Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
xai
wuce kwana biyu xasu yi ba xa su tafi Nigeria, don kudin jirginta da na ‘yan rakiyarta na
hannu an turo musu daga nigeria.”
Mambela ya fada cikin fushi, “bana son bayanan ki, ya ishe ni haka, tafi kawai.”
Xungwi-xungwi ta kama hanyar gida ba tare da sake waiwayowa ba. Mambela yaji
takaici a ransa har ya fin a kullum. Ya ji wani tsananin son kaltum ya kara mamaye
xuciyarsa. Ya ji ya tsani madina, ya ji daman ace xa a wayi gari a ga gawar sa shi ya fi
masa sauki. Ya yi kuka, ya dinga kwalla sunan kaltum shi kadai a bakin teku tamkar
tababbe ga magaruba ta yi, duhu ya bayyana. Ya tuna ranar day a tare kaltum a dai-dai
inda yake xaune, ranar da ta dinga ynakasa da wuka, kuma a ranar ta fara sonsa.
Bai bar wajen ba said a gari yayi duhu sosai. Ya isa gida ransa a bace. Sallah kadai yayi,
ya rufe kansa a daki ya kwanta ba don yana jin barci ba, sai don kawai xuciyarsa ba xata
iya jure surutun mutane. Xuciyarsa ta raunana, ji yake tamkar ta hadu da lahani tamkar
xata buga.
Sarki ya dinga aike a tambayar masa, anya mambela lafiya ya kwanta da wuri! Ta wundo
yake bas u amsa lafiyarsa kalau, barci yake ji.
Talatainin dare daf da asuba sannan barci ya dauke shi, sai ya gan shi tare da kaltum a
mafarki suna hirar so da kauna. Farin cikin sa a mafarki bay a musaltuwa, amma day a
farka ya ganshi shi kadai ba kaltum a xahiri, sai ya ji tamkar ya kurma ihu don takaici.
“me yasa kika tafi kika bar ni kaltum! Me yasa da aka xo daukarki ba ki rugo kin xo kin
fada min mun tafi tare ba!”
Haka mambela yake fada a bayyane a cikin yarensa na adon dawa.
ADON DAWA
.
TRUE LIFE STORY.
.
A dan mana hakuri na rashin jin mu dauke da ci gaban littapin nan, abun ne suka sha
gaban mu amma ba wai haka muka so ba.
Duba da posting din karshe 24 an samu akasi ba'a tashi daga inda aka tsaya ba yasa na
kawo muku shi yanzu...
Sai ata hakuri damu.
BismiLlah
,
sai bayan sallar isha i tafarfado ta tashi zaune daram zuciyarta cike damamaki ganin
yadda jama a suka kewayeta mata da maza ta lura da an burbursuna mata wasu
abubuwa a kofar hancinta saita tuno matsalar bugun aljanun da take dasu abaya sannan
ta gasgata sune suka tashi sai dai tambayar da take yiwa kanta meyatayar mata da
aljanun?
tana tunanin tabbas an fada mata wata magana dazu amma ta manta duban jama'a
take daya bayan daya sai kalmar sannu suke ambato mata can ta tabbatar asibiti take
tashiga tunanin me yakawota asibiti to ina kalah?
Sannan ta tuna ance mata kalah tarasu sai ta fashe da kuka,
jajanta mata ake ana bata hakuri ana jaddada mata addu'a mamaci ke bukata ba kukaba
ta tambaye su ina kalah take?
wata mata ta shaida mata tana matuwari taje ta kira manya domin ta mutu a lokacin da
babu wani dan uwanta ko wanda yasanta a wajen
kaltum ta diro daga kan gado ko takalmi bata saka ba tanufi kofar fita caraf aka damketa
ta fada cikin sanyayyiyar murya yayinda hawaye daya bayan daya ke kwaranyo daga
idanuwanta tace ku sakeni ina cikin haiyacina gida zanje in shaidawa yan gidan mu,
sai suka tabbatar a hankalinta take dan haka sai suka saketa ta tafi tafiya take batare
datasan inda take jefa kafarta ba saboda tashin hankali kuka take wi wi abayyane duk
inda ta gifta sai abata hanya kowa ya ganta yasan ba lafiya ba tana isa gidansu tashiga
tsakar gida sai ta kwarara ihu tazube akasa tana fadin InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un
kalah ta mutu,
da gudu a dimauce suka dinga bulbulowa daga dakunansu suna rafsa salati masu ihu
nataya ta ihu masu hawaye nayi masu tagumi nayi kafin ka ankara gida ya rude da
hayaniya har maza daga kofar gida suna lekowa suna tambayar me ya faru?
da zarar ance kalah ce ta rasu saikaga andau salati sannan su buga tagumi, sabo akewa
kuka ba halin mutum ba kowa yaji mutuwar kalah kasancewar ta dade sosai a Khartoum
tun lami batayi wayoba
malam Abdulkadir shine me gidan su kaltum
suke, kuma limamin masallacinda dake jikin gidan labari yakaimasa cewar kalah ta mutu
mata a cikin gida suna ihu suna burgima suna yarda zani duk da wasu ihun gani idone
kadan ke kukan gaske,
malam da tawagarsa suka dunguma zuwa cikin gida bayan da aka yimusu bayanin
cewar malam zai shigo kowacce ta daura dankwalinta sannan suka nutsu yashigo yace a
tattaro kowa yazo sannan ya musu nasiha da wa azi me ratsa jiki game da irin rayuwar
jahilcin da suke ciki, rayuwar daya na zaluntar danwansa basa taimakon juna yayi kira
dasu kama kansu da mutuncin kasarsu yayi musu
nasiha dasu daina ihu da koke koke idan mutuwa tasamesu don duk wani me rai
mamacine daga karshe yace zaitafi asibiti yasa hannucewar kalah yar uwarsa ce ayi
mata sallah abinne ta gobe da safe,
bayan rasuwar kalah da kwana uku sannan kaltum ta warware ta tsagaita koke koken
da take yi ni tana kwana tanayi idan ta tuna mutuwar lami da kalah saitaji zuciyar ta
bugu buf saboda tashin hankali ita kanta ta rasa shakuwa ko abun alkhairi da suka taba
mata a zamanda tayi dasu a lokacinda suke raye,
kaltum taji mutuwarnan sosai kallo daya zaka mata kaga rama da jajayen idanuwanta
saboda kuka da sanyin safiyyah kamar yanda kaltum da fatsuma suka saba sallace
kawai take sayardasu suna sallamewa zasu zari gwalensu su nufi kasuwar markadi sintar
kayan miya bawani abun kirki kaltum ke tsintaba saboda zuciyarta ta harba can tunanin
masananciyar rayuwa data tsinci kanta a ciki batason Khartoum haka ba dadin zaman
garin takejiba dama-dama ta dan tahadu da fatsuma kawa me kaunasta mai karfafa
mata gwuiwa, badan fatsuma ba da rayuwa kara yiwa kaltum zafi a khartum kasancewar
BABU RAWAN WANI da rayuwar wani babu....
Sai ku hada da part 24 ya xama daya Kenan.
.ADON DAWA 26
.
TRUE LIFE STORY
.
haka mambela yake ta fada abayyane a cikin yarensa na ADON DAWA.
KHARTOUM
lokacinda mambela yake neman dan rakiya zuwa Nigeria wajen kaltum dinsa ya nema ya
rasa badon babu kudin jirgiba ko guzirinda zai rike ba,
ita kuwa kaltum bata bukatar dan rakiyar da zai rakata bur sudan wajen mambela
matsalarta shine kudin jirgin kasa take fafutukar tarawa abu yaci tura, duk abunda take
samu baiwuci ta ci abinci dashiba sauran tasayi omon wanki da sabulun wanka da
sauran su,
idan taci sa a ta tara kudi mai dan yawa tafara tarawa sai wani abu ya bullo mata wanda
dole sai takashe kamar sayan magani idan batada lafiya ko idan takalminta silifas ya
tsinsinke dole ta sayi wani ko idan rigunanta ko lufayanta sun yayyage dole takai dinki.
yau idan akace maka babu mai taimakonka
kodada loman tuwone komai kaiza nema da kanka to babu sauki, kaltum na aiki tukuru
don neman abunda zatasa a yan hanjinta kokuma wanda zata iya shiga jama'a ba a
toshe hanciba saboda wari ko datti bata hutawa saboda haka tarame tayi kurket tayi
duhu rabonta da kitso tun na bur sudan saboda batada lokaci dakuma wanda zaiyi mata
amma ita ta iya kitson har gida gida ake kiranta tanayi ana biyanta.
watan azumi ya kama kaltum bata hutawa yini takeyi tana neman abumda zasuyi buda
baki saboda azumi.
yau babu masu zuwa gyaran jiki don haka jawahir ta sallamesu tace su daina zuwa sai a
satin sallah sannan zasu dawo saboda haka sukafi mayar da hankalinsu wajen tsinta
lemo da abarba sufere wajen rubar sukasa a faranti suje su sayar, kasancewar azumine
ba acika sayan kayan miya ba akan da, anfi sayan kayan marnari .
sak almajirai ga yunwa ga kishiruwar azumi gasu sun yini a Kasuwa.
wataran suyi sa'a su sayar wataran su yini suna yawo ba a saya ba, dagaa lasa an ya
ruba sai afasa saya daman dai masu rangwamen men kudi ne suke sayen irin wannan
masu kudi basa dosar nakan farantin yan talla sai wankanku ajere akan tebur ko acikin
firij.
ranarda rana takwabe musu kuwa babu mai saya idan akasha ruwa sai su zauna su
shanye abunsu babu kudin cefane bare su dafa abincin buda baki da sahur don haka
saisu zarzaya gidanda ake raba sadakar abinci da kwanukansu tun kafin dare yayi
abincin sadakan yakare,
kunu dagurasa ko sinasirne sukebin dogon layi ana raba musu shizasuci kobasu koshiba
su rage na sahur.
kaltum takanyi kuka cikin dare saboda masananciyar rayuwa da take ciki dumin
a bur sudan tawuce irin wannan rayuwarda ta
fatarar abinci. mambela yakara musu jari ita da madina suna sana'arsu kowannensu
abinci ya wadaceshi
sun daina bara asatin da azumi zai kare satin
sallah kenan alokacin watan cinikin jawahir ta
bude ake tururuwan zuwa gyaran jiki da gyaran kai saboda kwalliyar sallah a wannan
satin kaltum suka kaura gidan jawahir har kwana suke yi suna aiki saboda jama'a,
dogon layin babu masaka tsinke sakar gidan saboda mata a lokacin kudi yayi ta shigo
musu baja-baja duk da jawahir ce mai amshewa,
kalilan da ciki take guntsira musu su ta murna.
wasa wasa kuwa suka tara kudi da yawa ana jibi sallah fatsuma ta shawarci kaltum suje
kasuwa su sayi lafaya da takalmi mai kyau suyi kwalliyar sallah kaltum tace ita tara kudi
takeyi akwai abunda zatayi dashi bazatayi kwalliyar sallah ba.
fatsuma tayi tambayarta mezatayi da kudi da har bazata ki sayan sutura da sallah ba
wacce ko almajirai suna wanka su canza kaya ballesuda suke kudi mai dama.
kaltum taki fada kuma taki saya fatsuma ce tashiga kasuwa tayi sayayyarta tsaf harda
sarka da yan kunne
baya ga lafaya da takalmi coge chanjin kuma
taje kasuwa da ake sayar da wayan tafi da gidan ka (g.s.m)tsohowar waya gwabjejiya
wacce aka daina yayinta ta saya aka makala mata sim card yadda zataji dadin waya da
musa saurayinda take matukar kauna shima a kasuwar markadi yake dako su suke
sauke kwandunan kayan miya daga mota zuwa cikin kasuwa.
ranar sallah kowa ya caba ado cas gwanin sha'awa duk wanda yaga fatsuma sai yayi
mamakinta kamar ba fatsumar jiya bace mai
barkakkiyar riga da kanannandaddiyar lafaya
saboda rashin guga kanta duk gunji yau kuwa tayi tsaf bakinta har shekin dangwalin
yaba yake.
zanen fuskarta wato bille da uku ukun bakinta sunyi radau saboda jar hoda da ta
rarrangada ta dambara baki a bakinta da girarta kaikace tabarya ce masayin kwallin,
ta fito kwas kwas kwas daga dakinsu ta leko dakin su kaltum jama'ar gidansu suka ta
mamaki kyawun datayi a yau suna tunanin inda ta sami kudi haka,
fatsuma ta dubi kaltum ta girgiza kai don takaicin kin daukar shawararta datayi datakiyi
da tuni sunyi anko yayinda kaltum ta fito daga wanka tana shiryawa a tsaye akan buhun
kayanta tsofofin riga da siket ta saka burguza burguza sai ta dauko lafayarta koriya itace
mai rangwamen tsufa duk da tawanke tas tayi musu karin guga tana kwana akansu kallo
daya zaka yi musu ka tabbatar sofaffi
ne don haka batayi kyauba surutu da gori babu wanda fatsuma bata yiwa kaltum ba
akan taurin kan da tayi nakin yarda da shawararta.
kaltum bata damu ba shirinta take yi kawai ta linke dukkanin kayanta ta cusa abuhun ta
hada bakin buhun ta daure tace da fatsuma zo muje waje na fada miki wata magana
suka fito kofar gida suka tsaya kaltum ta dubi fuskar fatsuma taga yadda tayi wuri wuri
tanaso taji labari saita tuntsire da dariya tace fatsuma yau zantashi daga garin nan zan
kaura garinmu bur sudan
kaltum ta dafa kafadarta tace ki kwantar da
hankalinki zan dinga kawo miki ziyira akai akai ko kinaso kibini idan naje indawo in
daukeki muje can mu zauna?
fatsuma ta girgiza kai tace bazan iya zama
da wadannan mutanen naku na ADON DAWA ba,
kaltum ta harareta tace ADON DAWA ba mutane bane ko ba musulmai bane?
fatsuma tace ADON DAWA saike nikuwa sai ADON BIRNI sukayi daria dukansu.
kaltum tace don bakisan suwaye ADON DAWA bane kike fadar haka musulman cikin su
sunada kirki, kyauta, sadaka, zakka, sallah, azumi, tausayi, sunada ilimin addini,
masu kudi kuma kyawawa hanci zuwit..
fatsuma tace tunda kina son mambela fa ai dole kifadi haka nikuma bana son ADON
DAWA,
kaltum tace ashe bakya sona tunda ni inason ADON DAWA, a kabila daga hausa sai
ADON DAWA nafi so,
fatsuma tace inasonki tunda ke bahaushiyace amma fa banason ADON DAWA gashi
kuwa sun janyeki zaki koma wajensu duk abunda nafada miki kinki ji sai kintafi din,
suka isa tashar da kafarsu duk da nisa basu damuba sun saba da tafiyar kafa basajin
wahalarta.
suka jira har bayan la'asar jirgi kuwa sai bayan magarib zai tashi kaltum ta umurci
fatsuma tazauna acikin wata rumfa wacce aka tanadar don zaman matafiya gasu nan
reras a zauzaune suna jiran jirgi,
zataje tayi fitsari idan ta gama zataje wajen ma'aikatan jirgi ta tambayesu adadin kudin
tikiti da yadda ake sayansa,
fatsuma ta zauna da buhun kaya a gabanta tana duban kaltum hartayi nisa ta daina
hangota tadade bata dawo ba sannan ta dawo tana zuwa fatsuma ta mike tsaye tace
gida zata tafi saboda tafiyar mai nisa ne, ita kadai kada dare ya mata,
kaltum tayi tayi su sake zama suyi yar hira fatsuma taki tace gara ta tafi tayiwa kaltum
fatan alkhairi da Allah kiyaye hanya tajuya ta tafi.
kaltum tayi kuri ita kadai taci gaba da kallon
masu wucewa kowa da dan uwansa yana hira amma bata damuba, zama kadanne ya
rage mata a shiga jirgi tunda magrib ta kusa farin ciki mara misaltuwane ya bayyana
azuciyarta ya huda ya fito ta fuskarta musamman da jirgi ya iso anfara bin layi don
yankar tikiti kaltum cike da fara'a tabude bakin buhunta don dauko kullin ledar da ta
daure kudinta zataje itama tabi layi ta yanki nata tikitin idan ta tuna jirgi zata shiga
yanzu bur sudan tana wayar gari zata ganta kusa da mambela da Madina sai taji farin
ciki ya lullubeta jitake kamar rufe ido ta bude idanuwanta ta ganta a bur sudan,
ta kasa kwatanto irin farin cikinda su mambela zasu shiga idan sun ganta ta luma hannu
acikin kowane sako lungu da kusurwar buhun kayanta taji har yanzu bata jiyo kullen
ledar kudinta ba nan da nan ta fara zazzakulo tsummokaran ciki da sauri tana zazzagawa
tana ajewa akasa har buhunya zama wayam ba komai amma babu ledar kudin
don haka hankalinta yatashi matuka ta sake bin kowani zani daya bayan daya ko kudin
yamakale ajiki amma shiru kakeji bai fadoba, ta tsake wargaza kayanta akasa kowanne
siket riga zani ko lafaya saida ta shimfideshi akasa sanka-sanka babu ledar kudin ta,
saita rushe da kuka na takaici yayinda jama'a suka tabbatar ba lafiya ba tabbas akwai
matsala aka taru ana tambayarta bayani take cikin gigita da dinbun damuwa wasu sun
yarda ta ita sun kuma tausaya mata wasu kuma bayanenta yamusu kama da tatsuniya
gizo da koki ta mallece kawai domin sun saba ganin irin wadannan mutane wadanda
dazarar talauci ya ishesu sai suzo tashar suna ihu suna neman taimako kudin mota suce
nasu ya fadi idan aka hadamusu taimakon sai su zame su gudu daman ba motar zasu
hauba damfarane kawai,
wake daya yake bata gari inji masu iya magana sun shafawa masu gaskiya kamar yanda
suka shafawa kaltum kowa ya kalleta
saiya watsar yawuce abunsa ma'ana sunsaba ganin irinsu tuntuni,
kuka take haikam bayani take bilhakki rokon taimako take yi da duk karfin ta amma
dakyar ta samu jine goma sha daya ta garzaya bakin wundon mai sayar da tikiti cikin
kuka tayi masa bayani game da fayyace masa abunda take nema agareshi tace tana son
ya
taimaketa yabata tikiti tatafi bursudan wajen yan uwanta batada kowa a Khartoum,
ansace mata kudinta kakaf sai yanzune ma jama'a suka taimakamata da jine goma
shadaya ya
taimaka ya karbi abunda take dashi idan jirgin nan yatafi ya barta batasan yanda
zatayiba...
wani takaici yarufeshi tikitin jine dari biyu dahamsin ne zai bata a jine goma shadaya?
kallon tara saura kwata ya mata don haka basai yamata magana ba tasan abunda
ke ransa cikin fargaba ta sharce hawayenta ta sake neman wata alfarma cewar to ya
bata rancen tikiti suna isa bur sudan yasawani ya bita gidansu ya karbi kudinsa..
cikin wata dankararriyar murya ya fada cike da takaici ke matsami daga jikin wundo
kada ki sake dawowa, kika sake lekowa kika min zancen banza sai nasa yan sandan can
sun kamaki, kaji mahaukaciya tikitin gwamnatin ne zan baki bashi ?
Sum sum sum kaltum tayi tabar jikin wundonsa batare da ta sake cewa komaiba daman
itama tsausayine yasa ta tambayeshi don daga ganin bakar fuskar nan tasa baki kirin da
jajayen idanuwansa tasan bazaiyi mutumci ba ga wani tulelen ciki da kiba da kyar yake
juyi kuma tun nan kasa tsinke ka huda yace tush haka yake kamar katuwar balobolonda
aka cika da iska saita daina
kuka ta sharce hawayenta da yayi mata face face a fuska batada sauran dabaru ko
tunani bata da sauran wani tunani kuma ta cire burinta data kudira saitaje kayanta da ta
watsar akasa tana kadewa tana linkewa tana zurawa a buhu jikin ta kalau data gama
lenkewa saita koma gefe jikin wani dakali ta jingina da buhunta a gefe tana duban jama
ar da Allah ya musu rahma wadanda ya yalwatasu da kudin sayan tikiti sai yanka suke
suna shiga jirgi,
dukan uku uku kirjinta takeyi tamkar zata fas
ADON DAWA 27
.
TRUE LIFE STORY
.
ta fito waje yayinda takejin wani jiri na takaici na neman yakayarda ita kasa,
kuka yaki zuwa saboda abun yafi karfin kuka, don idan tashin hankali ya afku akayi kuka
to akwai sauran rangwamen masipa, amma idan masifa yayi masifa to kukama takansa
yake abun yafi karfinsa,
nasihar Madina ta tuna wacce a koda yaushe take shawarta ta yawaita addu'a tana
neman tsari daga masifun rayuwa, wanda ko Allah Ya aiko da masifa zata zo da sauki
kuma da maganinta ta shawarceta data yawaita karanta InnaLillahi wa ina ilaihi raju un
ako yaushe musamman sanda wani abu naki yafaru,
nan da nan kaltum ta cafko kalma InnaLillahi
wa inna ilaiyi raju un a harshenta tana fada
tanasake maimaitawa saita farajin wanan kululun nan daya shaketa awuya yafara
lafawa, bugun da zuciyarta ke famanyi ta sausauta tanaji tana gani jirgi ya cika ya tashi
yatafi ya barta, yayinda kuka ya kwace mata tana yi ta nanata kalmar InnaLillahi wa inna
ilaihi raju'un ta dade a zaune anan har karfe
sha daya na dare.
saida wani dan sanda ya zagayo ya sake zagayowa ya tabbatar ba tada niyyar tashi
daga wajen nan sannan ya tsaya ya tambayeta lafiya take zaune haryanzu cikin kuka?
tamasa bayani yace to ai gara ta tashi ta koma inda tafito saboda zamanta anan bai
dace ba, ga dare ya fara nausawa gara takoma ta tara wani kudin zaifi mata sauki saita
dawo ta yanka tikitin ta tafi baki alaikum don ba wanda zai dunkule wannan makudai
kudin ya bata, don kowa takansa yake yi,
kaltum ta mike ta daura buhunta aka tana zubar da hawaye tafiya take amma dakyar
take jefa kafarta ta isa gida zuciyarta tamkar tafashe taci sa'a duk yawancin ankwanta
saboda gajiyar sallah , ta sadada tashiga dakinsu ta ajiye kayanta a lungu tayi sallah ta
kudundune alungu yayinda duk sanda ta rintse ido saita tayhango Madina da mambela
sai ta fashe da kuka.
washegari da safe kaltum taci karo da yan gidan a lokacin da ta fito daga