Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
ta shiga bashi hak'uri had'i da rok'onsa tana kuka,
"dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
Allah yauma tsautaayi da k'addara ne,
ka tausaya min idan ka dake ni mutuwa zanyi,
baya ya ja a hankali had'i da cewa kina so na kyaleki?
Da sauri Sanah ta d'aga kai had'i da cewa "eh,
"to sai kin maimaita duk abinda kikayi da abinda kika fad'a kana na rabu dake ki fita salin alin,
ido Sanah ta zazzaro waje cikin tashin hankali,
yace " eh,
inba haka ba sai nayi miki irin dukan da kikaga nayiwa Siyah,
ai Sanah najin yace zayyi mata irin dukan da yayiwa Siyah tsoro ya k'ara kamata,
kerrrmar jikinta ta k'aru,
jikinta na rawa ta d'auki hular ta mayar kanta ta gyara tsayiwarta,
ya kalle ta yace " oh! dama haka nake tsaiwa?
Tayi shiru, yace "cigaba,
hannayenta da sark'e a k'irjinta,
yace " uhnnn ashe haka nake yi?
"Dama k'are min kallo kike yi?
"Duk abinda nake yi idanki na kai na ashe ni ban san sani ba,
kanta ta duk'ar k'asa, tana kuka,
yace " cigaba,
jikita na kerrrma ta soma maimaita duk abinda tayi,
da tazo wajen data ce ja'irin yaro sai tayi shiru,
ta sunkuyar da kanta,
yace "cigaba mana ke nake jira,
cikin sanyin murya tace " dan girman Allah kayi hak'uri,
yace " ashe rashin kunyar taki babbace?
Da ina tunanin k'arama ce ashe ta wuce tunani da sani na,
tun da harta kai daki d'auki suturar Malaminki ki saka kina kwaikwayonsa,
yanzu Sanah ni kike kira da ja'irin yaro?
"Fitsarar ki har ta haka?
"Gaskiya duk da ban san daga irin gidan da kina fito ba,
nasan gidan ku babu tarbiya, babu ganin girman na sama,
babu bawa babba daraja da k'imarsa,
saboda charity's begin at home,
tarbiyya tana farawa ne daga gida,
idan kana san sanin hali da tarbiyyar gida,
Bahaushe yace ka kalli d'an gidan,
gaskiya iyayenki sun cuce ki da suka kasa baki ingantacciyar tarbiyya,
duk mijin daya aureki ya shiga uku yaga ta kansa,
mijinki ya banu, yana shirin ganin ikon Allah,
dan nasan sai ya kwana yana la'antar iyayenki,
kukan bak'in ciki da takaicin cin fuskar da Moli yake yiwa iyayenta da ahalinta kawai take yi,
dan da wad'annan maganganun har kwara ya kashe ta,
amma k'iri-k'iri ba kunya babu kara da kawaici yana jefan iyayenta da munanan maganganu,
kodan ba laifin shi bane laifinta ne data zama d'an kuka,
mai jawa uwarsa jefa,
sosai Moli ya zage ya rink'a gasawa Sanah maganganu masu zafi san ranshi,
har ya gaji,
sai da ya gama kana ya kalle ta yace " jeki kira min Era, yanzu,
jikinta a sanyaye ta fita, yabita da kallo,
bata jima ba suka dawo tare da Era,
a office d'insa suka iske shi kwance,
idansa rufe, batare daya bud'e ido ba,
yace " kije da yarinyar nan ki bata hora mai tsanani,
cike da mamaki Era ta kalle shi, ta kalli Sanah dake duk'e sunkuye da kai,
bai bud'e idan ba, yace " ba magana nake yi miki ba?
Jiki na rawa Era tace " ok Sir, I will by God grace,
tayi maganar tana mik'ewa cikin murna da matsanannacin farin ciki,
saboda tsabar murna jikin Era har rawa yake,
dan tasan dole zata fanshe abinda Sanah tayi mata,
itace mutum ta farko data fara karya mata alk'adari, ta zubar mata da mutunci,
dan da a baya har mate d'inta tsorarta suke ji,
amma banda yanzu,
dan haka take ganin kamar wannan wata dama ce da Allah ya kawo mata,
da zatayi amfani da ita wajen dawo da martabarta data rasa,
ta kuma ganawa Sanah azaba mai matuk'ar rad'ad'i,,
jikin Sanah a sanyaye ta mik'e babu wani alamar tashin hankali ko tsorata a tattare da ita,
har sun kai bakin k'ofa suka ji yace " karki sake ki tab'a lafiyarta,
dan bance ki dake ta ba, kuma duk huran da zaki ba ta iya nayau ne kad'ai,
daga yau naji kin kuma bata huro......
shiru yayi had'i da cije leb'ensa na k'asa,
jikin Era a sanyaye ta fita dan ba haka taso ba,
shi kuma dama yace Era ne dan yasan har yanzu da haushin Sanah a ranta yasan zata bata bak'ar wuya.
Direct toilet Era ta wuce da Sanah ta kalle ta a Wulak'ance,
tace " na baki nan da 15 minutes ki tabbatar kin wanke su tass,
Sanah ta kalli Era tace " to ruwa da omo fa?
Hannu ta d'aga da niyyar kifawa Sanah mari,
Sanah tayi saurin rik'e hannunta,
had'i da cewa " la la ina tunanin a cikin jerin horon babu duka ko?
"Kuma in ba mantawa nayi ba kamar har kashedi yayi miki akan karki sake ki tab'a lafiya ta ko?
Tayi maganar idanta tarr cikin na Era,
had'i da yarfar da hannun Era da k'arfi gefe,
a fusace Era ta juya zata tafi Sanah tayi saurin cewa " bafa ki ban ruwa da omo ba,
dan haka kina iya dawowa ki ta tadda so yadda kika barsu,
kamar Era bazata jiyo ba, sai kuma ta tuni da halin Sir Moli,
dakyar Era tace " ruwa yana famfo,
omo kuma kiyi amfani da toka,
duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Era Moli na kallan su ta window,
kai ya girgiza had'i da cewa " majahulil hali.
_ni ko nace kamar dai yadda tace maka itama_
Kallan tazarar dake tsakanin toilet d'in da famfon tayi,
taga tazarar rayi ta rabin 1km,
kuma kowanne toilet zai ci ruwa bucket 10,
ga toilet d'in a k'alla sun kai 50,
ajiyar zuciya ta sauke kana ta d'auki bucket ta nufi tanker,
har aka tashi daga class Sanah bata gama wanke toilets d'in ba,
sai kusan 3:00pm na rana kana ta gama wanke su, Khulud na can tana ta bulayin neman Sanah,
lungu da sak'o amma ta rasata,
hankali tashe taje wajen Halan ta sanar da ita halin da ake ciki,
itama hankalinta yayi masifar tashi matuk'a,
Halan ta kalli Khulud tace " ina tace miki zata je?
Khulud tace " Uncle d'in mu ne ya aike ta staff d'iban chock tun daga nan ne nata dawo ba,
cikin kid'ima Halan tace " Allah dai yasa ba wani abun ta kuma yiwa Sir Moli ba,
ido Khulud ta zaro a tsoro ce, tare da cewa " please Aunty muje mu gani to,
ba musu Halan ta zari hijab suka fita, staff suka shiga suka duba amma babu ita babu alamarta,
Halan tace " zo mu zagaya ta bayan staff mu gani ko tana nan,
aiko suna zagayawa Khulud ta hango ta zaune kan bucket,
tana 'yan wak'e-wak'enta na fitsara tana yiwa Era habaici cikin wak'ar,
da sauri Khulud ta nufe ta tana cewa " lafiya meya faru my Sanah?
Halan ma da sauri ta nufe ta,
suka shiga tambayarta abinda ya faru,
bata b'oye musu komai ba, ta fad'a musu duk abinda ya faru,
tun daga farko har k'arshe,
kuka Khulud ta saka tana cewa " dama sai da nace miki ki fita harkar mutumin nan amma kika k'i ai ga irinta nan,
Sanah tace " kinga tunda akayi abin nan hankali na a kwance yake,
amma yanzu kinzo zaki d'aga min hankali da kukan ki,
Khulud zatayi magana Eta ta k'araso wajen tana hura hanci,
da sauri Halan da Khulud suka tare ta,
suka shiga bata hak'uri suna rok'onta akan ta kyale Sanah amma fur tak'i,
daga k'arshe ma noma ta kuma saka Sanah da hannu,
Khulud zata taya ta Era ta hana ta taya ta,
tace " wallahi idan kika tayata sai na kuma k'ara mata wata azabar,
Sanah tayi dariya had'i da cewa " wai azaba, ai babu wanda ya isa ya azabtar da d'an Adam face Ubangijin daya halicci abinsa,
Era bata kula ta ba ta juya tayi tafiyarta,
Khulud da Halan suka bi bayan Era,
babu irin hak'uri da rok'o gami da ban bakin da basu bawa Era ba,
amma tak'i hak'ura.
Sosai Era ta bawa Sanah wuya da duk taurin kanta sai da tayi laushi,
Era bata kyale Sanah ba sai 10:30pm na dare,
jikin Sanah duk yayi la'asar saboda bak'ar wuya amma har a lokacin bakinta bai mutu ba.
Bayan sati d'aya da faruwa al'amarin,
Sir Jeeb ya aiki Sanah dataje office d'in Sir Moli ta kira masa shi,
tunda aka yi abun daga Sanah har Moli babu wanda ya k'ara ganin wani,
da sallama ta shiga office d'in kanta a k'asa kamar mumi na,
Sir Moli nakan sofa yana kallanta amma yak'i yin magana,
jin shiru ba'a amsa sallamar ba yasa Sanah tad'o kanta,
ganin ba kowa yasa ta ware ido ta shiga dube-dube ko zata ganshi,
amma kwata-kwata hankalinta bai kai kansa ba,
takalminsa data hango a bakin gefe tasa hannu ta jawo,
ta d'aga su sama tana kallo gami da cewa " fasa zurmi badai kofatai ba,
idanta ne ya sauka akan hularsa da agogonsa dake kan table,
da sauri ta mik'e ta k'arasa inda suke,
ta d'auki hular tace " wai akan wannan banzar abar aka ban bak'ar wuya ko?
Ta tambayi kanta, tsoki tayi tasa hular akan ta,
jin hular ta shige zuruf cikin kanta ne,
yasa ta cewa dad'i na dashi badai ra'ason ba,
ta saka hular sosai akan ta, ta zura takalmi da gogonsa,
ta gyara tsaiwarta sosai tace " ranar nan hula kawai na saka aka kusa aika ni k'iyama,
aka zage ni tassss aka jefi iyaye da ahali na da bak'ak'en maganganu,
to yau nasaka har da takalmi da agogo sai a kashe ni idan an tashi,
wai harda cewa mijikin ya shiga uku,
yana shirin ganin ikon Allah tayi maganar tana kwaikwayon sa,
kai ba'ace maka matarka ta shiga uba sai kai zakace mijin wani,
ya shiga uku yaga ta kansa,
wallahi duk matar data auri wannan taga bani da arkani,
taga izajar rayuwa,
mai baud'add'en hali kawai,
majhulil hali,
duk abinda Sanah keyi akan idan Moli,
dan tashi ma yayi daga kwancen ya zauna dangwar-gwar yana kallan abinda yafi k'arfinsa,
ya girmewa saninsa da tunaninsa,
cike da tsantsar mamaki da al'ajabi,
a hankali ta cire hula da agogon ta mayar dasu yadda suke,
kamar babu wanda ya tab'a, haka ma takalmin ta juya zata fita,
jiyo muryarsa tayi yana cewa " har kin gama iskancin da fitsarar?
Cak ta tsaya a inda take had'i da runtse idanta ta cije hak'oranta........
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
8⃣
Cak ta tsaya a inda take had'i da runtse idanta ta cije hak'oranta,
a hankali tace " Subhanallah yauma rana ta b'aci,
murmushin takaicin halayyar yarinyar yayi kana yace " zo nan!
a slow ta juyo kanta a duk'e a k'asa tana murza hannayenta,
"zo nan nace,
yayi maganar a d'an hasale, a hankali Sanah ta d'ago kanta,
ta kalle shi, ganin yadda launin idansa ya canja kala zuwa red,
ne yasa jikinta d'aukar kerrrrma,
gaba d'aya yanayinsa da kamanninsa sun sauya,
take tsoro yayi masifar kamata,
jikinta ya d'auki rawa da tsuma,
a tsawa ce yace " ba magana nake miki ba dan ubanki?
Cikin kerrrmar jiki Sanah taje gabansa ta tsuguna had'i da fasa kuka,
dan tasan yau kashinta ya bushe,
takai a k'alla 10 minutes durk'ushe a gabansa ya zuba mata ido batare dayace mata komai ba,
kallanta kawai yake cike da tsantsar mamaki da al'ajabin halinta,
na taurin kai da dakewar zuciya,
tunda yake a duniya bai tab'a yarinya irinta mai shegen rawar kan tsiya da rashin jin magana irin ta ba,
ashe matar da zan aura taga bani da arkani?
Cigaba tayi da kukanta batare datace komai ba,
"me ma kikace d'ayan?
"Yauwa taga izajar rayuwa ko?
Ya kuma tambayar ta, k'ara k'asa tayi da kanta,
tana cigaba da kuka,
"mai baud'add'en hali, ya maimaita yana girgiza kansa,
idansa na kanta yace " wanne irin baud'add'en hali ne dani?
Bai bari tayi magana ba yaci gaba,
meye ma'anar majhulil hali?
yayi maganar cike da rainin hankali,
Ya kuma tambayarta,
to yanzu dai da farko meye ma'anar bani da arkani, da izajar rayuwa?
Shiru tayi batace komai ba, ganin bata da niyyar yin magana ne,
yasa shi daka mata tsawa had'i da cewa " ke dan kan uwarki badake nake ba?
Yayi maganar cikin zafin rai,
yadda yayi maganar ya k'ara firgitata sosai,
jikinta ya k'ara cigaba da kerrrmar da yake yi,
a tsorace tace " bani da arkani yana nufin bala'i da masifa,
"a wanne yaren?
Ya kuma tambayar ta,
cikin kuka tace " Sokkotanci,
"ke basakkwaciya ce?
Kai ta girgiza masa alamar a'a,
"magana zakiyi min dan ubanki kamar yadda nake yi miki magana nima,
ko finki bakin magana nayi?
" A'a,
yace " shegiya mara kunya fitsarariya,
kin iya zagewa kiyi rashin kunya da tsiwa san ranki,
amma da kin shiga hannu sai ki fara kuka,
ga rok'o da ban hak'uri kamar a bakin ki aka saukar dasu,
kince ke ba Basakkwaciya bace,
to gidan uban wa kika iya sakkwatanci?
"Ko wajen rawar kai da fitsarartaki kika iya?
Yayi magana duk a lokaci d'aya,
cikin muryar kuka tace " a'a nima ji nayi ana fad'a,
" wajen ubanki kika ji yana fad'a?
Tace "a'a bakin wata 'yar ajin mu, ita 'yar Sokota ce,
zama ne ya su Kano,
"ke 'yar Kano ce?
Ya kuma tambayar ta,
"eh tace,
"ok meye ma'anar izajar rayuwa?
"Taskun rayuwa, ta kuma bashi amsa,
" shi kuma wannan a wanne yaren ne?
"Larabci tace masa,
"oh dama ke Balarabiya ce?
"A'a tace cikin sanyin murya,
ya kuma cewa " wanne yare ce ke?
Fulani ta bashi amsa, ido ya zaro had'i da cewa " what!?
Tace " eh kakana har yanzu baijin Hausa sosai,
koyaya yayi magana saika gane ba cikekken Bahaushe bane,
yace " haba no wander kike irin wannan iskancin,
ai dama duk wani mugun hali Fulani sun had'a shi,
sune Kidnappings, Robbery, mugunta da k'eta,
ba mamaki dan kinyi irin wad'annan k'ananan halayen,
da wuya a kama Kidnapers ko Army Robbers babu ku a ciki,
kallansa tayi tana mamakin yadda yake d'ebewa fulani albarka,
dan ita a tunaninta shima Bafulati ne,
musamman data ganshi fari sol ga gashin kansa,
a kwance luf kamar na Larabawa,
tace " kai ba Bafulata ni bane?
"Allah ya kike yace da sauri,
ya d'ora da,
Allah ya tsare ni da zama Fulani,
ko kinga nayi miki kama da Fulani?
"Eh tace, yace "dayake kinganni fari ko?
"Ku dayake babu fari mai kyau a duniya sai ku,
"ai munfi yawa ne shiyasa da an ganka fari mai kyau ake cewa Bafulatani ne,
kuma kasan abinda yafi....
shiru tayi ganin irin kallan dayake mata,
kallanta yayi yace " shegiya kuna bayin mu amma kina min fitsara,
da sauri ta kalle shi, yace " eh ko Fulani ba bayin Barebari bane?
Sai yanzu ta gane shi Bababbare ne,
cike da mamaki ta kalle shi tace " kuma ya na ganka fari?
"Au dama Barebari babu farare?
"Eh Kakana yace min duk bak'ak'e ne, kuma masu k'aton kai da balle,
duk abi a cika musu fuska da tsagu tun suna yara,
gasu da san girma da fad'in rai,
kuma yace min Barebari bayin Fulani ne,
"tab Moli yace, amma ko zanso naga Kakan nan ki,
"saboda me?
Ta tamabaye shi,
yace " saboda ba gaskiya ya gaya maki ba,
tunda gashi kema yanzu kinga tabbas da idanki,
tunda kin ganni fari kuma babu tsagu,
murmushi tayi tana goge hawayenta,
danta gano d'an adawa ne yanzu,
dama Ganez yasha fad'a mata akwai zolaya da tsokana,
tare da wasa da dariya a tsakanin Fulani da Barebari,
tace " ai my Ulud ma.....
da sauri ya kalle, ido ya zuba mata na wani lokaci yana tunani had'i da sak'a abubuwa da dama a ranshi,
Allah kad'ai yasan meyake tunanin,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya murtuke fuska sosai kamar bai tab'a dariya ba,
fuskarsa kwata-kwata babu annuri,
Sanah na ganin haka jikinta ya soma kerrma,
tsoranta ya dawo sabo fil,
dan tasan andawo maganar laifinta,
tunda taga ya koma asalin Moli,
ya kalleta yace " yauwa dama kince kin saka hular kawai an kusa kashe ki,
ta yanzu kin saka har da takalmi da agogo a kashe ki ko?
Yayi maganar yana kallan kwayar idanta,
kuka ta saka sosai had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri,
Allah ban k'arawa, kayiwa darajar Annabi Muhammad S.A.W,
ka dubi darajar iyayenka dan Allah da Annabi,
dan darajar mahaifiyar ka kayi hak'uri ,
tayi maganar tana ci gaba da rikitaccen kuka,
ido ya runtse da k'arfi had'i da komawa kan sofa ya kwanta,
dan ko kashe shi aka ayi, aka had'a shi da girman Allah,
darajar Annabi da mahaifiyar sa,
sai ya hak'ura, duk girman laifin da akayi masa,
muddin aka yi masa wannan magiyar dole ya hak'ura,
amma da yaso ya d'and'ana mata kud'arta,
yaso tayi kuka har sai ta gaji da kuka,
amma taci darajar Allah da Annabi da mahaifiyar sa data had'a shi da su,
taje idan halinta ne zata k'ara,
yayi maganar cikin ransa, cikin kuka Sanah ta kuma cewa,
" wallahi Allah nayi maka alk'awarin ban k'ara yin wani laifin har in bar makarantar nan,
in sha Allah, Allah bama kai ba ko wani Malamin ka kama ni na kuma yi masa laifi,
kayi min duk abinda kaka dama,
a hankali ya bud'e idansa ya sauke su a kanta yace " kin tabbata?
Da sauri tace " Allah,
ya kuma cewa " ke da kanki kika ce duk abinda naga dama nayi miki ko?
Ta d'aga kanta,
yace " to ki rik'e wannan a ranki,
tace " to, in sha Allah ma bazan kuma ba,
yace " tashi kije,
da sauri jikinta na rawa ta mik'e ta fita har tana tuntub'e,
yabi bayanta da kallo,
had'i da cewa " evil girl,
sarai Sanah taji abinda yace amma ko juyowa bata yi ba.
Sir Jeeb gajiya yayi da jira yayi tafiyarsa,
dama cikin garin Roni zasu siyan abinci,
shiyasa yasa a kira Moli ko yana da sautu,
sanda ta koma class har an tashi,
dan haka ta wuce hostel, a tsaye ta iske Khulud