Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
suka dawo,
dukkan su sunyi shiru cike da tsantsar kewar gida,
ganin haka yasa Sanah tashi ta cire hijab d'inta taci d'an mara dashi a k'ugunta,
ta hau saman seat ta fara kid'a,
abinka da wad'anda ke cikin kewa,
ga kuma k'uruciya na damunsu,
ai ko suka zage suka shiga tik'ar rawa da wak'a, while Sanah naci gaba da kid'an tana rawa daga zaune saman seat,
Khulud na zaune bata ko motsa ba, tana ta dariya,
Sir Moli na SS2 yana teaching,
yaji kid'a na tashi, his face with surprise,
saboda yaune first time daya soma jin maka makamancin haka a school d'in,
a hankali tako ya biyo inda yake jin sautin na tashi,
jin sautin na fitowa daga JSS side,
yasa mamkinsa k'aruwa sosai,
bai tsinke ba sai da ya ganshi a k'ofar JSS1 class,
a hankali ya shiga, ganin Sanah ta tara yara tana yi musu kid'a da wak'a,
yasa shi tsayawa cike da tsantsar mamaki yana kallan ikon Allah,
a ransa kuma yana mamakin wannan wacce irin yarinya ce?
Sosai kid'a da wak'a ya d'auki zafi,
kwata-kwata hankakin su Sanah bai kai gare shi ba,
ya kai a k'alla wajen 15 minutes a tsaye yana kallan yadda Sanah ke zazzaga fitsara,
while Khulud na zaune a nutse tana bin su da kallo tana murmushi,
juyowar da Sanah zata yi idanta ya sauka akan Sir Moli dake tsaye hard'e da hannuwasa a k'irji,
cikin wani irin mugun zafin nama ta yunk'ura da niyyar guduwa,
yayi wuf ya rik'e ta, sai lokacin hankakin sauran ya kai ga Sir Moli,
kowacce ta koma seat d'inta ta zaune a matuk'ar tsorace jikinsu sai kerrrrma yake,
ajin yayi tsit,
tsawa ya daka musu " ku dan kan uwarku tun da kuka zo makarantar nan kun tab'a ganin anyi kid'a?
Duk suka ce " a'a,
" wa yasa ku kid'a da rawa yanzu dan ubanku?
Jikinsu na kerrrrma suka ce SANAH HAMRAZ,
"Idan tace ku shiga wuta zaku shiga?
"A'a,
" wallahi daga yau kuka kuma yi mana kid'a school sai naci kan uwarku,
yayi maganar while yana rik'e da Sanah gam a hannunsa,
tuni Sanah ta soma kuka, jikinta sai kerrrrma yake,
gaba d'aya tsoro ya gama cika mata ciki,
ji take kamar ta saki fitsari,
Khulud na zaune inda take cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar fargaba,
kuka kawai take dan tasan yau Sanah ta shiga ukku,
a fisace ya fita da Sanah, Khulud tayi saurin mik'ewa tabi bayan su,
jin taku a bayansa yashi juyowa,
tsayawa yayi cak ya zubawa Khulud ido,
" ke koma, yayi commanding nata,
shiru tayi tana kuka batare data motsa ba,
ya daka mata tsawa "ke dan uw.....
kasa k'arasawa gazin ta yayi, idansa ya runtse da k'arfi, kana ya bud'e yace " ki koma,
cikin kuka Khulud tace " please Sir kayi hak'uri, tare mukayi laifin ni da ita,
ba ita kad'ai ce tayi ba,
Sanah tayi saurin cewa " no Sir banda ita, ni kad'ai ce nayi laifin,
kafewa Khulud tayi akan harda ita,
while itama Sanah ta kafe banda ita,
kallan Khulud yayi yace " this is the last time da zance ki koma class,
Sanah tace " my Ulud idan baki san nayi fushi dake to ki koma,
tsawa ya daka mata "ke dan ubanki ubanwa yasa bakin ki,
shegiya 'yar iska fitsararriya,
yayi maganar yana matse hannunta dake cikin nashi,
kamar zai karyata,
tsananin azaba ne yasa Sanah sakin gigitaccen kuka,,
tana tsallen wuya,
cigaba da tafiya Sir Moli yayi rik'e da Sanah a hannunshi,
Khulud ta tsaya a inda suka barta tana kuka,
dan yadda taga idanshi, da yadda yake jan Sanah kamar zai b'alla ta,
yana tafiya a zafafe kamar mahaukaci tasan yau sai buzun Sanahrta..................... .
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣1⃣
Har cikin office d'insa ya shigar da ita,
"kneeling down, ya fad'a a tak'aice,
jikinta na rawa ta d'urk'usa bisa gwiwowinta,
zama yayi akan sofa, had'i da k'ura mata ido kusa 10 minutes batare dayace komai ba,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya,
yace " ke wacce irin yarinya ce, mai taurin kai?
Shiru tayi bata ce komai ba,
"na dad'e ina tunanin halayya da d'abi'unki,
me yasa baki jin magana?
"Dan ubanki ke 'yar bidi'a ce?
Kai ta girgiza masa, yace " ida kika kuma girgiza man kai sai na kifa miki mari,
shegiya bakin magana nafiki?
Da sauri tace " a'a,
"ah gidan ku akwai club, ko kuna zuwa yawan club?
"A'a tace, tana cigaba da kuka,
"to shaid'aniya ce ke, ko shad'aici yasa ki yin kid'a?
"A'a ta bashi amsa tana kuka,
ganin yadda take kuka yasa shi cewa " dukanki nayi?
"A'a,
" to uban me kike yi ma kuka?
"Bakomai ta fad'a tana goge hawayenta,
"yanzu dan ubanki bidi'a kika san kawo mana makarantar, ko so kike ki lalata mana yara,
ki kangarar dasu kamar yadda kike kangarariya,
ko irin taki fitsarar kike san koya musu?
"A'a, dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
"shegiya kullum maganar ki kenan,
"Allah da gaske nake, ban k'arawa,
" 'a'a ai dole kema ki d'and'ana dukan Moli,
ya fad'a yana mik'ewa, direct kan table ya nufa ya d'auki dorinar da yake duka da ita,
(bulala),
Sanah na ganin ya d'auki bulala ta mik'e tsaye a kid'eme tana yarfa hannunta,
kuka ta fasa masa sosai,
"please kayi hak'uri Allah ban k'arawa,
tayi maganar still tana kuka.
Nufo ta yayi gadan-gadan rik'e da zafgegeyar bular a hannunsa,
baya tayi tana yarfa hannu, dan gani take idan ya dake da bulalar hannunsa,
mutuwa zatayi,,
cikin kuka tace " Allah ban san duka, idan ka dokeni mutuwa zanyi,
"baki san bugu amma kike iskanci da fitsara?
Yayi maganar while yana takowa gare ta,
"Allah na daina ban k'arawa,
"k'arya kike,
"Allah da gaske ban kumawa,
dan Allah karka dokeni, tayi maganar tana shaking head d'inta,
"ke kima yi min shiru dan wallahi sai na dake ki,
gwara ma ki motsu na dake ki huta,
jin ya rantse yasata increasing cry volume d'inta,
cikin sanyin murya tace " yanzu duka na zakayi?
Yace " kwarai kuwa ko zaki hana ne?
"A'a, amma dan Allah kayi min a hankali ba mai zafi ba,
"tab yau nake ganin zunzurutun rainin wayo,
wato sai ma kin ban instruction d'in yadda zan dake ki?
A'a, zata kuma yin magana taji saukar bulala ajikinta,
da k'arfi ta saka gigitaccen kuka,
lokaci d'aya ta rud'e ta kid'ime ta fita fita daga hayyacinta,
ta zama kamar mahaukaciya sabon kamu,
saboda tsabar tud'ewa ta cire hijabin jikinta tayi cilli dashi gefe,
bata gama hucewa ba, ya k'ara zuba mata d'aya,
zillo ta fara yi tana tsalle,
ya kuma zuba mata biyu a jere,
durk'ushewa tayi a k'arasa tana murk'usu da juye-juye,
dan kwata-kwata Sanah bata k'aunar abinda zai tab'a lafiyar jikinta koyaya ne,
bata san duka,
duk abinda tasan muddin tayi za'a dake taba yi,
idan ko taji ciwo kota yanke, duk k'ank'antar ciwon an shiga uku ranar a gidan,
dan ta rink'a tsalle da ihuun kuka kenan,
gata da shegen san jiki kamar mage,
yanzu zata lafe a jikin mutum,
a gida shiyasa tafi shiri da Aarib dan kullum tana jikinsa,
idan kaga Sanah ta zauna ita kad'ai to babu mutum ne a kusa da ita,
amma muddin akwai mutum duk k'ank'antarsa koda ta girmeshi sai ta lafe a jikinsa,
Sanah kam akwai san jiki da shegiyar shagwab'a,
tasan darajar jiki da lafiyarta sosai,
sai dai akwai bakin tsiwa da fitsara,
gata masifaffiya dan mafad'aciya sosai,
uwa uba kuma bak'ar zuciya,,
jikinta tabi da kallo taga duk inda bulalar ta sauka yayi ja,
wajen duk yayi rud'u-rud'u,
yayi jajir kamar garwashin wuta,
shima jikin nata ya kalla, yaga wajen yayi mugun yin jajir,
ganin ya d'aga hannunsa zai k'ara zuba mata,
yasa ta mik'ewa da sauri ta rik'e hannunsa da k'arfi,
tana tsalle "dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa, tayi maganar cikin gigitaccen kuka,
bin jikinsa da ta rirrik'e shi yayi da kallo,
hannunta d'aya na rik'e da hannunsa wanda ya rik'e bulalar,
d'aya hannun nata kuma ta cukuikuye shi ta rik'e shi gam,
ta shige jikinta ta rungume shi yadda bazai iya dukan ta ba.
K'ok'arin kwace kansa ya fara yi,
amma ina Sanah tayi mishi mugun rik'o,
jin zai kwace kansa yasa Sanah zubewa k'asa had'i dayin ihuuuu,
da k'arfi kamar yadda taga masu aljanu nayi,
ta zub'e k'asa wanwar,
tana k'ifk'ifta idanu, kamar gaske,
idan ka ganta saika rantse da Allah aljannun gaske ta tayar,
da sauri Sir Moli ya ja baya, amma babu alamar tsoro ko firgice a tattare dashi,
ganin yadda take harba k'afa tana yarfa hannu kamar mai farfard'iya ya sashi fita da sauri yayi waje,
Sanah na ganin ya fita ta mik'e da sauri ta dira ta window tayi hostel,
anan ma tabar hijabinta,
yarinya Sir Moli ya aika kira masa Halan da Khulud,
sannan yayi alwala ya shiga Masjid ya d'auko Qur'an,
at the same time Halan da Khulud suka k'arso,
"ku biyo ni, yace a tak'aice,
jikin su kerrrrma suka bi bayansa,
office d'insa ya shiga kai tsaye rik'e da Qur'an,
ganin babu Sanah babu dalilinta,
yashi yin tsaye sororo,
kan sofa ya zaune gami da dafe kansa,
cikin ransa yana mamakin yadda tayi yanzu kamar gaske,
dan shi tsakanin sa da Allah ya yarda da gaske ta,
a hankali suka shigo, suka tsuguna gefe jikinsu na rawa,
zaton su ko Sanah ta jawo musu wani abun kuma,
kallan su yayi kana,
yace " zan tambaye ku tabbatar kun gaya man gaskiya,
dan idan na bincika naga k'arya kuka gaya man,
wallahi sai naci ubanku,
"to suka ce cikin fad'uwar gaba,
" Sanah nada aljanu?
Ya tambaye su gami da kafe su da ido dan yaga reaction d'in su,
kallan juna Halan da Khulud sukayi cike da mamaki,
baki suka had'a wajen cewa "aljanu kuma wanne iri?
" Tambayar ku nayi, ku ban amsa bawai ku maido min tambaya akan tambaya ba,
Halan data gane abinda ya faru,
tayi k'asa fakai tana b'oye dariyarta,
Khulud zatayi magana Halan tayi saurin cewa " a'a, gaskiya tunda muke da ita bata tab'a tada aljanu ba,
amma bamu sani ba ko tana da su ko kum.......
" Ba doguwar magana na tambaye ku ba,
abinda na tambaye ku Sanah tana da aljanu eh ko a'a?
K'asa Khulud tayi da kanta tace " a'a gaskiya bata dasu,
duk wanda ya gaya kama k'arya yake ba gaskiya ya fad'a maka ba,
"good yace, yana mik'ewa ya fita batare daya ce komai ba,
yana fita Halan ta kalli Khulud tace " me kuma ya faru?
Tass Khulud ta fad'awa Halan duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
ajiyar zuciya Halan tayi tana kallan Khulud tace,
"inaga fa k'aryar aljanu tayi masa danta kwaci kanta,
ido Khulud ta zaro tace " what! aljanun k'arya ta tayar mishi?
Halan tace " bani da tabbas amma ina tunanin hakan,
dan nasan halin kayana,
ajiyar zuciya Khulud ta sauke cike da tsoro,
Sir Moli na fita direct Hostel get yaje da kansa ya tsaya k'ofar shiga,
ya tura wata yarinyar kiran head girl,
bata jima ba suka dawo tare, a tak'aice yace " duk inda Sanah Hamraz take ki nemo min ita yanzu,
yayi maganar yana gyara tsaiwar shi,
"Ok Sir, ta amsa, tana mik'ewa ta koma cikin hostel,
Sanah na dirawa ta window tayi hostel dan tasan ba damar Sir Moli ya shigo hostel kai tsaye,
tun daga k'ofar room ta fara kwalawa Halan da Khulud kira,
taji shiru, tana k'ok'arin jiyawa head girl ta isa,
batayi mata magana ba ta rik'e hannunta,
Sanah tace " Malama lafiya, zaki zo ki rik'e ni kina ja ba wani bayani?
"Kallanta Head Girl tayi cike da mamakin irin maganar da Sanah ta fad'a mata,
amma sai ta dake tace " in munje can kya gani,
tana jin haka ta gane sak'on Sir Moli ne,
dan haka ta fara k'ok'arin turjewa,
juyowa Head Girl tayi tace " wallahi zansa a d'aukar man ke aka kaiki idan baki tsaya ba,
baki ta turo had'i tana cewa " sai kace wata dabba ko wani kaya,
bata kula ta ba ta cigaba da janta,
HG na mamakin irin halin Sanah,
na rashin jin magana da taurin kai,
a ranta tace " hmmmm tun tana yarinya kafin ta balaga ta zama cikekkiyar mace ma kenan,
ina ga kuma idan ta girma, zan so ganin 'yan matancin yarinyar nan,
dan nasa akwai ganin ikon Allah,
suna isa Sir Moli ya damk'i hannunta yayi office da ita,
kwata-kwata babu alamar tsoro ko firgice a tattare da ita,
sai ma baki da taka buro tana harare-harare,
gami da gunguni, k'asa-k'asa,,
suna shiga office d'in ya saki hannunta ya zauna kan sofa,,
ganin Halan da Khulud a office d'in,
yasa ta runtse idanta da k'arfi,
ya kalle ta yace " sakin aljanun ne ya zo?
Ta bud'e ido tarr cikin nashi, ya mik'e yana d'aukar bulalar shi,
dan ya fahinci tana mugun tsoron duka,
tana ganin ya d'auki bulala ta zub'e k'asa tana tab'a baki zatayi kuka,
hannun ya d'ora akan lips d'insa,
yace " shhhhhhhhhhhh,
da sauri ta had'iye kukanta,
yace " kin san Allah idan baki san na doke ki toki kiran aljanunki suzo,
kuka ta soma tana cewa " Allah bani da aljanu dama k'arya nayi maka danna kwaci kai na,
dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
"shegiya ga tsoro ga iskanci da fitsara,
ai 'yan iska fitsararru masu taurin kai da zafin zuciya basu saurin saduda,
ban hak'uri wuya yake yi musu,
"ni dai dan Allah kayi man hak'ura, Allah na daina,
"ba yanzu kika gama bada wani hak'urin ba?
"Amma few minutes tsakani kika kuma yin wani laifin,
cikin kuka tace " please kaban last chance yanzu,
idan na kuma yin laifi kayi man koma miye,
wallahi I promise ban k'ara yin laifi harna ban makarantar nan,
" are you sure you promise?
"Yes Sir, Allah idan na kuma kayi min komai kaga dama,
na yarda na d'auka, duk abinda kaga damanyi man kayi man,
murmushi yayi had'i da cewa " good, and keep it in your mind,,
I know one day you will pay for your promise,
kai ta gyad'a masa,
k'ura mata ido yayi wajen 10 minutes yana kallanta,
kana yace " tashi kije while idansa na kanta,
har ta kai bakin k'ofa, yace "Sanah cikin sanyin murya ya kira sunnan nata,
cak ta tsaya jin karo na farko a rayuwarta ya kira ta da real name d'inta,
a hankali ta juyo tana kallanshi ido cikin ido,
yace " kada ki tab'a raina matsayin tsoro,
lalle ki martaba matsayin tsoro,
wad'anda basa jin tsoro rashin tsoron su yakan jawo musu walaha da masifa, a rayuwa,
murmushi tayi tace " ya zaka ce bana jin tsoro Sir?
" Bayan yanzu ma ka gani da idanta,
yace " ni dai na fad'a maki, shawara ce na baki, nasan kuma ko gaba zata yi maki amfani,
murmushi ta kumayi tace " thank you Sir,
ido kawai ya zuba mata har suka fita,
while Halan na kallan su, deep down kuma tana cike tsantsar mamaki,
tana sak'e-sak'e kala-kala a ranta,
komawa kan sofa yayi ya kwanta had'i da lumshe idansa,
Bayan sun koma hostel sosai Halan tayi musu fad'a akan shiga case d'in teachers,
ta k'ara da basu shawarwari,,,
sosai jikin su yayi sanyi, Khulud ta kalli Sanah tace " please ki dai na kinji?
"Allah kwata-kwata ban san yadda yake yi miki,
tayi maganar wahaye na gangaro mata,
da sauri Sanah ta tashi daga inda take zaune ta koma kusa da Khulud,
tasa hannu tana goge mata tears d'inta,
itama kwalla na taruwa a idanta,
Khulud tace " please my Sanah karkiyi kuka,,
kukanta ta had'iye kana tace " to please kema karkiyi kukan kinji my Ulud,
wallahi bana san kukanki, bana k'aunar na ganki cikin damuwa,
ido Khulud ta zuba mata tana kallan yadda duk ta marairaice saboda tana kuka kawai,
cikin sanyin jiki da murya Khulud tace " my Sanah idan na mutu ya zakiyi?
Sosai Sanah ta zazzaro ido waje kamar zasu fad'o k'asa,,
tace " please ki bar wannan maganar,
inba so kike ki tada min hankali ba,
cikin sanyi Khulud tace " my Sanah kin san dukkan mai rai mamaci ne,
dole dukkan mu sai mun mutu,
sai mun d'and'ani zafin da rad'ad'in mutuwa,
ni dai abinda nake so idan na mutu ki rink'a yi man addu'a koyaushe,
ki zama mai sanyin hali, mai hak'uri da kawar da kai please,
a d'an zafafe Sanah tace " kina san tada min hankali ne?
Khulud tayi nodding kanta,
Sanah tace " ki na san na kafa miki kuka tun daga yanzu har safe?
Khulud tayi dariya tace " a'a Oga rigama,
tace " to kibar maganar nan please,
Khulud na dariya tace " na bari,
kasancewar wannan shine 3rth term, a wannan term d'in ana mugun repeating,
dan daga shi sai 1st term JSS2,
yasa Sanah da Khulud dagewa da karatu sosai baji ba gani,
Sanah da Khulud na tafiya, zasu koma hostel,
daga area class's,
Khulud ta kalli Sanah tana zaro ido had'i da ja baya,
Sanah ta kalle ta tace " lafiya?
Tayi maganar tana matsawa jikin Khulud,
da sauri Khulud ta ja baya tana kallan Sanah a tsoroce tana nuna mata kanta,
cikin tsoro Sanah tace " me?
Khulud tace "k'adangare, a razane Sanah ta saki k'ara tana cire hijabin jikinta,
tayi cilli dashi,
sosai Sanah ke tsalle tana ihuuuuuu,
Khulud ta kalle tana dariya while tana ja baya,
tace " wasa nake yi,
da gudu Sanah ta bita, tana dariya,
itama ta kwasa da gudu tana dariya,
suka shiga zage wajen, cikin matsanancin farin ciki,
sai da suka gaji da zagaye wajen kana Sanah ta rik'e Khulud,
rungume juna sukayi suna dariya cire da so da k'aunar junansu,
abin sha'awa.
_MAFARIN K'ADDARA_
Ranar Saturday dukkan su sanye cikin game were,
suka nufi filin game suna tafe suna wasa da dariya,
Sanah ta kalli Khulud tace " haka nan naji gaba na, na fad'uwa,
Halan tace "