Author : HAUWA A USMAN Category : Complete Novels
fara dube-dube,
da sauri Khulud ta k'arasa gabansa tace " please dan girman Allah kayi hak'uri ka tafi,
tattausan murmushi yayi mata yace " no badamuwa ki barta naga abinda zata iya,
Khulud tace " ni dai please ka tafi,
ta fad'a kamar zatayi kuka,
ya bud'e baki zayyi magana yaji saukar ruwan kwata a fuskarshi da jikinshi,
a hankali ya kalli jikinsa ya maiyar da kallansa ga Sanah,
da sauri Khulud tasa hannuwanta ta tushe bakinta,
had'i da zaro idanta waje cikin tsoro,
kafin yayi aune ta kuma d'ebo ruwan kwatar ta k'ara zuba masa, har a jikin motarsa,
abinka da mai hak'urin dabai iya fushi ba,
mutumin da bai san raini da wulak'anci,
take zuciyarsa tayi sama jikinsa ya d'auki kerrrma saboda tsabar b'acin rai,
kalar idansa ta koma pure red,
cikin tsuma Khulud tace " my Sanah meye haka?
Tace " oho ban sani ba abinda yayi ne akayi masa,
tayi maganar tana kallansa shek'ek'e,
cikin zafin rai ya kalle ta yace " ke ni kika watsawa ruwan kwata?
Tace " idan baka gani bane kake tambayata bari na tabbatar maka,
tayi maganar tana k'ok'arin k'ara d'ebo ruwan kwatar,
batayi aune ba sai jin saukar gigitattun marika kyawawa guda biyu tayi a jere,
yana shirin finciko ta Khulud tayi saurin shiga tsakiyarsu,
bata san sanda ta d'ora hannunta akan k'irjinsa dai-dai saitin zuciyarsa tana tura shi baya ba,
wata irin muguwar fad'uwa gaban Hanash yayi,
jin sabon al'amarin dabai tab'a ji ko tsintar kansa a ciki ba,
da sauri yaja baya while zuciyarsa na k'ara beating so past,
saboda tsabar rud'ewa Khulud ta k'ara binsa tana k'ok'arin k'ara d'ora hannunta akan k'irjinsa,
da sauri ya rik'e hannunta,
gudun karta sake haifar masa da abinda yaji,
hannunshi daya tab'a nata yasa shi jin mugun shock, saurin sakin hannun nata yayi yana ja baya,
a haukace Sanah ta fara neman abinda zata bugawa Hanash,
sanin halin Sanah yasa a kid'ime Khulud ta kuma d'ora masa hannunta akan k'irjinsa tana tura shi baya,
sororo Hanash yayi kamar wanda aka cirewa laka,
saboda yadda yake jin gaba d'aya mode d'in jikinsa ya canja,
shu'uman idonuwansa kawai ya zubawa Khulud yana kallan yadda ta kid'ime gaba d'aya,
sai da ta kai shi har bakin motarsa ta tura shi ciki kana ta koma wajen Sanah dake ta faman neman abun duka,
kasa tuk'in motar Hanash yayi dan wani iri yake jin jikinsa,
da sauri Khulud ta rik'e Sanah gam ta rik'e k'ugunta ta baya,
murya Khulud ta d'aga tana ce masa " ka tafi! ka tafi ,
jin muryarta yasa shi dawo hayyacinsa,
cikin mutuwar jiki yayiwa motar key yaja while idansa nakan Khulud.
Da sauri Khulud ta tare mai napep ta danna Sanah sukayi gida,
tun a harabar gidan Sanah tayi cilli da talami da mayafinta ,
batayi part d'in Halan ba, tayi part d'in Mamu direct bedroom d'insu ta wuce,
Mamu na tambayarta lafiya amma bata tsaya ba,
kai Khulud ta girgiza tana bin bayan Sanah da kallo,
kana ta sunkuya cikin nutsuwa ta kwashe kayan da Sanah tayi watsi dasu a harabar gidan,
tabi bayanta,
a parlor ta iske Mamu tana kallan k'ofar bedroom d'in su,
"Assalamu Alaikum, Khulud tace tana shiga parlorn ,
Mamu ta d'aga kai ta kalle ta tana amsa sallamar tata,
Khulud na niyyar shigewa Mamu tace " ita kuma wancan ita da wa?
Khulud tace " ita da wata mata ne,
tayiwa Mamu k'arya dan tasan muddin Mamu ta san Sanah tayi fad'a da Namiji sai ta ci ubanta,
Mamu tace " wata mata kamar ya?
Khulud tace " ban san sunnanta ba,
a wajen saloon muka had'u,tayi maganar cikin alamun rashin gaskiya,
Mamu tace " to da kuka had'u a wajen saloon sai akayi yaya?
Tayi maganar idanta nakan Khulud danta hango rashin gaskiya k'arara a tattare da ita,
" budurwa ce fa kamar mu Mamu,
Khulud ta fad'a danta kawar da wancan maganar,
Mamu ta bud'e baki tace " oh ashe fa ku 'yan mata ne ko?
Khulud tayi saurin rufe fuska tana niyyar shigewa,
Mamu tace " shiyasa kenan ake san yiwa Mamu wayo ko?
Mamu ta fad'a tana kallan yanayinta,
kana ta cigaba " meya had'a ku da matar?
Khulud tace " nothing but serious,
Mamu ta tab'a baki, kana tace " Allah ya kyauta,
kuma Allah idan na bincika na gano baku da gaskiya kun shiga uku,
Khulud tayi murmushi tabare datace komai ba,
ta shige ciki wajen Sanah'rta,,
a kan bed ta iske Sanah ta had'a kai da gwiwa tana sharar kukan bak'in cikin an mare ta bata rama ba,
da hanzari Khulud ta k'arasa gare ta tana d'ago kanta tace " my Sanah meye kuma abin kuka?
Tayi maganar muryarta na rawa,
kwace jikinta tayi ta d'an matsa gefe,
while tana cigaba da kukanta,
cikin sanyin murya Khulud tace " ni ce na b'ata maki rai?
Sanah tayi mata banza,
Khulud tace " kina san nima nayi kukan?
Tayi maganar muryarta na cracking,
jin yadda muryar Khulud ke rawa alamar tana san yin kuka ne yasa ta d'ago kanta,
had'i da zuba mata jajayen idanuwanta,
Khulud tace " wannan duk akan shine?
Ta fad'a tana nuna mata hawayen dake cigaba da zubowa,
cikin muryar kuka Sanah tace " I hate him , I really hate him more & more most,
I never hate someone like him,
murmushi Khulud tayi tace " har Sir Moli?
Sanah ta juya jajayen idanuwanta tace " ashe ke har tuna shi ma kike yi?
Khulud tace " ai naji kince before ne,
ni kuma nasan kin fad'i wannan kalmar akan Sir Moli yafi a k'irga,
Sanah ta zumb'uro baki tana cewa " Allah nafi tsanar wannan akan Sir Moli,
shi ai bai tab'a mari na ba,
kuma koma ya tab'a shi ai malami na ne,
amma shi wannan k'atilan mak'atulan ya kama ni ya mara haka nan a banza,
wallahi ban tab'a kyale shi sai na rama,
Khulud tace " ki rama me?
Sanah tace " marin dayayi man mana,
Khulud tace " ina zaki kuma ganin shi balle har ki rama?
Sanah tace " in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a had'u,
"hmmm wato har kina saka ran sake ganin shi kenan?
Sanah tace " sosai ma, kodan bashin marin daya d'auka nasan wata rana dole zamu had'u,
kuma wallahi a duk inda na ganshi sai na rama kuma duk yawan shekarun daza'a d'auka,
Khulud tace " alk'awari fa kika d'aukarwa kanki kenan,,
Sanah tace " sosai ma kuwa,
ki kuma aje wannan a ranki,
Khulud tace " ni dai tashi muje mu ji ya shirye-shiryen walimar mu,
Sanah tace " bari nayi wanka na canja kaya tukunna,
ta fad'a tana shiga bathroom,,
bata jima ba ta fito ta canja kaya,
kana suka fita, a parlor suka iske Mamu kamar yadda suka barta,
Mamu ta bisu da kallo tana tab'a baki tace " ikon Allah har anje an lallaso ta kenan?
Sukayi dariya suna zama akan sofa,
"wato duk fushin da d'aya tayi da d'aya ta bata hak'uri take hak'ura,
Sanah tace " ai dole a hak'ura Mamu,
Aarib ya shigo sanye da jallabiya,
Sanah na ganin shi ta zumb'uri baki had'i da kauda kanta gefe,
dariya yayi yace " me aka yiwa amaryar mu ne naga tana ta kumbure-kumbure?
Sanah ta kuma turo baki tana kauda kai gefe,
batare da tace komai ba,
hannayensa daya b'oye a bayansa ya ciro ya mik'awa Khulud walin sabuwar waya k'irar IPhone 10,
ihuuu Khulud tayi had'i da buga tsalle ta rungume shi,
light kiss tayi masa a chicks d'inshi ,
"nagode sosai Big Bro,
ta fad'a tana bud'e kwalin wayar,
hannunta na rawa ta ciro red color iPhone 10 d'in daga kwalinta,
Sanah na ganin wayar ta rud'e ta mik'e da sauri,
tace " Yaya ina tawa?
" Ke da kike fushi dani Matar mu,
baki ta turo tace " Yaya ai na fad'a maka ban san sunan da kake fad'a man,
yace " wanne sunan?
"Matar mu ko amaryar mu mana,
kuma kak'i fad'a man ma'anar sunanyen,
Mamu tayi dariya tace " bake kad'ai ba,
nima nayi-nayi ya fad'a man amanar sunayen yak'i,
kai ya shafa, had'i da fiddo kwalin wayar ya d'aga sama,,
dan ya kawayar da maganar,
cike da murna Sanah ta fara tsalle tana rirrik'eshi tana k'ok'arin kamo hannunsa danta karb'i wayar,
k'irjinsa na gogar nata,
jin tana neman canja masa emotions yasa shi saurin mik'a mata wayar yana dariya,
da sauri ta bud'e kwalin taga irin ta Khulud sak har color,
tsalle tayi had'i da fad'awa jikinsa ta rumgume shi,
tayi mishi light kiss itama a kumatunsa,
" Yaya nagode sosai tace cike da farin ciki,
da sauri ya raba ta da jikinsa yana dariyar yak'e,
fita tayi da gudu kanta ba ko d'an kwali tace " na tafi na nunawa Aunty Halan,
ta daina mana gori,
Khulud ma tabi bayanta,
Aarib yayi saurin bin bayanta danya rik'o ta ganin gidan akwai ma'aikata maza,
amma kafin ya rik'o ta harta kai farfajiyar gidan,
Khulud na biye da ita a baya,
ganin yadda ma'aikatan ke kalla Sanah ,
ga kanta bako d'an kwalli ya saukar mishi da bak'in ciki,,
ya runtse idansa da k'arfi,
da gudu suka shiga parlorn Halan suka iske bata nan tana kitchen,
da gudu suka bita kitchen ta baya suka rungumo ta a tare,
suna cewa " muma yanzu mun wuce gori,
sukayi maganar suna nuna mata phone d'in,
"woow Halan tace " tana karb'ar wayoyin daga hannunsu,
waya saya muku?
Cikin zumud'i suka " Yaya Aarib,
Halan tace " kai masha Allah,
amma shine ko yayi kara ya had'o da Auntyn taku,
tayi maganar cikin tsokana,
Sanah tace " ke da mijinki ya tashi siya miki wani yayiwa karar?
Daga bayan su suka ji muryar Ziyad na cewa " zanci ubanki Sanah,
da sauri ta juya bayanta,
taganshi zaune a parlor yana kallan labarai,
da alama ma anan suka wuce shi basu kula dashi ba,,
Sanah ta kulli Halan ta tab'a baki kana tace " ashe yana nan?
Halan tayi murmushi batare da tace komai ba,
ta mayar da hankalinta kan wayoyin tace " to yanzu daya siyo muku iri d'aya sak har color ya zaku rink'a bambamce ta kowa?
Sanah tace " wannan ai ba damuwa bace,
tunda kayanta nawa ne, kaya na ma nata ne,
kuma ba yau muka fara abu iri d'aya ba,
dai-dai da reborn, pand & bra iri d'aya ne damu sak,
Halan tace " to sarkin bada amsa,
ta fad'a tana mik'a musu wayoyinsu,
da sauri Khulud tace " lah ashe harda sim card?
Sanah tace " da gaske?
Tana duba wayar,
aiko da gaske MTN nema a ciki,
Sanah ta fad'a,
Khulud tace " aiko yanzu zamu bud'e Facebook, WhatsApp, Instagram, Twitter and Snap chart,
Halan tace " to fa ba'a samunba,
ai dama yanzu mun shiga uku kuma cewar Seenah tana dariya,
"lahh ashe kina nan Aunty?
Suka ce, tace " eh ,
yanzu zan koma gida dama shigowa nayi naga ya jiki-jikin nata,
Sanah "oh bamu kula dake ba,
Seenah tace " dama ya za'ayi ku kula dani, hankalinku nagan waya,
duk sukayi dariya.
Hanash na komawa gida direct ya wuce part d'in shi,
abinda bai tab'a yi kenan a rayuwarshi ba,
ya shigo gida ya wuce part d'in sa kai tsaye batare dayaje yaga Mimmeensa ba,,
kayansa ya cire yayi niked kana ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower,
ko wankan kasa yi yayi ya fito d'aure da towel a k'ugunsa ,
ya fad'a kan bed ta baya,
gaba d'aya ya rasa meke damunsa,
wani irin bak'on al'amari yake ji yana ratsa ruhi da gangar jikinsa,
gaba d'aya jikinsa babu dad'i wani iri yake jinsa kamar rashin lafiya ke san kama shi,
jikinsa duk yayi sanyi,
babu abinda yake gani sai yarinyar tsaye a gabansa,
haka ma zuciyarsa ta hana shi sakat,
da tunaninta, daya rufe ido ita yake gani tsaye a gabansa,
ko da daddare kasa shiga part d'in Mimmee yayi,
haka ya kwanta baici komai ba.
Washe gari tunda safe su Sanah suka fara shirye-shiryen walima har wajen 2:40pm,
suna aikin had'a coslow Halan tace " wai ni kun karb'o d'inku nan ne banga kun nuna min ba?
Tayi maganar tana cigaba da goga carrot,
ido duk suka zaro waje Khulud tace " Subhanallah wallahi Anuty Halan mun manta bamu amso ba,
da sauri Halan ta kalle su tace " what!?
Wai kuna nufin baku amso d'inkin kayan dazaku sanya ba ko me?
Sukayi tsilli-tsilli da ido,
Halan tace " to uban me zaku saka?
Ta kuma tambayar su, a k'ufule,
duk sukayi shiru,
cikin fad'a Halan tace " wai ba tambayar ku nake yi bane?
Cikin sanyin ta Khulud tace " we are sorry our Aunty Allah mun manta ne,
Sanah tace " sorry bari muje mu amsa yanzu,
ta fad'a tana mik'ewa, tsaki Halan tayi kana tace " duk ku biyun zaku tafi amso d'inkin ko me?
Sanah tace " eh mana,
" a' a d'aya taje ta amso muku d'inkin,
d'aya kuma ta zauna anan ta shirya tunda lokaci ya fara k'urewa,
tayi maganar batare data kalli inda suke ba,
tsayawa sukayi cirko-cirko akanta su basu tafi ba,
ba kuma su zauna ba,
ta kalle su tace " uban me kuke jira kuma?
Khulud tace " dan Allah Aunty ki barmu mu tafi tare please,
" mstwwwwwww sai ku tafi, kuma wallahi kuyi sauri ku dawo,
karku sake ku b'ata man lokaci,
Halan ta fad'a tana cigaba da aikin gabanta,
"to suka ce, kana suka koma part d'in Mamu suka jira simple dogayen riguna bak'ak'e suka sanya,
sukayi rolling kan su da mayafi,
Baba driver na hango su ya taso da sauri ya nufo yana murmushi,
yace " manyan gobe fita za'ayi ne?
Murmushi sukayi su duka biyun,
kana Khulud tace " eh Baba shagon Barrister mai d'inkin mu zaka kai mu,
yace " na sallari gidan bulo?
Suka ce " eh,
" manyan gobe ku shiga mu tafi,
yayi maganar yana k'ok'arin bud'e musu mota,
Sanah tayi tare shi tana murmushi tace " ka barshi Baba ka bari zamu bud'e da kanmu,
idan mu bamu bud'e maka ba,
ai bazamu bari kai ka bud'e mana ba,
ta k'arasa maganar tana zama a cikin motar,
yayi murmushi batare dayace komai ba yaja motar.
Gaba d'aya jikin Hanash a mace yake kwata-kwata ya rasa abinda yake damunsa,
jinshi yake kamar mara lafiya,
dan ko dad'in bakinsa ma baya ji,
dan haka tun jiya bai iya cin komai ba,
yadda ya kwanta tun dare daga shi sai towel haka ya kwana,
sai asuba kana ya mik'e yayi alwala ya zura jallabiyya yayi sallah,
ya dad'e sosai akan prayer mat yana azkhar da addu'o'i akan sabon yanayin daya tsinci kanshi,
anan kan sallayar ya kwanta,
bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,
dan bai wani samun ishashshan baccin dare ba,
Mimmee ta kasa zaune ko tsaye,
hankalinta yayi mugun tashi ganin har azhur bata saka Hanash a idonta ba,
abinda bai tab'a faruwa ba, dan muddin Hanash yana k'asar bai iya kwana batare daya ganta ko yaji lafiyarta ba,
tun jiya ta tambayi mai gadi ya shaida mata ya dawo ya shege part d'insa ne,
tun jiya taso ta bishi taji ko lafiya amma sai tayi tunanin bari ta bashi privacy,
a hankali ta d'aga kanta taga har wajen 1:50pm,
Hanash bai fito ba, jikinta a sanyaye ta fita ta nufi part d'in shi,
cikin sanyin jiki ta fara knocking k'ofar,
cikin baccinsa mai cike da mafarkinta yaji sama-sama ana buga k'ofar,
firgigit ya farka, cikin sanyin sa ya mik'e zauna yana cusa hannu cikin kwantaccen gashin kansa,
jin an k'ara buga k'ofar ne yasa shi d'aga kansa ya kalli k'ofar,
ya tabbatar Mimmee ce , dan ya san babu mai zuwa part d'insa balle har yayi masa knocking,
saboda yana da privacy ya hana duk masu aikin gidan zuwa part d'insa su gyara masa,
shi da kanshi yake gyara kayansa,
k'ara buga k'ofar Mimmee tayi,
da sauri ya mik'e a hankali yana cigaba da cusa hannunsa cikin kwantacciyar sumarsa,
a hankali ya bud'e mata k'ofar ta shigo,
idanta na kansa tace " lafiya Son najika shiru tun jiya?
Kansa ya kuma shafawa yace " lafiya lau Mimmee,
ido ta k'ura masa tace " amma shine baka zo ka ganni ba?
Yace " kai na ke ciwo nasha magani,
ban san sanda bacci ya d'auke ni ba,
ya fad'a cikin sassanyar muryarsa mai dad'in sauraro,
ido ta k'ura masa na wani lokaci kana tace "are you sure?
Yace " yes Mimmee yana kyataccen murmushinsa mai tsada,
hannunta ya kama yana cewa " muje ki bani breakfast Mimmee yunwa nake ji,
ya fad'a danya kawar mata da hankalinsa daga gano abinda shi kansa bai san takamaimansa ba,
dan yasan muddin Mimmee ta gano yana cikin damuwa koyaya take tada hankalinta zatayi sosai,
dariya Mimmee tayi tace " breakfast ko lunch?
Tayi maganar tana zaunar dashi akan sofa,
yace " ni dai abani koma meye yunwa nake ji,
Mimmee tayi mamakin yadda yau Hanash da ke kansa ke cewa a bashi abinci yunwa yake ji,
a bowl ta zubo mishi farfesun kan naman rago,
ta had'o masa da plantain & chips ,
ta kawo mishi da sauri ya amsa ya fara ci,
yana sanya lomar farko a bakinsa yaji kamar ya sanya mad'aci,
gudun kar Mimmee ta gane yasa shi cusa abincin kad'an badan yaso ba,
a hankali ya cire hannunsa daga cikin abincin,
yace " Alhamdulillah, thank you so much Mimmee,
Mimmee ta kalli d'an abincin daya yakusa kana ta mayar da kallanta gare shi tace " har kayi me?
Murmushi yayi daya fito da kyanshi sosai yace " na k'oshi Mimmee ya fad'a cikin shagwab'a,
Mimmee tace " ni dama nasan ba wani cin abincin zakayi ba,
yace " Mimmee naci sosai fa duba ki nani,
yayi magana yana nuna mata cikinsa,
dariya tayi tace " to Son, yanzu kuma ina zuwa?
Yace " kai Mimmee duk inda zaki sai kin tambaye ni,
yanzu fa na girma,
yayi maganar a shagwab'e,
Mimmee tace " oh! k'ato a dawo lafiya Allah ya tsare,
yace " amin ya Allah,
my Mimmee thank you,
kana ya fita,
bedroom d'insa ya koma ya watsa ruwa,
ya sanya simple t-shirt (red tag),
da 3 quarter shima na company red tag,
ya sanya takalmi boot Nike,
kallo d'aya zaka yi mishi kasan anci uwar kud'i wajen siyan kayan cikinsa,
kayan sunyi mugun yi mishi kyau da amsar cikekkiyar surar jikinsa mai zati,
kana ya feshe jikinsa da manyan perfumes,
kyan sura dana fuskarsa ya fito sosai,
idan ka ganshi sai ka rantse ba d'an Nigeria bahaushe bane,
idan ba Hausa yayi ba, zakayi tunanin he's Indian man,
ya d'auki key ya fita, har zai hau motar jiya KIA,
ya fasa ya hau Ferrari,
ya fita,
yana driving idansa ya sauka akan wasu yara k'anana dake ta faman k'ok'arin tsallaka titi,
amma motoci sun hana su, abinka da mutum mai kyakkyawar zuciya,
ya koma gefen titi yayi parking ya fito ya rik'e hannun yaran ya tsallakar dasu titin,
yaran sukayi masa godiya sosai,
har ya shiga mota suna d'agawa juna hannu,
ya shiga mota zayyi mata key,
ya hango wata tsohuwa tana bara a bakin titi,
kasancewar Hanash mai tsananin tausayi da taimako yasa shi fitowa ya nufi inda tsohuwar ke zaune niyyar ya bata sadaka.
Su Sanah na tafiya a mota kanta na jikin window tana kallan gefen titi,
karaf idanta ya sauka akan Hanash,
da sauri tace " Baba driver dan Allah d'an tsaya,
yace " to manyan gobe, yayi maganar yana gangarawa gefen hanya,
Khulud ta kalle ta tace " ina kuma zaki?
Sanah bata bata amsa ba, jikinta har rawa yake ta fita daga motar,
Khulud tace " wai my Sanah me zakiyi ne?
"Kina fa jin abinda Aunty Halan tace mana ko?
Sanah tace " eh cewa tayi muyi sauyi,
amma hakan bazai hanani cika buri na na minti 2 kawi ba na dawo ba,
" to Khulud tace tana gyara zamanta acikin motar tana