Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
kayi da gaske zaka tantance wannan bakar patace ko balarabiya sai kaga kamar
inka mata hausa zata fita da gudu tsabar firgita idan ka kalleta sae ka sake kallonta
tsabar kyauwun fatarta duk da akasarin shigarta na
dugowar rigace da dankwalin abaya wani
lokaci ma hijabine har kasa sbd mambela yana kishinta idan yaga kallon da ake yimata
yayi yawa sae yace ta saka nikafi.
da sukayi hutun makaranta sae shirya zuwa nigeria ganin gd sukaci sa a kuwa aranarda
suka iso kano ranar Madina ta haepi santalelen danta mae kama da babarsa abba, ranar
suna aka radawa yaro sunan kakan sa da babansa wato Tukur, ake kiransa da Khalifa
Abba Tukur.
kaltum da mai gidanta sunyiwa Madina Kaya iri iri da kudi masu yawa haka tayiwa
iyayenta da kannen ta tsaraba kala kala da akwatuna baya ga kudi masu yawa data
rarraba musu, sofi da 'yayanta mata kuwa harda sarkokin gwal da en kunnen su ta hado
musu.
satinsu kaltum uku a kano suka tapi Abuja gdn alh Adnan, shida matarsa sun karbesu
hannu bibbiyu sunyi musu hidima sosae suma kuma sun kawo musu tsaraba mae yawa.
satin su daya suka tapi sudan a bur sudan ma satinsu uku agarin en ADON DAWA, garin
ya gyaru anyi matukar sumun cigaba sarki yayi matukar wayerwa da talakawansa da
kae suna cin kudinsu yanzu suna sayan kayan more rayuwa sun fara gina gidajen siminti
suna dinka suturu masu kyau ankae musu ruwan famfo da wutan lantarki gami da titina
da makarantu duk acikin shekara guda.
su kaltum sunyita rabon tsaraba babu adadi, kaltum takai ziyara gidansu na da taga
dakunansu har yanzu kuwa akwae saura daga ire ire mutanen tawagarsu wadanda zama
Ya Mike sukayi aure suka hayayyafa sun ganeta kuwa kamar yanda ta ganesu tayi musu
kyautar girma sunyi farin ciki,
kaltum bata manta da abokinta ba Karim mae kamun kifi yana nan a inda tabarshi ya
auri yar ADON DAWA har sun haefu yayi farin ciki da ganin kaltum musamman data yi
masa kyautar kudi da kaya mae yawa,
kaltum ta zagaya bakin kogi enda suke zama sannan ta zagaya garin Jange daga can
suka shiga Jim Arab kasuwar yan ADON DAWA kae tsaye ta tunkari rumfar tsohon nan da
ya kwace ta ahannun mambela da abokansa ta
tarar bayanan sae dansa ya shaeda mata Allah Ya yi masa rasuwa, saeta bawa dansa
kudi tace mahaefinka ya taemake ni bazan manta da shiba zan zamo mae yi masa
addu'ah duk sanda na tuna shi, Allah Ya yi masa rahma amin.
suna tafiya acikin tsaleliyar motarsu mambela ke tukawa a hanyarsu ta tafiya Khartoum
suma takae musu ziyara taga yan gidansu suna nan kamar yadda ta barsu taga malam
Abdulkadir da matansa ta kuma gwangwajesu da kyauta daga nan aka rakasu
gidan Fatsuma da Musa a can wata unguwa suke nesa, sunyi aure suna zaune lafiya
harda 'yayansu guda uku. fatsuma tasha tsalle da murna da taga kaltum da kyar ma ta
ganeta sbd canjin da ta samu sae alokacin take ta bawa kaltum labarin mambelane ya
musu komae na aure hatta gidan nan shi ya kama musu ya biya musu hayar shekaru
biyu sanan ya ba su jari.
kaltum ta sha mamaki don ko kadan bai taba fada mata ba ya dai ce mata fatima da
musa sun yi aure a Khartoum.
agidan fatima kaltum da mambela suka kwana dayake gidan dakuna 2 ne kuma basu da
talauci suna rayuwa cikin rufin asiri, washegari suka koma bur sudan bayan sun ambulo
musu makudan kudi.
duk inda kaltum taje saetayi kuka saboda tana tuna baya tana tausayawa wadanda har
yanzu suke cikin wannan rayuwa Allah bae yanke musuba tukunna.
hutunsu ya kare sae suka koma Dubai sukaci gaba da rayuwarsu,
lokaci daya mambela ya kira kaltum ya danka mata kudinta dala dubu goma da alh
Adnan ya bata tun lokaci aurensu ya kara mata da wasu yace ta kira iyayenta a waya
tayi shawara dasu ta zabi kasuwancin da zata dinga yi tsakanin Dubai da zuwa Nigeria.
kamar da wasa suka fara yi da Madina tana turo da kaya tana sayar mata a Abuja sae
malam saleh ma ya ke karbar kayan yana rabawa yan kasuwar sabon gari da kasuwar
kwari bayan sati biyu sae su hado masa kudi ya dauki ribar sa ya turo mata uwar kudinta
da ribarta kafin kace kwabo kasuwanci ya Mike suna samun alkhaeri, gaba dayansu
kannen kaltum sun warware sun goge sunyi kyauwun gani suna karatu a makaranta
masu kyau sunyi sallama da talauci a rayuwarsu.
Madina kuwa haehuwace ta mike kafin ta yaye khalifa ta sami wani cikin ta kara
haehuwar namiji sae suka saka masa sunan Adnan sbd alkhairan da alh Adnan yayi
musu.
yaji dadi matuka alh Adnan da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar
mashkur ta haehu shima da namiji aka saka masa suna Adnan ake kiransa Amir, sae ga
waya daga Dubai aka shaeda wa alh Adnan kaltum
ta haihu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy.
sae alh Adnan yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu
basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da
siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun
gamsu ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta
taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar
suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da
uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka
kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
.
ADON DAWA 50
.
TRUE LIFE STORY.
.
da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar mashkur ta haehu shima da namiji
aka saka masa suna adnan ake kiransa Amir sae ga waya daga Dubai aka shaeda wa alh
Adnan kaltum ta haehu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy, sae alh Adnan
yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu
basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da
siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun
gamsu ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta
taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar
suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da
uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka
kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
haka ' yayanta Abdul Malik da Abdul hakim sun kammala karatun digiri dinsu Abba ya
samar musu da aeki, anan Abuja suke rayuwarsu yayindaduk wanda yasan shahida
abaya zaeyi wuya yaganeta yanzu, Abba ya dauketa yadawo da ita gidansa yace shi zae
riketa ko bayan ran Madina zae dau nauyinta harsae ya aurar da ita,
tashiga jami'ar A.B.U zaria tana karanta medicine.
Allah mai kyauta a duniya mae azurta wanda Ya so a lokacin da Yaso, tsarki ya tabbata
ga Ubangijin talikae.
misalin karfe tara na dare mambela ya dawo
daga wajen aeki daman yanada nasa makullin don haka sae ya bude kofar gidan ta baya
ya shigo kamar yanda ya saba ganin kaltum a falo tana zaman jiransa yau sae bai ganta
ba sae yayi tunanin ko tana daki ya leka dakinta yaga babu kowa daddy ne kawae ke
kwance a dan gadon sa yana barci saeya leka bandaki batanan sai yace aransa to tana
dakinta abun mamaki anan ma batanan ya leka kicin babu kaltum babu dalilin ta sai yaji
hankalinsa ya tashi nan da nan ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya fara kiranta sai ga
wayarta akan kujerar falo ba ta tafi da wayar ba, kamar wanda akace masa ya leka
barandar waje sae kuwa ga kaltum tsaye ta rike karfen baranda tana kallon kasa, ya
sadada yaje ta bayanta ya rufe mata ido ta zabura ta waewayo a firgice kamshin turaren
jikinsa ne ya tabbatar mata da cewa rabin ranta ne mambela sae su dukka sukayi dariya
yayi mata rada a cikin kunnenta cikin wata tattausar murya cikin harshen hausa,
kaltum tunanin kike yi anan?
akwae abun da na rage miki a rayuwa wanda
yake damunki baki fada min ba?
ko akwae wani hali wanda ba kyaso in daina?
kada ki boye min komae my love.
Sai tayi murmushi ta lumshe ido ta dubeshi sannan ta nuna masa kasa tace duba kaga
Dubai da daddare haske tar kamar da rana sbd fitilu duba kaga kololuwar benen mu
hawa harna ashirin, duba kaga motoci suna yawo a kwalta tamkar tururuwarda suka biyo
layi haka muke hango su daga sama, ga teku mae fitar da iska lafiyayyiya yana kusa da
mu saena tuna da Bur Sudan a inda muke bara muke kwalfo ruwan gishiri muna wanka
da wanki muna barar kifi, yau gamu a Bur Dubai wancen duhun ya zama haske
takalmanmu da yake tsinkewa mu daure da leda saboda yashi yanzu anan sae dai
motoci su zagaya damu tsakaninmu da ruwa sai dai mushiga jirgin ruwa ta tuka mu
shakatawa, gasashen kifi a faranti turawa zasu kawo mana cikin ladabi su ajiye mana.
Shi ne nake mai godiya da Allah da Ya yi mana wadannan sauyi. Duk inda ka ji balarabe
ya ce bur, to tsallake ruwa ne, don haka nake godewa Allah da Ya rubuto min rayuwa ta
a kusa da ruwa inda na ke shakar sanyayyar iska wacce take fitowa kai tsaye daga cikin
ruwa duk a cikin ni'imomin Ubangiji ne. Maganin yunwa da talauci ruwa ne duk sanda
aka rasa ruwan sama an rasa amfanin gona, idan zuciya tayi zafi, masu iya magana
cewa suke yi, "a yayyafa mata ruwan sanyi."
Mambela ya tuntsure da dariya ya ce, "duk me ya kawo wadannan maganganun? "
Kaltum ta yi fari da ido tace, "idan Allah Ya yi wa mutum wata ni'ima ya kamata ya gode
ma Sa, gobe se Ya kara masa wacce ta fi ta da."
Mambela ya gyada kai, yace "gaskiya ne sai wace ni'imar Ubangiji Ya yi miki bayan
wannan? "
Kaltum tayi dariya ta langwabar da kai ta kashe murya ta ce "daga cikin ni'imomin da
Allah Ya min, Ya azurtani da miji na gari, mai son ya ga farin ciki na, sai nima Ya jarabe ni
da tsananin son sa har na ke ji a jiki na, ba zan iya rayuwa ba idan ba ya nan.
Idan baka manta ba, a shekarar da ta gabata, tafiya ta kama ka zuwa Abu-dahabi har ta
tsawon KWANA ASHIRIN DA HUDU, sai na ji na damu, tun ina daurewa har ya kasance
ruhina ya tafi Abu-Dhabi ranar da ka yini baka kira ni ba, nima na rasa ka a waya, sai na
fara tunanin me yasa mambela be damu da ni ba?
Sai na fara tunanin ko dai, GANGAR JIKIN SA NA AURA, na fashe da kuka na dauki gyale
na zan fice daga gidan don banga amfanin zamana ba inason maso wani har naje kasa
saina tuna YARENA ADDININA bazan iya fita bada izinin mijina ba idan wani abu ya
sameni a titi INA RUWAN WANI babu wanda yasanni bubu mai taemakona don haka na
dawo gd na zauna nayi tagumi ina tunani naga dai KAI KAFI CANCANTA ka ce to ni daga
cikin wannan hali dana shiga kuma kai kadai nakeso a rayuwa tamkar na taabu na shiga
daki na canja kaya na caba ado da wannan tsadaddan leshen daka siya min na saka
gyale da takalmi mae tsinin gaske, baya ga jan baki da hoda dana rambada na dubi
kaena a madubi naga nayi kyau matuka na juya zan fita falo a tunanina kana can in
nuna maka kwalliyar sai na tuna ashe bakanan sai nayi turus nayi kwalliya a dawa kenan
babu mai gani na, wannan shine ADON DAWA sai na sulale na fada akan gado na goge
kwalliyar na rusa kuka mai tafe da hawaye sai na naji wayata tana ruri a falo na ruga da
gudu na dauka sai na duba nace a raina mambelane ina amsawa sai na jika kace ke
bude min kofa na shigo gani a bakin kofa,
ina bude kofa sai na ganka, dan farin ciki bansan sanda nayi ihu nayi tsalle ba ina
maraba da dan ADON DAWA.
mambela yayi dariya yace lalle kin iya hausa bayanan naki sunyi min tsauri ashe har
yanzu da saurana ban koyi hausa ba dole sai na nemi sabon littafin nan wanda zai fito
kwanan nan acikin 2011 din nan duk KYAN TALKALMI a kafa ake takawa don in sake
koyan hausa.
sai dukka suka tuntsire da dariya suka kama hannu suka shiga cikin gida asuba ta gari
kaltumbela.
.
KARSHEN LITTAFIN ADON DAWA
ALHAMDULILLAHI,
.