Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
xuciyarta a cike da mamakin inda suka hadu har
suka saba wasa da dariya haka. Tana mamakin yadda kaltum xata samu kudin da
xata biya mai ruwa dan a iya saninta kaltum bata da kudi. Mai ruwa yah au keken
jakunnansa ya kada su suka tafi, kaltum ta kinkimo bokitin ruwa ta kawo gaban
madina. Ta shiga cikin gida ta samo kofi ta dauraye ta ciko kofi da ruwa ta mikawa
madina, ta karba ta sha sannan itama kaltum din ta ciko kofi ta kwankwada yayin
da hanjin cikinsu ya fara karkadawa saboda a yau ko kwayar gero bata bakunci
cikinsu ba.
Madina ta gyara xama ta kalli kaltum t ace “ina kika samo tsohon nan, har kuka
saba ya baki ruwa kyauta!”
Kaltum tayidariya t ace “yanxu ma ce min ya yi in jira shi anan idan ya sayar da
ruwansa xai sayo min abinci, da na ce masa ba xan sha ruwansa ba saboda ban ci
komai ba, cikina xai yi ciwo.”
Madina ta sake tambaya “kin san shi ne!” kaltum ta bata labarin yadda suka hadu
rannan t ace yau ne haduwarsu ta biyu.madina t ace “to ai shine abunda nake fada
miki daxu kenan, maxa suna sonki, a wajen mata ne kike dab akin jinni, matan ma,
ba duka ba.
Kaltum ta gyada kai t ace “tabbas haka ne, na lura da haka da kika ankarar da ni.
Anty ina sauraronki ki ci gaba da labara, tun daxu labarin yana yi min yawo a
kwakwalwa. Kince ada ke bama musulma b ace, amma yanxu kin fi asalin
muslman sanin addini, ga karatun Qur’ani ga salla, a ina kika koya!”
Madina t ace “na karance Qur’ani tas na sauke kamar yadda kika sauke, na san
baki a duk inda aka buda min a cikin Qur’ani xan karance shi tsab, na iya hadisai
da dama da fassararsu ban san adadin sub a, sannan nasan tauhidi da hukunce
hukuncen musulunci. Ke in takaice miki ma ni malama ce a gidana mata suke
cincirindo suna xuwa daukar karatu.
Kaltum ta gyara xama tace “yaushe kika koyi duk wannan, a Onitsa ko a kaxaure!
Sannan kin c eke baki taba xua makarantar boko ba amma kin iya rubutu da
karatu da turanci har ma kina aiki a asibiti kina allura da dinkin ciwo, ta yaya kika
koya!”
Madina tayi dariya ta dafa kafadar kaltum t ace “Allah kenan, idan mutum y ace
“Allah” to karshen Magana ta xo. Kaltum, Allah ne Ya bani duk wannan a cikin dan
lokaci kankani. Ya mayar dani musulma ina kafura, Ya mayar dani mai ilimi alhali
ina jahila , Ya mayar da ni me gata alhalin ina marainiya, Ya axurta ni da miji da
‘ya’ya alhali ina ni kadai. Allah ne mai yawan kyauta, mai jin kan bayinSa, banda
Shi babu mai mayar da yaro babba, ya mayar da babba tsoho. Mai axurta talaka,
mai talauta mai arxiki a duk sanda ya so.”
Kaltum ta gyada kai t ace “hskiks haka ne, tsarki da aminci sun tabattata ga
Ubangijin talikai.”
Madina t ace Alhamdulillah, da kika yadda da wannan. Yanxu xan fara baki kadan
daga cikin labarina, xa kiji kadan daga cikin dinbin ni’imomin da Rabbussamawati
Yayi min, xa kiji yadda Allah Yake ikon Sa akan bayinsa.
Da farko ni sunana chidimma, haifaffiyar garin onisha ce, addinina addinin
gargajiya ne ma’ana mu ba musulmai bane ba kuma masu xuwa coci ba ne. akwai
bokan da yake yi mana duba da gumaka, shine yake iso mana da sakon abunda
xamu yiwa gumaka da wadanda xamu bari kada gumaka suyi fushi sai bala’I ya
same mu. Wa’iyyaxu billah, haka na taso na tarar kakannina da iyayena suna yi,
kuma a haka suka koma ga ubangijin su cikin tsantsan jahilci. Shiyasa nake kuka
duk sanda na tuna asarar da suka tabka a rayuwarsu a lokacin da suke duniya.
Musamman idan na ji hukuncin makomar wanda ya mutu yana shirka. Babu yadda
xan iya nemar musu gafara a wajen Mahalicci Ya gafarta musu kamar yadda naji a
kisser Annabi Ibarahim da mahaifinsa da kuma shugabanmu annabi Muhammadu
(saw) da kawunsa.” Sai madina ta rushed a kuka mai hade da tsantsar takaici,
yayin da idanuwan kaltum suka cicciko da hawaye itama.
Madina ta tsagaita da kukan ta ci gaba da cewa “sunan mahaifiyata chioma,
mahaifiyata wada ce.” Kaltum ta tambaya cike da rashin fahimata “wada!” madina
ta gyada kai t ace “wada dai da kika sani wadanda ake haifarsu gajeru masu katon
kai da guntayen gabobi wadanda aturance ake kiransu dawarf.”
Mamaki a bayyane xaka iya hangowa daga idanuwan kaltum, yayin da tambayoyi
suka cika xuciyarta amma ta rasa daga ina xata fara tambayar.
Madina tayi dariya t ace “ki kwantar da hankalinki xan baki labarin komai.
Mahaifina kuma sunansa emeka shi dogo ne sosai kamr duk wani dogon mutum da
kika sani dais hi kuma wani dogon mutum da kika sani sai dais hi kuma xabiya ne
wanda a turanci ake kiransa da albino.”
Kaltum ta xabura t ace “xabiya kuma!” madina ta kyalkyale da dariya, har kaltum
ta fara tsorata da dariyar da madina take tuntsurawa ta kasa dainawa kaltum tad
an ja da baya a tsorace, yayin da kwakwalwarta ta fara tunano mata abubuwa da
yawa akan madina. Ta ce a ranta “shin wannan wacce irin mat ace duk kwabe-
kwabe, ‘yar gidan xabiya da wada, inyamura, masu bautar gumaka!”
Madina ta katseta tunaninta da take yi ta ci gaba da cewa “dube ni sosai kaltum,
kin ga nayi kama da wadanni! Ko kinga alamar hasken fatata tayi kama da kalar
xabiya! Ko kinga alamar kamannina na inyamurai a fuskata ko harshena! Kon kin
ga alamar arnanci a dabi’una! Kin ga babu duk wannan, shine ma’anata cewar
Allah Y canxa ni a cikin dan kankanan lokaci.”
Kaltum ta gyada kai t ace “haka ne anty, babu duk wannan alamun da kika
xayyano min. a tunanin ke bafullatana ce.”
Madina tayi murmushi t ace “to haka yayana innamani yake, har ya fini tsawo da
fari don kamarmu daya sak. Da suka tashi haifar na uku sai aka Haifa wada aka
saka masa suna xuka, da aka sake haifar mai binsa sai aka mata suna Enena.
Daga nan sai rigima ta hautsine tsakanin dangin uwata da dangin ubana. Kinsan
basu san tawakkali ba saboda jahilci, sai dangin ubana suke cewa mama na mayya
ce sai an kasha ta, saboda me xata haifi wada kamar ta?
Suma danginta suka ce ai an haifi xabiya saboda haka baba na ne maye. Rigima
taki ci taki cinyewa, cikin dare dangin babana suka je suka kasha kanina xuka,
bayan kwana biyu aka tsinci gawar kanwata Enena a dawa suma dangin
mahaifiyata sun rama kenan. Aka tashi rigima kamar xa’ayi yaki a jinanasu,
tsakanin dangin wada da dangin xabiya daga karshe aka ce sai dai a raba auren
sannan a raba yaran wato ni da yayana kenan, mu masu lafiyar ana sanmu. Da
iyayena suka ji haka sai suka gaba xasu iya rabuwa da junansu ba saboda suna
mutuwar kaunar junansu, su suka san irin tsana da takaicin da suka sha a wajen
‘yan gari kowa yaki aurensu, saboda ita wadace shi kuma xabiya har saida Allah Ya
sa suka hada kansu suka xabi su rufawa juna asiri su xauna tare suka yi aurensu
babu mai yiwa kowa gori.
Cikin dare ya dauki ‘yar wadar matar sa, daman ya saba daukarta a kafadar sa duk
in da xasu je, ya shiga dawa suka gudu har yau ba’aji labarin suba. amma ana
kyautata xaton sun shiga wani kungurmin kauyukan arna sun tsafe su. Kinsan
kudu da arewa ba daya ba ne, yanxu a kudu sai kiga an kamo mutum an yi tsafi
dashi musamman aga irin wannan halittar ta wada da xabiya suna tafiya tare,
cewa xa su yi annoba ne ko su ce arxiki ne a kama su a yanka ko a binne su da rai.
Bawai na gaskata ba amma dodonsu y ace an kashe su a wani kauye don haka aka
yi bikin mutuwarsu aka raba gadon abunda suka bari, harda ‘ya’yan da suka bari a
rabon gadon wato ni da yayana. Shike nan gaba daya gidanmu ya waste daga ni
sai yayana muka rage, ba uwa, ba uba, babu kanne. Dangin uwata suka dauki
yayana, yayanta ya dauke ta ya dauke shi ya tafi dashi enugu garin da yake aiki,
dangin ubana suka dauke ni a nan cikin onisha nake. Kamar yadda kika sani da
xarar ance babu uwa, babu uba, a duniya to fa sai a hankali saboda gata yakare
sai wanda ya duba Allah xai dube ka.
A lokacin shekaruna takwas a duniya don haka na fara kiran kaina marainiya
domin na fara dandana maraici. Ba’a taba saka ni makarantaba sai talla da noma
koda yaushe, nice rainon ‘yayan ‘yan uwa, nice shara da wanke wanken a gidajen
‘yan uwa ba a gida daya ba. Baya ga duka, xagi da cin mutunci harda kala sata,
yau ace an ganni a gona na saci rogo gobe ace na balli ayaba a gonar wani ko
kuma ace na bude tukunya na saci naman miya. Kaltum ina bayan gari ina kuka ni
kadai gashi yayana innamani yayi min nisa baya onisha ya ci sa’a shi an saka shi a
makaranta. In takaice miki dai da wuya tayi wuya babu wanda bai san labarin
wahalar da nake sha ba a garin, ina tafe jama’a na nuna ni suna tausaya min.
kayan jikina a yayyage, tallar safe daban in koma in dauko abincin rana, idan na
sayar na koma na daukko na dare.
A kasuwa nake sayar da abinci anan ne na hadu da hausawa masu sayar da gyada,
man kulikuli, ridi, barkono da dai sauransu. Ta in da jini na ya fara haduwa da
hausawa shine suna da tausayi, suna da kirki, suna da kyauta, ga yawan fara’a.
muna xama tare muna sabawa sai na fara fahimtar ashe wadannan wadannan
mutane wato hausawa suna da wani addini da ake kira musulunci, suna bautawa
Ubangijinsu shine Allah madaukakin Sarki. Hakika idan musulmi y ace Allah xan yi
abu kaxa, tabbas suna tsoron Allah xa su yi din. Wannan al’amarin nasu yana
burge ni kuma yana matukar ba ni sha’awa, na ji ina son in yi huddar cinikayya
dasu. suna siyan kayana su bani kudina basa hanawa sabanin inyamurai ‘yan
uwana saisu cinye abincina su hana ni kudin, su ce in je in yi abunda xanyi, basa
tsoron Allah. A wanan dalilin ne yasa na fi so in sayarwa da hausawa abincina.
A haka muka saba da wani yaro saurayin mai suna Tasi’u, dan asalin wani kauye
ne da ake kira gurjiya, a hanyar wudil akwai wani kauye da ake kira kanyar babba,
daga nan ake daukar hanya sai ayi ta shiga kusurwa-kusurwa babu kwalta, sai
rigagen Fulani da kauyukan hausawa iri iri har a isa garin gurjiya.”
Kaltum t ace “yanxu daga surkukin kauyen na su tasi’u suke fitowa su tafi har
onisha neman kudi? ”
madina t ace “dabi’ar ‘yan garin ne duka shekara bayan amfanin gona yayi, anyi
roron gyada da wake saisu hada buhuhunan amfanin gonarsu maxansu da
matansu su hau mota su je garinmu onisha. Matan suna gida suna gyara gyada
suna yin man kuli da karago ko soyayyar gayada, maxan suna sayarwa a kasuwa.”
Kaltum t ace “har gidaje gare su a garinku kenan? ”
madina ta e “ba wasu gidajen kirki ba ne, tamfol ne suke bugawa a bayan gari, ko
suyi gidajen katako ko kuma su sami dakuna na kasa su kama haya. Suna xama
kamar watanni hudu ko uku sannan su hada kudinsu su sari manja, kwakwa, garin
kwaki, su juya garin su sai wata shekarar sannan su dawo.
Kaltum ta gyada kai tace “Allah mai hada mutum da mutum, idan ba ikon Allah ba
ta ina, ta yaya mutumin da yake hanyar wudil ya hadu da wacce take onisha. Yaya
kuka kare da mutumin da kika ce sunansa tasi’u dan garin gurjiya? ”
Madina tayi murmushi t ace “duk shekara muke haduwa da tasi’u, da yake bashi
da mata a wajena yake siyan abincin safe, rana da na dare ya siya ya bani kudina
cas har ma ya kara min, y ace na rike canjin komai yawan sa.
.
ADON DAWA 11
.
TRUE LIFE STORY
.
Don haka da xarar naga baki ‘yan garinsu sun fara xuwa sai nayi ta tambayarsu “ina
tasi’u?
ba xai xo ba ne?
yau she xe xo?
Me yasa bai xo bad a wuri? ”
haka kullum nake tambayar abokansa har sai ya xo hankalina yake kwantawa. Duk da
baya jin turanci sosai, amma duk da haka yafi sauran kokarin harhadawa in fahimce shi
ya fahimce ni don nima babu hausa a lokacin.
A lokacin da muka tabbatar wannan shakuwar tamu soyayya ce, sai a sannan na cika
shekara goma sha hudu. Na ji ina sonsa saboda yana tausayina ya fahimci ina shan
wahala a gidanmu, yana lallashina idan ina kuka haka yake cika min kudi idan cinikina
bai cika ba ina tsoro xa’a dake ni a gida. Haka yake kawo min atamfofi da soyayyiyar aya
da gyada duk sanda xai xo daga garinsu. Nima idan xai tafi sai in je gona in tsunko masa
kwakwa, abarba, ayaba da gwanda. Da kuka muke rabuwa duk sanda xai koma garinsu
sai inji duk bana jin dadin kasuwar idan baya nan.
Bana sha’awar samarin garinmu saboda ba abunda suka sani sai yiwa budurwa ciki, idan
taki amincewa sai suyi mata fyade (wa iyyaxu billa Allah Ya tsare mu da xuri’armu baki
daya.) da karfin tsiya ba’a kuma daukar matakin kirki idan haka ta faru dan haka nayi ta
taka tsan-tsan da duk namijin da yake kusanta ta. Da yawa samarin garinmu sun sha
kawo min hari, Allah Yak e kiyaye ni.
Wata rana na je na iske tasi’u a dakinsa bashi da lafiya yana cikin bargo yana
makyarkyata saboda tsananin xaxxabi mai xafi. Na xuba masa abinci nace ya tashi yaci,
yace ba xai ci ba idan yaci xai yi amai. Na kasa tafiya talla in bar shi cikin wannan hali
sai na xauna a gefen katifarsa ina shafa kafarsa. Sai naga ya xabura ya janye kafarsa. Ya
ce da ni baya so ina taba shi saboda haramun ne mace ta taba namiji idan ba mijin taba
ne, haka bai ma kamata in shigo dakinsa ba in xauna saboda gudun shaidan xai iya
shiga tsakaninmu, a takaice dai yana nufin in tashi in fita.
(ALLAH SARKI, JAMA’A SE A KIYAYE DOMIN KUWA WANNAN ITACE ADDININ MU KUMA
AL’ADARMU, DA YAWA MUTANE YANXU SUN XAMA DA SHI GANIN DAMA, DOMIN GUJEWA
SHARRIN SHAIDAN, JAMA’A SE A KIYAYE, A DAU DARASI, ALLAH YA SA MU DACE, KUMA
MU PI KARPIN XUCIYOYIN MU.
Aamiin )
Raina yabaci na dauki kayan talla na fice a tunanina yayi min wulakanci baya sona. Ina
shiga wani gida talla sai mutumin gidan ya rufe kofa da ni yana neman yi min fyade, da
kyar na kwaci kai na bayan da muka yiwa juna jini da majina. Ya fasfaska min mari, ni
kuma na rurrusa masa daron abincin tallar, na juye masa abincin aka duk abincin ya
xuxxube, da kyar na kwaci kaina na fito yaro-yaro kayana a yayyage. Sai a lokacin na
sake tabbatarwa da lallai tasi’u mai so na ne kuma baya niyyar cutar da ni, kuma
al’adarsu da addininsu yana da kyau yafi namu.
Kai tsaye dakin tasi’u na nufa ina rusa kuka, wannan karon sai na ki shiga cikin dakin sai
dai na kwankwasa masa kofa, ya fito da kyar yayin da hankalinsa ya tashi daya ganni a
cikin wannan halin. Yana tambayata cikin gigita dakyar na lafa da kukan na fada masa
abunda ya faru, na shaida masa cewar kwanukan abincin yana can a gidan mutumin
kuma abincina ya xube dukka ko cinikin sisi ban yi ba ina tsoran in je gida dan xa’a
kashe ni idan ban kai kudi ba. Haka tasi’u ya harhada duk ‘yan kudaden sa ya bani ya
saka ni a gaba na nuna masa gidan, muka iske gidan a rufe amma an watso min
kwanukan waje. Tasi’u ya harhada ya bani na tafi gida, duk da haka saida na ci duka
akan kayana da aka gani a yayyage.
Tun daga wannan lokacin na ji na kara son tasi’u kuma shi ya dace da rayuwata. Na
shiga tunanin ta yadda xamu fara domin na san ko a mafarki a gidanmu da wajen
bautarmu ba xa su bari na auri tasi’u ba ko xan mutu. Shima ya nuna min yana sona
amma fa ko xan mutu ba xa’a bar shi a gidansu ya su ya aure niba, a lokacin ma ya fada
min cewar har an bashi wacce xai aura shi ne baya so yake jan abun da tuni ma anyi
bikin.
Tasi’u ne ya koya min saka suturar da xata rufe min ilahirin jikina, na daina yawo da
shimi dadan siket iya gwiwa, shi ya nuna min kamun kai da kintsa jiki idan ina gaban
maxa saboda gudun sha’awa, muna son juna sosai har takai ta kawo sanda ya xo xai tafi
garinsu na rike shi ina ihu nace sai dai mu tafi tare ba xai tafi ya barni ba, dole ya fasa
tafiyarsa a ranar abokan tafiyar sa suka tafi suka barshi ya xauna yayi ta lallashi na
dakyar na yarda na koma gidanmu a bisa sharadin gobe xai jira ni mu tafi tare.
Cikin dare na sulalo na fito daure da kayana a dan buhu na xo na buga masa kofar
dakinsa nace ya fito mu gudu saboda gobe da safe xa’a a tashi a fadawa ‘yan uwana su
xo su kama ni. Da farko ya nuna ba xai tafi da niba, kukana da kalaman da nake fada
masa cewar ina so in musulunta in xauna da musulmai In baxe aure niba na yarda, na
shaida masa na gaji da wahalar aiki, talla, da duka kullum, in har ba xai tafi da niba to ya
sani kafin ya dawo wata shekara xan kashe kaina. Dole ya ji babu yadda xai yi sai ya tafi
da ni din. A daren muka shiga tasha muka kwana, da asuba muka shiga doguwar mota
xuwa kano. Babu wanda ya ganni har muka bar garinmu, daga kano muka hau motar
wudil kafin a isa wudil muka sauka kanya babba muka hau Babura suka shiga damu
garin gurjiya, garinsu kenan. Bamu isa gurjiya ba sai kimanin karfe goma sha daya na
dare a lokacin kowa