Advertisements
Chapter 38 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 46

111K to 114K   out of 137K words

dauki yarinyan nan sukutum na baka nasan duk da haka ban biyaka ba kuma
har abada bazan iya biyanka ba, ranka ya dade a duba maganata sosai agani idan da
yuwuwar yin hakan ayi idan kuma nayi kuskure a cikin maganata na bata maka rai ayi
hakuri kasan zuciya da sake-sake ni da sofi ne muka shawarta haka.
alh Adnan dai yayi shiru kansa akasa baya murmushi haka bai bata fuska ba da alama
dai yana sauraro kuma yana nazari.
malam saleh ya mike cike da tsoro yace alh na barka lafiya zan koma bakin get naji
motsi,
alh Adnan ya bashi amsa da to madallah sai anjima,
daga dukkan alamu dukkansu biyun sun shiga halin tunani da sake-sake kala-kala acikin
yinin wannan rana, don tun wannan lokacin alh Adnan bai tashi daga kan kujera dayake
zaune ba har karfe daya da rabi na rana, motsin shigowar danladi direba ne dajin
muryan kaltum ita ta katse masa tunaninda ya dulmuya aciki,
kaltum ta gaishe da mahaifinta sai ta juya ta dubi motar alh Adnan ta tambaye shi Abba
daddy bai fita ba yana nan ?
Malam saleh ya amsa cike da farin ciki, yau bai fitoba yana falonsa ta juya da sauri ta
nufi falon alh Adnan fuskarta cike da faraa bakinta cike da magana da alama wani labari
ta kunso masa,
malam saleh yayi tsaye ya hada hannu yana mamaki mai hade da fargaba yana tsoron
kada maganar da yayi wa alh Adnan dazu ta bata masa rai ya juya musu baya, taimako
da fara ar da yake musu ya daina, kada kuma ya dauka turo kaltum sukayi da tsigar
yaudara..
ta shiga falo shiga falon.
yanzu kada fa ya dauka kwadayin dukiyar sa suke yi shine suka kakaba masa 'ya?
zuciya da sake sake haka ya dinga sakawo malam saleh wadannan tambayoyi InnaLillahi
wa inna i ailaihi raji'un kalmar da malam saleh ya fada kenan a bayyane yayinda ya dora
hannu aka ya shiga dakin gadi ya kasa zama sai leke-leke yake ta jikin labule yana so ya
gada wanne irin yanayi kaltum zata fito, da farin ciki koda bacin rai idan ya Koro ta, ya
shiga zargin kansa da kansa me yasa ma ya furta wannan kalmar?
gashi zai raba zumunci musamman idan
saliha taji.
kaltum ta isa cikin falon da sauri gami da rada sallama yayinda suka yi kayi ido hudu sai
kowannensu yayi murmushi ta karasa gabansa ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da
fara a gami da mamaki hade da zumudin jin abunda zata fada,
ta bude jakarta ta zaro wata doguwar takarda ta mika masa ta ce daddy yau math
mukayi na fada maka daman nafi iya maths in shaa Allahu ''A'' zanci don na amsa dukka.
Yayi ajiyar zuciya ya lumshe ido gami da wani
laulausan murmushi ya amsa mata cikin tattausan murya, yayi kyau kaltum Allah Ya yi
miki jagora nikuma nayi miki alkawari idan kinci jarrabawar ki sosai zankaiki duk inda
kikeso kiyi karatu a fadin duniyar nan inhar kina so, zan saya miki duk abunda kikeso.
dadi ya lullube zuciyar kaltum ta rufe ido da tafukan hannayenta tayi godiya ta mike cike
da murna, zata tafi kamar daga sama taji ya kira sunanta ta dawo da sauri ta tsuguna a
gaban sa tana sauraron abunda zai fada,
ya dube ta yace kaltum wacece Madina?
waye kuma Abba?
saitaji kirjinta ya buga don fargaba sai hankalinta ya tashi, tayi sauri ta sunkuyar da
kanta kasa yayinda aka fara daukar dauki ba dadi tsakanin harshenta da labban bakinta,
magana daya sak ta kasa fitowa daga bakinta ya sake maimaita mata tambayarsa
haryanzu ba ta sauya zani ba, amsa ta gagara sai kame-kame takeyi.
ya tsuke fuska yayi magana cikin kakkausar murya Yace zauna kaltum ki nitsu ki
fahimce tambaya na kibani amsar gaskiya, inaso ki bani labarin, saboda in sani kafin
inshiga maganar, bansan kida karya ba ada ban san ki da munafunci ba bakya boye min
komai koda kin boyewa malam saleh da sofi, kada kiyimin karya don bana tare da mai
karya bana shiri da mutum mai kame-kame nafi shiri da mai gaskiya.
saita durgushe ta zauna a sanyaye yayinda idanuwanta suka cika taf da hawaye ta
tabbatar alh Adnan yaci karo da su Abba a jikin get, fargabarta kada ya zargi ko
saurayinta ne,
muryanta na kakkarwa ta bashi labarin Madina kakaf sannan ta gangaro ta fada masa
dalilin da yasa ta nemo Abba,
daga yadda ta fahimci alh Adnan ya tausayawa Madina kamar yadda ta san shi da
makurar jin tausayi, saita fara sakin jikinta tana koro bayanai, yayi shiru tsawon yan
mintina yana tunani,
yayi ajiyar zuciya ya dubi kaltum yace lallai Madina tanada mutunci kuma ta taimake ki
ya kamata itama ataimaketa yanzu idan taji Abba bai mutu ba ai zata yarda ta dawo ko?
ma'ana idan na aika alh sa'adu ya daukota.
.ADON DAWA 39
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum Tace bazata yarda ta dawo ba har sai dai idan anje da Abba, idan ta ganshi kila
ta yarda ta dawo saboda zuciyar ta tariga ta daskare ta sawa ranta har abada tabar
kasar nan bazata dawo ba.
alh Adnan ya gyada kai yace gaskiyane ke kika santa kika san ra ayinta, da
shawarwarinki za'a yi ampani, jeki ngd za a dawo da madinarki,
tayi murmushin jin dadi tayi godiya ta mike cike da farin ciki zata fice harta kai bakin
kofa zata fita taji yakara kiran sunanta sai taji hankalinta ya tashi mamaki ya rufeta ta
dawo cikin sanyin jiki ta durgusa agabansa tana sauraron sa,
yayi murmushi yace kin bani labarin rayuwarki a bur sudan kakaf keda Madina da irin
taimakonda Madina tayi miki amma koda wasa baki ambaci mambela ba?
daga inda yake yana juyo ajiyar zuciyar da tayi, saitayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa
tayi shiru,
yaci gaba da cewa ni tuntuni nake jira ki maimaitamin abunda kika fadamin a waya kin
samu miji dan ADON DAWA zaki bishi garinsu bur sudan, mutuminda ya taimakeki tun
zuwanki bur sudan ya biki har Khartoum yana shirin mayar dake bur sudan ya aureki ai
bai kamata ba har ki gama bada labari baki ambace shi ba,
Sai yaga tana kuka share-share da hawaye batada shirin magana don haka ya kyaleta ya
hakura dajin amsarta ya umurce ta data tashi ta tafi gida,
ta mike jiki a sanyaye ta fice, a bakin baranda ta tsuguna ta sharbi kukanta ta goge
hawaye sannan ta gangara ta shiga gidansu,
haryanzu mahaifinta yana labe a jikin labulen
dakinsa yana kallonta hankalinsa yayi matukar tashi daga yanda yaga tafito tana kuka,
abunda yake zargi ya tabbata cewar ya tafka kuskure daya furtawa alh Adnan zancen ya
auri yar sa kaltum gashi nan ya jawo mata tsana tunda daga lokacin yasawa ransa
zamansu ya kare a gidan nan sai ya shiga tunanin ta yanda zamansu yakare agidannan
sai ya fara tunani inda zasu fara babu gida babu gona babu sana a.
fitar kaltum keda wuya alh Adnan ya jawo wayar sa ya kira lambar alh sa'adu ta Nigeria
yajita a kashe saiya kira layinsa na sudan sai kuwa ya same shi bayan sun gaisa yake
shaida masa akwai wata mata da akeso anemo musu ita mai suna Madina a bur sudan
amma ana tunanin matar bazata yarda
tazo ba har sai an tafi da mijinta,
alh saadu ya zabura yace kai haba kamar bani?
aiko a daure zan daukota kamar bakasan dauki ba dadin da mukayi da wannan bararojin
ba mambela?
ai koshi kace in kawo maka duk da kasarsu ce sai na kawo shi da karfin tsiya balle yar ci
rani wacce ba kasarsu ba kuma mace ai karamin aikine wannan, alh ka bani wuka da
nama ka turo kudin jirgi kawai shine aikinka idan nakawota sai kabiyani yadda aka biyani
waccan karon, nikuma sauran aiki ya rage nawa nasan bur sudan nasan gidajenda
mutanenmu suke zama na tabbatar idan naje na tambayi sunanta za'a nuna min ba
boyayyiya bane tunda kowa yasan kowa a tsakaninsu.
alh Adnan yayi dariya yace karka damu da wannan zan fita anjima zanje banki zan turo
maka kudin komai ammafa kayi mata a hankali, ban saka dukan matar mutane ba koka
daureta da igiyaba, cikin lumana zaka tahoda ita idan taki kabata waya zanyi mata
magana in sha Allahu zata yarda ta biyoka, alh sa idu ya rusuna yayi godiya gamida
yarda dabin umurnin alh Adnan, suka yi sallama suka ajiye,
missed calls biyar ya gani da sunan Abba yanata kokarin nemansa a lokacin da yake
waya da alh Sa'adu ya amsa kafin Abba yayi magana ya bashi tabbacin cewar ya
kwantar da hankalinsa za'a kawo masa madinarsa har gida ba sai yasha wahalar zuwa
ba, Abba yaji labarin alh Adnan kamar tatsuniya bai fahimce shiba ma kwata-kwata sai
ya shiga jero wa alh Adnan tambayoyi cikeda magiya
yana neman alfarma ya taimake shi yadda Allah Ya taimakeshi,
alh Adnan ya fahimci Abba bai gane abunda yake nufiba baya da haka baisan waye alh
Adnan ba, shiyasa yake kokonton abunda ya fada masa, maganar karshe da alh Adnan
yayi itace Abba kabani sati daya za a kawo maka Madina insha Allah.
Abba yayi godiya suka ajiye waya batare da Abba ya yarda da abunda alh Adnan ke fada
ba kai har yanzu bai fahimci komai ba don haka sai hankalinsa yatashi, kamshin zuwan
madina da ya fara ji ada ya gushe, ya kwanta yaji kwanciyar ba dadi ya tashi zaune yaji
zaman ya gagareshi saiyayi zumbur ya mike yayi waje, a falo ya hadu da mahaifinsa ya
zauna agabansa ya fara koro masa bayanan da alh Adnan yayi masa,
sai mahaifinsa yace to ai shikenan mu jira zuwa sati dayan,
ba haka Abba yake son ji ba, yafiso mahaifinsa yace ya shirya yaje sudan din,
su kuwa mahaifansa da en uwansa bazasu taba barinsa yaje sudan yadda sukaji labarin
cewar Madina tace har abada ba zata dawo Nigeria ba to tabbas idan Abba yaje taki
biyoshi waje zai samu ya zauna da ita shima bazasu kara ganinsa ba.
Abba ya mike jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa ya dade a tsaye ba tare da yasan
abunda zaiyiba can ya dauki makullin motarsa ya fita da sauri ya kuwa ci sa'a babu kowa
a falon ya fizgi moto sai kofar gidan alh Adnan,
a wajen get ya ajiye motarsa ya fito ya nufi cikin gidan shigarsa keda wuya sukayi
kicibus da maigadi, malam saleh ya dubi Abba shima ya dubeshi sai hankalin malam sale
yayi matukar tashi saboda ya gane wannar fuskar, saurayin nanne dayazo wajen kaltum
ranan su biyu, malam sale ya tsuke fuska ya tambaye shi a fusace waka zo nema ?
Kamar yadda saleh ya gane Abba haka Abba ya gane mai gadinda yakoresu rannan ne
don haka shima afusace ya amsa masa wajen masu gidan nazo,
sale ya hasala yace kai yaro ba inda zaka wuce in har baka fada wajen wacce kazo ba.
Abba yace mai ya hadani da mace ai wajen mai gidan nazo alh Adnan yanzun nan muka
gama waya dashi kashiga kace masa barister Abba Tukur ne daga yankaba,
sai sale yayi sauri ya rabe ajikin get,
Abba ya wuce batareda wani ya sake magana acikinsu ba.
baisan kofarda zaibi yashiga wajen alh Adnan ba shikuma bayaso ya tambayi wannan
mara mutuncin mai gadin nan sai gashi Allah Ya
jeho masa kaltum ta fito daga cikin gida dauke da bokiti zata yi shanya a igiyar dake
daure a farfajiyar gidan kamar kullum daga ta dawo daga makaranta zata fara aikin
wanke kayan kazantan goggo fattu tana ganin Abba saitayi turus tana dubansa cike da
mamaki yayinda shi kuma farin ciki ya lullube zuciyarshi yayi dariya yace yauwa kaltum
ashe kinanan, yayanki kuwa yana ciki?
ya fadi hakane don yanaso yasan dangantakarta da alh Adnan,
saita dubeshi duba na rashin fahimta shima ya fahimci haka saiyace alh Adnan nake
nufi, sai tayi ajiyar zuciya ta nuna masa kofarda zai shiga jikinta a sanyaye maimakon
yatafi sai ya tsaya yana dubanta yana duban kayan shanyarda yake hannunta yana
duban kannenta da suka baibayeta yana duban mahaifiyarta datake daka agefe ga goyo
don ko ba a fada masa ba yana duban sofi yasan itata haifi kaltum da alama nan boys
quaters
shine gidansu amma kuma babban gidan ta nuna tace nan ne inda alh Adnan yake ciki,
tambayoyi fal acikin zuciyarsa babu damar tambaya saiya wuce zuwa bangaren da ta
nuna masa ya tura kofa yayi sallama sai suka
ci karo a tsakiyar falo har alh Adnan yayi wanka ya shirya da makullin moto a hannunsa
zai fice, yayi mamaki da ganin Abba don haka suka dunguma suka koma wajen kujeru
suka zazzauna,
alh Adnan dakansa ya dauko masa lemo da ruwa acikin firij sannan suka fara
tattaunawa.
malam sale tsaye a bakin get har yanzu yana zullumi, zuciyarsa tana ta tsaro masa
karya da gaskiya yace aransa wato dai alh Adnan yasan wannan saurayin kaltum ne don
haka ya aika akirawosa zai ba shi ita tunda shi bazai iya auranta ba amma tayaya
zandauki yata inbawa wannan fitsararren yaronda yake yi min magana cikin gatsali ba
mutuntawa?
saidai kuma bazan iya yiwa alh Adnan musu ba akan duk hukuncinda zai yanke akan yar
nan don shi yayi wahalarta, ni wani tsausayine ma yasa na furta masa wannan kalmar
taya auri kaltum?
malam sale ya nufi gida da sauri ya iske kaltum na shanyan har yanzu sofi na daka ya
dafe kirji ya fada cike da damuwa kaiku tsaya da aikin nan,
gaba daya suka sankare a tsaye suna sauraronsa cikeda fargaba yace wata katobara
nayi wacce ta dameni ga ta zata zame mana matsala, game da zancen yarinyan nan
kaltum da alh Adnan,
kaltum ta dafe kirji tace Abba lafiya?
mena yi?
ya juya ya dubi kaltum yace ina kika samo wancan yaronda ya shiga cikin gida?
kaltum agigice tace Abba ne ai wanda zai auri Madina.
wacece Madina zaki fara boye-boyen nan naki ko?
don ba a taba jin cikinki ba, basu bane kwanakin baya na koresuba?
saita fashe da kuka tana rantse-rantse,
sofi tajashi cikin daki don taji kan labarin saboda kar su alh Adnan din suji yanda yake
magana da karfi a fusace yayinda kaltum tazo ta labe a bayan wundo tana jiyo duk
abunda mahaifinta yake fada ya zayyanewa sofi duk yanda sukayi da alh Adnan da kuma
hukuncinda yake zargi alh Adnan zai zartar yana zargin Abba saurayin kaltum ne
wajenta yake zuwa kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita...
.
To jama'a wannan episode din yana nuna mana kuskure na mal saleh da matar sa Sofi
da aka daura su na rashin jituwa da er su da pahimtar juna,
Da akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin su da er su da ba'a kawo nan ba, da tun wuri
sun sake da ita da ta basu labarin komai, kuma da sun san komai da ya shape ta
maimakon ta sanar da wani,
Wasu yaran tsabagen babu puska a wajen iyayen su abokai suke baiwa labarin kukan su
da daria, idan akayi rashin sa'a abokin bana gari bane sai ya basu shawara marar kyau,
Ana so iyaye lokacin da dan su yake taso wa xuwa shekara 7 su nuna masa soyayya,
daga 7 xuwa wani 7 su nuna masa abu mai kyau da marar kyau (ma'ana su tarbiyyar tar
dashi,) daga wani 7 din kuma su mai dashi abokin su, ta haka ne baxai na boye musu
komai ba, xasu san irin halayen sa da irin abokan sa kuma xai koyi irin halin su.
Amma wasu iyayen sunan sun aihu ne kawai, sai su barwa dunia ta raina musu 'yaya.
Sai kaga uba bai san halayen yayan sa ba, bai san abokan yayan sa ba, banda gaisuwa
babu abun da yake hada sa da su balle a samu lokacin hira ya pahimci damuwar su ba.
Ina mai Jan hankalin iyayen mu mata da maza ake shiga lamarin yaya, a jasu a jiki, ba
sai abu ya kwabe ba azo ana dana sani, wani kapin a ankara yaro ya lalace.
Allah Ya tsare mu baki daya.
ADON DAWA 40
.
TRUE LIFE STORY
.
kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita daga nauyin da akeso a
daura masa.
sofi tayi tagumi tayi shiru can tace malam kayi kuskure daka amayarda wannan magana
abunda muke tunani muke addu'a dama yakasance shine zaka je ka fada?
yanzu ga irinta nan,
malam sale yayi ajiyar zuciya yace tsausayi ne wallahi nima ina dana sanin, don kaltum
bazata fadi abunda ya fada mata bane dazu da ta shiga ta dade aciki saita fito tana kuka
kila zaginta yayi ma.
kaltum dake labe a bayan wundo saitaji kamar zata kurma ihu don haka ta damke
bakinta kuka ma mai tsanani ya kece mata, hankalinta ya tashi matuka yayinda ta
fuskanci gaba daya zancen mahaifinta zargi ne baisan gaskiyar al amari ba,
na daya baisan abunda ya sata kuka ba dazu ba, haka baisan tsakaninta da Abba ba,
baisan dalilin zuwan Abba wajen alh Adnan ba, wannan kalmar duk bai dameta ba tunda
zargi yake, babbar matsalarta yadda yaje ya furtawa alh Adnan wannan kalmar ta aure
alhali ga mijinta can a bur sudan wanda a koda yaushe yana ranta, tana muradin
ganinsa babu wani da namiji a duniya dayakai mambela a cikin zuciyanta bata da wani
uba ko uwa dayakai alh Adnan a ranta, don haka kowa da matsayinsa, ta koma dakinta
ta zauna ta kifa kai da gwuiwarta tana kuka,
Goggo fattu na kwance akan gado tamkar gunki amma sai yunkuri take tanaso ta
tambayi kaltum me aka yi mata take kuka amma maganar bata fita,
kaltum ta fahimci abun da goggo futtu keson ji cikin kuka ta fara magana batareda ta
dubeta ba tace Goggo abur sudan kika tafi kikabarni ba uwa babu uba babu mataimaki
sai Allah, iya mairo kawarki da jikarta rakiya dakika hadani dasu suka dinga
tsangwamata sai na hadu da wata mata a cikin mu mai suna Madina, itake taimakona
bayan ita sai na hadu da wani saurayi a garin ADON DAWA mai suna mambela shima
yana sona kuma ya taimake ni, munyi alkawarin aure dashi, shi nake so na aura amma
sai gashi Abba yaje yatari alh Adnan yace ya bashini ya aureni alhali ni a matsayin uba
na dauke shi, babu mai kula dani babu mai yimin wahala babu mai bani abunda nake
bukata a duniya sai alh Adnan, kiduba kiga irin tashin hankalinda matarsa mummy
salaha ta jefamu, ki tuna kiga irin rigimar da za a tafka idan ta samu labarin maganar da
mahaifina ya furta a yanzu tun kafin ma azo ga auren,
ta tsaneni bazata bari inzauna lafiya ba gashi inason mambela har yanzu shine na
shaidawa kawayena zan aura har an yi mana baiko.....
ki auri Adnan kalmarda goggo fattu ta furta kenan radau ta dira a kunnuwan kaltum,
kaltum ta zabura ta dago kai ta dubi goggo Fattu wacce ke kwance luf kamar ba ita tayi
magana ba, matar da a shekaru biyu maba a taba gane abunda tafada ba sai yau,
kaltum ta share hawaye tace goggo me kika ce?
shiru bata sake magana ba amma hawaye yana ta kwaranya daga idanuwanta,
kaltum ta rushe da kuka ta saka gefen zaninta tana gogewa goggo fattu hawayen da
yake kwaranya daga idanuwanta,
kafin lokacin makarantar islamiyyah yayi kaltum ta saka kayan makaranta ta dauki
Qur'an nta tanufi makaranta saboda kawai kada Abba da alh Adnan su fito su kirawo ta.
Abba yayi shiru yana nazarin akan bayananda alh Adnan yayi masa, saiyaji

38 / 46