Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
shi ya shiga kana ta koma cikin gida.
Kullum sai Khulud tayi ta
faman kiran number Sanah amma not reachable,
haka itama Sanah kullum cikin kiran number Khulud take amma busy,
dukkansu basu kawo komai a ransu,
dan haka suka cigaba da harkokinsu,
haka ma sau uku Sanah na zuwa gidan Khulud mai gadi yana hanata shiga,
daga k'arshe ma rok'arta yayi akan dan Allah karta k'ara zuwa saboda mai gidan yace zayyi asarar aikinsa,
dole Sanah ta hak'ura ta daina zuwa gidan Khulud,
haka duk sanda Hanash zai kai Khulud gida,
sai ya tabbatar da Sanah bata gidan,
sannan zai kaita, kafin ta dawo kuma sun bar gida,
haka suka cigaba da rayuwa lokaci na tafiya har Khulud tayi wata hud'u da aure,
amma ko sau d'aya basu tab'a had'uwa da Sanah ba,
tun bayan aurenta,
su dukkansu basu tab'a tsammanin zasuyi kwana d'aya a rayuwarsu batare da sunga juna ba.
Su Khulud na zaune a parlor'n Mimmee ita dasu Zohal,
Mimmee ma na zaune gefensu,
Zohal ta kalli agogo tace " kinga har 3:30pm na rana tayi,
muyi sauri mu fita kafin Yaya ya dawo,
yanzu daya dawo sai yace yamma tayi babu inda zamu mu bari sai gobe,
Khulud tace " gaskiya kam muyi sauri dan nima ina san zuwa saloon d'in nan wallahi,
Mimmee tace " ta ku tashi kuyi sauri ku shirya mana,
kun tsaya kuna surutu, Khulud tace " mu ai mun shirya Wajnah kawai muke jira,
Mimmee tace " ina Wajnah nan?
Zohal tace " tana bedroom tana ta faman k'ak'ale-k'ak'ale kema ai kinsan halin shirinta,
Mimmee tace " ikon Allah ta kuje ku kirata mana,
kafin suyi magana Wajnah ta fito tana cewa " gani ma na fito ai,
babu wanda yayi magana duk suka mik'e Mimmee ta bisu da kallo d'aya bayan d'aya,
suna k'ok'arin fita Jaddah ta shigo,
tana binsu da kallo, kana tace " ina zuwa?
"Saloon cewar Zohal,
kallan Khulud Jaddah tayi kana tace " wajenki fa nazo,
Mimmee ta kalli Jaddah cikin mamaki batare da tace komai ba,
Khulud ta durk'usa har k'asa tace " ina yini?
Jaddah bata amsa gaisuwarta ba,
tace " ke wai har yanzu ba wani labari ne?
Khulud ta kalleta cikin rashin fahimta,
tace " me Jaddah!?
Jaddah tace " watan ku hud'u kenan da aure amma har yanzu banji kin fara 'yan amaye-amaye,
da rashin lafiyar laulayi ba,
ko har yanzu babu komai,
ni fa kin san babu abinda nafi so sama da ganin yaran Hanash ato kima dage,
Khulud durk'ushe agaban Jaddah kanta na k'asa,
daga Mimmee har su Wajnah babu wanda yace k'ala,
dan sanin halin Jaddah sarai,
Papu dake sakkowa daga samansa yace " Jaddah ba sai Allah ya kawo ba tukunna,
ai basu isa su bawa kansu ba,
sai idan Allah yaga dama ya basu tukunna,
kallan Papu tayi cike da mamaki dan hakan bata tab'a faruwa ba,
tunda take dashi bai tab'a mayar mata da magana ba sai yau akan Khulud,
Khulud ta kalla kana ta juya zata fita,
harta kai bakin k'ofar fita ta kuma juyowa tace " ni dai na fad'a miki,
kana tasa kai tayi ficewarta,
Papu ya k'arasa shigowa cikin parlor'n,
a hankali Khulud ta juya tana gaida Papu,
cike da fara'a ya amsa kana yace " kiyi hak'uri kinji?
Murmushi tayi tace " lah bakomai Papu,
yayi murmushi shima,
kana suka fita.
Washe gari Sanah bata shiga makaranta ba sai around 10:30am na safe,
saboda bata da lafiya zazzab'i da ciwon kai ke damunta sosai,
a hankali take tafiya dan ji take kamar zata fad'i saboda jirin dake d'ibarta,
in banda suna da test da Sir Moli babu abinda zai kawo ta makarantar,
tana shiga class Rose ta nufo ta da sauri ganin yanayin datake ciki,
dan tun da suka samu d'an sab'anin nan suke shiri,
Rose tace " meke damunki,
murmushi Sanah tayi kana tace fever & headache,
cike da tausaywa Rose tace " ayya sorry,
gashi har anyi test baki nan,
da sauri Sanah ta d'ago kanta tace " Sir Aryan har yayi test d'in!!?
Rose tace " yes! tun around 9:30am na safe,
kai Sanah ta dafe had'i da cewa " ya salam!
shiru tayi na wani lokaci kana ta kalli Rose tace " please ki raka ni office d'insa,
Rose ta zaro ido waje cike da tsoro tace " am sorry sister babu abinda zaki tambaye ni na kasa yi maki,
amma ban iya rakaki office d'insa,
shiru Sanah ta kuma yi,
batare data kuma cewa Rose komai ba,
ta nufi office d'insa,
sallama tayi ya bata izinin shigo,
a hankali ta tura k'ofar ta shiga,
yana kishingid'e akan sofa,
idanuwansa lumshe,
ta durk'usa a gabansa,
saboda ji take kamar zata fad'i,
cikin muryar marasa lafiya tace " Sir!,
bai ko motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi mata magana,
muryarta na rawa ta kuma cewa " Sir!
a dak'ile yace " fad'i,
"Sir banyi test ba,
" sai akayi yaya?
Ya fad'a bai motsa daga inda yake ba,
" bani da lafiya ne, ta fad'a muryarta ba creaking,
" me zanyi miki to?
Ya kuma fad'a bai motsa ba,
"dan Allah kayi man tawa!
ta fad'a tana kallanshi,
shiru yayi baice komai ba,
Khulud na kwance a parlor Hanash na gefenta zaune,
tayi saurin mik'ewa ta,
a hankali Hanash ya d'ago kansa ya kalleta,
yace " lafiya naga kin zabura!?
"Ki rink'a bi a hankali saboda unborn d'ina,
dariya tayi tace " kai komai Baby,
shima dariyar yayi kana yace " shine babban buri na a duniya,
wallahi komai za'a bani bai kai na samu Baby ba,
bani da wani sauran buri ko muradi daya wuce na ganni da d'a ko 'ya nawa na kaina,
idan naga Baby na bani da sauran buk'ata a duniya,
murmushi tayi had'i da cewa " Allah ya bamu basu albarka,
ta fad'a tana nufar bedroom d'inta,
wayarta ta d'auko ta dawo parlor ta zauna had'i da kunna data ta shiga WhatsApp,
ta shiga sunan Sanah jikinta na rawa dan basirar yi mata voice note bai tab'a zo mata ba sai yau,
muryarta na rawa tace " My Sanah kina kusa please?
"Idan kina kusa kiyi man magana,
Sanah na durk'ushe gaban Sir Moli taji notification na WhatsApp,
kamar bazata duba ba, sai kuma ta duba,
ganin Khulud ce yasa ta saurin kunnawa a speaker,
Sanah tayi murmushi kana tace " ina kusa my Khulud,
Khulud na rik'e da waya tana jiran amsa,
taji k'arar shigowar sak'o, da sauri ta duba,
kuka Khulud ta saka had'i cewa " me nayi miki My Sanah?
Sanah tayi playing, a hankali ta lumshe idanta jin Khulud tana kuka,
kana tace " meye my Ulud?
Khulud tace " au meye ko?
Sanah tace " eh mana,
cikin kuka Khulud tace " haba my Sanah yanzu fa na shiga 5 months da aure amma baki tab'a zuwa inda nake ba,
tunda nayi aure bamu sake had'uwa ba,
wallahi ko a mafarki aka fad'a min zamuyi 5 months bamu had'u ba ban yarda,
matuk'ar muna raye a duniya,
musamman ma a cikin gari d'aya,
dan Allah idan wani laifin nayi miki ki fito ki sanar dani sai na gyara,
na kuma baki hak'uri,
idan kuma akwai abinda ke faruwa please ki sanar da ni,
dan Allah hukuncin nan yayi man tsauri,
Sanah na danne kukanta tace " kiyi hak'uri kinji my ulud,
komai na duniya muk'addari ne kuma yana da iyaka,
Khulud tace " dan Allah kizo yau please,
Sanah ta lumshe idonta hawaye na zuba,
tace " kiyi hak'uri my Ulud ban iya zuwa dan bani da lafiya,
Khulud ta tura mata amsa cikin tashin hanakali " subhanallah meke damunki?
Sanah tace" fever & headache,
Khulud tace " kina ina yanzu?
Sanah tace " ina makaranta,
Khulud tace " yaushe zaki dawo gida?
" Sai dare, Sanah ta fad'a while hawayen bai bar fita ba,
Khulud tace " to dan Allah gobe karki je ko'ina zanzo,
Sanah tace " tom zan jira ki in sha Allah,
sai da sukayi hira kana sukayi sallama,
Hanash na jinsu, suna gama wayar ya jawo ta jikinsa ya rungume batare dayace komai ba,
suna gama chart d'in Sanah ta saka kukan da take dannewa,
Sir Moli yana nan yadda yake baiko matsa ba, idanuwanshi lumshe,
sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e zata fita,
har takai bakin k'ofar fita,
yace " meke faruwa tsaninku ku ukun?
Cak ta tsaya had'i da juyowa a hankali,
red eyes d'inta ta d'aga ta kalle shi,
taga yana nan yadda yake,
batayi niyyar b'oye masa komai ba,
dan haka ta fad'a masa tun daga zuwanta na farko gidan har zuwanta na k'arshe bata b'oye masa komai ba,
idansa rufe yace " yanzu kina san zuwa ganin Khulud d'in?
Ido ta k'ura masa batare datace komai ba,
a hankali ya bud'e idansa had'i da mik'ewa zaune,
yana kallanta yace " tambayarki nake,
cikin sanyin jiki ta d'aga masa kai,
yace " amma kin san ban san nodding kai ko?
Cikin sanyin murya tace " sorry،
ya kuma cewa " kina san zuwa ganin Khulud?
"Eh! tace tana kallanshi,
a hankali ya mik'e batare daya kuma kallanta ba,
ya zura talmi da hularsa,
kana yace " muje,
da sauri ta kalle shi tace " ina?
" Ban sani ba, yace yana fita daga office d'in,
bayansa tabi a hankali kasancewar jikinta babu kwari,
office d'in ya rufe kana yayi gaba batare daya kalle ta ba،
binsa tayi a baya har suka isa motarsa,
bayyi mata magana ba ya bud'e ya shiga,
tsaye tayi bakin motar tana kallanshi,
harara ya watsa mata,
ganin hararar dayiyi mata yasa ta zumb'urar baki kana ta bud'e motar ta shiga,
Sir Moli bai tsaya ko'ina ba sai a unguwar su Khulud,
dai-dai inda yaga Sanah da daddare,
batare daya kalle ta ba yace " ina ne gidan?
Nuna masa ta shiga yi har suka k'arasa bakin get,
sosai gaban Sanah ke muguwar fad'uwa saboda bata san abinda zai jawowa Khulud matsala a zamantakewar aurenta,
dandai babu yadda zatayi da Sir Moli ne,
yasa ta biyo shi, musamman ma da irin zargin da Hanash yake yi musu,
horn yayi mai gadin ya lek'o, kasancewar motar tine tac ce yasa bai ga Sanah ba,
kuma daya ga motar babbar motace d'auke da private number yasa shi,
tsayawa yana tunani dan shi ba'a sanar dashi akwai bak'i ba,
ganin haka yasa Sir Moli zuge glass d'in motar a hankali,
ya lek'o da kansa yace " bud'e,
ya fad'a a tak'aice,
ba musu mai gadin ya hangame get d'in,
Sir Moli ya danna motarsa cikin gidan kanshi tsaye,
lura da yadda Sanah take yasa shi cewa " fita،
fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please mu koma,
bai kalle ta ba, yace " nace ki fita ko!?
Yayi maganar a d'an hasale,
a hankali Sanah ta kwab'e fuska had'i da cewa " to dan Allah karka tafi ka jira ni,
bai amsa bata ba, ya kawar da kanshi gefe,
a hankali Sanah ta bud'e motar ta fito,
mai gadi na ganin Sanah, ya nufo ta da sauri,
jikinsa na kerrma, yace " Hajiya dan girman Allah ki taimaka min karki shiga,
Yallab'ai yana nan, kuma a gabanki yayi min gargad'i,
Sanah zatayi magana Sir Moli ya bud'e motar ya fito,
ya jingina da jikin motar had'i da hard'e hannayensa a k'irjinsa,
yace " gargad'in me yayi maka?
Muryar mai gadin na rawa yace " Yallab'ai ne yace muddin na kuma barinta ta shiga cikin gidan a bakin aiki na,
"Ok Sir Moli yace kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " shiga,
fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please!
mai gadin yayi saurin cewa " dan Allah ku taimaka min،
ina da yara k'anana,
da mata, sannan ga iyaye na,
ga yaran d'an uwana daya mutu,
duk a k'ark'ashi na suke,
ni kuma da wannan aikin kad'ai na dogara,
Sir Moli yace " idan ya koreka kazo zan baka aiki mai kyau,
ya fad'a batare daya kalli inda mai gadin yake ba,
mai gadin yace " ni dai dan Al.........,
hannu Sir Moli ya d'aga masa,
yace " please Baba kayi shiru nace idan ya kure ka zan baka aiki,
kuma dama matsalarka bata aikin bace,
idan kuma aikin ne baka so zan baka jari mai kyau,
shiru mai gadin yayi saboda kwarjinin da Sir Moli yayi masa,
karaf idan Sir Moli ya sauka akan Hanash dake nufar d'aya daga cikin motocin dake jere a harabar gidan,
da alama bai lura da su ba,
daga Sanah har mai gadin babu wanda ya lura dashi,
Sir Moli ya kalle ta yace " karna sake miki magana,
da sauri ta nufi hanyar shiga part d'in,
Sir Moli ya tsaya jikin motarsa had'i da hard'e hannuwansa a k'irjinsa,
ya zubawa Hanash ido,
yana nazarinsa,
shi dai a fuska baiga wani mugun hali ko alamar munana d'abi'u a tattare dashi ba,
sai nutsuwa da kalama had'i da suffar nagartattun mutane,
daya gani tattare da Hanash d'in,
abinda da marar lafiya Sanah na fara takawa tayi taku na uku,
k'afarta ta gurd'e kasancewar takalmin k'afarta mai tudu ne,
jiri ya d'ebeta tayi baya luuuuuu zata fad'i,
cikin matsanancin zafin nama Sir Moli yayi saurin tare ta,
ta fad'a jikinsa,
a tsorace Sanah ta saki 'yar k'ara,
saboda ta gama sadak'arwa ta fad'i,
k'arar da Sanah tayi ce tajawo hankalin Hanash kansu,
ya sauke idansa a kansu dai-dai lokacin da Sanah ta fad'a jikin Sir Moli.
A hasale Hanash ya juyo yana kallansu cikin matsanancin b'akin rai yace " hey! nan ba hotel ko club bane,
ba kuma gidan karuwai da 'yan iska bane,
idan zakuyi iskancinku kuje can kuyi,
tsabar rainin hankali kuzo man har cikin gidana kuna iskancin da kuka sabo yi,
ko an gaya maku nan gidan 'yan iska ne?
Da sauri Sanah ta fara k'oka'rin kwace jikinta daga na Sir Moli,
amma Sir Moli ya k'ara manneta da jikinsa,
idansa akan Hanash yana kallan cikin kwayar idansa,
yana karantar yanayinsa,
had'i da san fassara abinda yake hangowa cikin kwayar idan nasa,
ran Hanash ya kuma mugun b'aci cikin mugun takaici yace " get out from my house,
kwaratan banza, 'yan iska fasik'ai kawai,
guntun murmushi Sir Moli yayi yana k'ara shigewa jikin Sanah,
had'i da shinshinar wuyanta yana goga hancinsa a kumatunta,
ita ko Sanah sai k'ok'arin kwace kanta take yi,
amma ta kasa sai nuk'u-nuk'u take,
tana k'ifk'ifta idanuwa,
ido Hanash ya runtse cike da tsantsar bak'in cikin ganin abinda Sir Moli yake da mace kuma har cikin gidansa,
cikin b'acin rai Hanash yace " I said get out from my house,
nan ba hotel bane, gidan ma'aurata ne,
Sir Moli yayi dariya kana ya saki Sanah ya maida kallansa ga Hanash yacewa Sanah " jeki shiga,
tsayawa Sanah tayi bata ko iya d'aga k'afarta ba,
idan Sir Moli nakan Hanash ya had'e rai sosai,
yadda kasan bai tab'a yin dariya ba yace " nace ki shige ko,
Hanash tsaiwarsa ya gyara yana kallan Sanah,
yace " tazo ta wucen inta isa ita tacacciyar mara kunya ce,
cikin kuka Sanah ta kalli Sir Moli tace " please mu koma na hak'ura da ganin Khulud d'in,
gigitacciyar tsawa Sir Moli ya daka mata cikin b'acin rai yace " nace ki shiga ko!?
Jikin Sanah na kerrrrma saboda tsawar da Sir Moli ya daka mata
bawai saboda tsoran Hanash ba,
ta nufi hanyar shiga gidan,
Khulud dake zaune a parlor ta mik'e ta fito da sauri kasancewar gigitacciyar tsawar dataji Sir Moli ya daka,
dama tun d'azu take jiyo maganganu k'asa-k'asa,
Khulud na fitowa harabar gidan dai-dai lokacin Sanah ta rab'a ta gefen Hanash zata wuce,
a k'ufule Hanash ya maka mata kyawawan marika gudu biyu a jere,
wad'anda sukata zubewa k'asa ba shiri,
karaf akan idan Khulud........
cikin tsananin b'acin rai da zafin zuciya Sir Moli ya.........
Ya azumi da ibada?
Ubangiji ya amshi ibadun mu,
Allah yayi mana rahama da rahamarsa,
yaji k'anmu da jin k'ansa,
Allah yasa muna daga cikin wad'anda za'a yafewa a wannan watan mai albarka.
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣9⃣
Take duk ilahirin jikin Sir Moli ya d'auki kerrrma da b'ari,
zuciyarsa ta shiga tafasa tana yi masa k'una,
cikin matsanancin zafin rai da k'unar zuciya Sir Moli ya makawa Hanash kyawawan marika guda hud'u a jere,
had'i da sakar masa gigitaccen naushi a cikinsa,
zafin naushin ne yasa Hanash dafe cikinsa had'i da durk'ushewa ya saki k'ara,
Khulud tsaye tayi cak ta kasa koda motsa k'afarta,
ta k'ame a tsaye,
saboda tsantsar mamaki,
Sir Moli ya sunkuya ya d'ago Sanah had'i da manna ta da k'irjinsa,
kallo d'aya zakayiwa Sir Moli kasan ransa yakai k'ololuwar b'aci,
idanuwansa sunyi masifar yin jajir dasu,
ya kalli Hanash yace " kayi gangancin tab'a ta a gaba na,
how dare you da hannunka zai tab'a jikinta?
"Ko an gaya maka ita irin matan nan ce da kowanne Tom and Jerry yake tab'a su,
kaje kaci darajar masu daraja,
amma badan haka ba da sainayi maganinka,
Sir Moli ya fad'a cikin matsanancin zafin rai
a hankali Hanash ya d'ago had'i da nufar Sir Moli gadan-gadan,
cikin zafin nama Khulud tayi saurin shan gaban Hanash,
cikin bak'in ciki da suyar zuciya ta jefa idanta cikin nashi,
yayinda hawaye ke rubdugun zubo mata,
ta kallanshi idanta tarr cikin nashi tace " ashe dama haka kake?
" Wannan itace true color ka?
"Dama na dad'e ina zargin akwai wani abu k'asa,
dan nasan haka nan banza bazai tab'a yiyiwa Sanah ta iya jura getting to 5 months batare data zo ta ganni ba,
Hanash ka ban mamaki, ashe duk abinda kake fad'a k'arya ne?
Baki ta bud'e zatayi magana amma kukan dayaci k'arfinta ya hanata cigaba da magana,
da gudu Baba mai gadi ya rugu ya zabe a gaban Hanash,
had'i da cewa " Yallab'ai kayi min rai,
wallahi ba laifi na bane, sai da nayi musu bayani amma suka k'i ji,
tazo wajen sau biyar ina hanata shigowa,
cike da mamaki Khulud ta tsaida kukanta,
ta maida kallanta ga mai gadin tace " meye Baba?
Cikin rawar murya mai gidan yayi mata bayanin komai,
had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri,
ido Khulud ta runtse cike da bak'in ciki,
kana ta nufi Sanah,
Sanah da har lokacin tana manne jikin Sir Moli,
saboda rashin kwarin jikin data ke fama dashi ya hanata kwace jikinta daga gare shi,
duk ilahirin jikinta kerrrma yake,
ganin Khulud ta nufo ta yasa ta saurin barin jikin Sir Moli,
cikin kukan bak'in ciki Khulud ta rungume Sanah tana kuka,
tace " please my Sanah kiyi hak'uri wallahi kwata-kwata ban san abinda ke faruwa ba,
nayi sake da sakaci dana kasa tsayawa na maida hankalina na lura da abinda ke faruwa,
ta k'arasa maganar tana k'ara fashewa da gigitaccen kuka,
Sanah ma tana zubar hawaye dan bata da k'arfin yin kuka mai k'arfi ta shiga girgiza mata kai,
cikin bak'in ciki Hanash yace " ni ka daka ko!?
Ya fad'a yana nuna kansa,
cikin isa da tak'ama Sir Moli yace " an dake ka d'in,
kayi duk abinda zakayi,
kaci sa'a ma daban illata kaba,
akanta babu abinda zaban iya yi ba,
a hankali Sanah ta d'ago kanta ta kalli Sir Moli jin abinda yace,
Hanash yace " saboda tsabar rainin hankali da rashin sanin shari'a da hakk'in d'an Adam shine zaka shigo har cikin gidan ka dake ni?
Gyara Tsaiwarsa Sir Moli yayi kana yace " ko kana buk'atar k'ari ne?
Hanash yace " wallahi sai naga uban waye ubanka,
sai naga uban da ya d'aure maka gindi,
shege d'an iska fasik'i karuwan namiji kawai,
Sir Moli yayi guntun murmushi kana yace " kai inda kasan waye uban nawa,
da baka soma yin marmarin cewa zaka ganshi ta wannan hanyar ba,
kuma da kake maganar shari'a,
da sanin hakk'in d'an Adam kai abinda kake yi dai-dai ne?
"In banda rashin sanin daraja da k'imar mace,
har zaka iya saka hannu ka mareta,
har kana wani fiffik'a kana nuna k'arfi,
waya fad'a maka