Advertisements
Chapter 35 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 39

102K to 105K   out of 116.5K words

ta aikata alfasha da wanin ka ba da za ka wuce a kaina.”
Liyana ta faďa tare da kallon Aliyun da tun da ta fara magana idanunsa yake a kanta.




Ganin yaķi ďauke idanunsa a kanta ne ga shi still bai daina tuķin ba ya sanya ta saurin faďin sorry tare da
ďauke fuskarta zuwa gefe ďaya, dan ita sai a lokacin taji nauyin maganar da ta faďa masa.
Tafiyar minutes arba’in ne ya kawo su Chaoyang district a babban shopping mall ďin SKP dake babban
birnin Beijing ďin.




Mall ďin ya mugun haďuwa dan kyaun mall ďin tsoro ya ďinga bata, amma ganin ransa a b’ace yake da
ita hakan ya sanyata kame kanta tare da binsa sau da ķafa, gudun tijararsa.




Ta yi siyayya sosai, sannan suka wuce wajen cin abincin dake wajen sai da suka ďan yi yawo kaďan
sannan suka dawo gidan.




Ko da suka dawo gidan ta na kwance a ķasa wajen da take a durķushe suka barta, fuskarta duk ya bushe
da hawaye, bacci take amma shigowarsu ya yi sanadiyyar buďe idanunta da suka yi luhu luhu saboda
kuka.




Har ya so ya wuceta, sai Kuma ya dawo a hankali tare da ďagota daga ķasan resin beige cream floor ďin
tare da ďaura ta a kan luxurious cushion ďin living room ďin tare da tapping fuskarta domin ta tashi.
Fashewa Liyana dake tsaye ta yi da kuka tare da haurawa sama da ķyar ta shige ďakinta ba nasa ba.




Babu abin da Marwa Ke nanatawa sai Aliyu ya yafe mata, Kar ya ga laifinta a abin da ta aikata.




Shi dai bai ce mata komai ba ya tattara ta ya shigar da ita ďakinta tare da ja mata ķofar ďakinta ya wuce
nasa.




Ko da ya shigo ďakin nasa da bai ganta ba, bai wani damu kansa ba ya shige toilet tare da yin wanka
sannan ya shirya cikin kayan baccinsa tare da sanya sleep mask ďinsa.




Har ya kwanta yaji an banko ķofar tare da ďage duvet ďin da yake kwance aciki ta na mai rungume sa a
jikinta.
Washegari 🥰🫩




Da sassafe ta tashi tare da fara haďa kayan baby a cikin wani sabon trolly da ta siya a jiyan.



Kayan triplet ďin Kala uku ta zuba a ciki dan a lokacinma kiran sallahn farko a ka yi a wani ķaramin
masallacin dake kusa da su.




Ko da Aliyu ya tashi da zummar performing ablution har ta gama haďa kayan har Wanda za ta saka.




Kallon gefen ido ta bisa da shi sannan ta cigaba da arrangements ďinta.




Sai da ya yi wanka sannan ya yi alwala ya fito tare da nufar masallaci, ita ma shiga ta yi tare da yin
wankan haďe da alwala, ta daďe a toilet ďin sannan ta fito.




Ko da ta idar da sallar azkar ta yi tare da unveil ďin kanta sannan ta ďauko UV/LED nail lamp tare da
ďauko sauran equipment ďin da take da buķata, ta fara sanya nails a hannunta tare da painting nasu
black color, sannan ta jona LED ďin ta saka hannunta saboda ya yi ķarķo sosai.
Ko da ya dawo har ta shirya cikin dakakken half kimono da inner ďinsa, sai wani dakakken palazzo da ya
yi wa shigarta wani kalar mugun kyau, kimono ďin kamar da organza yard a ka yisa , kana ganin yard ďin
zaka san is not an ordinary organza yarda wannan mai tsada ne, ya na da faďi sosai sannan kuma ash
color ne sai wani manyan ķyalķyalli black color da aka zuba a jiki.




Palazzo ďin is black, sai veil ďin ma black color ne mai kyau ba kalar wanda take sawa a Nigeria ba.




Shigar ya mugun yi mata kyau barimma yadda cikinta ya turo sosai kamar zai faďo.




Around 7 O clock ya shigo cikin ďakin hannunsa riķe da coffee mug ya na ďan sipping sama-sama.




“Good morning Ya Alih, ka shirya please ka kaini hospital na matsu da yawa naga Babies ďina.” Ta
ķarashe maganar tare da kamo hannunsa.




Cikin murya mai ďan nuna kulawa da damuwa gareta ya ce “And ba kya jin zafin komai.?”
“Wallahi babu abin da nake ji, duk ķarya ne wannan cewa da ake yin haihuwa da zafi, because I can’t
figure out menene zafin da ake faďa , maganar gaskiya.” Ta ķarashe maganar tare da amsar mug ďin
hannunsa ta na mai kafa baki.




“Buh lokacin da Marwa ta haihu she even fainted har sau biyu and you naga na ki da ban yake.”



Sai da ta cire mug ďin daga hannunta sannan ta ce “She’s Marwa and I’m Liyana, when I’m broke I open
my wallet or call my Dad not my Legs, soo akwai banbanci.”




Bai ce mata komai ba ya wuce toilet tare da watsa ruwa sannan ya fito, ta na tsaye riķe da trollynta a
ķofar ďakin hannunta riķe da ķugunta alamun dai jiransa take.




Clotheset ďinsa ya b’uďe tare da ďauko wani wani black jallabiya da hulan Ana Muslim black color tare
da zira slippers ďinsa sannan ya fito daga ďakin clotheset ďin nasu.




Trollyn hannunta ya amsa tare da wucewa ya shige gaba, sannan ita ma ta bi shi a baya.




Ba su same ta ba a falon, hakan ya sanya su wucewa ba tare da wani daga cikinsu ya bi ta kan halin da
take ciki ba.
Tun a hanya take ta ďokin zuwa babban hospital ďin da tun dawowarsu nan ďin take zuwa awo anan ďin.




Cikin mintuna ķalilan suka iso asibitin inda direct Office ďin Doctor Zhu suka nufa.




Ta yi farin cikin ganin Aliyu da matarsa sosai dan da ita da shi akwai amana dan ita ce ta amshi haihuwar
Marwa.




“OMG, perfect couples.” Doctor Zhu ta faďa tare da zama akan kujerar office ďin.



Murmusawa Liyana ta yi tare da faďin “Good morning Maa.”

“Morning Mrs Aliyu, what’s wrong?, any problem?,naga kun zo hospital da sassafe haka.?”




A hankali Liyana ta ďago tare da faďin “ kin manta yau kika ce EDD ďina zai kama?, shiyasa na zo da kaina
kawai na haihu ďin.” Ta ķarashe maganar a sakarce.
Murmushi sosai Doctor Zhu ta yi , ďagowa liyana ta yi tare da faďin “ What’s Funny?.” Ta faďa tare da
ķure Doctor Zhu da idanu.




Ķara murmusawa Doctor Zhu ta yi tare da faďin “ Nothing my dear, kina jin ciwo ko wani discomfort
ne.?” A hankali ta ďago da kanta tare da girgiza shi alamun A’a.




Sai da Doctor Zhu ta ďan ķura mata ido sannan tace “ Okay kwanta A kan waccan gadon.” Ta faďa tare
da mata pointing wani ďan gado da yake gefensu.




A hankali ta kwanta a kan gadon ta na mai kallon Aliyun.




Doctor Zhu ta kusa mintuna biyar ta na dube dubenta sannan kuma ta ce “ Sauko.” Ta ķarashe maganar
tare da zama a kan kujerarta.
Marairaice face ďinta ta yi tare da faďin “Ni na zaci ma da na kwanta cewa zaki yi na haihu.” Ta yi
maganar a hankali.




“Noo sauko ki zauna.” Doctor Zhu ta faďa fuskarta ďauke da dariya.




A hankali ta sauko yadda doctor ďin ta faďa tare da zama a kan kujerar dake facing na Aliyu.




Cikin muryarsa mai amo ya ce “ ni naga yawancin mata yadda suke Shan wahala a labour, and da na
tambayeta ta ce nata is different, ni kuma a tunanina ko dan triplet ne shiyasa ba ta ji ciwon komai ba.”
Aliyu ya ķarasa maganar tare da kamo hannunta.




“Yeah haihuwan triplets is different sosai, abin da ya sa ma ba za a mata sugery ba saboda kwanciyar
yaran is very okay, yanzu abin da ya kamata ku koma gida, nan da one or two weeks zan zo har gida da
kaina, sannan yadda na duba yanzu ki ďinga cin dates da olive da shi Kansa olive oil ďin morning and
Night.” Doctor ta faďa tare da ajiye eye glasses ďinta akan table.



Sallama suka yi da Doctor Zhu Liya jiki babu ķwari tabi bayan Aliyu suka fita daga hospital ďin.




Wani wajen siyar da imported foods suka nufa tare da siyan olive ďin da Dates sannan suka dawo gida….
*THE REGRET*🥺




*PENDING AMARYA CE•*
*J•A•W*•👊🏿




THE NOBLE WRITERS TEAM



up we go🥰




(Our strength lies in dedication).




Pending Amarya59📓
A tear that falls from the eye due to fear of a sin and REGRET for it is more beloved to Allah than
mountains of gold spent in his part.




***************><




Wani wajen siyar da imported foods suka nufa tare da siyan olive ďin da Dates sannan suka dawo gida….




•••••••••••••••••••
Gida Nigeria kam an sanya ranar Sultan da Ilham Wanda bikinsu saura 2mons.




Kowa na gudanar da rayuwarsa cikin farinciki da kuma ķaunar juna.




B’angaren Ammie da Yayanta kam Soyyaya sai abin da ya yi gaba dan ba kullum ma yake fita office ba.
ALIYU dai tun ranar da suka rabu da Amir a ranar da suka zo gidan su ya ga Marwa har sannan ba su ķara
waya ba sai dai chats da shi ma sama sama kamar shi ya aike su su rabu.




Aunty Rufaidah tamu kam tun da ta bar gidan Nabil flight ta bi ta koma can Abuja gidan Yayarta
Nafeesat, dan sosai take Dana sanin duk wasu abubuwan da ta aikata.




Bangarensu Reedah da Rashanda komai ya zama steady dan gabaďayansu sun dawo Nigeria da zama
sakamakon gama makarantarsu da suka yi , hakan ya sanya Ummah Mansura dawo dasu gaban Neneh
inda ita ma Ily ta dawo gidan.
Sultan kam duk wasu hopes ďinsa suna wajen Ilham, dan a yanzu soyayyar da yake mata ya linka Wanda
yayi wa yayarta a baya.




••••••••••••
Koda suka dawo gida a living room suka yada zango, dan ita a yanzun ma haushin kanta kawai take ji,
Aliyun ma ji take kamar ta maresa.




A hankali ta buďe ķofar ďakin jikinta sanye da wani blazer purple color sai wani blue black jeans sai
turban light purple dake kanta da kuma wani heels shi ma light purple.




Shigar ya yi mata masifar kyau, a hankali ta ķarasa rufe ķofar, sannan ta tako har inda suke zaune .
A zaune suke su biyun suna facing junansu Aliyu na riķe da olive container da spoon ya na bata, a yayin
da wasu cartons Ke ajiye a ķasa Wanda Ke nuna alamun na olive ďinne da Dabino.




“Papa Good Morning.” Ta faďa da muryarta da ya ďan fara dishewa.




A hankali Aliyu ya ďago tare da amsa gaisuwar nata, sannan cikin sassanyar muryarta ta ce “Please Papa
if you don’t mind, zan iya samun aron motarka zan tafi lectures.” Ta faďa ta na mai ďan buga ķafarta da
jakar hannunta.
“ Ba sai kin yi mana tsaye ba a kai, ga key din can ki dauka sannan ki daina saka min wando a cikin gida
tun da ba club za ki je ba.” Liyana ta faďa tare da dalla mata harara.




D’aukan key ďin tayi tare da Jan wani kalar tsaki sannan ta banko ķofar falon.




Baki sake Liyana ta bita da idanu Sannan ta dawo da kallonta kan Aliyun da yake ta ķyalķyala dariya ya na
kallonta tare da nunata da yatsa.




“What’s funny ķanwarka ta min rashin kunya, and you’re laughing, are you okay?.” Ta ķarashe maganar
tare da dukansa da pillow.




“Sorry dear, the way da ta miki tsaki ne ya bani dariya.” Yayi maganar tare da ķara ķyalķyalewa da
dariya.
Tsaki taja tare da dungure masa kai sannan ta ďauki wani container dake cike da dabino ta nufi upstairs
da su.




Tsagaita dariyarsa ya yi tare da shiga kitchen ya haďa coffee sannan ya ďauki ďayar key ďin motarsa ķirar
Zakir ya nufi H&k ventures.




Liyana kam telegram ta hau tare da fara chatting dasu cousins ďinta inda har suke sakar da ita bikin
Assultanah da Amir da kuma na Sultan da Ily da duk ba a sanar da su ba.
Sai around ten o clock ya dawo gidan, a yadda ya bar gidan a hakan ya tarar da shi babu wani chanji da
aka samu.




Direct ďakinsa ya shiga da ledojin hannunsa, a kwance ya tarar da ita jikinta sanye da wasu kayan bacci
masu ďan taushi da nauyi.




Hannunta na riķe da remote Wanda da alamun kallo take.




A hankali ya ķaraso inda take fuskarta a ďaure babu alamun rahama.
Yaye bargon da take ciki yayi tare da tallab’o fuskarta Buh still ko kallonsa ba tayi ba.




Bai mata magana ba shi ma ya ciro wani milky donut daga wani kwali mai kyau tare da wani yoghurt ya
fara sha tare da donut dinsa .




Tun ya na sha ta na ďauke kanta har ta fakaici idanunsa tare da warce Yili yoghurt ďin hannunsa tare da
donut ďin tana mai ķyalķyalcewa da dariya.




Kallonta kawai yayi Sannan ya juyar da kansa ya na mai canza tashar zuwa Spoti Tv.
Wayarsa ce ta ďauki ring hakan ya sa shi kai dubansa kan bed sides inda ya ajiye wayoyin nasa.




Ganin number dake kiransa ne ya sanyata saurin rarrafowa daga ķarshen gadon da take tare da ďaukan
wayan da sauri.




Da kallo ya bita sannan ya ci gaba da abin da yake.
“Hello Papa, i won’t be coming back home today, saboda birthday party ďin zola, and bayan nan zamu je
Maldives a can za ayi sauran party ďin.” Daga can b’angaren Marwa ta faďa ta na mai shafa lips scrub a
leb’enta.




Warce wayar Aliyu ya yi daga hannunta sannan ya fara magana a fusace “Duk inda kike you better come
back to this house kafin jikin ki ya yi tsami, who’s Zola?.” Ya ķarashe maganar tare da tambayarta a
zafafe.




“Baddie Zola, Our friend back then, ko ka manta?, Izabela Lewandowska that Lady from Poland.” Tayi
maganar trying to reminds him her.




“And I said you should come back to this house na baki nan da minutes talatin or else ki zauna a nan har
ki gama abin da ya kawo ki.” Ya na gama faďin hakan ya katse wayarsa ba tare da ya tsaya jin abin da
zata faďa masa ba.
Har ķarfe ďayan dare babu Marwa babu dalilinta, Liyana da taga ba zata iya ganin ķwaķwaf ba,



ta samu waje ta baje a kan gadon wanda a take bacci ya kwasheta.




A take ya kira Amir ya sanar da shi abin da yake faruwa inda ya basa go ahead da da zarar ta dawo ya ci
ubanta ya ajiye ragowa, sannan Kar da ya ķara kiranta.




Daga haka suka ďan tab’a hira inda Amir Ke sanar masa aurensa da Sultana har da na Sultan da Ilham.




Ya yi mamaki sosai da jin hakan, dan shi dai ya san kusan kullum ya na waya da su Mami har da su Ammi
da Sultana da ma Ilham ďin Buh none of them even try to do sub’utar baki su gaya musu.
Ko da suka gama wayar bai koma bacci ba alwala yayi ya tada sallah .




Ko da ya idar ďinma bai kwanta ba addua ya yi ta yi na neman tsari daga kowani sharri.




Sai after sallar asuba sannan ya kwanta domin yau ba ya jin zai iya zuwa gym.




+++++After A Week ++++++
Sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin aminci da ķaunar juna.




Sannan har yau Marwa ba ta dawo gidan ba ita ma kuma ba ta tambayesa ba dan ita ba ta son zamanta
daman a cikin gidan.
Zaune suke a living room ya na tufke mata kanta dake tsife.




A hankali Marwa ta turo ķofar parlourn jikinta sanye da checkered jacket da jeans trousers.




Bata kalli inda suke zaune ba ta ci gaba da tafiyanta towards her room.
cikin muryarsa mai amo Wanda ke jagula lissafinta ya ce “ Ki koma daga inda kika fito, there’s no way da
za ki zauna min acikin gida, how dare you da zan kafa miki doka ki ķi bi kina zaman gidana.” Ya ķarashe
maganar a hasale.




“Buh ai na faďa maka birthday zanje, sannan naje inda zani dan haka wallahi babu inda zan je.” Ta
ķarashe maganar tare da ďaukan ķaramin trolly ďin da za ta shigar da shi cikin ďakinta.




“Ahh okay lalacewar naki har ya kai da zan miki magana ki ķi bi kenan abi?, toh wallahi sai kin bar min
gidana.”




“Lalacewar tawa kuma kaine sanadiyyar ta ai, kuma wallahi ban yafe ba, abin da kamin sai anyi ma
y’ay’anka mark my words.” Marwa ta faďa tare da kokarin bangaje Aliyun.
Jin kalmar Marwa na karshe ya sanyata sakin Wani kalar ķara tare da zubewa a wajen wani ruwa na bin
ta ķafarta.




Ķara ruďewa tayi dan ganin ruwan ya mugun tayar mata da hankali.




A ruďe Marwa da Aliyun suka juyo zuwa wajen da take, kusan a tare shi da ita suka ķarasa wajen
Liyanar.




Doke hannunta da ta riķe mata ķugunta da shi liyana ta yi tare da Fashewa da kuka ta na mai miķowa
Aliyu hannu.
Baya ta yi kamar za ta faďi ya yi saurin ka mota tare da ďaukanta, ya na mai zaunar da ita a kan cushion.




Wani kalar gumi ke keto mata, sam ta ma kasa masa magana.




“Marwa get me some water.” Ya faďa a ďan razane.




“Let’s take her to the hospital, she’s in pain.” Ta faďa a sanyaye dan Marwa duk rashin imaninta tana
tsoron ace mutum ba shi da lafiya.




“I’m not asking for your opinion, just get me what I asked for .” Ya faďa a ruďe.
Wani bell ya danna wanda a cikin seconds talatin yan aikin gidan suka fara shigowa cikinsu har da
wancan Chinese lady ďin dake gyara masa ďakinsa.




Su kansu sun yi mamakin ganin Boss ya kira su , because daga sun gama aikinsu ba sa sake shigowa
gidan dan su apartment dinsu a wajen main building din yake.




Ya ma rasa mai zai yi, koda aka ďauko wayar nasa ma manta sunan da ya yi saving Doctor Zhu da shi ya
yi.




A zafafe ya ķara danna bell ďin jikinsu na rawa suka fice.
Da sauri ya ďauki car key ďinsa tare da sunkutanta ya nufi bayan mota da ita.




“ Wayyo Allah na Ammi nah ki taimaka ki yafe min, wallahi ba zan ķara ba Ya, Innalillahi wa inna ilaihir
rajiun, mutuwa zan yi , Summa sabila yassara, fa inna ma’al usri Yusrah, Ya Alih ka fadawa Ammi nah
Abbhina Ilham dina su yafe min, na san mutuwa zan yi, kai ma ka yafe min.”




Ta ķarashe maganar ta na damķan kujerar motar.
A galabaice a ka ķarasa labour room da ita, hankalin Aliyu idan ya yi dubu toh ya tashi, dan ya kasa
lissafin komai a brain dinsa.




Doctor Zhu ce tazo da dan sauri ta shige cikin labour room ďin ba tare da ta jira jin abin da Hydar ďin zai
fada ba.




•••••••••••
Bai fito da wayoyinsa ba ballantana ya Kira gida a tashi da addua dan Allah na gani a lamarin Liyana ya
sare ba kaďan ba.




Har ķarfe shida na yamma babu wani labari game da Liyana labour kawai take.




Idan banda sallah babu abin da ke tashinsa a wajen da yake.




Ķarfe bakwai daidai na yamma ta sullub’o yaranta uku , wanda ko wannen su tazarar five minutes ne a
tsakaninsu.
“Congratulations Mr. Alih, Allah has blessed you with three beautiful little Queens of Jannah, Allah ya
taya ku

35 / 39