Advertisements
Chapter 1 Reading RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN

Author :  HAUWA A USMAN Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 38

1 to 3K   out of 111.2K words

_*RASHIN SANI.......*_




*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```



1⃣



Alhaji GANEZ HARD'O cikekken bafulatani ne usul gaba da baya,
dan kallo d'aya zakayi mishi ka fuskanci hakan,
mutum ne kamili mai cikekkiyar nutsuwa da kamala,
d'an asalin garin Adamawa ne,
yana da matar aure d'aya NISAH,
mace mai hak'uri da dattako, 'yar wan mahaifinsa ce akayi musu auren zumunci,
kuma cikin ikon Allah suna zaune lafiya,
bayan anyi auren su canjin aiki ya kai shi karin Kano, kasancewarsa Police,
a kwalli police barrack aka bashi gida,
amma yak'i zama ya nemi gida a jan bulo (BUK road) ya siya,
ya shirya musu gidan dai-dai gwargwadon k'arfinsa,
gidan yayi kyau ba laifi,
suka zauna da matarshi,
mak'ofcinsa DANISH, mutum ne nutsatse mai cikekkiyar nagarta,
shima yana da matarsa d'aya ERUM, mace mai mutunci da karamci,
su 'yan asalin garin Kano ne,
a k'aramar hukumar Yakasai zama ne ya kai su jan bulo,
lokacin da Ganez ya sauka a garin Kano ta tabo, bai san kowa ba,
balle kuma matarsa Nisah, a masallaci Ganez da Danish suka fara had'uwa,
inda Ganez ya gabatarwa da mak'ocin nasa kansa a matsayinsa na bak'o,
hannu bibbiyu Danish ya karb'e shi, cikin karramawa, tun daga wannan rana zumunci da alak'a mai k'arfi ta shiga tsakanin su,
haka ma matan su Erum da Nisah,
harta kasance basu da kamar junansu a duniya, kowa yana tsananin k'aunar kowa, babu wanda zayyi abu batare da sanin d'ayan ba.



Shi Danish d'an kasuwa ne, ba aikin gwamnati yake ba,
a kantin kwari yake da shagon atamfofi,
sosai alak'ar Danish da Ganez tayi k'arfi ta wuce tunanin mai tunanin dan jama'a da yawa suna tsammanin 'yan uwane,
bayan shekara d'aya da zuwan Ganez Kano, Nisah da Erum suka haihu rana d'aya,
duka yara maza suka haifa, sosai Danish da Erum sukayi farin ciki,
ranar suna d'an Ganez da Nisah yaci sunan HAMRAZ,
d'an Danish da Erum yaci sunan RAWAN,
yara suka taso cikin so da k'aunar iyayen su, duk bin kwakkwafin mutum bai isa ya gane ga d'an Danish ko Ganez a tsakanin Rawan da Hamraz ba,
yadda suka ga iyayen su suna matuk'ar k'aunar junan su haka suma suka taso da san junan su,
babu wanda ya isa ya tab'a d'aya,
komai nasu tare sukeyi dai-dai da kayan sawa iri d'aya suke yi,
kan Rawan da Hamraz a had'e yake sosai fiye da tunani,
idan d'aya na kuka shima d'aya sai yayi, ko rashin lafiya d'aya ya kwanta d'ayan ma sai yayi,
abin nasu har mamaki yake bawa mutane.


Haka suka girma har suka kai munzalin samari,
a lokacin Ganez yayi ritaya, dan girma ya d'an fara kama su,
Hamraz ya karanci medicine ya zama cikekken Doctor,
Rawan kuma ya karanci Low ya zama cikekken Barrister,
a lokacin ragamar gidajen su ta koma hannunsu,
babban fili suka siya suka ginawa iyayen su da su kansu katafaren gida wanda shine zai zama HARD'O FAMILY HOUSE,
sunyi tsarin gidan mai kyau, part d'in Ganez da Nisah, daban,
haka ma Danish da Erum daban,
sai suma sukayi part d'in su daban-daban,
da kuma wasu part d'in wad'anda babu kowa a ciki a k'alla zasu kai 7,
rana d'aya Hamraz da Rawan sukayi aure, suka auri 'yan biyu uwarsu d'aya uban su d'aya,
Hamraz ya auri Hassana
Rawan ya auri Usaina.


Rawan da Usaina yara uku suka haifa,
ZAFRAN shine babba sai k'aninsa AARIB, da k'anwar su mace AROOS,
Hamraz da Hassana yaran su biyu, IDRAK da k'aninsa ZIYAD,
har sun cire ran k'ara samun haihuwa ,
saboda a k'alla sunyi 7yrs,
rabon su da haihuwa,
Allah ya kuma bawa Hassana da Usaina ciki a lokaci d'aya,
a rana d'aya suka haifo yaran su mata,
kyawawan gaske san kowa k'in wanda ya rasa,
Ganez da Danish suka ce tarihi ya maimaita kansa,
ranar suna aka sakawa 'yar Hamraz *SANAH*
'yar Rawan *KHULUD*.


Yaran suka taso cikin matsananacin so da k'aunar junansu,
fiye da yadda iyayen su suka taso dashi,
babu abinda Sanah tafi so a rayuwarta sama da Khulud,
haka itama Khulud d'in bata san komai sama da Sanah,
basa had'a san da suke yiwa junan su da komai a duniya, suna k'aunar junan su fiye da komai da kowa,
tun suna yara k'anana bambamcin halayya da d'abi'u suka bayyana,
a tsakanin su dan ita Sanah tana da zafinzuciya gata da tsiwa da fad'a,
had'i tsokana da rawar kai,
ita kuma Khulud she's so silent,
kwata-kwata bata san yawan hayaniya da rigima,
dan ita magana ma ba damunta tayi sosai ba, sab'anin Sanah dake da shegen surutu kamar me,
idan har kaji surutun Khulud to da Sanarta ne dan muskilar gaske ce,
indai bada Sanah ba, ko a gidan su sai a yi tayi mata magana bata amsawa,
ita Khulud ko irin b'arnar nan ta yara bata yi,
amma oga Sanah akwai b'arna da k'iriniya gata bata jin magana,
makarantarsu da ajin su d'aya haka ma desk d'in su d'aya.


Duk duniya babu wanda ya isa ya tab'a Khulud a gaban Sanah,
koda kuwa su kan su iyayen nasu ne,
haka ko'a makaranta malamansu basu isa su tab'a ta ba,
muddin kuwa aka yi kuskuren tab'a ta to ranar ba zaman lafiya,
itama Khulud duk da rashin fad'a da san hayaniyarta, idan aka sake aka tab'a Sanah yanzu zata fututtuke ta rufe ido tayi ta ruwan bala'i,
komai nasu iri d'aya ne sak, har pant da ribbon,
ko color basa yarda a bambanta musu.


Ko laifi Khulud tayi sai Sanah tayi saurin cewa ita tayi,
haka zasuyi ta jayayya wannan na cewa shi yayi wannan ma na cewa shi yayi,
har wanda akayiwa laifin ya gaji ya hak'ura.


Sanah da Khulud suna wasa a tsakiyar compound d'in gidan su,
Sanah ta kalli Khulud tace " Ulud (dayake haka take kiranta, dan da wuya ta fad'i full name d'inta),
idan mun girma mun gama secondary me zaki karanta?


Dariya Khulud tayi had'i da cewa " tab ai ni ban sha'awar karatu mai zurfi,
dana gama Secondary school shikenan na gama karatu har abada,
kallanta Sanah tayi kana tace " tab ai ni ko sai naga k'arshen biro da takarda,
inasan nayi karatu mai zurfi sosai,
Khulud tace " ai dama ke kin saba banbanta mana ra'ayi, tayi maganar tana zumb'uro baki,
Rawan da Hamraz na tsaye suna kallansu suna jin abinda suke cewa,
Hamraz yace " da alama 'yata Khulud gado zatayi,
kallansa Rawan yayi yace " gadon me?


Dariya Hamraz yayi yace " gadon Aure da wuri mana,
dariya shima yayi yace " amma ni tawa 'yar boko zatayi,
"a'a karkace haka dan muna iya sauya muku ra'ayi,
Rawan yace " a'a ba wannan maganar,
kasan komai ra'ayin mu kuke bi,
dariya Sanah tayi tace " shikenan karkiyi kuka my Ulud na daina,
Ulud ta kalle ta da sauri tace " da gaske?


"Sosai ma, da gaske nake, "yauwa har kinsa naji dad'i cewar Khulud,
mik'ewa Sanah tayi tana cewa Khulud ni fa yunwa nake ji,
dariya Khulud tayi tace " acici kawai, muje na raka ki kici abincin,
" a'a muje na raka ki gida tukunna sai na tafi,
" a'a ni zan fara raka ki, tukunna,
"to muje cewar Khulud, har k'ofar part d'in su Khulud Sanah ta raka ta,
sannan Sanah tace " to kema muje na raka ki, suka koma part d'in su Khulud,
itama tace " muje na raka ki,
haka sukayi ta zarya suna rakiyar kura,
iyayen na kallan su suna dariya,
Rawan yace " k'uruci gangin hauka.


Yau su Sanah da Khulud suka kammala zana jarabawar fita daga primary school,
(Common in trace Exam),
cikin farin ciki suka dawo gida,
driver nayin parking suka fito da gudu suka nufi inda iyayen ke zaune,
da gudu suka fad'a jikin su, Sanah tace " Abbu sun gama exam yau,
murmushi yayi had'i da shafa kansu yace " masha Allah,
Ubangiji ya bada sa'a, Hamraz yace " da fatan dai anyi k'ok'ari sosai?


Khulud tace " mun dage sosai Dide,
"Rawan yace to yanzu wacce school kuke san zuwa?


Cikin mud'i Khulud tace " Boarding Abbu,
da sauri Sanah ta kalle ta tace " boarding kuma Ulud?


"Eh mana ko baki san boarding?

Shiru Sanah tayi tana kallan yadda Khulud ke farin ciki,
gashi ita kwata-kwata bata so ko sha'awar boarding school,
asalima ita ta tsani boarding school,
kallanta Khulud ta kuma tayi tace " ai boarding zamu ko?


Murmushin yak'e Sanah tayi kana tace " eh boarding zamu,
Abbu da Dide sun lura da Sanah bata san boarding,
dan haka Abbu ya rik'ota yace " Auta kodai day zakiyi?


"No Abbu nima boarding d'in zani,
tunda Ulud can take so, bana san abinda zai raba ni da Ulud d'ina,
ajiyar zuciya Dide ya sauke a hankali yana kallansu had'i jinjina irin k'aunar da suke yiwa junansu,
shafa kansu Abbu yayi yana murmushi yace " Allah ya albarkaci rayuwarku,
Ubangiji ya sanya haske da lumana a duniyarku,
ya k'arfafa dangantarku,
ya inganta alak'arku har abada,
duk wanda zai zama sanadin rabuwar kanku, ko kawo matsala da sab'ani Allah ya kawar muku dashi daga rayuwarku,
gaba d'aya suka amsa da Amin.


A gida bayan sun gama cin abinci sunyi wanka,
Sanah ta d'auko wayar Mamu,
(Mahaifiyarta) tace " Khulud zo muyi game,
"a'a kiyi kawai ni bacci zanyi,
Sanah ta zumb'uri baki tace " nima banyi to,
dariya Khulud tayi had'i da cewa " yi hak'uri kawo muyi,
na fasa baccin, ta fad'a tana mik'a mata hannu, garin Sanah ta mik'a mata wayar,
akayi rashin sa'a wayar IPhone X ta fad'i ta fashe,
ido duk suka zaro dan sun san Mamu bata san wasa,
Mamu dake shigowa parlor ta kalle su taga yadda duk sukayi tsuru-tsuru,
tace " lafiyarku?


Ido Khulud tayi rau-rau kana tace " Mamu kiyi hak'uri ban sani bane wayar ta fad'o ta fashe,
ido Mamu ta zaro, a d'an tsawace tace " wacce wayar, badai wacce na siyo jiya ba?


"Cikin tsoro Khulud tace " ita,
dan Allah kiyi...... tsawa ta daka musu tace " uban waye yace ku tab'amin waya?


Da sauri Sanah tace " Mamu nice na d'auko zamuyi game shine ta sub'uce daga hannuna,
Khulud tace " a'a Mamu nice na d'auko ba ita ba,
Sanah ta kalli Khulud tace " ba kyau k'arya fa, ta juya ta kalli Mamu tace " Allah ni ce ki doke ni amma please karki tab'a Khulud,
itama Khulud tace " Mamu ni ce ba ita bace ni zaki daka ba ita ba,
tsawa ta daka musu, cikin b'acin rai tace " wato ni zaku rainawa hankali ko?


" Dukkan ku sai jikinku ya gaya muku,
kuka Khulud ta saka tana cewa " Allah Mamu nice nayi laifin please karki dakar min Sanah,
itama Sanah kukan ta saka tana cewa " Mamu ni ce ba itaba, karki doke ta,
kai ta dafe dan nema suke su saka mata ciwon kai,
ta kalle su a hasale tace " ku b'ace min da gani, dan tasan ko dukan nasu tayi ba hucewa zatayi ba,
da gudu suka fita.



Computer Girls Sondary School Roni,
aka nemarwa su Sanah,
Khulud nata murna da d'oki,
amma Sanah ko'a jikinta dan banda Khulud babu abinda zai kaita boarding school ,
Abbu ne ya gama musu duk wani shirye-shiryen su na tafiya,
ranar Sunday kusan gaba d'aya Hard'o Family's ne suka raka su,
dayake makarantar akwai islamiyya Dide yayi magana aka sanya su,
sosai Sanah tayi kukan rabuwa da gida.



MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_




*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```



2⃣



Ganin yadda Sanah ke kuka ne yasa itama Khulud yin kukan,
Vice principal na office yaji yo sheshshekar kukan su, a hankali ya d'an tsaya da abinda yake yi had'i da kasa kunne,
dan ya tabbatar, jin sautin kukan su Sanah yasashi mik'ewa a hankali,
ya lek'a ta window dan yaga wad'anda ke kukan,
ganin new comers d'in da aka kawo yanzu ne yasa shi,,,
takawa zuwa inda suke, sai da yayi a k'allah wajen minti 8 yana kallan su,
kafin yace " ku zo nan,
ba musu duk suka mik'e suka nufe shi,
durk'usawa yayi dai-dai tsawon su yace " ku daina kukan,
kar kuyi rashin lafiya kunji?


Kai suka d'aga masa batare da sunce komai ba,
hannunsa yasa yana goge musu hawayen had'i da cewa,
" yauwa good girls, ina san yara irin ku masu jin magana,
da biyya, ku kasance masu haka har girmanku,
kai suka k'ara d'aga masa alamar to,
yace " idan kuna jin magana kuma kuna karatu sosai zan rink'a baku sweet,
kuma zamu zama friends, amma idan bakuyi b'atawa zamuyi,
na rink'a yi muku bulala, "to Khulud tace, cikin sanyin murya,
kansu ya shafa yace " sunanku?


Sanah tace " ni sunana SANAH RAWAN,
ita kuma KHULUD HAMRAZ,
" nice name Malam Jeeb yace,
sannan ya mik'e had'i da rik'e hannuwansu,
ya nufi Office d'in Dispeeling Master dasu,
shiga yayi dasu bakin sa d'auke da sallama,
bayan sun gama gaisawa ne
ya nuna masa su yace " they're new comers, so please ka basu hostel & class,
"Ok sir cewar Malamin da suka iske a office d'in,
Malam Jeeb ya mayar da kallansa ga su Khulud yace " yanzu za'a kai ku d'aki,
ku ci abinci ku huta kunji, thank you Sir,
Khulud tace, har cikin zuciyarsa yaji dad'in maganar Khulud,
dan haka yayi murmushi batare daya k'ara cewa komai ba ya fita.


Kallan su Malam Moli yayi yace " ya sunanku?


Cikin sanyin murya Khulud tace " ni sunana KHULUD HAMRAZ,
ita kuma SANAH RAWAN tayi maganar tana nuna masa Sanah,
bai k'ara cewa komai ba, har ya gama 'yan rubuce-rubucen sa a wasu file,
kana ya d'ago kai yana dube-duben student d'in da zai aika,
amma babu kasancewar weekend duk suna Hostel Area,
wata d'aliba ya hanga ta fito daga staff room,
yayi saurin kiranta, cikin ladabi tazo ta durk'usa a gabansa,
cikin sanyin murya ta gaida shi,
amsawa yayi had'i da bata umarnin ta kira masa House Captain d'in Turaki House data Lamid'o House,
had'i da head girl,
da sauri ta mik'e jikinta na rawa ta fita,
dan duk makarantar tsoran Sir Moli ake yi,
kasancewar baya wasa,akwai shi da zafi, magana d'aya tak yake yi,
sallama sukayi daga bakin k'ofar office d'in, had'i da d'an dakatawa,
sun kai wajen a k'alla minti 3 kafin ya amsa ya basu izinin shigowa,
zubewa sukayi a gaban table d'insa suka ce " good evening Sir,
ko kallan inda suke bayyi yace " fine, a tak'aice,
batare daya kalle su ba yace " new comers ne , ku aje d'aya a Turaki, d'aya a Lamid'o House,
Sanah dake tsugunne a gefe tana kallan iko da miskilancinsa,
tayi saurin cewa " raba mu za'ayi?


Bai kalleta ba balle yayi magana,
Khulud tasa kuka tana cewa " ni dai a'a please kar a raba mu a barmu tare,
k'afa d'aya ya d'ora kan d'aya had'i da kishingid'a ya rufe idansa,
sosai Khulud da Sanah suke kukan kar a raba su a barsu tare,
amma ko kallansu bayyi ba, jin kukan su na neman saka mishi ciwon kai yasa shi bud'e idansa dole,
ido kawai ya zuba musu batare dayace komai ba, kafin ya mayar da kallansa ga House Captains d'in,
jikinsu na rawa suka rik'o hannayen Sanah da Khulud dan sun fahimci irin kallan da MOLI yake yi musu,
fizge hannayensu sukayi had'i da cigaba da kukan su harda bubbuga k'afa,
gigitacciyar tsawa ya daka musu,
had'i da cewa " get loose a hasale yayi maganar,
a tsorace Khulud tayi hanyar fita, dan tsabar ba k'aramin gigitata tayi ba
amma fur Sanah tak'i ko motsi, balle ta fara k'ok'arin fita,
sauran students d'in jikinsu sai rawa yake,
saboda tsabar tsoro, ganin bata da shirin fita ne yasa shi mik'ewa ya hankad'o su waje had'i da cewa " ko uban ku ne yazo nan bai isa yasani abinda banyi niyya ba,sakarkaru kawai,
kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita,
har Sir Jeeb ya jiyo kukan su, yasan Moli ne yasa su kukan, dan kowa yasan halin miskilancinsa,
fitowa yayi yana kallan su kafin yace " oh friends har kunyi saurin sab'a alk'awarin mu?


Cikin kuka Sanah tace " no Sir,
yace " gashi kuwa kuna kuka,
Khulud tace " wai hostel za'a raba mana,
shiyasa muke kuka, dariya Jeeb yayi yace " karku damu ai zaku rink'a had'uwa kullum,
da sauri suka had'a baki wajen cewa " please Sir kar a rabamu dan girman Allah,
yadda sukayi maganar ne sukayi masifar bashi tausayi,
ya d'anyi shiru yana tunanin kafin ya kalli House Captain d'in yace " ku kai su d'aki d'aya,
ku kuma basu kwana d'aya, and please ku kula dasu,
Ok Sir suka ce,
da sauri Sanah da Khulud suka fad'a jikinsa suna cewa " thank you so much Sir,
a Lamid'o House aka ajiye su, aka basu gado da kwana, Halan itace House Captain d'in Lamid'o House,
sai da ta nunnuna musu komai da ko'ina sannan tace musu " daga yau na zama Auntyn ku, duk abinda kuke so ku tambaye ni kai tsaye, kunji ko?


"Eh suka ce had'i dayi mata godiya,
washe gari Monday da wuri Halan ta shirya su Sanah da Khulud,
suka tafi assembly gudun kar suyi late,
bayan an gama assembly an watse,
Halan ta kama hannun su ta nufi b'angaren JSS Classes,
a hanya suka had'u da Moli, Halan tayi saurin zubewa tana gaidashi,
ko kallanta bayyi ba balle ya amsa,
sai ma uwar harara daya watsawa su Khulud,
Sanah tace " wai Aunty Halan dole sai mun gaida wannan miskilin mutumin mai taurin kan tsiya ne?


Baki Halan tayi saurin toshe mata,
had'i da cewa " rufa mana asiri Sanah kar yanzu ki ja mana bak'ar wahala,
baki Sanah ta turo had'i da cewa " Allah Aunty ganin kuna tsoransa ne yasa shi yake yi muku haka,
Halan tace " ni dai please kiyi shiru dan jine dashi kamar zomo,
Sanah tayi tsaki had'i da juyawa,
aiko karaf idanta ya sauka cikin nashi,
yayi tsaye hard'e da hannu a k'irji yana

1 / 38