Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
da ďaukan wani auduga da
kwalban misk a hannunta.
“Liya Please ki yafe min.”
“Na ce kayi wani abu?, toh dan girman Allah ka rabu da ni, jeka wajen matarka zan nemeka.” Ta faďa
tare da ķara tamke fuskarta.
“Tom na gode, can I see my daughters dan Allah?.”
“Ga ka ga su.” Ta yi maganar a dakile.
Ya kusan hour ďaya tare da yaran ya na ta musu wasa sannan ya mata sai da safe ya bar mata ďakinta
haďe da kulle mata ķofar.
Wani kukan ta ķara fashewa da shi yadda ta ga ko wani damuwa bai yi ba.
Haka rayuwa ta cigaba har yaran suka yi wata hudu Aliyu bai taba nemanta ba, sai dai ya shigo ďakin ya
dauki yaransa ya musu wasa ya kuma Karawa gaba.
Abin tun baya damunta har ya fara damunta domin Ko da wasa bata sakarwa Marwa fuska gashi wani
shishige mata da take yi har tausayi Marwar ke bata.
Kamar kullum ta na zaune ita da su Alya da ta ajiyesu a kan kujera suna wasa ita kuma ta na zaune ta na
chatting a wani group dinsu na instagram _Cousins forum_ wan da na iya cousins na su ne.
Marwa ce ta ķaraso cikin falon cikin shigarta na wani atamfa mai kyau da ya gama shan crystal stones
masu tsadar gaske.
jikinta sai tashin ķamshi mai daďi yake.
Cikin sassanyar muryarta ta ce “Sis zan je gidanmu na dawo Abbah ya dawo daga Saudi tun shekaran
jiya.” ta yi maganar tare da mikawa Alynerh hannu da tun shigowarta take ta ďan shure-shure alamun
ta ďauketa.
Liyana ce ta ďago ta kalli Marwar da Alynerh ke sab’e a kafaďarta tare da faďin “ Toh a dawo lafiya, da
Alynerh za ki tafi?.” Ta yi maganar a dan sanyaye.
“Eh sis yanzu zamu dawo.”
“Ai kam kin taimaka min bara na ďauko miki madara da feeder da spare na kayanta.”
“Ina dasu anan ba sai kin sha wahala ba.” Ta karashe maganar tare da sakin wani lallausan murmushi.
Bayan sun fita ma babu abin da Liya ke yi sai judging ďin kanta da Marwar.
“Yeah Marwa is a very kind person, na dade ina testing hakurinta ba ta tab’a tanka min ba, ta na son
yarana, ya’n uwana idan sun zo ta fi mai da hankalinta a kansu , I think gwara na ajiye kaina mu yi zaman
lafiya , na bawa mijina peace of mind da yake da bukata, yeah a good idea.” Ta na faďin haka ta janyo
keken yaranta sannan ta sanya su a ciki, tare da kiran Salimah da ta dawo gida, dan tun da ba girki take
ba shiyasa ta bar Salimah a can gidan Nenehn.
Cikin hour biyu Salimah ta iso gidan suka fara abin da ya dace.
Misalin karfe shida motar Aliyu ta ķaraso cikin gidan, bayan ya yi parking ďin cikin gidan suka nufa shi da
Marwa da har Yarinyar hannunta ta yi bacci, dan bayan ya dawo daga office din Abbhu ya biya gidan
Kanin baban nasa dan gaida sa tare da dauko Marwar suka nufo gida.
Hannunsa cikin nata suka ķaraso cikin falon, Zaune take cikin wani lifaya lace black color ďinkin bubu
gown mai mugun kyau da tsada, ķafar ta na sanye da wasu flat designer shoes masu kyau da aji.
A lalace ya ďago da kansa tare da kai dubansa gareta, ta masa wani kalar mugun kyau mai tsayawa a rai.
Da sauri ya ďauke kansa daga dubanta tare da sakin hannun Marwa ya yi saman ďakinsa.
Tab’e bakinta ta yi tare da binsa a baya.
Har ya fara cire kayansa domin shiga wanka ta yi sauri ta shige jikinsa tare da Fashewa da Wani kalar
kuka.
Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da Kara rungume ta a jikinsa ya na mai shafa mata baya….
> Soft Noorah ☺️
> Pending Amarya as usual 🦋🇳🇬✨
> Pending Amarya’s Book corner Extra ordinary every day 😊
> I’m back 🙃
_Pending Amarya as usual_
✍🏻
THE REGRET
JAW
Pending Amarya 64
Ending……………
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
Death is a reminder that this worldly life is temporary, and the eternal life in the Hereafter awaits those
who obey Allah.🥹
Da sauri ya ďauke kansa daga dubanta tare da sakin hannun Marwa ya yi saman ďakinsa.
Tab’e bakinta ta yi tare da binsa a baya.
Har ya fara cire kayansa domin shiga wanka ta yi sauri ta shige jikinsa tare da Fashewa da Wani kalar
kuka.
Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da Kara rungume ta a jikinsa ya na mai shafa mata baya.
“I missed you badly Wife.” Ya fada da wata dasasshiyar muryarsa.
“Missed you More Tesoro.” Ta faďa tare da kankame sa.
They make love ❤️
Ganin yaran nata kuka hakan ya sanyata ďaukansu tare da yin bangarenta da su, a ranar dai a ďakin
Marwar yaran suka kwana dan har wajen 10 babu alamarsu.
Sosai suke zaune Lafiya da Marwa, komai idan Marwa ta gani sai dai kaji ta ce sis. Ita hakannan kawai taji
ta na bala’in son Liyana.
After 2 years 🥀💐
Yaran Liya sun girma sun yi wayo sosai, tsakanin ta da Marwa kam sai zallar soyayya.
Mr Aliyu namu kam a yanzu komai na electronics a duk faďin duniya a wajen sa ake samu , sosai ya
shahara fiye da yadda a ka san shi a baya, dan a yanzu arziki ya ci uwar na da.
A cikin shekarun biyun nan kam abubuwa da yawa sun faru, har da rasuwar Jiddah da kuma Haihuwar
Assultanah da Ilham, da kuma auren su Rashanda da aka yi.(Allah ya jikan Jiddah da gafara ya sa ya
huta).
Bangaren Liyana kam zaune suke ita da Marwa a living room suna kallo and at the same time suna shan
fruit salad a bowl ďaya.
Alynerh ce ta fito daga cikin ďakin da yake downstairs idanunta na zubar da hawaye ta ķaraso wajen
Marwa haďe da nuna mata hannunta da Alya ta mintsineta, cikin muryarta mai sanyi dake kuma nuna
yarinta ta ce “Ummi Alya ko.” Ta faďa tare da fashewa da kuka ta na pointing ķofar ďakin da suke wasan.
“Sorry Baby Maama.” Marwa ta faďa tare da ďaura ta a cinyarta da ķyar saboda ta na da jiki ma shaa
Allah.
“Babu wani sorry, your daughter will always be at fault, a tambayi su Alya ďin aji akwai abin da ta musu
ai.” Liya ta yi maganar tare da dungurewa Alynerh kai.
Ķara fashewa ta yi da kuka tare da faďin “Ummiii.”
“Naam yar Ummi, don’t mind Ammi kin ji, kwanta kiyi bacci Papi na dawowa zamu je shan ice cream
Okay.?” Marwa ta fada tare da kwantar da ita a kan kujerar falon.
K’amshin turarensa shi ya sanar da su isowarsa, a hankali ta ďago tare da kallon cikin idanunsa.
Murmushi ya sakar musu a hankali tare da faďin “Yau babu shopping ne?.” Shiru ta masa kawai tare da
ďauke kanta dan haushin rashin barinta zuwa bikin lily kawai take.
Kallon Marwa ya yi tare da faďin “ ya jikin ki?.” “Da sauki Papi.” Ta fada tare da sauke kanta kasa.
“Ma shaa Allah, mai kuka dafa?.”
“Idon ma tambayi.” Liya ta fada tare dalla masa harara.
“Ina uwayen masu gida for the first plac…?”
Bai karasa ba wasu yara Kananu suka fito da gudu “Papi, welcome.” Suka faďa tare da rungumesa.
Alynerh da har bacci ya dauketa ita ma ta tashi da sauri tare da shigewa jikinsa haka ya yi ta yiwa yaran
wasa, suna kyalkyala dariya.
Ta shi Marwa ta yi da tsohon cikinta dake jikinta sannan ta nufi hanyar kitchen ta zubo masa abinci suka
hau ci da yaransa.
Da kyar take tafiya ta sannan ta haura saman ďakinta.
Tashi ita ma Liyanar ta yi ta bar sa a falon shi da yaransa ta nufi ďakinta domin huta wa.
After 3 months.
Tun safe Marwa ta tashi da faduwar gaba , bayan ta Kira Umminta suka ďan yi hira sannan ta wuce
bangaren Liyana ta fara taya ta gyaran clothset ďinta dan ita ma Salimah ta yi aure kuma wadda aka
kawo musu ba su gama yarda da ita ba.
haka suka ďinga hira har da dariya har suka gama gyara clothset din.
Ko da suka gama ma kitchen suka nufa suka fara ďora girki saboda Aliyu ya na gari.
“Sis baya na ciwo yake min wallahi.”
“Kai Marwa mai ya kawo ciwon baya muna zaune kalau.”
“Laa kin manta Ina EDD dina yau?.”
“Yeah hakane, toh muje hospital mana.”
“Yeah bari na tambayesa toh.”
“Kin ga ki ajiye maganar tambayar nan agefe kin san yanzu wani iskanci ya tsiro da shi na hana mutum
fita, mu gama hadawa shi da yaransa abinci mu yi ficewar mu.” Liya ta fada da zallar bacin rai.
Ajiyar zuciya Marwa ta sauke sannan suka karasa girkin.
Ammi da Abbhi sun dawo da Neneh can gidansu da bata da abin yi sai maganar Jiddah, da anyi magana
za ka ji ta na faďin Allah sarki Jiddah na Ajiddeh.
Duk ta koma abin tausayi amma baķin halin nan nata na nan.
Ba su je hospital din ba a ranar sai washegari
Washegari da sassafe suka fara shirya breakfast bayan sun gama suka jera sa a dining.
A hankali yake saukowa daga stairs idanunsa akansu , sosai matan nasa ke burgesa yadda suka haďa kan
su suke zaune Lafiya babu wariya.
Karasowa ya yi ya zauna a kan dinning table din, cikin wani kalar sanyin da ba’a san ta da shi ba ta tashi
tare da fara serving ďin su abincin.
“What’s wrong Marwa?.” Ya tambayeta a sanyaye tare da kallon fuskarta.
Sunkuyar da kanta ta yi tare da faďin “ Nothing, I’m just missing something da ban san ko mai ye ba.” Ta
fada a sanyaye tare da share kwallar dake sauka a idanunta.
“In shaa Allah za ki haihu lafiya kin ji Mom Alynerh?, oya fara cin abincin ki kafin yaranku su farka.
Liyana kawai danne hawayenta take dan sam yanxu ta tsani Jin sunan mutuwa.
Har suka gama breakfast din ta na satan kallon Marwa.
Suna gama breakfast ďin suka fice daga gidan dan sai da Marwa ta tambayi Aliyun za ta je hospital.
Ji ya yi kamar ya bisu zuwa hospital ďin amma yanayin aikinsa yau da kuma yaransa ba zai sa sa ya fita a
gidan ba.
Tun kafin su isa hospital nakudar ta yi tsanani, kafin su karasa ma har wani ruwa da jini ya fara fito mata.
Da gudu Liyana ta Kara figar motar har suka karasa hospital ďin.
Ta yi kusan 5hrs ta na labour sannan ta haifi kyakkyawar ya’r ta mace fuskarta na fidda hawaye ta kamo
hannun liyana tare da faďin “Sis ba zan rayu ba na sani, ki kula min da wannan ya’r tamkar na ki , dan
Allah ki yafe min duk wasu abubuwan da na miki, ki rokar min yafiyar Ummi nah , sannan ki shafa min
kan Alynerh ki kula min da ita, and promise me ba za ki ďin ga nuna mata banbanci ba saboda ta rayu da
ni, sannan ki roki Kowa ya yafe min duk wani abu da na musu, sannan ki fada ma Papi Ina son sa ba zan
kuma daina son sa ba pls.” Ta faďa tare da fara kalmar shahada ta na iddasa wa ta cika.
A firgice Liyana ta ďago tare da kallon yadda take fidda wani siririn murmushi.
Da wani mugun ķarfi ta ce “Noooo, Marwa, sau nawa ki na cewa tare zamu tsufa mu aurar da su
Alynerh, where are the promises?.” Ganin ihun ya yi yawa hakan ya sanya doctors fitar da ita daga ward
din gabadaya.
Sannan suka gyara jikin Marwa tare da lullubeta hade da gyara yarinyar.
Kuka kawai take babu kakkautawa ta ma rasa wa za ta kira.
Daga karshe dai Aliyu ta Kira ta sanar masa.
A firgice ya tattara yaransa ya nufo hospital ďin kamar wani mahaukaci, in Banda Innalillahi babu abin da
yake nanatawa.
Alynerh ce ta karasa wajen Liyana tare da faďin “Ammi where’s Ummi?.” ta faďa da muryar kuka dan
ganin iyayen nata na kuka.
Wani zallar tausayin yarinyar ne ya kamata hakan ya sanya ta rungumeta tare da fashewa da kuka, dan
tafi sabawa da Marwa.
Kafin yamma har an hallara a cikin hospital ďin sannan aka nufo gida aka mata wanka aka nufi gidanta na
gaskiya da ita.( haka rayuwa take daman, Allah ya sa muyi kyakkyawar karshe).
Babu Wanda bai zo ba a dangin liyan dan sai a ranar ma Ammi ta san yadda dakin Liyar yake.
Amir ma kamar zai haukace haka ya yi ta kuka Sultan na taya sa yi.
Liyana kam idan ta yi ido hudu da clothset dinta take sake Fashewa da kuka.
Har aka yi sadakan bakwan Marwa Liya ba ta samu kanta ba.
Dan sai da ta saka Hydar siya mata sabon clothset ta fara sabon zubin kaya dan ba zata taba warware
linkin da Marwar ta mata ba.
After 5 years
Alhamdulillah suna zaune Lafiya tsakaninta da Aliyu.
Yaranta na da 7 years Ya’r Marwa da aka mata yanka da Maryam sunan mahaifiyyarta na asali kuma ake
kiranta da Marwa ta na da 5 years.
Rayuwarsu suke cikin farinciki da Qaunar juna.
Aliyu ya gina gidan marayu da masallatai uku da sunan Marwa.
Sannan ya mallakawa Liyana wajen shakatawansa.
Every blessed Friday kam sai sun je kabarin Marwa sun mata addua.
“Wife, ki shirya muje gidan Mami da Ammi gobe zamu koma China in shaa Allah.”
Wani kalar murna yaran ke yi banda Liyana da ta kurawa linkin da Marwa ta Taya ta kusan shekaru 6 da
suka wuce ido.
Kwallan da ya zubo mata ta share tare da kulle clothset ďin sannan ta nufi dayan da take zuba kayanta a
yanzun.
Kayan da zata saka ta zabo sannan suka wuce gidan Mami.
Ta Taya ta hira sosai daga nan suka bar gidan ta na kallon gidan Neneh ta Kara fashewa da kuka ta na
tuna memories da dama.
Daga nan suka wuce gidan Ammi sun yi hira sosai ta na kallon gidan da duk ya canza mata.
Sai da dare suka bar gidanta, dan Abbhi ba ya ma kasar, kamar za ta yi kuka sai da ya ce mata zai zo har
China sannan ta ware suka nufo hanyar gida.
Shima sai da suka biya gidan su Ilham da Assultanah, Amir nata tsokanar ta har suka dawo gida.
Washegari da safe jet dinsu ya daga zuwa china.
Ji take tamkar ta bar wani gangar jikinta a Nigeria.
Tun da jirgin ya daga take kuka har suka zo China ba ta bar shasheka ba.
Hydar har ya lallasheta ya gaji yaran ma duk sun yi bacci a jet ďin.
Sun isa China Ma shaa Allah sun fara gudanar da Sabuwar rayuwarsu duk da Liyana ba ta daina kewar
Marwa ba dan a ďakin da Marwar ke zaune a nan China take kwanciyyarta da rana.
ALHAMDULILLAH anan ni Faridat Aliyu Ibrahim (Pending Amarya) zan kawo karshen littafina mai suna
THE REGRET.
Allah ya yafe min kurakuren da suke ciki.
Littafin nan gaba daya na sadaukar da shi ga Yayyuna sannan Qawayena. Na gode sosai da gudumowar
da kuka bani Musamman my Aunty Maryama Allah ya raya miki yaranki ya sa ki fi karfin makiyanki ya
Baki duk abin da kike so Sannan ya shiga cikin lamarinki.
To All my friends who stood by me kuma Ina muku godiya , ban manta da ku ba.
Ga duk Fans dina masu karanta littafina kuma Allah ya saka muku da alheri. Musamman su Unaisah,
Dimple Oum daughter, Faiza Idris da ma wayanda ban kira ba Allah ya hada fuskokinmu a Aljannah ❤️
sannan Ina muku Albishir da sabon novel dina mai suna IMAM bayan sallah In shaa Allah, Ramadan
Mubarak to my lovely Readers 🥳🥳🥳🫡
Buh Imam is a paid Book
#Vip 1000
Regular 500
Ma’assalam
Fi Amanillah ❤️
Soft Noorah ✍🏻✍🏻
Kuyi haķuri mun fara kenan sai mun dire storyn Allah ya mana jagora 🥹