Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
bayan boot ya saka gaba d'aya kayan.
A baya Sanah ta ke bin su Abbu tana sauri harda tuntub'e,
Sanah na zuwa dai-dai flowers,
dake zagaye da staffroom taji wani abu ya fad'o mata a jikinta,
d'aga idan da zatayi taga............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣3⃣
D'aga idan da zatayi taga k'aton k'adangare (jangwali gwada),
ai kota tayi muguwar tsorata,
a rud'e ta nufi Zafran tana tsalle had'i da ihuuu,
ganin katon koren k'adangaren dake jikinta yasa shi yin baya,
shima a rud'e, saboda shima yana mugun tsoron k'adangare,
a kid'ime take binsa yana yin baya shima,
ga k'adangaren ya mak'ale mata,
da rud'e ta cire hijabinta tayi wurgi dashi,
tana cigaba da kukanta da tsalle,
ganin Zafran na ja da baya ga k'adangaren na neman shigewa cikin rigarta,
ya sata d'aga murya da k'arfi a matuk'ar rud'e tace " SIR MOLI! SIR MOLI!! SIR MOLI!!!,
dan girman Allah ka taimakeni zan mutu,
Sir Moli na kishingid'e lumshe da ido akan sofa cikin office d'inta,
ya jiyo muryarta tana kwala mishi kira,
da sauri ya bud'e idannasa, had'i da kasa kunne dan jin da gaske ko gizo muryarta ta keyi masa,
da k'arfi ya kuma jin Sanah tace " please Sir Moli zai shiga cikin riga ta kazo da sauri,
a mugun kid'ime ya mik'e ya fita ko takalmi bai sanya ba,,,,
lokacin daya isa tana gaf da cire rigar jikinta,
wani irin wawan tsalle Sir Moli yayi,
wanda shi kansa bai tab'a tsammanin zai iya yin irinsa ba,
bisa gwiwowinsa ya isa gabansa a durk'ushe ita kuma tana tsaye,
tana kuka da tsalle,
tana yarfa hannuwanta idanta sunyi jajir duk ilahirin jikinta kerrrrma yake,
gami da tsuma,
a zabure yasa hannu yayi saurin gyara mata rigar jikinta,
gudun karta k'arasa cireta a gaban mutane,
sannan ya fusge k'adangaren yayi jifa dashi,
kai da ganin yadda yayi jefa dashi kasan yana mutuk'ar jin haushin shi,
yana daga durk'ushen a gabanta ya d'auko d'ankwallinta,
ya d'aura mata, ya maida mata hijabinta jikinta,
kumatunta ya d'an tab'a a hankali yana murmushi yace " karki k'ara k'ok'arin cire kaya a gaban mutane kinji ko?
Ta d'aga kai a hankali hawaye faca-faca a fuskarta,,,
tunowa da tayi baya san d'aga kai yasa cewa " to ai tsoro nake ji tayi maganar a hankali,
idansa na kanta, while yana murmushi yace " ki zama d'aya daga cikin matan da ko kashe su za'ayi bazasu tab'a bayyanar da tsiraicin su ba,
bazasu tab'a zubar da k'ima da mutuncin su ba,
idansu sark'e cikin na juna tace " meye k'ima?
Murmushi yayi yana shafa kanta yace " k'ima da mutunci duk abu d'aya ne,
kuma abu ne daya fi komai mahimmanci a rayuwar d'an Adam,
muddin akace mutum bashi da k'ima da mutunci dashi da dabba duk d'aya suke ba zai tab'a zama cikekken mutum ba,
cikin sanyin murya tace " to ya za'ayi ni ma na zama mai mutunci?
"Kina san ki zama mai mutunci?
Ya tambaye ta idansa na kanta,
"Eh tace,
yace " meyasa?
"Saboda naji kace duk wanda bai da su,
dashi da dabba duk d'aya,
murmushi yayi kana yace " ki zama mace mai kunya, daraja,
tausayi da jin k'ai, mai jin magana da d'aukar gyara,
ki zama mai k'an-k'an da kai,
mai karrama mutane, mai gaskiya da amana,
mai tsoran Allah, mai addini, mai suturta jikinta wacce tasan darajar kanta da jikinta,
ki zama salihar mace, wacce iyaye, ahalinta da 'yan uwanta zasu yi alfahari da ita,
su kuma samu kwanciyar hankali da nutsuwa a duk inda take,
ido kawai ta zuba masa bata ko k'iftawa,
har ya kai aya sannan tace " ya za'ayi na iya duk wad'annan?
" Kiyi yak'ini a zuciyarki cewar zaki iya,
karki tab'a zama mutum marar kwarin gwiwa,
ki sawa ranki da zuciyarki, zaki iya cimma duka burikanki,
duk abinda kikaga mutum bai yi ko ya iya ba,
bashi da yak'ini ne,
a hankali tace " yak'ini?
"Meye kuma yak'ini?
Murmushi ya kuma yi kana yace " gaskatawa, yarda da tabbatarwa duk suna cikin yak'ini,
shiru tayi tana kallansa kana tace " duk wad'annan abubuwan d'aya suke nufi?
"Eh yace yana kallan kwayar idonta,
Abbu, Ziyad da Zafran suna tsaye cike da tsantsar mamaki suna kallan ikon Allah,
shi Abbu mamaki d'aya yake yi,
yadda duk jama'a da Malaman su dake wajen bata nemi taimakon kowa ba,
sai na wanda baya wajen,
bayan a wajen har da shi kansa mahaifinta, ga Ziyad, da Sir Jeeb,
amma babu sunan wanda ta kira sai na MOLI,
kanta Sir Moli ya shafa yace " bye,
juyawa tayi ta nufi mota, har ta d'ora k'afarta zata shiga motar,
ta juyo bisa mamakin kowa sai akaga tayi murmushi akaro na farko tun bayan faruwar abun tayi murmushi,,
cikin sanyin murya tace " nagode sosai,
bazan tab'a mantawa da alkhairin daka yi min ba,
thank you so much,
tayi maganar tana murmushi,
murmushi kawai yayi mata batare dayace komai ba,
motar ta shiga ta zauna, ta d'auki kan Khulud ta d'ora akan cinyarta,
Abbu na gaba Zafran na driving,
Ziyad na baya yana rik'e da hannun Sanah,
Halan bata bar wajen ba har sai da motar su tabar harajar makarantar,
shima Sir Moli yana nan durk'ushe bai motsa ba har suka fita daga get,
a hankali ya d'aga kansa sama had'i da lumshe ido,
duk Malaman suka yi jugum-jugum suna kallan ikon Rabbi.
A mota babu wanda yake cewa komai,
kowa da abinda yake sak'awa a ransa,
shi dai Abbu Sir Moli ne ya tsaya masa a ransa,
musamman yadda ya lura akwai sabo tsakaninsa da Khulud da Sanah,
dan yadda Sanah ta kira sunanshi ta nemi taimakonsa shi kad'ai bayan tarin mutanen dake wajen ya tabbatar masa da hakan, kuma tunda suka je baiga yayi magana da kowa ba sai Sanah,
kuma kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin tension,
saboda ya hango wani abu a cikin kwayar idansa,
a hankali Abbu yace " Sanah waye wannan?
Cikin muryar kuka tace " wa Abbu?
Yace " Sir Moli,
hawayen dake zubo mata ta goge kana tace,
"Malami ne a makarantar amma mu baya d'aukar mu,,
ba permanent teacher bane service yazo,
Abbu yace " daga gani yana da sauk'in kai da tausayi,
gashi nutsatstse,
shiru Sanah tayi bata kuma cewa komai ba,
dan ita kad'ai tasan me take ji a ranta,
ita kad'ai tasan irin zafi da k'unar da zuciyar ta keyi mata.
A harabar Aminu Kano Teaching Hospital suka yi parking,
dan Abbu yace wannan babban case ne yafi k'arfin private Hospital,
dole sai babban asibiti inda manyan Doctors zasu duba ta,
sai dai idan matsalar ta wuce nan su tafi Germany 🇩🇪,
suna yin parking Abbu ya fito da sauri ya shiga ciki,
bai shima ba ya fito tare da Doctors biyu da Nurse's hud'u,
d'auke da gadon d'aukar marasa lafiya,
da sauri aka d'auki Khulud, Sanah tayi saurin fitowa tabi bayansu hannunta cikin na Khulud tana cigaba da kukanta,
suna isa k'ofar Emergency room,
Doctor ya kalli Sanah yana dariya yace " Mrs Cry sake ta zamu shiga ciki,
jin abinda Doctor d'in yace ya sata sakin gigitaccen kuka,
" ni Allah ban rabuwa da Khulud sai dai mu shiga tare,
Doctor ya kalle yana murmushi yace " ina ai ba zai yiyu ba,
tana kukan ta fara buga k'afa " Allah ba mai raba ni da Khulud,
salan a fito ace man ta mutu,
Doctor yace " a'a ba wanda zai ce miki ta mutu in sha Allah,
sai dai ayi miki albishirin ta warke,
" ni dai a'a tace kana cigaba da kuka,
dai-dai lokacin su Abbu suka k'araso,
jin yadda ake ta fama da Sanah ya sashi hasala ya daka mata tsawa " ke badake ake ba?
Sosai Sanah ta rikice jin tsawar Abbu ta saka rikitaccen kuku,
kallan Abbu Doctor yayi yana girgiza masa kai yace " no Alhaji,
ba haka ake yiwa yaran dake cikin matsala da damuwa ba,
a hankali Doctor ya durk'usa a gabanta kana yace " kina san Khulud d'inki ta samu lafiya?
Da sauri ta d'aga kanta,
yace " kin tabbatar?
Ya kuma tambayar ta, ta d'aga masa kanta a karo na biyu,
yace " to matuk'ar kina san ta samu lafiya ku cigaba da wasa tare ki bari a duba ta,
cikin rawar murya tace " to na bari,
murmushi Doctor yayi had'i da goge mata hawayenta yace " ki dai na kuka kiyi mata addu'a kinji?
" To tace, mik'ewa yayi yana k'ok'arin shiga emergency room,
da sauri Sanah ta rik'o hannunsa tace " ka tabbatar My Ulud zata tashi bazata mutu ba?
Tayi maganar cikin wani irin yanayi mai ban tausayi hawaye na zubo mata,
wanda hakan yayi masifar saukarwa da duk jama'ar dake wajen tsananin tausayinta,
a hankali Abbu ya goge hawayen dake k'ok'arin zubo masa,
ido kawai Doctor ya zuba mata batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
ta kuma cewa " dan Allah kayi k'ok'arin ceto min rayuwarta idan ba haka ba nima mutuwa zanyi,
kai ya jinjina yana shafa kanta yace,
"da yardar Allah nayi miki alk'awarin zanyi iyakar bakin k'ok'arina,
murmushi tayi masa hawaye na zubo mata tace " nagode.
Gefe ta koma ta rakub'e a k'asa tana cigaba da kuka,
abin gwanin ban tausayi,
Abbu ya ciro waya ya kira Mamu bugu d'aya tayi picking,
bayan sun gama gaisawa Abbu yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and Emergency,
kuma nasan kwantar da mu za'ayi,
da sauri tace " ok ganin zuwa yanzu,
me za'a kawo muku?
A tak'aice Abbu yace " duk abinda ya kamata,
"ok tace tana mik'ewa da sauri,
Abbu yana kashe wayar Mamu ya kira Didi,
bugu d'aya yayi picking yana dariya yace " Abbun patient,
fuska Abbu ya b'ata kana yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and emergency idan kana iya zuwa,
Abbu na fad'ar haka ya kashe wayar,
murmushi Didi yayi yabi phone d'in da kallo,
kana ya kira wayar Juju,
yace ta shirya yanzu zasu je Hospital,
tace " aiko yanzu Mamu ta kira ni tace na shirya zamu tafi,
yace " ok to mu had'u acan.
Da sauri Didi ya k'araso inda Abbu yake,
duk fushin da Abbu yake yi da Didi yana ganin shi yaji zuciyarsa tayi sanyi,
yaji duk zafin ransa ya gushe,
yaji bai iya yi masa komai,
Abbu ya kalli Didi yace " wato dan kaga bana iya yin dogon fushi dakai shiyasa kake man san ranka ko?
Didi yayi dariya yace " ai ni ban ma iya fushin dakai koda wada ne, bama dogo ko gajere ba,
kuma nasan ai zakayi fiye da abinda ni zanyi,
Abbu zayyi magana Mamu da Juju suka shigo,
da sauri Mamu ta k'arasa tana tambayar ina Khulud,
Abbu yace "tana Emergency room,
shiru Mamu tayi tana safa da marma,
Juju ta kalle Abbu tace " Sanah fa?
Murmushi yayi kana ya nuna mata inda Sanah ke rakub'e a k'asa tana kuka,
har ta fara fita daga hayyacinta,
" Subhanallah Juju ta fad'a tana nufar Sanah,
d'ago Sanah Juju tayi ta rungume had'i da bubbuga bayanta,
Sanah ta saka gigitaccen kuka,
jikinta sai kerrrrma yake yana tsuma,
tace " Juju na kashe my Ulud da kai na,
Juju dan girman Allah kice mata ta tashi karta tafi ta barni,
idan ta tafi ta barni bazan tab'a jin dad'in rayuwar duniya ba,
tayi maganar a matuk'ar firgice,
a hankali Didi ya k'araso wajen,
ya zauna kusa da Sanah, shida Juju suka saka ta a tsakiya,
ta kalle shi bakinta na rawa tace " Did.....
bai bari ta k'arasa ba ya jawo ta jikinsa ya rungumeta,
yana shafa kanta, batare dayace komai ba.
An kai wajen 3grs kana Doctors suka fito,
da sauri Abbu da Mamu suka nufe su,
Sanah ma tayi sauri kwace kanta daga jikin Didi duk da yana k'ok'arin k'ara matseta a jikinsa,
Doctor bai kalli su Abbu ba, gaba d'aya hankalinsa nakan Sanah,
dan koda yana duba Khulud gaba d'aya hankalinsa na wajen Sanah,
dan mugun tausayin ta yaji ya kama shi,
a hankali ya durk'usa kusa da ita yana murmushi,
ido kawai Sanah ta zuba mishi ta kasa cewa komai,
yace " Alhamdulillah babu abinda ya samu Uludin ki, gogon suma ne kawai tayi,
sai numfashinta dayake sneezing,
amma munyi mata allura mun saka mata Oxygen dan numfashinta ya dawo normal,
jikin Doctor d'in Sanah ta fad'a ta lumshe idanta hawaye na zubo mata,
"thank you so much Doctor,
dariya yayi yace " ki godewa Allah,
tace " Alhamdulillah,
a gadon tura marasa lafiya aka fito da Khulud d'aure da k'arin ruwa da Oxygen,
d'aki aka kaita, d'akin mai kyau akwai bed, sofa toilet & bathroom, wardrobe,
da sauri Sanah ta zauna a bakin gadon ta d'ora kanta akan k'irjin Khulud tana cigaba da kuka,
abin tausayi,
Mamu ce ta zauna ta kwana dasu.
Har washe gari Khulud bata farfad'o ba,
al'amarin dayayi masifar d'agawa Sanah hankali kenan,
ta rink'a kuka tana jijjigata Khulud tana kiran sunanta,
"please my Ulud ki tashi, dan Allah ki tashi,
karki mutu dan Allah, tana maganar cikin matsanancin kuka,
Mamu dake gefe zaune akan sofa cike da tausayin 'ya'yan nata,
ta mik'e a hankali ta nufi inda Sanah take kwance akan Khulud tana kuka tana kiran sunanta,
Mamu ta rungume su duka, kana tacewa " Sanah jeki alwala kiyi sallah ki rok'i Allah yabawa Khulud lafiya,
da sauri Sanah ta d'ago fuskarta dake cike da hawaye tace " Mamu idan nayi addu'a zata warke?
Mamu tace " Addu'a ai maganin komai da komai ce Sanah,
duk abinda ya damu musulmi koya shige masa duhu,
ko mutum ya shiga matsala da damuwa idan yayi addu'a ya rok'i Allah,
sai Ubangiji yayi masa maganin matsalarsa,
ya kuma yaye masa damuwarsa,
ya kawo masa mafita,
baki ganin 'yan kowanne addini suna addu'a wa abinda suke bautawa,
dan haka ki rik'e addu'a Sanah aduk halin da kike ciki,
idan kika dage da addu'a sai Allah ya kawo miki d'auki, ya shiga cikin lamuranki,
ki zama mutum mai zafin addu'a da addini, wallahi sai kinfi k'arfin komai da kowa dake duniya,
sai kin zama gagara badau, sai kin zama murucin kan dutse,
ko aljani da mugayen mutane sai kin gagare su,
Annabi (S.A.W) yace " الدعاء سيف المؤمنين,
Allah maji rok'on bayinsa ne,
mai kuma amsa addu'ar su,
musamman addu'a daga bakin yara k'anana wad'anda basu balaga ba,
cikin sanyin jiki Sanah ta mik'e tace " Mamu zanje nayi alwala nayi ta Sallah da addu'a bazan daina ba har sai my Ulud ta farfad'o,
murmushi Mamu tayi mata kana tace " yauwa good girl.
Alwala Sanah tayi ta d'auko prayer mat & Qur'an, hislin muslim a inda Mamu ta aje,
sallah tayi raka goma sallama biyar,
kana ta bud'e hislin muslim tayi addu'a sosai,
ta aje ta d'auki Qur'an ta fara karanwa a fili muryarta na rawa irin ta masu kuka,
Abbu, Didi da Juju suka shigo tare d'auke da food flask na breakfast,
tun daga bakin k'ofar shiga d'akin suka jiyo muryar Sanah tana karatun Qur'an cikin kuka,
akan Sofa Abbu da Didi suka zauna Mamu na zaune a bakin gadon Khulud,
bayan sun gama gaisawa, Didi ya kalli Sanah yace " aje karantun kizo kiyi breakfast,
bata ko kalli inda yake ba taci gaba da karatunta,
babu yadda Didi da Juju basu yi ta aje ta karya ba amma bata ko kalle su ba,
Didi da Abbu suka fita tare suka bar Juju da Mamu,
tun asuba Sanah ke karatu tana addu'a har akayi sallar azhur,
alwala kawai ta tashi tayi,
ta dawo ta cigaba da karatun Qur'an da addu'a,
haka ma da akayi sallar alasur,
sau biyu Doctors na shigowa suna ganinta,
duk wanda yayi mata magana bata kallansa balle ta amsa,
sosai Sanah ta burge Doctors da Nurses d'in dake shigowa ta kuma k'ara basu tausayi.
Da daddare Abbu da Didi suka shigo d'auke da basket na abinci,
lokacin Doctor da Nurses sun shigo duba Khulud,
da sauri Didi ya turje ganin yadda suka bar Sanah tun safe haka suka dawo suka same ta,
Didi yace " Sanah lafiyarki kuwa?
Bata kalle shi ba ta cigaba da karatunta tana kuka,
Doctor ya kalli Dide da Abbu, Juju & Mamu yayi murmushi yace " wallahi duk inda kayi yau a cikin Hospital d'in nan maganar Sanah kawai akeyi,
Abbu yace " ikon Allah,
Juju tace " duk yau fa ko ruwa bata sha ba,
duk suka yi jugum-jugum,
Doctor yayi musu sallama ya fita cike da sha'awar halayyar Sanah,
_Ni ko nace hmmmm Doctor baka san Oga Sanah bane, ruwa ne ya k'arewa d'an kada, kaje ka tambayi Sir Moli wacece Sanah Hamraz_
Allah maji k'oron bayinsa,
wajen 11:00pm na dare,
Doctor ya shigo ya duba Khulud,
bayan ya gama dubata ya kalli inda Sanah ke zaune har lokacin tana addu'a,
yayi murmushi ya bud'e baki zayyi magana,
suka ji muryar Khulud na salati,
sai da tayi salati sau uku a jere,
kana ta kira sunan Allah, sai kuma tad'anyi shiru,
duk d'akin aka rasa wanda zayyi magana balle kwakkwaran motsi,
har shi kanshi Doctor d'in, da k'arfi suka ji Khulud tace...............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣4⃣
Da k'arfi suka ji Khulud tace " My Sanah!!!!,
Sanah dake ta faman karatu bata san wainar da ake toyawa ba,
sai jin muryar Khulud datayi tana kiranta,
da sauri ta juyo da kanta ta kalli inda Khulud ke kwance,
dan ta tabbatarwa da kanta abinda kunnawanta suka ji ye mata,
ganin da gaske Khulud d'ince yasa ta yin sujdul shukru ,
tana hawaye ta shiga gode ma Allah,
da sauri Mamu ta nufe ta tana kiran sunnata,
"Khulud kin tashi?
Taba ko kalli inda Mamu take ba,
gaba d'aya hankalinta yana wajen Sanah,
Doctor tsaye yayi yana kallan ikon Allah,
yadda suka yi ta faman k'ok'arin ganin Khulud ta farfad'o amma abu ya gagara,
amma sai gashi lokaci d'aya ta farka,
Abbu ya k'arasa inda Khulud ke kwance tana kallan Sanah ,
ya shafa kanta yana murmushin jin dad'i yace " Alhamdulillah Khulud kin tashi?
Kwata-kwata hankalinta baya kan gaba d'aya jama'ar dake wajen,
balle ma tasan abinda suke