Advertisements
Chapter 38 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 39

111K to 114K   out of 116.5K words

na mai nunawa Liyanar fushinta.




“Ammmiiiiii.” Ta yi maganar cikin damuwa da muryarta dake a sanyaye alamun kuka take yi.




Saurin ďago kanta Ammi ta yi tare da kallon Liya da hawaye ke ta zarya a idanunta.




“Ya’r Abbhinta, what’s wrong with you?.” Ammi ta faďa tare da miķawa Ily Alynerh.
Faduwa ta kusa yi hakan ya sanya Ammi saurin tallab’o ta tare da zaunar da ita a kusa da ita.




A take su Rash suka fiffito.




“Ammi kishiyya zai min, Amminah ki taimaka min Wallahi Ina son sa.” Ta yi maganar muryarta a dishe.




Wani kalar tsawa da Ammi ta daka mata shi ya sanya ta yin shiru tare da haďiye hawayen da ba ta yi
niyar hadiye shi ba.
“A kan kishiya kike wannan kukan kamar ba mace ba?, maza ki goge hawayen ki kiyi salatul istikhara
Allah ya sa hakan nè mafi alheri, wacece zai aura.”




Fashewa ta yi da kuka tare da faďin “Cousin dinsa ķanwar Amir.”




“Toh ki ajiye damuwar nan naki ki fuskanci abin da zai fishe ki, ba za ki yi koyi da haķurina ba Liyana?, Ni
da na zauna da kishiya mutuwa nayi?.” Bata yiwa Ammi magana ba kawai ta tashi da gudu tare da
shigewa dakinta na gidan Nenehn ta ķara fashewa da kuka.




A ranar dai yaranta sai madara aka basu.
Tun da ya koma gidan Mami yake kiran wayarta amma ba ta picking haka kawai ya hakura tare da kiran
Marwa suka ďan fara tab’a hira sama-sama.




Washegarin ranar da sassafe ta tashi tare da yin wanka ta saka wani atamfa mai kyau Wanda ya amshi
jikinta.




Around 12 na rana ta ďauki jariran uku tare da niyar daukansu ta nufi gidan Mami dasu.
Classy Reedah ce ta shigo ďakin tare da kallonta sannan ta ce “Ina za ki je Mrs. Kyari?.” “Gidan Mami.”
Liyana ta bawa Reedah amsa a takaice.




“Can I come along?.”



“Why not sai ki riķe min ďaya.”




Daga haka ita ma Reedah ta dauki backpack ďin da ďaya daga cikin yaran suke ciki.
ihun su Ily da Rash Ke ta shi hakan ya sanya su zuwa falon da sauri.




Unaisah ce ta shigo cikin shigar wani classy abaya hannunta rike da trollynta.




Waro idanunta Unaisah ta yi tare da cire glasses ďinta ta ce “Mrs Kyari.”




Ita ma Liyana Wani kalar murna ta yi tare da faďin “Yes Mrs Khaleepha to be.” A yangance suka bawa
junansu side hugs, sai da ta kalli yaran sannan ita da Reedah suka wuce.
Gidan shiru yake, amma kallo daya za ka masa ka Wanda cewa an ķara masa sabon paint, da wasu
abubuwan.




A hankali Liyanar ta shiga building din Mamin da shi nè a tsakiya, sai na Aliyu a bangaren dama da yake
sharing da Sultan sai kuma side din Abbhu.




Babu kowa a falon sai yan aiki dake ta gyaran falon duk da a gyare yake tsaff.




Neman ďaya daga cikin kujerun falon suka yi suka zauna tare da rugume biyu daga cikin yaranta, ita
kuma Reedah ta riķe kyakkyawar cikinsu Alya, dan ita kamnaninta da dan banbanci da na sauran.
“Hajiya, welcome Big Hajiya dey sleep she neva wake up.” In ji cewar Agnes da hannunta Ke riķe da
towel da glass cleaner.




Kallonta kawai Liyana ta yi sannan ta ďoke kanta ta ci gaba da kallon ya’r hannunta.




“Wooh, Matar Yaya, Awwn Ma shaa Allah, finally her Liyanar Yaya.” Assultanah ta faďa tare da fara
saukowa daga benen a hankali ita da wasu counsins dinta.




“Which kind Liyanar Yaya, Liyanar Abbhinta dai.” Ta yi maganar a sanyaye, dan haka kawai kowa
haushinsa take ji.
“Lemme see the kids, Ma shaa Allah, wallahi kamar Mamanta.” Ta yi maganar tare da amsan Alya daga
hannun Reedah.




Har za ta bawa Assultanah amsa daddaďan ķamshin turarensa dake sanya zuciyarta sanyi a koda yaushe,
ya daki hancinta.




Cikin aura ďinsa ya ķaraso har living room ďin, sai da ya ďan saci kallonta Sannan ya dauki kansa tare da
nufar dinning area din dake falon.
“Sir wetin you go chop?, Hajiya ta sa an dafa maka favorite food naka.” In ji cewar Agnes dake sanye
cikin uniform dinta iya gwiwa.




Sai da ya saci kallon Liyana kaďan sannan ya ce “To my room.” yana faďin haka ya miķe tare da barin
wajen ya nufi hanyar da zai sada shi da part ďinsa ta bangaren Mamin.
Da sauri Agnes ta nufi kitchen tare da ďauko tray ta fara haďa duk wasu abubuwan da Hydar ďin ke so,
har za ta wuce Liyanar, sai kuma taji muryarta na faďin “Stop there, thats my job i will do it, je ki karasa
cleaning ďinki.” Liya ta yi maganar tare da mikawa Sultana da cousins ďinta yaran hannunta sannan ta
barsu su da Reedah dake ta forming big girl.




Bata tray ďin Agey ta yi sannan ta cigaba da ayyukan nata.




A hankali take tafiya har ta ķarasa fita daga cikin living room ďin bangaren Mami, wani ķaton compound
ne a wajen da yake cike da flowers na ban mamaki, sai wani fitilu dake fita daga cikinsu duk da safiya ne,
ķasan gidan ma shi kansa da epoxy aka yi shi, the building looks rich and elegant, komai na ķamshin kuďi
a part ďin dan part dinsa ya fi na Mami kyau duk kyan na Mamin na sa kuwa.
walking slowly ta ķarasa shiga cikin building ďin dake cike da haske, da ķamshin turaruka masu mugun
ķamshi da sanyaya zuciya.




The living room seemed to be the most beautiful and peaceful living room she has ever seen, babu
hayaniya komai na falon fari ne tass tun daga bangon har ķasan falon fari ne tass sai kuma wani rock
Persian carpet dake malale a ķasa.




Furnitures ďinma fari ne tass babu alamun datti a wajen, sai wani signature Tv dake tsaye ķiķam akan Tv
stand. Everything about this living is odogwu babu Wanda aka siya da Naira, rock carpet kaďai ya ishi ya
cire mutane da dama daga talauci ba sai an kai ga sauran accessories da aka narka a falon ba.
Amma still falon ba shi da tarkace saboda abubuwa kalilan aka sanya.




upstairs ďin da ta gani a falon ne ya sanya ta bin ta ciki tare da wucewa ta fara hawan saman.




D’akuna biyu ne kaďai rak a saman, hakan ya sanyata buďe ķofar na farko a hankali.



Babu komai a ďakin sai wasu pictures da suke cikin frame da tun na yarintarsa har na yanzu da ya girma.
Tab’e bakinta kawai ta yi sannan ta wuce ta buďe next door ďin.




Zaune yake a kan cushion ďin da yake master room ďin nasa.




Jikinsa na sanye da Kayan da ya shigo da su b’angaren Mamin ďazu.
A hankali ta tako har inda yake zaune, ďauke kansa ya yi tare da kallon agogon dake hannunsa, sannan
ya fara ķoķarin tashi daga kan kujerar.




“Wai mai kake nufi da ni yau da safen nan ne?.” Ta yi maganar a raunane tare da kallon cikin idanunsa.




“Har za ki fassara ni da sanyin safiyar nan da ko karya wa ban yi ba.” Ya faďa tare da komawa ya zauna
akan kujerar da karfi.
“Kaga su Alya ba ka musu magana ba, nima na gaishe ka baka amsa min ba, dama da gaske ne idan maza
za su ķara aure sai sun wulaķanta wadda suka ajiye a gida, toh wallahi ka bini a hankali har yanzu da
sauran hauka na.” Ta yi maganar tare da zuwa har inda yake ta na mai dungure ma sa kai.




Janyo hannun na ta ya yi tare da murďesa sannan kuma ya ķara janyota jikinsa.




Wani kalar ķara ta saki bai jira ta dire ba ya haďe bakinsu waje ďaya Wanda kamar jira ita ma take ta
cafke bakin na sa ta na mai amsan sakonnin sa.




Ganin ya na ķoķarin wuce gona da iri ne ya sanyata saurin hankaďesa.
Janyota ya ķara yi jikinsa tare da sanya kansa akan kafaďarta.




“Idan na wulaķanta ki tamkar na wulaķanta yarana ne and kema kin san kalar soyayyar da nake ma
yarana, sannan Liya ki ji tsoron Allah da yaushe kika gaishe ni?.” Ya yi maganar tare da mur za yan
yatsunta a hankali.




“A cikin zuciyata na gaida ka mana zaka rantse kace baka ji ba?.”
“Allah ya shirye ki, what are you planning game da naming ceremony ďin yaran nan?.”




“Yar izala ce ni ai bana taro.”




“Na wash, abeg ke da kike Dajjal din kan ki kece kike claiming ďin ahlul sunnah?, kune ke b’ata mu ashe.”
Ya ķarashe maganar tare da kyalkyalewa da dariya.




“what do you mean?.” Ta faďa a hasale.




“I mean the way you dress, ko Christmas albarka.” Ya yi maganar ya na wani dariyar kuma.
“Waye Christmas kuma?, kowa ai da past life ďinsa babu Wanda bai da tabo, idan kaji na wani ai naka sai
dai kace Alhamdulillah, kuma har gobe dole naga wando a clothset dina na saka a…..”



har ga Allah ita maganarta ta yi bata kawo komai a ranta ba.



Da sauri Hydar ya katse ta da faďin “Ya kuma ishe ki motivational speaker.” Ya faďa tare da ďan b’ata
ransa.




“Ka tsargu ne?, Nifa magana ta ce ta biyo ta nan, idan ya b’ata maka rai toh a yayyafi juna, a Ina muka
kwana a zancan sunan.”




“Get out.”




“Mai na maka?.”
“I said get lost.”




“Allah ya baka haķuri, zan je lalle a bani kuďi.”




“Tun da kin bani ajiya sai ki zo ki warta.”




“Ni kuwa na baka ajiya.”




“Ke ya fa ishe ki.”




“Duniya, yanzu ni Aliyu yake cewa ke, Marwa aikin ki na kyau.”
Ko kallonta bai yi ba ta gama tsoki burutsunta sannan ta fice ta koma b’angaren Mamin da har ta fito.




“Mami Ina kwana.” Ta gaida Mamin cikin ladabi da biyayya kalar Wanda ta saba Mamin.




“Daughter nah ashe kina sashen mijin naki, ya kike ya su Umman naki?.”




“Lafiya lau wallahi, Mami, daman su Alya na kawo ki gani.” Ta yi maganar tare da sauke idanunta ķasa.
“Iyeee, da ba dan su Alya ba ba za ki shigo ki ga Mamin taki ba kenan ko?.” Mamin ta faďa a ďan
barkwance.




“Laa, Billah Mami ba haka bane daman can na yi niyyan zuwa tun ranar da muka dawo, toh da yake
kuma kina zuwa gidan Nenehn saboda shirye shiryen biki kawai sai na bari sai kin dawo gidan ki steady.”
Ta ķarashe maganar ta na mai ďan wasa da hannunta.




Ta ďan taya Mamin wasu abubuwan, aka ďan nuna mata danginsu Mamin wayanda suka zo bikin sannan
ita da Reedah suka fita daga gidan.
Mai lallen da ta yi ma Ilham har ta gama haďa kayanta za ta tafi, Liyana ta tsayar da ita aka fara yi mata
ita ma.




Da yamma aka fara gudanar da Mother’s Day inda a gidan Nenehn aka yi sa.
Gaba ďayansu abaya suka saka mai shegen kyau da ďaukan ido.




After three Days.




Rana ba ta ķarya, yau aka yiwa yaran Liyana yanka kuma a yau aka ďaura auren ABUBAKAR AHMAD
QASSIM KYARI (Sultan) da MAIMUNATOU NABIL ALIYU SHUWA (Ilham), da na UMAR ABUBAKAR
QASSIM KYARI (Amir) da FATIMA AHMAD QASSIM KYARI (Assultanah), sai kuma ALIYU AHMAD QASSIM
KYARI (Hydar) da kuma MARYAM ABUBAKAR QASSIM KYARI (Marwa).
Auren da dubunnan mutane suka shaida.




A can b’angaren Liyana kam tun safiyar ranar take kuka mai cin rai.




Har shi kansa Aliyu was shocked da Jin wannan maganar aurensa da aka ďaura, dan shi da ya ga Liyana
ba ta so sai ya janye ya bama Marwa hak’uri.
Jikinsa na rawa ya nufi gidan Neneh dan ya san duk inda Liyana take labari ya riske ta.




Gidan cike yake da mutanen arziki, a hankali ya yi ta ķeta mutane har ya shiga dakin da yake da tabbacin
ta na ciki.




Aikam tunaninsa ya basa daidai because ta na kwance ta na kuka, sauran sisters ďinta suna tare da ita
duk sun zagayeta sai kuma wayanda yaranta ke hannunsu.
Ganinsa da ta ķara yi ya ķara sosa mata zuciya da gudu ta tashi tare da juya masa baya ta fashe da Wani
kalar matsiyacin kuka.




Su Reedah da Unaisah na ganin hakan suka fice daga ďakin gaba ďaya da sauran ya’mmatan ďakin. Dan
Ilham na tare da Ammi.




A hankali ya karasa shigowa ďakin tare da zama kusa da kanta, haďe da kai hannunsa zuwa ga jikinta.




“Don’t touch me, ba dai aure ba, ka yi ai sai ka bar rayuwata na huta tun da ba sona kake ba daman.” Ta
yi maganar tare da jinginar da kanta a kan gadon.
“Liyana, please listen, ki tsaya ki saurareni.” Ya yi maganar tare da hawa kan gadon sosai.




“Ba na son maka magana, Just goo ka bar ni, daman ni I didn’t deserve to be happy a rayuwata, ka tafi ka
bar ni bana son dogon sharhi just leave me alone.” Ta karashe maganar tare da jan bargo har kanta.




“Okay.” Ya faďa a sanyaye tare da zura takalmansa ya bar ďakin.




Da ido ta bi ķofar tare da fashewa da wani sabon kuka hannunta riķe da kanta.
Da fitarsa bai zarce ko ina ba sai gidan Mami, dake cike da mutane because a gidan ake gabadaya
shagulgulan har da nasu Amir din, ďakin da abokansu ke ciki ya nufa a guest room din gidan nasu.




Ko da ya shigo cikin ďakin kwanciyyarsa ya yi akan gadon dake guest room ďin gidansu, Amir ne ya
ķaraso kusa da shi tare da ďan dafa shi Sannan ya ce “ Hope ba ta cikin damuwa?.” Wani kalar ajiyar
zuciya ya furzar tare da faďin “she’s there crying, ni na rasa ma yadda zan yi, tun da na fara maganar
auren nan ba kullum take bama yaranta Nono ba , wallahi na rasa ya zan yi, kai ma kuma ka san duk
biyun Ina son su.” Ya karashe maganar tare da dafe kansa.
“Shegee.” Amir ya fada tare da kyalkyalewa da dariya.




Tsaki kawai Hydar yaja tare da manne kansa a pillow ya na tunanin solution.




Daren ranar 🫠




Nasiha sosai aka yiwa Ilham dake kuka kamar ranta zai fice sannan aka wuce da ita ďakin mijinta.
Liya babu abin da take sai kuka, su Aida kam sai madara kawai aka dinga banka musu.




Neneh kam she’s busy da kawayenta da ma cousins dinta dan jira take a watse ta fara kinsawa jikarta
abubuwa dan wannan Marwar mai zubin karuwai da wannan halittar da ba a waye take ba barinta da
Marwa babban hadari ne.(kai Neneh Liyana ce ba ta waye ba 😆😆😂)?




Washegari bayan mutane da dama sun watse Neneh ta shigo ďakin Liyanar da ita ma ta gama shiryawa
su Unaisah da sauran yammatan na ta bata baki a kan Kar ta tafi ta bari ta gama wankan gidan.
“Oh ni Ajiddeh da ban da aure da naga takaici, yanzu akan kishiya kike kokarin barin abin da zai ceceki,
toh ai shikenan ruwanki ki zauna ruwanki ki tafi, amma kishiya kamar Marwa sai kin daina saka wannan
shaigun wandunan naki kin dawo kin fara saka riga Iya gwiwa, Allah na tuba Marwar da duk k’iba ya mai
data kamar saniya ai idan kika saka Kayan da nake fada miki ko kallo bata ishe sa ba.” Nenehn ta faďa
tare da ajiye mata wani haďin data kawo mata sannan ta fice daga dakin.




Fashewa ta ķara yi da kuka sannan ta kalli Salimah dake tsaye da suka shigo tare da Neneh.
Shanye abin da Nenehn ta bata ta yi sannan ta ďauki mukullin motar ta picanto dake gidan Nenehn.




“Wai Liya tafiya za ki yi yanzun?.” In ji cewar Reedah.




“Just think Wallahi Liya, yanzu ki dauko atm dinki Muje kasuwa muyi siyayyar Kayan shegu, sai ta Raina
kanta for sure.” Unaisah ta fada tare da ajiye laptop dinta akan standing mirror
“Toh ku taso mu tafi.” Liyana ta fada tare da turo bakinta.




daga haka suka fice daga gidan.




sai da ta biya ta gidan Lily sannan suka fita tare.




Kaya suka siya na gani na faďa, sannan suka dawo gidan.




still ba ta daina shirya kayanta ba dan a cikin satin nan zata koma gidanta.
B’angaren Baban gida Hydar kam sun nunawa junan su yadda suka yi missing junansu shi da Marwa.




Amma har lokacin bai sakar mata fuska ba.
After a week🥰




“Wallahi tafiya zan yi babu wani kwana arba’in da zan zauna yi, mijina na can tare da wata.” Liyana ta
faďa hawaye na zuba a idanunta.




Su Reedah ne keta bata baki da ta zauna Kar ta tafi amma hakan nan ta yi biris tare da ďaukan wani
basket ta zuba yaran gaba daya a ciki.
“Ku bar ta kar wanda ya hana ta , Nima daman na gaji da zamanki ki tattara ki tafi ďin tun da ba’a dole,
yara kuma an riga da anyi musu yanka to mai ya rage daman?.” Neneh ta faďa tare da shigowa ďakin
sosai.




“Ni ai ban miki magana ba.” In ji cewar Liya da fuskarta ke a haďe.




“Ke kin isa kiyi dani?, ai kin yi kaďan sai mai jan kunne.”
“Neneh ki daina zagar min Abbhina.”




“Ka ga masu Uba?, toh Allah ya jikan mahaifina da gafara.”




“Wannan ke ta shafa, Reedah ku Taya ni kai kayana mota mana yamma na yi.”




“Ba za ki je yiwa Khairatun Sallama ba?.”




“Ai ba uwar mijinki bace.” Liya ta fadawa Nenehn tare da dauke kanta.
“Ba shakka, ai Biri ya yi kama da mutum.”




Tashi su Reedahn suka yi tare da kama mata ďan trollynta da Aliyun ya kawo mata da ta yi fitar suna da
su ranar bikin Ilham.




Sai ķarfe biyar da minti 47 ta iso cikin gidan, ko ta kan trollyn ba ta bi ba ta kwa shi yaranta ta nufi cikin
gidan dasu.
Ba ta wani tsaya kwankwasa ķofa ba ta bude kofar living room din a hankali.




Guje-Guje suke a living room ďin kamar yara, kowannensu hannunsa riķe da throw pillow, Aliyu ne ya yi
nasarar kama Marwa hakan ya sanya sa buga mata pillow ďin a kai har sau biyu tare da rungume ta ta
baya ya na mai ďaura kansa a kan kafadar Marwar.




D’ago kansa da zai yi suka yi ido hudu da Liya da ta kusan mintuna biyu a tsaye a wajen ta na kallon su,
da sauri ya saketa tare da sosa ķeyarsa tare da faďin.



“Babe you’re back?.” Ya faďa ya na dan sinnar da kansa.
“Noo, I’m gone, Rubbish.” Ta karashe maganar tare da yin wani kafirar tsaki.




Jiki a sanyaye Marwa ta ce “Maman Triplets sannu da zuwa.”
“Riķe kayanki, za ta miki amfani.” Ta na faďan haka ta ďauki yaranta sannan ta wuce saman ďakinta da
su.




Ita ma Marwa bayanta ta bi ta shige ďakinta aka bar Aliyu kaďai a falon ya jinginar da kansa a kan kujera.




_”Buh you told me ta amince sannan ka aure ni , Ko dai ba ta sani ba.?_




Saķon da ya shigo wayarsa kenan, wani tsaki yaja Sannan ya mayar da kansa kan kujerar tare da lumshe
idanunsa.
A hankali ya tashi tare da nufar cikin ďakin nata.




A tsaye take jikinta daure da towel, Wanda alamu sun nuna daga wanka ta fito .




Ķura mata idanu ya yi dan ya rasa ma ta ya zai mata bayani.




“Malam ka faďi abin da ke tafe da kai zan kulle ķofa.” Liya ta faďa tare

38 / 39