Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
ce bakya ci yanxu
idan wani ya shigo ai sai yace hana ki aka yi. Idan ana so a ji hirarki sai idan daddy
ya xo, sai in jiyo muryarki ras tana bashi labari shi kuma yana ta dariya.!
Mamana ta yi murmushi t ace “haka suke yi tun tana yarinya daga ya ji kukanta
xai shigo har nan gidan ya dauke ta. Ya ce min “Safi, me kika yiwa gimbiya ta? ”
Babana y ace “ai abu da dama sai dai in ji a bakin direba, ko in gani tace daddy ne
ya saya mata na makaranta ko sayayyar amfanin gida. Sai addu’a tsakanina da
mutumin nan yana da matukar kirki.”
Sai ni kuma na yi Magana saboda babu yadda xa’ayi xancen daddy ban ji xuciyata
ta yi fari ba. Na ce daddy abokin hirata ne, daddy ne mai share min hawaye idan
ina kuka, shine mai sona a duniya wanda baya sona in shiga damuwa.”
Sai altine ta tabe baki tace “ko er gida xa’a yi a ci amanar mommy salaha? ”
Wannan Magana ta iya altine tasa gaba daya mun girgixa, muka dago kai muka
kale ta. Babana y ace “haba iya altine me yasa kike irin wannan maganar?
Ai hanyar jirgi daban ta mota daban, yadda uba ba xai iya auren yarsa ba haka
daddy yake da wannan yarinya.” Haushi ya sa baba ya tashi ya saka takalmin sa
ya tafi bakin get. Mamana ta girgixa kai tace “ai ko da wasa ma bai kamata a furta
wannan maganar ba.” Iya altine sai ta wayance ta share maganar data ga
dukkanmu ranmu yabaci. Bayan ta yi sallar magaruba ta cika tunbinta da tuwo sai
ta yi mana sallama ta shiga bangarenta ni da kannena muka ta fi makarantar dare.
Washe gari da safe lahadi ce ina gida ban je makarantar boko ba sai ga mummy
salaha ta diro a kofar dakina, ta biyo jirgin safe daga Abuja xuwa kano.
Sai muka ji tana fada da xage-xage wai ni da iyayena munafukai ne daga yau
xamanmu yakare a gidanta. A gigice muka firfito ba tare da mun fahimci abunda
take fadi ba. Duk da haka ni da iyayena da kanena muka durkusa a gabanta muna
bata hakuri. Ta kwalawa iya altine kira ta xo, t ace ta fada mana laifin da muka yi
mata don mun raina mata hankali muna nunawa ba mu san abunda muka yi ba.
Iya altine ba kunya, ba tsoron Allah ta maimaita sharrin da ta shirya mana a waya.
Ta ce da bakinta da nata na fada a gaban iyaye na nace daddy yace yana sona
nima ina son sa kuma yana saya min duk abunda nake so, wai har iyayena suma
sun amince ayi aure. Mu dukka muka dau salati muka hau rantse rantse ba ‘ayi
haka ba. Mummy salaha t ace ko ba haka ba ne ita daman xuciyarta bata kwanta
mata da ci gaba da xamana a gidanta ba saboda na xama budurwa, kyau ya taso,
tana fargaba ko ni ban ce ina son sa ba, shi xai iya cewa yana sona. Ga tsananin
shakuwar da ya yi da ni tun ina yarinya, don haka mu kwashe kayanmu mu fice
mata daga gida ta bamu kwana uku kafin daddy ya dawo daga London, kada ya
dawo ya hana mu tafiya. Ta shiga gidanta ta xauna tace ba xata koma Abuja ba
har sai ta tabbatar mun bar gidan.
Hankalinmu ya tashi muka rasa in da xamu saka ranmu. Ta ina xamu fara, kuma
ina xamu nuna?
Gidan kasarmu na xangon daura ya rushe babu ko daki daya a ciki. Tun dawowar
goggo fattu daga Makka ta yi aure a daura, mijinta ya kwashe dukiyar ya sake ta
yanxu haka a daura take xaune a gidan ‘yar uwarta babu cin yau ballena gobe
kasancewar gidan ba kowa duk ya rurrushe.
Babana ya dora hannu a ka yana rusa kuka, mamana har ta fishi tawakkali ita take
bashi baki ita ke cewa mu je mu sayi kara ayi bukka mu xauna gidan haka. Bayan
an yi haka da kwana biyu, saura kwana daya wa’adin kwanakin data bamu ya cika
mahaifana suka yi shawararsu, bansan me suke nufi ba suka ce in hado kayana
kocokan in shirya in fito. Jikina na rawa na hada kayana a jaka. Babana ya saka ni
a gaba muka fito daga gidan, bansan inda xamu je ba. Muka tsayar da acaba biyu
muka hau har kofar ruwa tashar kuka sai naga mun hau motar daura. Ni dai ina ta
lissafi a hanya ina tunanin wajen wa xa’a kai ni?
Sai gamu a gaban goggo fattu itama da alama tayi mamakin ganinmu. Koda suka
kebe da babana, ya fada mata cewar ya kawo ni, ni da ita xa mu koma Makka sai
ta fara washe baki tana farin ciki amma fa da yasa hannunsa a aljihunsa bai fito da
kudin kirki ba sai dai ya bata ixini ta sayar da gidansa na xangon daura mu yi
kudin jirgi. Da aka yi lissafi kudin gidan ba xai isa kudin jirgin ko mutum daya ba,
sai tace masa ya kwantar da hankalinsa xamu tafi ta mota mu shiga sudan sannan
mu haura Makka ta ruwa kudin xai isa. To a haka mahaifina ya tafi ya bar ni ko
sallama bai yi min ba, yana kallon hawaye da yake xuba daga idanuwana saboda
na tuno axabar da na sha a wajenta a wancen karon.
Na shafe wata guda a daura sannan gida ya sayu muka biya kudin tafiya da sauran
shirye-shiryenm
u muka taho. To shine wannan ganin namu da kika yi a cikin mota. Da idonki kinga
yadda take kyarata, take duka a cikin jama’a, kin ga horon yunwar da take yi min ,
kin ga horar da take min, duk da haka se da ta hada da jakar kayana kacokam ta
tafi dasu da gangan ta bar ni da kayan jikina kadai. Domin kawarta iya mairo ta
fada min cewar tun a can daura agent ya sanar mata cewar tunda bata cika kudin
bisa ba idan aka samu matsala ban wuce ba babu ruwansa tace eh ta yarda.” Sai
kaltum ta rushe da kuka.
Madina ta surnano da hawaye ta girgixa kai t ace “kaltum ki bar kuka ki sa
axuciyar ki duk abubuwan nan da suke faruwa mukaddari ne daga Allah , haka
madina tayi ta bata Magana a karshe ta ce “xamu haye mu shiga makka idan
shiga makkan kike so da ixinin Ubangiji.”
Kaltum ta girgixa kai yayin data dago da jajyen idanuwanta ta dubi madina ta fada
cikin takaici t ace “bana so in shiga makka don a kowanne lokaci xan iya haduwa
da goggo fattu ni kuma bana so in kara sakata a ido na har abada
. bana so in sake komawa Nigeria.
Alhaji adnan ne kadai nake tunawa nayi kuka, naji ciwon rabuwa dashi saboda na
san shi kadai ne xai yi kunar xuci idan ya xo ya tara bana nan.na fada xan
maimaita ko a gaban matarsa shine kadai yake sona nima nake sonsa a rayuwata.
Ba xan banbance wane irin so na ke yi masa ba, shi ne kadai a duniya wanda yake
mayar min da hawayena da yake shirin digowa kasa dariya. A ko ina ina ji dashi
sosai a gida ko a makarnta tsakanina da jama’a sai kyara amma shi yana
lallashina, Allah Ya dasa min sonsa a raina tun ina karama da son da ya kamata
nayiwa uwata da ubana shi nake yiwa haka ban taba tunanin wani ba a cikin
dinbun samarina da sunan wanda xan aura, sannan ban taba tunanin xan auri
daddy ba sai dai ban san me yasa na damu dashi ba, idan ban gan shi ba bana jin
dadi. Ina girma ina sake ganewa cewar shine mutum kwara daya me yi min
wahala.
Kyarar dasu rukayya suke min da kakarta da saura ma, du na saba domin haka
kakata goggo fattu ta ke min. a makaranta, kyara, da muka je hutu Abuja wajen
mommy salaha hutu ma be kare ba ta koro ni.. se ta fashe da kuka..
Madina ta girgixa kai ita ma kukan take t ace “daina kuka kaltum, ki nemi son
Allah bana mutum ba. Duk inda akwai alamar nasara to ba xa’a rasa mahassada
ba. Kema da kanki kin ce maxa suna sonki matan ne suka tsane ki, don haka mace
ba xata iya aurenki ba duk in da kika kai ga kyau sai dai ma ta yi kishi kin fita
kyau, ilimi, hakuri , fara’a da dai sauransu. Saurayinta ko mijinta xai aure ki ya
daina sonta shi kuwa burin namiji ya sami irinki ya aura don haka maxa xasu so ki,
amma baki da bakin jinni, iyayenki ma suna sonki kunya ce da rashin wayewa
kawai saboda basu da ilimi duka.
Wallahi da sun san haka xe faru ba xa su turo ki ba sun gwammace ku koma
xangon daura ku xauna ku duka a bukka. Kaltum waye Mambela? ”
Wannan tambayar madina ta fadarwa da kaltum gaba. Nan da nan ta dago ta dubi
madina har tsawon wani lokaci, tana tunanin mai xurfi inda madina ta ji sunan
mambela. Ta ina xata fara bayar da labarin mambela yadda xata fahimce ta.
Hakika ba don dole da ba xata bada wannan labari ba, saboda yana daya daga
cikin abunda ta tsana wanda bata so ta dinga tuno shi a ranta balle ace tana
furtawa da bakinta. Kaltum ta cije baki yayin da hawaye mai radadi yake xubo
mata.
Ta ce “Mambela! Mambela!! Mambela!!!
Wani dan ADON DAWA ne, wanda na hadu dashi a jim arab kasuwarsu, ranar wata
asabar da yamma. Mambela da abokansa sun kaisu goma sun yi niyyar cutar
rayuwata, yasa abokansa su dauko ni aka suna shirin turmusatsa ni a cikin wani
shago xasu yi min fyade wani tsoho ya xo ya ceto ni ya hana su, ya rako ni har
gida.”
.
ADON DAWA 10
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina ta dafe kirji ta ce “subhanallahi, daman mambela mutum ne! ai mu mun
dauka aljani ne gamo kika yi saboda mun ga kina xabura cikin dare kina ihu kina
kiran sunansa kina fita da gudu, kullum kina kokarin bude kofa ki fice kina cewa
gasu mambela nan xasu kama ni.”
Kaltum ta xabura ta dafe kirji ta tambaya cikin rudani hade da matsananciyar
damuwa t ace, “au har kiran sunansa nake cikin dare, ina fita da gudu!” sai
hawaye ya kece mata.
Madina ta dafa kan kaltum ta girgixa t ace “kwantar da hankalin ki, ba wani abu ba
ne daman haka ne idan mutum ya tsorata da abu. Babu abunda xai same ki in
shaa Allah. Shine ya ji miki ciwo a hannu!”
Kaltum ta soka hannu a cikin rigarta sai ga wani karfe mai kyalkyali kamar axurfa.
Yayin da madina ta bude baki tana dubanta cike da mamaki. Kaltum na danna
gefen karfen sai ga kan wuka ya fito mai tsananin kaifi da sheik ko ba’a fada maka
ba kasan wukar nan fit xata dauke kan kaxa. Madina tad aka tsalle ta ja da baya ta
tambaya cikin gigita. Ta ce “kaltum ina kika sami wuka! Me xa kiyi da ita!”
Kaltum ta tauna lebe, yayin da ta runtse idanuwanta tana rike da wukar tana
jujjuyawa.
Ta ce, “na sami wukar nan daga hannun wata mata a lokacin das u mambela suka
tare ni, na shiga gidanta da gudu sauran matan gidan suka koro ni waje. Na dai yi
mata bayanin duk yanda muka yi da mambela.”
Madina t ace “wa iyyaxu billah, Allah Yayi mana tsari da mambela. Shi ya kwace
wukar a hannunki ya yanke ki!”
Kaltum ta sunkuyar da kai kasa tace “n ice na yanka a gabansu na shaida musu na
yanka kaina ma balle wani, xan yanka duk wanda nake kuma xan iya yanka su
tunda na yanka hannuna sai suka ja da baya suka fasa taba ni.”
Madina ta girgixakai t ace “lallai kaltum kina ganin jarabawa kala-kala daga
Ubangijiki kina yarinyarki karama. Ki daure ki ci jarabawar nan kiga yadda Allah xai
miki sakayya nan gaba. Shawarar da xan baki anan shine sai kinyi taka tsan-tsan,
kid age da addu’a wajen tarkon maxan banxa.
Hakika kyawun da tsarin dirin jikinki tabbas xai ja hankali maxa da yawa.kina ganin
a cikin gidan nan ma kaxaman samarinsu da tsofaffinsu suna xuwa ,ta bayan gida
suna laka ki ta hudar bandakisunaganinki idan kina wanka. Suna leka kowacce
mace amma sun fi leka ki saboda suna sha awar kyawunki.
Kaltum ta dafe kai don takaici, bakin ciki ya hana ta Magana.
Madina taci gaba da cewa “yadda aka yi na gane shine duk sanda kika shiga
wanka saisu xo suyi kamar xasu shiga wanka sai a ce da mutum kaltum tana
wanka,sai kiga daya bayan daya suna fita ashe waje suke fita suna leka cikin
bandaki da naga haka nima sai na bisu baya sai gasu a jikin katako suna kyallara
idanuwansu, nayi musu tas na xaxxagesu na kuma ja musu Allah ya isa amma
yanxu na lura sun daina.
Kaltum nayi miki alkawarin tsaya miki tsayin daka wajen kare mutuncinki kamar
‘yar cikina. Idan ina raye a gidan nan ba xan bari wani da namiji ya nemi ya lalata
miki rayuwarki ba sai dai idan ke kika kai kanki. Wanda nayi imanin ba halinki ba
ne, ki kama kanki, dai –dai da rana daya kada ki bari wani da namiji ya taba miki
jiki. Ko taba jikinki namiji yayi ciki xaki dauka kuma mutuwa xaki yi a wajen
haihuwa tunda ke karama ce. Kiyi taka tsan-tsan da su membela kada ki sake bin
hanyar da kika san suna bi balle ku hadu. Ban hanaki adana wukarki ba don ki
kwaci kanki, haka ban baki goyon baya ki kara yanka kanki ba a banxa, sai dai ki
tsorata su da wukar in har yin hakan xai raxana su su kyale ki. Idan kuwa tsautsayi
yasa kika yanki waninsu da wuka ya ji ciwo akwai matsala saboda tabbas shi da
‘yan uwansa xasu kash ki. Ba sai sun kai ki kara hukuma ba, dan haka nake jin
tsoran rike wukar nan a gare ki. Da akwai yadda xan yi kaltum da sai in hana ki fita
bara kwata-kwata ma in dinga xuwa ina samo mana abuda xamu ci, to nima wata
rana dakyar nake samu sai na yini ina yawo ban samu ba. Shawarata ta karshe a
gare ki it ace ki sawa ranki kece uban kanki da kaki anan, ki sawa ranki idan kina
bukatar wani abu anan ke xa ki fita ki nemo babu wanda ya ajiye ki don haka bana
so ki xama wawuya a cikin mutane. Kin xama juji kowacce bola ke ake xubawa
dole ki kwaci kanki.
”kaltum ta tsurawa madina ido tana kallonta da alama bata fahimci abunda take
nufi ba.
Madina ta ce “ina Magana akan ‘yan dakinmu su rakiya da suke takura miki,koda
yaushe suna xagin ki kina kuka. idan sunyi miki kiyi musu sai ki sami sauki wata
matsala daga cikin matalolin da suka addabe ki. Xan iya faduwa na mutu a yanxu
haka, ni mai rama miki sai kiyi yaya kenan! Don haka kiyi maganin wannan
matsalar dakanki sai ki ji da matsalolin su mambela, su kuma Allah Ya fi su shi xe
yi miki maganinsu babu wanda ya gagari Ubangiji. Babu yadda xa’ayi a waje a
takura miki a gida ma a hana ki sukuni ina xa ki saka ranki kenan. Ka da kiyi
tsokana idan ba’a taba ki ba, kada ki taba kowa ki girmama duk wanda ya fi ki idan
ya kamata, nasan kina sallah akan lokacinta duk tsananin ciwo ko yunwa nayi miki
wannan shaidar bakya kin yin sallah sai dai kina da karancin yin addu’a. ki yawaita
addu’oin neman tsari daga sharin mutum da aljan, yaro ko babba, dare da rana. Ki
yawaita addu’a samun sauki a lokacin kunci, sannan ki ji tsoron Ubangijin ki a duk
inda kike ki san Allah Yana ganinki. Ki guji xina, ki guji xina kikiyaye kusantar xina
ko talauci xai kasha ki balle Allah ba Ya hana duk wanda ya fita nema. Yin haka
Allah xai xamanto jagoranki.”
Madina na rufe bakinta sai kaltum ta rushed a kuka ta rungume ta. Su dukka kukan
suke yi ba kakkautawa aka rasa mai lallashin wani, har xuwa lokaci mai tsawo
sannan kaltum ta janye jikinta daga jikin madina ta koma ta xauna. Ta sharce
hawaye ta dubi madina.
Ta ce “kina fada min gaskiya anty, kina sona, nayi alkawarin xan bi duk shawarar
da kika ba ni kin xama uwata, ke ce ubana, ke ce kika gaji daddy wanda yake
share min hawaye. Anty madina, xan so in ji labarinki kema, in ji asalinki, da dalilin
fitowar ki daga kasarku xuwa wannan kasar.”
Madina tayi murmushi t ace “so kike kiji labarina nima! Me yasa ki ke so ki ji
labarina! Hakika labarina ya hada da abun mamaki mai firgitarwa. Xa ki ji
abubuwan ban tausayi da yawa, abubuwan da baki taba jib a balle ki gani a
rayuwar ki”.
Kaltum ta gyara xama t ace “ki bani labara anty madina.”
BABI NA SHIDA
LABARIN MADINA
Madina ta dubi kaltum yayin da take Magana cikin muryar kuka amma ba hawaye
sai dai idanuwanta sun kada sun yi jawur da alamar tashin hankali a tattare da
abunda take shirin fada.
Ta farad a cewa “kaltum, xa kiyi mamaki idan n ace miki ni inyamura ce ko!”
Kaltum ta dafa kirji t ace “inyamura!”
Madina ta gayada kai tace “eh inyamura ce, inyamurar ma ba musulma ba, wacce
bata taba sanin akwai wani addini da ake kira musulunci ba. Ni yar asalin garin
Onitsa ce. Kaltum, ban taba xuwa makarantar boko ba, primary balle secondary,
amma a cikin ikon Allah ni ma’aikaciyar lafiya ce (nurse) a babban asibitin
kaxaure.”
Hakika kan kaltum ya daure yayin da al’ajabi gami da miliyoyin tambayoyi suka
feso a cikin xuciyarta. Ta tamba ya cikin mamaki “ta yaya!” madina tayi ajiyar
xuciya t ace “shine yanxu nake shirin in fayyace miki komai. A da ina tunanin
karancin shekarunki ba xai bari ki fahimce nib a amma na lura kaifin hankalinki da
nutsuwar ki xa su sa ki gane, tunda kin dandana axabar rayuwa kamar ni.”
Madina ta mike ta shiga dakinsu, ba jimawa ta fito dauke da katon kwali wanda
take kwana akai ta riko hannun kaltum ta tashe ta tsaye suka fice kofar gida, suka
samu inuwa suka xauna akan kwalin su dukka.
Madina tayi murmushi t ace “nag a rana ta iske mu a tsakar gida, shi yasa na dawo
da mu inuwa saboda mu ji dadin labarin.”
Tana rufe bakinta mai ruwa ya kwada talla akan keken jakunansa. Kaltum tana
daga ido sai tag a wannan tsohon ne mai sayar da ruwan nan daya taba bata jarka
daya ta ruwa kyauta. Sai suka yiwa juna murmushi a lokaci guda. Ya fada cikin
harshen larabci y ace “yarinya ga ruwan dadi.”
Ta ce “babana ina jin kishir ruwa sai dai yauma bani da kudi.”
Ya ce “yauma dauko bokiti in xuba miki jarka daya kyauta saboda nima Allah Y
dube ni.”
Kaltum tayi wuf ta mike da murna ta shiga gida ba dadewa sai gata dauke da
bokiti hannunta, ta xo ta ajiye a gabansa, yayin day a tittila mata ruwa garai-garai
mai sanyi cikin bokiti. Madina dai ta tsura musu ido tana duban bakinsu sai magan
suke bata san mai suke fada ba,