Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
duk hirarda za a yi a gaban
sumayyah akeyi sai dai a tsakanin waya wato text masseges yana turo mata dadad'an
kalamai masu shiga zuci sai tayi murmushi ta lumshe ido, amsar da take bashi bata
wuce na gode,
godiyarda take mishi ta ishe shi farin ciki ko bata biyashi daddad'an kalamai ba ya lura
Madina ta fara sakin jiki dashi, ta nuna a fili karara tana son shi,
koda yaushe Madina tana damun Abba ya kira alh Adnan a tambaye shi kaltum kuwa
lafiya bata zuwa gashi ba tada lambarta?
sai Abba yace sunyi waya dashi yace kaltum tananan lafiya.
hankalin Madina bai kwantaba harsai data sa sumayyah takaita gidansu kaltum ranar
alhamis da yammah ranar da suka tabbatar ba islamiyyah a karkashin wata katuwar
bishiya a kwance a tabarma suka hangota a farfajiyar gidan, kai tsaye suka tunkaro ta
tana daga kwance tana dubansu a zatonta bakin mummy salaha ne sukazo ne manta
don bata dade da komawa Abuja ba, kaltum tace aranta ko su waye wadannan masu
kudine da ilimi saboda kamshin turarenda ya daki hancinta tun basu karaso inda take ba,
sallama suka mata cikin wata lallausar murya saita amsa sannan tayi firgigit ta tashi
zaune ta dube su ta daka tsalle ta mike da sauri sannan ta rugumesu tana murna,
kaltum ta rike baki tana duban Madina tana mamakin irin wannan canjin data gani cikin
dan kankanin lokaci, tace aunty Madina haka kika wani canjawa?
Madina da sumayyah suka kwashe da dariya, sumayyah tace kema kya pada,
Madina tace ke kaltum kya yi zancen canzawa kinga inda kika zama wata katuwa fara
tas wa zaice kece yar yarinyar nan ta ADON DAWA.
kaltum tace aini na shekara uku da zuwa kefa bakifi watannin biyu ba, su dukka sukayi
dariya suka zazzauna suna hira sunajin dadin inuwar, zata kawo musu ruwan sha ma
suka ce yanzu suka sha swan water da juice a mota don haka kaltum ta koma ta zauna,
sumayyah ta dubi kaltum tace gaskiya kin canza saboda jiya madina ta nunamin
hotunanku a bur sudan tamkar an tono ku daga kabari wasu dakwal-dakwal daku yar
'kankanuwa dake amma yanzu dubi yadda kika girma kin zama cikekkeyar budurwa yar
gayu maganar ma kamar turawa,
suka sake kwashewa da dariya su dukka , Madina tace ai kuwa da kyawun p
hoton nan muke gani kaltum dashi take kwana a karkashin pilo a jima ta zaro ta duba ta
mayar,
sumayyah tace naga hotonta da wani zankadeden saurayinta mambela duk da a dawa
yake yanada kyau da ace a birni ne wayayye dan boko da matan kasarnan sun dinga
tuntube suna waiwayensa,
kaltum tayi murmushi yayinda idanuwanta suka cika da hawaye ta dubi Madina tace
aunty mun kasa samun damar da zamu zauna muyi labari tun ranar nake tambayar ki
ina mambela bakiban amsa ba .
Madina tace baki damu kiji labarinsa ba tuda baki sake dawowa ba tun ranar da nazo,
haba kaltum nice fa madinarki?
inzo kasarnan saboda ku amma ki shareni?
kaltum ta girgiza kai tace ba haka bane, nayiwa daddy laifine a ranar saboda nakai dare
shiyasa ya hanani fita ko ina kuma bani da numbarku shiyasa vankira va amma kullum
ina tunaninki, bani labarin mambela bayan tafiyana koya manta da nine?
madina tayi murmushi tace yaya za ayi mambela ya manta dake a rayuwar sa?
kema baki manta dashi ba balleshi dayafi son ki?
kaltum ta gyara zama tace kinsan ya biyoni har Khartoum zamu tafi bur sudan kenan
aka aiko aka tafi dani.
Madina tace kwarai ya gayamin amma na dauka karya yakeyi kokuma ince ya zautu ne
kawai yakeyimin shirme,
Madina ta dinga bawa kaltum labarin halinda mambela ya shiga na damuwa a sanadiyar
rashinta, da yadda ya daga musu hankali ya ce, duk sai sun bar kasarsu tunda kaltum ta
tafi, sai dai daga baya ya hakura, ya yadda da kaddara. Daga karshe ta bata sakon da ya
fada mata cewar ta fadawa kaltum har yanzu yana son ta ba zai dena ba har abada.
Kaltum ta rushe da kuka ta rungume madina, sai ita ma ta dinga hawaye. Sumayya ma
ta tausaya sai ta girgiza kai ta dafa kafadar kaltum.
Ta ce, "yarinyar Mai zai hana ki kwantar da hankalinki, ki cire zuciyar ki daga kansa, ki zo
ki gina sabuwar rayuwa da 'yan kasarku? Dube ki mai kyau ba mu da irinku da yawa a
kasar nan masu suffar larabawa, fulanin asali ki zabi saurayi ki darje, ke ko gwamna ya
ganki sai ya so ya aure ki. Ina ke ina dan ADON DAWA? "
Kaltum ta sharce hawaye ta ce, "zuwa na kasar nan na yi samari masu dimbin yawa,
kuma attajiran gaske, manya da samari, amma bana kula kowa, mambela nake so, sai
dai kash!!! Maganar nan da muke yi sati guda ke nan da a ka bayar da ni. "
Suka dafe kirji su dukka suka ce, "waye mijin? "
Kaltum ta yi murmushin karfin hali ta ce, "Alh. Adnan ne.".
Madina ta gyada kai ta ce, "yayi daidai, kin yi dace da miji na gari, mai tausayi wanda
yasan darajar mutum. Kin yi dace da mijin da yake matukar son ki ba don komai ba, sai
don Allah, kamar ni da Abba, tabbas mutum ne mai kirki, kun dace, Allah Ya barku tare ".
Madina ta dafa kafadar kaltum ta ce, "me yasa kike kuka alhali kin dade da sanin yana
son ki, ke ma kuma kina son sani? Mambela yana son ki, amma kin san auren ku, abu ne
mai wuya, saboda kun yi hannun riga wajen dabi'unku, yarenku da kasar ku, ba a san
asalinsa ba, ba a san inda ya fito ba, zai yi wuya a yarje masa ya aure ki".
Kaltum tace, "nasan da haka, amma ni ina son mambela, ina tsoron matar Alh. Adnan
mummy salaha, takura min zata yi ni da iyaye na".
Madina tace alh Adnan bazai bari ta cuce ki ba itama auranta yayi kamar yanda ya
auroki, babu abunda zata iya yi miki, yaya akayima ya furta zai aure ki?
kaltum tace bai fada ba, babane yace ya bashi ni, da farko bai amsa ba sai acikin
wannan satin yan uwan baba suka sameshi a zangon Daura suka sake mishi magana
sannan ya yarda , yanzu jira ake jarabawar jamb dinda nayi ya pito inga inda suka bani
domin nacika U.B.K Da gwagwalada Abuja, idan kano suka bani sai ya gina min gida a
kano ayi bikin idan kuma Abuja ne sai akai ni Abuja.
madina tace babu komai kada ki damu Allah Ya sa haka shine mafi alkhairi, kaltum na
lura duk hankalinki atashe yake har kin rame ba kamar sanda na ganki ba kwanaki, alh
Adnan din naki kike ki?
haba kaltum idan kikayi masa haka baki kyauta masa ba, suma iyayanki sunga babu irin
godiyar da zasu mishi ne illa subashi ke domin yayi dawainiya dake kowa yasan yana
son ki.
kaltum ta matse hawaye tace ba kiyayyarsa bace ta sani damuwa ba, nauyin sa da
kunyarsa nakeji tamkar babana na dauke shi, ramewa da kiga nayi bai wuce Zafin
mutuwar goggo fattu ba da har yanzu take damuna.
madina ta zabura ta dafe kirji tace InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu goggo fattu ta
rasu?
kaltum ta matse hawaye tace yau sati biyu kenan a zangon daura akayi jana izarta bamu
dade da dawowa ba, ai acan yan uwan baba suka hadu sukayiwa alh Adnan maganar
auren mu dayaje gaisuwa daga baya ma matarsa taje dana gaishe ta bata amsa ba,
shine yasa nashiga damuwa nasan halin kishinta zata iya babbakawa kishiya wuta.
madina da sumayya suka cigaba da bata shawara da nasihohi masu kwantar da hankali
sannan sukace ta rakasu wajen iyayanta don su musu gaisuwa,
Madina ta karbi numbar wayar alh Adnan tace idan taje gida zata kirashi tamishi gaisuwa
sannan su tattauna don taji ra'ayinsa akan maganar auren.
a haka suka rabu kaltum ta raka su har wajen get inda suka ajiye motarsu suka shiga
suka tafi ita kuma ta dawo gida.
tafiyarsu Madina da kwana uku alh Adnan ya kirawo kaltum a waya, cikin rawar murya
da fargaba ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a yace gobe ki shirya danladi yakaiki
gidansu Madina ki yini, da yamma ya koma ya dauko ki,
ta amsa da to na gode, bayan yakashe wayar sai mamaki ya rufe ta nan da nan takira
Madina tana tambayarta yadda sukayi da alh Adnan don yanzu ya kirata yace gobe taje
su yini,
madina tayi dariya tace dadin baki na masa na nuna ina goyon bayan aurenku dari bisa
dari shiyasa yaji dadi,
kaltum tayi dariya kawai ta kashe waya.
washe gari da wuri kaltum ta shirya ta caba ado da wata hadaddiyar shadda gezna kalan
jan duhu wato maroon colour wacce akama surfani da brown din zare, riga da siket da
dankwali, ta saka takalmi da gyale kalan brown, tayiwa iyayenta bayananin abunda alh
Adnan ya umurceta tayi sai sukaji farin ciki ya kamasu tunda har akasamu ya fara yi
mata waya a yanzu,
ta kame a bayan motar danladi yaja bai tsaya a ko inaba sai kofar gidan Doc sumayyah
Tukur,
kamar yanda ta umurceshi ta sake umurtarshi daya tafi ya dawo da la'asar, ta shiga ciki
kai tsaye ta iskesu a falo su uku ne kadai Madina , sumayyah da maigidanta Doc bashir,
sunata hira babu abunda yake damunsu arayuwa sai dariya suke kyalkyalawa, suna
ganin kaltum sai suka hau murna ta durgusa cikin fara'a ta gaishesu sannan ta sami
kujera ta zauna.
Dr bashir yace af dama wannan ce kaltum matar mambela dan ADON DAWA?
su dukka suka tuntsire da dariya.
sumayyah ta harareshi kaji har sunan ADON DAWA ya rike, kamar dashi akaje bur
sudan?
shigowar Abba da kaninsa Anas ita ta katse hirarsu aka hau gaggaisawa,
kai tsaye Abba ya wuce gaban Madina ya ajiye himilin ledoji a gaban ta,
ta dubeshi tayi murmushi ta fada cikin sanyanyar murya mai cike da sakon so da kauna
tace Abba bazaka yarda da maganarda nake gayamaka bako?
so kake muyi pada kenan?
nace saye sayen nan naka yayi yawa ka dinga hutawa kaki jiko?
sumayyah Tukur tace a'a mu munaso inke bakya so, da bakya nan ai bai sayo mana ba,
kudi ne dashi, me anfanin kudin in ba aci ba?
Madina ta bude ledojin daya kayan itatuwa ne lemo ayaba da abarba daya ledar kuma
tuffa ce da inibi, daya ledar kuma mayukan shafawane da turarurruka sai wani dan
karamin kati (greeting cart)mai dauke da sakon so da kauna, katin kadai madina ta
dauka ta karanta ta kalli Abba tayi murmushi ta ajiye a gefenta shima irin murmushin ya
mayar mata.
sumayyah Tukur ta dubi Anas tace kaga ka fita daga idona na rufe zan tona maka asiri
idan baka daina turamin sako cikin wayata ba,
sai kowa ya dubesu,
yace yi hakuri 6star ki rufamin asiri, Abba yace sako wani iri kuma?
dr bashir yace eh gaskiya a tona wannan sirrin kowa yaji, ya duk muna zazzaune ka
dinga tura mata sako don gulma?
sumayyah tace ya dade yanason kaltum wai ce min yayi in kira masa ita wancan falon su
gaisa wai in fada mata yana sonta.
su dukka suka kwashe da dariya.
kaltum taji kunya saita sunkuyarda kanta kasa bata sake dagowa ta dubi Anas ba,
madina tace wallahi kuwa kun dace saidai karigada ka makara anbayar da ita da sai na
tsaya maka kanina.
Anas yaji hankalinsa ya tashi yace ai tunda ba ariga an daura ba zan iya shiga filin dagar
adama dani mai rabo ya dauka.
sumayyah tace kadama ka fara shiga filin dagarnan don dakai zata kife wanda za aje
neman aurenta wajenshi shine zai aure ta.
ban fahimce kiba?
Abba ya tambayi yayar sa.
madina tace alh Adnan zata aura nan da yan watan ni,
Abba ya gyada kai yace lallekam babu mai jadashi yaro karma ka shiga bakin rijiya don
ba wajen wasan yara bane, nifa na dauka yayantane da farko sai nace ko babanta ne
ashe shi ya riketa yanzu zai aureta ko sun dace yana da matukar kirki.
Anas ya fice daga gidan, kallo daya zakayi masa ka tabbatar baiji dadin maganarnan ba,
madina taja kaltum dakinta a inda ta dinga nuna mata abubuwan alkhairin da ta samu
dawowarta nan, dinkuna kala kala wadanda Abba yayi mata ta nuna mata wasu
akwatuna masu kyau har guda hudu saiti tace kayan lefenta ne Abba ya fara hadawa,
auren nan da watanni uku, a Abuja zasu zauna sbd acan yasami sabon aiki shine lauyan
babban bankin nan CBN, Madina ta dubi kaltum ta fada cikeda fara a tace kaltum ki duba
kiga yadda Allah Ya canza mana rayuwa cikin dan kankanin lokaci, shi yasa duk halin da
musulmi ya tsinci kansa ya godewa Allah, jarabawa ne idan Allah Ya tashi sakayyah sai
ya juye maka dadin da baka taba zatonsa ba, banda Allah wazai yi mana irin wannan
kyautar?
kiduba kiga yadda ni dake muka canza kada kiyi bakin ciki da duk yadda kika tsinci
rayuwarki, alh Adnan alkhairine da rayuwarki, ko ba a fada miki ba nasan mambela ma
mai kaunarki ne Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya raba ku, ki godewa Allah a duk
halinda kika tsinci kanki.
kaltum ta gyada kai tace hakane aunty Madina nasan da haka ina addu'a kuma zanci
gaba da addu'a har karshen rayuwa ta.
.ADON DAWA P 46
LITTAFI NA HUDU
TRUE LIFE STORY
.
nasan mambela ma mai kaunar kine, Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya raba ku, ki
godewa Allah a duk halinda kika tsinci kanki.
kaltum ta gyada kai tace hakane aunty Madina na san haka ina addu'a kuma zancigaba
da addu a har karshen rayuwata, na godewa Allah kuma bazan taba raina abunda Ya
bani ba.
Madina tace Allah Ya yi miki albarka idan kika rike wannan bazaki taba danasani ba a
rayuwar ki, kiyi addu a kibarwa Allah zabi Shine abunda na rike tuntuni kuma bana
nadama, ta bude wata katuwar leda ta zazzabo mayuka, janbaki da hoda turarurruka da
atamfa ta zuba ta mikawa kaltuma tace gashinan na baki kije kitayin kwalliya naga kina
son ado.
kaltum ta rike baki tace haba aunty kin juyemin kusan dukka ai yayi yawa ki rage nima
duk karshen wata alh Adnan yana bani kudi inje well care super market in sayo kayan
kwalliya.
Madina tace ai ina da su dayawa keda Shahida na rabawa wannan, bakiji ina yiwa Abba
kashedi ba?
cewar ya isheni haka, shiga gowa fita goma sai yayi min sayayyah bansan irin kyawun
da yakeso inyi ba koso yake in koma indiya don kyau oho.
kaltum tayi murmushi tace Abba yana son ki ko minti daya kayi dashi zaka gane hakan,
Madina tace kwarai kuwa nasan dahaka tuntuni daddy Tukur ma yasha kirana har
falonsa ya yita bani hakuri a bisa wulakancinda sukayi min a rashin sani sannan ya
rokeni in saki jiki in kwantar da hankalina inyarda in auri Abba tunda ya tubure duk
duniya babu wacce yakeso saini, kuma ba haramun bane raya sunnah ne saboda
Manzon Allah (s a w)Ya auri nana Khadija (R.A)a bazawara kuma ta girmeshi ya
nuna min kuskuren da nayi a baya dana hana Abba ya bayyana musu halinda yake ciki,
ai ba zasu hana ba saboda sun yarda da tarbiyyata sunsan bazan cuci dansu ba, daga
karshe ya roke ni da rike dan su amana fiye da yadda na rike Tasi'u, inso Abba kamar
yanda duniya ta shaida Abba yana so na, irin wadan nan nasihohi mahaifinsa yake min
aduk lokacin da muka hadu.
kuma duk bayan kwana biyu ina zuwa gidansu Abba inyiwa mummy hafsat duk abunda
takeso kamar share-share da girke-girke,
nida Tasi'u kuwa general tukur yayi mana katangar karfe haka tsakaninsa da Abba,
saboda ya fara takurawa rayuwarsa koda yaushe saiya tari Abba a hanyah yanayi masa
hayania harda cewa sai yaga bayansa sannan nima ya dinga bina kenan har tsakar falon
mummy hafsat wai ni matarsa ce, shine ran daddy tukur ya baci allurar soja ta tashi
yasa sojojin nan suka wurgo shi waje sannan muka sami lafiya.
kaltum tayi ajiyar zuciya tace har ya bani tausayi ma daman haka dunia take hakkin
wani masifa ne idan ka cuce mutum tun a duniya Allah Ya ke fara nuna sakayyah dubi ni
da goggo fattu fa saida Allah ya kaskantar da ita kafin ta bar dunia, tayi nadama hade da
danasani ai ina tsoron daukar hakkin wani.
madina tace haka alkhairi yake idan ka gina alkhairi zaka girbe shi sbd bayan tafiyata
sanda gaskiya ya bayyana sai yan anguwa suka para tausayin 'yayana su kayi ta
kyautata musu musamman ma shahida ko abinci aka hana ta agidansu sai makwabta su
kirata su bata suce Madina muma ta taimakemu alokacinda bamuda shi, su bata sutura
suce madina ta cire kayan jikinta ta bamu idan mukayi sha'awar kayan, kin gani da abun
tsiya na shuka alocinda makwabta dana tsallake na tafi na bar 'yayana sai an zageni a
gabansu kuma baza ataimakesu va.
kaltum bata dawo daga wajen Madina ba harsaida ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali
saboda nasihohi da ta dinga yi mata, data isa gida da farin ciki kaltum ta nunawa
mahaifiyarta abubuwan alkhairan da Madina ta bata sannan ta kira alh Adnan a waya ta
shaida masa ta dawo.
sai yayi mamaki da yaji muryarta radau tana walwala harma da kirkiro masa hira take
sai ya tabbatar da Madina tayi masa gini mai karko a zuciyar kaltum, don haka ya sake
tabbatarwa Madina macece mai nutsuwa da sanin ya kamata.
akai akai kaltum na ziyartar madina haka itama madina tanasa sumayyah ko abba su
kawo wajen kaltum su dade suna tautaunawa da neman shawarwari akan abunda ya
shafi aurensu daci gaban rayuwarsu gaba daya har wata rana madina tazo da daddare
ita da abba koba a fada maka kaga ango da amarya masu matukar kaunar juna sun
burge kaltum matuka yanda taga suna tafiya suna hira wasa da dariya saisu ka mika
mata katinan bikin su,
daya na walima daya daya kuwa sunan alh Adnan dana malam saleh ne shine na daurin
aure,
farin ciki ya lullube kaltum bata san lokacinda tafashe da kuka ba ta rungume Madina sai
ita ma ta fara kuka irin wannan hawayen farin
cikin ne ya surnanowa abba daman ance kuka iri irine na bakin ciki shine mai radadin fita
na farin ciki kuwa sanyi kalau zai fito babu zafi idan ya fito shar sai a goge a yi dariya a
tafa.
.
RANAR DAURIN AURE
asabar ce ranar daurin auren barister Abba Tukur da Madina a farfajiyar gidan general
tukur shine uban amarya kuma daman Uban angone don haka tuwona maina kenan.
kamar yanda kowa yasani babban goro sai magogin karfe ba kasafai zakaga jifgin
talakawa ba a al'amuran attajirai kamar yadda ganeral tukur da iyalansa suke da
matsayi abokansu ma masu matsayine, danginsu masu kudi ne, abokan aikinsu daga ma
aikatan daban-daban sun hallara ma'ana manyan sojoji sunzo don general tukur haka
manya furofesoshi sunzo saboda da barista hafsat tukur jami'a daban-daban, sannan
manyan likitoci daga manyan asibitoci daban daban sun hallara saboda Doc sumayyah
da maigidanta Doc Bashir,
injiniyoyi ba abarsu abaya ba saboda engr Anas, sai dimbun dalibai daga jami'ar
unguwar sun hallara,
saboda Madina don kirkinta alh Adnan da malam saleh suma suna daga gaba gaba,
kusada ango maroka da makada suna nasu aikin yan jarida da hotuna da bidiyo suma sai
dauka suke kowa yana fadar albarcin bakinsa na alkhairi saboda farin ciki.
masu iya magana na cewa da dai dan wani tarkataccen wani, a lokacinda dubbannen
jama a suke cikin shagalin cin alewa da