Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
bango,
kanta fashe jini ya fara zuba, kwata-kwata bata damu da ciwon data ji ba,
dan bama tasan taji ciwon ba,
cikin kuka tace " dan girman Allah kayi min gurbi a zuciyarka,
wallahi idan kace a'a mutuwa zanyi,
please ta had'e hannayenta biyu tana rok'onsa.
Shiru kawai yayi yana kallan ikon Allah,
yarinya k'arama har ta san so?
Ta san ta haukace akan son d'a namiji haka?
Mik'ewa ta tayi ta nufe ta shi kanta na zubar da jini,
amma kwata-kwata bata damu da yadda jinin ke zuba daga jikin nata ba,
tana zuwa kusa dashi ta fad'a jikinsa ta rungume shi gami da k'ara saka kuka,
cikin matsanancin b'acin rai da zafin zuciya,
Moli yayi wurgi da ita gefe, kanta ya kuma bugar bango k'ummm,
goshinta ya kuma fashewa, a haukace ta taso tana sake k'ok'arin rungume shi,
wasu kyawawan marika ya shiga zuba mata a jere har guda shida 6,
had'i dayin ball da ita yayi mata k'afa a bayanta,
ta fad'a kan table d'in dake tsakiyar office,
cikinta ya bugu sosai, ta sulale k'asa cikin mawuyacin hali,
a kanta ya tsaya yana kallanta cike da tsantsar tsana yace,
"ni kuma bana sanki, na tsane ki,
ban zan tab'a sanki ba, bazan kuma tab'a jin ina sanki ba daga nan har k'arshen rayuwa ta,
wallahi ko mata sun k'are a duniya babu abinda zanyi dake,
shegiya 'yar iska fasik'a, kina shiga jikin nawa zaki ce naso ki?
"Nasan iya adadin mazan da kika yiwa haka,
kenan 'yar k'aramar yarinya dake har kin san so?
Kina da 14yrs kin san ki d'orwa kanki cuta mai girma akan d'a namiji,
to ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare ni da idan basira,,
ni Moli bana sanki, bazan tab'a sanki ba, bazan kuma aure ki,
da in aure ki gwara na mutu banyi aure ba,
useless girl kawai, k'ananan yara daku amma kun san ku so maza,
shegu, jakai, k'idahumai, lusaran banza,
Allah ya tsare ni da aure ki, ko laifi nayiwa Allah ya hukunta ni da sonki ko aurarki nasan nayi laifi mafi girman gaske.
Murmushin bak'in ciki tayi cike da takaicin zuciyarta na fad'awa san wanda bai san daraja da mutuncin d'an Adam kwata-kwata ba,
ta kalle shi ido cikin ido tace " bakomai nagode matuk'a, amma ka jira sakayyar Allah,,
a bisa wulak'anci da cin zarafin daka yi min akan abinda bani da d'orawa kai na ba,
nima da ina da yadda zanyi da tuni nayiwa kai na magani,
amma in sha Allah kai ma sai Allah ya d'and'ana maka irin ciwon danake ji,
sai Allah ya jarrabeka da soyayya mai rad'ad'i da zafin gaske fiye da yadda nake ciki,
in sha Allah kai ma bazaka tab'a samun macen dake so ba,
bazaka tab'a mallakarta a matsayin mata ba,
kuma in Allah ya yarda akan idanka kana ji kana gani za'a raba ka da ita,
bawai kuma dan an fi k'arfin ka ba,
sai dan Allah ya d'and'ana maka zafin rabuwa da masoyi da abinda zuciya ke so,
take mararin samu, kamar yadda nima naji,
da k'unar rashin mallakar masoyi,
kai ma sai kayi zafin rabuwa da abinda zuciya ke so,
da yarda Allah sai kayi kuka akan so,
kamar yadda nima nayi,
sai ka rasa tausayawar kowa,
kamar yadda nima na rasa tausayawa daga gareka,
in sha Allah sai kayi son maso wani,
sai soyayya ta gwara kanka, ta wahalar dakai da wannan bak'ar zuciyar taka,
sai ka d'and'ani zafin rabuwa da masoyi,
ka d'anani zafin da ake ji idan ka cewa mutum kana sanshi yace maka baya sanka,
In Allah ya yarda sai mace ta kalli tsabar idan ka tace maka bata sanka,
bayan ka sanar da ita kana santa,
sai an wulak'anta ka an k'ask'antar dakai,
daga lokacin ne zaka fuskanci meye rayuwa, meye duniya,
ina mai tausayawa rayuwarka a lokacin.
Kum.........
Saukar gigitattun marikan,
dataji ne ya hanata k'arasa maganarta,
tassssssss kauuuuuuu
ya fara janta a k'asa, saboda magaganun data fad'a masa,,
sun kawo shi har wuya, zuciyarsa ta hasala iya hasala,
jin k'irjinsa yake kamar zai kama da wuta saboda tsananin b'acin rai,
duk ilahirin jikinsa kerrrma yake, yana tsuma,
yayinda gumi keto masa yake tako'ina,
mak'ogwaransa nayi masa zafi,
yawon bakinsa nayi masa d'aci,
a k'asa ya fara janta yana nufar k'ofar fita daga staff room,
dai-dai lokacin Sanah da Khulud sunzo shigowa staffroom,
ganin yadda gaba d'aya kamanninsa suka sauya ne yasa Sanah da Khulud saurin ja da baya,
idanuwansa sun koma pure red,
a haukace ya fara dukan ta ba ji ba gani,
ganin yadda yake dukan ta ga jini na fita daga jikinta yasa Sanah da Khulud rud'ewa jikinsu ya d'auki muguwar kerrrma,
dan duk iskancin Sanah bata san abinda zai tab'a lafiyarsa,
sosai Moli yake ball da ita yana surfa mata ruwan ashar,
sosai tsoro yayi bala'in kama su Sanah, har Khulud ta saki fitsari a wando batare data sani ba,
itako Sanah saboda tsabar rud'ewa hannu ta d'ora aka had'i da fasa kuka,
daga Sanah har Khulud duk sun rud'e matuk'a sun fita daga hayyacinsu.
Da sauri Malamai suka taso suka rik'e shi,
dakyar suka iya kwatar Siyah daga hannunsa,
komawa yayi ya zauna akan step d'in shiga staffroom gami da dafe kansa da duka hannayensa,
kasancewar Sanah bata cikin hayyacinta yasa har lokacin kuka take jikinta na b'ari,
Khulud kam saboda tsabar tsoratar data yi ma kasa kukan tayi ita,
sai jikinta dake kerrrma, fitsarin datayi duk ya b'ata mata kaya,
kukan Sanah ne ya fara hawar mishi kai,
a hankali ya d'ago red eyes d'insa ya kalli inda yake jiyo kukan,
karaf idansu suka sark'e cikin na juna shi da Sanah,
ganin yadda idanuwansa suka koma red ya k'ara tsorata Sanah,
tsawa ya daka mata " shut up,
ai tun kan ya k'arasa Sanah da Khulud suka zunduma a guje,
basu tsaya a ko'ina ba sai a hostel d'in su, cikin kwanar su,
Halan na kwance suka shigo da gudu,
duk sun firgice sun fita daga hankalin su,
"Lafiya na ganku haka?
Cewar Halan, magana suke san suyi mata amma dukkan su sun kasa koda furta kalma d'aya ce,
kama su tayi ta zaunar dasu, sannan ta mik'e ta d'auko pure water ta mik'a musu da sauri suka amsa,
jiki nata b'ari suka sha,
sai da ta bari a k'alla sunyi 15 minutes,
ta zabbatar sun dawo cikin hayyacinsu,
nutsuwar su ta dawo normal kana ta kuma tambayarsu,
"wai me ya faru na ganku kun dawo a kid'ime,
kamar wad'anda suka ga mutuwa?
Cikin kid'ima Sanah tace " Sir Moli ne zai kashe wata,
ido Halan ta zaro cike da tsoro,
tace " ince dai baku mishi komai ba ko?
Cikin rawar murya Sanah tace " ai har abada babu abinda zamuyi mishi,
Halan ta tuntse da dariya tana cewa " tab yau Sir Moli ya furgita wasu,
ashe fa baku tab'a ganin b'acin ransa ba ko?
"Baku tab'a ganin yana duka ba ne shiyasa wannan ya d'aga muku hankali,
ai duk wacce ta sake ta kawo mishi wurgi ko ta shiga track d'insa,
ta kad'e daga ita har buzunta,
dan kwata-kwata bashi da tausayi idan ranshi ya b'aci, bak'ar zuciya ce dashi,
wannan dalilin me yasa nake matuk'ar mamakin yadda kike masa abubuwa da dama,
amma yake sharewa yana d'aga miki legs ta k'arasa maganar tana dariya,
Khulud da har yanzu jikinta ke kerrrma yake saboda tsananin tsoro da firgici,
tace " yanzu Aunty muma zai iya yi mana irin wannan mugun dukan?
"Ku a wa da idan kuka cika shi zai kasa jibgar ku?
Tsoro ne ya k'ara mugun kama su,
cikin rawar murya Sanah tace " ai bama zamu cika shin ba,
in sha Allah daga yau na daina yi mishi duk abinda nake yi,
bazan k'ara yi masa fitsara da rashin kunya ba,
daga yau duk abinda yace nayi zanyi,
bazan kuma yi mishi musu da rawar kai ba,
wai idan mu yayiwa wannan jahilin dukan ai mutuwa zamuyi,
Khulud da jikinta har lokacin kerrrma yake ta kasa cewa komai sai ido kawai datake bin Sanah dashi,
cikin sanyin murya Khulud tace " Allah Aunty Halan sai yayi mana irin wannan dukan?
Halan tace " wallahi har fiye da haka ma yana iya yi muku,
muddin kuka kai shi bango, hak'urin dayake yi a kanku ya k'are,
dan idan ransa ya b'aci, idansa rufewa yake yi ruf,
bashi d.....
fitsarin data gani a jikin Khulud ne ya hana ta k'arasa fad'ar abinda tayi niyya,
ta kalle ta cike da mamaki tace "Khulud fitsari kikayi?
Da sauri Khulud ta kalli jikinta,
dan ita bama tasan tayi fitsarin ba,
Sanah ta kalle ta cike da mamaki tace " Uludi na ya haka?
Khulud tace " wallahi ni bamma san nayi ba,
tayi maganar cikin sanyin murya,
Sanah da Halan suka saka mata dariya,
haushin dariya da suke yi mata yasa ta fashew da kuka,
Sanah tayi saurin mik'ewa taje inda take tsaye ta rungume ta,
tana cewa " yi hak'uri Uludina, ni ce ko?
"Na dai na ban k'arawa, muje na rakaki kiyi wanka, kuma mun b'ata da Aunty Halan bamu kuma yi mata magana.
Hakan tayi dariya tace " Auntyn guda za'a daina yiwa magana?
"Anya kuwa Auntyn ce?
Basu bata amsa ba suka yi hanyar Bathroom suna dariya,
Siyah bayan Malamai sun kwace ta dakyar a hannun Moli,
zubewa tayi a k'asa had'i da fasa fininannan kukan bak'in ciki,
bawai kukan dukan da Moli yayi mata take ba,
kuka takaicin zuciyarta take yi,
da har yanzu tak'i ganin koda laifin Moli ne,
balle ta rage ko ta daina san shi,
sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e,
ta zuba mishi ido tana kallansa,
tare da cewa " ita zuciya bata san rashin cancanta ko cancantar abinda ya kamata koya dace da ita ba,
haka k'unci da k'untatawa, muzantawa, wulak'anci,
duk basa hana ta cigaba da san abinda take so,
wallahi nasan koda zaka rink'a kashe ni a kullum ina dawowa,
zuciya ta bazata tab'a koda rage kad'an daga cikin azababban son da take maka ba,
harta juya zata tafi, ta kuma juyowa tace " ka sani Siyah nayi maka mugun mahaukacin so,
kuma zata cigaba dayi maka wannan son har k'arshen rayuwarta,
nayiwa kai na alk'awarin matuk'ar bakai zan aura ba, babu ni babu yin aure har abada,
idanko har zanyi aure a duniya to ka tabbatar da kai ne wanda zan aura,
idan ba kai bane wallahi Allah bazan tab'a yin aure ba,
har abada har in koma ga mahalicci na,
zan kasance mai jiranka a koyaushe,
a wanne lokaci na rayuwa ta da fitar numfashi na,
kowanne hours, minutes & seconds,
zan kasance mai dakon jirank.....
A harzuke Moli ya nufe ta....
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
7⃣
Da sauri Malaman suka kuma tare shi,
d'aya daga cikin Malaman ne ya buga mata tsawa "oya get loose,
da sauri tabar wajen jikinta na kerrrma,
dan yadda Moli ya taso ba k'aramin tsotsata ta yayi ba,
a harzuk'e Moli ya koma office d'insa,
ya zauna akan sofa gami da rafka uban tagumi yana tanani,
ji yayi gaba d'aya duniyar tayi masa bak'in k'irin komai ya fita a ransa,
ya kuma fara jin haushin kansa,
dan gani yake kamar rai ni ne yasa Siyah yi mishi haka,
ransa a matuk'ar b'ace ya mik'e ya rufe office d'in ya fita ya bar makarantar gaba d'aya,
kalaman da Siyah tayi na k'arshe su suka bawa sauran malaman damar fahimtar abinda ya faru,
a tsakanin su, Sir Jeeb shiru kawai yayi yana nazarin abubuwa da dama,
shi yanzu yaran ma sun fara bashi tsoro,
duba da abinda ya faru da Siyah,
wato dai idan ya fahimta son Moli take yi,
kuma hakan ne ya haifar mata da hawan jini,
a fili Jeeb ya furta "Ya Salam.
Kwance yake a kan k'atuwar katifarsa,
daga shi sai boxer,
gaba d'aya duniyar tayi masa zafi,
k'irjinsa sai tafasa yake yi yayinda zuciyar keyi masa k'una,
a hankali ya runtse idanuwansa,
yana tuna abubuwan da suka faru,
gami da kalaman Siyah, guntun murmushi yayi, bayan ya tuna wai sai yayi kuka akan soyayya,
sai ya durk'usawa mace, kuma sai ya ruk'i a soshi,
a fili yace " God forbid,
ni har akwai macen data isa nayi duk wannan abin akan ta?
"Ina babu ita, dan ko uwarta ma ba'a haifa ba,
tsoki yaja mtsssssss had'i da cewa " shegiya banlagaza,
tsoki ya kuma ja lokacin daya tuno rungumshin datayi,
yana bin jikinsa da kallan k'ama ,
"yar iska ya fad'a yana furza iskar saman leb'ensa,
tunowa da su Sanah yayi da yadda tsoro yasa Khulud sakin gitsari a wando,
da yadda yaga idan Sanah,
ya tuna yadda take kuka jikinsu na kerrmar tsoro duk sun furgice,
dariya yayi tare da cewa " k'aramar 'yar iska,
shegiya mara kunyar k'arya, ashe iya nan fitsarar taki ta tsaya yayi maganar yana dariya.
Washe gari da kamar bazai zo office ba,
amma kasancewar ya tashi yaji shi so fresh babu wani abinda ke damunsa,
ya sashi shiryawa ya tafi makarantar,
bayan ya shiga staff yayi signing,
ya fito ya nufi area classes,
daga bakin Hostel get ya hangi su Sanah na tahowa,
agogon hannunsa ya duba yaga 8:40am na safe,
komawa yayi ya tsaya had'i da sark'e hannunsa,
Khulud ce ta fara hango shi tsaye ya kafe su da ido,
ai cikin tashin hankali ta tab'a Sanah,
ganin yadda hankalin Khulud yayi masifar tashi lokaci d'aya yasa Sanah cewa,
"Ulud lafiya naga duk kin birkice?
Kasa magana Khulud tayi saboda yadda Moli ya kafe su da ido,
sai da hannun ta shiga nunawa Sanah Moli,
rolling idanuwanta tayi kana ta kalli inda Khulud ke nuna mata,
karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna,
saboda tsabar tashin hankali da firgicin da Sanah ta shiga baya tayi zata fad'i,
da sauri Khulud ta tare ta cikin k'arfin hali tace " my Sanah ki kula karki ji ciwo,
Sanah tace " please tayani duba gaban mu, kamar Sir Moli nake gani ko?
"Ba kama bace shine, cewar Khulud tana k'ifk'ifta idon tsoro,
k'irji Sanah ta dafe had'i da cewa " wayyo yau mun shiga uku,
Khulud tayi kiyi shiru please kar yayi tunanin ko wani mugun abun muke cewa a kansa,
d'if Sanah ta d'auke wuta jin abinda Khulud tace, har suka k'arasa wajensa,
kansu a k'asa suna k'ok'arin wuce shi,
tsawa ya daka musu kana cikin fad'a yace,
" ke dan uban ku zo nan,
sumi-sumi suka nufi inda yake tsaye kan su duk'e,
bisa mamakin Moli yaga Sanah tayi saurin duk'awa bisa gwiwowinta,
duk ilahirin jikin su kerrrrma yake,
ganin yadda jikinsu ke kerrma cike da tsoro ne ya kusa bashi dariya,
amma dayake muskili ne sai ya dake ya k'ara had'e ransa murtuk,
"ku dan uwarku yanzu ne lokacin zuwa class?
Cikin rawar murya Sanah tace " we are sorry Sir,
"cewa nayi yanzu ne lokacin fitowa class?
Ba hak'uri nace ki ba ni ba, amsa nake so,
yayi maganar a tsawa ce,
jikin Khulud na kerrrma tace " a'a, ba yanzu bane,
"ok wato iskanci da fitsara ce tasa ku k'in fitowa da wuri kenan?
Muryar Sanah na rawa tace " a'a ba haka bane, wallahi muna fitowa akan lokaci, yaune rana ta farko da muka tab'a zuwa class late,
tabbas Moli yasan basa makara dan bai tab'a tare su a cikin late comers ba,
"uban me tsaida daku yau?
Khulud tace " school bag d'ina na manta shine muka koma muka d'auko,
"lalle baki d'auki karatun da mahimmanci ba tunda har kike manta school bag kacokan a hostel,
shiru sukayi babu wanda yace wani abu,
yaja dogon tsoki mtswwwww bastard girls,
yayi maganar yana wucewa,
ajiyar zuciya suka sauke da k'arfi,
Sanah tace " Allah yayi mana gyad'ar doguwa,
Khulud tace " yau dai Allah ya kub'utar da mu,
waigowa yayi yaga har lokacin suna inda ya barsu a durk'ushe,
tsawa yayi musu a fusace " dan uban ku bazaku shiga class ba?
Tun kafin ya gama rufe bakinsa sun kwasa a guje sunyi cikin class,
sai da ya gama koyar da duk classes d'insa kana ya koma staff,
office d'insa ya wuce direct ya kwanta akan sofa,
bai dad'e da shigowa ba Sanah ta shigo, staff d'in d'iban chock,
jin taku ya sashi bud'e idansa dayake a lumshe,
ganin Sanah na sand'a a hankali yasa shi mik'ewa ya fita a hankali dan yaga me zata yi,
lek'awa ta fara yi ta window taga ba kowa a staff d'in,
kowanne malami yana class,
ganin haka yasa Sanah sakinF tsoki,
ta shiga staff d'in kai tsaye da takalmi,
har ta d'ebo chock d'in zata fito,
idanta ya sauka akan hular Sir Moli,
dashi kansa ya manta da ita, daya shigo da safe d'azu gaisawa da sauran Malamai ne ya manta ta,
komawa tayi ta aje chock d'in, akan table kana ta d'auki hular ta saka a kanta, zuruf hular ta shige,
"wai wannan mutumin badai ra'asun ba,
ashe k'aton kai gare shi yake yiwa mutane d'agawar banza,
saita hular tayi akanta sosai kana ta tsaya yadda yake tsayawa,
had'i da hard'e hannayenta a k'irjinta kamar yadda yake yi,
ta kwaikwayi maganarsa tace " ku 'yan daba ne?
Ta kuma gyara tsaiwar sosai taci gaba " ku yanzu ne lokacin fitowa class?
Tayi maganar tana duba hannunta kamar yadda yayi a lokacin,
duk abinda Sanah keyi Sir Moli na bayanta yana kallan ikon Allah,
tuntsewa tayi da dariya sosai ja'irin yaro mai girman kai da fad'in rai,
ta kuma gyara zaman hular akanta,
ta saka dariya , tana cikin dariyar ta d'ago kai,
aiko d'ago kan da zatayi karaf sai cikin nashi,
a fili Sanah ta furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
iya rud'ewa da firgice Sanah ta shige shi,
hankalin ta yayi mak'urar tashi,
tsoro yayi masifar kamata, lokaci d'aya duk ilahirin jikinta ya d'auki kerrrrma,
ganin babu sarki sai Allah yasa Sanah fara kuka, tana ja baya zata cire hular kanta.
Sosai Sanah take kuka kamar ranta zai fita
shiko yayi shiru gami da tsura mata ido batare dayace komai ba,
durk'usawa Sanah tayi a k'asa bisa gwiwowinta