Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
yi,
gaba d'aya hankalinta yana kan Sanah,
a hankalinta Sanah ta d'ago daga sujdar ,
ta tako inda Khulud take,hawaye na cigaba da zubowa daga idanta,
ta k'urawa Khulud ido,
da k'arfi ta fashe da kuka gami da fad'awa jikinta,
itama Khulud kukan ta saka a hankali tace " my Sanah ki daina kuka,
tayi maganar dakyar,
murmushi Doctor yayi kana ya k'araso bakin gadon,
idansa nakan su,
yace " Mrs Cry zan duba ta,
yayi maganar cikin tsokana,
baki Sanah ta turo kana tace " tafa warke,
cikin dariya yace " to fa Doctor Sanah,
wato ke har kin san ta warke ko?
Bata bashi amsa ba,ta kalli Khulud tace " ai kin warke ko my Ulud ?
Dariya itama tayi tace " eh my Sanah babu abinda ke damuna,
Doctor ya kalli Sanah yace " naga alamar dai baki san ta warke sosai yadda zaku koma gida da wuri ko?
" Ina so mana ta fad'a cike da k'uruciya,
yace " to idan kina so ki bari a duba ta,
batare data ce komai ba,ta matsa ta koma gefe ,
aune-aune da d'an gwaje-gwaje yayi,
kana ya d'ago kai ya kalli Khulud yace " akwai inda ke miki ciwo?
A'a, ta bashi amsa,
"babu inda ke miki ciwo ko zafi,
ya kuma tambayarta idansa na kanta ,
dan ya tabbatar da abinda zata fad'a,
" eh ta fad'a itama tana kallanshi,
yace " kiyi tunani dai kinji our Khulud yayi maganar cikin wasa,
dariya tayi,kana ta d'anyi shiru alamar tunani,
"babu ,ta kuma bashi amsa,
yace " kin tabbatar da gaske babu abinda ke damunta ko inda ke yi miki ciwo?
"Karki fa kiyi amfani da maganar our Sanah datace babu abinda ke damunki,
murmushi tayi kana tace " Allah babu abinda ke damuna,
sai baki na danake jin babu dad'i,
sai kuma jiki na dayake man ciwo,
idan shi na kanta yace " bakin ki rashin apartheid ne,
jikin ki kuma dad'ewar da kikayi a kwance ne yasa shi yin tsami,
da our Sanah tayi miki wanka da ruwan zafi zaki warware,
yayi maganar cikin tsoka na,
dariya duk sukayi batare da sunce komai ba,
yace bayan nan fa?
Tace " babu komai,
juyawa yayi wajen su Abbu dake tsaye suna kallan su fuskokin su d'auke da murmushi,
yace " Alhamdulillah, Allah maji rok'on bayin sa ne,
abinda muka kasa yi acikin 48hrs ,
gashi Sanah tayi a cikin yini d'aya kawai,
Allah ya amsa addu'arta,
gaskiya ko ni anan na k'aru,
k'aramar yarinya ta tunatar dani fahimmanci da amfanin addu'a,
ta nusarshe ni komawa ga Allah,
da kai kuka ga Ubangijin talik'ai mai kowa da komai,
gaskiya ne babu abinda ya gagari addu'a koya fi k'arfin Ubangiji,
wannan kad'ai ya isa ya nunuwa mutum akwai Ubangiji,
ya isa ya nunuwa wad'anda basu yarda akwai Ubangiji ba,,
cewar akwai mak'agin kowa da komai.
Ya k'arasa maganar yana kallan Abbu ido cikin ido,
murmushi Abbu yayi kana yace " Alhamdulillah mun godewa Allah,
Doctor yayi murmushi yace " kuma da gani akwai so da k'auna mai k'arfi a tsakanin yaran,
musamman yadda Sanah ta d'aga hankalinta,
tak'i ci da sha ,
da kuma yadda itama Khulud tana farfad'owa babu sunan wanda ta fara ambata sai na Sanah,
kad'ai ya isa ya tabbatarwa mutum suna mugun san junan su,
yayi maganar idansa na kan Khulud da Sanah,
cike da sha'awar su,
murmushi Didi yayi cikin jin dad'in yabon da Doctor yake yiwa yaran su,
yace " mun gode sosai Doctor,
Allah ya saka da alkhairi Ubangiji yabar zumunci,
Allah ya albarkaci iyali,
" amin ya Allah,ya amsa kana ya d'ora da cewa " ai babu iyalin har yanzu,
muna dai nema ya k'arasa maganar yana shafa kai idansa nakan Sanah,
murmushi Abbu yayi yace " to madalla Allah ya bada nagari,
"Amin, ya kuma cewa idansa nakan Sanah,
har ya juya zai fita Mamu ta kira sunanshi " Doctor,
a hanlaki ya juyo yana kallanta had'i da amsawa "na'am,
cikin murmushi Mamu tace " zuwa yaushe za'a sallame 'yar ta wa?
Dariya yayi kana yace " ko zuwa gobe ma in sha Allah,
dan babu sauran abinda yake damunta,
"Allah ya kai mu,Mamu tace,
ya amsa da "Amin,
ya d'ora hannunsa akan handle d'in k'ofa ,
Sanah tace " thank you so much Doctor,
juyowa yayi yana murmushi yace " don't mention it,
murmushi tayi a tak'aice tace " ai dole nagode ,
"saboda me?
Yace idansa na kanta,
" besouse you fulfilled your promise ,
dariya yayi kana yace " it's my pleasure,
suka yi dariya su duka,batare da sun ce komai ba,
Sanah ta mayar da kallanta ga Khulud tace " hankalina ya tashi sosai,
tayi masa cikin sanyi da karaya,
"karki damu muna tare har rai da mutuwa in sha Allah,
Khulud ta fad'a tana dariya,
Sanah tayi rau-rau da ido alamar tana san yin kuka tace " Allah nayi mugun tsora ta fa,
na gama sawa rai na...,
sai kuma tayi shiru had'i da k'urawa Khulud ido hawaye na zubo mata,
Khulud tayi rolling idonta " please my Sanah ki dai na kukan kinji?
Idan ba so kike na koma jinyar ba,
tayi fad'a tana gogewa Sanah hawayen dake zubo mata,
murmushi Sanah tayi tace " ke kyama so ma komawa,
Khulud tayi dariya,
d'an shiru Khulud tayi na wajen 5 minutes kana tace " my Sanah Sir Moli,
tayi maganar can k'asan mak'ogwaranta,
baki Sanah ta d'an tab'a kana tace " kamar ya Sir Moli?
A hankali Khulud tace " yana ina?
Cikin masifa Sanah tace " bangane yana ina ba?
"Ko an fad'a maki yawo nake dashi ko kuma shi d'an gidan mu ne ,
dazaki tambaye ni inda yake?
Cikin sanyin murya Khulud tace " kawai na tambaye ki ne,
saboda.......
sai kuma tayi shiru had'i da sunkuyar da kanta k'asa,
ido Sanah ta k'ura mata bata ko k'iftawa,
zatayi magana Mamu tace " hala an manta damu ko?
Da sauri Khulud ta d'ago ido tana mik'awa Mamu hannu tace " lah ba haka bane Mamu My Sanah ce ta d'auke man hankali,
Mamu tayi murmushi tana cewa " ai naga alama,
tayi maganar tana zama kusa dasu،
cikin sanyin murya Khulud ta gaida Mamu,Juju,Didi da Abbu duk suka amsa Abbu yana shafa kanta ,
cikin so da k'auna,
Abbu ya tambaye ta abinda take san ci ,
ta kalli Sanah tace " My Sanah me zamu ci?
Sanah da har lokacin idanta yana kan Khulud ta k'ura mata ido,
tun tambayarta Sir Moli datayi,
ta d'anyi guntun murmushi kana tace " anything,
tayi maganar a tak'aice,
Khulud ta kalli Abbu tace " nasan babu abinda my Sanah tafi so kamar shawarma da gashashshan kifi karfasa,
da kuma ice cream,
Abbu ka siyo kana su,
"to yanzu kuwa, Abbu yace ya fita,
Mamu ta mik'e ta had'awa Khulud ruwan wanka mai d'umi,
tayi wanka da brush,ta kuma rama sallolin da ake binta,
tana idarwa Abbu ya shigo ya mik'awa Sanah ledojin su ,
ya mik'awa Mamu nata, kana ya mik'awa Didi da Juju nasu,
suka amsa suna godiya ,Didi yace " wannan sauran ledoji ukun fa ,ko na amaryar ne?
Yayi maganar cikin zolaya,
" wacce amarya na iyayen mu ne,
Abbu ya fad'a yana dariya,
Didi yace " kai dai ka fad'i gaskiya ko kana tsoro ne?
Yayi maganar yana kallan Mamu,
murmushi Mamu tayi tace " tsoran wa zaiji?
Duk suka saka dariya,
hankalin Sanah da Khulud nakan Ice cream, shawarma da gashashshen kifin su,
Abbu yace " to ni fa zan tafi naga 12:20 ya fad'a yana kallan agogon hannunsa,
Didi yace " muna ai tafiyar zamu yi,
sukayiwa su Mamu sallah suka fice.
Washe gari da safe k'arfe 8:30am na safe Doctor ya shigo sanye cikin cot ,
fuskarsa d'auke da fara'a ,
ya kalli Sanah yace " good morning Mrs Cry,
"no ka bari na gaida ka,
tunda nice k'arama ,
murmushi yayi yana k'ara jin yaran na burge shi,
saboda hankali da nutsuwar su,
har k'asa Sanah da Khulud suka durk'usa,
had'i da cewa ina kwana?
" Lafiya lau,
ya amsa yana murmushi,
"an tashi lafiya?
" Alhamdulillah ya basu amsa،
duba Khulud yayi sosai yaga she is normal ,
babu abinda yake damunta,
dan haka ya basu sallama,
sosai Khulud da Sanah sukayi mishi godiya,
Mamu ta kira Juju ta sanar da ita an sallame su,
kar ta sha wahalar kawo breakfast,
Juju tace " ok badamuwa zanyi na naje muku idan kun k'araso sai kuyi break d'in a gida,
Mamu ta amsa mata da " to,
tana kashe wayar ta kira Abbu,
yayi picking bayan Mamu ta gaidashi ,
ta sanar da shi an basu sallama ,
yace " ok dama ganin nan na kusa k'arasowa,
"ok Mamu tace ,kana ta kashe wayar,
Abbu na k'arasowa ya nemi Doctor ya kuma yi mishi godiya sosai,
kana ya kwashi su Khulud suka yi gida,
kafin suje gidan har Mamu tasa 'yan aiki sun shirya breakfast akan dinning table ,
sai da suka karya kana suka shiga part d'in kakanin su,
saboda dakyar Abbu ya basu hak'uri suka zauna a gida ,
yayi ta kwantar musu da hankali yana lallashin su,
sannan suka hak'ura,
dan tuburewa sukayi sai an kai su Hospital d'in su duka,
bayan sun dawo suka shiga bedroom yin bacci.
_BAYAN SATI BIYU_
Sosai Khulud ta warke garau ,
dan har sun koma islamiyya,
ganin haka yasa Abbu kiran su parlor,
bayan sun zo ya kalle su yace " to yaushe za'a koma makaranta?
Kafin Khulud tayi magana Sanah tayi saurin cewa " Allah ni dai Abbu ban san boarding school,
a samar mana day school kawai mu koma,
amma ni ban k'ara yin boarding,
na gama yin boarding har abada,
Khulud tayi saurin kallanta dan ba haka taso ba,
dan ita taso su koma Computer Girls Secondary School Roni,
amma dole ta hak'ura tunda My Sanarta bata so,
ita kuma duk abinda Sanah bata so ta barshi har abada,,
saboda bata k'aunar duk abinda zai shiga tsakanin su ko ya raba su,
shiru tayi batare data ce komai ba,
ganin yadda tayi shiru yasa Abbu cewa " Khulud ko kinfi san boarding d'in ne?
Yayi maganar idanshi na kanta,
murmushin yak'e tayi tace " a'a Abbu nima ban san boarding d'in a canja mana kawai,
" wacce kuke so?
Abbu ya tambaye su,
duk suka ce " babu,kawai ka zab'a mana kowacce,
"ok ku tashi kuje,
Abbu ya fad'a,
washe gari Abbu ya aika Aarib da Ziyad suka amso musu transfer,
bayan kwana uku Abbu ya samu musu admission a Momy speed international School,
makarantar private School ce mai shegen kyau,
ranar Monday suka fara zuwa,
Ziyad ne yake shaidawa su Sanah Halan sunyi candy tun last week,
aiko suka addabe shi akan sai ya kai su wajenta sun ganta,
dole tasa ya kai su dan itama ta dame shi da maganar su,
yana yin parking suka fito da gudu suka shiga gidan,
Halan na zaune a parlor tana yankan salad taga su Sanah,
cike da murna da farin ciki ta rungume su,
dan kwata-kwata Ziyad bai sanar da ita zuwansu ba,
Halan ta kalle su tace " I really misses you so much my dears ,
dariya suka yi kana suka ce " we miss you too ,our Aunty ,
Sanah tace " Allah Aunty Halan kullum sai munce Yaya ya kawo sai yak'i,
yau ma dakyar ya kawo mu,
Halan tayi dariya tace " ni ma haka,har cewa nayi ya kai ni na gano ku amma ya k'i,
baki Sanah ta turo tace " aiko bamu komawa sai dai ya tafi shi kad'ai,
"yauwa My Sanah ku zauna anan,
Khulud tace " muna nan har sai randa zaki koma gidan mu sai mu tafi tare,
mahaifiyar Halan dake zaune kan sofa tace " aiko baku isa ba,
idan kuka zo kun zo kenan ban barin ku,
ku koma,tayi maganar cikin fara'a da sakin fuska,
kwata-kwata basu lura da ita ba,
sai da tayi magana,
cikin nutsuwa suka durk'usa har k'asa suka gaida ita,
ta amsa tana d'ago su,
wayar Halan ta fara ringing tayi saurin picking ,
yace " wato anga su Khulud an manta da ni ko?
" Lahhhh yi hak'uri Allah sun d'auke man hankali ne,
tayi maganar cikin shagwab'a,
mahafiyarta ta jefa mata uwar harara wanda tasa ta saurin mik'ewa tana dariya ta nufi bedroom d'inta,
tana shiga tace " ka sani na manta nayi picking gaban Nanan mu,
dariya yayi yace " ni dai ki fito ina waje,
"to tace ,fuskarta ta d'an gyara kana ta fesa perfumes masu sanyin k'amshi,
anan ya bar Sanah da Khulud,
sai dare ya dawo d'aukar su,
koda ya dawo k'in fitowa sukayi,
suka cewa Halan tace masa su sunzo kenan,
da Halan ta fad'a masa cewa yayi taje tazo dasu,
Sanah tace " Allah ko naje haka zan fad'a masa tayi maganar tana murgud'a baki,
daga bakin k'ofar sit room suka tsaya,
ya had'e fuska yace " muje ko?
Ya fad'a batare daya kalle su ba,
Khulud tayi gaba sumi-sumi ganin ya had'e rai,
dan har tsoro ya kamata ,
amma Oga Sanah sai ta shiga bubbuga k'afa tace " please Yaya ka barmu nan,
ido ya zaro yace " exam d'in da zaku fara next week fa?
Sanah tace " daga nan zamu rink'a zuwa ai,
yace " wazai rink'a kai ku?
Sanah tace " Aunty Halan mana,
ya zaro ido sosai ,kana yace " wacce Halan d'in,amma badai tawa ba ko?
Sanah tace " taka kuma Yaya ko ta mu,ko harka kwace mana ita?
Dariya yayi yace " a'a ,dan ya lura Sanah bata tsoran zare ido,
sai dakyar Sanah tabi Ziyad shima sai da yayi musu alk'awarin dasun gama exam zai kawo su,su zauna har ayi biki,
bayan sati uku da fara zuwan su Khulud school ,
aka fara 3thr term exam,
duk da a k'urarran lokaci su Khulud suka shiga school d'in su,
sai da suka yi matuk'ar bada mamaki dan Sanah ta d'auki 1st position Khulud second ,
a islmaiyya kuma Khulud ta d'auki 1st position Sanah second ,
dan dama Khulud tafi Sanah k'ok'ari a ismiyya,
suna dawowa gida suka tarar da duk 'yan gidan a parlor,
da gudu Sanah ta fad'a jikin Aarib ,
Zarfan kuma ya mashi result d'in su,
yana dubawa, Ziyad yace " meye kuma na dubawa kai da ka san na yadda suke zuwa?
" Ai dole a duba saboda sabuwar makaranta ce,
Mamu tace " to yanzu na nawa suka zo?
"Yadda dai suke,tayi murmushin jin dad'i tace " ai har abada ba'a canjawa tuwo suna,
Sanah ta kalli Ziyad tace " Yaya ya alk'awarin mu?
"Na me fa?
Ya tambaye ta,
baki ta turo tana buga k'afa tace " Yaya zaka fara ko?
" To ikon Allah,kin tab'a ganin an kama mutum da laifin dabai sani ba?
Khulud tace " Yaya kai fa kayi mana alk'awarin damun gama exam zaka kai mu gidan su Aunty Halan har a gama biki,
dariya yayi yace " yara ai yanzu an shiga Inconclusive,
dan haka kuma kun shiga inconclusive,
Sanah ta tab'a baki zatayi kuka Khulud tace " no please karki yi kuka ki bari muje idan yace bai kai mu nima sai ma tayaki kukan,
Sanah tayi saurin mai da kukan ,
duk suka zuba mishi ido suna jiran suji abinda zai ce su fara kuka,
"kambuuuu Ziyad yace yana dariya,
" wato tsabar rai nin hankali har mai da kuka ake yi ana jiran mai zance ko?
Duk sukayi shiru babu wanda yace masa k'ala,
ganin yadda duk suka kafe shi da ido,
yasa shi cewa " to ban kai ku,
aiko suka had'a baki suka saki kuka lokaci d'aya,
Aarib yayi saurin cewa " kuyi shiru please ni zan kai ku,
kamar d'aukewar ruwan sama suka yi tsit,
Ziyad ya kuma yin dariya,
Mamu tace " naga nan gidan ma bikin za'ayi,
kuma ai kamata yayi ku tsaya wajen Aroos (yayar Khulud wacce take bi),
Sanah ta zumb'uro baki,
Idrak angon Aroos (dayake auren zumunci za'ayi musu),
yace " au wato baku tsayawa ku taya tawa amaryar hidimar biki ko?
Sanah tace " ita ai bata san mutane,
tafi san komai nata tayi ita kad'ai,
Mamu tace " uwaki,Yayarki kike cewa haka?
Khulud tace " Allah Mamu haka take ,
shiyasa muma muke ja baya,bata da kirki gata da saurin dukan mutane da zagi,
Idrak yace " aiko sai na fad'a mata,
Sanah tace " ai halinta ne,ta juya ta kalli Aarib tace " Yaya kai yaushe zakayi auren?
Ido kawai ya kafe ta da shi batare dayace komai ba,
dole tasa su Khulud hak'ura da zuwa gidan su Halan dan biki uku za'ayi a gidan,
bikin Ziyad & Halan,
sai bikin Aroos & Idrak da bikin Zafran & Seenah,
Seenah 'yar mak'otan su,ce yarinyar mai hankali da nutsuwa kamar Aroos & Halan,
itama iyayenta mutanen kwarai ne,masu mutunci da kamala,
kamar na Halan.
satin biki na zagayowa aka shiga hidimar biki kowa ba zama yayi busy musamman Juju da Mamu,
ba wata bidi'a akayi sosai ba,
anyi yinin biki normal sai walima da wa'azi,
ranar Friday a babban masallacin juma'ar gidan sarkin kano bayan an idar da sallar juma'a millions mutane suka d'aura auren,
Halan & Ziyad
Aroos & Idrak
Seenah & Zafran,
a ranar kowacce ta tare a gidan ta dake Hard'o Family estate,
sosai mugun sabo da shak'uwa ta k'ura shiga tsakanin Halan da su Sanah,
suka kuma mai da hankali sosai akan karatun su.
_BAYAN SHEKARU 5_
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣5⃣
_BAYAN SHEKARU 5_
Tafiya suke sannu a hankali cikin nutsuwa kamar basu san taka k'asa,
sanye suke da uniform mai kalar peach color ,
da guntun hijab wanda k'irjinsu kawai ya rufe,
'yan mata guda biyu santala'sanatala,
san kowa k'in wanda ya rasa,
gaba d'ayan su kyawawan gaske ne ajin farko,
irin mata nan da zakaji ana kira da full option,
wato komai yaji, babu abinda zai k'ara d'aukar hankalinka a ajikinsu sai kalar fatar jikinsu,
wacce ita ba fara ba ba kuma bak'a ba,
wato chocolate color,kalar su tafi ta fararen mata kyau da tsada,
saboda fatar su tafi laushi da tsantsi,
duba nakai kan k'irjinsu naga na fulanin su tantsan-tantsan,
a hankali ya gangaro da ido na zuwa k'ugun su,
"masha Allah kawai na iya furtawa,
saboda sun wuce iya kar kyau da had'uwa,
matasan 'yan mata masu ji da kyau da k'uciya 'yan 16yrs,
daga bedroom d'in su suka fito,
cikin sauri da alama sauri suke yi,
cornflake naga d'aya daga cikin su ta d'eba takai bakinta ,
tana sauri ta kurb'i ruwan madarar dake gefe ajeye cikin glass cup,
wata dadtijiwar mata naji tace" SANAH bazaku tsaya kuyi breakfast bane?
Wacce aka kira da Sanah ta jiyo a hankali tana murmushin dayasa dimples d'in dake kumatunta lutsawa,
jerarrun fararen hak'uranta masu d'auke da siririyar wushirya suka bayyana,
hakan ne ya bani damar k'arewa faffad'ar fuskarta kallo mai d'auke da dogon hanci ,
da dara-daran idanu farare tass,
kalar kwayar idanta blue color,
badan a Nigeria na ganta ba da sai na rantse Pretty Zinta ce ,
domin babu abinda ya raba su ,
sai kalar fatar jikinta da lulu eyeball d'inta,
sai daga k'ugu tafi Pretty Zinta hip da fad'in k'ugu da cikar booms nesa ba kusa ba,
rolling lulu eyes d'inta tayi masu kamar tana jin bacci tace " no Mamu munyi late ,saura 2hr kawai mu shiga final exam,
Mamu tace " to kuma shine bazaku tsaya ku karya ba?
"Bayan naga kuna da sauran lokaci,
Mamu ta fad'a tana kallan Sanah,
d'an tsukakken bakinta mai d'auke pink lips ta turo tace " Mamu yau ne ranar Graduation's d'in mu,
shiyasa bana san muje a late,
Mamu tayi murmushi kana tace " au to cewa zakiyi duk murnar kammala karatun Secondary ne yau,
Sanah tayi dariya tace " ashe dai kin gane our Mamu,
daga yau bamu da fama da uniform,
Mamu tace " Khulud kema bazaki k'arya ba?
Wacce aka kira da Khulud na kalla ,
can k'asan mak'ogwaro na ,na furta masha Allahu,
Ubangiji yayi halitta anan,