Advertisements
Chapter 32 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 46

93K to 96K   out of 137K words

don nima na taya ku murna,
kaltum tayi sauri ta kiftawa fatsuma ido alamar kada tafada, sai fatsuma ta tunsire da
daria tace ba komai,
mambela yace kaltum ce ta hana ki ki fada ko?
Ai naganta tana kifta miki ido ki fada min gaskiya babbar suna ne garekifa masu sunanki
basa karya,
fatsuma tace to bari na fadi gaskiya murna mukeyi saboda yau munshiga moto don
rabonmu da mu shiga munfi shekara uku tun sanda muka taho daga nigeria, saidai muga
ana hawa bamu taba hawa ba, duk inda zamuje saidai muje da kafa....
kaltum ta ririketa saida ta tona musu asiri,
mambela da direba suka kwashe da dariyar da basu shirya ba, direban ya juya yadubesu
dan lekensu ta madubi bai isheshiba gara yasake duban kyauyawan nan ya juya ya dubi
mambela yace yan Nigeria ne ko?
masu shigowa sudan da niyar tsallaka ruwa su shiga jidda suke zube wa akasarnan suna
wahalar tsince-tsince da bara daman ina sukaga kudin shiga mota wani aiki zasu makane
ka dauko su?
Nan da nan mambela ya tsuke fuska yace wadannan ba irin almajiranda kake fada bane
daya matata ne dakuma kanwata,
sai direba yayi shiru bai sake cewa komai ba yayinda kwakwalwarsa ta rude yace aransa
yaya za ayi yace wadannan yammatan jininsane alhali yanayinsu ya bambamta kana
ganinsa kasan dan sudan kana ganinsu kasan yan nigeria ne daga ganin jikinsu kasan
almajiraine to amma meyasa zai boye masa wadannan?
tambayoyi fal a zuciyar direba saidai kash baiga fuskar tambayaba ya isa asibitin masu
mulki da masu arzikin kasar ne ke iya biya saboda tsadarsa da kwararrun likitocinsu,
suka firfito yayinda mambela ya biya kudin mota sannan suka nufi cikin asibitin,
haryanzu fatsuma da kaltum basu daina hada ido suna dariya ba, wannan karon dariyar
shiga hadadden gini suke mai benaye kamar london,
hadaddun matayene suke shiga asibitin da yayansu da mazajensu ajere-ajere cikin
sutura na alfarma da kamshin turare, fatar jikinsu jawur a simulce ko kurji daya babu
balle kasamu kirci irin nasu kaltum don haka mambela ya tsayardasu ajikin wata mota
ya hana su shiga yacesu jirashi anan yana zuwa,
cike da mamaki suka saya suna kallonsa ya fice da sauri wajen get ya dan jima bai
dawoba sannan ya dawo rike da ledoji guda biyu ahannunshi sannan ya mika wa
kowaccesu leda daya cikin sauri ku bude saiga lafaya (pink colour) mai kyan gaske da
takalmi masu kyau (flat shoe)suka zura masa ido lokaci daya, sai yayi murmushi yace
kusa wannan akan kayan jikinku ku nada sunfi kyau yayinda ya masu dagun don su
kimsa akan kayan da suka maka amma duk dahaka sunfito fes bakamar da ba,
yadawo sukabi bayansa har cikin asibitin,
kudi mai yawa aka karanto masa nayankan file da kudin ganin likita kawai ba ama
zancen aikin da za'a mata dana magun-guna, mambela yabiya sannan aka nuna masa
dakin da zasu shiga suga likita,
sanyin A.C ne da kamshi kawai yake tashi yana ratsa kasusuwan jikin su, farin ciki ya
bakunci zuciyoyinsu kasancewar sun gansu a cikin yan kasa suna wadakarsu kamar
kowa wanda a da basuda damar yin hakan,
kaltua ta manta da katon ciwonda ke kafanta ta biyewa fatsuma sai yake hakora sukeyi
suna murna bayaga kalle kalle da tabe-taben da sukeyi saidai idan mambela zai gansu
saisuyi sauri su daina su sunkuyarda kai kasa,
likita ya duba kafar kaltum sannan ya shaidawa mambela cewar zasu shiga da ita dakin
tiyata za awanke ciwon a yanyanke fatocinda suka babbako sannan a dinke wajen
sannan zai rubuta musu magunguna, dan haka ga takarda yaje kan kanta ya biya,
kudi mai yawa amma bashi yadami mambela ba illa wahalarda kaltum zatasha ji yake
dama ace ciwon yadawo kafarsa yaji zafin kaltum tahuta, kallo daya zaka masa kasan ya
shiga damuwa, jikinsa yayi sanyi kalau ya isa wajen biyan kudin da sayin magunguna sai
ya saka mai sayar da magunguna agaba da tambayoyi kala-kala yaci sa'a yasamu mace
mai fara'a domin tana bashi amsar tambayoyinshi harma takara masa bayani ta tabbatar
masa wadannan allurai da likita ya rubuta masu kashe zafin ciwone, ko ana dinkewa
bazataji zafin komaiba, sannan mambela yaji sanyi aransa ya biya kudin ya karba
yakawowa likita yayinda likita da ma'aikatan jinya mata suka shiga da kaltum dauke da
almakashi da tasoshi abaya ga iodine da shashshabalin, abunka da nauyin aljihunkane
darajanka a yanzu sai lallashi da wasa da daria sukewa kaltum babu kyara balle zagi irin
na asibitin yaku bayi ba irin wanda kalah ta kwanta ba.
aka umurci mambela da fatsuma su zauna akan wasu kujera na alfarma mambela ne
zaune ya rike kai da alamar damuwa atattare dashi,
fatsuma ta lura da hakan ta nisa tace kayi hakuri zataji sauki in shaa Allahu,
mambela yaji sanyi da kalaman fatsuma sai
ya gyara zama yace bakomai fatsuma mu tayata da addu 'a Allah Ya sausauta mata,
sukayi shiru na wani dan lokaci ba wanda yasake magana sai dai bakinsu yana motsawa
da alaman addu'a suke yi,
mambela ya dubi fatsuma yayi murmushi yace fatsuma naga alamar kina son kaltum,
kun shaku, kin san tane dama tuntuni ko anan kuka hadu?
fatsuma tayi dariya tace anan nasan ta gidanmu daya dakinmu yana kusa da nasu tun
zuwanta su kalah suka wulakantata suka hana ta abinci shine nace tazo mu dinga zuwa
wajen sana'ata don itama tasamu abunda zataci,
mambela ya yatsune fuska yace menene sana arki?
Fatsuma tace kasuwan markadi muke zuwa da sassafe a lokacin da ake sauke kayan
miya kwando-kwando ana ciccire masu kyau ana zubar da rubabbu, idan an zubar
mukuma sai mu dinga tsintar masu saukin rubar mu wanke muje kasuwar adare mu
sayar mu saya abinci.
mambela ya dafe kai yayi shiru don tausayawa takaici ya isheshi can ya dago ya dubi
fatsuma fuskarshi cike da damuwa yace kinyi maganan wata kalah da ta wulakanta
kaltum ta hanata abinci wacece kalah?
kibani labarin kaltum kakaf a Khartoum tun daga ranarda tazo Khartoum har rana irin ta
yau dana ganku abayan gari naje gidanku na iske yansanda suna kame wai meya farune
?
Fatsuma ta gyara zama ta fayyacewa mambela rayuwar kaltum kakaf a Khartoum bata
boye masa komaiba tunda bata boye masa sace kudin kaltum datayiba ai bazata boye
masa wani abuba,
hawayene ya dinga digowa daga idanuwan mambela saboda tausayin abar kaunansa
kaltum,
tambaya daya yasake yiwa kaltum da alama ita tafi tsaya masa arai itace game da
ABBAS,
yace kin tabbatar kaltum batason Abbas ko kadan aranta?
fatsuma tayi mamakin wannar tambaya nasa tabashi amsa cike da tabbatarwa kaltum
batason Abbas kokadan duk da irin nacin da yayi da irin lallabata danayi ta yarda amma
taki yarda don hakane ma yafara takura mana, har yasa aka hanamu tsintar kayan miya
shinema ya dinga turen ya sanda gidanmu don akoremu, yaji haushi kaltum bata sonshi,
mambela yayi murmushi ya juya ya dubi fatsuma yace kinci sa'a da kaltum bata yarda
taso Abbas ba duk lallabata dakikayi saboda nasha alwashin takurawa duk wanda yayi
kokarin raba ni da kaltum.
fatsuma taja da baya atsorace tana rawan jiki mambela yayi dariya yace kada kiji tsoro
babu abun da zan miki yanzu amma da ace da kika lallabata tayarda taso Abbas da ina
mai tabbatar miki da gaske har Abbas bazan raga muku ba,
don saina nemoshi koshi wayene kuma kodawa yake takama.
su dukka sukayi shiru nadan lokaci sai mambela yasake dagowa ya dubi fatsuma yace
kaltum bata taba baki labarin wata mata Madina a bur sudan ba?
fatsuma ta gyada kai ta fada cikin fargaba tace tabani labarin Madina.
Yace AlhamduLillah tunda kinsan shakuwa da soyayyarda ke tsakaninsu da taimakonda
Madina tayi wa kaltum a irin zamansu dakowa takanshi yakeyi ina girmamata kuma ina
matukar kaunar duk wanda yake kaunar kaltum kamar Madina amma yanzu bana raga
mata ko kadan saboda sanadin da tayi na rabani da kaltum.
fatsuma tayi caraf tace kayi hakuri bansaniba da farko amma daga ranarda kaltum
tafadawa Abbas cewar yarabu da ita, ita da mijinta a bur sudan mai suna mambela
tundaga ranar bansake takurata ta kula shi ba, shima daga ranar ya tabbatar akwai
wanda take so bazai sami soyayyarta ba don haka yatakura mata,
daga dukkan alamu mambela yaji dadin bayanan fatsuma saiya tuntsure da dariya yace
dagaske kike kaltum ce ta furta haka da bakinta takirani da sunan mijinta?
fatsuma ma dadi ya kamata ta gyara zama ta
bararraje akan kujera don ada a takure a karshen kujera tana gudun kar yakaimata bugu
tace duk abunda nafada maka agame da kaltum ba karya bane tayi niyyar komawa
wajenka Allah baiyi ba,
mambela yace tunda kika bani wannan labari mai dadi har nayi dariya tokema zansaki
dariya a rayuwar ki in shaa Allahu daga yau kindaina kuka fatsuma.
farin ciki ya rufe fatsuma tafara godia tunkafin ya fadi abunda zai yi mata,
mambela ya nisa yace menene matsalarki yanzu ?
Me kike so arayuwarki?
kinaso kikoma kasarku Nigeria inbiya miki kudin mota kokuwa a Khartoum kike son zama
nabaki jari?
Fatsuma tayi caraf tace nafiso nazauna a Khartoum inyi aure ni da mijina mutara kudi
mu tsallaka saudiya saboda abun kunyane yanzu in koma garinmu babu hakorin Makkah,
ace banje saudia ba dadinta ma nakoyi larabci a sudan, idan suka ji ina larabci wasu
zasu yarda amma kuma nayi baki na rame bazasu yarda saudiya naje ba.
mambela yayi dariya ya girgiza kai yace yaranta mai dadi, nikuwa aganina babu gatanda
za amiki kamar asaki a mota kikoma wajen iyayenki sune gatanki sai kiyi aurenki a
mutunce.
fatsuma tace ai saurayina da nake bala'in so musa anan garin yake yace bazai koma
nigeria ba saiya koma makka don da niyyar haka yataho.
mambela yace shima dan garinku ne?
fatsuma tace shi dan maigatarine nikuma yar
malam madorine duk acikin jahar jigawa muke bamuda nisa.
mambela yayi shiru kamar mai tunani can ya
nisa yace tunda haka kikafiso bari nafara ganin sa tukunna sai inji a ra'ayinsa game da
shawarar da kikayanke idan naga yanada hankali kuma yanason auren sai kuyi ku zauna
inbashi jari ya rike ki in Allah yasa kuntara kudi saiku shiga makka.
fatsuma ta kwashe da dariya tace bari inkirashi awaya ma yazo yasamemu anan asibitin,
nasan yanzu yataso daga gun aiki.
mambela yace har aiki yakeyi kenan aibakuda matsala ma sosai.
fatsuma tace eh dako yakeyi akasuwan markadi anan muka hadu bari na kirashi ka
ganshi ta zaro wannan gwabjejiyar wayanan ta ta wanda sai andaki bayanta take kawo
wuta takira abun kaunarta musa ta fara koro masa bayani kenan yahango ma'aikatar
jinya sun riko hannun kaltum suna fitowa da ita daga dakinda akayi mata aiki dan haka
yataso da sauri ya iso garesu cike da kulawa kalma daya ne ya fito daga bakin shi shine
sannu ,sannu kaltum da ciwon har yanzu ko ya daina?
da sauki tafada a kunyace
fatsuma ta taso da sauri ta rike hannun kaltum suna hada ido sai suka tuntsure da dariya
wannan dariya tasu tabawa mambela mamaki dominshi ya rasa abun dariya anan.
magunguna cike da leda ya saya mata suka dunguma suka fito daga asibiti,
tafiya sukeyi ahankali saboda dingishinda kaltum keyi, fatsuma na rike da ita mambela
kuwa a gabansu yake yana tafiya a hankali suna isa bakin titi sai mambela ya nufi wani
katafaren kanti a tsallaken titi, su dai suna biye dashi suna jiran suji abunda zai fada
musu suka shiga ciki sai suka iske kata faren waje ne a lailaye da tiles fari mai dauke da
teburi kashi-kashi masu kujera hurhudu a
kowani teburi fulawowiyi ne a kowace kusurwa ga A.C mai sanyi da fankoki kana tura
kofar gilashi sanyi da kamshi ne zai bugi fuskarka, da alama kamshin abinci ne na
alfarma ke tashi,
ma aikata suka taresu da fara'a yayinda aka
nuna musu wajen zama suka zauna doguwar
takarda aka mikamusu mai dauke da hotunan abinci kala-kala da sunayensu da farashin
ajiki ma'ana su zabi wanda sukeso sai akawo musu,
mambela ya zaba ya nuwawa ma'aikaciar, sannan ya mikawa su kaltum,
fatsuma ta zaba, kaltum kunya ya hanata ta zaba don haka mambela ya zabar mata,
shinkafa da taliya mai tiriri aka fara kawowa farati uku sai ga farantin miya kala-kala, kifi
ne a bankare game da wasu dakwalen kaji sun yi rashe-rashe akan faranti , salad ne
hadadde gami da kayan marmari a yanyanke wato fruit salad . lemuna (freshe juice )a
kofuna aka kawata shi da tsinken tsotsa.
kamar a mafarki haka sukejin kansu yayinda
farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu,
mambela da fatsuma basu jira komai ba suka fara ba cikinsu hakkinsa yayinda nauyi da
kunya ya hana kaltum ci ya juya ya dubi fatsuma yace me ya hana kawar ki cin abinci ?
Fatsuma tayi dariya tace tun dazu take taka min kafa tana mintsinina wai intashi mu
chanza tebur ba zata iya ci a gaban ka ba,
mambela yayi dariya ya dauki farantin abincinshi ya canja tebur ya juya musu baya
sannan kaltum tazage ta dinga tura abincin nan, kasancewar da dad'addiyar yunwa ce
atattare da ita rabonsu da cin abinci tun na jiya da rana basuci ba suka kwanta da safe
suka farka da gagarumar rigima a gidansu, don haka da kyar suka tsira babu zancen
nemo na karin kumallo,
suka ci suka yi nak duk cikinsu babu wanda bai yi cinda da kyar yake juyiba.
mambela ya biya kudi mai dunbim yawa saboda restaurant ne mai tsadar gaske yana
daya daga cikin wajen cin abinda yake tashe a babban birnin Khartoum,
kai saye bakin titi suka nufa a inda suka tsayar da taxi suka shiga suka zauna kamar
dazu,
mambela ke zaune a gidan gaba ya juyo ya
dubi fatsuma fada masa sunan anguwanku da mu saukeki, nida kaltum zamu wuce
tashan jirgin kasa zuwa bur sudan,
cikin fargaba ta dafe kirji tace '' yanzu da kaltum zaka tafi yaya zanyi ni kadai?
sai hawaye ya surnano daga idanun ta, kaltum kuwa farin cikine mara misaltuwa ya
kamata sai itace tafadi sunan anguwan domin fatsuma ya hanata magana, kaltum ta
dafata tana lallashinta game dayimata tayi idan tanaso ta biyosu ta kaura bur sudan suje
cen suyi zamansu,
fatsuma ta girgiza kai cikin harshen hausa tace aure zamuyi da musa bari ma insake
kiransa awaya kafin ku wuce yazo kofar gidanmu su hadu da mambela, yace yanason
ganinsa zaiyimasa zancen auren mu idan da gaske yana son aurena mambela yace zai
bamu jari mu zauna,
farin ciki ya rufe kaltum ta mika mata hannu suka tafa ta ce ai shikenan tunda duk muna
tare anan, kizo nima inzo,
fatsuma tayi murmushi dadi ya lullubeta tazaro wayanta ta bugawa musa kafin tayi
magana yace na shirya ganinan zuwa wanne asibiti zanzo yanzu?
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,...
.
Allah sarki, har mambela ya bani tausayi, yadda naga yana ta rawar jiki akan kaltum bai
sai ina dap da kwace ta ba..
Yayi abu mai kyau tunda yana kiwata min mata

ADON DAWA 30.
.
TRUE LIFE STORY.
.
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,
suka isa kofar gida yayinda mambela da direba suka tsaya a mota, fatsuma da kaltum
suka nufi cikin gida harsun kusa shiga gida mambela yayi kiran sunansu suka waiwayo
atare sai suka ga mambela ya tunkaro inda suke,
suka tsaya suna dubansa suna mamakin Kiran, yakaraso inda suke yace kaltum ki shiga
kiyiwa mutanen gida sallama kifito mu tafi kada mu rasa jirgi, duk tarkacen kayan nan
na tsummakarai kibarsu zan saya miki wasu a can,
kaltum da fatsuma suka hada ido suka tuntsure da daria,
kaltum ta ce wanka zanyi da sallah kawai na fito,
mambela yace nidai bazan sallami direba ba bari inje nima inyi sallar azahar kafin ki
fito...
kafin mambela ya rufe baki fatsuma tace lah ga musa yazo kuzo mu gaisa, musa ya
karaso inda suke gami da mika wa mambela hannu suka gaisa, musan sun kuwa dace da
fatsuma dai-dai gajere bakikirin shan koko daukan rai shine wanda takeso duk duniya
bata ganin ko wanne namiji da gashi sai shi, shine gwaninta, musa babu kamarsa musa
ya mikawa mambela hannu suka gaisa duk da fatsuma ta fara masa bayani amma bai
gama fahimta dukka ba don haka sai ta fara kara masa bayanin tunda gashi ga
mambela, wata murya ne abayansu akace yauwa ga kaltum din don haka dukkansu suka
waiwoyo atare cike da mamaki,
mariya sukagani daya daga cikin yan dakin su kaltum tare take da wasu dattijai guda
biyu mai kiba da siriri senye suke da manyan rigunan malum-malum da alama dai
hausawa ne, tafiya suke suna sabe riga suna sauri kamar zasu kifa da kasa, da alama
awahale suke mariya tace kaltum ina kika shiga wadan nan mutanen tun tsafe suke
neman ki?
kaltum ta dubesu cike da mamaki amma bata san su ba don haka sai ta zura musu ido
tana sauraro taji meke tafe dasu haka mambela ya sankare a tsaye yana sauraronsu
kafin su yi wata magana sai wayan mai kibar ta fara ruri yayi sauri ya duba sai ya latsa
gami da cewa AlhamduLillah ga kaltum din muna tare da ita sai yanzu aka nemo mana
ita, rike wayan ya mikawa kaltum waya ta mika hannu ta karba a sanyaye kafin ta daura
a kunne sai ta kalli mambela ya gyada mata kai alamar ta amsa sannan ta daura waya a
kunne tana sauraro batare da tayi magana ba, kaltum ta zazzaro ido ta dafe kirji da
alama zuciyarta ce ta buga saboda mummunan firgitan da tayi, kan kace kwabo ta fara
karkarwa idanunta ya kawo nan take su zatonsu mutuwa aka fada mata, mambela ya
fada cike da damuwa cikin larabci kaltum lafiya dawa kike waya?
meyake faruwa?
Ta katse wayar da sauri dan gigicewa ta fashe da kuka.
yaya kika kashe wayan bayan baku gama magana ba?
inji katon mutumin ya karbi wayan ya sake latso lambar ya mikawa kaltum a fusace ya
fada cikin fushi ki amsa waya malama ana nemanki tun tsafe meyasa zaki kashe wayan?
ta karba ta sake karawa akunne haryanzu batayi magana ba sauraro kawai take
mutuminda yake mata magana awaya ya sake magana yace hello kaltum kina ji kuwa?
ni ne alhaji Adnan daga kano kitattaro kayanki ki biyo wadannan mutanen yau din nan
ku taho Nigeria, nabasu kudi zasuje office din immigration ayi miki passport ku hawo jirgi
ku taho gida kinji na fada miki kada ki yarda ki sake subucewa a rasaki arasa yan aike.
kaltum ta juyo ta dubi mambela ta cigaba da sauraron abunda alhaji Adnan yake fada
yayinda tashiga rudani mai yawa takasa tantance yanda zuciyarta ta karkata, saboda
tana matukar son mambela tanaso ta zauna dashi don tana da kyakkyawar zato akansa
zai riketa amana, ta yarda da tsantsan sonda yake mata saboda Allah haka bataso ta
sabawa alhaji Adnan a matsayinshi na mutum da yake kulawa da ita wanda bayaso yaga
ta tozarta, mutuminda yake ta salwantar da dukiyansa wajen kokarin nemota ta dawo
gida, ya damu da ita kamar yar da ya haifa ta cikinsa shine cinta da shanta iliminta da
lafiyarta, magana yake mata cikin damuwa da fargaba don kada ta subuce..
kwakwalwar kaltum ta dinga jujjuyawa a kokarinta na tantance da tattace abunda zaifi
alkhairi a rayuwarta don gudun fadawa dana sani nan gaba, sai ta tuno kyakkyawan
kulawa da alhaji Adnan ke bata tasan tabbas idan ta koma Nigeria makaranta zata koma
ta karasa sakandari harzuwa jami'a, babban burinta kuwa a rayuwa shine ta ganta a
jami'a ta hada digiri amma data tuno halin ko inkula da iyayenta ke mata da irin
gallazawa irin na goggo fattu da take mata don kadan daga cikin halin goggo

32 / 46