Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
bin Sanah da kallo,
idan Khulud ne ya sanka akan Hanash,
tayi saurin maida kanta k'asa saboda yadda taji gabanta yayi mugun fad'uwa,,
tunowa da alwashin da Sanah tayi ne,
yasata d'ago kanta cikin tashin hankali,
ta kalli inda Sanah ta nufa,
gani tayi ta nufi shi gadan-gadan,
a kid'ime Khulud ta bud'e motar ta fito da gudu,
amma ina kafin ta k'arasa har Sanah ta cimmasa,
Hanash ya mik'awa tsohuwar kud'i ya juyo da niyyar komawa cikin mota yaji saukar gigitattatun maruka tassssssss a jere har guda biyu...................
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣8⃣
Tsayawa cak Khulud tayi jin aikin gama ya gama,
babu abinda jikin Khulud keyi sai kerrrma da tsananin tsuma,
tsoro da fargaba sun cika mata cikinta fal,
dan bata tab'a tsammanin fitsara da rashin kunyar Sanah yakai ta iya d'aga hannu ta mari zafgagen namiji kamar Hanash ba,
Hanash wanda ya gama gigicewa,
saboda kwata-kwata bazato ba tsammani yaji saukar mari,
shu'uman idanuwansa da suka gama rinewa zuwa jajaye ya zuba mata,
jin zuciyar shi yake kamar zata fashe,
k'irjin ko yadda kasan an zazzaga fetur an kunna wuta,
haka yake ji, dan tunda Hanash yake a duniya ba'a tab'a koda mangarinsa ba,
balle har ya kai ga ammare shi,
sai yau, da k'aramar yarinyar da yasan ya kusa haihuwarta a haihuwar kaji, dan ya tabbatar ya bata kyakyawar 15yrs,
tunowa yayi da yadda k'annansa keyi masa biyayya kamar zasuyi masa sujjada,
ya tuno shi dai a iya sani da wayonsa Mimmee ko Papu babu wanda ya tab'a koda yi mishi kallan banza,
saboda kasancewar shi mai biyayya da sanyin rai,
had'i da sauk'in kai gashi da girmama na gaba dashi.
Ido kawai ya zuba mata batare daya ce komai mata komai ko yayi yunk'urin yi mata wani abu ba,
Sanah ta murgud'a baki tana kallanshi ido cikin ido,
tace " an fad'a maka ana cin bashin na batare da an biya ba?
Kallanta kawai yake, bai iya koda furta kalma d'aya ba,
ta cigaba " ko an fad'a maka banza marar galihu ka mara?
"To idan ma kana tunaninka haka,
ka gaggauta canjawa dan Sanah ta wuce sani da tunninka,
haka kawai k'aton banza dakai ka kamani ka mara batare da nayi maka komai ba,
sannan kayi tunanin kaci bulus,
a hankali Hanash ya d'aga kansa ya kalli yadda jama'ar dake wajen ke kallan su cike da tsantsar mamaki,
suna nuna su had'i dayin magana k'asa-k'asa,
nazarin su Hanash yayi sosai ya fahimci da alama basu gane wanda aka mara ba,
kawai dai sunji k'arar marin ne,
dan haka ya gyara tsayyuwarshi had'i dayin murmushi yace " am I your mate?
Yayi maganar while idanshi cikin nata,
murmushi itama tayi idanta nakan shi tace " oho maka ban sani ba,
a hankali ya kuma satar jama'ar dake wajen yaga still hankalin su na kansu,
yayi guntun murmushi mugunta,
yace " dan ubanki daga yau kya kuma,
gashi nan kin cajawa kanki a banza na mare ki,
gobe ma ki koma,
shegiya 'yar iska , k'aramar yarinya dake sai iskanci da san maza,
wallahi daga yau duk ranar da kika koma tare ni a hanya ko kika nuna kin sanni sai nayi miki abinda yafi na yanzu,
dan zagewa zanyi nayi miki mugun duka,
shegiya 'yar iska fitsararriya, ko dole ne,
haba kin fiye nacin jaraba, ance ba'a sanki amma kin nace man duk inda nayi sai kin bini,
wallahi daga yau kika kuma bibiyata sai nayi miki abinda harki mutu baki mantawa dani,
yayi maganar azafafe cikin d'aga murya dan jama'ar dake wajen su ji sosai,
cike da tsantsar mamaki Sanah ta bud'e baki,
zatayi magana ya d'auke ta da gigitaccen mari yace " shut up idiot kawai,
idan kika kuma bud'e baki zakiyi magana sai na nad'a miki na jaki,
ya fad'a yana nunata da yatsa,
kumatunta ta dafe danjin fuskarta tayi kamar an maka mata rodi,
saboda da iya k'arfinsa ya mare ta,
abinka dame ciwo a zuciyarsa,
Sanah dafe da kuncinta ta d'ago kai a hankali ta kalli jama'ar wajen,
taga gaba d'aya hankalinsu na kanta,
sai nuna ta suke suna magana a hankali,
karaf taji wani yace " halan irin banzayen 'yan matan nan ne marasa kamun kai,
da aji,
shiyasa ya bugeta,
kinga yanzu kinjawa kanki marika har uku a banza,
d'aya kuma yace " ai ni ya burge ni wallahi,
d'ayan yace " nima dai yayi man dai-dai,
daga ganinta fitsararriyar yarinya ce, mara kunya,
shegiya in banda ballagar mace wake bin namiji yana masa naci,
" gata masha Allah, a fuskarta da jikinta kamar ita tayi kanta,
amma a zuciya babu kyau,
wani mai saida lemo da ayaba ya fad'a idanshi kan Sanah,
" waya gaya maka mata masu kyau abin so ne yanzu?
"Ai yanzu babu abinda yakai mace mai kyau had'ari,
dan koda kayi dace ka same ta da kyan hali mazan waje basu tab'a barinka ka zauna da ita lafiya,
haka zakayi ta fad'a maza da mata,
baga mazan ba baga matan ba,
haka zakayi ta fama, kuma yawancin su kud'i kawai suke so,
babu abinda ke gabansu sai duniya,
amma sai kaga wasu mazan saboda tsabar rashin hankali da tunani,
burin su kawai su auri mace mai kyau ko bata da hali,
har kaji suna cewa Allah ya basu farar mace ko mayya ce,
basu san hali, taribiyya da addinin mace sune farkon abin dubawa ba,
amma burin wasu mazan a samu farar mace kyakkyawa ta sawa a gaban mota,
ana fashion ana burga da bagu,
ana bud'awa ana nunuwa abokanai,
duk kyan mace idan ka aure ta babu hali kayi a banza, saboda sai an wayi gari kaji ka tsaneta ka tsani kanka da ma duniyar gaba d'ayanta,
idan ko ba kayi sa'a ba haka zakayi ta sharing d'inta da wasu mazan banza,
ana kwaso 'yayan wasu na zina ana kawo maka gidanka da sunan naka ne,
batare daka sani ba,
ko da fita mace 'yar uwanta tazo ta danne maka mata har cikin gidanka,
mai sai da rake ya fad'a,
d'ayan yace " ai ba duka suka taru suka zama d'aya ba,
dan a cikin kyawawan akwai na Allah,
kamar yadda kace haka akan kyawawan mata,
haka ma munanan suma da nasu,
dan sai kaga wata macen kamar a yanka b'oye wuk'a amma tana yin fiye da abinda kyawawan keyi,
baka san wasu matan 'yan fashi bane?
Wasu 'yan cult, (matsafa) wasu sun aure kane dan su kashe ka,
wasu dan abun hannunka, suka aure ka su raba ka da kowa da komai naka,
sannan su zama maka alak'ak'ai,
daga k'arshe idan sun gama cin moriyarka su aunaka lahira su fad'awa wani,
tsautsayin kuma,
wasu kuma setup ne ma,
abokinka ko mak'iyinka zayyi maka da mace,
kai dai muyi addu'a kawai, Allah ya taimake mu ya rufa mana asiri,
Ubangiji ya iya mana maganin abinda bazamu iya ba,
duk abinda zaifi k'arfin mu koya wahalar damu Allah yayi mana maganinsa,
duk suka amsa da "amin.
A hankali Khulud ta runtse ido tana hawayen bak'in ciki da takaici,
ita bak'in cikinta d'aya yadda aka muzanta mata Sanarta a bainar jama'a,
Hanash hard'e hannuwansa yayi yana murmushi, while idanshi na kanta,
deep down kuma shi kad'ai yasan me yake ji,
a cikin ransa da zuciyarsa,
idanshi cikin nata ya d'age mata gira d'aya,
yana nuna mata jama'ar dake wajen yana murmushin gefen baki,
gigitaccen kuka Sanah ta saki na takaici,
ta nufi Hanash gadan-gadan,
cikin zafin nama Khulud tayi saurin shiga tsakiyar su Sanah nagaf da isa ga Hanash,
batare da Khulud ta kula ba, k'irjinta dana Hanash suka had'u ,
k'ijinta da nashi suna gogar na juna,
lips d'inta da kumatunta suma suka had'u da nashi,
tsaye kawai Hanash yayi idanshi na kanta,
ya kafe ta da shu'uman lulu eyes d'inshi,
bugun zuciyar shi ya k'aru yana bugawa da tsananin sauri,
gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa yana kerrrma,
still Khulud ta na k'ok'arin rik'e Sanan ta bayansa ta zura duka hannayenta,
ta rumgume shi suka saka shi a tsakiyarsu,
Khulud ta rik'e duka hannayen Sanah da nata hannun,
har lokacin k'irjinta na kan nashi,
booms d'inta na gogar k'irjinshi,
hab'arta na kan kafad'arshi,kumatunta na gogar nashi,
hawayenta na sauka akan kafad'arshi,
Hanash na nan tsaye yayi sororo ya kasa yin koda gwaggwaran motsi,
babu abinda yake ji sai mugun shock a duk ilahirin jikinsa,
gaba d'aya jikinsa tsuma yake yi.
A hankali Khulud ta d'aga hannunta sama ta zagaye Hanash,
ta rik'e Sanah gam, cikin nutsuwa ta juyo ta fuskance shi while hawaye na cigaba da gangaro mata,
cikin muryar kuka tace " bani da baki ko kalmar da zan iya baka hak'uri dasu,
but dan girman Allah kayi hak'uri,
duk mumunin kwarai an sanshi da hak'uri, yafiya, afuwa ga mutane,
please if it's possible forgive us,
tayi maganar tana duk'ar da kanta k'asa,
hawaye na cigaba da zubowa daga idanta,
while tana rik'e gam da Sanah,
Hanash bai san sanda his cutie smile d'inshi ya kwace masa ba,
martanin murmushin ta mayar mishi,
tana goge hawayenta, kana ta juya ta nufi mota da Sanah,
Baba driver da duk wainar da ake toyawa bai sani ba ya ja motar,
zuwa gida dan sun amso d'inkin,
sosai Khulud ke kuka har suka k'arasa gida,
suna isa haraba gidan Khulud ta d'auki kayan tayi part d'in Halan batare data ko kalli insa Sanah take ba,
baki Sanah ta zumb'ura kana tabi bayan Khulud,
a porlor Khulud ta zube tana cigaba da kukanta,
zama Sanah tayi kusa da Khulud had'i da dafa ta,
Khulud tayi saurin ture hannun Sanah daga jikinta,
cike da tsantsar mamaki Sanah tace " wai meye haka?
" Kike ta kuka kamar wacce aka daka,
batare da Khulud tace mata komai ba,
ta cigaba da kukanta,
Sanah ta zumb'uri baki kana tace " menayi miki kuma?
Khulud tayi banza da ita,
Sanah ta kai hannunta tana k'ok'arin dafa Khulud,
Khulud tayi saurin gocewa ,
a tsorace Sanah ta zaro ido tana cewa " wannan duk na meye?
Shiru Sanah tayi kana tace " ko dai akan shi ne?
Tayi maganar batare data kalli inda Khulud take ba,
shiru Khulud bata kulata ba,
Sanah ta ciji leb'enta had'i da runtse idonta tace " I hate him,
I really hate him madly,
tunda muke dake baki tab'a yin fushi da ni ba,
sai akan shi, sai a kuma dalilinsa,
wallahi na tsane shi ba kuma zan tab'a san shi ba har abada,
tunda a dalilin shi ne kika fara yin fishi dani a iya tsawon rayuwarmu,
Sanah tayi maganar kanta gefe,
jin Khulud tayi shiru bata da niyyar yin magana yasata yin tsaki " mtswwwww ta mik'e zata bar wajen,
Khulud tayi saurin rik'o hannunta tana goge hawayenta tace " ba akan shi bane,
akan gaskiya ne,
ni ina ma ruwa na dashi,da har zanyi fushi dake akan shi,
ni da bamma san shi ba, ban kuma san daga inda ya fito ba,
Sanah ta koma ta zauna tana cewa " to idan ba akan shi bane akan meye kike fishi dani?
Khulud tace " ke yanzu abinda kikayi kina ganin kinyi dai-dai kin kyauta?
Sanah ta zumb'uri baki tace " me kuma nayi?
" Auke yanzu kina ganin bakiyi komai ba kenan?
Sanah batace komai ba, ta cigaba da zumb'urar baki abinta,
" Ai kowa ya b'ata ya sani kowa kuma ya gyara ya sani,,
wallahi ban tab'a zaton zaki iya saka hannu ki mari zabgagen namiji saurayi ba,
idan gaya man akayi bada ido na,
na gani ba , sai na rantse k'arya ne, ba gaskiya bs,
in banda yana da hankali, hak'uri da tunani da yasanin akamata me kike tsammanin zai iya faruwa?
Sanah tace " oho shiya sani, ai dama nace maki sai na rama,
dan ban tab'a yafewa in bari ina ji ina gani wani k'aton banza ya mari ni a wofi,
Khulud tace " ok yanzu baki ganin kinyi abinda ba dai-dai ba kenan?
Sanah ta kuma zumb'uro baki kana tace " naji kiyi hak'uri ban k'arawa,
Khulud tace " idan kina san na hak'ura kiyi man alk'awarin duk abinda yayi maki baki kuma ramawa,
Sanah tayi dariya kana tace " ina zan kuma ganin shi?
" Ai kuma shikenan target d'in mu ya k'are,
Khulud tace " k'addara ,
Sanah ta juyo a hankali tana kallanta kana tace " k'addara, k'addara kamar yaya?
Khulud tace " k'addara mace ce marar tabbas,
da akoyaushe tana iya canjawa,
da kin san zaku tab'a had'uwa ke da shi a rayuwa?
Sanah tace " a'a ,ba kuma na fatan sake had'uwa dashi har abada,
Khulud tace " k'addarar data had'amu dashi a baya ita zata sake had'amu dashi a gaba,
so ni dai dan Allah kiyi man alk'awarin baki kuma rama duk abinda yayi maki,
Sanah tayi dariya tace " ai akwai sauran marin daya kuma yi man ban rama ba,
ki bari idan na rama sai nayi miki alk'awarin,
Khulud ta zaro ido tana mik'ewa tsaye tace " ke yanzu sai ki kuma iya sake marin shi?
Cikin dariya Sanah tace " da gudu ma,
tayi maganar tana ja da baya,
Khulud ta d'auki pillow ta jefa mata tana binta da gudu suka shiga zageye parlor'n,
jin hayaniyar su tasa Halan fitowa da sauri tace " kun shir......
ganin su tsaye suna wasan jefe-jefen pillow yasata tsayawa sororo tana kallansu kana tace " au baku shirya ba, shine kuka tsaya kuna wasa?
"Lalle ta kai muku karo,
duniyar tayi muku dad'i,
sukayi dariya su duka cike da tsantsar farin ciki,
Halan tace " to oya maza aje a shirya,
kunga lokaci na niyyar k'urewa,
suka amsa da "to kana sukayi cikin gidan da gudu Halan tabi bayan su da kallo tana dariya cike so,
basu d'auki lokaci ba suka shirya cikin riga da siket na atamfa,
d'inkin yayi bala'in yi masu kyau,
ya amshi jikinsu, irin d'inkunan da zaka gani ana talla a Facebook & Instagram,
dayake sunyi masifar iya make up kamar me,
suka tsarawa kansu fitacciyar kwalliya irin wanda kuke ganin celebrities nayi,
dan sun kai 2yrs a makarantar koyar make up & food training centre,
shiyasa sukayi masifar iya make up,
da girkin abinci, dan babu irin girkin da basu iya ba,
kafin su fito an gama komai na shirya wajen,
har k'awayen su sun fara hallara.
Hanash yakai wajen 10 minutes tsaye a inda suka barshi,
still jikinsa bai bar kyarma, sai dakyar ya jan k'afarsa ya shiga mota,
a cikin motar ma yakai a k'alla 6 minutes kafin ya iya jan motar,
fasa zuwa inda yayi niyya yayi,
dole ya karya kan motarsa ya nufi gida,
yanayin parking a harabar gidan ya fito,
ko tsayawa zare key da rufe motar bayyi ba,
direct part d'insa ya nufa tun a parlor ya cire kayan jikinsa yayi naked,
ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower,
dan haka Hanash yake tun yana yaro k'arami muddin ransa ya b'aci ko yana cikin damuwa,
naked yake yi ya shaga bathroom ya sakarwa kansa ruwa na tsayin lokaci,
sai da Hanash ya d'auki lokaci a bathroom kana ya fito d'aure da towel,
kan sofa ya zube yana tunani biyu,
na farko tsabar rashin kunyar Sanah da fitsararta,
yayinda lokaci d'aya yaji tsanarta da k'iyayyarta ta dira a zuciyarsa,
dan dama shi haka yake yayi bala'in tsanar mace mai fitsara da rashin kunya a rayuwarsa,
ji yayi kwata-kwata yayi masifar tsanarta ko san sake ganin fuskarta ba yayi a rayuwarsa,
daga b'angare d'aya kuma shi kansa bai san tunanin dayake yi ba,
bai kuma san meke shirin faruwa dashi ba,
shi dai still yana jin shock a jikinsa,
haka duk lokacin daya tuno ta yana jin yarrrrr a jikinsa,
yana jin duk tsikar jikinsa ta mik'e,
gaba d'aya ya rasa samun sukunin ransa,
ya rasa nutswarsa, babu abinda ke k'ara burge shi da yarinyar sai sanyin halinta,
gata da hankali, hak'uri, nutsuwa da sanin ya kamata,,
da gani tana da ingantacciyar tarbiyya,
ba ita ke yin laifin ba, amma ita ke kuka tana bada hak'uri,
da gani tana da sanyin hali kamar shi,
dama ya dad'e yana addu'ar Allah ya bashi mace mai sanyin hali da zuciya irin shi,
mai tausayi da sanin ya kamata,
mai cikekkiyar nutsuwa da tarbiyya,
yasan muddin ya same ta matsayin matar aure yayi sa'ar mace,
yasan ya shiga sahun wad'anda Manzan Allah (S.A.W) yace sun samu farin cikin duniya,
domin Annabi S.A.W. yace mace ta gari itace jin dad'in duniya,
duk namijin dayayi sa'ar mallakar mace ta gari,
ya gama samun fari ciki da kwanciya hankali,
murmushi Hanash yayi batare daya sani ba,
had'i da cusa hannunsa a cikin kwantacciyar sumar kansa,
while yana cigaba da murmushi.
K'annan Hanash Zohal da Wajnah,
suka shirya tsaf domin zuwa wajen walimar k'awayen su da suka gama Secondary School tare,
tun a makaranta suka gayyace su,
fitowa sukayi suka iske Mimmee a parlor zaune tana shan fruits salad,
ta kalle su cike da kulawa tace " har kun shirya?
Suna zauna kusa da ita suka amsa da " yes our Mimmee,
tayi murmushi kana tace " me zaku kai musu gift?
Zohal tace " perfumes & bangles,
Mimmee tace " eh yayi, to kuyi maza ku tafi karku makara,
kuma ku tabbatar kun dawo da wuri karkuyi dare,
suka amsa mata da " in sha Allah Mimmee,
light kisses sukayi mata a kumatu kana suka fita,
basu dad'e da fita ba suka dawo,
cikin shagwab'a Wajnah tace " Mimmee duka drivers d'in basu nan,
wai Jadda ta aiki d'aya kasuwa,
ta kuma aiki d'ayan Pharmacy,
d'ayan kuma ke kika aike shi gidan k'awarki,
ta fad'a tana turo baki,
Mimmee ta dafe goshinta alamar mantuwa tace " ops na manta,
duk suka shiga diddira k'afa had'i da kukan shagwab'a,
"a'a yau me akayiwa 'yan lelan Mimmee?
Papu dake shigowa yayi maganar yana dariya,
da gudu suka fad'a jikinsa,
kana cikin shagwab'a suka shiga fad'a masa abinda ke faruwa,
" naga kamar Yayanku yana nan,
kuje ya kai ku mana, in yaso sai ya tsaya ayi walimar dashi ya dawo da ku,
Papu yayi maganar yana zama akan sofa,
Zohal tace " Papu kasan fa ba kai mu zayyi ba,
" kun tab'a ganin na sashi abu yak'i yi?
Cewar Papu yana kallansu,
suka ce "a'a ,
yace " tom kuje kuce Papu yace ya kai ku,
ya kuma zauna ayi walimar dashi sannan ya maida ku,
cikin murna suka fita da gudu suka nufi part d'in Hanash,
yana kwance akan sofa abun duniya ya dame shi,
yaji knocking dakyar ya iya cewa " waye?
Wajnah tace " mune Yaya, yace " ya akayi?
Yayi maganar cikin sanyinsa idanuwanshi a rufe,
Zohal tace " Papu ne yace " wai ka kaimu walimar k'awayen mu,
ka kuma tsaya ayi walimar da kai sannan ka maido mu gida,
" sai da yayi d'an shiru kana yace " ku je ina zuwa,
basu kuma yin magana ba, suka juya,
suka koma part d'in su,
Papu ya kalle su yace " ya akayi?
Sukayi dariya kana suka ce " shiryawa zayyi ya fito,
Mimmee tace " sai kuyi koyi wajensa,
dakyar Hanash ya mik'e ya sanya d'anyan boyel sky blue,
ya sanya takalimi da hula da agogo duk black colors,
ya feshe jikinsa da arnan perfumes,
kana ya fito cikin takunsa na izza,
a parlor ya iske Mimmee da Papu da su Wajnah,
har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nashi,
suka amsa cikin kulawa, kana yacewa su Zohal su fito,
suka mik'e suka bi bayanshi,
bayan su Sanah sun shirya sun fito kamar wasu taurari sai shek'i suke,
duk inda suka juta walk'iya sukeyi,
Khulud ta kalli Sanah tace " bafa kiyi man alk'awarin ba,
Sanah tace " alk'awarin me?
Khulud tace " na bazaki kuma rama duk abinda yayi maki ba,
Sanah tayi rolling lulu eyes d'inta,
tace " wai ke meye na damuwa dashi ne?
Khulud tace " badashi na damu ba,
dake da mutunci da kuma k'imarki na damu,
ba wai dashi na damuwa