Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
" am sorry Sir ban gani ba ne,
tayi maganar kanta na k'asa,
tsaki yayi mtswwwwww had'i da cewa " fool yayi gaba,
bayansa tafi da kallo cike da takaici tace "wicked & stingy man.
Tsawa yayi cak a inda yake had'i da juyowa ya zuba mata idansa,
Khulud tace " mun shiga uku wallahi yaji abinda kika ce,
tayi maganar tana zaro ido waje,
kanta ta duk'ar k'asa batare datace komai ba,
sai da yad'an d'auki lokaci yana kallanta kafin ya girgiza kansa,
ya juya yaci gaba da tafiyarsa,
har ya kai bakin k'ofar class d'in dazai shiga ya juyo,
aiko karaf suka had'a ido cikin na juna,
k'in kawar da idanta tayi shima haka,
a hankali ya motsa bakinsa yace " jackass,
ido ta rufe tana jin k'onar abin har cikin zuciyarta,
Khulud tace " sai mu tafi ko?
Tayi maganar tana rik'o hannunta,
ba musu ta bita kamar rak'umi da akala,
har Sir Moli ya gama koyar da class d'in hankalinsa yana kan kalmar da Sanah ta fad'a masa,
bayan an tashi daga class direct masallaci ya wuce yayi sallar zhur,
kafin ya wuce office d'insa, ya kwanta akan sofa yana tuna kalmar wicked & stingy man,
kai ya girgiza had'i da furta kalmar a fili " wicked & stingy man,
a fili yace " yarinya dole ki biya da kanki,
yayi maganar yana mik'ewa had'i da had'a kayansa,
ya fita daga office ya nufi gida dan kwata-kwata school d'in ma ta fice masa a rai.
Su Sanah kam babu abinda ya dame su,
hankalinsu kwance suke harkokin su,
dan sun san da zai d'au mataki da tun d'azun da akayi abin ya d'auka,
bayan sun tashi daga class, sunje maasjid & dinning hall,,
Hostel suka nufa, Aunty Halan suka iske tana gyara musu kwana,
da sauri suka k'arasa inda take,
Khulud tace " kai Aunty maimakon ki bari muzo mu gyara da kan mu?
"Lah bakomai ai ku k'annena ne,
dan na gyara muku ba fad'uwa nayi ba,
nima k'aruwar kai na ce, tunda lada zan samu,
murmushi Sanah tayi hannuwanta sark'e a k'irjinta tace " Aunty Halan tun da nake a rayuwa ta ban tab'a ganin mutum mai sauk'in kanki da sanyin zuciya irin ki ba,
dariya tayi tace " sai Uludin ki,
dan nasan itama zata iyayin fiye da abinda nayi,
Sanah tace " kai Aunty Halan ni fa?
Tayi maganar cikin shagwab'a tana zumb'uro baki,
Halan tace " ai duk ku biyun nake nufi,
amma fa idan mutum ya daina zafin rai da tsiwa,
dariya Sanah tayi had'i cewa " ai na daina, naji fad'an ku ke da Uludina,
Khulud tace " ina fa kika daina tunda yauma kin kuma,
" na kuma me?
"Ni dai duk abinda nayi aban iya nake ba, kullum nice cikin laifi,
Halan tace " hala yauma ta kuma tsokanar tasa?
Tayi maganar tana cigaba da gyara kwanar,
Sanah tace " au tsokanarsa ma nake yi?
"Sosai ma cewar Khulud, Halan tace " ni ina mamakin yadda Sir Moli yake bala'in d'aga miki k'afa haka,
abin har d'aure min kai yake, gaskiya kina cin sa'arsa, Allah kuma yana d'ora ki a kansa,
dan Sir Moli asalin mugu ne ga bak'ar magana,
dan idan ya fad'awa mutum wata maganar wallahi har gwara ya dake ka,
Khulud tace " ai jiya taga ni da idanta,
ta kuma ji da kunnanta, amma yau tsabar rashin ji ta kuma ce masa wicked & stingy man,
ido Halan ta zaro a tsorace tace " ya kuma ji ta?
"Sosai ma tunda har juyowa yayi ya kalle ta,
dan yama dad'e yana kallan nata,
ido Halan ta zuba mata na wani lokaci,
sannan ta sauke nannauyen ajiyar zuciya had'i da cewa " Allah ya kyauta,
Khulud tace " Amin,
cikin sanyin murya Sanah tace " Aunty Halan badai fushi kikayi da ni ba ko?
Murmushi Halan tayi had'i da shafa kanta tace " a'a ko d'aya,
kawai dai ina tunanin abubuwa da dama ne, ina kuma tausaya miki ranar dazaki shiga hannunsa,
dan nasan ranar da kika cika shi,
idan ya damk'ek'i kika shiga hannunsa,
wallahi sai an tausaya miki sai buzunki,
baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " a tausaya mana dai,
Halan zata kuma yin magana Khulud tace " dan Allah Aunty Halan ki kyale ta ki daina wahalar da kanki a banza,
Halan tace " wallahi kuwa, ku tashi kuyi wanka dan yau game za'ayi,
cikin rashin fahimta suka kalle had'i da cewa " game kuma?
"Opss sorry ban sanar daku ba,
duk ranar Friday around 4:00pm na yamma lacture akeyi ta addinin musulunci (wa'azi) ,,
kamar dai yadda kuka gani jiya anyi,
haka duk Saturday & Sunday (weekend),
around 4:00pm na yamma game akeyi,
kamar su basketball, football, handball & basket ball,
ya danganta da ra'ayin mutum,
Club d'in da yake so nan zai shiga sai yaje wajen shugabar club d'in ta bashi team & group ta kuma sanya sunansa,
baki Sanah ta tab'e kana tace " kuma dole kowanne student sai yayi koda bai ra'ayin yin hakan?
Kallanta Halan tayi cike da mamaki dan tunda take bata tab'a ji ko ganin wanda yace baida ra'ayin yin game ba sai Sanah,
a ranta tace " wannan wace irin yarinya ce mai shegen iyayi da kwainane?
Ta tambayi kanta, taci gaba da gama a cikin ran nata,
wannan yarinya da baud'add'en hali take,
mijinta ya shiga uku yaga ta kansa,
kamar ba yarinya k'arama ba, kwata-kwata bata yin wani abu na yara,
sai na manya kamar rainon tsuhuwa kowacce takai 100yrs a duniya,
cikin murna Khulud tace " kai amma naji mugun dad'i wallahi,
nayi farin ciki, ko ba komai mutum ya motsa jikinsa,
Sanah ta kuma tab'e baki,
tace " ni dai bazanyi ba gaskiya,
Halan tace " aiko dole kiyi dan doka ce mai k'arfi yin game a makarantar nan,
Khulud tace " ni dai ko ba doka bace ina son yi,
kuma tsarin ya burge ni sosai,
Halan tasa su sukayi wanka suka shirya,
jikin Khulud sai rawa yake saboda murna da d'oki
yayinda oganniya keta kumbure-kumbure ita a dole an takura mata,
dan in banda Khulud da dole babu abinda zai kaita wajen wani game,
kansewar basu da club & team yasa basu da kayan game,
sai yau idan sun zab'a shugabar team d'in zata basu kayan,
haka suka fita suka nufi babban filin da aka tanada dan yin wasannin,
Khulud nata murna da farin ciki,
Oga Sanah kam an sha murr an had'e rai murtuk.
Filin wasan ne ya k'ara burge Khulud sosai,
fuskarta cike da murmushi ta kalli Halan tace " wooow masha Allah,
amma gurin yayi bala'in kyau,
an shirya wajen sosai, ga kayan game d'in ma masu kyau,
Halan tayi murmushi tana shafa kanta tace " ai sai ma kin fara wasan,
zaki ji wani nishad'i na shigar ki tako ina,
Halan ta kalli Sanah dake ta ciccin magani,
tayi murmushi had'i da cewa " Oganniya wanne wasan zaki yi?
Had'a idan da sukayi da Khulud ne yasa ta sakin murmushin dole,
tace " anyone ni bani da choice,
kowanne ma yi zanyi,
Khulud tace " wasa d'aya zamuyi?
Sanah ta kalle ta cike da mamaki tace " ke da a tunanin ki daban-danan zamuyi?
"Ko kina tunanin wasa zai raba mu ne?
"Ai team & club d'aya zamu yi,
Khulud tayi murmushi, dama tsokace tasa ta tambayar Sanah,
dan ko cewa akayi dole sai an raba musu team sai dai su hak'ura da wasan,
amma matuk'ar suna raye babu abinda zai iya raba ta da Sanarta,
koya shiga tsakanin su koma meye shi,
Khulud tayi maganar cikin ranta,
Halan ta kalle su tace " to kunga dai nau'ikan wasan sai ku zab'i wanda yayi muku,
Sanah ta kalli Khulud tace " zab'ar mana Ronaldo tayi maganar cikin tsokana,
Khulud tace " baki da ra'ayinki ne Ozil?
Murmushi Sanah tayi tace " ni fa nace kowanne ma yi zanyi,
tunda matsa min akayi dole badan rai na yaso ba,
Khulud tace " to ni dai a tunani na Ronaldo & Ozil football suke yi ko?
Tayi maganar tana juya idanta,
Sanah ta tab'a baki had'i cewa " oho ni na sani,
Khulud zatayi magana Halan tayi saurin cewa " na gaji da jiran ku fa,
ku zab'a na kai ku, ni ma na wuce nawa team d'in,
Sanah tace " Aunty Halan ke wanne wasan kike yi?
"Football, ta bata amsa a tak'aice,
Khulud tace " to Aunty Hakan wanda kike yi muma shi zamuyi,
Halan tace " no ba wai abinda wani yake yi lalle shi zaku yi ba,
abinda ran su ke so shi zaku yi,
Ku dai na bin san zuciya ko ra'ayin wani, ku zama masu ra'ayin kan ku a koda yaushe kun ji ko?
Duka suka amsa da "tom, Hakan ta kuma cewa " to yanzu ku fad'a min wanne kuke so?
Khulud tace " muma football d'in muke so,
tayi maganar cikin sanyin murya,
Halan ta d'an k'ura mata ido had'i da cewa kun tabbata?
Kai suka d'aga mata alamar eh,
b'angaren da akeyin football d'in ta kai su,
dayake itama tana d'aya daga cikin shuwagabannin team d'in,
babu wani b'ata lokaci aka yiwa su Khulud duk abinda ya dace,
aka basu team & game ware, suka fara wasan,
sosai Sanah taji dad'in wasan dan sai yanzu abin ya fara burgeta yana bata sha'awa,
ba'a kad'a bell ba sai 6:00pm na yamma,
kowacce students ta nufi hostel dan yin alwalar sallar Magrib,
dan makarantar ana koyar da yara addini da ibada sosai,
cikin farin ciki sosai Sanah take tsalle tana cewa Khulud da Halan,
"kai gaskiya tunda nazo makarantar ban tab'a tsintar kai na a farin ciki irin na yau ba,
wasan yayi masifar burge ni, naji dad'in wasan sosai,
tayi maganar tana dariya cike da annushuwa.
Ranar Monday tunda sassafe suka shirya suka nufi assembly,
dan tsoran kar Sir Moli ya tare su dan har yau bai tab'a tare su a late comers ba,
bayan an tashi daga class Sir Moli na office d'insa,
Sir Jeeb ya shigo, hannu Jeeb ya mik'ewa Moli suka gaisa,
bayan sun gama gaisawa ne Sir Jeeb yace " ka tambayi yarinyar nan abin da ke damunta kuwa?
Shaf Sir Moli yama manta da maganar kwata-kwata dayake shi ba mai damuwa da harkokin jama'a bane,
kai ya dafe yana cewa " oh! na shafa'a ne,
amma kayi hak'uri bari na tura a kira ta yanzu,
murmushi Sir Jeeb yayi kana yace " ok badamuwa dama mahaifinta ne ya kira ni shiyasa nima na tuna,
yayi maganar yana niyyar fita,
Moli yayi saurin cewa " yama sunanta?
"SIYAH ya bashi amsa,
"ok bari na aika a kira ta yanzu yayi maganar yana k'ok'arin fita,
Jeeb yace " no ka zauna bari zansa a kira maka ita,
"nagode, Moli yace.
Yana daga kwance akan sofa idanuwansa a rufe,
tayi sallama daga bakin k'ofar office d'in,
a dak'ile ya amsa, tare da bata izinin shigowa,
a hankali ta shigo ta durk'usa cikin nutsu ta gaidashi,
ciki-ciki ya amsa gaisuwar, murmushi tayi dan idan da sabo sun saba da halin sa,
har a lokacin idansa a rufe yake,
a k'alla takai wajen 5 minutes batare daya ko motsa ba balle yayi mata magana,
cikin sanyin murya tace " cewa akayi kana kira na,
tayi maganar kanta a k'asa,,
shi ko rasa ta inda zai fara tambayarta abinda ke damunta yayi,
shiyasa yayi shiru baice komai ba,
a hankali ya mik'e ya zauna, gami da zuba mata ido,
ganin yadda take sissine kanta cikin hijab yasa cewa " munafuka, a cikin ransa,
a hankali yace " ke!,
ta d'ago idanta karaf idansu suka sark'e cikin na juna,
tayi saurin kawar da idanta,
ya cigaba da magana " Vice Principal ne yace na kira na tambaye abinda yake damunki,
a hankali ta d'ago kai ta kuma kallansa,
ganin ita yake kallo yasata saurin duk'ar da kanta,
ganin tayi shiru bata ce komai ba yasa shi cewa " ke nake jira fa,
wasu zafafan siraran hawaye ne suka shiga zubo mata,
tasa hannu tana gogewa amma still k'ara zubo mata suke yi,
d'an guntun tsaki yayi kana yace " ke ni fa ba kuka na kira kiyi min ba,
idan kuka zakiyi tashi ki fitar min daga office yayi magana a d'an zafafe,
d'ago idanta tayi da suka gama rinewa ta zuba masa su,
tsaki ya kuma gami da mik'ewa yana shirin barin office d'in,
har ya kai bakin k'ofa yaji tace " zan fad'a maka damuwa ta,
saboda kai ne wanda yafi kowa cancanta daya san halin dake ciki,
a hannunka maganin cutar dake damun ruhi da zuciya ta yake,
amma da farko kayi min alk'awarin babu wanda zaka sanarwa,
tayi maganar cikin sanyin murya,
tsayawa yayi cak yana mamakin kalamanta,
cikin ransa yace " ni ne wanda maganin cutar ta ke hannunsa kamar ya?
"Ni ne wanda yafi kowa cancanta yasan halin data ciki akan wanne dalili?
" Me hakan yake nufi?
Yayi maganar cikin ransa.........
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
6⃣
Ido ya k'ura mata na tsayin lokaci kafin yace " ina jinki,
cikin rawar murya tace " ka zauna,
ba musu Sir Moli ya koma kan sofa ya zauna,
ya karkata gaba d'aya hankali da nutsuwarsa gare ta,
yana sauraren abinda zata ce masa,
hawayenta ta kuma gogewa tare da d'ago kanta a hankali ta zuba masa ido,
cikin muryar kuka tace " ba ni da matsalar komai a rayuwa ta,
tun daga kan ci da sha, da kuma gata,
duk ina dasu, bansan wata matsalar rayuwa ba sai a wannan shekarar da k'addara ta,
ta soma, mahaifana nayi min mugun so kasancewar mu uku suka haifa a duniya,
biyun duk maza ne ni kad'ai ce mace,
hakan ne yasa iyaye na suka d'auki so da k'auna had'i da duk wani burin duniya suka d'ora a kai na,
iyaye na ba talakawa bane, mahaifina yana da kud'i sosai,
shekarar sa takwas (8yrs) yana d'an majalisar tarayya,
kuma..........
Katseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu yace " ni duk ban tambaye ki wannan ba,
abinda na tambaye shine meye damuwar data haifar miki da hawan jini?
Yayi maganar cike da k'osawa,
murmushin gefen baki tayi gami da jefa idanta cikin nashi,
kai tsaye tace " SOYAYYA ita ce damuwa ta,
cikin mamaki ya kalle ta gami da cewa " what!?
"Wai kina nufin so shine silar gamuwa da cutarki?
Ya tambaye a k'agauce,
murmushi ta kuma yi kana tace " eh, so shine ya jefa ni cikin mawuyacin halin danake ciki,
ina san mutumin da bai ma san ina yi ba,
bai san a wane hali nake ba, bana kuma san sanar dashi ina san shi da kai na,
saboda bana san zubar da mutunci da k'ima, had'i da darajar da Allah yayi man a matsayi na,
na d'iya mace,
tasa hannu ta goge hawayen dake zubowa daga idanuwanta,
cike da tausayawa halin datake ciki yace " waye shi wanda kike san?
D'ago kai tayi tana kallan sa eyeball to eyeball,
ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da cewa " KAI NE WANDA NAKE SO,
wata mahaukaciyar zabura Moli yayi gami da mik'ewa a tsorace,
"what!?
Ya furta a zafafe, kana yaci gaba " ke ni abokin wasan ki ne?
"Ko kinga nayi miki kama da wanda ban san me nake yi ba?
D'an shiru yayi yana yarfa hannu kana yace " ni zaki rainawa hankali?
Yayi maganar yana nuna kansa,
fashewa da kuka Siyah tayi tana cewa " wallahi Allah da gaske nake maka,
KAI KAD'AI NE DAMUWA TA,
kai me wanda tunda na d'ora ido na a kansa na haukace a san sa,
tun daga kallo d'aya a kuma ranar farko,
kai ne farkon wanda na fara so a rayuwa ta,
a kanka ne na fara sanin meye so,
na kuma fara sanin zafi, k'unci da bala'in so,
akan ka nasha kwana na yini da yunwa,
sanka ya sha hana ni bacci da walwala,
sanka ne yaja na zama kamar mahaukaciya,
dan Allah ka taimake ni kayi min gurbi a zuciyarka.
"Ka taimake ni ka so ni, ko da kwatankwacin irin san da nake yi maka ne,
ka taimaki rayuwa ta, ka cece ni daga fad'awa halaka da musiba,
kai kad'ai zan so har k'arshen rayuwa ta,
kai kad'ai zan iya mallakawa zuciya ta,
kai ne kad'ai wanda nake iya gani nayi murmushi da dariya,
koda ina cikin matsanancin k'unci,
kai kad'ai nake gani naji ni cikin farin ciki da walwala,
ko da ina cikin damuwa da b'acin rai,
kai me hasske na, kai ne ji da gani na,
idan babu kai babu ni,
wallahi idan kace baka so na mutuwa zanyi,
dan nasan k'arshen numfashi da rayuwa ta sun zo,
ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai k'ona zuciya.
Ido kawai Moli ya zuba mata cike da tsantsar mamakinta,,
a hankali ta rarrafo ta rik'e k'afarsa,
gami daci gaba da magana cikin kuka,
" ka dubi girman Allah ka so ni,
ka tausayawa rayuwata, wallahi ina cikin mawuyacin hali,
halin da a koyaushe jiran mutuwa ta nake yi,
INA SANKA, dan Allah kai ma ka so ni,
ta k'arasa maganar cikin mahaukacin kuka had'i da kifa kanta akan k'afarsa,
please Sir Moli ka tausayin ka ceci rayuwa ta,
I really love you more & more much,
wallahi kai ne rayuwa ta, dan girman ka so ni,
ta k'ara fashewa da kuka tana rik'e k'afarsa.
Da sauri ya ja baya had'i da zuba mata ido kawai batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
ganin tana k'ara rarrafowa gare shi ne,
yasa shi daka mata gigitacciyar tsawa " ke!!! dalla tsaya anan,
amma ina bata ma san yayi ba,
dan ta gama makancewa idanta ya rufe ruf,
cigaba da nufarsa tayi, a hasale ya kuma ja baya tare da cewa karki kuskura kizo inda nake,
bama ta saurare shi ba harta k'arasa inda yake ta kuma mik'a hannu zata rik'o k'afarsa,,
cikin b'acin rai yayi ball da ita,
ta fad'a ta baya kanta ya bugi