Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
ma ka.'' ta ƙarashe maganar hawaye na fita daga idanunta.....
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 49**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Mai nayi wa kowa ya tsane ni, ni Fatimatu, mai nayi?, ba ga uwar da ta
haifeni ba ba ga kowa ba, saboda zallar tsana da Neneh ta yi min ɗan bariki ta aura min, wanda ba ya
daraja Mahaifina, why me??, why now?, why not later?, ya Rabbi I'm still young for all this, wayyo Allah
na Aliyu zai min lahani, Allah ya ishewa mahaifina kalar cin mutuncin da kake yi ma sa, kai ma Billah sai
an ma ka.'' ta ƙarashe maganar hawaye na fita daga idanunta.....
Tun da ta yi cilli da wayarta take wani kalan kuka mai cin rai sannan kuma a hankali ta sanya kayan
baccinta haɗe da yin kwanciyyarta.
Ko ta kan wayar ba ta ƙara bi ba wani kalar bacci ya kwasheta.
Washegarin ranar ma bayan ta gama abubuwan da ta saba ita da Salimah, shirye take cikin wani hijjabi
mai kyau da tsada, wanda ya mugun dacewa da fatarta.
Fuskarta ya yi wani haske ya yi kyau sosai, hannunta riƙe da wayarta da car key ɗinta, ta matso tare da
fara ƙoƙarin yin breakfast ɗin dake jere saman dinning.
Fresh milk kawai ta sha wanda Salimah ta dafa ma ta da Lipton da kuma kaninfari, sannan ta wuce tare
da sanya Salimah buɗe ma ta gate ta fita daga gidan.
Sosai ta wataya a school ita da Lily sai da suka sha yawo, dan kalamansa na jiya sosai suka taɓa ma ta rai.
Ko da ta dawo gidanma su Ily da Reedah da Rashanda har da Unaisah duk suna cikin falon suna jiranta.
Hakan ya sanya ta farin ciki sosai suka ɗinga hira har sai da suka ja ta yau tayi post ɗin reel a Instagram,
wanda acikin second talatin sai da ta samu almost 20k likes comments 1k ina ta shiga, sun daɗe ba su
ganta ba( she finds her self again on social media, Dan hakan sosai ya sanyata farinciki).
After 2 months 📚🥀💎
Zaune take fruits na cike taff a gabanta, jikinta na sanye da wani silky gown wanda ya kame ma ta jiki,
har ya yi sanadin bayyanar da ɗan ƙaramin cikinta.
Salimah na gyara falon, ita kuma ta na shan fruits ɗin da take mugun jin daɗinsa.
Wayarta ne ya fara ringing hakan ya sanyata ɗagawa ganin Reeda ce ke kiran na ta, ''Hello Babe.''
Reedah ta faɗa a ta ɗayan ɓangaren.
''Yeah Babe, mai ya faru.?" Ta yi maganar a sanyaye.
''Nothing na kira ki ne mu ɗan gaisa.'' Okay dear I really appreciate.'' daga haka ta katse wayar, dan har
ga Allah yanzu ta tsani magana mai nisa.
''Wai ke Salimah uban mai kike gogewa tun ɗazu a jikin TV ne, duk kin cika waje ke ba ƙiban arziƙi ba.''
Liyana ta faɗa a zafafe dan yanzu kowa ma haushinsa take ji.
Shiru kawai Salimah ta yi mata, dan yanzu wani kalar faɗa Liya ke tsiro ma ta da shi kamar jiƙar Bahubali.
Wayarta ne ya ƙara yin ringing na wani baƙon number da tun kusan mintuna goma da suka wuce yake ta
faman kiranta.
A zafafe ya ɗaga wayar tare da karawa a kunne tare da faɗin ''Wayee?!." Ta yi maganar da zafi duk da
zuciyarta na dukan uku uku.
Cikin muryarsa mai daɗin sauraro ya ce ''How dare you keep me waiting a airport tun ɗazu ina kiranki a
waya?." Sassauta muryarta ta yi tare da faɗin ''Yi haƙuri ban san kai ne ba shiyasa.''
A tsawace ya ce ''Za ki zo ki ɗauke ni ne ko za ki tsaya haukan ki anan wajen.?"
Ba ta bashi amsa ba ta katse wayar tare da ɗauko wani dogon hijabi da ta dawo da shi daga hospital
yanzu, sai safar hannu da na ƙafa tare da ɗaukan mukullin motarsa ta na ƙara jaddadawa Salimah ta ƙara
gyaran gidan sosai.
Ikon Allah ne kaɗai ya kaita zuwa Airport ɗin, ta cikin mudubi ta hangesa, hakan ya sanyata parking
motar na ta ɗan nesa da shi haɗe da saukowa daga cikin motar.
Tsaye yake hannunsa ɗaya a kunnensa wanda da alamu sun nuna waya yake, ɗayan hannun kuma dake
ɗaure da agogon Rolex explorer ll na dafe da trollynsa.
A hankali ta sauko daga cikin motar iska na ɗan kaɗa hijabinta, ba tare da ta damu da hakan ba ta ci gaba
da nufar wajen da yake.
Tun da ta nufo wajen da yake ya fara ƙafe idanunsa da ita, dan da tafiyarta ya gane saboda wani ƙiban
da ta yi, walking slowly ta ƙaraso wajen da yake tare da faɗin ''Yaya, sannu da zuwa.'' ta yi maganar tare
da sauke idanunta a ƙasa.
Ta yi kusan second biyar a hakan sannan ta ɗagoda kanta a hankali, a tunaninta ya na tsaye ya na
kallonta, sai ta ga akasin hakan, because har ya nufi cikin motar , ya na zaune kujerar kusa da driver.
Wani kalar baƙin ciki ta haɗiya, har ƙwalla na niyyar zubo ma ta , gudun kar ya dizga ta a cikin jama'a ya
sanyata ɗaukan trollyn da ya bar ma ta ta nufi bayan motar da shi.
Bayan ta saka trollyn ma wucewa ta yi ta zauna a driver sit ɗin motar tare da yiwa motar key ta na mai
barin airport ɗin.
Acikin motar ma da dukkannin hankalinta take tuƙi gudun kar ta yi mistake da zai sanyata shan mari
yadda ta ƙular da shi ɗin nan.
''By your left hand.'' ya yi maganar tare da ɗan mazewa, ba ta ma sa musu ba ta cigaba da jan motar.
Ƙara tsintar muryarsa ta yi ya na faɗin ''Kai ni wajen da ke da sugar daddies ɗinki kuke zuwa.'' ya ƙarasa
maganar tare da mayar da kujerar motar baya domin ya ɗan fara hutawa.
Shiru ta yi domin ita har ga Allah ba ta taɓa fita da wani sugar daddies ba, parker motar ta yi tare da
faɗin ''Yaya ina ne zamu je?, ban gane wajen sugar daddies ɗin ba.'' ta yi maganar innocently a ɗan
marairaice tare da turo bakinta kaɗan.
Ƙurawa kyakkyawan lips ɗinta ido ya yi, sannan a hankali ya sa hannunsa haɗe da damƙo kanta ya fara
ba ta wani kalar french kiss.
Ba tayi jayayya ba ta bashi haɗin kai acikin motar, jin ana musu wani kalar mahaukacin horn ne ya
sanyata realising cewa akan titi ma ta yi parking motar.
A hankali ya saki bakin nata ba tare da yaso ba, ita ma sam ranta bai so ba, hakan ya sanyata tayar da
motar tare da barin titin.
Wani kalar jaa idanunsa suka yi, murya a shaƙe ya ce ''Hydar's garden, right now.'' ya ƙarasa maganar ya
na ɗauke kansa gefe, dan kallonta kwance ma sa lissafi yake.
Gudu take shararawa a titin a hankali ta na jin yadda kanta ke wani mugun sara ma ta, a hankali ta shiga
cikin tamkeken gate ɗin da ya gaji da haɗuwa, tare da yin parking a wajen da ya dace ta yi.
Sauka ya yi a cikin motar, ita ma ta bi shi, ko ta kan reception bai bi ba ya danna wani kalar remote a
hannunsa wanda hakan ya sanya glass ɗin wajen juyowa ya zama kamar ƙofa, shigewa ya yi ciki, ita ma
ta bi shi, yanayin ginin kaɗai ya isheka ka san da cewa kuɗi sun zauna sosai.
Because ginin penthouse ne, looking very rich, ta cikin glass ɗin za ka iya ganin wanda yake waje,
musamman yadda wajen yake idan ba ku manta ba.
Ta na tsaye ta na kallon kalar yadda gidan ya tsaru, taji mutum ya wani kalar ɗagata sama.
Ba ta musa ma sa ba ta ba sa haɗin kai, then they made love.
Wani kalar jinta yake a ransa, barin ma idan ya tuno kalar ɗawainiyyar da ta yi da mahaifiyyarsa, and
then idan ya tuna a Virgin ya sameta, ya kan ji daɗi sosai.
A kwance take a jikinsa , he can feel the over heat da yake fita daga jikinta wanda shi kansa zafin jikin ya
na affecting na sa, ga wani kalar surutai da take marasa kan gado.
''What's wrong with you.?'' ya yi maganar ya na mai shafa bayanta, ka sa magana ta yi wasu kalar
hawaye na fita daga idanunta.
Jin saukar hawayen a kafaɗansa hakan ya sanya shi mirginota ta koma ƙasan sa tare da kallonta daga
sama har ƙasa, cikinta ya ɗan taso ba kamar yadda ya kusanceta ba aranar farkon su.
Hannunsa ya sanya akan cikin nata tare da ɗan dannasa, saurin riƙe ma sa hannu ta yi cikin muryarta da
ba ya fita ta ce ''Stop.'' ta yi maganar hawaye na sake gangarowa daga ƙuncinta.
''Mai yake damun ki wai ko kin fara hauka ne.?" Ya yi maganar ya na ƙara ƙafeta da ido.
Ƙanƙameshi ta yi da sauri ta na sauke wani kalar ajiyar zuciya, wanda hakan ya ƙara firgita tunaninsa.
''Ki yi wanka mu koma gida.'' still shiru ta yi ba ta ma sa magana ba.
''Liyana!." Ya kira sunanta da ɗan zafi.
Fashewa ta yi da kuka sannan a hankali ta ce ''Yaya, jini na zafi, cikin fata na zafi yake min.''
''Ya na miki hakan ne.?" Ya tambayeta ya na mai ƙafeta da idanunsa.
A sanyaye ta ce ''Just today.''
''Shirya muje hospital, can you dress up ko na taya ki.?"
''Your wish is my command sir.'' ta yi maganar da ƙyar.
Bayan sun shirya, direct nearest hospital suka nufa bayan sun fito daga ƙauyen, test aka yi ma ta,
because it's emargency kuma Hydar ya sakar musu kuɗi, 7 hours aka basu kafin test ɗin ya fito.
7 hours suka yi a hospital ɗin, suna jiran sakamakon, Liyana ce kwance akan gadon emergency room,
hannunta riƙe da cikinta kamar mai tsoron ka da wani abu ya samu abin da ke cikin nata. Hydar na tsaye
hannunsa goye da bayansa yana ta safa da marwa, ya na kallonta a kai a kai.
Ƙarar buɗe ƙofan da ya ji ne ya ba shi daman juyowa da sauri, wa ta matashiyyar nurse ce ta shigo, ta
kalli Hydar ɗin tare da faɗin ''Sir doctor is calling you for the results.''
Sai da ya kalli Liyana da kyau sannan ya matsa kusa da ita tare da shafa kanta ya fice daga room ɗin.
Lumshe idanunta ta yi hawaye masu zafi na gangarowa, sannan a hankali ta ƙara rufe idanunta kamar
mai bacci.
><><><><>><><><>
Doctor Lamil na zaune akan kujerar da aka tanada ma sa ya na duba takardun da sai confusing ɗinsa
suke, kallon giant guy ɗin da ya shigo ya yi sai da suka ƙara gaisawa, sannan a hankali ya ce '' We found
something unusual, the scan bayyana womb...... Amma ba mu ga fetus ba. The cavity is blocked by a
mass, we can't figure out what's actually wrong with your wife Sir.'' ya ƙarashe maganar tare da kallon
Hydar ɗin da idanunsa suka yi ja.
Sai da Hydar ya ja wani kalar numfashi sannan ya ce ''Mass kuma?, mai kuke nufi da Mass ɗin.?"
Sai da Doctor ɗin ya ɗan numfasa sannan ya ce ''Mass a nan na nufin wani abu ne da bai dace ba a cikin
mahaifa, yana iya zama cyst, growth, ko wani abu da ke mamaye wuri. Mass na iya leading to Cancer,
amma ba zamu iya tabbatar da hakan ba tukunna, Wannan shi yasa muke buƙatar ƙarin tests.'' doctor
ɗin ya ƙarasa maganar ya na ƙara ƙafe Hydar da ido.
Wani kalar firgici ne ya ziyarci Hydar ɗin a lokaci ɗaya, cikin wani kalar murya wadda bai san kansa da shi
ba ya ce ''Cancer fa ka ce Doctor.?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe...... ''
''Love is blind.''😌
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 50**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Wani kalar firgici ne ya ziyarci Hydar ɗin a lokaci ɗaya, cikin wani kalar murya wadda bai san kansa da shi
ba ya ce ''Cancer fa ka ce Doctor.?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe...... ''
''Bamu tabbatar ba tukunna.'' doctor ɗin ya faɗa tare da gyara eye glasses ɗinsa.
Wani kalar iska Hydar ɗin ya furzar haɗe da ficewa daga office ɗin, direct ɗakin da aka ajiye Liya ya nufa.
Ta na kwance yadda ya barta, ba ta canza position ɗin kwanciyarta ba, a hankali ya tako zuwa inda take
tare da zare first aid ɗin da aka ba ta, ba ta da wani ƙarfin hana sa abin da ya yi niya, saɓa ta ya yi a
hannunsa ya fice daga hospital ɗin ba tare da ya kalli Nurses ɗin dake ta ma sa magana ba.
A hankali yake driving har ya ƙaraso Babban hospital ɗin birnin Kano, wato Aminu Kano teaching
hospital, dake ya san wani doctor a hospital ɗin saboda same school suka yi da shi, hakan ya sa akai
saurin fara gwaje gwajen da ya dace a yi a kanta, tare da ba ta injection domin ta samu bacci, dan har
ƙarfe sha biyun dare ya yi kuma babu wani ci gaba da aka samu.
Around 12:30am results ɗin suka fito, thesame with na wancan hospital ɗin, kuma abin mamaki wannan
na nuna Cancer mai ƙonar da jini ya na yawo a jikinta, wani kalar tashin hankali Hydar ya shiga a wannan
daren wanda bai taɓa ganin kalarsa ba.
Hannunsa ya kai jikinta ya ji wani mugun zafi fiye da na ɗazu, hakan ya sanya shi saurin janyewa tare da
kallon kyakkyawar fuskarta da ya ɗan rame a lokaci ɗaya.
So yake ya kira iyayen su ya sanar da su amma he can't do that duba da yanayin daren da ya tsala.
Wayarsa dake jikin gadon da take kwance a kai ya ɗauka tare da duba notification ɗin telegram ɗinsa tun
bayan da ya yi wa Amir reply lokacin da ta zo ɗaukansa.
Message ɗin Amir ya fara karantawa kamar haka ''Hey Man, barka da shigowa, hope ka huta sosai yadda
ya dace, na je hotel na ka kuma ban gan ka ba, still naje gidanka Salimah ta ce min ba ku dawo ba, hope
say you did nothing to that girl OOO.'' wani kalar jaa idanunsa suka yi tare da dannawa Amir ɗin kira.
Sai da ya yi ring huɗu sannan ya ɗaga, ''Assalamu alaikum, kai ba ka yi bacci ba za ka takura rayuwata
ko.?" Amir ya yi maganar da magagi.
Hydar bai yi magana ba sai wani kalar ajiyar zuciya da yake saukewa, a can ɓangaren Amir wani kalar
bugawa zuciyarsa ta yi, tare da faɗin ''Hydar hope babu abin da ka yiwa yarinyar nan.?"
Still bai yi magana ba ya yiwa Amir ɗin banza ya cigaba da ajiyar zuciyarsa.
''wai wannan wani kalar iskanci ne Hydar, ka yi min magana mana.''
Juyar da kansa Hydar ya yi tare da kallon Liyana da take numfashi da sauri da sauri, idanunta na saukar
da wani hawaye mai zafi, jikinta na wani kalar kakkarwa.
Hakan ya sanya shi fashewa da wani kalar kuka tare da buga kujerar da yake kai ya ce ''Amir zan rasata,
Amir mai sa sai na so Abu nake rasa shi?, why?, Wallahi Amir kai ma ka san kalar son da nake yi ma
Liyana, please talk to her, tell her not to leave me, idan na rasa Liyana zan iya rasa raina.'' ya yi maganar
ya na ƙara kallon yadda kakkarwan ke ƙaruwa kamar jijjiga.
Ganin hakan ne ya sanya shi kiran sunan doctor a ɗimanche, tare da cilli da wayar hannunsa ganin ta na
ƙoƙarin faɗowa.
Sauri ya yi ya kama hannunta, ya ji tafin hannunta na wani kalar zafi, iska ya yi ta hura ma ta, dan shi ya
rasa ma abin da ya dace ya yi.
.
Doctors biyu ne suka shigo haɗe da saka ma ta Oxygen, sannan suka ƙara ba shi ƙarfin gwiwa akan za ta
rayu because za'a magance shi duk da cancer is not a curable disease.
Washegarin ranar da sassafe Amir ya kira Abbhu da Maami, sannan ya sanar da Umminsa duk abin da
yake faruwa.
Kiran Hydar ɗin ya yi tare da tambayarsa hospital ɗin da suke wanda a take Hydar ɗin ya sanar da shi
haɗe da kashe wayarsa ya ajiye shi a gefe ya na kallon yadda take kwance cikin kayan patients da kuma
yadda a take ta yi wani kalar haske.
Doctor ɗin dake gaban sha'anin Liyanar ne ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa, ya sanar da shi
cewa suna da buƙatar jini.
Sai da ya kallesu sosai sannan ya ce wa doctorn da a ɗauki jininsa, bayan an yi gwaje-gwaje aka tabbatar
jininsa na da cikakkiyar lafiya, sannan aka ɗauka.
Wayarsa ce ta fara ringing hakan ya sanya shi zira hannunsa a aljihunsa tare da ɗaukan wayar da number
Mami yake bayyane a kai, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan a hankali ya ɗauka tare da kara wayar a
kunne tare da faɗin ''Assalamu alaikum, Mami ina kwana.'' ya yi maganar a ɗan sanyaye.
''Ban kwana ba Aliyu, wannan ai iskanci ne, ta ya za'a ce daughter babu lafiya amma kuma ba zaka iya
sanar da ni ba.?" Ta yi maganar a ɗan tsawace.
Sai da ya nisa sannan ya ce ''Ba na son na tayar wa da kowa hankali ne shiyasa ban faɗa muku ba, buh
I'm sorry Mami.''
''A wani hospital kuke?."
''Malam Aminu Mami."
Katse wayar ya yi tare da kallon agogon dake ɗaure da tsintsiyar hannunsa.
><><>>•••••••••<><><
Zaune take a kan sallaya hannunta riƙe da carbi, idanunta na zubar da ƙwalla, cikin takunsa na mazan
jiya da na yau, ya shigo ɗakin cikin shigarsa wanda ya dawo da su daga masallaci.
Ƙarasa shigowa cikin ɗakin ya yi tare da zama a edge ɗin gadon ya na kallon yadda ta ɗaga hannayenta
ta na addu'a, hakan ya faranta ma sa ransa sosai.
A hankali ta tashi tare da kallon Nabil haɗe da faɗin ''Yaya ba ka kirata ba ɗin.?" Ta yi maganar ta na mai
naɗe sallayarta.
Murmushinsa ya sakar ma ta mai kyau tare da faɗin ''Ina kwana Aunty Iki.'' waro idanunta ta yi tare da
faɗin ''Yaya ina kwana.''
Janyota ya yi jikinsa sannan a sanyaye ya ce ''Liyana