Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
duniyarsa da tsinke،
a hankali ya zuro d'aya k'afar kana ya fito gaba d'ayan sa,
sanye yake cikin arnan Man material,
mai laushi, color blue black,
takalmi, agogo da hularsa black color,
cikin nutsuwa ya d'auki laptop & brief case d'insa,
ya fara takawa a hankali ya nufi class d'insu.
Sir Moli na gaf da shigà yà fara jiyo hirar su rose,
dan haka ya d'an tsaya kad'an,
Sanah na zaune a baya taji wasu Christians suna hira,
d'ayar mai suna Rose tace " ni fa ina mamakin Muslim,
d'ayar tace " mamakin me?
Rose tace " yadda suke bautawa wanda basu sani ba,
ba kuma su tab'a ganinsa ba,
d'ayar ta tab'e baki tace " nima abin nan yana bani mamaki fa,
yanzu da zaka tambaya su ina Allah su yake shiru zasuyi suyi tsuru-tsuru,
a zafafe Sanah ta mik'e ta nufi inda suke zaune,
tana zuwa bata jira wata-wata ba ta kifawa kowacce mari bibbiyu,
Sir Moli dake tsaye jikin window yayi saurin kallan Sanah cike da mamakin rashin tsoranta,
dan dukkannin su gidiga-gidiga ne,
masu k'irar k'atti babu wacce bazata iya sab'ar Sanah ta zagaye garin Kano kaf da ita ba,
Rose da d'ayar suka mik'e da sauri cike da mamaki,
suna kallan Sanah Rose dafe da kuncinta tace " kika mare mu?
Sanah ta zaro idanta kamar gaske tace " ni yaushe na mare ku?
Sir Moli ya gyara tsaiwarsa yana kallan ikon Allah,
Rose tace " yanzu fa kika mare mu,
Sanah tace " idan har da gaske kuke yi na mare ku,
ku nuna min marin,
Rose ta nuna kuncinta tace " gashi,
Sanah ta kalli kuncin had'i da sanya hannunta ta rik'e fuskokinsu tana duddubawa kamar gaske,
tace " ni fa banga komai ba,
gaba d'aya ajin akayi tsit kowa ya maida hankalinsa kansu,
Rose tace " kamar ya baki ga komai ba?
Sanah tace " eh banga marin ba,
amma ke tunda kina ganinsa kina iya nuna min shi na ganshi,
d'ayar tace " ke karki raina mana wàyo,
Sanah ta sanya hannunta ta rik'e hab'arta had'i yin sautin da bakinta,
tana kallansu cike da rainin hankali,
" in banda rainin hankali dama ana ganin mari ne?
D'ayar ta fad'a,
Sanah tayi murmushi kana tace " au dama ba'a ganin mari?
Rose tace " tayaya za'a ga mari?
Sanah tace " to yaya kika san na mare ki?
Rose tace " naji shi ne,
Sanah tace " yauwa anzo wajen,
kin tabbata ba'a ganin mari,
amma ana jinsa,
dana mareki baki ganshi ba amma kinji shi har cikin kwakwalwarki da zuciyarki,
to kamar yadda bakiga marin nan ba,
amma kika yarda akwai shi, zuciyarki da kwakwalwarki suka amince suka kuma gaskata shi gaskiya ne,
haka Allah Ubangijin mu mai komai da kowa yake,
shi dayake shine Ubangijin gaskiya shiyasa ba'a ganinsa,
amma zuciya, rai ,ruhi , kwakwalwa, duk suka yarda suka kuma amince akwai shi,
zati da k'udurar Ubangijinmu tafi k'arfin ido ya ganshi,
yafi k'arfin zuciya ta siffatanshi,
yafi k'arfin rai ya misaltashi,
kana ta kalli jakarta tace " yanzu Rose idan kika shigo ajin nan kika ga ba kowa sai wannan jakar kad'ai,
kin san akwai mai ita,
akwai kuma wanda yake mallakinsa ce,
sannan kin tabbatar akwai wanda ya k'era ta ko?
Rose tace " haka ne, duk wani da kika gani akwai meshi,
Sanah tace " good, to kamar haka be akan duniya,
Rose ko kwano kika gani ajiye kin san akwai meshi,
balle kuma duniya da abinta ke cikinta,
ke kanki kin san akwai mai ita,
saboda babu abinda yake halittar kansa
komai kika gani a duniya yinsa akayi,
idan kika kalli shuke-shuke da ruwa, jini da mutum kad'ai ya isa ya tabbatar miki akwai Ubangijin gaskiya,
so please ku bar irin wad'annan maganganun a cikin al'umma saboda hakan yana iya haifar da fitina,
ayi ta kashe rayukan da basu ji ba,
basu gani ba,
ba su Rose kad'ai ba, duk wanda ke wajen sai da jikinsa da zuciyarsa tayi sanyi,
Sanah ta koma inda take zaune ta zauna kamar babu abinda ya faru,
Rose ta kalli Sanah tace " I'm sorry,
then thank you so much,
Sir Moli dake tsaye yayi guntun murmushi,
yau karo na farko da Sanah tayi abu a rayuwarsa yaji ta burge shi,
sosai yayi mugun mamakin basira da hikimarta,
a hankali ya taka ya shiga class d'in,
sai da ya gama koyar da su as usual kana ya fita.
Hanash sai da ya tabbatar Sanah ta tafi makaranta kana ya shirya cikin Man lace,
ash color, takalmi, agogonsa gucci,
hularsa kalar aikin jikin kayan yayi masifar kyau,
idan ka ganshi sai ka rantse bai san Hausa ba,
dama abinka da bafulatani usul back and front,
duk inda kake tunanin had'uwa ko kyan namiji Hanash ya kai koma in ce ya wuce,
yana da bala'in kyau kamar aljani,
dan da yawa wad'anda sukayi karatu tare basu yarda d'an Nigeria bane,
waya ya ciro daga aljihunsa ya sanar da ita yazo yana set room,
itama tayi kwalliya cikin riga da skirt na atamfa tayi simple make up,
bakinta d'auke da sallama ta shiga,
har k'asa ta durk'usa ta gaida shi,
ya amsa fuska cike da fara'a,
a hankali ta zauna akan sofa had'i da satar kallanshi,
karaf suka had'a ido,
tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa,
yayi murmushi cikin nutsuwa yace " ya dai ake satar kallo na,
a fito kai tsaye a kalle ni mana,
kiga angon naki sosai, kar sai daga baya kice nahi,
tayi murmushi,
yace " ina our Sanah,
tana ji yace " our Sanah, tayi saurin d'ago kanta ta kalle shi cikin jin dad'i,
tace " tana makarata,
kansa ya d'an dafe yace " oh! zuwa fa nayi na bada hak'uri,
ance jiya nayi laifi,
dariya tayi had'i da saka hannu ta rufe face d'inta,
yace " ya kukayi da Abbu yau?
Tace " ai my Sanah bata dawo ba,
dole sai idan ta dawo zamu ji komai,
sannan koma meye kayi magana da ita kawai, duk abinda tace is okey to me,
murmushi yayi yana danne abinda ke ransa,
sosai sukayi hira kana da zai tafi ya mik'o mata laida,
k'in amsa tayi,
dan dama sun saba haka duk lokacin da zai mata kyauta sai ya sha fama kafin ta amsa,
yace " to zaki fara ko?
"Wannan ai ba naki bane ke kad'ai,
ke da our Sanah ne,
jin yace harda Sanah ta amsa had'i dayi masa godiya,
har bakin mota ta raka shi ya fita,
tana shiga gida ta aje kyautar tak'i b'ud'ewa tana jiran Sanah ta dawo.
Ko da Abbu yajewa da Didi da maganar masu neman auren Khulud zasu zo,
cewa yayi shi ina ruwansa ai shine ubanta yayi duk abinda ya dace kawai,
hakan da Didi yayiwa Abbu yasa Abbu yaji dad'i sosai,
Didi yana komawa gida ya sanar da Juju,
jikinta a sanyaye tace " to ita Sanah fa?
Didi yace " itama Allah zai kawo mata,
mu dai addu'a ce tamu,
Abbu ya sanar da Mamu ta fad'awa su Sanah cewa su zo ranar Friday,
kana Abbu ya Sanar da Ziyad da Zafran,
ko da Ziyad ya sanar da Halan itama cewa tàyi Sanah fa,
Sanah yau da wuri ta dawo daga school,
wanka tayi kana tayi sallah taci abinci,
sai data gama komai kana Khulud ta d'auko ledar da Hanash ya kawo musu,
tace " My Sanah Hanash yazo ganinki baki nan,
amma yabar sak'o,
Sanah tayi dariya kana tace " ayya dan Allah ki bashi hak'uri,
Khulud tace " ai badamuwa ya fahimta yace zai dawo da weekend sai ku gaisa,
Sanah ta amshi ledar ta bud'e wasu arnan perfumes suka gani masu shegen kyau da k'amshi,
da gani kasan masu shegiyar tsada ne,
Sanah tace " wow! amma gaskiya naji dad'in kyautar nan,
please kice masa nagode sosai,
Khulud tace " in ce masa kodai ki kira shi kiyi masa godiya da kanki,
Sanah zatayi magana Mamu ta shigo,
a bakin bed ta zauna kana ta kallesu tace " to ku sanar da su suzo ranar juma'a,
Khulud tasa hannu ta rufe fuskarta,
Mamu tace " kwaji dashi dai 'yan nema,
ta fita tana dariya,
Sanah tace " kira shi a fad'a masa,
ba musu Khulud tayi dialing number sa,
kashewa yayi ya kira ta, tayi picking sai da ta gaida shi kana tace " magana zakuyi da my Sanah,
yayi murmushin k'arfin hali yace " ok bata,
Sanah ta amsa tana murmushi ta gaida shi,
ya amsa ba yabo babu fallasa,
godiyar perfumes ta fara yi masa,
kana ta sanar dashi sak'on Abbu,
yayi d'an murmushi yace " nagode,
a tak'aice, itama murmushin tayi kana ta mik'awa Khulud wayar,
suka shiga shan love,
suna gama wayar Hanash ya nufi part d'insu Mimmee,
a parlor ya tararda su,
har k'asa ya durk'usa ya gaida su,
suka amsa cikin so da k'auna,
zayyi magana Papu yace " ya kukayi a BUK?
Kansa ya shafa kana yace " Papu ban samu ganin shi ba,
Papu yace " kamar ya baka ganshi ba?
Hanash yace " naje har sau biyu amma ban samu ganinshi ba,
kana yace " wai Papu dole ne sai su Zohal sun cigaba da karatu?
" Mai zai hana ayi musu aure kawai,
Allah yawancin malaman jami'a 'yan iska ne,
basu da wani aiki sai lalata yaran mutane,
a d'an hasale Papu yace " saboda baka san suyi karatun shiyasa kak'i maida hankali?
A hankali Hanash yace " kayi hak'uri Papu ban san magana ta zata b'ata maka rai ba,
kayi hak'uri in sha Allah ranar Monday zan koma,
zan kuma yi iya bakin k'ok'ari na,
zuciyar Papu tayi sanyi jin kalaman Hanash,
cikin sanyi Papu yace " yauwa nagode Allah yayi maka albarka,
Ubangiji ya baka zuri'a ta gari,
Allah ya albarkaci rayuwarka,
Hanash da Mimmee suka amsa da Amin,
Papu ya kalle shi yace " naga kamar da magana a bakinka ko?
Hanash ya d'an shafa kansa kana yace " eh!,
Papu ya karkata hankalinsa gaba d'aya gare shi,
yace " ina jinka,
baki Hanash ya d'an turo kana yace " to ka daina kallo na Papu,
yayi maganar cike da shagwab'a,
Papu yayi dariya yace " nama rufe ido na,
Hanash yace " iyayen Khulud ne suka ce ku je ranar juma'a,
Papu da Mimmee suka bud'e baki cikin matsananciyar murna,
Papu yace " kai masha Allah, rabon danaji labari mai dad'i irin wannan har na manta,
Hanash yasa hannu ya rufe fuskarsa wai shi kunya,
Papu yace " kayi min text d'in details na gidan,
Hanash yace " tom,
Mimmee ta mik'e zata fita,
Papu yace " ina zaki?
Tace " wajen Jadda mana a sanar mata abin farin ciki,
abinda ta dad'e tana jira,
Zohal da Wajnah dake lab'e suka fito da gudu suka yi waje suna dariya,
sukace " Mimmee mu zamuyi mata albishirin,
koda suka sanar da ita bata yarda ba,
sai da tazo har part d'in Mimmee,
suka fad'a mata da kansu kana ta yarda,
dan murna har rawa ta taka.
Kamar yadda aka tsara ranar Friday iyayen Hanash suka je,
Yayyan Papu biyu da abokinsa ne suka je,
an karb'e su hannu bibbiyu, cikin mutunci da girmamawa,
suka gabatar da kansu, ashema sun san juna sosai,
Papu abokin Didi da Abbu ne tare sukayi primary da secondary,
set d'in su d'aya, sosai sukayi farin cikin sake ganin juna rayuwarsu,
dan sun nemi juna har sun gaji da neman junansu har sun hak'ura,
dayake an san juna Abbu yace karsu damu zai sanar dasu duk halin da ake ciki,
a cikin kwana biyu Abbu yayi bincike sosai akan Hanash dama gidansu,
babu wani abun k'i a tattare dasu,
sai ma yabo da suka samu daga wajen mutane,
sosai Abbu da Didi sukayi farin cikin jin yabon da al'umma keyiwa Wassef,
duk da dama sun san halayyarsa,
Abbu ne ya kira a waya cewar sun gama duk abinda ya kamata,
mutanen da suka zo da farko su suka k'ara dawowa,
duk abinda ya kamata sunyi,
sun kawo goro da alawa da kud'in neman aure,
goro da alawa kad'ai Abbu ya amsa shima dakyar,
yace " sadaki kawai zasu kawo shima sai ranar d'aurin aure,
aka sanya bikin wata biyu kad'ai,
shima dan Mamu ta dage ne,
saboda tanasan shirya 'yarta sosai,
amma da wata d'aya aka saka.
Tafiya kawai take a matuk'ar gajiye lik'is,
dan dakyar take iya d'aga k'afarta,
ga yauma Aarib yana busy bazai samu damar zuwa d'aukarta ba,
fita tayi daga get tana neman mai adai-daita,
daga gefenta taji haushin kare,
a hankali ta juya taga wasu tik'a-tik'an karnuka guda biyu,
suna lasar harshe,
da k'arfi gabanta ya fad'i, jikinta ya d'auki kerrrma,
saurin tafiyarta ta k'ara,
taga karnukan sun mik'e daga kwancen da suke, suna kallanta,
juyawa tayi taga lungun babu kowa,
dan haka tsoro ya k'ara kama ta,
ta fara gudu-gudu sauri-sauri,
ganin yadda jikinta ke tsuma yasa karnukan zaton ko bata da gaskiya,
san haka suma suka fara binta a hankali suna haushi,
jin haushinsu yayi masifar gigita ta,
dan haka ta tattare doguwar rigar material dake jikinta,
ta zage iya k'arfinta ta soma gudu,
aiko karnukan suka ce dawa Allah ya had'a mu,
suka bi bayanta a guje,
ganin sun biyota yasata yin cilli da mayafinta datayi rolling dashi,
gaba d'aya gashinta kanta ya zubo bayanta ya barbaje,
ya hargitse,
tayi kuma yin cilli da takalmi da jakarta,
tana gudun tana kuka,
tana kuma juyawa baya tana kallan yadda karnukan ke binta,
direct baya Sanah ta koma ta nufi cikin makarantar,
karnukan suka bi ta,
a hankali ya fito daga office d'insa,
ya nufi motarsa cikin takunsa na izza,
cikin nutsuwa ya bud'e d'ayan b'angaren ya ajiye laptop da brief case d'insa,
kana ya zagayo zai shiga motar,
hangota yayi tayiyo kansa gadan-gadan,
American dogs na biye da ita,
bako d'an kwalli bare takalmi da mayafi,
sai iska dake faman kad'awa tana yin baya da rigar jikinta,
had'i da d'aukar gashin kanta yayi sama ya barbazu,
ganin direct shi ta nufo yasa shi zaro ido,
had'i da girgiza mata kansa alamar no,
saboda yadda compound d'in ke cike da students,
ganin bata fasa nufo shi ba,
yasa shi ce mata " a'a fa,
amma kafin yayi aune ta fad'a kansa,
daga shi har ita sukayi baya,
suka fad'i k'asa,
shiya fad'i a k'asa ita kuma ta kansa, gashinta ya bazu ya rufe musu fuska,
fuskarta kan tashi,
bakinta kan nashi, hancinta na gogar nashi,
hannayenta duka akan k'irjinsa,
ita kuma gaba d'ayanta akan jikinsa................
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣4⃣
Gaba d'aya Malamai da students dake wajen,
suka tsaya cak had'i da sanya hannu suka rufe bakin su,
cikin tsantsar mamaki,
suna tunanin wanne irin hukunci Sir Aryan zai yiwa Sanah,
gashin Sanah ya rufe musu fuskarsu ta yadda babu mai iya ganin fuskokin su,
eyeball to eyeball suke kallan junansu,
dukkan su sun shagala suna kallan juna,
daga shi har ita babu wanda yayi motsi balle suyi k'ok'arin tashi,
karnukan kuwa yadda kasan anyi musu magana suka juya suka koma,
bakin Sanah nakan na Sir Moli,
sun k'urawa juna ido basu ko blinking,
Leem dake tsaye ya zuba musu ido fuskarsa d'auke da murmushi,
d'an gyaran murya Leem yayi had'i da cewa " a compound dai ake,
da saurin Sanah ta mik'ewa tsaye had'i da duk'ar da kanta k'asa cike da kunya,
shima mik'ewa yayi had'i da tsuke fuskarta,
ya had'e rai tamau, yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,
a hankali ta d'ago kanta cikin rawar murya tace " kayi hak'uri,
ta fad'a tana gyara gashin kanta,
daya zubo mata, tasa hannu ta mayar dashi baya,
harara ya watsa mata batare dayace mata komai ba ya shiga motar,
gaba d'aya mutanen dake wajen tsananin mamaki ne ya hana su yin koda kwakkwaran motsi ne,
Leem ya kalli Sanah yace " shiga mu tafi,
kai ta girgiza masa alamar a'a,
Sir Moli ya kalleta cikin takaici yaga yadda jama'a ke kallanta,
wasu ma sun shagala da kallanta,
sun k'ura mata ido kamar mayu,
gata jikinta babu ko d'an kwali babbe mayafi,
jajayen idansa, dasuka gama komawa pure red saboda tsabar b'acin rai,
ya d'ago ya kalle ta dasu kawai,
ta gane abinda yake nufi,
jikinta na kerrrma ta bud'e bayan motar zata shiga,
cikin masifa yace " driver ki ne ni?
Da sauri ta rufe k'ofar baya ta bud'e ta gaba ta shiga,
Leem zayyi magana Sir Moli ya figi motar cikin b'acin rai,
batare daya kalli inda take ba yace " ina kika zubar da kayanki?
Cikin rawar murya tace " waccen lungun ta fad'a tana nuna masa lungun da hannunta,
bai kuma magana ba, yayi hanyar data nuna masa,
parking yayi a inda yaga jakarta da mayafinta,
bayyi mata magana ba ta fita da sauri,
jikinta na rawa ta d'auki mayafinta ta yafa,
kana ta d'auki takalmi da jakarta,
ta bud'e motar ta shiga,
kanta a k'asa,
dan tayi mugun tsorata dashi,
musamman yadda kalar idansa ta canja kala in few sec,
a k'ofar gidan su yayi parking batare dayace mata komai ba,
ya kauda kansa gefe, jikinta a sanyaye ta bud'e motar ta fita,
zatayi magana ya bugi motar yayi gaba,
bayan motar tabi kallo kana ta shiga gida.
Tana shiga cikin harabar gidan,
ta iske motar Hanash, daga bayanta taji Khulud na kiranta,
da sauri ta juya bayanta,
Khulud ta nufo ta cikin fara'a,
tsayawa tayi cak tana bin jikin Sanah da kallo,
kana tace " my Sanah lafiya?
Ta fad'a tana bin jikin Sanah da kallo,
itama jikinta tabi da kallo kana tayi dariya tace " karnuka ne suka kusa murmushe ni,
Khulud ta zaro ido tace " wayyo a ina?
Sanah ta bata labarin duk abinda ya faru,
Khulud tayi dariya tace " baki tashi sanin Sir Moli sai kinga bala'i,
wallahi in nine shi banko kallanki,
Sanah ta tab'a bakinta tace " shi ya sani,
Khulud ta rik'o hannun Sanah tace " Hanash tun d'azu yake jiranki kan maganar shirye-shiryen biki,
Sanah tace " ayya to muje,
tabi bayanta,
tare suka shiga set room d'in,
hannunsu sark'e cikin na juna,
Sanah tayi dariya tace " ango kasha k'amshi,
ayi man afuwa na bar ango da kansa yana zaman jira,
yayi murmushi yana bin kayan jikinta da kallo,
" iskancin yarinyar nan fa ya wuce tunanin,
wato har a k'asa take kwanciya wannan shegen d'an iskan ya hau kanta,
a fili kuma yace " ah ai girmanki ne,
ba damuwa, kuma naga yanzu kika dawo, kamar ma a gajiye kike ko?
Tayi murmushi tana zama akan sofa,
tace " badamuwa our groom manta da gajiya,
ya kuma yin murmushi mai sauti wanda har sai da dimple d'insa suka lutsa,
yace " badamuwa our Sanah kije ki huta,
tunda yau Friday kinga gobe weekend ne muna da free time sosai,
sai in dawo muyi magana ko?
Khulud na tsaye gafe ta k'ura masa ido,
tana jin sansa da k'aunarsa yana ratsa duk wata gab'a da jijiya dake jikinta,
tana jin zata iya bada rayuwarta akansa,
ta rasa meyasa yake yi mata bala'in kama da Seif Ali Khan,
ido kawai zai fi Saif Ali Khan,
da yake Hanash akwai manyan ido dara-dara,
shi kuma Saif abu d'aya zaifi Hanash d'inta,
shine fari, da yake Hanash ba fari bane sosai,
skin color d'insa chocolate color ne,
mai shegen kyau, wanda wasu mutanen ma suke ganin kamar sunfi fararen fata kyau,
fakaitar idan Sanah yayi, ya kashewa Khulud ido d'aya dan ya lura da irin kallan datake yi masa,
da sauri ta kawar da kanta gefe tana murmushi,
Sanah tace " to in baku waje ne?
Dan ta lura da abinda ke faruwa a tsakaninsu,
Khulud tayi saurin cewa " me akayi my Sanah?
Sanah ta kalle ta tana dariya tace " oho maki ban sani ba, karki raina man wayo,
Hanash yace " a'a our Sanah karki tafi,
Sanah tace " to ai gani nayi an kira ni an zaunar dani ana shan love,
ba'a ko jin kunya ta balle ayi man kara da kawaici,
" hmmm kaji shigiya wai ita 'yar duniya,
kowa zata nunawa ita ta Allah ce,
fasik'a kawai shegiya,
ya fad'a cikin ransa,
a fili kuma yace " ayi mana afuwa kin