Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
tana safa da marwa,
idan Halan ne ya fara sauka a kanta,
da sauri Halan tace " Sanah daga ina kike, ina kika je?
Da sauri Khulud ta juya ta kalli inda Halan ke kallo,
ido kawai ta zubawa Sanah tana kallanta,
a hankali Sanah ta duk'ar da kanta k'asa,
tana wasa da 'yan yatsunta, Khulud tace " yauma laifin kika kuka yi masa ko?
Tayi maganar idanta na kanta,
cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta,
alamar eh, Halan tace " yau kuma me kika yi masa?
Cikin sanyin murya tace " irin na last week,
ido Khulud ta zaro a tsorace tace " yauma hular tasa kika kuma sawa?
"Na yau yafi haka ma,
Halan tace " yafi haka ma kamar ya?
"Yau har da takalmi da agogonsa na saka bayan hular,
Khulud da Halan suka zaro ido had'i da cewa " me!?
A lokaci d'aya sukayi maganar,
cikin sanyi Sanah ce " eh Allah,
Halan tace " yau kuma dawa ya had'aki ta baki punishment d'in?
Khulud tace " wanne irin punishment aka baki yau?
" Dan nasan na yau sai yafi na last week,
shiru Sanah tayi kanta a k'asa,
cikin tashin hankali Halan da Khulud suka ce " mai matuk'ar wuya aka baki yau ma ko?
Baki ta tab'e kamar zatayi, Khulud ta runtse idanta da k'arfi,
Sanah ta buga tsalle had'i dayin ihuuuu,
tace " yau kam naci mubus,
Halan da Khulud suka had'a baki wajen cewa " bulus kamar?
"Tana dariya ta fad'a musu duk abinda ya faru a tsakanin su,
Halan cike da mamaki ta tsaya tana kallan Sanah,
cikin ranta tace " yau Sir Moli ne ya tsaya da wata d'aliba sukayi magana haka?
Bayan tayi mishi laifi mai girma irin haka,
har ya tsaya yana fad'a mata yare da jinsa sa?
Rasa abin cewa tayi saboda tsananin mamaki,
shiru kawai tayi ta k'urawa Sanah ido,
Sanah tayi murmushi kana tace " Aunty Halan lafiya, wannan kallan fa?
Tayi maganar cikin shagwab'a,
Halan tayi dariya had'i da cewa " wallahi ina mamakin wannan abu ne kawai,
gaki yarinya k'arama ba babba ba balle ace ko sanki yake,
Khulud da Sanah suka had'a baki tare suka ce " SO!!!?
Murmushi Halan tayi had'i cewa " eh mana,
zasu kuma yin magana Halan tace " ban san yawan surutu ku tashi kuje kuyi wanka,
kuci abinci ku tafi karatu kun san dai ranar Monday za'a fara exam ko?
"Eh duk suka ce, kana suka mik'e suka fita,
sosai Sanah da Khulud suka dage da karatu baji ba gani,
ko baccin kirki basu samu har sai da aka gama Exam kana Halan ta sarara musu,
dan hana su sakat tayi da karatu,
Sanah ta d'auki 1st result Khulud ta d'auki na 2rd,
dama haka abin yake tun suna primary school,
Sanah ke d'aukar na d'aya Khulud na biyu,
Ranar Friday ta kama ranar hutu duk d'alibar daka gani cikin murna da matsanannacin farin cike take,
kasancewar ranar duk wani d'an boarding school zai samu 'yan cin kai,
ranar zasu koma gida su sadu da dangi da iyayensu,
ana gama assembly bankwana,
students d'in suka fara watsewa dan komawa hostel ,
dan makarantar akwai tsaro sosai basu sakin yara sakaka,
kamar dabbobi su fita ranar hutu,
dole sai anzo d'aukar d'aliba sannan zata fita,
koda a cikin garin Roni kike wanda gangarawa kawai zasu yi,
amma doka ce dole sai an zo d'aukar d'aliba,
wanda yazo d'aukar yaje ya bada sunanta da sunanshi,
yayi signing,
an kira d'alibar dayazo d'auka an tambaye ta sanshi,
an tabbatar akwai dangantaka a tsakanin su sannan za'a bashi ita,
idan Sir Moli ya sauka akan Sanah da Khulud,
"ke ku zo nan, ya kira su,
jiki na rawa suka k'araso suka zube a gabansa,
hannu ya mik'a musu alamar su bashi result d'in su,
dake rik'e a hannunsu, ba musu suka mik'a mishi ya amsa ya bud'e yana dubawa,
na Sanah ya fara gani ya d'ago kai ya kalle ta yace,
"ashe dai ba laifi, ba iskancin kad'ai bane,
ana fahimtar karatu,
sunkuyar da kanta tayi k'asa batare datace komai ba.
Na Khulud ya bud'e, ganin na biyu yasa shi had'e fuska yana kallan Khulud,
kanta ta sunkuyar k'asa,
"ke ya akayi wannan ta fiki k'ok'ari?
Cikin sanyin murya Khulud tace " dama haka muke d'auka tun daga primary,
rai ya k'ara had'ewa kana yace " to nan ba Primary school bane,
Secondary school ne, dan haka ki dage sosai,
kema ki fita, dan so nake ki zarce ta komai a rayuwa kinji ko?
Shiru tayi batare data ce komai ba,
tsawa ya daka mata had'i da cewa "ba magana nake da ke ba?
Jikinta na rawa tace " bana fatan Allah ya bani abinda zanfi Sanah a rayuwa,
duk abinda zaizo mana na cigaba da k'aruwa ina fatan Allah ya bamu tare,
ina addu'a ina rok'on Allah, kada ya bani ikon mallakar abinda Sanah bazata tab'a samun abinda ya fishi ba,
idan ko har zan samu ina addu'ar Allah ya sanwantar dashi,
daga gare ni ya bata,
a d'an tsorace Moli yace " ke kina da hankali kuwa?
"Sosai tace had'i da d'aga kanta sama ta kalli al'arshe tace " ina fata Allah da Mala'iku su zama shaida,
akan abinda na fad'a yanzu, koma miye a duniya muddin na samu abinda Sanah bazata samu mafificinsa ba,
Allah ka kwace shi daga gare ni ka bata,
ka mallaka mata shi mallakawa ta har abada,
koda tare da rai na da rayuwa ta ne,
shiru Moli kawai yayi yana kallan su cike da mamaki,
dakyar ya iya mik'a musu result d'in tare da cewa " ku tashi ku je,
suka mik'e a tare suka bar wajen,
ya bi bayan su da kallo yana jinjina abin a ransa.
Hango Yayyan su Zafran da Ziyad da sukayi tsaye,
yasa rugawa a guje suka fad'a jikin su,
kowa ya d'aga d'aya sama suna dariya,
batare da b'ata lokaci ba aka sallami su Sanah,
a Hard'o Family kowa ka gani cike yake da murna da farin cikin ganin Sanah da Khulud,
an shirya musu abinci kala-kala na tarbar su,
Sanah sai zuba surutu take tana bada labarin boarding school,
yayinda Khulud tayi shiru tana tunani,
wanda ita kanta bata san tunanin me take yi ba,
haka nan kawai ta tsinci kanta a cikin k'unci da kewar dabata na meye ba,
Sanah ta kalli Khulud tace " muje na raka ki, ki kwanta,
kasancewar a gidan su Sanah suka sauka,
Khulud tayi dariya tace " a boarding school ma bamu rabu ba balle a gida,
daga yau har muyi AURE a part d'aya bedroom d'aya zamu rink'a kwana,
daga yau bedroom d'in mu ya dawo d'aya,
cikin murna Sanah ta kalli Abbu da Mamu (iyayenta Hamraz & Hassana) tace " Abbu kaji wai Khulud ta dawo nan,
dariya yayi yace " sai aji dad'in k'iriniya ba,
Mamu tayi murmushi tana jawo su jikinta ta rungume tace " Allah ya barku tare,
Ubangiji ya k'ara had'e mana kanku,
duk suka ce Amin,
Khulud tace " raka ni na kwaso kaya na daga part d'in Juju da Dide (iyayenta Rawan & Usaina),
Mamu tace " ku bari mana sai gobe da safe,
"a'a suka ce tare,
Abbu yayi dariya had'i da cewa " maza a dawo lafiya.
A parlor suka iske Juju da Dide,
da gudu suka fad'a jikinsu Sanah tace " albishirinku, Dide da Juju suka amsa da "goro suna dariya,
kasancewarsu masu sauk'in kai da wasa da dariya,
Sanah tace " my Ulud yau zata bar part d'in nan,
Dide da Juju suka cewa " zuwa ina?
Sanah tace " zuwa part d'in Abbu da Mamu,
dariya sukayi, Juju tace " Allah ya raka taki gona, kuje can ku k'arata kuda Mamunku,
ni nama huta, Sanah tace " au dama an gaji damu?
Dariya suka kuma yi, Abbu yace " ku dai da Mamu kusan halinta,
suka yi dariya suna shiga d'akin Khulud,
Dide da Juju suka ce "Allah kabar min kan yaran nan a had'e har abada,
Ubangiji karka kawo sab'ani a tsakanin su,
suka amsa da "Amin lokacin da suke fitowa,
ko tsinkenta basu bari ba, sai da suka kwashe komai, suka mayar dashi d'akin Sanah,
tun daga wannan rana Khulud ta koma part d'in su Sanah,
suka koma bedroom d'aya kansu ya k'ara had'ewa shak'uwa da sabo mai k'arfi ya k'ara shiga tsakanin su.
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
9⃣
Washe gari da safe da wuri su Sanah suka tashi,
suka gyara gidan ko'ina yayi fesss,
koda Mamu ta fito k'anshin bonar turaren wuta ne ya daki hancinta,
da sauri ta k'araso parlor'n dan ganin meke wakana,
ganin ko'ina tsaf ya sata tsayawa cak,
cike da mamaki take bin ko'ina da kallo,
"good morning Mamu, suka fad'a tare suna dariya,
juyowa bayanta tayi inda taji yo muryarsu,
fesss suma ta gansu sunyi wanka,
cike tsantsar mamaki Mamu tace " wa yayi duk wannan aikin?
Suna dariya suka amsa da mune Mamu,
" ku ne?
Tace, cikin mamakin,
"yes Mamu, mu mukayi komai,
dan ma bamu iya had'a breakfast ba,
da sai dai ki tashi ki ganshi jere a dinning table,
cikin mamaki Mamu tace "ikon Allah,
ku ce yanzu dai kun girma kunyi hankali, kun san meya kamata?
" Sosai ma Mamu, cewar Khulud,
"waya koya muku duk wannan aikin?
"Aunty Halan, cewar Sanah,
shiru Mamu tayi na wani lokaci kafin tace " wacece kuma Aunty Halan?
"Wacce muke wajenta ce a makaranta,
ita keyi mana komai, bata barin kowa ya tab'a mu,
"kai amma baku da kirki, amma shine da muka je visiting baku kirata mun gaisa ba?
Sanah tace " murnar ganin ku tasa muka manta,
itama sai da tace meyasa bamu kirata ta gaida ku ba,
Mamu tace " gaskiya dai bamu kyauta ba kam,
"masha Allah cewar Abbu yana saukowa daga samansa,
da gudu Khulud da Sanah suka fad'a jikinsa,
"good morning Abbu,
shafa kansu yayi yana murmushi yace " Alhamdulalillah,
how was your night?
Ya tambaye su, "Alhamdulalillah suka bashi amsa,
Mamu dake tsaye tace " ka ganni nan cike da mamakin yarana,
Abbu yace " mamakin me?
"Mamakin canzawar su mana,
kalli gidan fa gaka yadda suka gyara ko'ina yayi fesss,
parlor'n yabi da kallo yana mamaki shima yace " wai su suka yi duk wannan?
"Eh Mamu tace, kansu ya kuma shafawa yace " Alhamdulalillah yara na sun girma ko?
Sanah tace "eh Abbu, damma bamu iya girki ba da har breakfast sai dai ku tashi ku iske mun gama,
"wannan aikin Mamunku ne ta koyar da hazik'an yaranta girki,
Abbu yayi maganar yana kallan Mamu,
dariya tayi tace " ai dole ma na fara koya musu girki daga yau,
dan nan gaba kad'an duk masu aikin gidan nan sallamar su za'ayi,
Abbu yace " idan aka sallame su suwaye zasu aikin?
"Ina fatan dai ba yara na za'a d'orawa hidimar kula da gidan ba?
Mamu tace " to in ba su ba suwa?
Abbu yace " aiko tun wuri ma ki nemi masu yi miki aiki dan baza'a mayar min da yara bayi ba,
yayi maganar yana dariya,
Mamu tace " gani da 'yan mata har biyu zan tsaya ina d'aukar masu aiki,
suna samin ciwon kai?
"Duk abinda nake so nasan 'yan mata na zasuyi min ko?
Ta k'arasa maganar tana kallan su,
da sauri suka ce " yes Mamummu,
dariya Abbu yayi yace " wato kun gwale ni, kun bi bayan Mamun ki ko?
Khulud tace " haba wane mu, mu gwale Abbun mu guda,
kawai dai muma muna san mu taimaka muku ne,
dai-dai gwargwadon k'arfin, Aunty Halan tasha ce mana duk d'an dabaya tausayi da taimakon iyayensa,
bazai tab'a cin nasara a rayuwarsa ba,
kullum yana cikin wulak'anta da tab'ewa,
ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana kallan Mumu yace " gaskiya ya kamata muga Halan d'in nan,
Mamu tace " gaskiya kam,
hanyar fita Abbu yayi Mamu tabi bayan tana cewa " bazaka tsaya kayi breakfast ba?
"Inda anyi niyyar bani da antashi anyi da wuri,
kin dai ga hazik'an yara na, na neman koya miki yadda akeyi idan ke baki iya ba,
yayi maganar yana murmushi cike da wasa,
dariya tayi tace " oh! abin gori ya samu fa yanzu,
har bakin motarsa ta raka shi kana ta dawo gida,
tare dasu Sanah suka shiga kitchen suka had'a breakfast,
ta nunnuna musu duk abinda ya kamata,
da rana ma daza'a girka abincin rana,
tare suka shiga kitchen tana koya musu,
bayan sallar la'asur suka tafi islamiyya.
A islamiyya sosai k'awayen su sukayi murnar ganin su,
dan duk cikin su babu wad'anda aka kai boarding school sai su,
yara suka zagaye Oga Sanah tana basu labarin boarding,
sai zuba take, yayinda Khulud tayi shiru kawai ta zuba mata ido,
dan ita bamai san yawan magana bace,
ranar dai kam haka suka taso babu wani karatu da sukayi sai labarin boarding school kawai da Sanah tayi ta basu,
suna komawa gida suka iske Mamu a parlor,
da murna ta tare su, suka fad'a jikinta,
tace " maza aje a cire uniform,
a huta, kuje ku gaida Jujunku kuzo mu d'ora abincin dare,
Khulud tace " ba wani hutu da zamuyi, bari kawai mu cire uniform mu gaido Juju sai muzo muyi girkin,
"to maza yaran kirki cewar Mumu,
bedroom d'in su suka shiga suka shire uniform d'in,
"Mamu mun cire bari mu gaido Juju mu dawo yanzu,
"sai kun dawo, tace.
A kitchen suka iske Juju na aikin abincin dare,
da sallama suka shiga, fuskarta d'auke da fara'a ta amsa musu,
tana cewa " 'yan boarding sai yanzu aka tashi?
"A'a Juju mun tashi tun safe, munje islamiyya ne,
tayi murmushi tace " masha Allah,
ana dai karatun sosai ko?
"Eh, Juju muna yi sosai, cewar Sanah,
kana ta cigaba da cewa " Juju bari mu tayaki girkin,
"a'a na yafe kuje ku taya Mamu,
Khulud tace " ai tare muke yin girki da ita, yauma tare mukayi breakfast & lunch,
dariya Juju tayi tace " oh su Mamu manya, wato harta fara mayar da yaran ta 'yan mata?
Didi dake zaune a parlor yana karatun jarida yace " ai gwamma hakan kinga sai tayi musu aure da wuri,
dayake basu kula dashi ba,
suka juya da sauri suna cewa " lah Didi dama kana zaune a parlor,
muka wuce bamu kula da kai ba?
"Ina fa zaku kula dani hankalin ku nakan Jujunku,
dariya sukayi suna fad'awa jikinsa,
suka ce " ina yini Didi?
Kansu ya shafa, kana yace lafiya lau, yaran Abbu,
ya Abbun naku da Mamu?
"Duk muna lafiya, Khulud tace " bari mu tafi gida,
Mamu nacan na jiran mu, girki zamuyi,
tunda nan baza'a barmu muyi ba,
tayi maganar tana kallan Juju tana dariya,
Juju tace " ita da taga zata iya cin jagwalgwalanku sai taci,
amma ni da mijina bamu iyawa,
dariya sukayi Khulud ta rik'o hannun Sanah tana cewa " zo mu tafi kinji my Sanah,
tunda basu iya cin girkin mu,
dariya Didi da Juju sukayi suna bin bayansu da kallo.
Da daddare bayan sun gama girki sun jere a dinning table,
Idrak da Aarib,
Ziyad da Zafran suka shigo tare duk su hud'un,
zama sukayi akan sofa, Sanah da Khulud suka fad'a jikin su,
cike da shagwab'a Sanah tace " Yaya kace fa zaka kai mu yawo ni da my Ulud,
murmushi yayi yana k'ara kwantar da kanta ajikinsa yace " sorry Auta na manta ne,
amma ku shirya gobe zan kai ku in sha Allah,
tsalle suka farayi cike da murna,
Abbu da Mamu suka fito tare fukarsu d'auke da murmushi,
gaba d'ayan samarin suka zube suna gaida iyayen nasu,
suka amsa cikin walwala,
Abbu ya kalli Sanah da Khulud yace " murnar me 'yan matan naki suke yi haka?
Yayi maganar yana kallan Mamu,
tace " ina zan sani ne, tayi maganar cikin sanyi tana kallan su,
cike da tsantsar so da k'auna,
kana ta kalle su tace " 'yan matan Mamu murnar me akeyi haka?
Khulud tace " Yaya Aarib da Idrak ne zasu kai mu yawo gobe,
Abbu yace " uhnmmm 'yan gatan Yayyan su,
zama sukayi suka duka akan dinning table,
suna cin abincin cikin farin ciki,
Abbu ya kai spoon d'aya bakin sa yace " uh uhn uhn carkwad'i wayayi girkin nan?
Da sauri Sanah da Khulud suka ce mune Abbu,
Abbu yace " wai badai dad'i ba, tunda nake ban tab'a cin abincin mai dad'in na yau da Yara na suka girka ba,
Mamu ta kalle su tace " oh! kuji k'arfin hali,
daga koyo kuma sai ku zak'e kuce ku kukuyi?
Sanah ta kalli Khulud tace " my Ulud, waya gyara kayan miya?
Khulud tace " mu ne mana,
Sanah ta kuma cewa " waya yanka albasa, ya wanke shinkafa, ya zuba maggi da gishiri?
Khulud tace " mu ne, tana dariya,
" waya rink'a kula da girkin?
"Mu me,
" waya kwashe ya zuba food flask,
ya kuma shirya dinning table?
Khulud tace " duk mune my Sanah,
Khulud ta kalli Abbu da Mamu da Yayyansu tace " to yayi girki?
Duk sukayi kana suka ce " Sanah da Uludinta,
bayan sun gama cin abincin Sanah ta kama hannun Khulud zasu fita,
Mamu tace " ina kuma zaku?
Sanah tace " wajen wad'ancan tsofaffin da suka k'i mutuwa har yanzu,
Abbu ya zaro ido had'i da cewa " uwaku! yana yi musu dak'uwa,
" iyayen namu ne tsofaffin da suka k'i mutuwa?
Khulud tace " Abbu ko sun mutunne bamu sani ba?
"Uwaku cewar Mamu tana dariya,
Sanah tace " ina fa zasu mutu my Ulud, bayan suna jin dad'in duniyar dan na lura ma jin kansu suke yi kamar samari sa'annin su Yaya,
Abbu yayi kwafa yana dariya yace " Ziyad muk'o min yaran can,
da gudu suka fita suna dariya,
washe gari sosai yakai su Sanah yawo, har da su shopride ya kai su kallo,
daga nan ya wuce dasu gidan zoo da rockzy,
da zasu dawo ya kai