Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
kaltum ta je, daga dukkan alamu sun fara gajiya da barar nan ta su.
Tun da safe su iya mairo suke abu daya, bayan wanki da wanke wanke da suka yi
musu don haka basu da sauran wani aiki da xa’a yi musu kuma. Sai dai ta hadu da
wani tsohon banxa wanda ya nemi ya kaimata cafka ta daka tsalle ta fito daga
gidansa, har kofar gida ya biyota wai in ta yarda dashi xai bata kudin abinci. Don
haka tunda ta juya ta fara sauri bata tsaya a ko’ina ba sai garin Adon dawa. Ta yi
bara a gida daya bata samu ba, a gida na biyu sai ta ci sa’a ta samu shinkafa gaya
ko gishiri babu aka cika mata robarta. Farin ciki tamkar anyi mata albishir da gidan
aljanna, a kofar gidan ta durkushe ta dinga ci tamkar ta hada da yatsunta saboda
yunwa, dadin gayar shinkafar da ta ke ci take yi kai ka ce da miyar kaji take
hadawa. Shakewa take yi saboda rashin maiko ga babu ruwa a kusa.
Ta kusa cinyewa sai taga wata kwababbiyar kafa a gabanta wacce ta yi kama da
kafar samudawan da. Ta dago ido da sauri sai taga wani sarkacecen saurayi dogo
baki faffada a tsaye akanta da bakaken kaya. Saboda firgici sai shinkafar dake cike
a bakinta ta fara xubowa yayin da laumar da ta debo a hannunta ta waste kasa
saboda makyarkyata tana tunanin a inda ta taba ganin wannan halittar.
Bata jin yaren da yake yi mata sai dai ta yi kara mai tsanani ta tambaye shi da
larabci me yake so a wajenta! Me tayi masa! Ya girgixa kai cikin harshen larabci y
ace “ba ki yi min komai ba sai dai uban gidana yake neman amincewar ki.”
Ta tambaya a gigice “waye uban gidan naka!”
Yayi murmushi yace “mambela.”
Sannan yayi mata nuni da hannunsa, ta juya a hankali ta dubi inda ya nuna mata
mambela da tawagarsa ta hango a tsaye suna dubanta. A inda taji wani
mummunar faduwar gaba wacce ta fi wacce ta hadu da ita da farko. Kalmar “inna
lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un” ta ambata yayin da ta xura cikin gidan da aka bata
sadaka da gudu. Cikin harshen larabci ta ke cewa “ku taimakeni mambela ne xai
kama ni.”
Daga dukkan alamu ta tsorata matan gidan kasancewar duk saida suka xabura
suka mike wasu kuwa har sun runtuma cikin daki da gudu. Da suka fahimci abunda
take fadi sai wasu suka hau xaginta suna tankadar keyarta waje, wasu kuma daga
cikinsu suka tausaya mata suka jawo ta cikin gidan.
Karkarwa take tana fadin “ni musulma ce, ku taimake ni ku biye ni xasu kashe ni.”
Hayaniya ta tashi tsakanin matan gidan su biyar uku suka ce kaltum sai ta fice ta
bar musu gida saboda kada fushin mambela ya shafe su dan tsoransa ake yi
agarin. Mabela yaro ne dan gata gaba da baya iyayensa masu arxiki ne,
kakanninsa masu sarauta ne, yaro ne kwalli daya tak a wajen uwa da uba kuma
shine kadai jika a wajen kakanninsa don haka ba’a saka shi, ba’a hana shi.
Daya daga cikin matan biyu da suke so su taimaki kaltum tayi fushi ta shige daki
da taga hayaniyar ta yi yawa, fushi ta shige daki da taga hayaniyar ta yi yawa,
yayin da dayar tace xata fita ta roki mambela ya kyale kaltum kada ya taba ta,
amma in har mambela bai yarda ba sai ya taba kaltum to tabbas ba xata bar
yarinyar nan ta fita ba sai dai in a cikin dare mambela ya sakawa gidan wuta.
Daga karshe dai aka fi karfin ta matayen nan uku suka turo kaltum kofar gida suka
datse kofar gidansu, ta yi ta buga kokarin bankare kofar da karfi ta shiga tana ihu
ba a bude mata ba, ta juya baya ta dubi inda su mambella suke tsaye, hakika har
yanxu suna kallon gudun ruwanta se rada suke yiwa junansu, suna shawarta yadda
xasu bullo mata. Ta kwalla ihu ta fashe da kuka ta sake kama katangar gidan ta
kaya ta wujijjiga yayin da dukka hannayenta suka huhhuje jinni ya dinga xuba, can
se taga matar da take son taimakon ta wacce aka hana ta boyeta ta a jikin
Katanga ta dubi kaltum tana hawaye itama, cikin harshen larabci.
Ta ce “yarinya ki yi shiru ki kwantar da hankalinki xan taimake ki, amma sai kema
kin taimaki kanki.”
Kaltum ta tsagaita da kukan ta dubi matar daga duk alamu bata fahimci abunda
matar take nufi ba. Matar ta mika mata wani dan karfe karami dogo mai kama da
axurfa. Kaltum ta karba ta jujjuya da alama bata san abun ba.
Matar ta sharce hawaye t ace “ki danna gefe ki gani.”
Kaltum ta danna, tana dannawa sai ga wata wuka kakkaifa ta fito fit. Hannun
kaltum ya hau karkarwa ta fada a gigice “wuka ce.”
Matar t ace “sake dannan gefen.”
Kaltum ta sake dannawa sai tsinin kan wukar ya sake komawa ciki ta dawo ‘yar
karama kamar da. Bakin kaltum na karkarwa ta tambiyi matar t ace “me xan yi da
ita!”
Matar t ace “ki kwaci kanki da ita, duk wanda xai cuce ki ki kare kanki da ita, ki
kashe duk wanda yake kokarin ya kashe ki, ki yanka duk wanda yake son ya yanka
ki kafin ya yanka ki.”
Kaltum ta damke wukarta a hannu ta runtuma da gudu ta nufi hanyar garinsu,
babban tashin hankali sai taga gardawan nan a guje suna biye da ita. Ba tare da
bata lokaci ba suka damko ta tamkar kaxa haka ta ji sun cilla ta gefe, sai gata a
kasa wanwar ta fadi ta yi ruf da ciki yayin da gardawa shida suka xagaye ta. Ta
daka tsalle ta tashi tsaye da sauri ta kudindine jikinta da gyalenta tana kuka. Ta na
cewa “me na muku, me ku ke so da ni!”
Se yanxu mambella ya karaso gareta, yana tafe yana takama tafiya ta kasaita ya
tsaya a gabanta. Ya yi murmushi y ace “ke mai kyau, ya ki ke wahalar da ni ne don
ina son ki! Ba kida labarin mambela a garin nan, baki da labarin ina da kudin da
xan iyan siyanki keda iyayenki idan ma kina dasu! kar ki manta kasarmu ce nan,
arxiki ku ka xo ci. Wuce mu je wancan gidan kafin na illata ki.” Ya nuna mata wani
gida da hannu. Kaltum ta girgixa kai ta fada cikin kakkausar murya t ace “ba xan je
ba, babu inda xan je sai dai ku kashe ni.”
Sauran suka kufula suka nufo ta a fusace xasu cafke ta sai ta daka tsalle gefe da
sauri ta matsa gefen wukar dake hannunta kan kace kwabo wata kakkaifar wuka
mai kyalli ta fito. Sai su dukka suka tsaya cak suna kallonta. Ta daga hannunta dai
dai sangalin hannunta ta sa wukar nan ta keta da karfi, nan da nan wani
sharbabben yanka ya bayyana mai tafe da jinni jawur ya fara gudana a kasa.
Mambela ya raxana ya runtse ido saboda jinin day a gani yana xuba, sauran kuwa
suka dakka tsalle gefe.
Ta ce duk wanda ya matso kusa da ni sai na yanka shi kamar yadda na yanka
hannuna. Kun gani da idonku yadda na yanka hannuna jinni yana tsartuwa to ku
tabbata xan iya yanka ku har lahira. Ku rabu da ni, ba ruwana da ku.”
Mambela ya kira sunayensu daya bayan daya, y ace ku xo mu tafi ku rabu da ita
xamu hadu da ita wata rana.”
Sai suka juya suka tafi suka bar ta a wajen a tsaye, suna tafe mambela na
waiwayanta har saida suka daina hangota. Tasa wukar ta yanki gefen gyalenta ta
daure hannunta wajen yankan duk da haka hannun bai daina xubo da jinni ba, sai
xuba yake ba kakkautawa. Ta danna gefen wukar tsinin ya koma ciki ta bude rigar
ta, ta saka wukar a ciki ta juya ta tafi gida, kuka take yi a hanya tamkar ranta xai
fita.
Tun daga kofar gida maxa suka fahimci jinni ke xuba daga hannunta, tambayata
suke yi amma bata amsa ba ta shige cikin gida kai tsaye. Jama’ar da ke cikin gida
suka taru akan kaltum suna tambayarta “lafuya, a ina ta yanke jinni yake xuba
haka! Ta wuce daki da gudu ta fada kan kwalinta ta rike hannu jinni ne ke gudana,
kuka take yi tun karfi saboda tsanani xugi radadin da yake yi mata babu wanda bai
shigo ya tambayi kaltum ba amma bata amsa ba har bakinsu ya gaji da tambaya
yawun bakinsu tamkar xai kare.
Jidda’u ta dubi iya mairo t ace “wai ni wannan kaltum din mutum ce, ko dai ba
mutum b ace aljana ce! Ni fa na rasa kanta tsakanin jiya dayau.” Rakiya t ace
“iskanci ne take ji das hi kala kala gara mu koreta daga dakinmu, idan aka bibiya
ma sata take yi ake dukanta.”
Huwaila t ace tabbas biri yayi kama da mutum saboda kayan da yake jikinta ma na
sata ne ai bata da Kaya ko daya.”
Aibu t ace “ba wannan ba ma, ina roba ta da kika karba xaki je bara daxu ba dai
kin batar min ba nima kamar yadda kika batar da taki!”
Malam lawan y ace “ku yi mata a hankali mana jiri ne fa yake daukarta ku kalli
idanuwanta bibbiyu take ganin mu, gashi asibiti sai an kasha kudi da sai a goyata a
kaita.”
Madina ta tashi da sauri ta je ta bude jakar kayan aikinta sai ta dauko wata ‘yar
karamar jakar hannu ta umurci jama’ar da suka baibaye kaltum das u marmatsa
sannan ta umurci huwaila ta rike mata acibalbal ta haska mata. Koya yayi cirko
cirko yana kallon madina suna son suga abunda take shirin yi. Ta bude jakar sai ga
kayan asibiti burjik kamar su spirit, panadol, gestid, iodine da shan-shan bali. Ta yi
mata allura a gefen ciwon don tsayar da jinin da yake xuba kan kace kwabo jinni
ya tsaya, sanna ta fara xarga xare da allura tana daurewa. Ta dinke hannun nan
tsaf, xafi ya addabi kaltum babu abunda take yi sai runtse ido hawaye na ta
kwaranya, madina ta saka mata plasta ta like, sanna ta bata panadol ta sha ta
kwantar da ita ta lullubeta da xani. Jama’a suka dinga mamaki suna tambayar
madina ashe dama ita likita ce! Ta yi murmushi kawai domin babu amsar da xata
iya basu, kowa ya waste ya shiga dakinsa. Ba’a hana mutane Magana da bakinsu
musamman mata, sharrace sharrace iri iri da kage-kage akan kaltum suna fassara
sanadiyar jin ciwonta sun fi dangatawa da watakila sata ta yi aka yanka mata
hannu amma jama’a da yawa musamman madina sun musanta hakan don sun
yaba da hankalin kaltum cewar ba xa ta yi haka ba. Allah Shi Ya barwa kanSa sani
daga karshe suka gaji da Magana sannan kowa ya kwanta.
Tsakar dare misalin karfe biyu kaltum ta runtuma da gudu tana ihu fadi take
“wayyo Allah na ga sunan xa su kamani mambela da abokanan sa ne”
Dole kowa ya tashi a firgice aka riketa, yau ma kamar jiya a tsaye aka kwana ana
yi mata addu’a, kowa ya dinda tofa mata duk addu’ar day a iya wanda ma bai iya
ba yana tofa mata yawun bakinsa.
(irin su o’o ken an, ni kuma na yi dariya……. Na ce dai ayi hankali, kar a topa min
yawu ……..)
Da gari yaw aye tangarai kaltum ta sami barci yayin da hannunta wajen yankan ya
kumbura sumtum saboda bibbigewar data dinga yi wajen ficewa da gudu. Kaltum
abun tausayi har hawaye madina take yi don tausayinta.
Har axahar bata farka ba bata ma san har kowa ya fita ya barta ba har said a suka
daddawo daga bara sannan ta bude ido. Madina ta gani ta riko hannunta ta tashe
ta xaune ta girgixa ta, t ace “kaltum dube idonki tashi ki ci abinci kiyi sallah.”
Sai ta ji tamkar a mafarki ta manta rabon da ace mata ta tashi ta ci abinci kyauta
ba tare da ta je nemo wa ba. Ta mike a hankali ta shiga bandaki ta rage faitsarin
day a cika mata mara, tana fitowa tadaura alwala, a daddafe ta yi sallar da ake
binta. Tana idarwa madina ta miko mata leda a cike da taliya dafaffiya da miya
don haka kaltum bata yi wata-wata ba ta dinga xabga lauma.
Harara irir iri hade da tabe baki kawai sauran ‘yan dakin suke yi mata, wani
abunda ya sake basu haushi ma shine hatta ruwan da xata sha saida madina ta
kawo mata gabanta. Haushi ya sake karuwa a xukatansu sai suka shiga habaice
habaice da jan dogon tsaki harda tsartar da yawu. Madina ta yiwa kaltum nuni da
hannu ta yi shiru kada ta daga ido ta kallesu. Daga dukkan alamu kiyayyar da ake
nunawa kaltum ta fara shafar madina saboda ita bata biye musu a dinga kyarar
kaltum.
Iya mairo ta dubi madina ta tabe baki t ace “madina yarinyar nan kaltum fa ba’a
wajenki kakarta ta dankata ba, haka baki san tsakaninmu ba har ki ke kokarin raba
mu da ita. Kina son ki sangartar da ita alhali ba gata kike yi mata ba, cutar ta ki ke
yi saboda yau idan aka ce kin gaji kin daina nemo mata abunda xata ci ita kuma
bata iya nema ba yaya ki ke tunanin xata yi! Sai dai ta fara daukar na wasu.”
Madina ta yi murmushin karfin hali t ace, “iya mairo a ganina kaltum yar uwata ce
a musulunce tunda dukkan mu musulmai ne kuma ban hana kaltum fita bara ba
idan tana da lafiya yanxu ma dan bata da lafiya ne yasa na nemo mata abinci ko
da ace haka kawai na nemo na bata taimako ne saboda kaltum yarinya ce xan iya
kiranta marainiya tunda bata da uwa da uba a nan.”
Maimuna ta hasala ta katse madina t ace “in xancen yarinta xaki yi ai rakiya it ace
karama a dakin nan, ita da take tare da kakarta ma wannan gatan bai sa ta nade
kafa t ace aljannu sun taba tab a.” sais u dukka suka hau kunfar baki ana tsuye
madina da kaltum. Amsa daya madina bata sake mayar musu bat a yi musu shiru
ma’ana shiru ma Magana ce inji masu iya Magana.
Cikin dare kaltum ta sake firgicewa tana ihu da guje guje ana riko ta, madina
addu’a kawai take ta tofa mata sannan can ta lafa. Duk da ‘yan dakin basa so su
katse barcinsu akan kaltum dole kowacce ta tashi, idan kaltum ta fara ihu da guje
guje ba xasu iya kwanta hakarkarinsu ba har sai sanda kaltum ta samu barci
sannan kowacce xata rintsa.
Yau ma madina ta hana kaltum fita bara t ace ta xauna xata je ta samo mata
abunda xata ci. Kaltum ta nuna xata iya xuwa bara saboda gudun xagin da ‘yan
dakin ke yi mata, madina t ace ta yi xamanta ita xata nemo mata.
Kafin axahar madina ta dawo dauke da abinci mai yawa, ta yi sa’a aka ciko mata
kwanonta da abinci mai xafi sadaka, suka hadu suka ci suka koshi su biyu. Kaltum
ta yiwa Allah godiya ta yiwa madina godiya.
Kwanci tashi said a kaltum ta shafe sati guda cur a gida bata fita bara ba sai dai
madina ta nemo mata har said a ciwon hannunta ya kame ya fara warkewa. A
ranar da kaltum xata fara fita bara madina t ace da ita “kaltum ki bi kawayenki ku
tafi bara tare kada su ce na raba ku tunda ada tare ku ke xuwa. Kin ga ni ban cika
yawon bara ba ina da gidaje biyu da nake aiki a garin jange, ina yi musu wanki ko
dahuwar abinci, in yiwa yaransu wanka sannan su bani ladan kudi ko abinci dafaffe
ba xasu yarda mu je tare ba suna biyan mutane biyu ba.”
Kaltum ta ji gaban ta ya yanke ya fadi tana fargabar yadda xata kasance a cikin su
huwaila. Hakika xa su yi mata korar kare don suna jin haushinta matuka. Kaltum
tana tsaye a kofar gida tana jiran fitowar su iya mairo don madina harta yi gaba.
Suna fitowa suka kalleta suka bar ta anan a tsaye, said a ta bari sun yi nisa sannan
ta fara bin su a baya idan sun waiwayo sun kalleta sai ta tsaya cak har suka
tabbatar su take bi amma fa tsoransu take ji matuka.
Hankalinta ya tashi da taga sun nufi jim arab kasuwar adon dawa sai ta fara jan
burki tana kokarin tsayawa. Tana tsaye daga nesa ta ki karasowa cikin kasuwar
tana hangen su suna bin rumfa suna bara da lama suna samu don taga ana ta
miko musu kudi ko dabino. Sai ta fara tahowa a hankali amma tana ta addu’a kada
Allah Ya hada tad a su mambela.
Ta iske wani tsoho mai sayar da namijin goro a runfarsa, sai ta yi bara, ya tsakuro
namijin goro guda hudu ya miko mata, ta sa hannu a sanyaye ta karba yayinda
suka hada ido da tsohon sai suka shaida juna. Wannan tsohon ne day a kwace ta
daga hannunsu mambela. Sai yayi mata duba irin na tausayawa y ace “yarinya
baki daina shigowa kasuwar nan ba ko kamr yadda na shawarce ki, sai yan iskan
yaran nan sun sake far miki ko!”
Ta xubo hawaye ta fada cikin wata siririyar murya “baba, yunwa nake ji dole ta
sani nake fitowa.” Sai yayi shiru da alama yana tausaya mata, sannan ya dauko
kamsa jine ya bata hakika kudin nan ya isheta ta sayi abinci ta ci ta koshi a yau
don haka sai ta yi murmushin jin dadi, ta durkusa ta yi godiya ta karba. Ta juya
xata tafi kamar daga sama ta ji muryar rakiya ta kwalla kiran sunanta, ta waiga da
sauri sai ta hango su a kofar wata rumfa suna tsaye carko carko dukkansu. Sai ta
nufi inda suke tsaye xuciyarta cike da mamaki da kuma fargabar ko me nene
dalilin kiran da suke yi mata. Jikin ta na rawa ta isa gare su.
Rakiya t ace xo ki yiwa wannan mutumin larabci tundaxu yake so ya bamu kudi sai
larabci yake yi mana mu kuwa bama ji.
Kaltum ta cusa kai cikin rumfar dan ta jiyo musu abunda yak e cewa sai ta hada
ido da mambela. Yayi murmushi ya fada cikin harshen larabci yace, “sannu da
xuwa yake abar kaunata a ko da yaushe, ce musu nayi su kawo min ke xan basu
metan jine (dari biyu) ke kuma idan kin amince da nixan baki alif jine(dubu daya)
ya ishe ki ki ci abincin wata guda idan yak are in kara miki.
Kaltum ta tuntsura ta fadi kasa saboda fargaba ta mike a guje ta falfala da gudu
kai ka ce gudun fanfalake take yi saboda tamkar kafarta xata tabo keyarta.
Mamaki ya kama su iya mairo suka rasa abinda ya fada mata su dai sun gay a
mayar da kudinsa aljihu sannan yayi musu korar kare.
ADON DAWA 6
BABI NA HUDU
Gari yaw aye hantsi ya keto, yayin da fataken gidan nan suka dinga baxama
neman abunda xasu kai bakin salati. Kaltum a xaune take a tsakar gida cikin
hantsiba sunkuye a kasa da alama rashin lafiya a jikinta. Mutanen gidan mata da
maxa suka yi ta