Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
lokaci d'aya,
ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba,
dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai,
take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye,
ya kuma kallanta yace " fool an idiot,
stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki?
"Ke a cikin matan ma wacece ke?
"Tatsitsiya kwaila kawai, shigiya empty head,
kanki ba komai sai rawar kan banza,
dama kwailayen nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci da san masa,
'yar iska ko irgen dangi baki fara ba amma har kin fara zak'ewa maza,
wannan iyayenki idan basu da gaske ba, KARUWA za'ayi anan,
ajacakar banza, iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa,
saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa,
jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red,
ta kafe shi da ido cike da tsantsar tsana bata ko k'ifta idanta,
ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " jeki kira min head girl, da Era,
cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita,
ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi tarrrr ko k'iftawa batayi,
ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,,
a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya.
Yace " ke daina kallo na mayya kawai,
karki cinye ni, ni ba d'an iska bane,
yayi maganar yana kowa kishingid'ar,
yana daga kishingid'en yace " kinci sa'a bana zina da wallahi sai sauke miki rawar kan nan taki,
oh! na manta ashe cewa zanyi kinyi rashin sa'a ni ba d'an iska bane bana zina, balle ki samu abinda kike so dan nasan babu abinda ke d'awainiya dake sai feelings d'ina,
to sai dai kici kanki witch,
sallamar su Khulud ce ta katse shi,
a dak'ile ya basu izinin shigowa,
daga gefe suka rakub'e ya kalli Khulud yace " meya had'a ku?
Yayi maganar a tak'aice, su Era da suka shigo da suka ga yanayin Sanah, suka kuma ga Khulud na kuka sai sukayi zaton dukan su Sir Moli yayi,
aiko take mugun farin ciki ya lullub'e Era,
cikin sanyin murya Khulud ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
shiru yayi na wani d'an lokaci yana nazari,
murmushi yayi a cikin ransa dan ya gano logon Sanah yanzu,
a ransa yace " Era Khulud ta tab'a shiyasa zuciyar Sanah tayi zafi har idanta ya rufe ta dake ta,
wato daka tab'a Khulud gwara a tab'a ta kenan?
Murmushin gefe baki yayi, wato wannan dalilin ne yasa d'azo dana zage ta bataji haushi ba amma dana zagi Khulud take yanayinta ya canja?
Kai ya girgiza cike da matsanancin farin cikin gano lagwanta,
ya kalli Khulud yace " ke idan na bincika naga kinyi min k'arya sai naci uwarki, yayi maganar yana satar kallan Sanah,
aiko ido ta runtse da k'arfi,
ya kuma yin murmushin mugunta,
ya kalli su Era yace " haka akayi?
Kanta a k'asa tace " eh Sir,
yace " ba'an hana ku aiken JSS ba?
Shiru Era tayi kanta a k'asa, ya kalli Head Girl yace " ba an hana ku dueling ba?
Itama shiru tayi had'i da sadda kanta k'asa,
ya cigaba da cewa " ina tunanin kamar principal ta hana ku koda aiken 'yan JSS musamman JSS1 ko?
Duk sukayi shiru, a fusace ya daka musu gigitacciyar tsawa " bada ku nake magana ba?
Yayi maganar cikin b'acin rai, take cikin su ya d'auki kerrrma yana b'ari,
a tsorace Head Girl tace " wallahi Sir ban san hakan ta faru ba,
ina class ina karatun test, aka kira ni,
ita kuma Era tace " am so sorry Sir,
cikin b'acin rai ya daka musu tsawa " get out!,
zanyi bincike akan mate d'inku,
wallahi matuk'ar na gano kuna zaluntar na k'asa daku sai kun raina kanku,
jiki na b'ari suka fita, Era na cewa " na shiga uku, kashi na bushe,
dan nasan muddin Sir Moli yayi bincike akan mu sai buzuna,
Head Girl tace " kuma kin san shi magana d'aya yake yi,
muddin yace " zayyi abu to sai yayi babu kuma uban daya isa ya hana shi sai Allah.
Sir Moli ya mayar da kallansa ga Khulud yace " ke ku 'yan daba ne?
"A'a ta bashi amsa cikin sanyin magana,
idansa nakan Khulud ya kuma cewa shaye-shaye kuke yi?
Ta kuma cewa a'a,
yace " abinda kuka taso kuga ana yi a gidan ku kenan, ko shi iyyen na ku suka koya muku fad'a da makami har da fasa kai?
Kai ta girgiza masa tana kanne kukan ta,
ganin halin da Khulud ke ciki yayi masifar d'agawa Sanah hankali,
tasa hannunta ta dafe sai saitin zuciyarta kota samu sauk'in abinda take ji,
duk abinda take yi Sir Moli yana lura da ita,
ya kuma cewa " to amma gidan su akwai 'yan daba masu sare-sare da yanka mutane da wuk'a ko?
Kukan da Khulud take dannewa ne ya kufce mata,
tana k'ok'arin yin magana Sanah tayi saurin cewa,
" ni ce nayi laifi ba ita ba, dan haka ni zaka yiwa hukunci ko ka tsare da tambayoyi ba ita ba,
Khulud tayi saurin cewa " a'a Sir tare mukayi komai dan haka duk hukuncin da zakayi kayi mana tare,
Sanah tace " wai meyasa kike haka ne Ulud,
please ki bari ni danayi laifi ya hukunta ni dai-dai da abinda nayi,
Khulud tace " kin fara ko?
"Amma ai sanin kanki ne tare mukayi amma shine kike san zamewa,
Sir Moli ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah,
kowacce na k'ok'arin kare 'yar uwarta,
Sir Moli ya kalli Khulud yace " ashe kema 'yar iskarce,
da k'arfi Khulud ta saka kukan bak'in ciki,
aiko zuciyar Sanah ta hasala,
a tsawace cike da tsantsar masifa tace " don't say it again,
haba kai wanne irin d'an Ada.......
Kafin ta k'arasa Sir Moli ya d'auke ta gigitaccen mari,
tassssssssssssssss
a razane Khulud ta d'ago kanta,
ganin Sanah aka mara yasata fita daga hayyacinta ta nufi Sir Moli gadan-gadan,,,
da sauri Sanah ta rok'ota, bak'in ciki ne yasa Khulud durk'ushewa had'i da saka gigitaccen kuka,
a hankali Sanah ta durk'usa a gabanta tasa hannu ta d'ago kanta,
hannu Sanah tasa hana gogewa Khulud hawayen dake zubawa daga idanta tace " Uludi na ki daina kuka please,
kai Khulud ta girgiza mata alamar a'a,
ido Sanah ta zaro tace " meyasa?
Cikin rawa murya tana danne kukan bak'in cikin dake cinta,
Khulud tace " marinki fa akayi a gaba amma bani da yadda zanyi,
please barni nayi kukan kona samu sassaucin abinda nake ji,
murmushin bak'in ciki Sanah tayi tace " wallahi marin da akayi min bai kai kwatankwacin zafin zubar hawayenki a cikin rai na ba,,
da sauri Khulud ta share hawayenta had'i da yin murmushi tace " na dai na kukan to,
Sanah na murmushi tace " kinyi alk'awari?
Dariya Khulud tayi had'i da cewa " eh nayi alk'awarin daga nan har k'arshen rayuwar mu duk abinda kika ce na bari zan bari,
duk kuma abinda kikace nayi zanyi,
in sha Allahu,
Sanah ta kuma yin dariya tace " ni kuma nayi miki alk'awarin daga nan har mutuwar mu bazan tab'a bari kiyi kuka ba,
ba kuma zan tab'a barin ki cikin damuwa da matsala ba in sha Allah,
dariya sukayi a tare had'i cewa alk'awari,
Sir Moli na gefe yana kallan yadda yara k'anana ke k'aunar junansu,
ashe ba Sanah ce kad'ai ke san Khulud d'in ba,
itama tana santa,
yayi maganar cikin ransa, dan yadda ta taso a haukace badan Sanah ta rik'e ta ba, tana iya fad'a masa,
can k'asan mak'ogwaro yace "aiko da kinci ubanki yarinya da kinga ne shayi ruwa ne.
Jin an shiga Sallar Magrib ne yasa shi fita da sauri dan ko kiran sallar bai ji ba,
sai da ya tsaya yayi sallar ishsha kafin ya tafi gida,
kwance yake rufe da ido amma ba bacci yake ba,
tunani da mamakin yaran yake yi,
babu abinda yafi d'aure masa kai sai tarin so da k'aunar da suke yiwa junan su,
ya kuma san ba uwarsu d'aya uban su d'aya ba,
saboda ita SANAH RAWAN sunanta,
ita kuma KHULUD HAMRAZ,,,
a fili yace " so halitta ne dan ko uwa d'aya uwa bazasu yi wa junan su irin wannan mugun son ba,
yasan k'aunar da suke yiwa juna daga Allah ne,
ido ya runtse yana tunanin shi yaushe ne zai san so?
Yaushe zai san zafin so, zai san abinda ake ji a cikin so,
dan shi a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a yin soyayya ko ya so wata 'ya mace ba,
asalima bai san abinda ake kira da so ba, tunda aka haife shi har zuwa yanzu da yake da 22yrs,
yana da 3yrs aka saka shi a primary school,
ya gama yana da 10yrs saboda yayi nursery 1&2,
yana da 16yrs ya gama secondary school,
sai yanzu dayake service, amma idan ka ganshi sai ka rantse ya haura 30yrs,
saboda tsabar kwarjini da kamalarsa,
had'i da nutsuwarsa,
yana cikin tunani bacci yayi awon gaba dashi batare daya sani ba.
Su Khulud ganin ya fita yasa Sanah rik'o hannun Khulud tace " tashi mu tafi hostel,
Khulud bata ko motsa ba, ta kafe Sanah da ido,
kana tace " muje ina Sanah?
" Salan ya dawo bai iske mu ba ya samu abinda yake so,
ya kuma samun damar zagin iyayen mu da ahalin mu,
ya kuma ci mana fuska da mutunci,
yanzu ke zagin da yayiwa iyayen mu da ahalin mu damu kanmu kinji dad'insa?
Shiru Sanah tayi bata furta kalma ko d'aya ba,
Khulud ta cigaba " ke yake zaga amma ni nake jin k'unar abin a zuciya ta,
ke yake jifa da munanan kalaman amma ni nake jin zafi da bak'i ciki a rai na,
dan girman Allah my Sanah ki daina shiga sabgar mutumin nan,
mu lallab'a mu rabu dashi lafiya,
ido Sanah ta zaro had'i da cewa " wacce sabgar tasa nake shiga?
"Wacce idan yace kiyi abu kike k'inyi,
please daga yau duk abinda ya saki ko ya umarce dayi muddin bai sab'awa shari'a ba kiyi,
idan kina yin abinda yace ai sai yaci kansa,
muga kuma ta inda zai b'ollo ganin yadda Khulud ke magana ne yasa cikin sanyin jiki Sanah tace " to in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyaye duk abinda zai kawo sab'ani a tsakani na dashi,
saboda ke kodan hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa.
Amma wallahi badan ke ba da sai dai ya kashe ni,
idan shi k'aramin d'an iska ne,
da sai na nuna masa ni babba ce,
shege d'an iska mai girman kan tsiya,
muskilin banza, wai harshi zai cewa wani d'an iska bayan shine cikkekken kwarto,
ja'irin yaro kullum bashi da aiki sai ya kwanta haka, ta kwanta akan sofa tana kwaikwayon yadda yake kishingid'a,
ta kwaikwayi maganar sa tace " ke kina shaye-shaye ne?
Tayi maganar kamar yadda yake yi,
tace kaji munafuki shida yayi kama da masu shaye-shayen ma ba'a ce yana yi ba sai shine zai cewa wani yana yi,
wama ya sani ko irin sune masu lab'ewa a uncompleted buildings suna 'yan kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e,
zata kuma magana Khulud ta rok'o hannunta tana nuna mata agogon bangon dake manne a office d'in,
tace kalli har 10:05pm na dare,
zo mu tafi nasan shima ya tafi,
Sanah tace " mugu azzalumi kawa ya ajiye mu kamar ba mutane ya jibge ba,
ba ci ba sha balle bacci, sai gobe yazo yana tare late comers,
shi yana can saki baki yana bacci har da munshari,
Khulud taja hannunta tana cewa " mu tafi ni dai yunwa da bacci nake ji,
kuma nasan hankalin Aunty Halan nacan a tashe.
Washe gari bayan an kad'a break Sir Moli ya tafi office, har ya kishingid'a ya tuna da voice recorder daya kunna ya aje ye dazai fita yabar su Sanah a office d'in sa,
dan ya tabbatar da sai sunyi wata magana a kansa,
d'aukowa yayi daga inda ya b'oyeta a gefen table d'insa yana murmushi ya koma kan sofa had'i da kunnawa.
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
5⃣
Playing yayi zai fara ji, Vice Principal ya shigo office d'in,,
cikin sallama, Sir Moli yayi saurin kashe record d'in,
ya tattara hankalinsa kan VP batare daya mik'e daga inda yake ba,
dayake VP ya riga da yasan halin Sir Moli bai wani ji haushin abin ba,
dan idan da sabo sun sabawa baud'add'an halinsa,
VP yace " Malam Moli dama wata alfarma nake nema a wajenka idan ba damuwa,
ido Moli ya zuba masa had'i da cewa " kamar ta me fa?
"Please dama wasu students za'akai Hospital,
saboda ciwon zu yafi k'arfin sick bay d'in mu,
dole sai an kai su babban asibiti, cikekken Doctor ya duba su,
to kuma ni ina da aiki a office,
shine nake san ka taimaka ka tayani aikin ko kuma ka kai yaran Hospital,
d'an gutun murmushi yayi kana yace " ok badamuwa Sir,
ka zab'i wanda kake ganin zaka iya ni sai nayi kowanne ne,
murmushi shima Sir Jeeb yayi kana yace " no choose anyone kawai,
ni bani da damuwa zan iyayin kowanne,
dan yasan halin Moli idan yace zayyi mai gatse-gatse sai yak'i yi,
sai dai duk abinda zai faru ya faru,
shi kuma Moli saboda baya san yawan magana yasa shi cewa " ok zan kai su asibitin,,
yayi maganar yana mik'ewa,
"thank you, cewar Sir Jeeb,
Moli bayyi mishi magana ba sai murmushi kawai da yayi.
Private Hospital dake cikin garin Roni ya kai su,
batare da wani b'ata lokaci ba aka karb'e su aka shigar dasu da hanzari,
a gaggace aka shiga duba su, ba'a shima ba likitan ya fito,
a wajen jira ya iske Sir Moli zaune ya jingina kansa da bayan kujerar dayake zaune had'i da rufe idanuwansa,
sallamar Doctor d'in ce tasa shi bud'e idansa,
ganin Doctor tsaye akansa yasa shi mik'ewa a hankali had'i da mik'a masa hannu,
bayan sun gaisa ne Doctor yace " d'aya hawan jini ke damunta,
ido Sir Moli ya zaro waje, cikin kid'ima yace " what! hawan jini fa kace?
"Yes abinda ke damunta kenan kuma yayi mata mugun kamu,
yama zama dole mu d'ora ta akan magani yanzu,
cikin sanyin jiki Sir Moli yace " d'ayar fa?
"Malaria ke damunta, "wannan is normal cewa Moli,
magunguna Doctor ya rubuta musu, sannan ya sallame su, sai da Moli ya biya ta Pharmacy ya siya kafin ya wuce school,
kallan yarinyar da Doctor yace tana d'auke da hawan jini yake ta mirror,
babu abinda yake bashi mamaki sai k'arancin shekarunta,
dan ya tabbata bazata wuce 14yrs zuwa 15yrs ba,
kuma tun fitowar su daga makaranta take kuka har suka je asibiti kukan take, har zuwa yanzu kukan take bata daina ba,
kanta na k'asa tana wasa da fingers d'inta tana zubar da hawaye,
tausayi yarinyar ta bashi dan haka Moli yace " ajinki nawa?
Yayi maganar batare daya kalli inda take ba,
bata motsa ba tana yadda take ta bashi amsa cikin rawar murya " JSS3,
sake kallanta yayi ta cikin mirror kana yace " shekarunki nawa?
"Sha hud'u (14yrs) ta bashi amsa,
har a lokacin kanta na k'asa tana cigaba da kukan ta,
a ransa ya maimaita "sha hud'u, amma harta kamu da hawan jini?
"To meye damuwarta haka?
yayi maganar cikin ransa, a fili yace " kin san me likita yace yana damunki?
D'an murmushi tayi kana tace " nasan bazai wuce hypo tension ba,
tayi maganar tana goge hawayen dake k'ara zubo mata,
sake kallanta yayi ta cikin mirror cike da mamaki,
yace " kin san abinda ke damunki kenan!?
"A'a ban sani ba, kawai dai nasan halin danake ciki yakan iya haifar min da hakan,
shiru yayi batare dayace komai ba,
taci gaba " ainahin cewon dake damuna yana cin zuciya ta,
da ruhi na, yana kuma wargaza duk wani farin ciki da walwalata bashi da magani,
har gwara hypo tension ma yana da magani,
tayi maganar sabon hawaye na zubo mata,
bai kuma cewa komai har suka isa makaranta,
direct office d'in Sir Jeeb ya wuce yayi masa bayanin abinda ke faruwa a tak'aice,
sosai hankalin Sir Jeeb yayi mugun tashi ya kalli Sir Moli yace,
"kaga yara kenan ma, ina kuma ga mu manya?
Sir Moli yace " al'amarin sai dai addu'a kawai,
Sir Jeeb yace " tab yara k'anana na hawan jini lalle zamani ya lallace,
Sir Jeeb ya d'an dafa kafad'ar Sir Moli yace " please idan ka samu dama ka kira ta ka bincike ta abinda yake damunta,
kodan mu sauke hakk'i, amana da nauyin da iyayen su suka d'ora mana,
abinda yasa nace kai ka tambaye ta matsalarta saboda yaran suna jin tsoranka,
tana iya sanar dakai damuwarta kai tsaye batare da an sha wahala ba,
kodan tsoranka da suke ji, amma idan wani ne sab'anin kai,
tana iya yi masa yawo da hankali,
ajiyar zuciya Sir Moli yayi, badan yaso ba, dole tasa shi amsawa Sir Jeeb " ok badamuwa i will try my best in sha Allah,
amma har ga Allah bai so hakan ba,
dan shi a nashi ganin wannan abinda ya shafi rayuwarta da sirrin ta ne,
bai kamata a matsa mata akan lalle sai ta fad'i ba,
yana ganin hakan kamar takura ce, kuma idan akayi mata an shiga hakk'inta.
Area classes ya nufa saboda yana da ajin da zai d'auka a lokacin,
a hanya ya hangi Sanah da Khulud na tahowa amma su kwata-kwata basu kula dashi ba,
hakan yasa Sanah bangazar sa batare data sani ba,
da k'arfi ya hankad'a ta had'i da saurin ja baya,
dan kar jikinta ya tab'a nashi,
tafiya Sanah tayi taga-taga zata fad'i Khulud tayi saurin tare ta,
a hasale ta juyo cike da tsiwa tana shirin zazzage ruwan bala'i,
hard'e hannayensa yayi a k'irji yana jiran jin abinda zata ce masa,
bisa mamakinsa tana sauke ido a kansa tayi saurin ja da baya,
had'i da d'an rusunawa tace