Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
ya yi gyaran murya tare da faɗin ''dama tashi kayi ka shirya da ya fiye maka wannan fake
emotions ɗin naka dan class mates ɗinmu babu wanda ban gayyato ba.''
Sultan ya amshe da faɗin ''Ko kai ma ka faɗa Amir, da ni ne ake min maganar anyi min mata ajiye wadda
muke soyayya da ita zan yi a gefe in amsa hannu bibbiyu daga ƙarshe na ƙaro ta ana biyu.''
''Shege.'' Amir ya faɗa da ɗan barkwanci.
Bai ma kallesu ba balle su saka ran amsa ya cigaba da danna wayarsa.
Ɓangaren Amarya Liyana kuwa tun da taji an ɗaura zuciyarta ke duka uku³ ta rasa yadda zata yi.
Kuka zata yi ko dariya bata sani ba.
Wani mahaukacin shadda da ya lalace da ɗinki ta saka wanda alamun kayan ma kaɗai kasan ba ƙaramin
shadda bane sannan ba ƙaramin tailor ne ya ɗinka sa ba.
Ɗinkin yafi kama da na ƙasar Gambia dan aɗinke yake a cikin lefenta.
Shaddar milk color ne sai aka yi design da coffee color thread, sai aka yi mai ruwan stones, sai kuma
wani coffee heels dan sam bata sa ka zani ba kamar sauran amare.
Duk da ba kwalliya tayi ba, amma wannan hasken na amare ya karaɗe fuskarta, duk ɗakinta ayarin
cousins ne and all of them are very classy.
Rashanda da Classy Reeda da Unaisa da Ilham sun saka kaya kala ɗaya har da Lily.
Farinciki a wurin Ammi baya misaltuwa, ta aurar da headache ɗinta a rayuwa.
Rufaidhat kam ranta a ɓace yake yadda ta ga kowa ya yi banza da ita.
Kamar mayu sai da suka je shan ice cream ɗin, dan Liyana ma bata ci komai ba sai ice cream ɗin data
sha.
Misalin ƙarfe shida na yamma Aka yi mata wanka da ruwan lalle sai da aka ƙara dafa ta, sannan aka sa
mata wani lifaya purple color da ratsin white color aka saka mata sai da aka turara mata jiki gaba ɗaya
sannan aka kaita wurin Jiddah ya mata Nasiha, ita ma Neneh aka kai ta ta mata tare da faɗin ''Ni dai
Fatima aure ne an riga an miki rashin kunya, da waƙe -waƙe sai ki ajiye tun da dai Davido ba ƙanin ubanki
ba ne ba, in kunne ya ji jiki ya tsira daga azabar Allah, akai ta wurin Salamatu ta ja mata Aya.''
Sai da Liyana ta ɗage abin lifayar ta dallawa Nenehn harara, wadda ta cigaba da surutun ta.
Daman ta saba kiran Ammi da Salamatuh that's why kawai wurin Ammi aka kai Liyanar, ita dai Addu'a ta
mata tare da mata fatan samun daidaito a rayuwarta ba ki ɗaya.
Daga haka aka kaita wurin Abbhi.
Rungume shi ta yi ta na kuka shima bai san lokacin da ya fashe da kukan ba dan har ga Allah ba zai iya
zama bai ga ɗiyarsa ba ace har sai wani ya bata izni yanzu akansa.
''Don't worry dear every friday zan ɗinga zuwa ganin ki okay?." Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan aka wuce
da ita gidan su Mami sai da suka samu tarba mai kyau, itama Mamin ta mata nasiha sannan aka ɗauki
hanyar sharaɗa da ita dan acan gidan Hydar ɗin yake.
Duk ƙawayenta da kuma ƴan uwanta na jiki sai bayan one week zasu koma gidan Neneh dan al'adar su
ce hakan, wanda a yaren shuwa Arabi muke kiransa da Sabbayats.
Ko kaɗan bata daina kukan ba haka tai ta kukanta su Reeda da Unaisa na rarrashinta.
A haka har ta daina kukan.
Daga ƙarshe ma dai ta ware suka cigaba da hira tun suna jiran angwaye har suka kwanta bacci.
A haka har kwanaki bakwan da zasu yi ya ƙare.
Ranar da zasu ta fi babu kalar magiyyar da Liyana bata musu ba har diamond ɗaya ta ce zata basu da
dubu ɗari biyar su ƙara sati ɗaya amma suka ce su basu san zancen ba gida zasu koma.
Itama Ilham ta ce zasu koma makaranta Lily kam ita ma preparations tace zata koma ga fara dan next
week zasu koma.
Ta sha kuka sosai ahaka har suka gama shiri suka kama hanya suka ɓacewa ganinta.
Gidan wani kalar faɗi ne da shi na ban mamaki, dan gidane babba sosai, readers gidan Liyana sai a novel
babu shi a reality, because ya gama haɗuwa komai na gidan looks luxurious.
Ga marble tiles kaca -kaca, gidan dai soo Ma sha Allah.
Haka ta yi ta rayuwarta ita kaɗai ta girka abin da take so taci.
Shi ma Abbhi yayi ƙokari sosai wurin haɗa mata gara domin har da Hollandia strawberry ya sa mata her
favorite drink.
Kullum tana online ko Sultan ya mata magana bata basa amsa dan bata canza layinta ba.
Monday Morning 🫂
Yau ta kasance Monday yau kuma za'a koma makaranta tun safe ta shirya cikin shigarta na wani black
abaya mai mugun kyau da tsada sannan ta sanya Gucci flat shoes ɗinta black color haɗe da saka wani
ziconic leg chain mai mugun ƙyalli da stones ajiki green and red.
Ta yi mugun kyau sosai sam sam babu wani locality ajikin Liyana komai na ta mai kyau ne.
A hankali ta sanya hannu tare da ɗaukan one in town wayarta, da ta fara amfani da shi last week her
pink iPhone , sai da ta gama pictures sannan ta shiga dakakkiyar motarta mai numfashi da Abbhi ya siya
mata na gudumowar bikinta.
A hankali ta nufi wurin jeep ɗin nata da yake Black color mai ƙirar G_Box, ta masa wuta tare da barin
cikin gidan gaba ɗaya.
Wasa wasa har ta kai one month a gidan bata taɓa ganin wanda ta aura ba
Zata ji fitarsa da dawowarsa duk a kunnenta amma basu taɓa clashing ba ko da wasa.
Yau dai basu da lectures, wani kalar yunwa ke nuƙurƙusan cikinta dan haka ta fito dan nemawa kanta
abin da zata sa ma cikin ta.
Misalin ƙarfe biyu ne na rana, wani palazzo trousers ne mai kyau da kuma faɗi ajikin ta sai crop top
black color mai ɓulallen ƙirji.
Ko da ta shiga kitchen tea ta haɗa tare da futowa living room ɗin, ganin waƴanda ke falon ba zato babu
tsammani mug ɗin tea ɗin da yake hannunta ya faɗi a ƙasa ji kake tassss...........
Let's meet tomorrow in page 26 muji yadda zata kaya.
Pending Amarya ce ✍️
THE REGRET
(Dana sani).
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
The Noble Writters 🦚
Dedication is Our Strong 🤝
_ Pending Amarya 26_
Ko da ta shiga kitchen tea ta haɗa tare da futowa living room ɗin, ganin waƴanda ke falon ba zato babu
tsammani mug ɗin tea ɗin da yake hannunta ya faɗi a ƙasa ji kake tassss...........
Cikin muryarta mai sanyi da kuma nuna tsantsar farincikin da take ciki ta ce " Ilham!, Farida, Rashidat,."
ai da gudu ta ƙarasa wurinsu tare da rungumesu gaba ɗaya, tare da fashewa da kuka.
Rungumeta suka yi tare da sakin ta Reeda ta ce " ashe za ki iya missing namu har haka."
Tsaki Liyana taja tare da faɗin kaɗaici ne kawai buh na rasa wa zan yi missing sai ku? Is impossible ai, dan
Allah ku tashi ku dafa min abinci am starving." Rashanda ce ta dalla mata harara tare da faɗin "Ily kaɗai
kika girma anan ba mu ba."
"Ni na ce ke ne?."
"Kin ma isa."
Reeda dake zaune cikin wani paper less mai mugun kyau ce ta ce "zaku fara ko?."
A haka suka yi ta hira har sai yamma liƙis sannan suka kama hanyar zuwa gidan Neneh shima da ƙyar
sannan ta barsu suka tafi.
Ɓangaren Hydar kam bai wani damu da ya ga what soo called wife ɗin da ake kirarin an masa ba shi dai
kawai yana rayuwarsa, daga gidan Mami sai gidansu Amir da kullum cikin tsokanar sa yake da yayi fresh
menene sirrin?.
Baya tanka masa balle ya sa ran answer.
Almost a month da bikinsu buh he didn't even bother ya ga wacece ko chanyar corridor ɗinta baya bi
balle idonsa ya kai ƙofar da yake sa ran nata ne.
Yau tun safe ta shirya cikin wani up and down masu kyau sai tayi ɗaurinta na matar minister sannan ta
saka gucci heels da kuma bag sai wani passion eye wear masu kyau, yau data yi waya da Neneh tace
mata zata aiko mata Salimah tun da ba Salimah kaɗai bace ba ƴar aikin Nenehn.
Hollandia strawberry kawai ta kwankwaɗe tare da fita daga cikin flat ɗin, ta shige mota haɗe da zuge
glasses ɗin motar ƙasa dan zata yiwa mai guard magana.
Bayan ta shige Jeep ɗin nata haɗe da sanya seat belt tare da yiwa motar key, kafin ta ƙaraso ma har ya
buɗe gate ɗin.
Parker motar nata ta yi tare da yiwa mai guard ɗin magana, cikin muryarta mai sanyi ta ce " Malam mai
aiki zata zo da anjima, ka buɗe mata gate, am I clear?, and......."
Bata kai ga ƙarasawa ba wani mota ƙirar Lexus RX ta kutso kai saura kaɗan motar ta shafi ta nata.
Bayan motar ta wuce sai da ta futo da kanta waje ta dallawa motar harara haɗe da kallon mai gadi tace "
da maƙota a gidan nan ne?." "Hajiya ke kaɗai ce ai da Alhaji a gidan nan, kuma ina fatan har abada daga
ke ba ƙari."
" Idan ya ƙaro sai ka fitar da ita ai, kaji bayanin dana maka?."
" Eh hajiya Allah ya bada sa'a."
" Tun da ance maka gasar kyau zanje ai."
" Allah ya ba ki haƙuri."
" Haƙuri kaya ne." Daga haka taja motar zuwa school.
Ko bayan ya dawo daga gym daya shigo gidan, idanunsa suka gane masa yarinyar da take cikin motar he
was shocked to see her for the fourth time, buh how comes?, mai ya kawo ta gidan sa wa tazo nema? Ba
dai ƙawar wannan j'airar aka aura ma sa ba.
Kwata -kwata zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa wani kalar tunani suke basa, ga zuciyarsa wani kalar tafarfasa
yake, tunaninsa da hankalinsa sunƙi ba shi nutsuwa, haka nan kawai yaji ya tsinci kansa da shiga
ɗakinta."
A hankali ya tura ƙofar ɗakin tare da shiga ciki, wani ƙamshin turare ne ya daki hancinsa a take ya ɗan
lumshe idanunsa.
Ɗakin kaca - kaca yake, kwalin pizza na kan gado, sai kwalin hollandia, ga wani ɗan container kamar na
milky donut shima akan gadon, sai kuma wani bra dake yashe a ƙasa wanda tun shigowarsa ɗakin shi ne
abin da ya fara masa sallama, duk ɗakin kaca -kaca.
" Daman nasan tsaftar biri ne, just look at."
Ji yayi kamar amai zai taso masa har zai fita daga ɗakin, sai a hankali idanunsa suka sauka kan wani
picture dake bedsides na Ilham, jalbab ɗin himar ke kanta har ƙasa, tayi folding hannunta tana murmushi
dimple ɗinta ya loɓa.
Sai kuma ɗayan su biyu ne ita da Liyana, still dai hijab ne ajikinta, ita kuma Liyana palazzo trousers da
corset top tayi alamun kiss da bakinta.
A hankali ya ijiye frames ɗin tare da faɗin "might be the one in hijab in shaa Allah."
Daga haka ya fita daga ɗakin.
Ko a mota sai da ta kira Salimah akan lallai idan taje gidan ta gyara mata ɗakin dan jinta take wani iri da
ta bar ɗakinta kaca -kaca, dan abin da bata saba da shi ba kenan."
A school ma lecture ta ɗau daɗi, bayan sun fito sai da ta biya gidan Lily ta yi rayuwarta sannan ta kamo
hanyar gidanta.
Gidan sai ƙamshi yake dan Salimah sai da ta mata girki ta gyara gidan tsaf ta saka mata turaren wuta.
"Aunty Liyana sannu da zuwa." " Yawwa Salima, mai kika dafa?." " Cous cous ne da sauce."
" Serve me please."
"Okay Aunty."
Daga haka ta shiga kitchen ta zubo mata abincin, sai da taci sannan ta haura sama, shima fess ko ina.
Kayan bacci ta saka tare da feshe jikinta da turare masu tsadar gaske, sannan ta fito dan taya Salimah
hira.
Sai kusan Arround 10 O'clock sannan ta haura sama ita ma Salima ta shige ɗakinta na downstairs.
Arround twelve O clock ta tashi tana jin ƙishin ruwa wanda sai da ƙyar ta sauko downstairs dan tsoron
gidan take ji, kitchen ɗin ta shige tare da kunna switch ɗin kitchen ɗin, wanda a take idanunta suka gane
mata bayan wani faffaɗen mutum mai tsayi, jikinsa sanye da pyjamas white color wanda alamu sun nuna
tea yake haɗawa.
Wani kalar razananniyyar ƙara ta saki dan a tunanin ta aljani ne ko ɓarawo.(Ɓarawo da haɗa tea😂).
Shi ma a kiɗime ya juyo dan ƙarar har kwanyar kansa ta ratsa, a hankali ya sauke idanunsa akan............
Let's meet tomorrow
Thanks for reading 🤗🦋🤌
THE REGRET
(Dana sani).
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
The Noble Writters 🦚
Dedication is Our Strong 🤝
_ Pending Amarya 27_
Arround one O clock ta tashi tana jin ƙishin ruwa wanda sai da ƙyar ta sauko downstairs dan tsoron
gidan take ji, kitchen ɗin ta shige tare da kunna switch ɗin kitchen ɗin, wanda a take idanunta suka gane
mata bayan wani faffaɗen mutun mai tsayi, jikinsa sanye da pyjamas white color wanda alamu sun nuna
tea yake haɗawa.
Wani kalar razananniyyar ƙara ta saki dan a tunanin ta aljani ne ko ɓarawo.(Ɓarawo da haɗa tea😂).
Shi ma a kiɗime ya juyo dan ƙarar har kwanyar kansa ta ratsa, a hankali ya sauke idanunsa akan
kyakkyawan shape ɗinta na baya data juya da gudu domin nemawa kanta mafita, dan wannan baya ma
kama da mutum, bare ma ace ɓarawo ne ko what soo called her fucking husband.
Ko upstairs bata nufa ba ƙasan ɗakin Salimah ta bubbuga da ƙarfi, a firgice Salimah ta buɗe ƙofar ta na
tambayarta mai ya faru?.
Ko kallonta Liyana ba tayi ba ta shige cikin bargon Salimahn ta kwanta tana maida numfashi.
''Aunty Liyana lafiya?."
Tsaki taja haɗe da faɗin ''Lafiya ce tayi sanadiyar shigowata ɗakin ki ai tun da penthouse ne ɗakin naki.''
ta ƙarashe maganar haɗe da shigewa cikin bargon.
''Allah ya ba ki haƙuri Aunty.''
Ko kallonta ba tayi ba ta kwanta wani wahallalen bacci ya kwasheta.
Da safe ma bata yarda ta fita ba komai Salimah ke zuwa ɗakinta ta ɗauko mata.
Dan yau babu school ɗin da zata iya zuwa.
Zama tayi a parlourn tare da da kallon Salimah da ta gama kwashe kwanukan da suka yi break fast ta ce
'' Salimah ɗauko min hand bag daga sama please, sai ki haɗo min da veil black color, da kuma slippers.''
''Toh Aunty.''
Da sauri ta hau saman tare da ɗaukan abin da ta aiketa sannan ta dawo mata da su.
Shiryawa ta yi tsaf daman already jeens trouser da long sleeve shirt ne ajikinta black color amma
wandon fari ne.
Sai kuma slippers baƙi, sai baƙin mayafi da jakarta ƙirar Gucci, chewing gum ɗin dake kan center table ta
ɗauka haɗe da cilla shi a baki.
''Salimah shirya muje mu dawo.''
''Aunty kuma a haka za ki fita.''
''Bana son shishshigi, yaushe muka fara wannan dake, je ki ciki ki shirya mu wuce dallah.''
Sum- sum Salimah ta shirya ta saka wani zumbulelen hijab har ƙasa ta fito.
''Wa za ki bi a haka, nifa ba gidan mutuwa zanje ba kika wani saka hijab kamar za ki tafi musabaƙa.''
''Toh Aunty Liya ban da mayafi.''
Tsaki taja sannan ya kuma faɗin '' sai ki taho muje dan ba zan shiga sama ba.''
Daga haka ta wuce wurin dinning room ta ɗauki mukullin motar ta a inda ta bar shi jiya da ta ci abinci,
dan tsarin gidansu kenan, idan kana goge - goge, ka ga abu ka bar shi a wurinsa.
Ta nufi jeep ɗinta, tare da sanya seat belt ɗinta. Taja motar ta bar gidan.
Bata zarce ko ina ba sai rijiyar zaki gidan Neneh.
Shigowarsu ma Neneh da fadila ne a zaune ƴar aikinta suna hira.
''Ni Ajiddeh matar Aliyu na ga abin da ya kai min wuya.''
Ko kallon Nenehn bata yi ba ta nufo falon tana ƙoƙarin zama a parlourn.
'' ke kam rainon Nabil bai miki kyau ba, mai wannan?, dubi ki ga yadda nake hango ƙasusuwa, duk kin
bar Lami a buɗe.''
''Neneh ke ko missing mutum ba kya yi kya bari na zauna kafin ki fara halin naki ai.''
Matsowa ta yi sosai kusa da Liyanar tare da faɗin.
''Kin haɗu da Khairatu a waje ne?."
''Wace hakan?."
''Ashaa, Uwar mijinki mana.''
''Ni ina da mijina?, ko akwai wanda ku ka yi da shi zan aure sa?."
''Na yarda bayan tsalle tsalle harda shaye shaye a tattare dake, tun da Allah ya jeho ki sai ki zo muje can
bachirawa wai Ummaru ba lafiya.''
''Subhanallahi, Tsohon manyan ne ba lafiya?."
''ni fa iyayinki ke haɗa ni dake, ba komai ba, kice Babi, kawai kin tsaya wani kalacen jaraba.''
''Ke ta shafa ai, ban tambayi mijina ba babu inda za na je.''
''Aatouh mai ruwan Neneh uban uwarki ne dai.''
''Ba ubanki ba.'' ta faɗa tare da murguɗa baki.
''Fatima ni kike zagi?."
''La Salimah kuji Neneh za ta min sharri fa, dan Allah wannan zagi ne?."
Neneh baƙin ciki ma ya hanata magana, sai can bayan some minutes sannan ta ce ''Dan kaza kazanki zo
ki fitar min a gida.''
''Babu inda zani, Salimah ɗauko min Apple dan Allah.''
''Kizo ki fita ko na tuno miki ranar da Ikimat ke naƙudar ki a duniya.''
''Da naji daɗi.''
Sai misalin ƙarfe shida da ƴan canji Liyana ta bar gidan ta koma nata da ita da Salimah.
Aliyu kam tun da ya ga ta fita da gudu bai ma bi ta kanta ba dan shi a rayuwarsa idan aka ce menene
dislikes ɗin da kake da shi a rayuwarka toh mutum mara nutsuwa ne, he's an introvert sam wuri mai
hayaniya yana nisantar kansa da shi ne, idan yaji ihu ko wani abu makamancin disturb, ya kan ɗan tsinci
kansa da ciwon kai, shiyasa idan kana magana da yawa ma baya hulda da kai.
Bayan ya gama haɗa tea ɗinsa ya sha sannan ya yi sallah raka'a biyu haɗe da kwanciya.
Washegari ma da sassafe ya bar gidan ya tafi gidan Mami da kullum ba ta da magana sai na Liyana.
Shima Amir kullum cikin maganar zuwa yake shi da mamansa, amma kullum cikin hana shi yake duba da
yadda ko sanin yanayin yarinyar bai yi ba balle a kai magana kan kawo manyan baƙi.
Ya maida hankali kan business ɗinsa sosai, dan ko da wasa ba zaka taɓa ganinsa wai da sunan he's not
busy ba because shima ya san he's damn busy with his business, trying to achieve more goals, kuma
babu laifi managers na yin abin da ya dace.
Dan a iya month, sai a samu riba fiye da five billion tun da shi ɗin akwai factory waɗanda su ne suke
ƙerawa daga kan android, laptos tablets, fridge, etc sune suke samar da shi.
HYDAR na da mahaukatan kuɗi, idan yazo wurin spending ɗinsu he spends it roughly, because