Advertisements
Chapter 2 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 46

3K to 6K   out of 137K words

cika sati uku a bur sudan dole tasa suka fito neman
abunda xa su kai bakinsu, mata da maxa, yara da manya kowa ya ja xugarsu suka
shiga gari.
Tawagar ‘yan mata su biyar kaltum, rakiya, huwaila, jidda’u da amina suka
fankama garin ADON DAWA don yin bara. Suka kuwa ci sa’a suka samo kudi da
yawa wanda xai ishesu su ci abincin yinin yau. Kalmar da suke ambata itace
“karama fisabilillahi” sai kaga an miko musu kudi. Su kan basu wahid jine wato
kamar naira daya kenan, wasu se su basu hamsin jine ficika kenan idan kuwa suka
ci sa’a sai a rana daya saisu hada maitan jine daga nan saisu wuce cikin gari maka
makan wajen sayar da abinci (restaurant)su sayo abunda suke so, kamar su kisra
wato sinasir ko su sayi esha wato gurasa, wani lokaci saisu hada da ful. Ful wake
ne manya manya sai a dafa shi ba gishiri ana ci da gurasa. Idan suka samo kudin
bara da yawa saisu sayi baitil mandi shima dafaffiyar shinkafa ce fara sai a
kwarara madara akai, a yanka tumatiri da albasa, a yanka karas da kabeji, sannan
a dora gasashshiyar kaxa a barbada dan gishiri sannan a ci.
Daga dukkan alamu yunwar da ke addabar su ta fara sauki har sun sami karfin da
suke iya debo bokitai da manyan darukan ruwa akansu, su niki tafiya mai nisa
sannan su samo ruwan da xa suyi amfani dashi wajen wamka, wanki da wanke-
wanke. Ta cikin makabarta suke bi sannan su isa gabar kogin da suke debo ruwan.
Ruwan baya shawuwa saboda jajawur ne mai dandanon gishiri.
Jikin kaltum yakan yi sanyi har takan fashe da kuka idan taga yadda ake binne
mutane a makabarta. Saboda sahara ce don haka suke yin dogon rami mai xurfi
sosai, wanda mai hakawar sai ya shige ciki sosai yayi xurfi.sai an daina hango shi
sannan ya miko hannunsa a kamo shi waje dan ba xai iya fitowa ba. Sannan saisu
taru su saka gawa, sannan su jera bululluka a maimakon itace saboda yashi ne
itatuwa ba xa su tsaya ba. Allahu Akbar!
Allah Ya sa mu cika da imani, Y a jikan musulman da suka riga mu gidan gaskiya.
Ameen.
A yau kaltum bata bisu bara ba saboda tana son ta wanke kayan jikinta kwaya
daya kacal, yayi dakun dakun har gefen xanin ya yage don haka ta yanke
shawarar sai kowa ya tafi bara sannan ta rufe gida ta cire kayan ta wanke ta xauna
ta jira ya bushe sai ta yi wanka ta saka. Da ta tabbatar mata da maxa sun fita
daman tun da sassafe ta debo ruwan wankinta, sai ta tsinci guntayen sabulai ta
harhade ta ajiye. Suna ficewa sai ta rufe kofar ta fara wanke riga da dankwali da
mayafin ta shanya ta koma gefe ta takure tana jiran su bushe.
Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa na gidan sai tace a ranta “yanxu fa a
makabarta muke rayuwa alhalin muna raye.”
Ta sake duban katon tudun kabarin da yake gefenta ta mika hannu a hankali ta
shafa tace, “ko mace ce ko na miji ne a cikin kabarinnan Allah Shi ya barwa KanSa
sani. Allah Ya jkansu da gafara.”
Ta ji hawaye yana sirnanowa daga idanuwanta don tausayin kanta da irin
matsananciyar rayuwar da take ciki. Ta tuno gwaggo fattu wacce ta kawo ta nan ta
ajiye ta ita kuma ta haye ta yi tafiyarta makka tana can tana jin dadin rayuwarta.
Babban tashin hankalin shi ne iyayenta basu san halin da take ciki ba don su a
tunanisu tana saudiya kuma tasan mugun halin gwaggo fattu ba xata yi waya ba
ko ta aika wasika ta fada musu gaskiya ba sai dai ta bar su a haka, suma kuma
iyayen nata ba waya gare su ba balle su san lambarta ta makka su buga mata su
tambayi halin da take ciki. Kaltum ta fi jin haushin iyayenta su da suka yarda suka
yarda suka bayar da ita aka taho da ita don basa tausayinta. Ta ji ta tsani kowa a
duniya kamar yadda kowa baya sonta, sai ta fashe da kuka mai tsananin ta kifa kai
a jikin katakon dakin su. Kuka take yi haikan amma tana fada cikin daga muryar ta
“inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Tsananin bugun da ake yiwa kofar gidan ne ya sata tsagaita da kukan da take yi,
ta kasa kunne tana sauraro sannan ta gaskata wani ne yake buga kofa. Sai ta mike
tsaye ta yi wuri wuri tana tunanin yadda xata yi. Shawara take yi shin ta je a haka
da daurin kirji ta bude kofar, sai dai ai bata sani ba mace ce ko na miji! Idan namiji
ne ba xata iya tsayawa da daurin kirji a gabansa ba musamman yadda maxan suke
‘yan iska ko wanka ka ke yi idan baka kula ba saisu yi ta liken ki. Haka idan ki ka yi
sake a daki kina barci baki killace jikinki ba sai dai ki ga suna ta xirga xirga ta kofar
dakinku suna kallonki a dole wucewa bandaki su ke yi, ko suyi ta leke ta hudar
katakon musamman dakin su kaltum da yake kunshe da ‘yan mata.
Ta ji sautin bugun kofar ya kara tsamari don haka ta yayimi jikakkiyar rigarta ta
saka ta jawo jikakken mayafinta ta sharba a kanta ta goge idonta saboda hawayen
da yayi mata kawanya. Ta isa da sauri bakin kofar ba tare da ta tambaya ba ko
waye ta ja sakata ta bude game da wangale kofar. Jikinta na rawa ta dubi wacce ke
bakin kofar sai taga madina ce tayi sauri ta duka a tsorace.
Ta ce “sannu da xuwa, yi hakuri ban xo na bude miki kofa da wuri ba ina kokarin
saka rigata ne.” madina tayi murmushi t ace”lah ai ba komai kaltum.”
Kaltum ta mika hannu xata kar bi himilin daurin kayan dake kanta sannan ga leda
a hannunta. Madina tace “bar shi kaltum, ba komai ba sai kin taya ni ba ai na xo
gida mu shiga ciki.”
Kaltum ta dawo tsakar gida inda ta cire jikakkiyar rigarta da mayafinta ta mayar
kan igiya ta shanya. Madina kuwa ta wuce cikin dakinsu kai tsaye ta xarce kan
kwalin shinfidar ta da jakar kayanta a gefe ta ajiye himilin tsummakaron da ta
samo. Ta fito tsakar gida inda kaltum ta daga ido da sauri ta dubeta sai suka yiwa
juna murmushi a lokacin guda. Kaltum ta mayar da kai kasa don kunya da
girmamawa. Madina tace “kaltum me yasa yau baki fita bara ba!”
Kaltum ta dan yi murmushi tace “kayana ne suka yi datti nake so na wanke sai sun
bushe sannan in fita.”
Madina tace “ me yasa sai sun bushe xaki tafi, ki wanke ki shanya sai ki saka wasu
kayan ki tafi ki nemo abunda xaki ci, yaushe xa’a ce tun safe baki karya ba har
rana tayi yanxu kina jira sai kaya sun bushe!”
Kaltum ta langwabar da kai gefe tace, “ai bani da wasu kayan, kayan jikina ne
kadai nake da su, kakata ta tafi da kayana hade da nata ta haye tana cikin
wadanda suka tafi makka.” Hawaye ya sarnano daga idanuwan kaltum.
Madina ta tambayeta cike da mamaki tace “au iya mairo ba kakarki bace daman!”
Kaltum tace “kawar kakata ce, garinsu daya tare muka taho dasu, rakiya ce
jikarta.”
Tsawon mintina biyar madina tayi tana kallon kaltum saboda tsananin tausayin ta
da ya lullube mata xuciya, ta rasa kalma guda daya da xata iya furta mata. Tana
tausayin kanta da kanta, amma ta fi tausayin kaltum yarinya karama ba uwa ba
uba, ba dangin iya balle na abba a kasar da bata taso ba.
Kaltum ma ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa sai kwalla data cika mata ido ta rasa
abunda yake damunta saboda kuncin rayuwa.
Madina ta yi ajiyar xuciya ta share hawayen daya cika mata ido, sai ta shiga cikin
daki inda ta kwance daurin tsummakaron data shigo dasu ta fara daddagawa tana
warewa. Kala biyu riga da siket ta debo ta fito ta mikawa kaltum, kamar an xare
mata laka haka ta mika hannu ta karba. Ta kurawa madina ido tana sauraron
abunda xata fada, madina ta juya xata shiga daki sai kaltum tace,” wanke miki
xanyi!” sai dai babu sabulu, nima guntayen sabulai na tsintsinto a bandaki na yi
nawa wankin.”
Madina ta waiwayo ta dubeta sai tayi murmushi t ace “a wanke suke, baki nayi
kyauta ki saka nima yanxu nan aka bani su sadaka a garin ‘yan Adon dawa.”
Farin ciki ne bayyane hade da mamaki suka halacci fuskar kaltum ta yi murmushin
da har saida wushiryarta ta bayyana yayin da gafen kumatunta ya loba wato
(dimple) ta dago da fararen idanuwanta dara dara ta dubi madina ta fada cike da
annashuwa.
“anty kin bani kyauta in saka!”
Madina ta yi dariya tace “na baki kyauta kaltum, me ye sa kike mamaki!”
Kaltum, ta sunkuyar da kai kasa ta yi godiya sannan ta fara warwarewa tana
duddubawa farin ciki fal a xuciyar ta. Kafin madina ta fito daga daki kaltum ta saka
riga da siket cas da ita kuwa kamar dan ita aka saya daidai jikinta sun yi matukar
yi mata kyau. Madina ta fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunta tana
duban kaltum sai suka yiwa juna murmushi a lokacin guda. Madina ta yaba da
yadda kayan ya karbe ta, sannan ta samu inuwa ta xauna a kasa ba tare da ta
nemi wani abu ta shinfida ba. Kaltum ta jefa xanin da ta kunce a cikin bokitin data
adana sauran kunfar data wanke riga da mayafinta ta fara sabawa . madina ta
kwance leda sai ga kisra da ful.
Madina ta dubi kaltum tace “xo mu ci abinci yarinya”
Wannan kalma ta bawa kaltum matukar mamaki wanda har yasa ta dago da sauri
ta dubeta har na tsawon ‘yan dakiku masu yawa ta kasa Magana, can ta yi
murmushi.
Ta ce “na koshi, nagode.| madina tace, “me kika ci da xaki ce kin koshi.! Ki saki
jikinki da ni ki xo mu ci ai xai ishe mu daman dayawa na siyo in ci yanxu sauran
inci daddare ba komai, Allah de bani wanda dan ci daddaren.” Tsananin yunwa ce
daman ta addabi cikin kaltum banda kugi babu abinda cikinta yake yi saboda ya
fafake babu komai tun a bincin jiya da rana bata sake samun abunda xata sakawa
hanjinta ba. Ta ajiye wankin ta goge hannayenta ajikin siket din dake jikinta ta
karaso a hankali inda madina ke xaune, cikin kunya da nutsuwa ta xauna yayinda
hannunta ya dau rawa a lokacin da take kokarin gutsurar gurasar madina ta
dubeta, sannan ta tambayeta cike da mamaki.
Ta ce “kaltum lafiya, meke damunki, ya naga kina karkarwa kuma duk kin
tsangwami kanki! Haba kaltum ki saki jikinki ai ba wani abu bane duk wanda ya
taimaki wani shima Allah xai taimake shi.” Kaltum ta sunkuyar da kai kasa ta fada
cikin sanyin jiki.
Ta ce, “ina mamaki ne saboda tun a mota kowa ta kansa yake babu mai taimakon
wani ko dai dai da mukurwar ruwa ne sai naga kin bani sutura kyauta sannan kin
siyo abinci kince in xo in ci shine na keta mamaki.”
Madina ta yi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum tace “yarinya ba haka
bane duk masu yin haka jahilai ne, babu yadda xa'ayi musulmai su hadu a waje
daya su ce babu wanda xai taimaki dan uwansa musulmi. Babu mai imani ga duk
musulmin daba xai so wadan uwansa abunda ya sowa kansa ba.
Ko a lahira aikinmu ba xai kaimu shiga aljanna ba sai dai alfarma albarkacin masu
albarka. Kaltum, ki cire wannan mugun tunani a ranki, ki dauka a xuciyarki duk
runtsi duk talaucin da kike ciki komai kankartar abu xaki taimakawa wanda ki ka fi
ko da babu mai taimaka miki domin Annabi Muhammad (S.A.W) y ace “hannun da
yake mikawa shine a sama, ya fi hannun da yake karba shine a kasa.”
Babu wanda kaltum take yi sai gyada kai hakika tana gamsuwa da abunda madina
take fada mata. Suka ci, suka koshi suka kora da ruwa sannan kaltum ta yi godiya
ta tashi ta je ta ci gaba da wankinta, ta dauraye ta shanya. Dai dai lokacin iya
mairo da tawagarta suka shigo, a jigace suke saboda tsananin yawon bara da suka
yini suna yi da alama kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu saboda kowaccensu
hannunta dumu dumu da ledoji. Cikin fara’a kaltum ta tare su gani da yi musu
sannu da xuwa. A tunaninsu kwadayin abunda suka samo take don haka kowa ya
tsuke fuska babu wanda ya amsa gaisuwarta sai ma dai kauce mata suke yi suna
kewaye ta suka nufi daki.
Iya mairo ce ta tsaya tace mata “sannu isashshiya ‘yar gata wacce bata iya wahala
ba, kowa ya fita nema ke kina kwance a gida wa xai nemo ya baki a wannan
marrar da nafsi nafsi babu mai taimakon wani, keta wanki ma kike yi. Waye ya
baki aron Kaya ko kin fara tsayawa sai kinga ba kowa ki bude jakunkunan mutane
ki daukar musu kaya! To kada ki sace kayan wani a kama ki kice kin sanni ko kice
ni kakarki ce.
Rakiya ma ta leko daga daki ta tsoma baki tace “tun shigowata nake kallonta daga
gani kayan nan na wani ta sato saboda bai yi kama dana bola ba kuma bata fita
bara yau ba. Tun da safe ta debo ruwan wanki bata kara fita ba.” Sai sauran ma
suka tsoma baki babu wacce bata yi mata cari ba a cikinsu.
Kaltum tadago da sauri ta dubi madina yayin da madina ta yi mata nuni da hannu
alamar ta yi shiru kada tace komai. Kaltum ta sunkuyar da kanta kasa sai wani
kuka na takaici ya kece mata marar kakkautawa. Ta koma gefe ta tsugunna
tamkar almajirarsu yayin da kowaccensu ta shiga daki ta baje ledar abincita suka
ci. Wasu shinkafa ce da miya, wasu baital mandi, wasu taliya, wata macaroni. Abun
mamaki sai suka dinga yiwa madina tayi wai ta xo su ci. ta ce ta gode a koshe take
amma babu wacce ta tuntubi kaltum.
Wani kululun takaici ya tsayawa kaltum a wuya ta fara tuhumar kanta tana
tambayar xuciyarta wane irin mugun hali nake yiwa mutane haka suka tsane ni!
Me nake yi wanda kowa baya sona aka tsane ni!”
Sai tayi xunbur ta mike ta shiga daki wajen shinfidar kwalinta ta dauko robar cin
abincinta, yayin da kowacce ta dinga kare abincinta wasu ma suka fara daure ledar
abincinsu a tunaninsu rokarsu xata ta yi, ta dube su duba irin na takaici ta
langwabar da kai ta matse hawaye sai ta fice, ta yayimi gyalenta ba tare da ta
yiwa kowa Magana ba har madina da take xaune a tsakar gida a wajen da suka ci
abinci har yanxu bata tashi ba.
Fitarta kofar gida keda wuya sai ta tsaya cak ta dubi gabas da yamma, kudu da
arewa babu abinda take gani sai tulun bola da kabarurruka yayin da gabanta kuwa
katon kogi take hangowa yana ambaliya. Ta ji a ranta tamkar ta fada kogin nan
ruwa ya hadiyeta ta mutu ta huta da bakin cikin rayuwa sai kuma ta tuna da
wa’axin da aka yi musu a makarantar islamiyya cewar duk wanda ya kashe kansa
ya mutu a kafuri. Ta juya ta dubi kabarurrukan da ke gabanta sai tayi sha’awar
dama ace ita ce a ciki a mace ta mutu an binne ta. Ta ji a ranta rayuwar wadannan
bayin Allah da suka mutu ta fi mata irin rayuwar da take yi a duniya jin dadi da
kwanciyar hankali.
Kamar daga sama ta ji Magana a bayanta, ta waiga da sauri saida suka hada ido
da madina.
Ta ce “kaltum ina xaki je!”
Kaltum ta saki fuskarta ta yi murmushin karfin hali. Ta ce “xan je bara.”
Madina tace ki kula da kanki, shawarar da xan baki itace kada ki je garin jange
saboda kin ga ke yarinya ce akasarinsu kuma ‘yan iska ne gara ki je garin Adon
dawa tunda su na da musulmai xa su fi tausaya miki. Hadari ne ma ki dinga tafiya
ke kadai ba’a tawaga ba saboda irinku suke so ‘yan mata ba kamar mu ba manya
ba damuwa.
Kaltum ta gyada kai tace “to anty bari in je garin Adon dawan.” Ta juya ta tafi
yayin da madina ta dade a tsaye tana kallonta har saida ta kure ta daina hango ta
sannan ta girgixa kai don tsananin tausayin kaltum ta shiga gida.
Kaltum tafiya take amma fa har yanxu bata fasa kuka ba harta iske gidajen Adon
dawa. Ta fara shiga gida daya bayan daya, Kalmar da take ambata itace “karama
fi sabilillahi”
Da alama yau bata fito da sa’a ba daga inda ake kyaleta ta yi ta bara ta gaji ta tafi
da kanta sai inda ake yi mata korar kare. Ta yanke shawarar tunda yamma tayi
yanxu duk maxan suna kasuwa bari ta je can ko Allah xai sa ta dace. Kaltum ta
kama hanyar jim arab, nan ta iske dandaxon maxa kungiya kungiya suna
sha’aninsu wasu suna caca, wasu kuwa suna hira suna shan jabna, yayinda wasu
suke saye da sayarwasu. Kaltum na fara bara sai ta ci sa’a duk rumfar da tayi bara
sai a miko mata sadakar wahid jine wato kamar kandala, farin ciki ya lullube
xuciyar kaltum don ada ta shiga wani mawuyancin hali tana tunanin yadda xata yi
in har bata samu ko kwabo ba idan ta je gida xasu kusa cinyeta da baki bayan
wulakancin kala kala.
Ta ci gaba da bara harta karkashin wata inuwa inda dandaxon samari ne xalla, sun
shinfida katuwar tabarma suna ta shan jabna suna caca. Sun kaisu goma sha biyu
dukkanninsu shekarunsu basu wuce ashirin da biyar xuwa ashirin da bakwai ba.
Shewa da ihu kawai suke yi da alama basu da matsala a rayuwa. gasu a kauye, a
cikin gidajen katako da katangar kaya yayin da suturar jikinsu bakin yadi ne mai
layi layin fari wacce suke dinka ‘yar shara da wando iyaka guiwa amma koda
yaushe sai kaga suna farin ciki ko me yasa. Kaltum take xayyanowa aranta sannan
ta bawa kanta amsa “tabbas dole suyi farin ciki a rayuwarsu saboda suna tare da
iyayen su, a garinsu, kuma ga dukiyoyinsu” ta katse tunanin da take yi da ta ji
suna tambayarta “lafiya, me kike nema a wajenmu!”
Tayi firgigit t ace “karama fi sabilillahi.” Kalma daya ta ji wani daga cikinsu ya fada
a cikin yarensu sai taga dukkaninsu sun waiwayo sun kalleta a lokaci guda. Ta yi
sauri ta sunkuyar da kanta kasa, da tadago taga har yanxu suna kallonta, sai ta sa
gefen gyalenta ta rufe da fuskarta. Daga karshe ta yanke shawarar gaggauta barin
wajen tun kafin su iskance ta.
Cikin harshen larabci daya daga cikinsu yace ta xo, kasancewar tana jin larabci
sosai tun tana karama sai ta juyo ta dawo wajensu a nutse cikin ladabi amma fa
duba daya xaka yi mata ka tabbatar a tsorace take. Ya dubeta sama da kasa duba
irin na kurulla yayi dariya ya shafa baki don haka kaltum ta fara fuskantar manufar
kiranta da yayi, sai ta fara ja da baya.
To pa, ko ya data kasance tsakanin kaltum da en samarinnan!
Sai ku biyo mu dan jin yadda xata kaya
ADON DAWA 4
Ya fada cikin shagobe

2 / 46