Advertisements
Chapter 3 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 46

6K to 9K   out of 137K words

“ke me kyau, yaya sunanki!”
Ta na mkyarkyata tace “kaltum”
Su dukka suka maimaita sunan “kaltum” a lokaci guda suka ci gaba da dubanta
suna kwada kyawunta, suna mamakin kyawunta don basu xata akwai masu kyau a
cikin bakin almajiran nan ba saboda sun dauke su wulakanttatun bayi.
Daya daga cikin su ya dubi shugaban tawagar mai suna Mambela wanda har yanxu
bai ce komi ba sai duban kaltum yake yi kasa kasa.
Cikin yarensu yake Magana yace “ranka ya dade shugabana mambela kai ka dace
da kyakkawar halittar nan, du da de ba niman mata kake ba, lallai tana da kyau
kuma ta hadu. Ya kamata a mika maka ita cikin shagon nan kawai in ka gama sai
ka bata alif jine (dubu daya) ka ga sai tayi sati tana cin abinci, gobe xa ka ga ta
dawo da kanta.”
Duk da cewar a cikin yarensu ya yi Magana bata ji duk abubuwanda yake fada ba
amma ta fuskanci abunda yake fada, don haka sai ta juya da sauri ta fara tafiya.
Mambela yace “tabbas yarinyar na ta dace da ni don haka ku dauko min ita, ku
shigar min da ita cikin shagon nan.” Ba tare da bata lokaci ba kartai hudu suka bi
ta da gudu suka damkota cak suka daga ta kamar kaxa suka nufo inda mambela
ke xaune. Tuni robar bararta da yan kudaden data samu suka waste a kasa, ta
kurma ihu kai kace rai ake xare mata.
Cikin kuka tace “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Laa ilaha illa anta subhana inni
kuntu minaxxawalimin.”
Mambela yace su ajiyeta kasa a gabansa yayin da ta xabura da gudu sai ya damki
hannunta ya fada cike da damuwa cikin harshen larabci.
Ya ce”kaltum bkya son kudi ne! bakya son mambela dan sarki, mai kudi da
dukiya!”
Ta fada cikin firgicewa da kuka mai tsanani .
“eh, bana so.”
Ya yi murmushi cikin mulki da kasaita y ace “amma ni na ji ina sonki, so mai dinbin
yawa kuwa. Yaya xa’a yi ken an!”
Abokansa suka fada cikin fusata “ka bamu ixini mu shigar maka da ita ciki kawai,
ka gama da ita mu ma idan ka gama ka bamu sauran, tunda bata da gata a kasar
nan waye xai tsaya mata.”
Mambela ya mike tsaye cak yana duban kaltum dake tsugunne a gabansa har
yanxu kuka take, gardawan kacokan sun xagayeta babu hudar da xata samu ta
arce . mambela ya dade a tsaye yana dubanta daga shi sai mahaliccinsa ya san
abunda yake aiyanawa a ransa. Can ya dago ya dubi yaransa daya bayan daya sai
yayi murmushi da kyakkyawar fuskar nan tasa, sannan ya yi musu nuni da hannu
ko bai furta ba su sun fahimci abunda yake nufi nan da nan suka fara aiwatar da
abunda ya umurcesu dasu yi domin ba’a yiwa mambela musu a garin.
Kartai uku ne suka damko ta suna kokarin shiga da ita shago. Ta kurma ihu ta ci
gaba da kiran “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.”
Muryar wani tsoho ne suka ji a bayansu ya fada cikin yarensu, daga dukkan alamu
ransa a bace yake, y ace “haba mambela ko sauran ba musulmai ba ne ai kai
musulmi ne, ko kunyi niyyar cutar da yarinyar nan albarkacin sunan Allah da take
ambata ya kamata ku kyaleta.”
Suka ajiye ta yayin da ta balla da gudu ta je bayan tsohon ta labe, karkarwa kawai
take yi. Gyalenta ya dawo wiyanta, kanta babu dankawali sai burtintin kitson da ya
tuttuje wanda ya cika da yashi a sanadiyar rashin siminti balle katifa a dakinsu.
Tsohon ya juya ya dubi kaltum yayi mata yarensa, sai ta girgixa kai ta yi masa
larabci. Ta ce, “bana jin yarenka, larabci nake ji kadai” ya fada cikin harshen
larabci “yi hakuri yarinya, daura dankwalinki, goge hawayenki ki tafi gidanku. Ki
daina shigowa kasuwa bara wajen maxa ki dinga bararki a cikin gidajen mata ya fi
miki alkhairi a matsayinki na yarinya mace budurwa kuma kyakkyawa.”
Ta gyada kai t ace “ nagode, ba xan sake xuwa ba. Baba karaka ni gidanmu tsoro
nake ji kada su bini su sake tare ni a hanya.”
Ya ce to muje in raka ki.
Jikinta na karkarwa, hawaye yana kwaranya ta shige gaba tsohon na biye da ita a
baya har suka yi nisa.
Mambela ya cije baki ya gyada kai ya dubi abokinsa.
Ya ce “xan jinyata tsohonna idan be daina shiga shirgata ba. Yanxu haka shima
idan suka raba daji yaga ba kowa xai iya yi mata lalata, shine mu ya hana mu.
Xamu hadu da kaltum wata rana wallahi ba xan hakura da ita ba duk ihunta.”
Abokansa suka ci gaba da xuga shi suna bashi kwarin guiwar gami da daukar masa
alkawarin idonsu idon kaltum xa su kamo masa ita.
Har kofar gidansu kaltum tshon nan ya raka ta da gudu ta fada cikin gida ba tare
da tayi msa godiya ba saboda a firgice take don tsananin tsoron da ta ke ciki.
Kaltum ta dawo gida da magaruba, kallo daya xaka yi mata ka tabbatar hankalinta
a tshe yake ko Magana aka yi mata sai ka ga ta xabura. Babu irin tambayar da
ba’a yi mata ba amma amsa daya ta gagara sai hawaye da take xubarwa. Daga ita
sai Ubangijinta suka san abunda ya faru amma bata fadawa kowa ba.
Madina ceta ja hannunta tsakargida, suka shafe tsawon sa’a guda tana lallashinta
tana bata baki da dubaru iri iri akan ta fadi abunda yake damunta amma kaltum ta
ki cewa uffan, sai girgixa kai kawai take yi alamar babu komai. Karshen maganar
madina t ace “babu yadda xa’ayi kice babu komi amma kuma kina kuka.”
Ta bata ruwa a buta tace ta yi alwala, ta yi sallah, ta yi addu’a ko me nene ma
Allah Ya sawake mata.
Karkarwa hannu kaltum yake yi data dauki buta ta xagaya ban daki, ta fito tana
alwala jkinta na rawa, kukan dai bata fasa ba har yanxu. Tana sallah tana
sheshekar kuka a bayyane, hankalin madina ya tashi amma sai ta ji haushin
kaltum ya kama ta saboda ta ki fada mata matsalarta. Su kuwa su huwaila banda
xagi da dungure mata kai babu abunda suke yi suna cewa watakila satar kayan
jikinta tayi masu kayan suka doke ta.
Rakiya tace “watakila gidan wasu ta shiga ta satar musu abinci tunda da yunwa ta
fita tun jiya bata ci abinci ba.”
Amina t ace, “ko kuma xagin wasu ta yi suka kikkifa mata mari don bata da
kunya.”
Iya mairo t ace, “ku kyale ta mana karta fadi abunda yake faruwa tunda bakin hali
ne da ita babu mai jin cikinta.”
Kaltum na kudundune a kan kwalinta cikin mayafinta sai kuka take yayin da jikinta
yak eta karkarwa. Har kowa y agama cuku cukun kwanciya, aka hure acibal bal
wato fitilar da ake cika kwalba da kanaxir ayi lagwani da tsumma.
Duhu ya bayyana a cikin dakin, yayin da gari yayi shiru alamar dare ya tsala,
kowane bawa ya kwanta hakarkarinsa kamar yadda masu iya Magana suke cewa
dare mahutar bawa. Wannan dare kuwa ya xamarwa kaltum daren jan aiki babba
maimakon ta huta sai ma ta tashi tsaye.
Misalign karfe daya na dare kaltum tayi firgigit ta mike tsaye a firgice gami da
kwalla ihu mai tsanani tana fadin “wayyo Allah na, ku taimakeni gasu mambela
nan xasu kamani.”
Ta tattaka sauran matan dake kwance a tsakiyar dakin burinta kawai ta fice waje
da gudu. Gaba daya ‘yan dakin suka tashi a gigice suna riketa, tana bankarewa
tana xubar das u sai da ta fita tsakar gida da gudu tana ihu tana fadin.
“su mambela ne xasu kamani, gasu nan xasu kashe ni.”
Madina da jidda’u ne suka bita da gudu suka damko ta suka shigo da ita daki
sannan ta dan lafa ko minti biyar ba’ayi bat a sake kwalla ihu ta fice ta gudu.
Wannan karon harda iya mairo a masu bin ta da gudu suka cafko ta. Ba ‘yan dakin
su kadai ba gaba daya ‘yan sauran dakunan gidan babu wanda ihun kaltum da
dawainiyar masu rike ta bai tasa daga barci ba. Kowa ya fito ido luhu luhu saboda
barci suna tambayar “me ke damunta!”
“ba mu sani ba.” Amsar da su madina ke bayarwa ken an. Su duka suka kewaye
kaltum suna tambaya,
“waye mambela, mutum ko aljan!”
Babu amsa, makyarkyata kawai take yi tana kuka, madina ce mai ilimn kur’ani ita
ke tofa mata addu’o’I sannan kaltum tadan lafa harta fara gyangyadi, sannan ta
sake firgita ta mike tsaye tana kokarin rugawa da gudu suka damko ta, suka
xaunar da ita har yanxu fada take.
“ga mambela nan da abokansa xasu kamani.”
Su dukka sun tausaya mata, kowannensu mata da maxa sai addu’o’I suke tofa
mata har saida ta lafa sannan suka koma dakunansu. Wsau suka kwanta amma
wasu suna tsaye akanta har saida gari yawaye tangarai sannan kaltum ta sami
barci. Sai kowa ya shiga neman ruwan alwala da sauransu.
Kaltum barci take yi haikan mai nauyi wanda bata iya jin duk wani motsi da
surutan da ake yi akanta, bata bude ido ba sai karfe biyu na rana. Ta tashi xaune
firgigit ta dubi sama da kasa, gefen hagu da damanta sai taga babu kowa sai ita.
Ta dinga kokarin tuno komai. Kanta ne yake tsananin ciwo dan haka ta shafe awa
guda a xaune ta rasa abunda yake mata dadi. Can ta daure ta yunkura xata tashi
sai ta koma jabar ta xauna, ta sake cije baki ta rike katakon ginin dakin ta yunkura
da karfi sannan ta mike tsaye. Ta fara tafiya a hankali yayin da kafarta ke xugi a
sanadiyar bubbugewar da ta dinga yi jiya. Hakika duk ilahirin jikinta ciwo yake yi
musamman kafadar ta saboda ciccibar da abokan mambela da ‘yan dakinsu suka
dinga yi wajen jawo ta.
Ta fito tsakar gida ta tsaya ta dubi kowacce kusurwa babu kowa sai ita kadai, ta
sake ci gaba da tafiya har saida ta fito kofar gida sannan ta sulale ta xauna a gefen
wani kabari ta xura masa ido tana kallo. Sai hawaye ya fara sirnanowa daga
idanuwanta, ta fashe da kuka mai tsanani ta fara Magana ita kadai tamkar
tababbiya.
Ta ce “a ina nake! Ni wacece! Wa nake da shi a duniya! Me na ke yi a duniya!”
Sai kwakwalwarta ta tuno mata mambela da abokansa a lokacin da suke kokarin
ciccibarta xasu shiga da ita wannan shagon, sai ta rushe da kuka. Ta ce “inna
lillahi wa’inna ilahi raji’un. Yaya xan yi da rayuwata! Kowa ya tsane ni, kowa baya
sona, kowa yana hantara ta, ga kishirwa ga yunwa. Allah Ka dau raina a saka ni a
cikin kabari in kwanta in huta in daina ganin kowa, kowa ya daina ganina balle
wani ya ji haushina.”
Ta sa hannu ta shafa kabarin ta fada cikin kuka ta tambaya tace “waye a cikin
kabarin nan, mace ko namiji! Ina so in xama kamar ku, in mutu kamar yadda kuka
mutu. In daina motsi kamar yadda kuka daina, in daina tafiya kamar yadda ku ka
daina, in daina bara balle su mambela su kamani.” Yayin da kuka ya ci karfinta ta
kasa ci gaba da Magana.
Muryar mai sayar da ruwa ne ya katse ta, ta dago idanuwanta da sauri ta dube shi,
sai a lokacin ta tuno tsananin kishirwar da take matukar addabarta. Ta fada cikin
wata marainiyar murya “saga dagiga moya hilwa wala murra!” ma’ana mai ruwa
tsaya ruwan dadi ne ko na xartsine!
Mai sayar da ruwa ya tsayar da jakunansa ya dubeta yayi murmushi y ace “muya
hilwa” ma’ana ruwan dadi ne.”
Ta ci gaba da Magana cikin harshen larabci tace “ka sauke min jarka daya.”
Ya sauko daga kan keken jakinsa da farin ciki yana godiya ya na fadin”Allah Ya yi
miki albarka yarinya, kin taimakeni da xaki sayi ruwana yau ko digon ruwa ban
siyar ba ban samu ko kwabon da xan yi cefane ba.
Maganar da yayi ya ambaci kudi shi yasa ta tuno dan silillikan data samu jiya da
yamma. Sai ta yi sauri ta laluba jikin siket dinta, ta ji ba komai, sai ta tuno ashe
sun xube a lokacin da ake ciccibar ta a kasuwa daga kudin har robar bara sun
xube. Sai ta ji hankalinta ya tashi ta shiga tunanin abunda xata fada masa. Ya
katse tunanin da ta ke yi ya tambaya, “a ina xan juye miki ruwan!”
Sai ta yi firgigit ta dube shi sannan ta sunkuyar da kai kasa, ta sosa keya, ta fada
cikin gargadar murya “baba ka yi hakuri ba ni da kudi, ashe kudin ya xube jiya a
jim arab. Ko xaka bani kofi daya in sha sadaka saboda Allah kishirwa nake ji.”
Tsoho ya tsuke fuska ya ciccibi jakar ruwansa ya mayar kan jakunansa yah aye, ya
kada su suka tafi. Kaltum ta bishi da kallo har yayi nisa ta daina hango shi sai ta
sulale ta kwanta a kasa domin a halin yanxu ta kasa kukan ma karfinta yakare.
Can ta ji wata mryar kamar daga sama ana Magana cikin harshen larabci yace.
“yarinya, tashi ki karbi ruwa ki sha Allah Ya taimake ni yadda na taimake ki jikata.”
Ta daga ido da sauri sai taga mai sayar da ruwa ne ya dawo . ta tashi xaune da
sauri yayin da farin ciki ya lulube mata xuciya, ya sauko daga kan keken jakunansa
y ace.
“a ina xan juye miki jarka daya!”
Ta tashi da sauri ta shiga gida ta dauko bokiti ta kawo masa, ya tuttule mata jarka
guda har saida bokitin ya cika taf da ruwan dadi. Ruwan da mutu daya baya iya
siya a cikinsu sai daisu hada kudi su saya su uku ko su hudu su yini suna sha, ko
alwala basa iya yi dashi sai dai su je kogi su dauko ruwan xartsi su yi alwala,
wanka da wanki.
Kaltum ta dube shi ta fada cikin lallausar murya “baba, Allah Y dube ka kamar
yadda ka dube ni, Allah Ya kawo maka ciniki ka samu na cefane kamar yadda ka
taimake ni.”
“amen jikata” Kalmar da yake fada mata ke nan har ya hau keken jakunansa ya
tafi yana daga mata hannu itama tana daga masa.
Ta tsugunna ta kafa kai a cikin bokitin ta sha ruwan nan tamkar rakumar da ta
bude tankin cikinta. Ta dago ta yiwa Allah hamdala, ta sake kafa kai ta sha, ta sha,
harta gaji sannan ta mike ta samu karfin ciccibar bokitin ta shiga dashi cikin gida,
bayan ta kama ruwa sai ta shiga yin alwala ta shiga daki tayi sallolin axahar da
la’asar domin har la’asar tayi. Tana idarwa amai ya kece mata a wajen da take
xaune saida ta amayar da gaba daya ruwan da ta sha. Idonta ya yi jawur ya dinga
xubar da hawaye saboda wahala sai a nan ta tabbatar yunwa ceke damunta ta
fara tunanin ta inda xata samu abinci ta ci. Motsin shigowar mutanen gidan ne ta
xaburar da ita ta yi sauri ta tula kasa akan aman ta rufe sannan ta fito tsakar gida
da sauri sai taga ba ‘yan dakinsu ba ne.
Su na ganinta suka fara tambayarta yaya jikinta ta amsa da sauki. Duk da ta shiga
rudani bata fahimci sannun da suke yi mata ba . tana tambayar kanta da
kanta.’daman ba ni da lafiya! To ciwon me nayi da har ‘yan wasu dakin suke yi min
sannu!”
Ta tambayi xaibu ko taga su iya mairo! Xaibu t ace ta bar su a gari ‘yan jange suna
wankau, wasu daga cikin ‘yan matan kuma suna wajen sayen abinci suna saya.
Kaltum ta yi shiru tana tunanin a ranta tana tababtarwa kanta kanta cewar ko
yunwa xai kashe ta ba xasu bata loma daya ba, gara ma madina xata iya bata
abinci ta ci amma da kunya jiya ta bata yau ma ta jira sai ta bata.
Xaibu ta katse tunaninta t ace “baki fita bara ba ne yau!”
Kaltum ta gyada kai tace “ban je bara ba saidaI yanxu xan tafi. Ko xaki bani aron
robarki in tafi bara tawa ta bata jiya.”
Xaibu ta shiga ta dauko mata roba, a cikin robar da gutsurin gursa. Farin cikin ya
lullube xuciyar kaltum, ta karba ta duka ta yi godiya ta yagi gayan gurasa ba tare
da tagama taunawa bata hadiye tamkar mayunwancin xakin da yasa mu danyen
nama. Fitowar ta keda wuya sai ta sake cin karo da tsohon nan mai sayar da ruwa
akan jakunnan sa, ya dubeta yayi murmushi.
Ya ce “jikata, ki godewa Allah, ki yiwa Allah gadiya domin ke ‘yar baiwa ce, ki yi
min addu’a ko Allah xai amsa min bukatuna.”
Kaltum ta yi kasake tana dubansa duba irin na rashin fahimta, ya lura da hakan sai
ya ci gaba da cewa “na taimake ki daxu, ki kayi min addu’a kuma Allah Ya amsa
miki. Ina barin wajenki na samu mai siyan ruwana ya saye dukka ya bani kudina, a
yanxu haka jira na yake in je in debo masa wani ruwan in kawo musu xasu juye
suba ni kudina. Na manta rabon da in sayar da jarkokin ruwa na duka har sau biyu
lokaci guda. Yaya sunan ki!”
Ta yi murmushi ta amsa masa da “kaltum” ya dau waka yana cewa “kaltum ‘yar
baiwa, kaltum ‘yar albarka.”
Ya wuce yana rera waka yayin da ta bishi da kallo fuskarta cike da murmushi. Ta
fara xaiyano mutanen da suka fara sonta a rayuwa. madina, mai ruwa sai kuma
xaibu wacce ta bata gurasa yanxu.
Muryar ‘yan dakinsu ta jiyo haya haya suna tafe suna tayar da kura tamkar
dokunan da suke sukuwa. Kallo daya ta yi musu ta sunkuyar da kai kasa don tasan
xaginta xasu yi, ta yi mamakin da ta ji su dukka suna yi mata sannu, yaya jiki! Ta
amsa musu “da sauki.”
Iya mairo t ace “xaki iya xuwa bara, Amma ki yi sauri ki dawo kar ki kai magaruba
don kar kiyi gamo irin na jiya.”
To pa, anya kaltum tana sane da halin da ta shiga jiya kuwa!
Meye dalilinta na shiga wannan halin!
ADON DAWA 5
.
Kaltum ta tambaya a bayyane “gamo, wane irin gamo!”
Rakiya t ace “kin fi kowa sani ki ke tambayar mutane.”
Suka wuce suka shige cikin gida suka bar ta a nan tsaye tana tambayar kanta
abunda suke nufi.
“shin me ya faru da ni jiya har ake ta min sannu!”
Ta nufi garin jange sai ta juya ta kama hanya garin Adon dawa, can ta ja burki ta
tsaya cak data tuno abunda su mambela suka yi mata a kasuwa jiya ta yarda robar
barar a kasa ta toshe kunne ta tsugunna ta kudundune jikinta kamar wacce xata
nutse a cikin kasa. Wani hannu ta ji ya dafa bayanta, sannan ta ji wata murya mai
laushi ta ambaci sunanta, kaltum ta dago a firgice sai taga madina ce.
Ta tashe ta tsaye, ta tambaye ta lafiya! Me take yi a tsugunne a nan! Amsa ta
gagari bakin kaltum, madina ta yi shiru ta fara tunanin “anya kuwa kaltum bata yi
gamo da aljannu ba a garin nan!”
Kaltum tace “bara xanje.” Ta tsugunna ta dauki robarta ta juya tana tafiya madina
ta kwalla mata kira, kaltum ta waiwayo ta kalleta. Madina t ace “kin tabbata xaki
iya xuwa bara yau! Domin baki da lafiya.”
Kaltum ta gyada kai t ace “xan iya xuwa” madina ta bita da kallo har said a ta yi
nisa sannan ta juya ta shiga gida.
Garin jange

3 / 46