Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
xo ya durkusa a gabana yana furta min
kalaman sanyaya rai dan hankalina ya kwanta amma sai suka xame min tamkar wuta
yake hura min a xuciyata. Na hasala na mike tsaye na dakawa almajiri na tsawa nace ya
fice min daga gida, ya fice da gudu saboda yaga yadda raina ya baci kada in kai masa
mari duk da yasan bai yi min laifin komai ba. Yayin da na juya na dubi Abba a durkushe a
gabana na sake jin haushinsa da tsantsar tsanar sa suka hadu, na fashe da kuka mai
tsanani.
Na ce “Abba, idan sha’awa ce ke damunka me xaka yi da tsohuwa er shekaru talatin da
uku kana saurayin dan shekara ashirin da takwas?
Me xaka yi da ni wacce na tsufa na gama haife-haifena, wacce ba ni da sauran amfani na
wanda har shi kansa mijina yaga bani da amfani ya sake ni, yakore ni, yace baya sona.
Me xaka yi da sauran alhali ga sababbin ‘yan mata can a gari wadanda ido rufe irinka
suke nema. Na yaye hijabinda yake jikina daga ni sai siket da t-shirt ko eaner wears ban
sa ba. Na ce me kake sha’awa a jiki na?
Idan sha’awata ka ke yi mushiga daki in har daga yau xaka rabu da ni in huta.”
Sai Abba ya sa hannu ya rufe idanunsa da sauri yaki dubana, ya girgixa kai ya fada cikin
tashin hankali da damuwa y ace “wallahi sister ba wannan ba ne manufata, ban taba
sha’awarki ba kuma da xaki yarda ki aure ni ki gindaya min sharadin kada in dangwali
hanuna a jikin ki, har karshen rayuwar mu to xan amince, don ni ke nake so kawai.”
Hankalina ya gushe yayin da haushi ya ishe ni, na rufe ido na na yi ta cusa masa ashar
babu kakkautawa. Na ce ya tashi ya bar min gida kafin na dauko tabarya in fasa masa
kai. Ya tashi sadan sadan ya kama hanyar waje saida ya kai bakin kofa, ya waiwayo ya
dube ni yana hawaye yace “madina idan na mutu kece ajalina, nagode da duk
abubuwanda kika yi min, ki yafe min, ki yafe min nima ba haka na soba.” Sai ya fice ya
bar ni a nan a tsaye kamar gunki.
Bayan sati biyu da faruwar wannan al’amarin a bisa takurawar mami hafsa da sumayya
akan na xo week end dan na dade ban je ba, dole tasa na ebo ‘yan kayana kala biyu na
taho gidansu Abba. Abba na fara iskewa a falo yana xaune sai gumi yake yi shi kadai duk
da AC dake kunne a falo, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar yana cikin matsananciyar
rayuwa. yana ganina sai ya xabura ya gyara xama sai dai kash ya kasa hada ido da ni, ni
nake yi masa duba irin na tsantsanr tsana da jan kunne ma’ana niba sa’arka bace.
Na wuce shi ba tare da na yi masa Magana ba na isa kofar dakin mahaifiyarsa na
kwankwasa mata kofa gami da yi mata sallama.
Kasancewar tasan ina tafe nan ta dau muryarta t ace “madina ki shigo mana.” Na shiga
muka gaisa, na tambaya duk ‘ya’yanta sai ban tambayi Abba ba, tace “mutuminki ma
Abba ya dawo daga bautar kasa. Bai je ya nuna miki motarsa ba? ”
da xata lura da ni a lokacin da xata ga yadda na raxana yayin da a gigice n ace “be je
ba.”
Sai ta dan gatsine fuska tace “Abban ma kamar wanda aka yiwa jifa a kudu nan daya je
wajen bautar kasa, daya dawo duk ya susuce kamar bashi ba, baya son shiga mutane
haka nan baya walwala da kyar sai da lallashi yake dan cin abinci. Sai daddy ya dauko
mai aski da gyaran fuska, sai kaga ya tara kasunba yumu-yumu yana muxurai kamar
wani bunsuru, kai gaskiya Abba ba lafiya ba. Shiga dakinsa ki ganshi ko ke da yake
mutuniyarsa ce xai yi miki bayani.”
Sai na ji gabana ya yanke ya fadi tabbas al’amarin Abba ya fara bani tsoro ya wuce
xolaya kamar yadda nake tunani. Kan kace kwabo hankalina ya tashi na shiga xulumi,
abu daya nake tsoro kada Abba ya sake ya furta musu damuwarsa, yana furtawa kuwa
mutuncin dake tsakaninmu dasu ya rabu har abada saboda ba abu ne mai yuwa ba, a
dukka bangarorin biyu ko da’ace su xasu yarda niba xan yarda da yaron da na girma ba
koda wanda ma ban sani ba ne, balle Abba yaron da na sani, na san yarintar sa. Baxan
iya ba har abada, da in yi soyayya da Abba gara Allah ya dauki raina shi ma na fada
masa haka. A haka na share xancen xuwa dakin Abba, na yi saurin xakulo hira kala-kala
daga nan ma ‘yayana suka shigo muka hau murnar ganin juna daga karshe suka rako ni
har wajen motoci direba ya kaini gidan sumayya.
Ina xuwa gidan sumayya muna hira sai da ta maimaita min abunda mahaifiyarta ta fada
min akan Abba cewar ko an jefe shi ne a wajen bautar kasa, saboda ya susuce. Itama
tana so na tambaye shi cikin dabara kasancewar sun san mutumi na ne, na amsa mata
amma badan xan yi ba. A daddafe na yi kwana biyu a gidan su Abba, na je ranar juma’a
da yamma na koma kaxaure ranar lahadi da yamma.
Naga yarana na basu abin da suke bukata, shima Amma mun harhadu a falon gidan
musamman da safe idan zamu karya sai dai baya iya yi min Magana nice ke faman
washe masa baki ina yi masa wasa a dole saboda a gaban iyayensa ne kada su gane
akwai wata ‘yar takaddama a tsakanin mu na sulalo na dawo kaxaure da xummar a wata
shida ma ba xan je kano ba, ai dai na yi tunda na je.
Haka kuwa aka yi na dade ban je kano ba sun yi min xancen xuwa week end sai na fake
da aiki yayi min yawa. Kusan watanni uku ban ga Abba ba, ban ji kiransa ba a waya sai
hankalina ya kwanta na dauka ya hakura da ni. Wata rana da daddare ana tafka ruwan
sama kamar da bakin kwarya. Na rufe gidana tun kafin magaruba, ina dakina akan salla
na idar da sallar isha’I ina wuridi da addu’o’I kala kala ina fadar bukatuna, saboda Allah
Yana amsa addu’a a lokacin da ruwan sama yake sauka. Na ji yo da gaske ana buga min
kofa sai jikina ya dau rawa, kwallawa nake yi ina tambaya “waye? ” shiru ba amsa, sake
bugun kofar ake yi da karfi na wawuri lema na fito tsakar gida na tsaya, can dai na isa
bakin kofa na yi Magana “waye? Waye? ”
shiru sai bugun da ya karu. La’ilaha illa Anta subhanaKa inni kuntu minaxxwalimina” na
yi ta karantawa sannan na bude kofar jikina na rawa.
Dogon namiji sanye da shadda taxarce koriya da hula na gani a tsaye yaro-yaro yana
digar ruwa ya jike sharaf. Ban gane ko waye ba na tambaya cikin firgici “bawan Allah wa
kake nema ne, ko kayi batan kai ne? ”
sai yace “ke nake nema.” Na jima a tsaye ina dubansa saboda duhu ba wuta ban gane
ko waye ba ne amma ni xuciyata bata bani mutumin nan xai cuce niba saboda nayi
addu’a Allah xai kiyaye ni. Sai na ji ya bani tausayi saboda yana tsaye har yanxu a cikin
ruwa, yana dukansa. Na sa Allah daya a raina ko daya xo da niyyar cutar da ni Allah xai
kare ni sai na matsa ya shigo xauren. Ban de rufe kofar ba muka iso falo a inda na kunna
fitila sai ga Abba duban farko na gane shi sai na ji tamkar an hura min wuta a xuciyata
dan haushi.
Na fada a hasale “Abba, baka rabu da niba ko? Sai ya fada cike da tabbaci “ba xan iya
rabuwa da ke ba, har sai ranar da na rabu da raina.” Sai a lokacin na tabbatar na hadu
da alakakai, na hadu da masifar rayuwa.
Na ce “ni kuwa gara a raba ni da raina da in yi soyayya da kai.” Sai kuma ya rushe da
kuka harda dora hannu a kai, yana tambaya ta waishi a duniyar nan me yayi min haka
nake yi masa wannan wulakancn?
Wai me yasa na tsane shi alhalin yana so na?
sai naga ya dafe kirji da alama xuciyar sa ke yi masa ciwo, yaro yana kokarin kakkafe
min xai fadi ya mutu.
Nan da nan na fara lallashinsa ina cewa ya kwantar da hankalinsa na amince. Wannan
Kalmar na fitowa daga bakina sai naga Abba ya lafa, ya koma ya xauna ya mike kafa a
tsakiyar falon. Da yake babu kujeru a falon leda ce da labule kawai, ni ma na samu lungu
na xauna muka yi jugum kamar a gidan makoki. Idan ya dago ido ya dube ni sai yayi
murmushi ya sunkuyar da kai kasa da alama yau farin ciki ya same shi kasan cewar na
amsa masa . ni kuwa tuni takaici ya dame ni.
Fiye da awa guda muna xaune a cikin wannan yanayi, sai na dube shi na ce “ruwan
sama ya tsaya sai ka tafi gida ko? ” ya juyo ya dube ni yace “a ina xan hau motar kano?
” na fusata na harare shi na ce “da ta ina ka biyo ka xo? ”
sai ya dukar da kai kasa cikin ladabi yace “nagode xan tafi saida safe.” Ya mike ya fara
tafiya, ban amsa masa ba na saka shi a gaba muka fita har kofar gida. Na waiwaiga ban
ga motar daya xo da ita ba, ashe da gaske bada mota ya xo ba a motar haya ya xo. Ina
lekensa ya nufi hanyar get xai tafi tasha ga nisa, gashi garin tsit babu ‘yan Babura, ga
tsananin iska da sanyi, ga kayan jikinsa a jike sharkaf. Yana ta rawar dari ya tafi yayin da
ni kuma na ji ko a jikina bai dameni ba shiya dorawa kansa wahala, na jawo kofata na
rufe na shiga daki na kwanta. Ina ta sake sake a raina, idan na fara saka soyayyata da
Abba sai na yi maxa na warware baxan iya soyayya da kanina ba sai dai duk mu rasa
rayukan mu ni dashi gaba daya.
Wayata ceta hau kara na xabura na duba Abba ne, sai na yi sauri na katse dan ba xan
amsa ba , ya ci gaba da kira, ina ta rejecting. Sai ya turo rubutaccen sako yana shaida
min ya isa gida lafiya. Na tabe baki nace “ina ruwana, ni na aike ka.” Yaron nan bai iya
barci ba haka har cikin dare bai daina turo sakonni ba, har saida nayi masa reply, sannan
ya runtsa. Ka da ki dauka wata Kalmar soyayya na rubuta masa kalma daya na rubuta
itace. “ok” sannan ya kyale ni na runtsa.
Kaltum na rike haba ta afka cikin mamaki tace “cafdijam, haka soyayya take daman ko a
fim din indiya ban taba ganin irin wannan soyayya ba.”
Madina ta yi dariya tace “so ya wuce haka ma kaltum, ai ke yarinya ce karama baxa ki
sani ba sai dai nan gaba. Ke in takaice miki duk wannan halin da Abba ya shiga ban fada
miki komai ba ma saboda kwakwalwarki karama ce ba xaki fahimta ba, kadan nake
takaice miki, kuma duk wannan rigimar da aka yi ba’ayi komai ba. Bala’I na gaba sai kin
tausayawa Abba, ko makiyinsa xai tausaya masa idan ya ga halin da yake ciki.
Hakika daga baya na tabbatar bada gangan yake yi ba da gaske Allah Ya saukar masa
da jarabawar sona wacce ta xame masa matsala a dukkanin lamarinsa. Na fuskanci shi
kansa baya son nacin da yake yi min yana iya kokarinsa wajen danne son da ture shi
amma abu ya ci tura, ko baya so xuciyarsa xata tursasa shi sai yayi min waya idan ban
amsa ba sai ya taso ya xo ya ganni. Bayan na amsa gaisuwarsa bana kara kallonsa balle
na kara yi masa Magana, a gidana ko a office, da daddare ko da rana ya kara ci xamansa
ya karaci xamansa ya kara ci satar kallona in yi kamar bansan yana yiba, daga karshe
sai yayi min sallama ya tashi ya tafi idan ya dame ni da waya in amsa in ce masa
“menene? ” sai yace ya kira ya gaishe ni ne.in ce “nagode”. In kashe wayata, idan ya
fara turo sakon daya danganci soyayya sai na ja masa kunne cewar ya daina niba sa
arsa ba.
Sai gashi rannan a gidana shi da wani amininsa mai suna mukaddam. Na san mukaddam
sosai abokinsa ne tun suna sakadire suna shigowa gidana, tare ma suka yi jami ‘a shima
lauya ne.bayan sungaishe ni sai mukaddam ya kai-kai –ce xai tsara ni cewar abokinsa ya
shaida masa komai game da halin da muke ciki, wai in daure in kula shi ba hargetse na
daga musu hankali gaba dayansu, na xage su tsaf na kore su daga gidana. Na ce da
mukaddam ya fadawa abba kada ya sake nemana ko a waya balle a ido biyu, jikinsu na
rawa suka tafi.
Abba yayi ta kuka ya dinga turo sakonnin bada hakuri kala-kala a waya, na ce duk halin
da xai shiga ya shiga baxan cuci kaina ba na aikata abunda xai dame niba.
Wata rana da yamma ina cikin garin kaxaure ni da abokan aikina nurses muna bikin wata
abokiyar aikin mu. Sai wata kawata da muke xaune tare tace “wayar ki na ringing tun
daxu fa.”
Na yi sauri na bude jakata na dauko wayar sai naga 30 missed calls. Sai na ji gabana ya
yanke ya fadi na fara dubawa sai naga missed calls din Abba 19 ne 6 kuma na
mukaddam abokinsa, 5 kuma wata bakuwar lamba ce. Na fito gefe saboda kidan da ake
yi a wajen da kuma hayaniya, ina kokarin kiran lambar da ban sani ba amma ban damu
da in kira Abba ba balle mukaddam na san dai abu daya ne, shine su yi min magiyar
soyayya ni kuma ba xan yi ba, kuma bana yi. Na kira number na ji number busy ana
amfani da layin, ba’a jima ba sai naga lambar tana kara kirana na yi sauri na dauka sai
na ji muryar wani inyamuri yana Magana cikin harshen turanci.
Ya ce dani “madina ce? ” na amsa cike da mamaki “eh, madina ce.” Ya ce “to gamu a
kofar gidanki, kofarki a rufe.” Na tambaya cike da mamaki “waye kai? Lafiya? ” ya fada
cike da damuwa “madam, ki yi sauri ki xo, emergency ne muna tare da marar lafiya ne
yana neman taimakon gaggawa.” Na fada cikin mamaki marar lafiya a gidana kuma? Me
xan yi masa ni da ba likita ba, kuma ko ni likita ce gidana ya kamata akawo shi ba asibiti
ba?
Sai na ji mutumin ya hargitse yana Magana a fusace y ace “ina Magana ne akan mai
gidanki daya yi hadari a hanyarsa ta xuwa onisha, gashi nan rai a hannun Allah be san
ma a inda yake ba, jini ne ke xuba.”
Na ji gaba daya tunani naya hautsine na rasa me yake fada, kafin in ce wani abu ya kara
da cewa “muna nan a kofar gidanki ki xo idan baki xo ba nan da mintina goma sha biyar
xamu ajiye miki shi a kasa mu tafi da motar asibiti ce na roka aka kawo mu tun daga
onisha dan kawai na ceci ransa ya na gama fada ya kashe waya.”
Kaltum ta dafe kirji t ace inna lillahi wa inna ilaihi ra ji’una, waye wannan marar lafiyar ko
dan uwanki ne daga onaca? ”
Madina ta share hawaye t ace “xaki ji ko waye, ki ci gaba da saurarena. Mutumin na
kashe wayarsa sai ga lambar mukaddam ta shigo na yi sauri na amsa jikina na rawa. Sai
na ji y ace “sister madina wai me yake faruwa ne da Abba? Na ji ana ta kirana da lambar
sa idan na dauka sai na ji muryar wasu inyamurai daga karshe ma naji wayar a kasha.”
Na ce “nima ban sani ba, amma ka je gidan su ka duba shi ka gani.”
Sai mukaddam yace “ai Abba baya gida tun da asuba na kaishi tasha yahau doguwar
motar xuwa onisha.”
Sai na dora hannu a ka, n ace “inna lillahi wa inna ilaihi raji’una. Mukaddam me Abba xai
yi a onisha? ”
Sai y ace “babu yadda ban yi ba kada ya je y ace sai ya je wajen ‘yan uwanki su bashi
kwatancen inda xai samu yayanki innamani a enugu, yana ganin idan ya nemo miki
yayanki uwa daya uba daya wanda shine kadai dan uwanki wanda rashin sanin inda yake
yana damunki to yana ganin xaki dan tausaya masa ki aure shi ki tabbatar da gaske
yake sonki da aure. Abba yace kada na fada wa kowa a gidansu baya so ki ji.”
Ai ko rufe bakinsa bai yi bana katse wayar na rusa ihu na yi bakin titi da gudu, saura kiris
mota ta kade ni na tsayar da mai babur nahaye da sauri, kawayena da gudu suna kirana
tuni mai babur ya figa da ni, ce masa nake kara gudu malam yi sauri bamu tsaya a ko
ina ba sai kofar gidana, a inda na hango motar asibiti da marar lafiya a kwance abaya
tamkar gawa sai wadansu maxa guda uku. Na karasa gare su ina karkarwa suka bude
min bayan motar na leka dakyar na gane Abba daga kafarsa na shaida shi amma babu
mai gane fuskarsa saboda ta yi kaca kaca da raunuka. Kunnensa ma an manne shi dan
saura kiris ya fadi dan haka fuskar ta kunbure sumtum an nade da bandeji fari, bashi da
riga se dan gajeren wando saboda dorin karayar da aka yi masa a hannun hagu da kafar
dama kara bibbiyu sai kafadarsa wani katon rauni ne, an like shi da bandeji, sanna duka
ilahirin jikinsa babu inda babu rauni jini jage jage, a jikin shinfidarsa farare gasu nan a
gefansa a yayyage jawur da jinni tamkar an tsoma su a bokitin jinni a ka tsame su suna
ta diga.
Na tsala ihu na gigice ina tambayarsu me ya faru das hi? Ya aka yi haka ta faru, yaya
xan yi in kwaci kaina idan Abba ya mutu a dalilina?
Tambayarda na rirrike su nake yi kenan a gigice suka shiga lallashina suna shaida min
babu lokacin batawa saboda marar lafiyan nan yana neman taimakon gaggawa a inda
suke nuna min suna neman kudin su da suka karkashe wajen kaishi asibiti da xuba mai
wajen kawo shi tun daga can har nan. Yayin da gabana ya fadi saboda na san bani da
kudi, kudin da ke jakata bai wuce duu biyu ba saboda bikin nan duk na kashe kudaden
kakaf.
Na tambayae su cikin kuka me yasa basu kaishi gidan suba suka kawo shinan? Sai suka
ce min ai sanda yayi hatsarin yana Magana shine ya fadi sunanki yace matarsa ce, yana
so mu kira ki kuma ke ce last call dinsa da muka gani a wayarsa, ke yake kokarin kira a
sanda hadarin ya afku shi yasa muka kira ki, baki dauka ba daga nan muka ga wani
lambar mukaddam shima mun kira baya