Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
ana nuna k'arfi akan mace?
" Idan k'arfi kake da buk'atar nunawa kaje ka tari maza 'yan uwanka mana,
amma saboda kai lusarin namiji ne,
wanda ya rako maza duniya,
wanda bai san mutunci da k'imar kansa ba,
bai kuma san darajar da Allah yayiwa 'ya mace ba,
shine har kake fiffik'ar dukan mace,
Hanash yace " au kai har maganar k'ima da sanin darajar kake yi?
"Kai yanzu inda kasan kunya har zaka kalle ni kayi man maganar sanin mutuncin kai,
lalle kamm!
kodan dama ance 'yan iska basu data ido,
banzaye 'yan iska fasik'ai kawai,
wad'anda basu da aikin yi sai yad'a b'arna a doran k'asa,
then da kake cewa inda nasan waye ubanka banzanyi marmarin ganinsa ba,
waye shi!?
Kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " karuwa! fasik'a kawai,
Sir Moli ya matso daf dashi ta yadda har suna iya juyo mumfashin juna,
had'i da kallansa ido cikin ido,
ya nuna masa yatsansa yace " kul karka sake ci mata karuwa,
inba haka ba... ya cije lips d'insa da k'arfi had'i dayin kwafa,
sannan idan kana san sanin waye ubana sai ka nemi ganin nashi kamar yadda kace,
kana Sir Moli ya juya cikin takunsa na isa ya nufi mota,
Khulud ta kalli Hanash tace " karka kuma ce mata karuwa,
dan ba karuwa bace,
ido Hanash ya runtse da k'arfi kana ya kalli Khulud yace " please karki saka kanki cikin wannan maganar,
a hankali Khulud ta saki Sanah ta nufi Hanash,
Sanah tayi saurin rik'o ta,
amma ta fizge,
ta taka har gabansa ta kalli cikin kwayar idansa tace " ban gane kar na saka kaina cikin wannan maganar ba, me kake nufi Hanash?
"Yama za'ayi a gaba na kuma ina tsaye ka rink'a kiran Sanah da karuwa fasik'a,
wallahi in banda arzikin aure da kuma matsayinka na mijina,
had'i da girman igiyoyinka dake kaina,
dana nuna maka mai hak'uri bai iya fitina ba,
kai da kake da k'anne mata, kuma kake neman haihuwa har kake aibata 'ya'yan wasu,
kamar yadda k'annanka suke mutane haka Sanah da Sir Moli suka mutane,
masu cikekken gata,
Hanash kabi a hankali dan haihuwa zakayi,
kuma shi ciki mai haife-haife ne,
ba'a san abinda zai haifu ba,
ka daina zagi kana aibata 'ya'ayan wasu,
dan baka san kaima abinda zaka haifa ba,
ina jiye maka tsoran kada Ubangiji yayi maka jarawar da zata fi k'arfinka,
jarabawar da zara gigitaka,
Hanash ka kiyayi duniya da rayuwa,
dan ita duniya tamkar mace mai ciki ce ba'a san abinda zata haifa ba,
haka kuma k'addara mace ce mara tabbas da akoyaushe tana iya canjawa,
hannu Hanash ya yarfe cike da takaici ya kalli Khulud,
yace " idan ba karuwar bace mecece?
" Ko kin san sau nawa ina kama su da ido na,
suna aikata masha'a?
" Sau hud'u ina ganin su, biyu a office d'in abokin karuwancin nata,
d'aya ranar d'aurin mu,
sannan da ido na naga ya kaita gidansa,
lokacin Papu ya aiki ni gidan abokinsa a unguwar,
tsaiwarsa ya gyara kana ya kuma cewa " sai ki fad'a man yanzu duk macen da take bin namiji har zuwa gidansa mecece?
Shiru Khulud tayi tana kallan Hanash cikin takaicinsa,
murmushi yayi yace " baki da amsar bani ko?
" To idan baki da amsa ni ina da amsa,
sunan macen dake bin namiji har zuwa gidansa KARUWA!, FASIK'A!!, MAZINACIYA!!!,
dan haka wad'annan sunayen duk sunanta ne ya fad'a yana nuna Sanah,
cikin zafin rai Khulud ta d'aga hannu da niyyar kifawa Hanash mari,
tsaida hannun nata tayi a dai-dai fuskarsa,
ta kasa k'arasa abinda tayi niyya,
hannunta dake kerrrrma Hanash yabi da kallo,
cikin tsantsar mamaki,
yace " what! Khulud da marina zakiyi danna fad'i gaskiya?
Hannunta ta yarfe had'i da durk'ushewa kasa,
ta fasa gigitaccen kuka mai cin rai,
a hankali Sanah ta tako inda Khulud ke durk'ushe tana kuka tasa hannu ta d'ago ta,
tana zubda hawaye itama,
a hankali Khulud ta d'ago kanta ta kalli Hanash tace " Allah ya isar musu,
ya kuma saka musu a bisa zargin da kake yi musu,
Hanash yace " wai baki yarda ba kome?
"Kina nufin sharri da k'arya nayi musu?
" Ko kina nufin k'age nayi musu?
" Ko so kike kice ba karuwar bace?
A fusace Sir Moli ya juyo cikin k'araji yace " i said don't dare you call her karuwa!
ya fad'a yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa,
cikin sanyin jiki Khulud da Sanah suka mik'e tsaye rungume da junansu,
Hanash ya kuma gyara tsaiwarshi,
cike da dagara yace " if i repeat it again what will you do!?
Tsaiwa Sir Moli ya gyara had'i da tattare hannun rigarsa,
kana ya zuba hannunsa cikin aljihun wandansa,
had'i da jefa idansa cikin na Hanash yace " ok k'ara fad'a inka isa kai cikken mara kunya ne,
Hanash yace " I said it in capital letter she's *KARUWA!!!*,
yadda kasan mahaukacin zaki Sir Moli ya nufi Hanash gadan-gadan,
yana wani irin takun k'arfin,
had'i da fitar da huci mai zafin gaske,
kai da ganinsa kasan ransa yazo iya wuya,
ran 'yan maza yayi mugun b'aci,
shima Hanash nannad'e hannunsa rigarsa,
yayi yana jiran k'arasowarsa,
ganin abinda ke shirin faruwa yasa Sanah saurin shan gaban Sir Moli tana kuka kamar ranta zai fita kana tace " please no!
a harzuk'e Sir Moli ya zagaye ta yana k'ok'arin k'ara nufar Hanash,
da sauri ta kuma shan gabansa,
had'i da sanya hannunta a saman k'irjinsa tana k'ok'arin dakatar dashi,
cikin kuka tace " a'a dan Allah,
jajayen idansa ya zuba cikin nata,
na tsayin lokaci, batare dayace komai ba,
ya dad'e yana kallanta ido cikin ido,
kana cikin zafin rai ya furzar da iskar bakinsa,
had'i da naushi motar dake kusa dashi ta Hanash,
inda ya daka a jikin motar ya lotsa,
hannunsa daya naushi motar yaji ciwo,
ya shiga zuwar da jini,
cikin furgici Sanah ta zaro ido had'i da saurin rik'o hannun,
tace " kana bleeding, ta fad'a cikin tashin hankali,
ganin yadda ta kid'ime yasa shi kafe ta da shanyayyun idanuwansa,
da sauri ta zame d'an kwalin kanta,
ta d'aure mishi hannun while tana cigaba da kukanta,
a hankali Sanah ta rik'e hannun Sir Moli ta jashi cikin mota,
ta bud'e mishi ya shiga, Sanah ta zagaya zata shiga cikin motar Khulud tace " my Sanah jira ni na d'auko hijab mu tafi gidan tare,
murmushi Sanah tayi kana tace " ok maza jeki d'auko,
a hankali Khulud ta juya ta shiga cikin gidan,
Sanah na ganin ta shige tayi saurin bud'e motarta ta shiga,
cikin muryar kuka tace " zaka iya driving d'in?
Baice mata komai ba yayiwa motar key,
jikin Baba mai gadi na rawa ya bud'e get,
Sir Moli yazo zai fita ya tsaya ya d'auko card d'inshi ya mik'awa mai gidan,
yace " ka kira ni letter, cikin rawar jiki Baba mai gidi ya amsa,
had'i da yin godiya, Sir Moli bai kuma yin magana ba yaja motar,
sai da ya fita daga gaba d'aya unguwar kana yayi parking a gefen hanya,
had'i da kwantar da kujerar motar ya kishingid'a gami da lumshe idansa,
yana fitar da huci had'i sauke ajiyar zuciya akai-akai,
ido Sanah ta k'ura mishi tana mamakin abubuwa da dama,
abu na farko daya tsaya mata yadda yayi akanta,
da yadda gaba d'aya yayi loosing control,
akan ance mata karuwa, dan taga yadda kalar idansa ta canja,
ta kuma hango tsananin b'acin rai acikin kwayar idansa,
ta tabbatar in banda tayi gaggawar shiga tsakiyarsu da Allah ne kad'ai yasan me zai faru,
can k'asan mak'ogwaranta ta maimata,
kalmarsa _akanta babu abinda bazan iya yi ba_,
sake kallan yadda yake ta faman huci tayi،
yana fitar da numfashi had'i da sauke ajiyar zuciya,
a ranta tace " yanzu wannan duk akai na ne?
"Idan akai na ne yayi wannan abun me hakan ke nufi?
" Idan dan ance man karuwa ya shiga cikin wannan matsanancin halin,
yanayinsa ya canja haka, to meye manufar yin hakan!?
Tana cikin yin zancan zuci taji yace " meyasa idan yayi maki abu baki iya ramawa!?
Yayi maganar batare daya motsa ba,
idanta na kansa cikin muryar kuka tace " nayiwa my Ulud alk'awarin duk abinda yayi man ban kuma ramawa,
"Ok tasan yana yi miki hakan kenan?
" A'a bata sani ba!
ta fad'a still idanta na kanshi,
" idan bata sani ba ya akayi kikayi mata alk'awarin?
Cikin sanyin jiki Sanah ta bashi labarin komai,
tun daga farkon had'uwarsu a ranar da sukayi graduated har zuwa ranar data yiwa Khulud alk'awarin bata kuma yi mishi komai har abada,
" ashe rashin kunyarki ce ta ja maki?
Ya fad'a yana bud'e idansa a hankali,
" yanzu in banda tsabar rashin kunya ina ke ina marin namiji?
" Duk abinda yayi maki ma dai-dai ne wallahi,
damma yana da sauk'in kai da sauyin zuciya,
inda irin mu ne hmmm ya k'arasa maganar yana yin murmushin gefen baki,
ido cikin ido Sanah ke kallan Sir Moli,
tana kallan cikin kwayar idansa,
wani irin abu take gani daga cikin kwayar idan nasa,
mai kamar brown color,
idan kuma ta kalli farin cikin idansa sai taga yayi mata wani iri,
kwata-kwata ta kasa fassara abinda take hangowa cikin kwayar idansa,
shima cikin kwayar idanta yake kallo,
jin yanayinsa ya fara canjawa yasa shi saurin kauda idansa,
daga kallanta ya mayar da kansa gefe,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi,
kana ta kalli hannunsa, a kid'ime tace " har yanzu yana bleeding fa,
dan Allah muje hospital, ta fad'a tana k'ok'arin rik'o hannun,
saurin janye hannunsa Sir Moli yayi had'i da tsuke fuska,
" please muje hospital kaga still yana bleeding,
a hankali ya kalle ta, yaga duk ta marairaice masa,
ta zama wata kalar tausayi,
key yayiwa motar batare dayace mata komai ba,
suna fara tafiya Sanah tace " amai nake ji,
bayyi mata magana ba ya gangara gefen hanya yayi parking,
yana tsaida motar ta fito da sauri tun kafin ta tsugunna ta fara shek'a aman,
a hankali ya bud'e motar ya fito,
ya zagoyo inda take,
a hankali ya tallafo ta cike da tausayi ya shiga mata sannu,
sai da ta gama yin aman kana,
ya bud'e mota ya d'auko ruwa ya zuba mata ta wanke jikinta,
jikinta sai kerrrrma yake yana rawar sanyi,
a hankali ta mik'e tsaye jiri na rib'arta,
ganin tana neman fad'uwa yasa shi d'aukarta cak ya sakata cikin mota,
kana shima ya zagaya ya shiga,
kwantar mata da kujerar motar yayi,
kana ya kashe Ac saboda yadda take rawar sanyi.
Direct standard hospital ya nufa da ita,
yayi parking a harabar asibitin bayyi mata magana ba,
ya zagayo ya bud'e motar ya tallafo ta,
a hankali Sanah ta zuro k'afafunta waje,
cikin sanyin jiki ta shiga takawa zuwa cikin asibitin,
while Sir Moli yana tallafe da ita,
da sauri nurses suka tare su,
suka amshi Sanah daga hannun Sir Moli,
but bai sake ta gaba d'aya ba,
yana rik'e sa ita ta d'aya b'arin,
office d'in Doctor aka nufa dasu,
a hankali suka zaunar da ita akan kujera,
Doctor ya mik'e da sauri yana murmushi yace " sannu!
kai kawai ta d'aga masa,
Doctor yana shirin fara dubata ta kalli Sir Moli tace " please kaje ayi maka dressing hannunka,
kallanta yayi batare dayace mata komai ba,
ta k'ara marairaicewa tace " please!
yace " bari a fara dubaki tukunna sai inje,
Sanah zatayi magana, Doctor tace " wow! amazing lovers gaskiya kun burgeni,
da yadda kuke bala'in so da kula da junanku,
Sir Moli zayyi magana Nurse d'in tayi tayi dariya tace " bari kaidai Doctor they're wonderful and best couples of the whole world wallahi,
sunyi masifar dacewa da junansu,
d'aya nurse d'in tace " saboda yab'ar yadda yake caring da san matarshi yama bari mu rik'e ta k'i yayi,
Doctor yace " Allah yasa dai Baby ne,
inyi maka babban albishir, dan da ganinku sabon aure ne,
kuma akwai soyayya a wajen,
kaga idan Baby ne amarci yayi kyau,
d'aya nurse d'in tace " aiko da gani ma laulayin ne,
d'ayar tace " aiko da kaya na zan kwaso na dawo gidanku ganin ikon Allah,
dan nasan akwai abu a goyon cikin nan.
Tunda suka fara magana idan Sir Moli yana kan Sanah yana karantar yanayinta,
bai iya gane yanayinta ba saboda halin rashin lafiyar datake ciki,
kallansa ya maida ga Doctor da nurses d'in,
yayi musu murmushi batare dayace komai ba,
kana ya fita ya nufi dressing room.
Da gudu Khulud ta fito hannunta rik'e da trolley,
ganin babu motar su Sanah yasa ta fashewa da kuka ta nufi hanyar fita,
Hanash dake tsaye yadda tabarshi,
baiko motsa ba, cike da tsantsar bak'in ciki da takaici,
yayi saurin shan gaban Khulud,
ya marairaice face yace " please kiyi hak'uri,
ban k'arawa,
bata ko kalli inda yake ba ta cigaba da nufar get tana kuka,
rik'eta yayi tayi saurin fisge jikinta,
tace " karka kuma tab'a ni,
da sauri ya janye hannunsa had'i da cewa " na bari,
dan Allah kiyi hak'uri kinji,
kallansa tayi tace " wallahi kaban mamaki Hanash,
na yarda dakai 100%,
idan wani ne ya fad'a man zaka yi duk wannan wallahi ban tab'a yarda,
na d'auka kai mai gaskiya ne,
na zata kai daban ne a cikin millions of millions na maza,
ban tab'a k'in yarda ko gaskata ka ba,
ban tab'a yin kokonto akanka da magarka ba,
Hanash na yarda dakai sosai,
meyasa zakayi haka!?
"Meyasa zaka tarwatsa duk yardar danayi maka?
" Meyasa zaka kawo kokwanto da zargi a zamantakewar mu?
"Mai yasa zaka zama mai fuska biyu?
" Why kake k'ok'arin raba ni da Sanaha, why Hanash! ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka,
muryarsa na rawa yace " wallahi Khulud nima ban san meyasa nake yin haka ba,
amma dan Allah kiyi hak'uri,
kallansa tayi tace " ina ai ba maganar hak'uri Hanash,
idan baka manta ba tun farkon alak'armu na fad'a maka,
cewar Sanah itace komai nawa,
ina matuk'ar santa fiye da komai da kuma kowa,
na fad'a maka bana k'aunar duk wani abu dazai shiga tsakani na da Sanah,
dan haka rabuwa dakai ta zama dole Hanash,
ta fad'a tana jan trolley d'inta,
da sauri Hanash ya fara k'ok'arin karb'ar trolley'n hannunta,
cikin tsawa tace " live me alone,
da sauri ya sake ta ya d'aga murya yacewa " Baba mai gadi " karka sake ka bud'e mata get,
kar bari ta fita,
jin abinda yace yasa Khulud durk'ushewa a wajen ta saki gigitaccen kuka,
a hankali Hanash ya durk'usa a kusa da ita,
cikin rawar murya yace " dan Allah kiyi hak'uri,
ki tashi mu shiga cikin gida,
red eyes d'inta ta d'ago ta kalle shi,
tace " wallahi ko yunwa da rana zasu kashe ni ban shiga cikin gidan da aka haramtawa my Sanah shigarsa,
sosai Hanash ya shiga lallab'a ta yana bata hak'uri,
amma fafur tak'i ko sauraronsa,
sosai Hanash yayi mugun mamakin taurin kan Khulud,
a ransa yace " dama ance masu hak'uri basu iya fushi ba,
ganin tak'i sauraronsa yasa shi mik'ewa cikin sanyin jiki yace " tashi muje na kaiki gidan da kaina,
babu musu Khulud ta mik'e, da kanshi ya bud'e mata gaban mota,
amma tak'i shiga ta bud'e bayan motar ta shiga ta zauna,
murmushi yayi had'i da girgiza kansa,
kana ya zagaya ya shiga motar yayi mata key,
tunda ya fara tuk'i yake kallanta ta mirror yana bata hak'uri had'i da rarrashinta,
amma tayi masa banza,
ta cigaba da kukanta,
har suka k'arasa gidan yana ta faman bata hak'uri,
a harabar gidan yayi parking,
da sauri ya fito jikinsa na rawa ya zagaya b'angarenta,
fitowa tayi itama tana jan trolley,
dai-dai lokacin Abbu da Didi suka fito,
turus sukayi a harabar gidan suna kallan ikon Allah,
cikin nutsuwa Hanash ya k'arasa inda suke had'i da durk'usawa har k'asa ya gaidasu cikin girmamawa,
cikin fara'a suka amsa masa,
Khulud ta k'araso inda su Abbu ke tsaye ta durk'usa ta gaida su,
Abbu bai amsa gaisuwar ba yace " lafiya na ganki da akwati?
Shiru Khulud tayi had'i da sunkuyar da kanta k'asa,
Abbu yace " tambayarki nake yi,
lafiya na ganki da akwati, me kikazo yi gidan harda zuwa da akwati?
Abbu yace " biki ake yi ko suna a gidan?
Kan Khulud na k'asa tace " a'a,
Abbu yace " to uban me ya kawo gidan?
Cikin kuka Khulud tace " Abbu na dawo gida ne?
Abbu yace " ban gane kin dawo gida ba?
"Me kika dawo yi?
Shiru Khulud tayi batace komai ba,
Abbu yace " magana nake yi miki,
cikin kuka Khulud tace " ban kuma zama dashi,
Abbu yace " shiwa?
Khulud tace " Hanash!
Abbu yace " akan wanne dalilin?
Khulud tayi shiru,
Abbu yace " ci da sha ne baya baki ko hakk'ink'i na auratayya ne baya biya miki?
"Ko mutuncinki ya kasa karewa, ko kuma nauyinki dake kansa ne bai saukesu!?
Cikin sanyin murya Khulud tace " a' a!
Abbu yace " Allah yake sab'awa,
ko kuma mashiriki ne?
"A'a Khulud tace,
" giya yake sha ko lud'u yake yi?
" A'a!
Abbu yace " a cikin sharadd'an rabuwar aure da Allah ya gindaya akwai d'aya a tsakaninku?
A hankali Khulud tace " a'a!
Abbu yace " auren dole mukayi miki ko mu muka kawo miki shi muka matsa maki kika aure shi?
"A'a tace tana zubar da hawaye,
Abbu yace " mu muka had'aki dashi?
Nan ma Khulud tace " a'a,
Abbu yace " ke kika wo kayanki kikace kina so ko?
Tace " eh!
" To shine dan iskanci daga yin auren dududu wata biyar zaki kwaso kaya kice kin dawo gida?
" Ni dai dan Allah Abbu ku raba ni das.......
gigitaccen marika Abbu ya maka mata guda biyu a jere,
cikin fad'a yace " dan ubanki mu zaki maida k'ananan mutane,
daga yin auren zaki dawo, ki dawo gidan kiyi uban me?
" Tunda kike cikin gidan nan kin tab'a ganin anyi yaji?
"Ko tunda kuke dasu Mamu kin tab'a ganin sun kwashe kayansu sunce sun koma gidansu?
" Kin tab'a ganin su Halan sun fita ko k'afar gida da sunan yaji, ko so kike yi ke ki fita zaka kibar tarihi?
" Idan baki sani ba, gwara ki sani haka dokar Hard'o family take,
idan suka aura ko aka aure su babu saki ko yaji sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah,
ki bud'e kunne dakyau kiji ni daga yau duk ranar da kika sake d'auko k'afa da sunan yaji to ki nemi wani gidan da kuma uban ba ni ba,
zan cire ki daga jerin yara na,
kinji ko baki ji ba, cikin kuka ta amsa " naji! dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
ajiyar zuciya ya sauke kana yace " yauwa good girl,
Allan yayi miki albarka kinji aje ayi ta hak'uri,
duk wacce kika gani gidan mijinta zaman hak'uri da juriya takeyi,
duk matar datace maki bata da matsala gidan mijinta k'arya take yi,
da zarar anyi aure so da soyayya sun k'are sai dai ayi zaman hak'uri,
idan kika bar mijinki na yanzu saboda wani dalilin,
kin san wanda zaki sake aura?
"Ko shi kin san halinsa, kin san nashi d'abi'un?
" Kinga baki san hannun wanda zaki kuma fad'awa ba,
dan haka kiyi hak'uri kinji my daughter,
nasanki da hak'uri da juriya had'i da kawar sa kai da saurin yafiya fa,
Abbu ya fad'a cikin tsokana, kanta ta kuma sunkuyarwa k'asa,
Abbu yace " maza tashi ki koma d'akinki kinji,
mik'ewa tayi a hankali kana ta kalli Abbu tace " bari na gaida su Mamu,
Abbu yace " a'a ba sai kinje ba,
suma zaune suke a gidajen mazajensu suna hak'uri,
dan haka kema ki koma naki gidan mijin,
kyazo ki gaida su daga baya cikin dad'in rai,
ba musu Khulud taja trolley d'inta ta koma mota,
Hanash ya mik'e tsaye had'i dayiwa su Abbu godiya sosai,
Abbu yace " kai ma kayi hak'uri,
kasan mata 'yan a lallab'a ne,
sai anyi hak'uri dasu, muma duk abinda mukeyi kenan har yanzu,
shiyasa kaga ankawo har tsayin wannan lokacin ana tare,
kansa ya sunkuyar