Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
kallanta cike da mamaki,
ji tayi gabanta yayi muguwar fad'uwa,
kwafa yayi had'i da girgiza kai ya zubga mata uwar harara,
ya juya yayi tafiyarsa, batare dayace mata komai ba.
JSS 1A suka shiga, halan tayi sallama,
Class master suka iske a cikin class d'in yana kiran suna,
cikin girmamawa suka gaida shi,
ya amsa cikin fara'a kana halan tace " Sir new comers ne akace na kawo su,
"Ok amma sai dai a aje d'aya anan akai d'aya 1B,
ai baima k'arasa ba, Khulud ta soma tab'a baki zatayi kuka,
yayi saurin cewa " meye na kuka?
Halan tace " please Sir karka raba su,
zayyi magana Sanah da Khulud sukayi saurin durk'usawa a gabansa had'i da langwab'ar da kai suka ce " please Sir don't separate us,
we bag you in the of almighty God,
jikinsa yayi sanyi tausayinsu ya kama shi,
ya d'ago su a hankali yana murmushi yace " ok,
cikin farin ciki suka ce thank you Sir,
kansu ya shafa yace " then promise me you will read harder,
" We hope so Sir, cewar Sanah
"not hope so, promise!
murmushi sukayi had'i da cewa " we promises you Sir,
yayi dariya sannan ya nuna musu sit, suka zauna.
Bayan an tashi daga class direct masallaci suka wuce,
tare da sauran students dan haka al'adar makarantar take,
sai an ja su sallar adhur jam'i kafin su shiga hostel area,
sai bayan sun fito daga masjid suka yi dinning hall,
abincin rana aka basu, sannan kowa ya wuce hostel,,
Halan tasa sukayi wanka suka shirya cikin islamiyya uniform tun kafin time d'in islamiyyar yayi,
gudun kar suyi late Sir Moli ya samu damar cin uban Sanah,
dan ta tabbatarwa kanta yaji abubuwan datace d'azu a kansa.
Suna kan hanyarsu ta komawa hostel daga islamiyya wata senior ta kira su,
"ku kuzo nan, tayi maganar tana watsa musu kallan banza,
d'an tsayawa sukayi had'i da juya bayansu dan sunga alamar bada su take ba,
ganin sunk'i zuwa ne ya hasala senior d'in ta danna musu ashar,
had'i da daka musu tsawa " ku banzaye bazaku zo bane ni nazo,
Sanah zatayi magana, Khulud tayi saurin rik'e ta had'i da girgiza mata kai alamar a'a,
had'iye yawo Sanah tayi saboda takaici batare datace komai ba,
Khulud taja hannunta zuwa inda senior d'in ke tsaye,
kasancewar basu san al'adar boarding school ba yasa suka tsaya a tsaye had'i da zuba mata ido,
" baku da hankali ne dazaku tsaya min k'erere akai na,
dalla ku rage tsayin ku,
tayi maganar cikin fad'a tana yi musu wulak'antaccen kallo,
ganin still suna tsaye yasata mik'ewa a hasale tace " bazaku durk'usan bane?
Da sauri Khulud ta kama hannun Sanah suka durk'usa a gabanta,
bokitin k'arfe ta jefa musu tace " kuje tanker ku ciko min shi,
cikin rashin fahimtar abinda take nufi Khulud tace " me zamu yi miki?
" Ni keke tambaya abinda zakuyi man?
Tayi maganar tana nuna kanta,
kai tsaye Khulud tace " eh mana,
ai bamu gane abinda kike nufi b............
tasssssssss senior d'in ta d'auke Khulud da wani gigitaccen mari,
har sai da ta hantsila, a gigice Khulud ta fashe da mahaukacin kuka tasa duka hannayenta ta dafe kuncinta,,
tab abinka da mafad'acin mutum da bak'ar zuciya, Sanah tayi fad'an banza ma balle mai dalili,
ita da kamar jiran fad'a take, dan ita kad'ai ma yi take, sai dai ka ganta tana jijjige-jijgen jiki,
tana magana ita kad'ai, aiko zuciya tazowa Sanah har wuya,
cikin b'acin rai da zafin zuciya,
Sanah ta wawuri bokitin k'arfen ta shiga kwad'awa senior d'in a jikinta da kanta a haukace,
idanta gaba d'aya sun gama rufewa ruf saboda bak'ar zuciyar ta,
take jini ya fara zubowa Senior d'in kanta ya fashe, saboda azaba bata san sanda ta shiga kwarara ihuuuuun a taimake ta za'a kashe ta ba,
kafin kacame dandanzon students sun cika wajen mak'il,
duk Junior d'in da suka zo suka ga ERA ake yiwa duka sai tsoro da farin cikin ya kamasu,
tsoron da suke yi na sun san sum shiga uku ne,
saboda kwata-kwata Era bata da imani ko tausayi, gata bak'ar muguwa azzaluma, duk wanda ya sake ya shiga track d'inta ya shiga uku dan bata yafiya balle wani abu hak'uri,
mutum d'aya ne zayyi mata laifi amma saita had'a gaba d'aya students ta zane saboda zalunci,
wannan dalilin ne yasa suke tsoro da murna.
Dakyar SS3 suka taru suka kwace Era daga hannun Sanah,
suka rik'e Sanah dan sai kici-kici take tana san kwacewa, babu yadda ba'ayi Sanah ta hak'ura ba amma tak'i hak'ura,
sai dai Khulud ta mik'e daga inda take durk'ushe taje ta rik'e, had'i da ta rungume ta,
sannan Sanah ta hak'ura ta bari, itama ta rungume ta duk suka saka kuka,
wasu daga cikin Juniors suka fara magana k'asa-k'asa,
"yau dai Allah ya kawo mana k'arshen wannan shegiyar mara imani,
wata tace " wallahi kedai bari kawai,
ai yau saboda tsabar farin cikin sai na zuba ruwa a k'asa na nasha,
d'ayar tace " aini yau wanka zanyi da k'asa,
wata daga gefe cikin sanyin murya tace " wallahi ni tausayin yaran nake ji kar ayi musu rufdugu,
"Hhhhhhh tab ke yanzu kinga alamar waccen zata daku?
Tayi maganar cikin dariya taci gaba " baki hango ruwan bala'i da masifa a kwayar idanta ba?
"Ke da ganin wannan kinsan zatayi taurin kai da bak'ar zuciya,
jifa yadda bakinta yake kumfa, idanta yayi jajir, saboda tsabar fitina da ruwan fad'a,
gaskiya wannan bazata tab'a dakuwa ba,
sai dai duk abinda za'ayi ayi, kuma tana da taurin zuciya, kuma da ganin kwayar idanta bata da tsoro ko kunya,
kuma zatayi tsiwa,
d'ayar tace " kamar ma new comers ne ko?
"Eh, jiya bana baki labarin wad'anda sukayiwa Sir Moli taurin kai ba?
"Eh, kar dai kice man su ne, tayi maganar tana zaro ido,
murmushi d'ayar tayi kana tace " wallahi sune,
k'ara kallan su tayi tana girgiza kai,
ganin abin ya girmama yasa head girl zuwa staff room ta sanarwa da Dispeeling Master,
yana daga kishingid'en idansa a rufe, ya bud'e baki dakyar yace " je ki kira su,
yayi maganar a tak'aice, dan shi mutum ne wanda kwata-kwata baya san yawan magana,
ko hayaniya dan zai iya irga yawan maganar dayake yi a wata d'aya,
gashi miskilin gaske, Service yazo(bautar k'asa),
ainahin Dispeeling Master ne ya tafi Malaysia k'arin karatu shiyasa aka bashi rik'on kwarya,
saboda yadda students d'in ke bala'in jin tsoransa,
kai bama iyakacin students ba har Malamai da Principal shakkarsa suke ji,
saboda yana da bak'ar zuciya, kuma bai shiga harkar kowa,
saboda kyansa da gwarjininsa yasa 'yan mata da yawa haukacewa da mutuwa a haukan sansa,
amma shi ko kallo basu isheshi ba,
dan ko gaisuwarsu dakyar yake amsawa , wani lokacin ko amsawar bayyi.
Jikin Head Girls na rawa ta koma ta kira su Sanah, Khulud da Era,
sauran student najin ance Sir Moli na kiransu jikinsu ya d'auki tsuma,
saboda tsananin tsoransa da suke ji,
take tausayin su Sanah ya gauraye zukatan students d'in,
Halan na Hostel wata Junior ta ruga ta sanar da ita abinda ke faruwa,
dan Halan bata san abinda ke wakana ba,
sosai hankalinta yayi masifar tashi tsoro da fargaba suka dirar mata,
dan ta tabbatar yau sai buzun su Sanah,
tana san zuwa taga halin da suke ciki amma ba dama dan tasan waye Sir Moli,
dan yana fasa dukan su ma ya jibge ta, saboda baya san tsurku,
dole ta hak'ura ta zauna tana jiran dawowar su.
Office d'insa suka shiga suka tsugunna a gaban table d'insa,
sun kai a k'alla 10 minutes batare daya motsa koya bud'e idansa ba balle su saka ran zayyi musu magana,
jin sheshshekar kukan Era yasa shi bud'e idansa a hankali,
had'i dabin inda yake jiyo sautin kukan da kallo,
wata irin muguwar zamura Sir Moli yayi had'i da mik'ewa zambur,
saboda tsoratar dayayi naganin ciwo da uban jinin dake zuba daga kan Era,
cikin zaro ya kalli Era had'i da cewa wannan had'arin mota tayi?
Shi tsakaninsa da Allah yayi tambayar,
saboda yawan jinin dake zuba,
cikin kuka Era tace " ba had'ari nayi ba Sir,
wannan ce ta dake ni, tayi maganar tana nuna masa Sanah,
bin inda Era ta nuna masa yayi da kallo,
ganin baiga kowa ba yasa shi yin waige-waige had'i da cewa " ni banga kowa ba,
wa kike nufi?
Cikin kuka ta kuma nuna Sanah tace " wannan Sir,
kallan ta yayi had'i da nuna ta yace " wai wa?
A hankali Era ta mik'e taje har inda Sanah take ta dafa ta,
had'i da cewa " Sir wannan yarinyar,
cike da tsoro gami da mamaki Moli ya zaro ido yana kallan Sanah,
had'i nufarta gadan-gadan yana yi mata wani irin kallo.
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣
_A PAGE 2 NAYI MISTAKE WAJEN SUNAYEN SANAH & KHULUD_
_RAWAN SHINE BABAN KHULUD_
_HAMRAZ KUMA BABAN SANAH_
*KHULUD RAWAN*
*SANAH HAMRAZ*
Yana isa wajen Sanah yasa hannu ya d'ago ta yana kallan Era yace " kina nufin wannan yarinyar itace ta ji miki wannan ciwon?
Kai tsaye Era tace " eh Sir,
shiru Sir Moli yayi had'i da k'urawa Sanah ido,
ganin yadda idonta yayi jajir ne ya tabbatar masa da zafin zuciyar da take da ita,
shiru yayi yana nazarinta na wani lokaci,
yaga kwata-kwata babu alamar nadama ko danasani a tattare da ita,
sai ma cika take tana matsewa had'i da jefawa Era kallan banza tana cije leb'e da alama idan ta samu dama k'ara jibgar Eran zatayi,
a cikin kwayar idanta ya hango bak'ar zuciya da zafin ran dake gareta,
yadda take motsa bakinta tana magana ciki-ciki ne yasa shi fahimtar tsagwaron masifa da tsiwar dake cinta,,,,
mayar da kallansa yayi ga Khulud yaga yadda jikinta ke rawa,
tsoro ya bayyana k'arara a fuskarta,
kamar zaka ce mata k'et ta ruga,
ya kalli idanta yaga alamar tausayawa Era a tattare da ita,
kallo d'aya yayi mata ya fahimci kwata-kwata bata san fitina da hayani balle fad'a,
sab'anin Sanah dako a jikinta yadda kasan ma bata yi komai ba.
Kallansa ya maida ga Era ya ganta jibgegiya, k'atuwa mai k'irar k'atti,
dan ko namiji Era tana iya yi masa mugun duka balle mace,
ya kalli yadda jini ke zuba daga jikinta, ya kuma kallan Sanah,
wacce a haihuwar kaji Era ta haife ta,
ya dubi girma da tazarar dake tsakanin Era da Sanah, dan bambamcin a bayyane yake,
yadda kasan rak'umi da zakara,
haka bambamcin Sanah da Era yake,
shi abinda ma yafi d'aure mai kai shine,
yadda Sanah ta iya tunkarar Era kai tsaye batare da wani tsoro ko fargabar komai ba,
bayan a k'alla Era tayi goman Sanah,
abu na biyu daya k'ara bashi mamaki shine dame Sanah ta daki haka?
Kuma ya akayi JSS 1 ta iya dambe da SS 3 kuma LABOUR PREFECT,
shi abimma dariya ya bashi, dan tunda Era tace Sanah ce ta dake ta yake kanne dariyar dake neman kufce masa,
Head Girl ya kalla yace " ku kai ta sick bay ayi mata treatment,,
yayi maganar kamar baya so,
"to ta amsa had'i da mik'ewa suka fita,
komawa kan sofar dake office d'in ya kishingid'a had'i da rufe idansa,
batare daya k'ara furta koda kalma d'aya ba,
shiri-shiru har akayi 1hr, amma bai ko kalli inda su Sanah suke ba,
har aka kira Sallar Magrib bai kalli inda suke ba,
jin an kira sallah ne ya sashi mik'ewa a hankali yayi hanyar fita,
da sauri Sanah tace " Sir ka manta da mu ne?
Ko ta kanta bai bi ba, balle ya juyo ,
Sir Moli yana yin sallar Magrib ya wuce gida batare daya k'ara bi takan su ba,
babu abinda yake tunani sai halayyar yarinyar,
wacce bazata wuce 10yrs ba, yana tuno ruwan bala'i da rashin kunyar daya hango a kwayar idanta,
ya tuno yadda ya hango bak'ar zuciya a tattare da ita,
a hankali ya gyara kwanciyarsa had'i da furta " girman yarinyar nan da kallo,
mijinta da iyayenta suna shirin ganin ikon Allah,
yayi maganar can k'asan mak'ogwaronsa.
Har akayi sallar ishsha shiru Sir Moli bai dawo ba,
cikin tsiwa Sanah tace " wai wannan d'an iskan ya manta ya ajiye mutane ne?
" Ko yana tsammanin gumaka ya ajiye marasa jini a jikinsu?
Da sauri Khulud ta rufe mata baki ta zaro ido cike da tsoro, tace " kai Sanah idan ya kawo kai yaji abinda kike cewa fa?
Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " to ya jin mana idan yaji sai me, mai zayyi?
"Ai dai bai isa ya d'auki ran mu ba,
iyakacinsa ya dake mu ko ya bamu wuya,
wuya kam bata kisa, sai dai ma ta k'ara hora mu,
Khulud tace " ni dai dan Allah kiyi hak'uri kiyi shiru kar yaji,
dama muna cikin wani case d'in bamu san makomar mu ba har yanzu,
Sanah tace " ke kin cika tsoro wallahi,
duk irin ku aka tara a makarantar shiyasa yake jin kansa wani shege,
Khulud zatayi magana Sanah ta mik'e tana karkab'e jikinta tace " tashi mu tafi Hostel,
ido waje Khulud tace " Hostel?
Batare data kalle ba tace " amma dai kin san yanzu dare yayi sosai ko?
"Dan nasan a k'alla yanzu 9:00pm na dare yayi,
kuma muma musulmai ne ya kamata muyi sallar Magrib da Ishsha,
kuma koba komai ai mutane ne mu zamu buk'aci hutu, bacci da abinci,
dan nasan shima mugun daya aje mu ya tafi,
Khulud zatayi magana Sanah ta ja hannunta,
tana tafiya da ita " gobe kice ni nace mu tafi Hostel, ni kuma zan bashi amsa dai-dai shi,
suna tafiya Sanah na mitar ajiye sun da Sir Moli yayi " tsabar ya rai nawa mutane hankali,
ya jibge mu a waje batare daya furta mata ko kalma d'aya ba,
shege miskilin banza mai girman kai,
wannan matarsa ta shiga uku,
har suka k'arasa Hostel Sanah na mitar Sir Moli da tsoran Khulud da yayi yawa,
ita dai Khulud kallanta kawai take yi batare data ce mata komai ba.
_Ni ko nace hmmmmm shima haka yace mijinki yana shorin ganin ikon Allah_
Washe gari bayan sun shirya zasu tafi class Halan ta kalle su tace " ku tabbatar baku tafi class kai tsaye ba,
ku wuce office d'in Sir Moli, dan baya san irin haka,
ko kallanta Sanah batayi ba ta wuce abinta,
sai Khulud ce amsa mata da "to,
kana tabi bayan Sanah ganin tayi hanyar classes area yasa Khulud kallanta cike da mamaki,
tace " Sanah ina zaki?
Batare data kalle ta ba, ta bata amsa kai tsaye " abinda iyayen mu suka kawo mu muyi,
Khulud ta kuma kallanta cikin rashin fahintar abinda tace,
tace " kamar ya?
"Ban gane abinda kike nufi ba,
tana ci gaba da tafiya tace " karatu mana,
ko ba karatu iyayen mu suka kawo yi ba?
"Ai ba yawon zuwa staff room da teachers office aka kawo mu yi ba,
dan haka ni class zani, shi daya matsu yazo ya same mu,
ace mutum babu abinda ya iya sai wulak'anci da wulak'anta mutane,
sai wani jijji da kai yake kamar yafi kowa,
babu abinda ya sani sai muskilanci da girman ka......,
idanta daya sauka akan nashi ne ya hana ta k'arasa abinda tayi niyyar fad'a,
gabanta yayi muguwar fad'uwa tsoransa a karo na farko ya shige ta,
tsaye yake sanye da sky blue na material yard,
takalmi da hularsa, da agogonsa duk blue black ne,
yayi masifar kyau,
tun da suka taho yana tsaye hard'e da hannayensa a k'irji yana kallansu,
ya kuma ji duk abinda suka fad'a,
sosai Sanah tayi muguwar tsorata amma ta dage, bata bari tsoran yayi tasirin dazai bayyana a fuskarta ko jikinta ba,
Khulud kuwa tunda ta ganshi jinkinta ya d'auki rawa,
saboda tsoro da fargaba, a hankali Sanah ta saci kallansa,
irin kallan daye mata ne yasa gabanta bugawa da k'arfi,
dakewa tayi ta kama hannun Khulud taja tana k'ok'arin rab'awa ta gefensa ta wuce,
shiko in banda tsabar mamakin hali da k'ok'arin ta, had'i da rashin tsoranta babu abinda yake yi,
bajintar yarinyar da halayyarta ma shi tsoro suke bashi,
ace tun tana k'arama take haka,
ina kuma ga idan ta girma, ta zama cikekkiyar mace?
Yayiwa kansa tambayar, kallan yadda ta had'e rai, ta murtuke fuska yayi,
tana k'ok'arin bi ta gefensa ma ta wuce,
a ransa yace " ikon Allah, lalle yarinyar nan ta cika cikekkiyar mara kunya da fitsara,
amma zan nuna mata ni kakanta ne a wannan fagen,,,
tana zuwa daf dashi zata wuce ya fisgo ta baya had'i dayin cilli da ita,
ta fad'a, sosai taji fad'uwar har cikin ranta,
saboda da k'arfi ya wullata,
cikin tashin hankali Khulud ta isa inda take ta d'ago ta had'i da saka kuka,
tana tambayarta idan taji ciwo,
daurewa Sanah tayi ta mik'e tana murmushi tace " ke meye na kuka kuma?
Ba fa wani babban abu bane 'yar fad'uwa nayi,
da mamaki ya kuma kallanta a ransa yana cewa " lalle yarinyar nan wato bayan tsiwa, zuciya da fad'a, rashin kunya da fitsara ta had'a har da taurin kai da dakewar zuciya,
shi kansa yasan tayi muguwar buguwa amma ta daure ta tashi kamar babu wani abu,
a fili ya maimaita 'yar fad'uwa yana murmushin mugunta,
fuska cike da tausayawa idanta yana zubar da hawaye,
tace " kai Sanah wallahi kin mugu da yawa,
hannu Sanah tasa tana goge mata hawayen dake zubo mata,
tace " zafin buguwar danayi bai kai zafin hawayen nan da kike zubarwa ba,
dan ji nake kamar zuciya ta zata fashe,
Please ki daina kukan kinji Uludi nah,
tayi maganar tana dariya, shikam tsaye kawai yake yana kallan ikon Allah,
abinda ya kuma d'aure mishi kai,
shine kalaman da Sanah tayi akan Khulud, yadda take maganar ya tabbatar masa daga zuciyarta kalaman ke fitowa,
daga irin kallan da sukewa juna ya tabbatar suna matuk'ar k'aunar junan su.
_Kamar ni da my Zainab Shagumba_ 💘💘💘
A dak'ile Sir Moli yace " ke!
tasan