Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
xaman lafiya a garin nan. Kaltum ta tafi ta bar ni, ban san ta inda xan fara nemo
Nigeria ba, da garin da kaltum ta ke a Nigeria.
Ni mambela na yi alkawarin takura muku, kun daina walwala kamar yadda na daina,
ciwo nake yi a kwance a ranar da kaltum ta xo duba ni, na warke da nag anta, daga
lokacin da na ji an dauke ta a lokacin ciwona ya dawo har yau na kasa samun lafiya. To
daga yau kun daina xaman lafiya don duk sai na kakkarya kafafuwanku daya bayan
daya.”
Kiri-kiri suke yi da ido, yyayin da kowannensu yah au kammala sangalalinsa kada a fara
ta kansa. Madina kuwa ta yi tsuru a gefe kanta a sunkuye a kasa, tasan kowanne
hukunci xai xartar daga kanta xai fra, don haka ta fara tunanin inda ake siyar da sandar
guragu, gara tun da wuri ta tanada.
Mambela ya ci gaba da Magana cikin kakkausar murya, y ace, “babu sana’ar sayar da
komai a kofar gidan nan, haka kada inga kafarku a bakin kogi, wajen kamun kifi. Haka
kada inga kafarku a kasuwarmu jim arab, kad a wata ta xo garinmu bara, sai na karya
duk wanda ya saba wannan doka. Sannu a hankali idan yunwa tai she ku xaku tarkata ku
tafi inda kuka fito, yadda kaltum ta tafi ta bar ni.”
Malam nura wani tsoho daga cikin su madina xai yi Magana, mambela ya dunkule hannu
xai kai masa bugu, abokansa da ke tsaye a gefensa suka rike shi. Suka ja shi suka tafi,
da kyar mambela yake daga kafarsa don tananin tashin hankali. Ya rasa akan wanda xai
huce, takaicin rashin kaltum amma ya fi jin haushin madina wacce ta hana su su yi aure
tuntuni. Sannan da yaradarta aka dauke masa kaltum dinsa.
Suka rushed a kuka suna kiran, sun shiga uku sun lalace, ya ya xa su yi su rayu idan ba
sana’a, ba bara! Madina ta mike a fusace ta fara Magana cikin fushi.
Ta ce, ‘haba jama’a kamar ba musulmai ba, kun manta Allah ne mai rayawa, Shi ne mai
kashewa!kun manta Shi Ya ke tsare mutum, Ya yi masa Katanga da duk wani mugu! Ko
gexau ban yi bad a mambela ya hana mu sana’ar da xamu ci abinci, Allah da Ya
haliccemu Shi xe fito mana da wata hanyr da xa mu ci abinci mu rayu. Jahilci ne ku dinga
kiran shiga uku, ku kira Kalmar “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah Xai yi mana jagora.
Ko me ya samu bawa mukaddari ne, shan ruwan kaltum ne yak are a bur sudan dole ta
tafi, da shan ruwanta yak are a duniya da wayar gari xa a yi a tarar ta mutu ma karewar
tafiya Nigeria.’
Sai suka ji xuciyar su ta yi dan sanyi, sannan kowannensu ya dinga kinkimar kayan
siyarwarsa yana shiga gida don kada mambela ya xagayo ya iske su a kofar gida sana’ar
yau dai ba a yi ba. Sai asarar da suka yi, saboda mai kosai ta yi markade, mai koko ta
dama, haka mai danwake ta kwaba, har gara ma masu shayi da biredi ruwan xafi ne
kadai da lipton suka dafa.
Kwanaki biyu haka su madina suke xaune babu mai sayar da komai, babu bara, babu
xuwa kogi kamun kifi har sun fara jin jiki.
“mambela ya cuce mu, mugu marar imani”. Kalmomin da suke ta nanataw ken an, duk
dakin da ka xo giftawa xaka dinga jiyowa. Suka ga Magana, xage xage a bayan fage ba
xai yi musu magani ba sai suka shiga tunanin hanyar neman sulhu, domin komai da
sulhu ya fi sauki.
Shawara day ace suka tsayar, maxa su hadu su yi kungiya su je su sami mai martaba
sarkin ADON DAWA su kai kukan su, ba kuma karar mambela xa su ce sun kawo ba, a’a
neman a rokar musu mambela ya taimaka ya janye takunkumin day a yi musu, ba laifin
sub a ne da kaltum ta tafi suma bah aka suka so ba.
Haka aka yi said a suka tabbatar mambela ya fice, an tabbatar yana jim arab shi da
abokansa suna shan jabna sannan suka dunguma suka tafi fada, da kyar dai aka yi musu
iso, suka fadi gaban sarki suka yi gaisuwa cikin yaren ADON DAWA, sannan suka koro
masa bayani cikin harshen larabci don shi suka fi iyawa. Suna gama bawa sarki labara
sai ya bushed a dariya ya fada a bayyane har sau uku, “mambela! Mambela!!
Mambela!!!”
Ya ce su tashi su tafi duk su fito da kayan sana’ar su, xa su iya xuwa bakin kogi, haka xa
su iya xuwa jim arab ba damuwa. Babu abunda mambela xai yi musu, su kwantar da
hankalinsu xai yi masa Magana har sai ya huce, daman kuma xafin rabuwa ne.
Godiya suke, addu’ar fatan alkhairi iri-iri suke jerowa sarki. Suka shiga gida suka fesawa
mata bayani, yayin da buda da kidan kwarya ya gauraye gidan nan da nan aka sami
masu taka rawa mata da maxa.
“ga mambela nan da tawagar san an xuwa”. Inji walidi ya rugo da gudu daga kofar gida.
Gudu da buga kafa a jikin katako kararaf ka ke ji ana karo, yayin da aka yi cilli da
kwaryar kida. Wasu suka shige dakuna yayin da wasu bandaki suka cunkusa suka rufe
kofa, wasu kuwa da suka gudu suka buya, ashe karya yake yi, xolayarsu yake. Dariya
hard a faduwa yake yana fadi, “wasa ne ba mambela ba ne”.
Ran kowa y abaci suka firfito daga maboya suna masu jan Allah Ya isa, saboda tsorata su
da yayi, har wasu da yawa sun karkace kafa da jinni.
Washe gari da safe aka rasa wanda xai fara fitar da kayan sana’arsa, kowa ya fito da
kaya tsakar gida amma sun kasa karaswa kofar gida. Wannan ya leka ya dawo, wancan
ma ta leka kofar gida ta dawo daga karshe aka sami xakakura daya ta fara firfita da
kayanta, it ace madina, sannan sauran suka fara firfitar da kayansu su ma. Suna yi suna
waige-waige da suka ji shiru sai suka saki jikinsu suka kwantar da hankalinsu, mambela
ya hakura.
Kan ka ce kwabo jama’ar jange da ADON DAWA dauke da kwanukansu suka taho siyan
abinci domin su ma kwana biyu rashin siyar da abincin ya shafe su.
“ga mambela nan!”. Sama’ila ya fada da karfi, yayin da yake rugawa cikin gida. Dogon
tsaki suka yi yayin da ko waigawa bas u yi ba saboda sun san karya ne, tsorata su yake
so yayi irin yadda walidi yayi musu jiya.
Dif! Kamar an jeho shi gaban su haka suka ga mambela da tawagarsa a tsaye a kansu.
Xancen sama’ila gaskiya ne ashe ba wasa yake yi ba.
Madina bata yi karya ba, Kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’una tana sanyaya xuciyar
mugu ya xamanto mai tausayawa.
Yawancinsu Kalmar da ta xo bakinsu ken an a tare suka fada, kuma a bayyane. Wasu
kuwa cewa suka yi, “ihu mun shiga uku, mun gat a kanmu”.
Suka yi wuki-wuki haka kake ganin idanuwansu a waje saboda tsorata.
Ya tsaya cak! Ya na duban rawar jikin da suke yi ba tare day a ce uffan ba.
Malam gali tsohon da yake sayar da goro ya kasa goronsa a fai-fai. Ya ce, “yaro ka yi
hakuri, na samo maka labarin kaltum. Kaltum na sudan xata dawo kwanan nan”.
Mambela ya tuntsire da dariyar da bai shirya ba, ya sake kyakyacewa da dariya.
Ya ce, “baba, ka sayar da goronka ba xan hana ku sana’a ba, amma kaltum bat a sudan
tana Nigeria. Ko xaka fada min a inda take idan tana sudan!”
Baba ya marairaice y ace, “fada na yi dan ka ji sanyi a ranka don mu ma mu sami sauki”.
Sai gaba daya suka rude da addu’a suna fadin “in Allah Ya yarda kaltum sai ta dawo.
Kuma da yaradar Allah kaltum matarsa ce, duk inda take sai ta dawo.”
Mambela ya ji dadin addu’arsu, sai jikinsa ya yi sanyi, ya sunkuyar da kansa kasa yayin
da kwalla ta cika masa ido. Ya dade a tsaye yana sauraron dadin bakinsu sai ya yi
murmushi ya juya ya dubi madina wacce ke xaune ta sa kaskon kosanta a gaba ta kasa
Magana ta kasa sakin kosan sai hawaye take xubarwa kawai. Ya juya ya dubi gefenta sai
ya ga kamar xai ga kaltum a tsugunne a kusa da ita tana yi masa murmushin nan nata.
Sai ya girgixa kai ya juya ya tafi, yayin da abokansa suka bi bayansa.
Doguwar ajiyar xuciya kake ji a jere a jere. Su madina na yi saboda farin ciki day a same
su, sai kiran hamdala suke da godewa mambela.
A yammacin wannan ranar madina ta sami sammacin kira daga mambela cewar, ta
same shi a bakin teku. Xuciyarta ta harba, amma sai ta yi addu’a ta xari gyalenta ta tafi
ta yrada da cewa Allah xai kare ta, kuma mutum ba xai iya yi wa mutum abunda Allah
bai kaddara xai same shiba.
Rayuwarta da mutuwarta duk suna hannun mahaliccinta. Labarin gixo dai bay a wuce na
koki, ta san xancen bai wuce na kaltum ba. Ita kuwa duk inda gaskiya ta ke ita xata fada
komai dacinta, ba xata fada masa karya ba don yaji dadi. Iyakar abunda ta sani shi xata
fada, abun da xai yiwu shi xata fada masa. Haka idan kaltum matarsa ce xai aureta, idan
ba matarsa ba ce duk inda ya kai ga mayatar sonta sai dai ya mutu ba xai aure tab a,
kamar yadda Abba ya kasance. Har ya rasa rayuwar sa a dalilin damuwar so.
Tana tafe tana matse hawaye yayin da irin wannan kidimewar da mambeala yake yi
suke tuno mata da yanayin da Abbanta ya shiga a lokacin da yake raye a sanadiyar so.
Madina ta isa bakin teku ta karasa inda mambela ke xaune turmus cikin yashi yana rike
da wani dan karamin kara a hannunsa yana wasa das hi a cikin tashi tamkar yaro.
Ya dago ido ya dubi madina, sai tag a ya yi firgita domin hankalinta a tashe tamkar ta fi
shi shiga tashin hanakali. Sai ya yi xumbur ya mike tsaye ya dub eta cike da damuwa ya
tambaye ta cike da damuwa da kuma fargabar amsar da xata bas hi.
“madina lafiya!”
Sai ta rushed a kukan dab a ta shirya ba, jikin mambela ya dau rawa, yayi sauri ya
warware rawaninsa ya shimfida mata. Ta xauna yayin da shima ya xauna a hankali yana
fusakantarta. Ya dafe haba da hannayensa biyu yana dubanta xuciyarsa cike da mamaki
da kma faragabar jin abun day a saka ta kuka daga kiranta.
“madina, me yasa kike kuka! Ki kwantar da hankalinki ba cutar da ke xan yi ba,
tambayar ki kawai xan yi, kuma in nemi shawarar ki game da yadda xan yi in sami
kaltum’. Mambela ya fada cikin sanyin murya.
Madina tad ago da jajayen idanuwanta ta dube shi xuciyarta cike da tausayi. Cikin kuka
mai yawa ta fara Magana.
Ta ce, “mambela, ba kukan tsoron ko xaka cutar da ni nake yi ba, nasan ba xaka iya
cutar da nib a saboda xuciyoyinmu suna son abu daya, ba wani abu ba ne illa kaltum.
Ina son kaltum, ina mata kaunar da nake jinta raina tamkar ‘yata shahida. Ina tausayin
kaltum fiye da yadda nake tausayin kaina. Kana son kaltum na shaida son da kake so ta
xama uwar ‘ya’yanka kana so ku kasance tare har sai mutuwa ta raba ku, ita ma na lura
tana sonka haka.
Mambela ba xan so in xama sanadin raba wannan kyakkyawar soyayyar taku ba, haka
ba xan yi wa xuciyata manakisa ba in raba tad a yarinyar da take kauna tamkar ‘yar da
na Haifa ba saboda ba ni da kowa a nan, ita kadai nake gani inji dadi. A duk lokacin da
nag a kana tayar da hankalin ka akan kaltum sai hankalina ya fin aka tashi, saboda kana
tuno min da Abba wanda ya rasa rayuwarsa a sanadiyar soyayyar soyayya. Mambela na
fi son ka bi abun a hankali kada ka halaka kanka akan rashin kaltum”.
Hawaye ya fara kwaranyowa daga idanuwansa, sai ya tambaye ta cikin sanyayyar
murya, “madina waye Abba!”
Ta dade tana kuka kafin taiya fara ba shi labarinta. Ta bas hi labarin rayuwata tun daga
farko har karshe kamar dai yadda tab a wa kaltum a baya.
Mambela ya dade yana duban madina ya kasa Magana saboda tsananin tausayinta, yayi
nadamar takura musu da yayi, yayi nadamar laifinda ya dora mata a game da tafiyar
kaltum. Ya tsunduma tsundum! Wajen tunanin yadda rayuwar Abba ta kare, ya kuma
sake firgita akan yadda rayuwarsa xata kasance a nan gaba dan ya lura cewar soyayya
ba abu b ace da xa’a ce maka ka rage ko ka kara, ko kuma ka daina.
Yana matukar iya kokarinsa wajen cire son kaltum da dannewa amma abu ya ci tura,
kullum sonta karuwa yake a xuciyarsa. Ba ya addu’ar haka ta faru, amma daga dukkan
alamu haka ne xai faru, yana ganin xai rasa ransa a hanyarsa ta xuwa nemo kaltum
kamar yadda Abba ya rasa ransa a hanyar sat a xuwa garin su madina.
Madina c eta katse tunanin da yake yi t ace “abun da nake so da kai , ka yi hakuri, ka yi
ta addu’a ka xubawa sarautar Allah ido, Ya yi muku hukunci akan abunda Yak e so.”
Mambela ya dub eta y ace, “ina so ki taimake ni kiyi min alfarma daya bad an kina so ba,
sai don ki ceto rayuwata don gudun kada in rasa raina kamar Abba. Ki janye ra’ayin nan
naki nab a xa ki kara komawa Nigeria ba har abada, saboda ni da kaltum xa ki janye, mu
shirya ki rakani kano in nemo kaltum a jirgi ko a mita, duk wanka kike so.”
Tashin hankali marar musaltuwa xaka iya ganewa daga duban idanuwan madina. Ta ji
kirjinta ya harba “bum!” saboda bata kaunar ta koma kano, bat a fatan ta sake yin ido
hudu da duk wanda ya santa da.
Mambela ya sake nanatawa, ‘ki taimake ni madina mu tafi a satin nan. Don yau wata
hudu da kwana hudu kenan da tafiyar kaltum kada mu dade aje ayi mata miji ko wannan
Alh. Adnan din ya aure ta don daga labarinda ta bani na lura yana sonta, damuwar da
yayi a kawota na san auren ta yake so ya yi.”
Madina ta ci gaba da kallon mambela tana mamakin yadda ya san labarin Alh. Adnan ,
tabbas kaltum na son shi da yawa tun da hart a saki jiki take yi masa hira duk wannan
xurfin cikin nata.
Can ta nisa ta sunkuyar da kai kasa, don tambayar da xata yi masa ba xai yiwu ta iya
hada ido das hi ba, saboda nauyinta, ta tabbatar ba xata yi masa dadi ba.
Ta ce, “misali idan ka je Nigeria aka nemo gidan su kaltum ka ci sa’a ka iske kaltum ka
tambayi aurenta, iyayenta suka ki amincewa ko kuma ka je ka tarar har an ba wa Alh.
Adnan ya riga ya aure ta. Yaya xaka yi, kuma me ne amfanin xuwanka!”
Kallo daya xaka yiwa mambela ka tabbatar xuciyarsa c eke tafasa saboda xaxxafan
kalamanta. Ya kasa ba ta amsar tambayarta .
“mambela ina mai baka shawara ka yi hakuri ka kara hakuri, ka yi addu’a Allah Ya xaba
muku abun day a fi alkhairi”. In ji madina.
Ya sunkuyar da kansa kasa saboda takaicin furucinta, don idan ya ci gaba da kallonta
xuciya xata iya daukar say a yi mata diban karan mahaukaciya.
Madina ta yi ajiyar xuciya t ace, “a rayuwa babu wanda ya fi mahakurci cin riba, babu
wanda ya fi mai tawakkali nasara, haka babu wanda ya fi mai yarda da kaddara morewa
a nan gaba. Ka sake hakuri kuma ka tsananta addu’a…..”
Mambela ya katse tad a cewa, “shin xan mike kafa in dinga kallon gajimare ina jiran
kaltum ta fado gabana! Ba sai na je nemanta ba Allah Xai dubi xuciya ta sannan Ya amsa
addu’ata in nemota ba! Xaki raka ni kasar ku ko ba xaki raka nib a!”
(DARIYA, SU ‘DAN ANTY HO!)
Madina ta yi murmushin karfin hali, t ace, “mambela, ban san kaltum ba sai a mota,
haka ban san daga inda ta bullo ba.”
Ya fada a fusace, “amma dai kasarku daya, kuma garin daya, kano ko! Idan muka je
kano mun yi mai wuyar. Ni kadai xan iya xuwa kano, amman ban san kowa ba, ban san
ko’ina ba, idan babu ke ina nasan hanyar da xan fito daga airport ko tasha! Gara da ke a
kalla kin san garin kano, kin san sunan unguwar su kaltum. Kin iya yaren ‘yan garin
yadda idan kika tambaya xa a nuna miki. Ban day arena sai larabci nake ji, wanda kun ce
ba a larabci a kano sai hausa sai turanci, ni kuma ban iya ba. Shine taimakon da xa ki iya
yi min a rayuwata madina.”
Ta girgixa kai ta sharce hawaye t ace, “mambela, ba xan yaudare ka ba, baxan boye
maka ba, ko gawata ban a so a kai ta kano saboda abun kunyar da jama’a suka lika min.
ka yi hakuri ba xan iya xuwa Nigeria ba, har abada.”
Mambeala ya ji tamkar ta dauko wuka ta kirba a kirjinsa. Ya dub eta, duba na takaici ya
cije lebe hawaye yana xuba.
Ya ce, “babu wani taimako ko amfani da xa ki yi min a rayuwata wanda ya wuce wannan,
kum kin ce ba xaki yi ba, alhali kina da halin yi min. madina ba kid a sauran amfani a
wajena, ba kya kaunar kaltum, ba kya kaunata ki sani duk halin da na shiga ke ce sila.
Bana so in sake ganinki a gabana, bana fatan mu sake xama ni da ke irin wanan tun dab
a kid a niyyar ceto rayuwata.”
Madina ta fashe da kuka cikin mummunan tashin hankali, don jin kalaman mambela.”
Ya daga hannu ya dakatar da uta, yayin day a nuna mata hanyar gidansu, ma’ana, ta
tashi ta tafi. Xata yi Magana ya daka mata tsawa y ace, ta yi shiru bay a bukatar
bayananta ta tshi ta tafi kawai.
Madina ta mike cimak ta saka takalminta, t ace, ‘ka yafe min, ka yi min afuwa.”
Ya dago da jajayen idanuwansa ya dubeta y ace, “madina, ba xan yafe miki bat un da
kika raba soyayyata da kaltum. Ba na kaunar duk wanda bay a so na tare da kaltum. Ba
xan ragawa duk wanda ya raba ni da abar kaunata kaltum ba.”
Madina ta girgixa kai t ace, “Allah Yan a tare da mai gaskiya, Shi xai fitar da ni daga cikin
wannan dabaibayi.”
Ta sharce hawaye ta wuce, kamar daga sama ta ji mambela ya kira sunanta. Ta waiwayo
a hankali ta ganshi har yanxu a xaune a inda ta bar shi, ya jya mata baya kansa a
sunkuye a kasa.
Ya ce, “da aka dauki kaltum daga nan ina aka ce xa a kaita!”
Madina t ace, “jirgin kasa suka hau suka tafi khartum babban birni.”
Ya ce, “khartum a ina, wacce unguwa!”
Madina t ace, ban taba xuwa khartum ba, ban san ko’ina ba, dan haka ban tambaya ba.
Saboda bas hi da amfani in sani don an tabbatar min da xarar sun isa khartum ba