Advertisements
Chapter 16 Reading RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN

Author :  HAUWA A USMAN Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 38

45K to 48K   out of 111.2K words

dan itama kyakkyawa ce ta gaban kwatance,
siririya dogowa mai doguwar fuska ,
abu d'aya Sanah zata nuna mata shine wushirya da dimples,
sai kuma bam-bamcin halitta,
ita Sanah 'yar duma-duma ce irin jikin Jennifer Lopez,
ita kuma Khulud siririya ce mai irin jikin Thamanna Batia,
Sanah tad'an fi Khulud jiki da k'ira,
ita Sanah dirarriyar mace ce,
Khulud kuma irin matan nan ne da ake kira American Lady,
saboda irin jiki da shape d'in turawa ne da ita,
silent smile tayi tace " no Mamu ba sai mun karya ba,
idan muka je maci abincin,
baki Mamu ta tab'e tace " kwaji dashi dai,
ai dama nasan tunda Sanah tace " a'a kema a'an zaki ce,
Khulud ta kuma yin murmushi tace " eh mana Mamu ai ba'a tab'a raba d'aya biyu,
Mamu tace " ku dai kuka sani, idan zaku wuce ku d'auki Mash su mik'awa Halan d'anta ya dame ni da k'iniya,
baki Sanah ta turo tace " yanzu sai an samu d'aukar yaro Mamu?


Mamu zatayi magana Khulud tace " bakomai Mamu bari sai mu mik'a shi tayi maganar cikin sanyinta,
a hankali Khulud ta d'auki Mash dake ta wasa,
har sun kai bakin k'ofa Mamu tace" Khulud idan kunje kucewa Halan ta turo man da Maheen tazo,
"to Khulud tace kana suka fita,
direct part d'in Halan suka shiga,
a bakin k'ofa suka iske ta rako Ziyad ,
suna tura k'ofa Halan takai bakinta tayi masa kiss,
Sanah ta zumb'uri baki had'i da cewa " 'yan iska kawai,
tayi maganar cikin ranta,
Khulud ko kauda kanta tayi gefe ,
Halan tayi dariya tana cewa " ah ah kaga 'yan candy yau,
Sanah bata kulata ba, sai Khulud ce tace " Allah Aunty Halan yau ji nake kamar anyi man bushara da aljanna,
Halan tayi dariya tana cewa " ai haka ne dama ,
musamman kuna ganin zaku shiga sawon'yan mata,
Sanah tace " au yanzu mu ba 'yan matan bane?


Dariya Halan tayi tace " kwailaye dai,
Sanah ta turo baki " haba Aunty Halan we are 16yrs now and you call us kwailaye?


Halan zatayi magana Ziyad yace " dan ubanku baku iya gaisuwa bane?


Sanah ta kawar da kanta tana turo baki,
Khulud tace " yi hak'uri Yaya bamu lura da kai bane,
ina kwana?


Ta fad'a cikin girmamawa,
lafiya lau ya amsa mata fuskarshi a sake,
kallansa ya maida kan Sanah yace " ke zanci uwarki fa,
shegiya mai fad'in ran tsiya,mai bak'in hali,
Halan tace " a'a Abban Maheen karka kuma ce mata mai bak'in hali ba kyau,
a fusace yace " ai daman ke ke d'aure mata gindi take zubawa mutane iskaci da fitsara san ranta,,,
Khulud tace " please Yaya kayi hak'uri,
Halan ta kalli Sanah taga ko ajikinta yadda kasan bada ita yake magana ba,
idan Halan na kanta tace " Sanah!,
Sanah ta juyo ta kalle ta,
Halan ta nuna mata ta gaida shi da ido,
Sanah tace " oh! wai dama dani ake?


"Ai ban sani ba,
tayi maganar tana mik'ewa tace " sorry Yaya good morning,
ko kallanta bayyi ba yayi tsaki yayi ficewarsa,,
ta bi bayan sa da harara,
Khulud ta kafe ta da ido had'i da cewa " it's not good my Sanah, bai kamata ba,
Sanah tace " to shi abinda yayi yanzu ya kamata?


Halan tace " mai yayi?


"Ai ke dama bazaki ga abinda yayi ba,
Halan tace " oh ni Halan shi yace bana ganin laifinki ko ban san laifinki,
kema kice ban ganin laifin sa ko ban san laifinsa,
ni dai kun sani a tsakiya ,
ta fad'a tana dafe kanta,
Sanah tace " ina Maheen?


"Tana kitchen wai breakfast zata koyi had'awa,
Sanah ta zaro tana cewa " she's 4yrs fa,
Halan tace " a to na sani kotayi gadan rawar kai wajen k'aramar uwarta,
"wajen wacce uwar tata?


Halan tayi dariya tace " ni dai ai ban ambaci sunan kowa ba balle a kama ni da laifi,
"hmmmm kima ji da tsohon cikin ki,
bada tsokanar mutane ba,
" ai dole naji dashi tunda a jiki na yake,
Sanah ta mik'e had'i da dafe bayanta,
tana gwada irin tafiyar Halan tace " to mu zamu tafi,
Halan takai mata duka tana dariya,
itama ta goce tana dariyar,
Halan tace " rai dai ,ni ma zan rama,
wama yasan irin naki cikin ke,
Sanah tace " aiko bazaki rama ba,
dan ni ba anan k'asar zanyi goyan ciki na ba,
balle har ki gami,
Halan tace " ai in dai nan cikin duniyar zakiyi ciki sai na bi ki,
ko'ina ne na gano,
Sanah na shirin fita Halan ta kalli bayanta,
ta zaro ido tace " Sanah bleeding kike ne?


A d'an tsorace Sanah tace " bleeding d'in me?


Halan tace " period mana,
"ina period d'in yake?


Sanah tayi maganar tana zaro ido,
Halan tace " gashi nan ya b'ata ki,
dariya Sanah tayi tace " wai ni zaki ma wayou dan ki kama ni ko?


Halan tace " Allah da gaske nake yi maki,
jin Halan ta rantse yasa Sanah zaro ido tace " please seriously da gaske kike?


Halan ta kuma cewa " Allah da gaske ,
ta kalli Khulud tace " zo ki gani sai ki fad'a mata,
cikin sanyinta Khulud ta mik'e ta zo tana duba bayan Sanah,
kallanta kawai Khulud tayi ,Sanah ta gane da gaske ne,
ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace " just 2 weeks back ba nayi wanka,
Halan tace " ai tun kuna SS 1 nace miki kije kiga Doctor kika a'a is normal,
amma bleeding d'in yayi yawa ,kuma duk after 2 weeks period ya dawo ai da matsala idan kikayi aure,
a tsorace Sanah ta kalli Halan idanuwanta duk waje tace " wacce irin matsala kuma?


Dan kwata-kwata bata fahimci abinda Halan ke nufi ba,
murmushi Halan tayi kana tace " ke is not so serious issue ,
"are you sure?


Sanah tayi maganar cikin sanyin jiki,
Halan tayi dariya kana tace " yes Ma'am,
Khulud tayi murmushi tace " oh! ni dai na huta da wannan jidalin,
"wanne jidali?


Halan ta tambaye ta,
Khulud tace " na period mana,
Halan tace " kamar ya kin huta bayan kowacce mace bata da hutu akan shi?


Khulud tace " aiko ni Allah ya hutashe ni,
Halan tace " wai kamar ya Allah ya hutashshe ki?


Kai tsaye Khulud tace " ai ni ban fara ba ,
a kid'ime Halan ta zaro ido "what!?


Tace a razane,
murmushi Khulud tayi kana tace " yes mana,
a firgice Halan tace " wai kina nufin baki fara period har yanzu ba?


Ta tambaye ta cikin tension ,
Sanah tace " eh bata fara ba,
akwai damuwa ne?


"Innalillihi wa'inna ilaihirraji'un,
Halan tace ,Sanah da Khulud suka kalli juna cike da tsantsar mamaki,,
cikin tsoro Sanah tace " meye Aunty Halan?


Halan tace " tunda kika fara 2yrs back dama ita bata fara ba?


Cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta,
a sanyaye Khulud tace " lafiya Aunty?


Halan tace " amma shine baku fad'a anje hospital ba?


"Hospital kuma?


Khulud tace,
" eh man ai dole aje hospital dan aji meke faruwa,
mace 16yrs bata fara period ba ai akwai damuwa,
ta kalle su tace " uban me ya hana ku fad'a?


Cikin sanyin murya Sanah tace " bakomai ,ai mun d'auka there's no problem ne,
"ubanwa yace muku babu problem?

Halan ta fad'a a tsawace,
tunda suke da Halan bata tab'a yi musu ko kallan banza ba,
balle har ya kai ga tsawa ba yau sai yau,,
gasu yanzu a k'alla sun kai wajen 6yrs da ita,
saboda yadda take nuna musu so da k'auna take kuma jan su ajikinta sosai,
yasa suma suka fi sabawa da sakin jiki da ita sosai akan Seenah da Aroos,
tunda sun fahimci halin Seenah da Aroos kusan d'aya ne,
shiyasa ta su ma tafi zuwa d'aya akan Halan,
duk da babu wani rashin jituwa ko matsala a tsakanin su ,
su duka ukun,suna zaune lafiya babu wata damuwa,
tare suke yin komai,kan su a had'e yake sosai sai dai d'an abinda ba'a rasa na yau da kullum ba,
ko yaran su kan su a had'e yake suma sosai, komai na su iri d'aya ne,
dan Danish da Ganez suna iya bakin k'ok'arin su wajen ganin sun had'e kan zuri'ar su,
ta yadda ko bayan babu su,sun san basu tafi sun bar baya da k'ura ba,
kuma Alhamdulillah family'n su yana zaune lafiya cike da so da k'aunar juna,
basa tare da wata matsala ko rashin jituwa a tsakanin su,
haka ma Rawan da Hamraz suna iya yin su dan ganin sun kafawa zuri'arsu zumunci mai k'arko da dank'o,
shiyasa kullum suke k'ara nusar da yaransu mahimmanci, amfani da k'arfin zumunci,
suna koyar dasu su zama tsintsiya mad'aurin su d'aya ,
kuma cikin ikon Allah sunyi narasar kafa hakan a zukutan ahalinsu,
kowa cike yake da san d'an uwansa babu wani nuna bambamci ko ware-ware,
duk sun d'auki kansu d'aya,babu abinda wani zai zartar batare da sani ko shawarar junansu ba,
dan k'ara k'arfafa zumuncin su yasa every last Saturday ta k'arshen wata suke family meeting,
yaran Halan biyu mace da namji Maheen itace babba sai k'aninta mash,
sai yanzu data ke tsohon ciki haihuwa yau ko gobe,
Aroos kuma yaranta biyu duk mata Aabish ce babba sai Aairah bata kuma da ciki,
dan tace sai ta huta,
Seenah yaranta d'aya namiji Ejaz itama tana da ciki.......


Duk sukayi shiru cikin sanyin jiki ta kalle su tace " saura awa nawa ku shiga last exam?


"1hr 40 minutes Khulud ta bata amsa cikin sanyin jiki,
dan tunda suke da ita basu tab'a ganin b'acin ranta irin na yau ba,
ta kalli Sanah tace " na baki just 10 minutes kije ki gyara jikinki kizo yanzu mu tafi holital,
Hospital ?


Sukace cike da mamaki,
batare data kalle su ba , ta d'auki wayarta tayi hanyar bedroom tana dialing number Ziyad,
duk suka bi bayanta da kallo,
Khulud tace " kiyi sauri ki shirya naga alamar yau ranta yayi masifar b'aci,
"ok kawai Sanah tace tana barin wajen,
a parlor ta tarar da Mamu zaune akan sofa da remote a hannunta tana canja channel,
cikin mamaki Mamu ta kalle ta tace" au dama baku tafi ba?


Sanah tace " eh jiki na zan gyara tayi maganar tana shiga d'aki da sauri,
cikin gaggawa Sanah ta shirya, ta fito da gudu zata fita,
Mamu tace " kin d'ibi pad & pant spare?


Kanta ta dafa alamar mantuwa kana ta juya ta kalli Mamu tace " thank you,
ta koma d'akin da gudu ta d'ebo ta watsa cikin school bag d'inta ,
ta fita da gudu, a harabar gidan ta iske Khulud da Halan tsaye ,
suna ganinta suka shiga bayan mota ,
driver ya ja motar,
a harabar Nasarawa Hospital sukayi parking,
batare data kalli inda suke ba ta fita suka bi bayanta,
bayan ta gama yiwa Doctor bayanin matsalar data kawo su,kana ya kalli Khulud yace " kina jin ciwo ko wani abun ne?


Tace " a'a ,
yace " baki jin wani sigh a mararki ko cikin ki?


Tace " eh ban jin komai,
a hankali ya mik'e yaje bakin gadon dake cikin office d'in,
ya kalle ta yace " Bismillah,
ba musu ta mik'e taje inda yake tsaye,
yace " kwanta,
gyara mata kwaciyar yayi ,
sannan ya d'an d'aga rigarta yayi k'asa da wondon uniform d'in dake jikinta,
yasa hannu a hankali yasa d'an danna mararta,
yace " duk inda na tab'a kikaji zafi ko wani emotions kiyi man magana,
tace "tom,
yakai wajen 10 minutes yana tab'awa amma batayi magana ba,,
ya kalle ta yace " baki ji komai ba?


Tace "eh,
" sakko yace mata,yana barin wajen,
'yan rubuce-rubuce yayi kana ,ya kira nurse yace " kije da ita,
ki kaita Scanning room,
za'ayi mata Scanning kala biyu,
na mara dana mahaifa,
sannan ki kaita lap a d'ebi jininta,
"Ok Sir tace cikin girmamawa,
sai da suka yi wajen 1hr a hospital d'in ana gwaje-gwaje da aune-aune,
sannan Doctor ya dawo , ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan,
yace " gaskiya munyi mata duk abinda ya kama,
munyi mata Scanning & tests amma bamu ga komai,
asalima lafiyarta k'alau tana cikin k'oshin lafiya,
babu wata matsala ko damuwa,
kana ya d'ora da cewa " kowanne mutum da kika gani akwai irin nau'in halittarsa,
da kuma kwayayensa,da organs & cell d'in jikinsa,
dama ana iya samun irin haka,
sai kiga wata macen ma takai 22yrs bata fara period ba,
ko kuma kiga mace bata da ciki ,
asalima bata da auren amma sai kiga tayi wajen 5monts batayi period ba,
muna kiran abun a likitance Hormonal imbalances,
kuma abubuwan dake haifar da haka suna da yawa akwai,
Birth Control,
Thyroid irregularity ,Polycystic ovary syndrome (PCOS),
Early peri menopause,
Stress ,weight loss and Breastfeeding,
wad'annan abubuwan suke iya haifar da dad'ewa ba'a fara period ba,
ko mace ta dad'e bata ga yazo ba,
amma ita Khulud lafiyarta k'alau kawai Allah ne yasa bai zo ba,
ajiyar zuciyar Halan ta sauke,kana tayi masa godiya suka fice,
ana saura 15 minutes su shiga exam suka isa makaranta,
d'alibai na ganin Sanah suka saki ihuuu ,
dan Sanah popular student ce,Halan taita dariya had'i dayi musu addu'ar sa'a.


Suna fitowa daga exam hall suka fara sakin ihuuu,
wasu daga cikin students d'in na yayyaga uniform d'in su,
duk d'alibin daka kalla a ranar kasan yana cikin tsananin farin ciki,
assembly principal da teachers sukayi musu as usual sukayi musu nasiha mai ratsa jiki da jijiya,
aka basu shawarwari akan rayuwar duniya,
daga wajen assembly wajen bikin murnar yaye d'alibai suka nufa ,kowa yaci yasha cikin tsantsar farin ciki,
kana aka sallami kowanne students d'auke da kyautar da yasamu,
kasancewar Khulud itace mosque prefect yasa aka bata kyaututtuka masu tarin yawa,
harda Qur'an da litattafan addini,
itama Sanah dayake itace Labour prefect itama tasha kyauta sosai,
dan principal naji da ita sosai,
dama su Sanah sunce kar azo d'aukar su daga gida dan zasu biya wajan saloon da henna,
saboda Abbu ya shirya musu walima a gida saboda tare sukayi Candy da saukar Al Qur'an mai girma,
fita sukayi daga cikin get d'in makarantar suka nufi bakin titi dan shiga napep.


Sanah ta kalli Khulud cikin tsananin farin ciki tace " my Ulud ya kike ji yau?


Khulud tayi murmushi kana tace " wallahi ji nake kamar na zuba ruwa a k'asa nasha dan murna,
muma yau mun girma mun zama 'yan mata Classy & big Beb ,
"ke ya kike ji yau my Sanah?


Tayi maganar tana kallan Sanah,
Sanah tayi gaba had'i da juya bayanta tana tafiya tana fuskantar Khulud,
tace " ni kuma yau ji nake kamar nayi ta burgima a k'asa ina ihuuuun dad'i,
Khulud tace " my Sanah kin juyawa titi baya fa,
kuma kina tafiya da baya-baya bayan kin san ba kyau,
Sanah ta d'aga hannayenta sama cikin farin ciki tana tsalle tace " barni my Ulud yau d'aya nad'an sha iska na wataya,
ta fad'a tana dariya,
d'aga idan da Khulud zatayi taga wata sabuwar mota dalleliya kirar Kia 2019 ,
ta nufo Sanah gadan-gadan,
a kid'ime Khulud ta saki k'ara had'i da d'ora hannu aka,
ganin haka yasa Sanah juyawa a firgice,
shima matuk'in motar kwata-kwata bai lura ba sai da yaji ihuuun Khulud,
a gigice ya taka burki da k'arfi k'uuuuuu,
duk da haka sai da motar ta gogi Sanah,
ta fad'a cikin ruwan dake tare gefen hanya kasancewar kwana akayi ana ruwan sama jiya,
hijab d'inta da d'ankwalinta suka fad'i gefe,
kwantaccen gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuskarta,
hannunta ta saka ta kawar da gashin gefe,
bakin bud'e take bin jikinta da kallo ,
taga yadda duk ruwan ya gama b'ata ta,
taga mai motar kwata-kwata bashi da alamar fitowa da alama ma jira yake ta tashi ta bashi hanya ya wuce,
cikin tashin hankali Khulud ta k'araso tasa hannu tana k'ok'arin d'ago Sanah,
tace " my Sanah baki ji ciwo ba dai ko?


Sanah tace " babu abinda ya same ni,
ki koma gefe ga guri can ki zauna yau zanga k'aryar iskanci,
ta fad'a tana kallan motar,
Khulud tayi dariya kana tace " a'a my Sanah ki tashi mu tafi,
zamanta ta gyara sosai a cikin ruwan kana tacewa Khulud " kin san Allah ban tashi,
sai dai mu kwana anan naga k'aryar taurin kai,
d'an gutun tsaki yaja had'i da gyara zansa a cikin motar ya k'ara k'arfin ac,
kana ya kwantar da kujerar motar baya,
ya kishingid'a gami da lumshe idonsa,
sun kai wajen 30 minutes a haka Khulud na tayiwa Sanah magiyar ta tashi su tafi amma tak'i,
idansa ya d'an bud'e gami da kallan agogon hannunsa k'irar Gucci,
ya ja tsaki ganin tana niyyar b'ata masa lokaci,
cikin isa da tak'ama gami da aji ya zuro k'afarsa d'aya k'asan motar ,
sanye da takalmin Gucci sau ciki,
wacce kallo d'aya zakayi mata kasan k'afar d'an hutu da jin dad'in duniya ce,
sai da akayi 2 minutes kafin ya k'ara fito da d'aya k'afar tasa,
nan ma sai da yayi wajen 2 minutes kafin ya fito gaba d'ayansa,
ya taka k'asa kamar baya so,
dai-dai lokacin idan Sanah ya sauka akan.................





MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_




*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```




1⃣6⃣




Idon Sanah ya sauka akan pant & pad d'inta da suka watse a k'asa,
kallanta ta mayar kan matashin saurin daya fito daga cikin motar,,
wanda bazai wuce 30yrs ba,
hannayensa ya hard'e a k'irjinsa,
kwata-kwata fuskarsa babu alamar annuri,
cikin izza yace " hey common from here ,
yayi maganar cikin zazzak'ar muryarsa,
wani irin wulak'antaccen kallo Sanah ta watsa mishi,
kana tace " baka iya bada hak'uri bane?


"Ko ba'a koyar da kai sanin darajar 'ya mace ba?


Tayi maganar cikin tsiwa,
a k'ufule yace " ina macen take anan?


Ya fad'a yana yi mata kallan banza,,
"ok tunda baka ga mace ba,ai kaga mutum kuma 'yar Adam ko?


Tsaki yayi kana yace " ni banga komai ba sai dabba,
"oh! kai kuma naka salan rainin wayan kenan,
tayi maganar tana mik'ewa tsaye,
tsawa ya daka mata " dalla can bani hanya ko na bi ta kanki ta taka banza,
Sanah tayi murmushi had'i tattare hannun rigar ta ,
ta hard'e hannunta a k'irji had'i da zuba masa lulu eyes d'in ta,
kana tace " Bismillah,
tayi maganar cikin tsiwa ,
"Ok yace yana komawa cikin motar had'i da cije leb'ensa,
Khulud tayi saurin cewa " a'a dan Allah kayi hak'uri ,
tayi maganar cikin sanyinta,
sai lokacin idansa ya sauka akan Khulud,
kallanta ta mayar kan Sanah tace " My Sanah please bashi hanya,
kinsan ban san rigima da tashin hankali ko?


Sanah tace " barni dashi idan kanshi hayak'i yake ni nawa wuta yake ci,
barni naga iya inda tashi rashin kunyar ya tsaya,
ta fad'a tana kallan shi ido cikin ido,
takowa yayi a hankali har zuwa gabanta,
yayi guntun murmushi kana yace " kinci sa'a, wallahi badan darajar wannan 'yar uwar taki ba, da sai na koya miki hankali,
ki kuma godewa Allah sai bayan na ganta kika ce kina san ganin kalar tawa rashin kunyar,
da sai na nuna miki bambamcin fitsara ta da taki,
idonta na cikin nashi tace " ok to mai zai hana yanzu ma nuna min,
tunda na fuskanci mara tarbiyya ne kai,
a fusace ya d'aga hannu zai wanka mata mari ,
tayi saurin rik'e hannunsa, tayi guntun murmushin gefen baki tace " hey! karka kuskura ka soma,
dan ba kunyar ramawa zanji ba,
nonsense kawai,
cike da tsantsar mamakin rashin kunya da fitsarar ta yake kallanta,
a ranta ya maimaita nonsense,
ya bud'e baki zayyi magana, Khulud tayi saurin shiga tsakiya tana kallan Sanah tace " wai me yasa kike haka ne My Sanah?


" Na fad'a miki ban san hayaniya,
baki Sanah ta turo tace " bakiga abinda yayi man ba?


" Amma shine dan iskanci

16 / 38