I'm talking joor, sai shegen iyayi, kamar kina da wani wayewa bayan kaff arewa babu mai
daƙiƙanci kamar ke.''



''Ka na kai ni bango fa?."



''Kin manta ƙarshen duniya nake kaiki.''



''Hmm.'' ta faɗa haɗe da cije lips ɗinta sannan ta cigaba da girgiza ƙafafunta, alamar masifa na cinta.
Daga ƙarshe shiru ne ya ratsa motar fuskar kowa a tamke barimma na Hydar.



Ko da suka isa gidanma komai neat kamar suna gidan, sai a lokacin take tunawa da wata Salimah.



Tsaki taja tare da hawa stairs ɗin ta bar shi a falon.



Remote ya ɗauka haɗe da furta ''Ƙazama.''




Liyana bayan ta ƙarasa ciki ma wayarta ta ɗauka haɗe da kiran Salimah akan ta dawo gidan.

Wanka ta shiga, ta daɗe a toilet ɗin sannan ta fito haɗe da goge jikinta da towel sannan ta fara shiryawa
cikin mini skirt da kuma wani polo top.



Polo ɗin babba ne sosai dan kar ya takurata hakan ya sa ta tattara shi haɗe da kulle top ɗin sai ya tsaya a
dai-dai cibiyarta. Wanda ya ƙara fito da farin shafaffen tummy ɗinta.



Slippers ta saka white color, haɗe da ɗaura normal hula akanta.



Shigar ya mugun yi mata kyau sosai, sannan ta cilla mint chewing gum ɗinta a bakinta da ya sha lipstick
mai ƙamshin pineapple.



Neman wuri ta yi ta kwanta ta na daddana wayar hannunta dan yunwa take ji amma ta rasa ta ya za ta
shiga kitchen ɗin ko noodles ta dafa.

Gashi har an fara kiran sallahr asar.



Ganin zamanta haka yunwa zai hallakata ya sa ta tashi daga kwancen da take haɗe da fita parlourn.
Ko da ta fita ma baya falon hakan ya saka ta shigo da ɗan gudunta cikin kitchen ɗin.



Tsaye ya ke ya ɗaura noodles a transparent glass pot ɗin dake kan standing gas, ya yi folding ɗin
hannunyensa ya ɗan jingina da kitchen island ya na mai ƙurawa tukunyar ido.




Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa, ba kayan safe bane ba ajikinsa, wannan karon combat ne ajikinsa sai t
shirt milk color a gaban rigar an rubuta _NEVER STOP ROMANCE._ da black ink.

Kallon fuskarsa ta yi tare da ɗan ƙure sa da manyan idanunta, gaskiya guy ɗin ya haɗu ya na da pointed
nose, ga gemunsa baƙi siɗik, idanunsa manya ne sosai, ga wani ɗan baƙi yale - yale dake wurin idanunsa
da suka ƙara masa kyau.



Lips ɗinsa pink ne sosai musamman na ƙasa.



''What are you staring at?."



''Mai za'a kalla anan ɗin?."



Tana faɗin haka ta buɗe fridge haɗe da ɗaukan hollandia strawberry yourghurt ɗinta.....




Na gaji mu ƙarasa gobe in shaa Allah please
To be countinue on tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩




*Durrah Hydar.*✍️




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️




*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



_Pending Amarya 35_




Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa, ba kayan safe bane ba ajikinsa, wannan karon combat ne ajikinsa sai t
shirt milk color a gaban rigar an rubuta _NEVER STOP ROMANCE._ da black ink.

Kallon fuskarsa ta yi tare da ɗan ƙure sa da manyan idanunta, gaskiya guy ɗin ya haɗu ya na da pointed
nose, ga gemunsa baƙi siɗik, idanunsa manya ne sosai, ga wani ɗan baƙi yale - yale dake wurin idanunsa
da suka ƙara masa kyau.



Lips ɗinsa pink ne sosai musamman na ƙasa.



''What are you staring at?."



''Mai za'a kalla anan ɗin?."
Tana faɗin haka ta buɗe fridge haɗe da ɗaukan hollandia strawberry yourghurt ɗinta.




''Leave my presence.'' ya faɗa cikin Muryarsa mai amo.

''Nifa da na shigo ban maka magana ba, yadda ka shigo girki nima girkin zan yi.''



''I said leave!." Ya ce tare da ƙafe ta da idanunsa.



''Buh I did nothing.''

Ta faɗa ta na marairaice face ɗinta dan ita yanzu har ga Allah guy ɗin burgeta yake.



Bai ƙara tanka mata ba ya nufi wurin dish rack haɗe da ɗaukan plate tare da juye noodles ɗin aciki.



Stool ɗin mini dinning table ɗin dake kitchen ɗin ya janyo haɗe da fara cin noodles ɗin sa hankali
kwance.



Bata ƙara kallonsa ba itama ta ɗaura na ta abincin, ta yi shi da romo sosai ga yaji da ta zuba mai shiga
maƙogwaro dan shi ma dakewa ya yi kawai ya zauna.

Juye noodles ɗin ta yi cikin ceremic plate da sai swimming suke kamar kifaye acikin red sea, sannan ta zo
ta wuce ta bayansa daman da hannu ɗaya ta riƙe plate ɗin ga shi ceremic ne ya ɗauki zafi sosai zafin ne
ya rinjaye hannunta hakan ya sa plate ɗin ya suɓce mata sai ga romon noodles da shi kansa plate da abin
da ya ke cikinsa a bayan Hydar.



Ƙara ta saki haɗe da kallonsa sosai, sai kuma ta ɗauke kanta haɗe da tsallake noodles ɗin da niyar fita
daga kitchen ɗin.




Cikin muryarsa mai amo da taushi tare da ɓacin rai ya ce ''You did it deliberately right?."



Juyowa ta yi ta ƙafe shi da idanunta sannan kuma ta cigaba da tafiya.



''Ko da wasa kika saki kika fita a kitchen ɗin nan sai jikin ki ya faɗa miki.''



''Toh ni mai na maka?."



''Gidanku kika min, za ki zo ki kwashe wannan abin da kika zubar ko saina illata ki da yamman nan.''



''Toh ba kai ne ka tsaya a hanya ba, shi yasa na na juye maka.'' ta ƙarashe maganar haɗe da yin ƙat - ƙat -
ƙat da chewing gum ɗin bakinta.



HYDAR da yajin ke ta masa nasiha a jiki ne ya ta shi daga zaunen da yake, tashin da ya yi ne ya sa ta arce
da mugun gudu tare da yin up stairs.




Wani kalar tsaki ya ja tare da yin ɓangarensa, cire kayan jikinsa ya yi da duk yaji ya gama zagaye ko wani
angles na bayansa.
Yana cire kayan ya na tsaki sannan cikin wata kaliyar shaƙaƙƙiyyar murya wadda ba ta fita sosai ya ce ''
Wallahi this girl no go make heaven at all, just take a look at.'' ya ƙarashe maganar ya na duba bayansa a
madubi haɗe da yin tsaki a karo na ba adadi.




Da ruwan sanyi ya yi wanka haɗe da kwanciyarsa because already ya yi sallar Asr.



For almost hour ya na kwance ba bacci ya ke ba, wayarsa da ke kusa da shi ta ɗauki ringing.

Ɗaga wayar ya yi sannan ya amsa sallamar da Amir ke yi masa.

''Man ga mu a street ɗin gidanka ni da Ummi.''

''Okay.''

kawai ya amsa a taƙaice.




Ta shi ya yi haɗe da zira jallabiyarsa maroon color haɗe da saka normal Muslim cap, tare da zira slippers
ɗinsa ya nufi downstairs.



As usual ko ina ƙamshi buh the living room is more neater than some hours ago.



Kamshi yake ji na fita daga kitchen ɗin, very classic aroma.

Just mind ɗinsa ya bashi cewa Salimah ce ta dawo.



Kiran sallar da ake a masallacin street ɗin ne ya sanya sa nufar compound ɗin ya yi alwala haɗe da fita
masallacin street ɗin.
Bayan ta shiga ɗakinta ma ranta fess, dan ita yanzu duk abin da zai janyo mata hankalinsa shi take so a
yanzu, dan all of the sudden son yaron nan ya gama da ita, she can feel it sosai a yanzun.




Wanka ta ƙara yi bayan shigarta ɗakin sannan ta ƙara shiryawa cikin shigarta na kullum wato palazzo
trousers da long sleeve shirt white color.




Zira slippers ɗinta kawai ta yi sannan ta fara gyara cikin gidan, sai da ko ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta
shiga kitchen ta fara ɗaura abinci mara nauyi.

Chips ne ta soya sannan ta haɗa da miyar Sauce, sannan ta nufi dinning room ta jera komai kan dinning
ɗin dan hakan nan kawai yau take son gyara gidan.




Ta na gama jerawa ta nufi hanyar ɗakinta ta ƙarayin wankan haɗe da yin sallar magrib sannan ta saka
wani Classic Egyptian abaya da ya gaji da haɗuwa black color.

Wanda ya ƙara haskaka fatar ta.




Lipstick mai ƙamshin pineapple ta shafa a saman tsararren laɓɓanta, sannan ta ɗaura mayafin rigar haɗe
da saka slippers tare da ɗaukan phones ɗinta ta nufi hanyar falo.
Zama ta yi haɗe da kunna tashar Aljazeera dan yanzu kewar gidan rasuwar ma take dan da yanzu suna ta
kwasar cacar baki da wannan lutiyar matar, mai siffar gorilla.




Sallamarsa ce ta katse mata tunaninta, wani jaka ne a hannunsa wanda dukkanin alamu sun nuna na
mace ne , macan ma Uwa.




''Welcome to my home Ummi.'' kalmar da ya sake faɗa ne bayan sallamar ya dawo da ita daga
tunaninta.



Muryar matar ne dake cike da sanyi ta ce ''Ma shaa Allah Son gida ya yi kyau sosai.''

Ɗago kanta ta yi suka haɗa ido da matar dake sanye da lifaya masu kyau, hakan ya sa ta tsugunnawa
haɗe da gaisheta cikin girmamawa haɗe da amsar jakar dake hannun Hydar ɗin.



Wani kalar harara da ya watsa mata ne ya sanya ta ja gefe haɗe da ƙara yiwa Ummin sannu da zuwa,
sannan ta nufi hanyar kitchen.




Cikin mintuna ƙalilan t a haɗa komai cikin wani resin tray sannan ta fito falon haɗe da ajiye tray ɗin
sannan ta ƙara musu sannu da zuwa.

Ummi kallonta kawai take haɗe da yi mata zallar murmushi.



Dan wannan karon harda Amir ta tarar a falon ya na ta washe mata baki.




''Follow me.'' shi ne abin da ya faɗa haɗe da yin upstairs.
A hankali itama ta bi shi, adaidai corridor ɗin ɗakinsa ya tsaya sannan ya ce '' mai Salimar ta dafa?."



''Salimah ba ta dawo ba ni na dafa.''

''Mai kika dafa ɗin?."

''Abinci mana.''



''Okay!, kin ga matar dake falo?.".....

Bai ƙarasa ba ta ce ''Na ganta mana.''



''Toh Maman Amir ce, also my Mom, Soo ki shiga kitchen ki dafa mata abinci, Heavy food nake nufi.''



''Buh ko thirty minutes ba'a yi ba da na gama wancan abincin and it's tastes good.''



''I don't care about the good, just do as I said.''

Har ya juya zai ta fi ta ce ''Ni ba zan iya ba, ko a gidanmu ba na girki, wannan ɗin ma dan kar na kashe
kaina da yunwa shiyasa nayi.'' ta ƙarashe maganar ta na wasa da diamond ring ɗin dake sanye da ring
finger ɗinta dan wayarta a falo ta bar shi.




''Ba shakka ai a maganar ki dan kin ce ba kya yi a gidan ku, kin ga yadda nake cikin fushin nan idan ba kiyi
abin da na saki ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daɗi.''



''Wai kai ba ka san wasa ba.'' ta faɗa haɗe da tattare abayarta tayi hanyar fita daga corridor ɗin.



Har ta sha kwana sannan ta kuma dawowa.



''Toh amma kuma babu nama.''
''Ke ba mace ba ce?."



''Sai aka ce na saida nama?......''




Kwana biyu kun ji ni shiru 🤭😩Temu ne ya tiso ni gaba.




*Durrah Hydar.*✍️
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."

*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️




*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



_Pending Amarya 36._
''Buh ko thirty minutes ba'a yi ba da na gama wancan abincin and it's tastes good.''



''I don't care about the good, just do as I said.''

Har ya juya zai ta fi ta ce ''Ni ba zan iya ba, ko a gidanmu ba na girki, wannan ɗin ma dan kar na kashe
kaina da yunwa shiyasa nayi.'' ta ƙarashe maganar ta na wasa da diamond ring ɗin dake sanye da ring
finger ɗinta dan wayarta a falo ta bar shi.




''Ba shakka ai a maganar ki dan kin ce ba kya yi a gidan ku, kin ga yadda nake cikin fushin nan idan ba kiyi
abin da na saki ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daɗi.''



''Wai kai ba ka san wasa ba.'' ta faɗa haɗe da tattare abayarta tayi hanyar fita daga corridor ɗin.



Har ta sha kwana sannan ta kuma dawowa.



''Toh amma kuma babu nama.''

''Ke ba mace ba ce?."



''Sai aka ce na saida nama?......''
Kallonta kawai yayi haɗe da ɗauke kansa tare da shigewa ɗakinsa dan canja kayan jikinsa.

Ko da ta fito matar da Amir na zaune kan cushion ɗin falon.

''Sannu Maa.''

''Yawwa sannu daughter, Allah ya miki albarka.''



Murmusawa Liya ta yi tare da faɗin ''Amin Maa.''



Ɗaukar wayarta ta yi daga wurin haɗe da shiga kitchen tsayuwar mota ta ji a compound ba ta damu da
ta leƙa da ta ga su waye ba, sai da ta ji sallamarsu Unaisah, Reedah, Sandy, da kuma Ily har da kuma
Salimah.

Ta dai ji suna gaisawa da su Amir sannan anyi directing ɗinsu zuwa wajen da da take.



''Yaya, ya kike naji wai inji Ammi ba ki da lafiya.''



''Don't worry yourself I'm okay ai yanzun.''



Idanunta ne suka sauka kan Salimah da take ta danne dariyarta, Liyana wani kallo ta wurga mata haɗi da
faɗin ''Almura, sai ki zo ki dafawa baƙi tuwo da miyar zogale, kina ganin na taho ba za

19 / 39