Advertisements
Chapter 17 Reading RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RASHIN SANI Abokantaka Mai Gwada Ƙaddara by HAUWA A USMAN

Author :  HAUWA A USMAN Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 38

48K to 51K   out of 111.2K words

ba zai iya bani hak'uri ba,
a ransa yace " tab ,yana jinjina rashin kunya da tsoranta,
Khulud tace " to sai me dan bai baki hak'uri ba?


"Ko kuma sai akace kin ragu da wani abun,
sai ki bashi girmansa a matsayinsa na babba kuma namiji,
ki barshi da halinsa yaje, idan ma bazaki iya yafewa ba ,
sai ki barshi da Allah, dan sakayyar Ubangiji tafi ta kowa,
gwamma shi ya saka miki akan hak'urin da zai baki,
amma fitsara da rashin kunya babu inda zasu kai mutum ,
Khulud tayi maganar a hasale,
kana ta juya wajensa dake tsaye ya kafe Khulud da dara-daran idanuwansa,
tace " we are very sorry,
lokaci d'aya haji halayyar yarinyar da d'abi'unta sun burge shi,
tasan shine bai da gaskiya amma take yiwa sister ta fad'a,
take kuma bashi hak'uri akan laifin daba nata ba,
murmushi yayi wanda ya bayyanar da tsantsar kyawunsa,
jerarrun fararen hak'oransa suka bayyana,
ya kuma kafe ta shu'uma idanunsa masu kamar dana mashaya,
yace " bakomai ,kema kiyi hak'uri,
yayi maganar cikin zazzak'ar muryarsa mai icon ,
martanin murmushin shi ta mayar masa batare datace komai ba,
dogon tsaki Sanah taja mtswwwww gami da kauda kanta gefe,
kallanta yayi cike da jin haushinta,
danji yake kamar ya rufe ta duka ,
har zayyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya shiga motarsa,
Khulud bata kalli Sanah ba ta durk'usa ta kwashe kayan su dake zube a k'asa ,
kana ta tsaida mai napep sukayi gida.


A harabar wani katafaren gida yayi parking,
tsayawa fad'ar had'uwa ko girman gidan b'atawa kai lokaci ne,
dan irin gidajen turawa ne da muke gani a films ,
cikin isa da tak'ama yayi parking ,ya d'auki lokaci kafin ya fito yana taka k'asa kamar baya so,,
wata k'ofa naga ya shiga dan haka nayi saurin bin bayansa,
dan na kashe kwarkwatar ido na,,
"woww nace,saboda had'uwar parlor'n,
iya kud'i kam an kashe su wajen tsara parlor'n,
akan sofa naga ya zauna had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya,
masu aikin gidan suka fito sun kai biyar suka jiru daga gefensa kansu k'asa ,
suka ce " me za'a kawo Sir,
a tak'aice yace " babu,
batare da sun k'ara cewa komai ba suka bar wajen,
dan haka al'adarsa take baya san yawan hayaniya ,
ko gadarma,
wata hamshak'iyar mace naga tana sakkowa daga kan steps,
fuskarta d'auke da farin glass,
dagani medical ne,
murmushin fuskarta ta fad'ad'a ganinsa zaune a parlor'n,
yana ganinta ya mik'e tsaye yana murmushin jin dad'in ganin mahaifiyar tasa,
dan duk tarin bak'i ciki da damuwarsa muddin ya ganta sai ya ji duk sun gushe,,
ta bud'e masa hannayenta alamar yazo ,
aiko da sauri ya fad'a jikinta ya rungume,
kansa ta shafa kana tace " what's wrong with you my son?


Dan kallo d'aya tayi masa ta fuskanci ran d'an nata a b'ace yake,
murmushi yayi yana kwantar da kansa akan kafad'arta,
a shagwab'e yace " nothing so serious,
"nothing so serious amma shine naga ranka a b'ace?


" MIMMEE (sunan da suke kiran mahaifiyarsu dashi) yace yana k'ara shegewa jikinta,
dariya tayi ta shafa kansa,
tace " HANASH kaci abinci?


"No Mimmee ba yanzu ba ,bari nayi wanka tukunna,
d'ago shi tayi daga jikinta tana facing d'inshi tace " zaka fara ko?


Dan tasan Hanash baya san cin abinci,
a shagwab'e yace " Allah Mimmee wanka zanyi kawai,
" to yi sauri ina jiranka ta fad'a tana zama akan sofa,
yace " ok Mimmee gv me just 20 minutes،
ya wuce part d'insa da sauri.


Alhaji WASEEF DIKKO sanannan d'an kasuwa ne Nigeria,
harma da k'asashen k'etare,yana da matar aure d'aya tak AFROOZ,
wacce sukayi auren soyayya ,duk da ta kasance 'yar k'anwar mahaifiyar sa ce,
yana da yara uku mata biyu namiji d'aya,
HANASH shine babba ,sai da yayi wajen 13yrs sannan Mimmee ta k'ara haihuwar twins duk mata ZOHAL & WAJNAH,
mahaifin su wanda suke kira da PAPU,
mutum ne adili mai tausayi da j'in k'an talawa,
yana da kyauta sosai shiyasa mutane keyi masa lak'abi da DIKKO RUWAN SAMA NA KOWA,
saboda tak'aice sunan ake kiransa da DIKKO RUWA,
duk inda yaji ana buk'atar taimako da gudu yake yakaiwa,
mutum ne shi mai imani da tsananin tsoran Allah, kwata-kwata bashi k'aunar yaga wani acikin matsalar rayuwa,
burinshi kullum taimakon mutane koda duk abinda ya mallaka zai k'are bai damu ba,,
gashi da san zumunci,
mutum ne shi mai san raha da barkwanci,
mai kyautatawa na k'asa dashi,
zuciyarsa a tsarkake take matuk'a,
bai san wani abu fushi ko b'acin rai da fad'a ba,
duk iya shekarun da zaka d'iba dashi,
bazaka tab'a ganin yayi fushi ko yana fad'a ba,
kullum fuskarsa da ransa a sake suke cikin fara'a,
haka ma matarsa Hajiya AFROOZ,
mutunyar kirki ce,
kwata-kwata ba ruwan ta rayuwar duniya ko kyalele,
macece kamilar gaske nutsatstsiya ,mai hak'uri da tausayi,
Hanash yaro ne Classic, handsome and ajebota guy,
d'an gayu mai ji hutu,
mai tsananin biyayyar iyaye ,
da duk wanda ya girmeshi,
yana da matuk'ar hak'uri da kauda kai,
duk tarin dukiyar mahaifinsa hakan bai saukar masa da girman kai ba,
sai dai bai d'aukar raini daga wajen koma waye,
yaro ne mai tausayi da jin k'ai,
kwata-kwata bashi da girman kai ko raini da wulak'anci,
ko irin jijji da kan nan irin na yaran masu kud'i bashi dashi,
yana zaune da kowa lafiya,gashi da san wasa da dariya,
yana da d'an surutu amma ba sosai ba, kuma ba koyaushe ne yake san magana ba,
dan akwai randa zai iya kwana ya tashi batare da yayiwa kowa magana ba,
Allah yayi shi mutum mai sanyin rai da zuciya,
amma bai iya b'acin rai ba,
dan idan ranshi ya b'aci zai iya yin komai,
zai kuma iya taka kowa ,
kusan mutum mai hak'uri bai iya fushi ba,
babu abinda yafi tsana a rayuwar sa kamar raini da wulak'anci,
muddin kace zaka raina shi koka wulak'anta shi,
bazaku tab'a shiryawa dashi ba, balle ku zauna inuwa d'aya,
muddin kana san ganin b'acin ran Hanash to ka nemi kawo masa raini da wulak'anci,
anan zakaga fuskanci tantirancin rashin mutuncinsa,
baya san mutum bai tsiwa da rashin kunya, da mutum bai yawan hayaniya da surutu,
muddin kana san kaga b'acin ransa,
to ka nemi kawo masa rai ni, ko ka wulak'anshi,
anan zaka fuskanci tantirancin rashin mutuncinsa.


Hanash nutsatstse ne kamili, mai aji da izza gami da tsafta dan kallo d'aya zaka yi mishi kasan cikekken d'an gayu ne,
duk abinda zakaga yayi amfani dashi to mai tsada ne (designer),,,
yana da muguwa tsafta da gayu kamar mace,
dan idan kaga yadda yake gyara d'akin shi zaga sha mamaki,
gaban mirror d'insa kuwa jere yake da kayan shafa iri-iri da perfumes,,
yayi mugun tsanar mace marar kamun kai, da fitsara,
ko tsiwa, muddin yaga mace da irin wad'annan d'abi'un yanzu zaiji ya tsane ta,
sai dai duk sanyin ran Hanash yana da fushi
dan idan ransa ya b'aci idansa rufewa yake yi,
sai dai kaga yana ta faman huci kamar mesa,
Hanash bai iya k'iyayya ba ,dan idan ya tsani abu ya tsane shi kenan har abada,
ko ganinsa bai san yi, duk duniya babu abinda yafi so kamar iyayensa da k'annansa ,
akan su babu abinda bai iya yi,
mahaifiyar Waseef Papu wacce suke kira da JADDA,
tana nan a raye, macece mai tsananin iko da mulki,
duk Family tsoranta ake ji,
dan haka sai abinda tace akeyi a gaba d'aya Familyn,
muddin Jadda ta zartar da hukunci toya zartu babu makawa,
idan ko tace eh, duk duniya babu wanda ya isa yace a'a,
hakama idan tace a'a babu wanda ya isa yace eh,
sai Allah, babu wanda ya isa tayi magana kota zartar da hukunci yace ba haka ba,
kwata-kwata bata san rai ni, duk duniya babu abinda Mimmee da Jadda suka fi kamar suga Hanash yayi aure,
gashi shi ko buduwar bai da ita,
dan gani yake kamar har yanzu bai samu kalar macen zai so ko zai iya zama da ita ba.


Su Sanah na shiga gida ta wuce part d'in Halan ,
Khulud tabi bayanta, a zaune suka iske Halan tana shan fruits,
da sauri Maheen ta tare su tana cewa " oyoyo Aunty's,
ko kallanta Sanah batayi ba ta wuce bathroom,
Halan tabi bayanta da kallo, kana ta mayar da kallanta ga Khulud data d'auki Mash,
tace " waya tab'a ne?


Khulud tayi dariya kana ta bawa Halan labarin duk abinda ya faru,,,
Halan ta saka dariya harda hawaye,,
tana cikin dariyar Sanah ta fito,d'aure da towel ta kalli Maheen tace " jeki bedroom d'in mu ki d'auko man kaya da pant,
batare data kalli inda Halan take ba ta wuce kan dinning table danta lura da dariyar da Halan ke kannewa,
tuwon semota miyar agushi ta zuba ta fara ci,
Khulud tace " my Sanah laifin me nayi ne?


Batare data kalle ta ba tace " me kika gani?


Khulud tace " gani nayi ana cin abinci bako tayi,
Sanah tace " da tayi nake yi miki inzamu ci ?


Ta kuma yin maganar batare data kalli inda take ba,
Khulud tayi murmushi kana tace " a'a,
Sanah bata kuma cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta,
Halan tace " lalle yau ran 'yan maza ya b'aci,
tunda ba'a kyale Ulud bama waza'a kyale,
bari muyi ta kammu mu shafawa kammu ruwa,
Sanah tayi kwafa kana tace " kuma dai,
Maheen ta shigo da gudu ta mik'awa Sanah kayan,
ta amsa ta shige ciki, Halan da Khulud suka saka dariya,
Halan tace " badai mu muka kar zamon ba,
bata juyo ba tayi ciki fuuuuu,
Khulud ta kalli Halan tace " uhmm bari inbi kaya na in lallab'a ta,
bazan bari ki had'a mu ba,
tayi maganar tana bin bayan Sanah,
Halan tayi dariya tace " ki tsaya kici abincinki dan ya fiye miki,
Khulud bata kuma magana ba ta shige ciki wajen sanah,
tsaye ta iske ta agaban mirror tana zipping doguwar rigarta,
Khulud ta shiga ta zauna a bakin gado had'i da zubawa Sanah ido,
taga bata kwata-kwata Sanah bata bi ta kanta ba balle ta kalli inda take zaune,
'yar ajiyar zuciya Khulud ta sauke a hankali kana tace " me nayi miki my Sanah?


Batare data kalle ta ba tace " wani abun kika gani ne?


Khulud tayi rau-rau da ido zata fara kuka,
cikin rawar murya tace " idan wani abun nayi miki kiyi hak'uri please,
tayi maganar tana kama kunnanta,
alamar sorry, ganin Khulud nasan yin kuka yasa Sanah rolling sexy eye's d'inta,
had'i da zama kusa da ita tace " meye kuma na kukan?


Khulud tace " ba ke ba ce,
ta fad'a a shagwab'e,
Sanah tace " to yi hak'uri na daina ban k'arawa,
kema ai kece kika zab'i wani can bare a kaina,
sannan kuka yi man dariya ke da Aunty Halan ,
Khulud tayi murmushi tace " I'm sorry ban k'arawa,
Sanah tayi murmushi tana rik'o hannunta,
"ta so muje kici abinci nasan kina jin yunwa ,
tayi maganar tana rik'e da hannun Khulud zuwa dinning table,
Halan tayi gutun murmushi tace " hmmm kudai kuka sani,
ai _*RASHIN SANI*_ ne zai saka mutum shiga tsakanin ku,
basu kula ba ta,Sanah ta zubawa Khulud abincin tace " kici sai mu shiga mu gai da Juju da Mamu,
"to Khulud tace tana saka hannunta cikin abincin.


Cikin sauri yayi wankan ya shirya cikin 3 quarter da t shirt max,
ya shafa lotion olay kana ya feshe jikinsa da perfumes kala-kala,
da sauri ya fita dan ya tabbatar Mimmeensa nacan na jiransa,
kamar yadda yayi tsammani haka ya tarar da ita zaune akan sofa kamar yadda ya barta ,
tana zaman jiransa,
da sauri ya k'arasa yana cewa " I'm so sorry Mimmee na,
na barki kina jira na, mik'ewa tana murmushi ta rik'e hannunsa tayi dinning table dashi,
da kanta ta shiga bashi jollop couscous daya sha vegetables & dry fish,
dan kwata-kwata Hanash baya san cin abinci tun yana yaro sai an sha fama dashi kafin yaci abinci,
dakyar yaci rabin plate shima saida Mimmee ta matsa masa sannan,
a hankali ya mik'e cikin takunsa na isa da tak'ama,
dan duk da Hanash bashi girman kai ,
akwai shi da takun isa,tak'ama da izza,
idan yana tafiya sai ka rantse baya san taka k'asa,
haka ma duk da kasancewar shi mai sauk'in kai baya barin takwana,
akwai shi da bak'ar magana, dan idan ya yab'awa mutum bak'ar magana sai kaji kamar kabar garin,
sai dai mutum ne shi mai yawan murmushi da fara'a,
ko ransa ne ya b'aci wani lokacin sai dai yayi murmushi kawai,
Mimmee ta kalle shi tace " ina kuma zuwa?


Yace " zan shiga wajen Jadda mu gaisa daga nan kuma zanje ball,
"Ok Allah ya tsare, Mimmee tace tana murmushi.


Bayan Khulud ta gama cin abinci Sanah ta mik'e tace " muje ,
ba musu Khulud ta mik'e tabi bayanta,
har sun kai bakin k'ofa Sanah ta dawo ta d'auki Mash,
dayake ta faman kukan sai ya bita,
Khulud kuma ta rik'e hannun Maheen suka fita,
Halan ta bi su da dariya,
part d'in Juju suka fara shiga suka iske bata nan dan haka suka koma part d'in Mamu nan bata nan,
Sanah ta kalli Khulud tace " ina kuma suka je?


Khulud tace " kin manta gobe ne walima wata k'ila sunje siyayya ne,
Sanah ta zaro ido ,tace " wallahi na manta yi sauri kiyi wanka ,
muje sallon & henna d'in,
kinga har wajen 2:00pm na rana yanzu,
"ok kawai Khulud tace ,
batafi 20 minutes ba ta fito sanye da irin doguwar rigar jikin Sanah sak,
ta material purple color, takalmin su vine plate shoe mayafan su ma duk iri d'aya,
black color,
sukayi rolling da mayafan su, suka fita,
suna fita driver ya taso yana murmushi yace " 'yan matan hajiya ina zuwa?


Dariya sukayi masa, kana Sanah tace gyaran kai da k'unshi,
yana murmushi yace " inda na saba kai ku dai?


Khulud ta amsa masa da "eh,
a bakin wani babban wajen saloon da wankin k'afa & henna dake Lamid'o crescent yayi parking,
suka fito, cikin girmamawa suka ce " mun gode,
yayi murmushi yace " injira ku ne manyan gobe?


Cikin girmamawa Sanah tace " a'a Baba ka tafi kawai idan mun gama ma hau napep,
dayake duk halinta tana ganin mutuncin ma'aikatan gidan su,
babu wani abu na rashin mutumci ko fitsara daya tab'a shiga tsakanin su,
tana basu girma da mutuncinsu,
yace " manyan gobe, bazan barku ku hau napep ba,
meye amfani na, ku dai kira ni idan kun kammala,
Sanah tace " to mun gode Baba,
yayi murmushin jin dad'in, kana yaja motar ya tafi
su kuma suka shiga ciki,
dayake wajen babba ne sosai akwai ma'aikata da yawa yasa babu layi,
ba'a jima ba aka fara yi musu bibbiyu,
wata na gyara musu kai,wata kuma na wanke musu k'afa,
kafin daga baya aka fara yi musu k'unshi mai 2 colors red & black,
wajen 5:30pm na yamma aka kammala musu komai suka fito,
sunyi masifar yin kyau sai kace amare,
kamar mutum ya sace su ya gudu,
Khulud ta kalli Sanah tace " oh! kinga mun manta bamu sanarda da Baba driver bamu da phone ba,
Sanah taja d'an gutun tsaki " mtswwwww, yanzu irin haka ne ko matsala mutum ya shiga babu yadda zayyi ya sanar a gida,
Khulud tace " gaskiya nima dai rashin wayar nan ya fara damuna,
Sanah tace " ai dai ance da mun gama Secondary School za'a bamu ko?


"To ai yanzu mun gama,
Khulud tace " sai mu tsaya muga iya gudun ruwan su,
suna tafiya suna maganar,
Khulud tace " ga wajen nan shiru ,
yanzu ko a ina zamu samu napep?


Sanah ta kuma jan dogon tsaki " mtswwwwww, ga magrib ta kawo kai ba,
_*RASHIN SANI*_ ne yasa Khulud cewa " muyi trekking zuwa bakin titi,
Sanah ta kuma jan tsaki mtswwwwww,
cike da haushi tana turo baki,,
hand bag d'in dake hannun Khulud ta sub'uce mata ta fad'i k'asa,
d'an tsaki taja "mtswwwww kana ta sunkuya k'asa zata d'auka,
Sanah na cigaba da tafiya,
dan bata san Khulud ta duk'a d'aukar jaka ba tace " wa...............!
bata k'arasa ba sakamakon jin wani irin ruwa a fuskarta da bakinta,
a razane ta d'ago kanta da niyyar kallan wanda ya watsa mata ruwan amma sai me....................!!!




MOMYN ZARAH

_*RASHIN SANI.......*_




*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```


1⃣7⃣


Amma sai me?
wanda ya jefa ta cikin ruwan kwata d'azu,
taga irin motarsa sak, jikinta tabi da kallo taga gaba d'aya ya b'ata mata jikinta ruwan kwatar,
har fuskarta da bakinta,
Hanash na d'ago kansa yaga 'yan matan d'azu,
still ya kuma b'atawa da ruwan kwata,
a hankali ya furta " ya salam ,
had'i da runtse idansa,
Khulud ta d'ago tana cewa " jakar m........,
tsaida maganarta tayi ganin abinda ya faru,
Khulud ta kalli Sanah kana ta mayar da kallonta ga motar,
Sanah na tsaye takai iya wuya,
ta k'ufula sosai, Khulud tace " my San.....
dakatar da ita Sanah tayi ta hanyar d'aga mata hannu,
muryarta na cracking saboda tsananin b'acin rai tace " ai yanzu kinga ni ko?


" So sai ki barni dashi naga dame yake tak'ama,
ta fad'a idanta nakan motar,
Khulud ta sauke ajiyar zuciya had'i da zubawa motar ido,
ganin bashi da niyyar fitowa ne yasa Sanah takawa zuwa bakin motar,
Khulud tayi saurin rik'o ta ,ta fisge ,
cikin zafin rai ta fara dukan glass d'in motar da k'arfi,
a hankali ya bud'e idansa had'i da sauke su a kanta,
yayi mugun mamakin ganin yadda eye color d'inta suka canja ,
saboda tsabar masifa da ruwa bala'i,
bata tsoran koshi irin mugayen mutanan nan ne,
gaba d'aya idanta ya rufe saboda tsiwa,
murmushin takaici yayi kana yace " bari na bud'e naga mai zata iya yi,
cikin isa yayi k'asa da glass d'in,
ga mamakinsa yaga ta kalle ido cikin ido tace " fito,
tayi maganar cikin fad'a,
Khulud ta k'araso wajen da sauri tana cewa " wai meye haka ne My Sanah?


Bata kalle ta ba ,ta kuma cewa " fito,
"my Sanah meyasa baki da hak'uri da kau dai kai ne a rayuwa?


Cikin masifa ta kalli Khulud tace " ko?


Khulud batayi magana ba ta fara k'ok'arin rik'o hannun Sanah,
ta kuma fisgewa, tace " Allah ban tafiya sai na d'auki mataki,
murmushi ya kuma yi a karo na biyu,
kana cikin isa da tak'ama ya ziro k'afafunsa k'asa ya fito,
had'i da sark'e hannuwansa a k'irji ya jingina da jikin motar yana kallanta,
yana san yaga mai zai zata iya yi,
Khulud tace " dan Allah my Sanah kizo mu tafi gida,
Sanah tace " idan ban rama ba bazan huce ba,
d'azu ma haka yazo har inda nake ya b'ata man jiki ,
yanzu ma shine ya kuma biyo ni ya b'ata man jiki,
Khulud tace " ki rama me?


" Shifa Namiji ne Sanah,
ina ke ina fad'a da Namiji,
ko kina tunanin idan kinyi akwai ribar da zaki samu?


" Kuma da kike cewa yana bimmu,
baki tunanin hanya ke had'a mu?


" Hanya ai ta kowa da kowa ce,
shi dai ba sanin mu yayi ba ,balle muce ko yana bibiyar mu ne,
da d'azu da yanzu duk Allah ne ya had'u mu hanya d'aya dashi,
batare da sanin mu ko sanin shi ba,
please my Sanah ina baki shawarar duk mutumin da Allah ya had'aki dashi kiyi k'ok'arin zama da rabuwa dashi lafiya,
saboda babu wanda yasan gobe sai Allah,
Sanah tace " gobe akan wa kenan?


" Wai kina nufin wannan?


Tayi maganar tana nuna shi a wulak'ance,
kana ta cigaba " kin san Allah sai na rama na koya mishi hankali,
murmushi takaici yayi yace " wazaki koyawa hankalin?


Tace " kai! a fad'ace,
yace " ok Bismillah ina jira,
ya fad'a yana gyara tsaiwarshi,
batayi magana ba ta

17 / 38