Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
bandaki zatayi
alwalar sallar asuba, mamaki mara misaltuwa zaka gani a fuskokinsu
musamman ma kawarta fatsuma,
lah kaltum baki tafi ba?
Meyasa baki tafiba ?
Amsa ya gagari bakin kaltum saitayi shiru tana tunanin abunda zata fada sai can tayi
dan murmushi karfin hali tace fasawa nayi ai tun jiya da daddare na dawo,
kika fasa meyasa ?
Suka sake tambayarta ko amsa bata basuba taci gaba da alwalarta kawai,
fatsuma tayi dariya tace gaskiya naji dadi dakika fasa don har ina tunanin yanda
zandinga yawo nikadai a garin nan gara muyi zamanmu anan, kaltum ga wuta ga ruwa
ga titina ga wayar sadarwa ga samarin birni mezakiyi a bur sudan?
kince babu wuta baruwa babu network na waya gaku a zaune a makabarta duk
kabarurruka a dakunanku na katako kamar yadda kika fada min...
sai ko wacce ta tsoma bakinta tanayiwa kaltum nasihar tayy zamanta anan kada ta
koma kauye suma yan kauyen addu'a sukeyi sudawo birni.
ta mike sam ta shiga daki batare da tare da tayi musu magana ba, takaicinda ya isheta
ya isheta kauyen nan da suke kushewa ita yafi mata birninnan dasuke muradi
kamar yadda suka saba kaltum da fatsuma suka bazama neman na abinci duk da sallah
ce amma sunyi sammako suntafi kasuwar markadi , ahanya suna tafiya kaltum ta dubi
fatsuma ta langwabar da kai gefe tace bakisan abunda ya sameni bako?
Fatsuma ta dubeta cike da mamaki tace bansaniba me yafaru?
Kaltum tayi ajiyar zuciya tace sace min wannan kudin nawa duka akayi ban gan su ba
shiyasa bantafi ba .
fatsuma ta zabura ta dauki dogon salati game da dafe kirji ta tambaya cikin gigicewa
yanzu wannan kudin an sace su dukka?
Fiye da jine dari bakwai nefa yanzu wa kike zargin ya dauke miki a dakinku ko atasha
aka
dauke ?
Hawaye ya sirnano daga idanuwan kaltum
ta girgiza kai tace bansan inda aka daukeba ni dai nasan ko a daren shekaranjiya ana
gobe zantafi kenan saida naga kudin harna sake kirgawa na daure na mayar asanda
zamu tafi tasha dai ban duba ba wata kilan sanda nashiga wanka aka dauke,
fatsuma tace watakilan sanda kike kirgawa wata ta ganki kina tashi ta dauke,
nidai kina ganin sanda na dauki buhunki bansaka hannu acikiba agabanki na ajiye miki a
tasha natafi, kuma niban hudaba nazakulo da Kinga buhunki huje....
kaltumta zabura tace nifa bance kekika daukanmin kudina bafa ko a mafarki nasan
baza ki min sataba,
suka cigaba dajajatawa har suka isa masana'antarsu wato babbar bolan da suke
sintar kayan miya suka fara gudanan da ayyukansu kamar kullun,
Abbas dai yanakan bakansa na naci dabin kaltum aduk inda take, a yau ma ya riskesu a
inda yake tunanin zai samesu adaidai lokacin daya san zai riskosu , yakwada sallama
cikin wata kamilalliyar murya mai sanyaya zuciya
lokaci guda suka daga kai don gani mai wannan sanyayyiyar murya sai sukaga fuskar
Abbas cike da murmushi irin wannan murmushi fatsuma ta mayar masa gami da amsa
sallamar itama a yayinda abangaren kaltum akasamu akasin haka, domin jitayi ranta ya
baci nan da nan ta tsuke fuska takawar dakai gefe yasake tsungunawa kanta ya rafka
sallama don dama ita yakewa sallama, kuma ita yakeso ta ansa ba fatsuma ba,
kaltum ta fusata ta mike afusace tafada cikin fushi Abbas karabu dani kakyaleni in sake
saboda ni ina da mijina a bur sudan don haka kaje kanemi wata,
fatsuma tarike baki don mamaki game da
fargaban kada kaltum tajawo musu dan kudin da dan turaren da yake basu ya pasa,
fadi take ke kaltum me haka karya takeyi batada miji a bur sudan,kaltum taji tamkar ta
zageshi,
kishi da tsantsar fusata suka damki zuciyarshi yacije lebe yace nikike fadawa wannan
magana kizo kasarmu kinacin arzikinmu dan kin samu anasonki shine zaki zageni?
To zan nuna miki ko ni wanene, ya juya yatafi afusace.
fatsuma na kwala kiran sunan shi tana bashi hakuri yayinda kaltum ke tunzurashi tana
cewa ya tafi din wazai tsoratar babu abunda
zai sameta sai alkhairi,
fatsuma ta fara yiwa kaltum fada itama dayake zuciyar akusane saita hargitsa suka hau
hayaniya kamar zasu cinye kansu,
ranar dai kowa gabanta takama ba a tafi tallar tareba haka basu daura tukunya dayaba
sai washegare fatsuma tabiyo wa kaltum suka hadu suka tafi tare kowaccensu ta huce
sai hira suke suna wasa suna daria,
gidan jawahir mai kunshi suka fara zuwa don suji sanda zasu fara zuwa aiki tunda tace
musu sai bayan sallah zasu dawo sai suka tarar ana zaman makokinta, Allah Ya mata
rasuwa ranar biyu da sallah sukata kuka da ihu ana basu hakuri sannan suka yi shiru a
gidan, suka nufi kasuwa jikinsu a sanyi kalau suna isa wajen sana'ar su sai suka iske
labari yasha bamban don yau ana kwashe bolan da suke tsintar kayan miya yau a
manya-manyan abun kwashe shara ana tarawa sai aje ajuye a motar kwashe shara,
suna isowa wasu ma'aikata masu uniform suka taso sukace oh kune daman masu tsintar
rubabbun kayan miya ku wanke ku sayarwa mutane suci ko?
Don haka yanzu zamu wuce daku wajen hukuma a hukunta ku,
hankalinsu yatashi sai suka hau rokonsu afuwa da alkawarin sun daina daga yau, da kyar
suna koke-koke aka kyalesu suka tafi akace kada su sake dawowa, daga wanna ranar su
kaltum basu sake zuwa bola ba sai suka shiga tunanin sabuwar sana'ar da zasuyi su
dinga samun abinci,
aranar kaltum da fatsuma suka jeru ajikin bangon kofar gidan su yunwa ya addabi
hanjinsu fatsuma ta daga kai da kyar ta dubi kaltum tace meza mu dingayi muna samun
abinci ?
Kaltum tace ni bakuwa ina na sani, kece yar gari kikasan kowa suma suka sanki,
fatsuma ta zabura ta mike tacewa kaltum taso muje wani waje kaltum na biye da ita
abaya har suka isa wani gida alungu gidan wata hajiya Maryam mai saro kaya daga
makkah sababbi da gumama, ,
fatsuma ta lankwashe kafa ta langwabe kai ta koro mata bayani cewar suna neman
sana'a suna so tabasu tallah ta dinga biyansu
dayake tasan kanwar babarta asabebe tasan
gidansu saboda haka tasan ko sun cuceta ta san inda zata zakulosu, ta amince ta daura
musu tallah, idan sunyi ciniki dayawa ta biyasu dayawa idan ciniki kadane ta biya su
kadan,
bayan sati guda ne sukaje daukar tallah sai hanasu dauka tayi, tayi musu korar kare
batare da sunsan abunda yake faruwaba, kuma bata fada musu daliliba suka koma
wajen mai sayar da gurasa suna yimata tallah, bayan kwana biyu ta koresu,
duk Abbas ne yake hada musu tuggu ashe,
kwanci tashi watannin kaltum bakwai cur a Khartoum haka shekarunta uku kenan
rabonta da Nigeria,
wulakanci da walagiigi sai karuwa sukeyi maimakon suragu al-amura sun cunkushe
musu har gara da abincin da zasukai bakinsu yazam wahala kasancewar anhanasu
tsintar kayan bola sannan jawahir mai kunshi da gyaran jiki ta rasu har maigidan yasake
aure ko gidan ba a shiga balle su sami wadanda
zasuyi wa gyaran jiki,
Abbas sisinshi ya daina basu tunda batasonshi tuggu iri iri yake hada mata duk wata
hanya da yasan kaltum zata bi ta sami
taro ko lomar tuwo sai yaje ya toshe ya batata da bakin shi,
gobe idan ta dawo sai kaga anyi mata korar kare ta shafawa fatsuma, '' idan bera da
sata daddawama da wari, idan babu rami mai yakawo zancen rami ?
Inji akuyarda kura tace ta tsallako babu rami abun nufi shine duk wata tsanarda
sangwama da akeyiwa mutanenmu yan Nigeria su suke jawowa kansu saboda sau tari
idan suka gingimo wata badakalar saikaga ko a labari ko a mafarki yan wannan kasar
basu tabajinta ba abubuwa rashin gaskiya da rashin da'a akasashen jama'a mutanenmu
ke nunawa, wadanda abun kunya ne da bata sunan wadanda babu ruwansu kuma
mutanen kirki ne kamar su kaltum sun zaune agidan amma basusan me
yake faruwaba, kashin kaji aka shafa musu aka hadasu akayi musu hukunci iri daya koda
yake wasu masu irin mugayen dabi'u ba yan Nigeria bane wasu yan Niger
ne,Ghana ,Togo ,Cameroon ,Chad ko Kenya amma sai ahadasu ace yan nigeria ne,
jama'a da gwamnatin Khartoum ta fara gajiya da rashin bin doka da rashin da ar yan
gidansu kaltum aka kira malam Abdulkadir mai gidan su kaltum, ance yamusu gargadi
bisa munanan halayen da akace suna kamar zubarda shara a ko ina, kafa teburin
sana'o'i ko ina, sayarda rubabbun kayan dasuke tsinta abola kamar irin sana'arsu
kaltum,
maza suna haura gidaje suyi sata haka ana ganin mata suna fita karuwanci yan kasa
suna daukar su amotoci atafi dasu.
malam yatarasu mazansu da matansu ya shaida musu abunda aka umurceshi daya
gargadesu dashi duk da wasu ya sani wasu kuma bai saniba wasu gaskiyane wasuma
karyane koma ma menene aka kara acikin maganar gaskiyar tafi yawa haka ba bukatar
bincikensu waye suke aikata wannan badakalar kosu waye babu ruwansa burinsa kawai
su daina idan bahaka shizai kori kowa agidanshi,
sai su kayi kamar sun gamsu suka yi ta bashi hakuri,
gobe wani sabon rashin mutuncin zasu suka,
yasake kiransu yayi wa'azi yayi lallashi ya jawo ayoyi daga AL QUR'ANI MAGIRMA yayi
fadan da kumfar baki,
in shaa Allahu jibi ta'andanci saiya karu
saboda sabbabbin mutane suke zuwa su yada zango agidan ba yan zangon daura
kadaiba ko yan daura harda kanawa,zazzagaw
a,zamfarawa,sakkwatawa.gida yazama gidan baitil mali bangaren maza daban saboda
malam yace kowa azauna
sadaka ga wuta ga ruwa ga dakuna lailaye da
siminti ba biyan ko sisi abinci ne kawai zaku nema shine suke bin gurbatacciyan
hanyarda suke zubarda mutuncin su data kasarsu abunda yake tambaya anan shine wai
mutane idan suka bar kasarsu cikin en uwansu inda akasansu sai suyi tayin abunda suka
ga dama don ba asansu ba balle ayi musu gori ko ayiwa yayansu gori?.
me yasa mutanane basa kare mutuncin kasarsu aduk inda suka tsinci kansu ?
dadine ace yan kasa kaza basu da gaskiya ko karuwai ne marasa tarbiya ne.
masu iya magana sukace shadda bata wari banza dole muma da halinmu shiyasa ake
tsanarmu, babban tabon ma shine ha'inci da rashin gaskiya
Duk yanda kahada hulda da mutanen mu sai
ancuceka wannan itace illarmu babba a kasashen waje da cikin gida,
wani sabon salo kuma wanda su kaltum basu san shiba shine gudun gardi irin nawasu
makarantun kwana da akeyi a wasu makarantun kwana na yan mata da akeyi garada ne
suke tubewa tsirara su hauro dakunan mata da talatainin dare suyi ihu gardi.
asabebe alokacinda taji motsi a bayanta tana juyowa taga sarkacecen mutum akan
akwatinta bayan ya tsinke musu wayoyinsu da suka jona a chaji a bakin kofar dakin
yafice da gudu yahaura katanga yayinda gida ya rude da kururuwa matan kowanne daki
sun firfito tsakar gida a firgice, dole malam Abdulkadir da sauran mutanen anguwa suka
firfito hankali a tashe ana hashaskawa ba a ganshiba,
a safiyan wannan ranar ne kuma fada ya kaure tsakanin wasu mata biyu akan shiga
bandaki harda dambe da fashe fashen kai, nan ma dakyar aka kirawo wasu mazan suka
rabasu don haka yansanda suka diro
gidan suna kama duk wanda suka samu idan
kukaga irin gudunda kaltum da fatsuma su kayi da tsalleka katanga saikuyi mamaki
amma da kyar sukasha bayan gurgurjewa da bubbugewar dasukayi a kafafuwansu, wani
sharcecen yankane a gwauri kaltum dajini jage jage amma bata lura ba saida suka isa
maboya suka tabbatar sunsha sannan ta duba tagani asanadiyyar radadi mai tsanani da
takeji awajen hankalinsu yayi matukar
tashi a sanda suka yi arangama da jinin mai yawa,
fatsuma ta fashe da kuka mun shiga uku kaltum yaya zamuyi da jinin nan kada jinin
jikinki fa ya kare ki mutu,?
ADON DAWA 28
.
TRUE LIFE STORY
.
kaltum ta matse hawayenda ya cika mata
ido tace Allah Ya biye bakinki fatsuma,
dama jinin jikina yakare in mutu in huta, banajin dadin duniyar nan banaso na koma
nigeria haka ma yanzu banaso nakoma bur sudan dama in mutu abayan garin nan kada
intashi daga inda nake yanzu,
suka rushe da kuka lokaci guda, fatsuma tace gara muyi addu'a mukoma kasarmu ke ai
iyayenki sunsan bakya makkah harsun aiko miki da kudin jirgi ki koma, nifa da iyayena
suke zaton ina makka inajin dadi kanwar babatace ta dauko ni asabebe muguwace ta
gaske.
harkokinta kawai takeyi na iskanci, dama akamata yanzu akaita nigeria idan taje gida
zata fada inda nake nima azo a dauke ni, fatsuma ta sake rushewa da kuka tace kaltum
kiyafe min don Allah nina jawo miki duk wannan abun da kin tafi dabakyanan akayi
wannan rigima, dabaki yage kafa abanza ba,
mamaki mara miraltuwa zaka iya gani a idanuwan kaltum ta dubi fatsuma da sauri tace
me kika jawo min ?
ai ni baki jawomin komaiba kalah tajawo min ta tafi tabarni...
fatsuma ta girgiza kai tace bawan nan zuwan naki nake fada ba kaltum da tuni kina bur
sudan nice nadauke miki kudinki a jakarki don kada kitafi ki barni.
kaltum taji ta tsani fatsuma harbataso tasake ganinta ta runtse ido don takaici yayinda
taji zuciyarta kamar zata fashe da alama fatsuma ta gane haka sai taja da baya ta
lankwashe kafa ta zurawa kaltum ido tana jiran hukuncinda zata yanke mata,
kaltum tayi shiru ba tare data furta komai ba sai hawaye dayake fita daga idanunta,
fatsuma tacire dankwalinta ta kama
kafar kaltum ta daure saboda jininda yake zuba haryanzu.
kaltum ta runtse ido yayinda ta jingina kanta
ajikin bishiyar da suke rabe tayi shiru kamar mai gyangyadi nan kuwa rayuwa ce ta
tsananta a gareta,
fatsuma ta nisa tace da na dauke kudin ba
wani abun nayi dashiba ajiya nakai da niyar in an kwana biyu inbaki wacce nabawa ajiyar
daga baya tace min wai an sace nikuwa nasan karya take cinyewa tayi don haka nayi
shiru banfada miki ba don babu kudin..
kaltum dai har yanzu bata bude idanun ta ba bare tabata amsa,
fatsuma ta mike tsaye tace zomuje mu leka kofar gidan mu ga ko an gama kame,
kaltum bata ansa ba sai ta sake cewa kokuma kizauna tunda kafarki nada ciwo inje
indawo shiru ta mata fatsuma ta tafi sannan kaltum ta bude ido tabita da kallo yayinda
kuka mai yawa ya kece mata marar kakkautawa tayi ta kuka tana tuje kososon gashin
nan nata dake dandankare asanadiyyar rashin kitso har tsawon watanni bakwai daman
kanta bata ba dankwali dayar
ahanya wajen haura katanga burgujejen skirt ne da bakar t shirt duk a huhuje itama
sadaka aka bata kafafunta babu takalmi kallo daya zakamata ka tabbatar almajirace ko
kuma tababbiya sabon kamu, fatar jikinta kososowa yake ana ta abinci waketa man
shafawa abincin ma dazasuci shima badon dadi ba sai donsu rayu,
data tsagaita dakukanta saita bingire ta kwanta tana barci bata damu da kashin
tsunsaye da suke tsarto mataba haka bata damu da tika tikan jangwale gwadar
katangaru da suke dauki ba dadi da matansuba sunata zagayeta barci take kuma kamar
bugun aljanu datasaba ta dai fita daga haiyacinta koma dai menene batacikin haiyacinta,
cikin barci kamar ido biyu taji muryan fatsuma tana fadin ga kaltum din ta bude ido da
kyar ta dubi mutanen da ke tsaye akanta dusu dusu take ganinsu don haka bata gane ko
suwayeba ta komawa jabar tayi ta kwanta
saitaji an girgizata antasheta zaune kaltum kaltum bude idonki ki gani taga fatsumace
rumgume da ita cikin larabci, murya tayi magana wacce nan da nan taji ta wartsake
gaba daya daga barcin kai wannan ba kaltum dinda nake nema bane daya daga cikin
mazajen biyu da suke tsaye akansu ne ya fada, ta dubeshi ya dubeta duba na ido cikin
ido yayinda gaba dayan su suka rude mamaki ya bayyana fuskokinsu mai tafe da
tsananin farin ciki ya fada cikin wata murya mai sauti abayyane yace kaltum kece kuwa?
AlhamduLillah
yayinda ya durgusa gwiwoyinsa biyu akasa ya daga hannu da idanunsa sama yana gode
wa Allah, itama ta zabura ta mike tsaye ta dafe kirji ta fada cike da mamaki lah mambela
ya akayi kasan ina nan ?
Fatsuma tafada cike da murna au kaine mambela daga bur sudan ?
Yaji dadi ya dubi fatsuma cikin murya mai sanyi yace nine mambela ashe kinada labarina
?
ya juya ya dubi mutumin da ya rakoshi yace malam itace yarinyanda nake nema, yau
sati biyu kenan muna yawo a Khartoum tare dakai saiyau Allah Ya yanke min nagode
malam
Allah Ya biyaka sannan mambela yasa hannu a aljihu ya debo kudi mai yawa ya bashi
saida
mutumin ya bude baki don mamakin wannan kyauta mai tsoka mambela yakara dacewa
kaje masaukina ka dau jakan kayana karike na baka kyauta don bazan koma cikin gariba
daganan sai tashar jirgi zamu tafi daman ita nazo nema Allah Ya taimaka na same ta.
farin ciki da godeya ba adadi mutumin nan ya
dinga yi yana mai yimusu adduar Allah Ya basu tare yana tafiya yana nanatawa kamar
karatu,
mambela ya tsunguna agaban kaltum yayi tagumi yazura mata ido yana dubanta sama
da kasa yayinda itakuma kunya ta rufeta tana rurrufe jiki,
hawaye yacika masa ido ya fada cike da tausayawa yace kaltum yanzu kece kika zama
haka kin rame kinyi daka-daka kamar bakece mai tsaftar nan ba?
dubi kanki yanda ya zama duk kura babu kitso har kawarki tafiki kyawun gani,
yasake dubanta sama da kasa yayinda yayi arangama da dankwali jage-jage da jini a
daure akafarta yasa hannu ya kwance sai ga yankan namar kafanta awaje, ya firgita ya
tambaya cikin gigita meyasameki akafa haka?
kaltum ta sunkuyar da kanta kasa yayinda hawaye ke zuba a idanuwanta, mambela
yazubo da hawayen daya ciko masa ido magana yake har cikin zuciyarsa yace yanzu
kaltum daman irin matsananciyar rayuwarda kike ciki a Khartoum?
amma kikaki ki hado kayanki kidawo bur sudan?
yanzu kaltum ina raye a sudan amma kika zauna kika zama almajira?
.ADON DAWA 29
.
NA JAMILA UMAR TANKO (JUT)
TRUE LIFE STORY.
.
PART 29
.
kamar bola, yanzu kaltum kika kasa daukar shatar mota kitaho bur sudan inyaso inkinzo
nabiya ko nawane?
kaltum ta dago da sauri ta dubi fatsuma yayinda fatsuma tayi sauri ta sunkuyar da kanta
kasa gami da haduwa da matsananciyar faduwar gaba kada kaltum ta fadawa mambela
cewar ita tasace mata kudin tafiyar,
kaltum tamayar da kanta kasa batare datace
komaiba ya juya ya dubi fatsuma yace akwai wani chemist ne anan kusa dazasu dinke
mata wannan ciwon?
fatsuma tace akwai sai dai da dan nisa.
mambela ya dubi kaltum duba na tausayi hade da kulawa da tsansar so da kauna ya
fada cikin laulausar murya zaki iya takawa ko muje mu taho da masu chemist din?
ta langwabe cukuikuyeyyen kan nan nata tace zan iya tafiya, tayunkura zata mike tsaye
mambela yacewa fatsuma yimaza ki riketa karta fadi.
fasuma ta cafketa ta taimaka mata ta mike tsaye yayinda ta shiga tsakanin hannun ta
suka dinga takawa a hankali mambela na binsu abaya ransa yana matukar baci idan ya
dubi jikin kaltum da kayan jikin ta,
saiyaji tamkar ya kurma ihu, taya akayi yana
raye aduniya kaltum tazama haka?
menene anfanin dimbin dukiyarsa tunda kaltum na nan abincin da zataci ma ya
gagareta?
sunyi tafiya mai yawa sannan suka shigo gari suka isa wani chemist karami da sukaga
girman ciwon sai suka ce bazasu iya dinkewaba gara sukaita asibiti,
mambela ya tambayesu a inane asibitin?
aka kwatanta masa asibitoci guda biyu,
daya na yaku bayi daya kuma na masu hannu da shuni ne amma kowanne sai anshiga
mota,
suna fito daga chemist mambela yatare musu taxi yashiga gaba su biyu suka shiga baya
babban abunda yabashi mamaki shine yadda ya hasko fuskokinsu ta madubi suna murna
suna dariya sai rade sukeyi suna kashewa da hannu,
Ya rasa dalilin yin hakan bayan dazunnan suke hawaye ko bayan fitowarsu daga chemist
kafin su shiga mota, yakasa daurewa dai sai ya juya ya dubi fatsuma yayi murmushi
yace fatsuma murnan me kukeyi?
Ki fada mini gaskiya