Advertisements
Chapter 11 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 46

30K to 33K   out of 137K words

yayi barci, sai ya kaini gidan wani abokinsa mai suna Dauda da
matarsa ramma itama mun saba da ita a garinmu, suma basu dade da dawowa ba daga
onisha. A nan na kwana shi kuma ya tafi gidansu har gari yawaye”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya ta gyara xama t ace “yaki na gaba ahse, yaya kika kasance a
garin gurjiya da dangin tasi’u musamman ga wacce aka bashi ya aura ya bujire ya kawo
ki, ke ba bahaushiya ba, ba muslma ba?
Kuma can gidanku yaya xasu ji idan suka ji an ce kin gudu? ”
Madina ta digo da kwallar data cika mata ido ta yi murmushin karfin hali tace, “idan ki ka
ce yaki daya kenan. Yake-yake xa kice. An tafka yaki badan kadan ba tsakanin tasi’u da
‘yan uwansa harta kai ta kawo dole ya dauke ni muka gudu kano saboda sun ki su tsaya
su fahimce shi. Ba su ma saurari abunda yake fada musu ba, yana kokarin shaida musu
ba aurena xai yi ba. Ya kawo ni ne dan a musuluntar da ni in xauna a cikin musulmai dan
ni yanxu kafura ce. Sai gudu da tsallake Katanga ake yi a garin duk gidan daya shiga da
ni wai ga arniya, ko giftawa nayi ta gefen randa sai an fasa randar ko an kwalfe ruwan an
xubar. Kiyayya iri-iri har naji jikina yayi sanyi, dan ban dauka haka wasu musulmai suke
ba. A tunanina duk musulmai masu kirki ne da son jama’a, sai naga suna kora ta suna
guduna har nace masa ya mayar da ni garinmua na fasa xama da musulmai. Tasi’u yaki
yace in dauko kayana mu gudu cikin garin kano, haka kuwa aka yi ya kawo ni kano
unguwar yan kaba wajen limamin unguwar. A nan aka musuluntar da ni kuma a lokacin
tasi’u ya biya kudin sadakina aka daura mana aure a take
A lokacin ‘yan uwa musulmai suka dinga tallafa mana, masu bamu sababbin suture kala-
kala. Aka bamu kudi masu yawa sannan wani attajiri a unguwar mai suna general tukur
ya bamu aron wani dan karamin gida a jikin gidansa, gidan mai kyau kuwa daki biyu, sai
kicin da bandaki ga tsakar gida a sumulce da sumunti. Matan unguwar suka hada kudi
suka dinka min hijabai aka ce in dinga xuwa makarantar islamiyya a unguwar. Ni da
mijina muka sayi katifa, labulaye da kayan kicin muka xauna, xaman aure cikin farin ciki.
Turanci ya fara ratsa bakin tasi’u yayin da ni kuma hausa ta fara kama bakina don haka
muka dinga fahimtar juna.
Tasi’u yana jin dadin xama da ni saboda duk sanda matar bahaushe ta hadu da matar
kabila tabbas kabilar nan xata kwacewa matar bahaushe miji badan komai ba saidan mu
mun saba da aikin karfi ba aikin gida ba ma kawai. Kinga daga inda aka kira sallar asuba
nagama barci sai wani daren kuma. Ni ce shara, wanke-wanke, wankin bandaki, wankin
kayana, wankin kayansa, gugar kayansa dama sauransu. Ladabi da biyayya kuwa ba
iyaka domin ba ma mikawa miji abu a tsaye sai mun durkusa, idan ya ajiye min tsinke
yace, kar in tsallake bana tsallakawa, ban taba yi masa musu ba balle mu yi fada duk
abunda yace min ko bana so haka xan yi. Ina jin dadin xamana da tasi’u saboda bana
aikin wahala irin na da wanda nake yi a garinmu. Tsakanina da makwabtana sai gaisuwa
da hirar mutumci, haka na yi kawaye da dama a makarantar islamiyya. Kwakwalwata
kuwa tar ta bude duk wani karatu da xa’a koyamin sai ya shige, gani da nacin koyo.
Tasi’u ma bashi da ilimin addini sosai shima makarantar maxa ya shiga da daddare suke
yi a masallaci. A kasuwar bakin asibitin murtala tasi’u yake kasuwancinsa yana sayar da
danyen abinci kamar shinkafa, masara, gero, citta da ma sauransu. Sai a lokacin damina
yake xuwa garinsu ya noma gonar gadonsa domin babansa ya dade da rasuwa
mahaifiyarsa ce kawai sai ‘yan uwa jibgi guda mata da maxa. Tun mahaifiyarsa na kin
amsa gaisuwarsa har dai ta huce ta fara amsawa, ta huce amma koda wasa baya
marmarin kai ni garin, nima bana marmarin xuwa garinmu. Shima tasi’u bai sake
waiwayar onisha ba sai dai labari ya kai kunnen ‘yan uwana cewar ina tare da tasi’u a
kano. Da sun yi shawarar su xo su tafi da ni, sai bokansu yace a kyale ni xan dawo da
kaina, akwai tsibbun da xai yi xan dawo da kaina. Amma fa karya yake domin addu’ata
tafi tasu karfi.
Na dade ban samu haihuwa ba don haka na dinga kokarin neman ilimi ta dukka
bangarorin biyu Qur’ani da boko.”
Kaltum ta tambaya cike da mamaki tace “ta yaya kika shiga makarantar boko alhali kina
matar aure kuma ko primary baki yi ba?
To, mu hadu a #LITTAFI kashi na biyu,
ADON DAWA LITTAFI NA 2 (P 12)
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina t ace “da kyau, na ji dadin tambayarki, wannan yana nuna min kina fahimtar
labarin da nake fada miki. Da farko dai ban taba xuwa makaranta ba kamr yadda na fada
a baya amma duk yaran gidanmu ‘yan boko ne don haka tun ina karama na koyi A B C D
har xuwa xed sannan na iya 123 har xuwa dubunnai, xan iya kirgawa kuma na iya
rubutawa. Sannan nasan yadda ake rubuta sunan abubuwa da yawa kamar su hen, cup,
ball da dai sauransu. Dalilin da yasa ba xan wahala a boko ba saboda na iya turanci duk
da turancin ba turanci ba ne sak (broken English) ne amma muna jin mai kyan din, duk
abun da ka fada min da turanci xan ji kuma xan mayar. Don haka satifiket din primary na
je aka yi min a dakata special primary school.
A makwabtan mu wato gidan attajirin nan daya bamu aron gida wato general tukur .
akwai wata budurwa ‘yarsa mai suna sumayya tukur. Sumayya sa’ata ce shekarunmu
goma sha takwas har ta gama secondary, ajinmu daya a islamiyya. General tukur
mahaifin sumayya babban soja ne, mai arxiki ne, gawurtaccen dan boko ne, gidansa
rayuwar turai ake yi tsantsa. Yana da ilimi matarsa hajiya hafsa cikakkiyar lauya ce har
ma tana koyarwa a jami’ar bayero ta kano, don haka su sumayya da kannenta ‘yan gata
ne basu san talauci ba balle wahalar rayuwa.
Sumayya tukur itace babba a gidan kuma itace kadai mace, duk kannenta maxa ne har
guda hudu. Mai bin ta sunansa tukur tukur ana kiransa da abba shekarunsa goma sha
uku a lokacin, kinga kenan sumayya ta girme masa da shekarunsa goma sha daya, sai
Hassan da hussain ‘yan auta shekarunsu bakwai bakwai. Tabbas mun shaku da ‘yan
gidan duk unguwar ana mamakin ni da mijina kadai muke wadaka a gidan, mu shiga
gidan mu fita a duk lokacin da muke so, haka suma yaran suke safa da marwa a gidana
koda yaushe. Duk da sojojin da suke gadinsu suna hana kowa shiga gidan amma ni basa
hana ni saboda hajiya hafsa tukur ta ce kada su hana ni shiga komai dare. Maigidana ma
duk sanda ya bukaci ganin general tukur kai tsaye yake shiga ayi masa iso, ya shiga ya
gan shi ya taimaka masa da duk abunda yake nema.
Allah ne gatanmu, general tukur da iyalansa sune gatanmu. Barrister hafsa itace uwar
dakina itace tamkar uwata a kano tunda bani da kowa a kano. Ita take ba ni shawara, ita
take fada min gaskiya idan na kuskure. Abubuwa da yawa idan ta sayawa ‘yarta
sumayya nima sai ta saya da ni musamman dinkunan sutura ko bata yi mana iri daya ba
tana kwatantawa nima tayi min. yawanci duk abunda suka dafa xata sa masu aikinta su
xuba su kawo min. nima kuma ina iya kokarina wajen xage karfina in tsaftace mata gida
ko tana nan ko bata nan xan hau sama bangarenta ko bangaren mijinta in tsaftace shi
tsaf,
(TAB!!! NI SADIN MAA ME TYPING NA CE “SAM, BANNA YARDA WATA TA GYARA MIN
DAKIN MIJI EHE. DAN ANTY ME POSTING, KO KUWA DA KA YARDA WATA TA GYARA DAKIN
KA BAYAN MATAR KA? )
( tab , ai ni Sadin Maa ko er aikin ma baxan yarda da ita ba, idan kawai naga aikin xai yi
wa mata ta yawa sai na karo wata ta biyu ta xo a taimaki juna )
Har bata so masu aikinta suyi mata gayarn daki idan ba niba, bata ganin dai-dai saboda
na fi su iyawa. Haka take aikawa in xo in yi mata wankin bandaki ko goge gogen kura, ko
dahuwar abinci kala-kala irin na garinmu musamman dakan sakwara.
Daga in da na fara sha’awar boko sai yadda naga ana rugurguxa turanci, ana
xaxxankada rubutu a gidan ni ban iya ba sosai. Kullum mummy hafsa t ace min “madina
dama ace kin yi boko da kyawunki ya kara futowa, haka da kin fi xama ‘yar gayu da
gogewa.” Sai na ji na fara tunanin ta ina xan fara karatun boko dan haka na sauke
girman kai na xauna xaman dirshen da biro da littafina, kawata sumayya take koya min
idan bata nan kaninta tukur (abba) yake koya min idan na iske mummy hafsa a gida
bata je aiki ba itama sai ta koya min, kan ka ce kwabo na fara gane me nene boko, ko
ina gida na abba yana shigowa ya koya min ni kuma ina nacewa ina tilawa har cikin
dare. Tasi’u mijina baya hana ni duk abunda nake so shima dai bai yi boko ba amma
bashi da niyyar koya kuma bai hana ni inje in koya ba. To kin ji yadda na koyi boko daga
wajen makwabtana don karfin hali ma harda biology da chemistry sumayya take koya
min da yake science tayi.
Ina da shekaru goma sha tara a duniya na haifi dana na fari, aka saka masa suna Abdul
malik, na yaye shi kenan na haifi kaninsa Abdul hakim. ‘ya’yana biyu kenan tamkar ‘yan
tagwaye kamarsu daya sak. Farare sol da ni suka yi kama basu dauko kamannin
mahaifinsu ba. Sumayya kuwa karatun likita take yi a B U K yayin da kaninta abba ya
kusa kammala secondary, shima dai ya dage yaketa koya min karatu, ni dole sai na koyi
boko nima. Yana matukar burge su, su duka har daddy su ya fada ya sake maimatawa
cewa shi kuwa in har xan dage in koyi karatu in nemo makaranta duk tsadar ta xai biya
min. sumayya da abba kaninta suka shiga tunanin ta in da xan fara karatu a makaranta.”
Da muka nemi shawarar mummy hafsa wacce makaranta ya kamata in shiga , gani
harda ‘ya’ya, sai t ace tunda ina da kokari har ma na fi wata wacce ta gama secondary
sanin karatu, to inje in yi register a wata private school wacce ake yin lesson a duk
lokacin da jarabawar WAEC ta karato wacce ake koyar da darussan da akayi a SS3, ana
amsa past question papers na WAEC.daddy ya biya min nayi register WAEC sannan nake
ta xuwa daukar darasi har na tsawon watanni uku kafin ranar jarabawar.
Na xana jarabawar WAEC na sami credit shida aka bani certificate da testimonial, kamar
yadda na fada miki daman na sami certificate da testimonial na primary school tutuni.
Kaltum tayi dariya t ace “’rabo ne wannan, ba kiyi boko ba amma kin xama ‘yar boko
dole.”
Madina t ace “sa kai ance ya fi bauta ciwo in ji masu iya Magana. Naci ne da son karatun
na saka a xuciyata sai kuma kwarin gwiwa da na samu daga masu koya min, musamman
abba yana mutukar karfafa min gwiwa.
Haka xa kiji yana cewa sister madina xa ki iya karatu ki dage.
To ko jikina yayi sanyi na daina koyo sai yasa in dauko littafi in ci gaba. Da yake abba
yana matukar jin turanci ya taimaka min wajen gane abunda yake koya min, haka irin
tsadaddiyar makarantar da suke yi mai kayu ita ta kara musu sanin abubuwa da yawa
suma suka koya min, ga lesson teachers dinsu ko wane subject suna da malaminsa.
A bamgaren addini kuwa idan ban koya musu ba, su ba xasu koya min ba, islamiyyarmu
daya dasu haka malamin da yake koya musu a gida nima ina shiga ya koya min , bikin
saukar mu tare aka yi mana da muka sauke Qur’ani mu uku, ni sumayya da abba babu
abunda suka bambata ni.
Abu kamar wasa sakamakon jarabawar WAEC dina ta fito, ina da credit shida da pass
uku haka ya taimaka min na shiga school of hygine inda na karanci aikin jinya. To kinji
yadda na xama ma’aikaciyar asitbiti kenan shi yasa na iya dinke miki ciwo, na iya allura
da bada magunguna.
Kaltum tace “na ji duk wannan sai dai na damu in ji dalilin da yasa ki ka rabu da mijinki
da ‘ya’yanki ki ka taho nan alhalin kina cikin rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali.
Mijinki mai sonki, ‘ya’yanki a hannunki kina kula dasu ga makwabtanki masu son ki suna
taimakonki. Ba dai mai gidanki ba ne ya rasu, ‘yan uwansa suka debe ‘ya’yanku suka
kore ki?
Madina tayi murmushi sai ga hawaye yana ta sirnanowa daga idanuwanta. Hankalin
kaltum ya tashi ta shiga yiwa madina tambayoyi “me yasa kike kuka?
Ma ya faru da tasi’u? ”
Madina ta rushe da kuka tana Magana cikin kuka mai tsanani t ace “kaltum, dole ne inyi
kuka dole ne in ji ciwon abunda ya faru da ni har bakin cikin abun ya fito dani xuwa nan.
Kaltum ta tambaya “anty me nene ya far? ”
Madina ta sharce hawaye da gefen hijabinta t ace “na kammala school of hygien nakarbi
certificate dina yayi kyau cinye dukka. Haka sumayya ta xama cikakkiyar likita ta auri
abokin karatunta shima likita dan gidan shahararren masu kudi ne sunansa dr basher,
gidansu na korau road. Kaninta abba kuma ya yi nisa da karatunsa na lauyer a BUK har
yaje law school .
Ni kuma har na sake haihuwa na haifi ‘ya mace mai suna shahida, yarinyar nan duk ta fi
mu kyau duk da itama ta yi jawur da ita mai hanci dadan karamin baki, mahaifinta ya fi
sonta haka su sumayya da mahaifiyarta suke son shahida, musamman abba ko da
yaushe yana yi mata siyayya ya dauketa a mota ya xaxxagaya da ita. Alhamdulilla duk
da tasi’u bai yarda inyi aiki ba amma na yi karatun na ajiye kwalin shi kuma harkar
kasuwancinsa ta bunkasa dan saida ya sayi gidan da muke ciki na genersl tukur, duk da
yayi masa rangwame sosai amma ya biya fiye da rabin kudin gidan na xahiri, har ma ya
kara da wani fili da yake bayanmu ya hade yakere mana gidnmu ba laifi dai irin na rufin
asiri ga ‘yar motarmu a gareji. ‘ya’yana suna karatu a makaranta me kyau don haka
hankalina a kwance in ci mai kyau ga sababbin kayan daki dana falo duk tasi’u ya canxa
min, sutura sai dai in bawa talakawa jace.
Sumayya na taimaka min da kayan sawa kal-kala haka ma duk sanda na je ko ta xo tana
ba ni, haka abba kaninta aminina ne sosai, duk wata damuwata ko ta yarana idan na
fada masa xai yi min komai yawan kudin. da yake mahaifinsu yana wadata su da kudi
mai yawa. Ni da ‘yayana shar damu, bana tunanin wani abu wanda xai batamin raina in
ba tunanin dan uwana ba innamani, sai takaicin rashin sanin addinin musulunci da iyaye
na suka mutu cikin rashin sani da jahilci bana marmarin daidai da rana daya in leka
garinmu. Amma dangin mijina sun huce dani suna xuwa nima ina xuwa sai daga baya ne
ma surukata ta rasu.
Abu na farko da tasi’u ya fara shine bayan ya wadata mu ni da ‘yayana sai ya tarki Karin
aure don daman na lura da yanayin gini da yayi (MAXA……….) na xaman mata biyu ne
ban yi masa Magana ba sai na xuba masa ido har sanda ya gama xagayensa ya sanar
min xai kara aure. Dole ne in jiba dadi amma ban isa in nuna masa ba saboda tsoronsa
da nake ji, ban isa yana fada ina fada ba sai dai nayi kukan xuci sannan nayi kukana a
daki na lallashi kaina saboda ban ga inda na ragi tasi’u ba da har xai yi sha’awar kara
aure, nayi addu’a Allah Yasa ya auro min ta gari wacce xamu xauna lafiya.
Allah cikin ikon Sa aka auro min kishiya mai suna sa’ada ‘yar cikin garin kano ce sai dai
kash bata kaunata bata kaunar ‘ya’yana, bata so a xauna lafiya. Duk da bana kula ta
muyi fada amma duk shiru na sai tayi abunda sai na yi Magana. Tasi’u har mamaki yake
bani, bamu taba fada da sa’ada ba tasi’u yabi bayana koda yaushe nice marar gaskiya
itace mai gaskiya kullum ina ta hakuri ko sumayya bana fadawa haka ban taba fadawa
mahaifiyar sumayya ba halin da nake ciki ba sai dai sun kula ina ta rama, walwalata ta
ragu kamar ina cikin damuwa, ko sun tambaye ni sai in ce babu komai.
Abu yayi taci gaba kullum wulakanci karuwa yake, tasi’u da matarsa suna yi min abunda
suka ga dama bana iya ramawa harta kai ta kawo tasi’u ya fadawa sa’ada asalina da
yadda muka hadu. Sai na ji yarinya kullum tana yasar min da habaici tana cewa da
ba’asan asalin balbela ba da sai tace madina ne sunanta na asali kuma madina ne
garinsu.
Na san madina sunana ne amma kuma madina garin ne baxan kulata ba sai taga kamar
dai ita kadai take rawarta take kidanta bani da lokacinta don haka ta tare ni kiri-kiri ta
goranta min cewar ni arniya ce inyamura, shegiya ce marar uba, na biyo saurayi kano na
musulunta. Ko a mafarki yadda nake da tasi’u ban xaci xai kwance min xani a kasuwa ba
komin dadin xama komin duk dadin xance da amaryarsa ba, amsa daya na bata shine
nace “nagode Allah da har na gane na dawo hanyar gaskiya na musulunta har na xo nafi
ta ilimin sanin Ubangiji ita da take takama asalinta musulma ce, n ace tayi asara tunda
aka haife ta a musulma ta girma a musulma amma bata iya karatun sallah ba har yanxu,
kuma kar kice nayi mata sharri da gaske nake, jahila ce bata iya ba din.”
Kaltum tayi dariya ta yi tafi hade da shewa harda buga kafa kasa tace, “kin burge ni
anty, amma abun da kika fada mata yayi mata ciwo ko? ”
Madina t ace “lallai kuwa abun ya kona mata rai sosai harma ta fini damuwa, ta dauki
kuka ta shiga daki ta dauko gyalenta ta fice ta tafi gidnsu kinsan me tace?
Kaltum tace “a’a”.
Madina tace, “gayyar ‘yan uwanta ta dauko min mata da maxa suka iske ni har falo suka
xage ni harda yayarta daya da take kokarin dukana aka rirriketa sannan suka fita daga
gidan da kyar, suna kira na da arniya.”
Madina ta fashe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kuka t ace “sa’ada ta bi ‘yan uwanta
suka koma gidan su, tasi’u ya dawo daga kasuwa da rana, na kawo masa abinci ya fara
ci sai ya tambaye ni ina sa’ada yaga dakinta a rufe? Na c eta tafi unguwa amma ina
tunanin gidansu ta je. Nan da nan ya buga mata waya, sai ta fara fada masa cewar
xamansu yakare tunda matarsa take

11 / 46