Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
da ɗauke kai ta cigaba da lazimin ta.
''Neneh dan Allah cewa masu aikin ki su haɗa min gireba ko ke da kanki ki haɗa min, na biya AFSHKUR
BITES a kulle shagon ya ke kuma bayansu ke kaɗai ke iya gireba mai daɗi kin ji my Neneh.''
Sai da ta Idar lazimin sannan ta ce ''Sannu maryamu uwata sannun ki yemu, wallahi abin na ki iskanci ne,
wallahi iskanci ne, ni dai a wurinmu da safe ake wannan.'' bata ƙara bi ta kan Liyana ba.
Ita ma dai da ta ga ba ta tanka mata ba ta ɗauki wayarta tare da shigewa ɗakinta.
Ko da dare ya yi cikin shirin ta na kayan bacci ta fito purple color wanda ya amshi jikinta ga wani kalan
glowing da fatarta ke yi, she looks soo take a way, ƙafarta sanye da slippers na bacci masu kyau da
taushi.
Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ne ke dinning wan da ya gaji da haɗuwa.
Ko da ta ƙaraso wurin kowa ya hallara ita kaɗai ake jira, bayan sun gama ci Neneh ke faɗin "Liyana kike
ko Libiya, ma za ɗauko min mayafina muje gidan Alhaji kyari na mai barka da dawowa, duk da dai
mutumina baya nan amma sai ki saba sosai da sirikan na ki."
"Jiddah ka shiga tsakanina da matarka?."
Tana faɗan haka ta cigaba da shan fruit salad ɗinta.
Murmushi kawai yayi tare da ɗaukan walking stick ɗinsa ya koma ɗakinsa.
Matsowa Neneh ta ƙara yi kusa da ita tare da yaficota ta ce " kin ga yaron nan da nake faɗa miki ƙaff
Nigeria babu wanda ya ke da arziƙin kyari, ki ajiye kai wallahi ki ci arziƙi, kin ga, kuma fa wallahi ƴaƴansa
ma kaff duk sun ci sun tada kai, barimma wan da na ke gaya miki.
Ga mahaifiyyarsu mai kirkin tsiya kusan kullum sai ta shigo nan ta gaida ni kuma har ta tafi gwiwarta a
ƙasa kaman mai neman gafara, ai in gayamiki matar nan ta yi, amma fa mahaifiyyarta Yarabawa ce ita
Khairat ɗin amma akwai sauƙin kai wallahi."
Earplugs ɗin ta ta jona da wayarta ta kunna waƙar _RUSH _ na _ayra star_ ta cigaba da bi tana nishaɗi
tare da tashi da ga wurin Nenehn gaba ɗaya.
Neneh ta sa ki baki hangangan ta na kallon Liyana ta ƙara cewa " ai wannan iskanci ne, ni dai a wurinmu
da safe ake wannan, abin da kike min Allah ya kawo ƴaƴanki su yi wa Ikimat., kiji in da daɗi.
Mai farar fuska shiyasa duk wan da ya ganki ba ya son auren ki saboda baƙin hali, ni da na ke son ma na
kaiki gidan daula, shi ne kike min haka, kya tsofe a gida wallahi ba miji, ni dalla gafara min tun da ba
falon mijinki bane ba."
Ta faɗa tare da zama a kusa da Liyanar a 2sitter.
"Neneh na tambaye ki mana za ki bani amsa?." "Mai zai hana." Ta faɗa tare da washe baki.
"Dan Allah bakin ki ba ya iya shiru da surutu mara jigo da asali?, kusan one hour da cin abinci amma tun
ɗa zu sai ihu kike min for once lemme enjoy this moment mana, na tabbatar in ba ki je police station yafi
sau goma lokacin da kike budurwa saboda surutun ki kan iya raba auren da ba soyayya . Mata sai surutu
mara sababi, ni sai da safe."
"Wallahi Ikimat ce zata je police station ba ni Ajiddeh ba, kiyi ta rashin kunya, ƙila a haka kika kori mijinki
bamu sani ba."
"Kya ji da shi, wallahi kika ƙara min maganar ɗan kyari sai an buɗe mana fili da ke a gidan nan."
Baki hangame Neneh ta ce"Ni dai a wurinmu da safe ake wannan wallahi."
"Ko da asuba ne za ki san shayi ruwa ne."
"Duka na za ki yi?."
"Za ki gani a aikace." Daga haka ta kulle ƙofarta har da da key......
After 2 Weeks
Liyana ke zaune a parlour ta na ta jiran Lilian ta kira ta za su fita siyayyan birthday ɗin ta.
Sai kusan ƙarfe biyu sannan Lily ta kirata, ta shiga ɗakin Neneh ta sanar da ita sannan ta nufi hanyar fita
daga parlourn tare da faɗawa driver ɗin inda zai kai ta.
Bayan sun ɗauki Lily kam boutique suka nufa sukai siyayya sosai sannan suka nufi wurin pictures.
Sai yamma liƙis ta dawo gida shi ma ta na wanka kawai kwantawa bacci ta yi dan tana off day ɗin sallah,
kuma ba ta son takurar baiwar Allahr nan.......✍️
Ku yi manage please Bacci nai sosai yau kuma bana son na bar ku babu update.
THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12pam follow for more 🎊🫂📚
> EDITED 🤍> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
> MY YOUTUBE CHANNEL LINK👇
https://youtube.com/@pendingamaryasbookcorner?si=ua40w5qJhdjEpXRT
> THE REGRET COMMENTS SECTION ✅👇
https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=ac_t
> PENDING AMARYA'S PEN WORLD 💎📚👇
https://chat.whatsapp.com/BimAgGC0XKpAObEGTBJf3x?mode=ac_t
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
She just wanna think of me like a bee 🐝
Hmmm uthman bee, if we're meant to be we gonna be🤗
Hmm my melanin, ta buɗe zuciyarta na shiga soo she got my time sabida na isa tell me what's your
name 💎
Ta ce min A'ishah let's have a ride na ce mu ɗan fitaa 😅
ta so come make i run your overall 🤭🤫 ..........
The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko
ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!
Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂
Mallakar Pending Amarya ce_
NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl
THIS PAGE IS DEDICATED TO MY DEAR SIBLINGS MY STRENGTH
Every page I write carries a piece of our laughter, our fights, and our unshakable bond
This story is not just mine it's ours 🤗🤝
CHAPTER EIGHT : BEIJING 💎
_PENDING AMARYA _
Page 17
Sai yamma liƙis ta dawo gida shi ma ta na wanka kawai kwantawa bacci ta yi dan tana off day ɗin sallah,
kuma ba ta son takurar baiwar Allahr nan.......✍️
ILY ta kira suka yi hira har da Ammi sannan ta kwanta bacci mai nauyi ya ɗauketa.
Ɓangaren su Ammi kuwa tun ranar da Abbhi ya dawo su ka rasa gane ta kansa, ga faɗan da ya kewa
mutane na babu gaira babu dalili.
Ita a tunaninta ko dai gamo ya yi da aljanu dan wannan nutsuwar ta sa dukka ba rabi duk ya yi wani.
Ga Rufaidhat da ta tisa shi a gaba ko bacci ya ke sai ta tashe sa ya rasa gane meke damun Rufaidhat ta ke
wannan hali.
Ɓangaren Ilham kam ta samu ta fara zuwa school dan itama rijiyar zaki ta ke son dawowa idan har
komai ya kankama amma in tuna da Ammi sai ta ji duk ta fasa saboda barin Ammi gida ɗaya da
sheɗaniyyar matar nan masifa ne.
China, Beijing, Shunyi district :
Kwance ya ke akan lallausan gadonsa da ke shinfiɗe da _ peacock Alley _ bedsheets na alfarma.
Jikinsa sanye da pyjamas white color, idanunsa sanye da sleep mask ma su kyau.
Duvet ɗin jikinsa ya yaye a hankali tare da diro da ƙafafunsa ya lalubi wayarsa da ke kan bedsides.
A hankali ya gama zare sleep mask ɗinsa ya kai dubansa ga wayarsa wanda time ke nuna masa 9:00
saura two hours jirginsa ya ɗaga zuwa Nigeria.
Da sauri ya ajiye wayar tare da shiga changing room ya sanya bathrobe ɗinsa white color.
Ya nufi toilet ɗin da marble tiles ke malale a ƙasa, komai na toilet ɗin is golden color, a gaggawce ya yi
wanka haɗe da brush.
Ya fito sanye da bathrobe ɗinsa, sannan ya shirya cikin _ Tom Ford Suits _ black color da ya amshi jikinsa
sosai, sannan ya zaro agogon _ Rolex Explorer ll _ daga valet tray ɗinsa ya manna a tsinsiyar hannunsa
da ke da yalwar kwantaccen gashi da sai sheƙi ya ke. Shoe shelf ɗinsa da ya ke cike da manyan luxury
shoes ya zaro ɗaya daga cikin _ John lobb_ shoes ɗinsa da ya ke sawa a kan suits, tare da feshe jikinsa da
turaren _ Valentino haɗe da Giorgio Armani.
Ta ke wani kalar sihirtaccen ƙamshi ya mamaye ɗakin, kallon kansa ya sake yi a wall mirror ɗin da ke
ɗakin tare da shafa gemunsa da ya gaji da shan gyara, wani kalar malalacin murmushi ya sakarwa kansa
da ya ƙara mai kyau da kuma tsari.
LV trolly ɗinsa da ke shirye da kayansa na amfanin yau da kullum ya janyo a hankali cikin aura ɗinsa ya
fara ta ko wa cike da izza, ya fito daga master room ɗin nasa ya nufi hanyar living room.
Ko da ya fi to daga Master room ɗin na sa ƴar aikinsa ce a tsaye ta na goge dinning table ɗin da ke
dinning area, cikin muryarta mai sanyi ta ce "Xiānsheng, zǎoshang hǎo." (Good morning sir).
Amsawa ya yi a taƙaice sannan ya ce mata ta tabbatar kullum zata gyara mai gida sannan ba zai daɗe ba
zai dawo.
Da toh ta amsa mai sannan ta cigaba da gyaran gidan nasa.
Ko da ya fito daga entrance ɗin gidan, parking lot kawai ya nufa, tare da shiga cikin motar da ke da kyau
da tsari ya nufi hanyar office ɗinsa domin submitting some documents kafin ya bar ƙasar.
Ko da ya ƙarasa compayn, companyn na da kyau da girma, komai na ciki contains white color, ga ko ina
wani kalar securities aka baza, ko wani uniforms nasu na tattare da logo na Company da kuma sunansa
H&K Ventures.(Hydar&Kyari ventures) H is for Hydar, K is for Kyari, which is his father, saboda
mahaifinsa na da share a cikin companyn.
Staffs and local staffs sai gaida sa su ke, sai dai ya kaɗa kansa ya cigaba da tafiya har ya ƙarasa cikin
ƙantamemen luxury office ɗinsa da ke shaƙe da office equipment.
A natse ya zauna tare da danna bell ɗin da ake kiran secretary da clearners, ta ke wata ƴar matashiyyar
budurwa wadda daga ganin ta ka san Chinese ce ta shigo, ta gaida sa tare da tsayawa agabansa,
"Coffee." Shi ne abin da ya furta cikin muryarsa mai amo da taushi kamar algaita. Sannan ya ƙara da
faɗin a kira masa manager da assistant manager (shi CEO ne akwai manager da kuma assistant manager,
su ne masu kula da lamarin compayn idan baya nan).
Ba'a fi minti biyar ba su ka shigo. Bayan sun zauna aka kawo musu coffe gaba ɗaya sannan suka zauna
can gefe da ya ke kama parlour acikin office ɗin CEO ɗin tare da CEO.
Cikin muryarsa mai cike da nutsuwa da izza ya ce " Yau zan yi tafiya, a kula da companyn nan sosai, kar a
ɓatawa manyan dealers rai in na dawo na tarar da hakan You people will be fired, am I clear? ." "Yes
sir."." Sannan manyan dealers na mu kamar su Adafar Ventures na Singapore, da sauran dealers ɗin a
haɗa musu fita shakatawa da iyalansu, ga documents ɗin da za ku buƙata na bar ku lafiya.". Sai da su ka
amsa masa, daga haka ya bar office ɗin gaba ɗaya tare da bawa driver car key ɗinsa ya kai sa Beijing
Capital International Airport (PEK).
A motar ma babu wanda ya yi magana har ya ƙarasa drivern ya fito masa da Luggage ɗinsa, cikin
mintuna ƙalilan jirginsu ya ɗaga.
A cikin jirgin ma wine kawai ya sha sannan ya ci hamburger, jirginsu ya cigaba da lulawa.
Ɓangaren Liyana kuwa bayan ta tashi daga bacci tai brush sannan ta ɗora da wanka ta ci kwalliyarta cikin
shigarta na jeens trouser da black silky long sleeve da ya lafe a jikinta.
Kitchen ta nufa ta bawa masu aiki order na pepe soup ɗin kidney da kuma French fries and egg.
Daga haka ta nufi ɗakin Neneh can upstairs, sai da ta gaida Nenehn sannan ta zauna kusa da ita, tace "
Neneh lafiya ba ki fito falo ba?, ko dai ba kya jin daɗin jikin ki ne?." " Wallahi ba na jin daɗi, kai na ciwo
ya ke wallahi ni da ina da kishiya sai na ce ko ita ta aiko min da bama -bamai, wallahi ba ki ji kai na ba,
Rafiƙ in zai fita business ɗin sa zan bi sa ya ajiye ni à asibiti." "Ayya Allah ya sawwaƙe ni na zata ma
ƙaruwa za mu yi in fara tara kayan baby."
Sai da Neneh ta ƙanƙance ido ta kalleta sosai, sannan ta ce "Ni wallahi ban san ke ɗin ma kin fita daga
yarinya ba sai yau, dole na wa Rafiƙ magana a yi sauri a kau da ke kafin ki kawo wa mutane abin kunya,
wallahi wannan iskanci ne, ni dai a wurinmu da safe ake wannan."
" Ai da safe mu ke magana yanzu ba dare ba ne ba."
" Libiya ki ke ko Liyana ki fi ta ido na na rufe."
"An ƙi a fita ɗin, ki zo ki wuce in kin je ki ce a miki test ƙila a dace ma ba ki sani ba." Ta faɗa tare da
gimtse dariyarta.
Fitowarta daga ɗakin Neneh ke da wuya, Salimah ta jera mata komai a dinning ta na cikin ci Jiddah da
Neneh su ka sauko cikin shigar alfarma.
Tana zaune a dinning ɗin tai wa Jiddah barka da safiya, sannan ta kalli Nenehn ta ce " Allah ya raba
lafiya." Harara kawai Neneh ta watsa mata sannan tai gaba suka fita daga gidan.
Bayan ta kammala cin abincin, ɗakinta ta nufa tare da dailing number Sultan, su ka sha soyayyarsu, cikin
mauryarsa mai daɗin sauraro ya ce " Big Brother na dawowa yau zuwa next week sai a fara maganar
auren, tun da kin hana ni zuwa gidan Grand ma ɗin ta mu, kin dage a school za mu na haɗuwa." " Jehova
of Nazareth", is not like that oo, kawai ban iya kwantace ba." "Bana hanaki ambatan Jehova ba ? Is like
idan mun yi aure zan hana ki ƙawance da Lilian....."
" Sorry Habibi bazan ƙara ba." Daga haka su ka shiga wani hiran.
Ko da su ka kammala wayar arround 1 O clock, wanka ta ƙara yi tare da sa wani Classic Abaya ɗinta milk
and brown color, sannan ta sa hula brown, tare da zura wani slippers masu kyaun gaske, da ya ƙarawa
ƙafarta kyau.
Message ta gani a wayarta na Sultan kamar haka "come online, I wanna talk to you dear."
Da murmushi a fuskarta ta shiga what's app tare da shiga chat ɗinsu, su ka fara chatting, sannan ta nufi
hanyar parlour ta zauna a ɗaya daga cikin lafiyayyun kujerun parlourn.
Tana chatting ta na kurban strawberry Hollandia ɗin da ke kan side table ɗin kujerar falon.
Hankalinta gaba ɗaya ya na kan chatting ɗin da take yi.
Sallamar da ta ji ne har sau biyu da kuma salon canzawan da ƙamshin ɗakin ya yi shi ya bata daman
ɗagowa da kanta tare da kai dubanta wurin wadda ke shigowa cikin parlourn.
Mata ce ko kuma mu ce uwace ta shigo cikin gidan cikin shigarta na Atamfa Exclusive da ya mata kyau
ɗinkin doguwar riga mayafin da matar ta yana akanta da ya ƙara mata kyau kuma ya fito da siffarta na
uwa sannan baƙin mayafin ya ƙara fitar da colorn fatar ta ruwan ƙwai.
Cikin sassanyar muryarta ta ƙara yin wani sallama a karo na uku, sannan liyana ta amsa tare da faɗin
"Sannu da zuwa Maa, ina wuni." Tare da yi mata alamar zama akan ɗaya daga cikin kujerun masu kyaun
gaske.
Murmushi mai kyau matar ta sakar mata tare da amsa mata da " Lafiya lau ƴammata, ya kike?."
" Lafiya lau Maa." " Neneh na ciki?." "A'a ba ta nan ta fita tun safe." Mai aiki ce ta zo tare da faɗin"Aunty
Liyana mai za'a kawowa Mamin?." " Bar shi zan zo na haɗa ma ta."
Daga haka ta shige kitchen ɗin tare da haɗa mata abubuwan motsa baki.
Table ta janyo tare da ajiye tray ɗin a kai. Godiya matar da mai aiki ta kira da Maami ta mata sannan ta
ce " Ina Nenehn ta je?." " Ai tun safe ba ta ji daɗi ba shi ne mijinta ya kai ta hospital." Ɗagowa matar ta
yi, Liyana tai sauri ta ƙara faɗin " Jiddah kai." Murmushi matar ta sake yi sannan ta ce " Subhanallah,
Allah ya sa kaffara ne, in ta dawo ki ce ma ta na zo amma zan dawo in ta dawo gida, ki ce mata Mamin
Sultana ce ta zo, ya sunanki ƴammata?." Cikin sanyin muryarta ta ce " Fatima." Ma sha Allah fatiti." Sai
da ta sha ruwan sannan ta ce mata ta tafi ta kula da kanta.
Toh kawai Liyana ta ce ta na jin matar ta kwanta mata a rai, ga nutsuwar matar mai ratsa jini, dan ita
kam matar ta yi mata kwarjini sosai.........✍️
Akwai ƙura faa a gaba 😂😂
> THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> Pending Amarya's book corner
Extraordinary Everyday 🦋 posting channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
Na saba da ke 😉