Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
ya sanya hannu ya fara ci,
yana kai lomar farko bakinsa yaji babu dad'i,
a hankali ya d'an yamutsa fuska,
duk abinda yake Mimmee na kallansa,
abincin itama ta zuba ta fara ci,
ganin yana ta juya spoon d'in tun daga lomar farko bai k'ara ci ba,
yasa Mimmee cewa " wacece ita?
Ta fad'a batare data kalle shi ba,
ta jefa masa tambayar bazata,
da sauri ya d'ago kansa ya zubawa Mimmee shu'uman idanuwansa,
dan bai tab'a tsammanin wannan tambayar daga gare ta ba,
shiru Hanash yayi , yayi kamar bai ji abinda Mimmee tace ba,
Mimmee ta kuma cewa " wacece ita?
Ta kuma tambayarsa,
Hanash yace " wa kuma Mimmee?
Batare data kalle shi ba ta kuma cewa " nace wacece yarinyar da kake so?
Cikin shagwab'a Hanash yace " Mimmee,
Mimmee ta ture abincin da take ci gefe,
ta tattara dukkan hankali da nutsuwarta ga Hanash,
tace " Hanash babu wani hali dazaka shiga a duniya wanda zan kasa fahimta,
wanda bazan gane kona lura ba,
ka tuna nice mahaifiyarka ni na tsuguna na haife da kai na,
ni nayi goyon cikinka wata tara da kwana tara,
na shayar dakai daga gare ni,,
na raine ka, kayi wasa dani ka kuma yi kuka a jikina,
na sanka tun kafin kai kanka kasan kanka,
nasan damuwrka da matsalarka tun kafin kai kanka kansan damuwa da matsalar taka,
dan haka zan tambaye a karo na k'arshe wacece yarinyar da kake so?
Shiru Hanash yayi had'i da k'urawa Mimmee ido,
yana tsananin mamaki bai tab'a yarda da maganar da bahaushe ke fad'a akan uwa ba sai yau,
duk duniya babu wanda ya gane damuwarsa koya fahimci matsalarsa sai ita,
lalle uwa dabance rayuwa duk wanda ya rasa uwa yayi kuka,
"uhnnmmm ina sauranka Mimmee ta fad'a,
idanta yana kan Hanash,
'yar ajiyar zuciya Hanash ya sauke kana yace " Mimmee ni ma ban santa ba,
ya fad'a cikin sanyinsa,
"kamar yaya baka santa ba?
Mimmee ta fad'a cike da mamaki,
yace " Allah Mimmee ban santa ba,
"amma kake santa?
" So kuma Mimmee?
" Ba wani so kawai dai......
sai kuma yayi shiru,
Mimmee bana tunnin sonta nake yi,
"saboda me kace haka?
Ta tambashi idanta na kanshi,
Mimmee haka nan, kawai dai ina yawan ganinta a cikin mafarki na ko tunanina,
sannan tana yawan hana ni suku ni,
murmushi Mimmee tayi irin na manya kana tace " Hanash wannan ai shine san,
a hankali ya d'ora idansa akan Mimmee,
ta cigaba "Hanash kana santa,
kai ne dai har yanzu baka yarda kana santa nata ba,
ka yarda koda na rana d'aya ne ka bawa zuciyarka dama akanta,
ka saurari bugun zuciyarka a tun sanda ka ganta,
ko tazo maka,
daga yau zuwa gobe kawai zaka gane abinda nake fad'a maka,
yayi murmushi kawai, Mimmee tace " tashi kaje, amma gobe ka dawo bayan 24hrs.
Su Sanah basu gama lecture's ba sai wajen 6:30,
tayi muguwar gajiya,
tana fitowa ta hango Aarib zaune akan mota yana jiranta,
murmushi kawai tayi masa dan bazata iya magana ba,
saboda tsabar gajiyar data yi,,
Aarib da kansa ya bud'e mata motar ta shiga,
kana ya zagaya ya shiga ya ja motar,
duk abinda sukeyi akan idan Sir Moli,
baki ya tab'a kana yaja motarsa shima yayi waje,
Khulud na jiyo k'arar parking d'in mota ta lek'o ta window,
dama abinda take yi kenan tunda taga 4:00pm tayi,
ganin Sanah yasa ta fita da gudu ta tare ta,
tana zuwa ta fad'a jikin Sanah ta saka kuka,
Sanah tayi rolling sexy eyes d'inta,
tace " kai my Ulud daga dawowa ta,
sai kuka, so kike nima nayi kukan?
Khulud ta girgiza kanta kana goge hawayenta,
Sanah tayi murmushi itama tasa hannu tana gogewa Khulud hawaye,
parlor suka shiga tare Khulud rik'e da jakar Sanah,
sai da Sanah tayi wanka ta canja suka ci abinci tare sannan ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Aryan Rayyan cikekken Bababbare ne na asali,
d'an garin Maiduguri, wato k'asar barno,
suna zaune a unguwar polo dake garin Maiduguri,
General Rayyan Moli shine mahaifinsa,
mutum mai adalci da sanin ya kamata,
mai tsoran Allah, tausayi da taimakon talawa,
mutum kamili nutsatstse mai dattako,
General Rayyan Moli shine shugaban sojojin Nigeria har yau har gobe yana nan akan muk'aminsa bayyi retaya ba,
mutum ne daya samu lambobin yabo dama,
tau daga kan halayyarsa har zuwa nasoririn dayasamu a wajen aikinsa,
dan yana kan yiwa k'asarta aiki irin na mazajen jiya,
duk Nigeria babu wanda bai san MOLI'S FAMILY ba,
dan ko jika ne kai a gidan saikayi amfani da MOLI,
matarsa Hinah ba 'yar asalin Nigeria bace balarabiyar k'asar Kuwait ce,
suna da yara 9 mata 6 maza 3 Sir moli shine dansu na 5 yana da babban yayanshi wanda shine d'an farinsu sunashi Aliyu suna kiranshi Haiydar, Haiydar yanada mata har biyu da yara 6, sannan Sir moli yanada yayu mata 3 mai bin Haiydar Anty Kubra itace sai Anty Nina ta uku sai Anty Ayyam ta hudu, sannan shalelensun dan daga kan Haiydar basu kuma samun d'ana mijiba sai kan, ARYAN RAYYAN MOLI (SIR MOLI),
sai k'annenshi masu binshi MEELAH, da NAJMAH, sai d'an auta Jabeer
mai tsananin kama dashi,
dan suna muguwar kama dashi,
gidan su gida ne daya ginu akan turbar addinin musulunci,
da tarbiyyar da kuma wayewar boko dai-dai musali,
dan mahaifinsu da suke kira da HILWA
da kuma mahaifiyar su da suke kira da NAINAH,
mutane ne masu matuk'ar sauk'in kai,
Allah yayi mugun jarrabarsu da mugun san yaransu musamman ma Aryan, duk family nasu anfi ji dashi, yayunshi da k'annenshi suna mishi wani irin so na musamman, duk da halin miskilancin shi, suna mishi matsanaicin so sabida tsananin kamanshi da mahaifinsu, shi kuwa wani irin so yakewa yaran yayun nashi, suma yaran komai nasu zakaji suna Uncle Moli, dan shi kusan yafi gadar sunan inkiyar mahaifin nasu
Meelah da Najmah suna gama secondary school akayi usu aure,
mazansun suma barebari ne suna zaune a cikin garin Maiduguri,
a anguwar low cost.
Duk wata mota da zaka gani da sunan MOLI'S ta gidan suce,
Allah yayiwa MOLI'S tarin arziki,
wanda su kansu basu isa suce ga abinda suka mallaka a duniya ba,
yana da estate manya-manya a nan gida Nigeria dama sauran k'asashen duniya,
duk k'asar kaje kaga estates ko malls,
da sauraran abubuwa da sunan MOLI'S na General Rayyan ne,
Aryan Moli (Sir Milo) yayi karatun degree & master da PHD d'insa duka a Oxford University dake America,
bayan ya gama degree ne ya dawo Nigeria yayi service dan haka dokar k'asar take,
duk inda kaje kayi karatu dole ka dawo gida kayi bautar k'asa,
bayan ya gama service ne ya koma yayi master & PHD duka a America,
Aryan ya kasance mutum ne mai bin ra'ayin kansa,
shi kwata-kwata bai damu da tarin dukiyar da mahaifinsa keda da ita ba,
Aryan tun yana yaro yake mugun so da sha'awar yin aikin government,
musamman koyarwa, mahaifinsa bai hana shi ba, ya barshi dan shi mutum ne mai matuk'ar sauk'in kai,
bai san koyaya ne ya tauyewa mutum hakk'in shi.
Washe gari da safe bayan Sanah ta shirya dakyar Khulud ta barta ta tafi school,
dan harda kukanta, tare Aarib da Sir Aryan sukayi parking,
Sanah ta d'an jima a cikin motar kafin ta fito,
Hanash yayi kamar yadda Mimmee ta sashi,
ya kuma tabbatarwa kansa san Khulud yake yi,
a parlor ya iske Mimmee zaune,
tana ganinshi ta sakar masa murmushi,
har k'asa ya durk'usa ya gaida ita,
tana murmushi tasa hannun ta d'ago shi,
ta zaunar dashi a kusa da ita ,
tace " son ya ake ciki?
Murmushi yayi yana kallanta batare daya iya cewa komai ba,
"Son!
ta kira sunanshi cikin sanyin murya,
kansa k'asa ya amsa amsa mata " na'am,
tace " ya kaji yau d'in?
Ya kuma yin shiru,
tace " Son kayi man bayani mana,
murmushi yayi yana kallanta had'i da d'aga mata kai alamar "eh,
murmushin jin dad'i tayi tana shafa kansa tace " Alhamdulillah abinda muka dad'e muna jira yau yazo kusa,
to yanzu ina ne gidansu?
"Ban sani ba Mimmee ya fad'a kamar zayyi kuka,
kansa ta kuma shafa kana tace " ina kuka had'u?
Bayanin komai yayi mata tun daga farkon had'uwar su har zuwa last had'uwar da sukayi,
abu d'aya kawai ya b'oye mata,
marin da Sanah tayi mishi,
kai ta jinjina kana tace " babu wani abu da zaka iya tunawa akanta wanda zai baka damar gane ta?
Shiru yayi na wani lokaci kana ya d'ago ya kalle ta cikin alamun karaya ya girgiza mata,
yace " no Mimmee,
tace " try please,
ya k'ara shiru can yace " I can't,
"try ta kuma fad'a tana shafa kansa,
Mimmee ban iya tuna komai fa,
ta kalle shi cike da tausayawa,
tace " bakomai karka damu kaji Son idan har Allah yayi ita matarka ce babu makawa sai kun had'u,
so karka d'aga hankalinka kaji,
kansa ya d'aga mata cikin sanyin jiki,
kana yayi mata sallama ya mik'e zai fita,
har ya kai bakin k'ofa ya tuno ranar daya fara ganinsu,,
da irin uniform d'in makarantar su Zohal ya gansu,
da sauri ya dawo kusa da Mimmee yace " Mimmee na tuna wani abu,
tace " meka tuna?
"Ranar dana fara ganin su da irin school uniform d'in su Wajnah na gansu,
" yauwa Mimmee tace, kana ta shiga kwalawa Zohal da Wajnah kira,
da sauri suka fito daga bedroom d'insu,
Mimmee ta kalle su tace " yayanku ke nemanku,
suka mayar da kallansu kansa,
ido ya zaro yana kallan Mimmee yace " ni kuma Mimmee?
Mimmee tayi mishi alama da ido da yayi magana,
kana ta kauda kanta gefe,
ajiyar zuciya ya sauke had'i dayin gyaran murya yace " akwai wasu yara a school d'in ku,
d'aya tafi d'aya fari, wacce tafi farin tafi jiki,
sannan d'ayar doguwa ce sirirya,
tafi d'ayar tsayi, d'ayar tana da dimples da wushiya,
kun san su?
Duk shiru sukayi suna tunnani,
kana suka ce " gaskiya Yaya bamu gane su ba,
kuma kai baka san sunan su ba?
Shiru yayi yana tunanin,
ya jima sosai yana tunanin kafin ya tuno sanda Khulud tacewa Sanah,
"wai my Sanah meye haka ne,
lokacin daya watsa mata ruwan kwata,
tana yi mishi rashin kunya,
a hankali yace " sunan d'ayar SANAH,
da sauri suka zauna kusa dashi suna dariya,
kana sukace " oh! Sanah Hamraz & Khulud Rawan kake nufi ashe,
Mimmee dashi sukayi dariya,
Mimmee tayi saurin cewa " yaya halayyar su take?
Zohal tace " suna da kirki basu da wani munin hali,
sai dai ita Sanah tana da tsiwa da bak'ar zuciya,
sab'anin Khulud da babu ruwanta,
nan suka kwashe halayyarsu suka fad'awa Mimmee,
Mimmee taji dad'i sosai jin daga Sanah har Khulud basu da wani mugun hali na kyama wanda uwa zata hana d'ansu auren su,
Wajnah tace " ai ranar nan gidan su mukaje walima ma,
sune suka gayyace mu walimar,
class d'in mu d'aya,
Zohal tace " amma fa suna matuk'ar so da k'aunar junan su,
dan tunda nake a duniya ban tab'a ganin wad'anda suke san junansu kamar su ba,
wallahi idan d'aya bata san abu,
to duk sanda d'ayar keyiwa abun ta hak'ura dashi,
haka ma komai nasu iri d'aya ne,
hatta reborn ko color basu canjawa,
idan d'aya na kuka d'ayar ma sai tayi,
nan suka kwashe irin so da muguwar shak'uwar dake tsakanin Sanah da Khulud suka fad'awa Mimmee da Hanash,
har labarin abinda ya faru a Roni sai da suka basu labari,
dan sun samu labarin komai,
Mimmee ta jinjina kai tana mamakin irin wannan mugun son dake tsakanin su,
Hanash yayi shiru dan yaga tabbas da idansa yaga zahiri,,
amma duk da haka shi kansa sai da yayi mamakin son da suke yiwa junansu,
Zohal tace " bari na d'auko waya ta na nuna maka pictures d'in mu dasu a wajen walimar,
ta shiga bedroom d'insu ta d'auko wayar,
mik'a mishi wayar tayi ya amsa hannunsa yana kerrma.
Ido sosai ya k'urawa Khulud yana kallan yadda take murmushi da dariya,
kayan da kwalliyar sunyi mata kyau sosai,
kyanta ya fito, take yaji shi cikin matsananin farin ciki da walwalar daya dad'e bai tsinci kansa a ciki ba,
amma yana d'ora idansa akan Sanah lokaci d'aya yaji mugun bak'in cikin ya saukar masa,
ya nemi gaba d'aya walwalarsa ya rasa,
danba k'aramar tsana yayiwa Sanah ba,
yana jin tsanar ta har cikin ransa da zuciyarsa,
sosai Hanash yake jin k'iyayyar Sanah a cikin jinin jikinsa da tsokarsa,
tunowa da maganar su Wajnah yasa jikinsa yin sanyi yaji gabansa yayi muguwar fad'uwa,
lura da yanayin daya shiga yasa Mimmee cewa su Zohal "ku mik'oman wayar nima naga pics d'in walimar ku shiga ciki,
ba musu suka bata wayar, su kuma suka koma bedroom d'insu,
Mimmee ta kalli pics d'insu,
sosai taji tana matuk'ar k'aunar su gaba d'aya duk da bata san ainahin wacce Hanash yake san ba,
ta kalle shi tace " waccece a ciki?
Murmushi yayi kana ya mik'e ya koma kusa da ita,
ya nuna mata Khulud,
tace " wow! masha Allah she's so beautiful as so mush as I think bf,
yayi murmushi, ta kalle shi tace " meye naga duk yanayinka ya canja,
bayyi niyyar b'oye mata komai ba,
dan haka yace " Mimmee wallahi kwata-kwata ban san sister nan tata,
bata da kunya sosai, kinji ma su Zohal sun fad'a,
murmushi tayi kana tace " eh kamar yadda naji sun fad'i rashin jinta haka naji sun fad'i so da k'aunar dake tsakanin su,
dan haka muddin kana san Khulud dole ka b'oye k'iyayyar abinda tafi so a duniya,
inba haka ba ka rasa ta, dole ka daure ka rink'a pretending na kana santa,
murmushi ya kumayi kana yace " nagode Mimmee a ransa kuma yana tabbatarwa kansa muddin ya samu soyyayar Khulud har ya kai ga ya aure ta dole ne ya raba ta Sanah,
dan bai ko k'aunar ganinta,
kuma muddin ya bar Khulud tana mu'amula da Sanah yasan sai ta lalata ta,
ta watsa mata tarbiyyarta.
_Ni ko nace kuji man mutum da k'afin hali ka same su tare tsawon rayuwarsa kace zaka raba su, dacan bata lalata ko ta canja mata tarbiyyarta ta ba sai yanzu, tare fa gansu_
Mimmee tace " yaushe zaka je ka sanarta da ita?
Dariya yayi yace " da wuri haka Mimmee?
Tace " idan baka je yanzu ba sai yaushe zaka?
"Kasan bahaushe yace " a bari ya huce shike kawo rabon wani,
ka tabbatar yau ka shirya kaje ka sanar da ita,
yayi dariya kana yace " in sha Allah yau zani wajen 4:30pm,
"Allah ya taimaka ,Ubangiji ya kuma baka sa'a ya zama muku abinda yafi alkhairi a tsakaninku,
ya amsa da " Amin,
kana mik'e ya fita cike da farin ciki,
barin ma daya tura duka pictures d'in a wayarsa,
part d'in sa ya koma ya zauna a parlor yayi editing pics d'in,
ya cire Sanah, duk inda ta fito ya yanke ta,
yabar Khulud d'insa ita kad'ai,
4:00pm nayi ya tashi ya shiga wanka,
ya shirya cikin shiga ta alfarma,
kyansa da haibarsa suka fito,
sai da ya biya yayiwa Mimmee sallama tayi masa addu'a sosai,
kana ya fito, driven daya kai su Zohal gidan walimar yasa shi raka shi gidan,
ya saka shi gaba yana binsa a baya har suka isa gida,
kana ya sallame shi,
shi kuma ya shiga get d'in gidan,
get man ya aika akayi masa sallama da Khulud,
tana zaune kusa da Mamu cike da cewar Sanarta,
mai gadin yayi sallama a bakin k'ofa,
Mamu ta amsa kana ta bashi izinin shigowa,
bayan sun gaisa da Mamu kana yakai dubansa ga Khulud yace " manyan gobe ana sallama dake,
ido Khulud zaro had'i da cewa " ni?
Ya bata amsa da "eh ke yace,
" kai badai ni ba, dan ban kowa ba,
ka dai koma ka k'ara tamyarsa,
yace " ke yace manyan gobe,
zata kuma yin magana,
Mamu tace " jeka ce tana zuwa,
ya fita, kana ta mayar da kallanta ga Khulud tace" tashi kije,
Khulud tace " Mamu ni fa ban san kowa ba,
Mamu tace " ai da haka ake sanin kowan,
tunda kikaga yazo gidan ku, ya kuma ambaci sunanki,
ai ya sanki kenan,
dan haka tashi kije,
tayi shiru bata da alamar mik'ewa,
Mamu ta daka mata tsawa tace " dan ubanki ba magana nake yi maki ba?
Ta mik'e ta zari mayafi zata fita,
Mamu tace " haka zaki fita baki gyara fuskarki ba bakiyi komai ba?
"Dalla koma ciki ki canja kaya ki gyara fuskarki ki fesa turare,
Khulud ta d'an turo baki kana ta nufi bedroom d'insu,
shiru bata fito ba,
Mamu ta d'aga murya tace " zaki fito ko sai nazo na iske ki a d'akin nan?
Khulud ta fita, zata wuce Mamu tace " sakaran yara kawai,
kince bazakiyi karatu ba, so kike mu tasaku gaba muna kallo bayan kun isa aure,
har ita mai karatun idan ta samu miji aure zatayi,
duk mu aurar daku mu huta fargaba da tsoran mu ya k'are,
baku san duk mai 'ya mace cikekken bacci ma bai iya yi ba,
da ido d'aya yake bacci, har sai ya kawar da ita ya huta kana,
Khulud ta fita batare data ce komai ba.
A gajiye lik'is su Sanah suka fito daga second to the last lectures d'in su,
in badon lectures d'in Sir Moli ce next lactures d'insu ba, da dalibai da yawa zasu tafi gida, dan yadda suka gaji, ga yunwa ga yanayin garin da ya fara sauyawa, hadari ne daga k'asa ya fara shatawa sai iska dake dan busawa a hankali tana ratsa, illahirin bani adam dake wurin, sai d'aga kai students d'in suke yi, wasu suce "ruwafa za'ayi, wasu kuwa suce, hadarin zai fa watse, bakuji iska mai sanyi ke kadawa ba". haka dai suke ta hasashen su, gudun dai kar su taka k'aidar Sir Aryan (Sir Mili) shima ya tattakesu yasa dole, suke ,tsumayin lokacin zuwansa,
A hankali Sanah, ta d'an ja tsaki, dan yunwar da taji tana k'wak'wularta, hannu tasa ta d'an dank'i cikin nata, gyara zamanta tayi akan kujerun SUG, dake
a tsakiyar shuke-shuken dake zageye da department d'in nasu,
shiru tayi dan ita kadai keta green, kasan cewar har yau batayi k'awaba,
jin shirun ya mata yawa yasa ta zaro woyarta, ta fara lallatsawa, dan ta d'an d'ebe mata kewa kafin yazo,
tana cikin danne-dannen taji, motsi a saman bishiyar ayaban da take zaune cikin inuwarsa, ido ta lumshe, dan k'amshi da wurin yakeyi gaba d'aya, sabida bananan da ke zagaye da wurin, gasu sunyi sutu-sutu, dai-dai ci, Amman ba damar tab'awa, kamar dai irin dokar dibinon dake cikin G,S,U duk d'alibin daya tab'a ya tab'owa kanshi C/O. da sauri ta d'ago kanta jin motsin yayi yawa sosai, ido ta zazzaro woje, dan ganin wasu k'attin k'adangaru, suna hard'e da juna suna fad'a, cizo juna sukeyi harda jini, a firgice ta mik'e ,dan tsoron karsu rikito a kanta, har ta juya zata tafi, sai kuma taji gyalenta ya sule ya fad'in cikin tsoron, ta sunkuyo da sauri ta d'auke mayafin, tana mik'ewa tare da yafawa a jikinta, tana gama mik'e tsawonta kenan, suka rikito kanta, wani irin tsalle tayi tare da k'am-k'ame jikinta, ta bud'e hannayenta duka buying, tuni ta cilla woyarta gefe, ihu ta saki da iya k'arfinta tare da furta, "innalillahi". k'ara ta kuma cillarawa jin d'aya k'adangaren yabi wuyan rigarta ya shiga jikinta, tuni yabi tsakiyar k'irjinta yana neman wurin b'uya a jikinta, dan d'ayan ya fishi k'arfi duk ya jikkatashi, shiko d'aya k'aton sai huci yake yana kumbura kai, ya shimfid'e a fuskarta, kanshi na k'atsan idonta,