Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
jegon sannan ta bude gida mahaifina ya shigo ya iskemu tsaf.
Haka danginsu su kayi tayi mata sannu da kokari yadda ta karbi haihuwar sofi
tamkar ‘yar cikinta don sun iske mai jego sumul da jaririyarta kalau.
Bayan an yi suna aka saka min Ummu Kaltum sunana da goggo fattu ta xabar
musu kenan wai sunan mahaifiyarta ne, basu isa su saka sunan mahaifansu bad a
suka rasu tuntini. Sai dangin sofi suka xo suka dage xasu tafi da ita da kyar goggo
fattu ta bari suka tafi da ita, mahaifina ya fi son haka daman. Bata dawo ba said a
nayi wata uku nayi kwari sannan muka dawo xangon daura tun daga lokacin na
fara shiga halin da nake har yanxu yak e bibiyata a rayuwata.”
Tab ashe haka wasu suke da busashshen imani!!!
Allah Ka sanya mu pi karpin xukatan mu, sannan Ka dada kare mu daga sharrin
miyagu.
Se a saurara nan gaba domin jin yadda ta
ADON DAWA 7
.
.
“kamar yaya halinda kike ciki har yanxu yake bibiyarki!”madina ta tambaya cikin
rudani kaltum ta xubo da hawayenn daya cika mata ido tace “goggo fattu ta hana
mahaifina ya dauke ni balle yayi min wasa ko ya rungume ni mu shaku. Ko kallona
yayi sai ta dauki dogon salati kai kace mutum ya kashe. Ta ce wannan ai rashin
kunya ne don haka kwata kwata baya kusanta ta. Haka mahaifiyata bayan nono da
xata bani babu sauran soyayyar uwa da ‘yarta, idan kuwa ta cika daukana da
tattalina sai xagi da Allah wadai take yi mata kala kala. Komai aka yi da ni, sai
goggo fattu tace rashin kunya ne.
Wata rana har kuka goggo fattu ta ke saka musu, ta ce dan bata da haihuwa,a
haka iyayena suka kyaleni, sai yanda goggo fattu ta yi da ni.kar ki dauka kulawar
take bani, sai ta ajiye ni a dakinta in ta kuka, sai taga dama sannan tace sofi ta
dauke nita bani nono. Har aka yaye ni na bar dakin mahaifana xuwa dakin goggo
fattu, ba komai kuma take min ba sai duka da rankwashi musamman idan nayi
fitsarin kwance, aka ce komai sanyin asuba xata kore ni waje tsirara bayan ta xane
ni.
A lokacin karayar arxikii ta far wa baba na bashi da cin yau bare na gobe sai ya
nemi shawara xai sayar da kiwonsa da mahaifinsa ya bar masa gado, akuyoyi da
yawa da gonaki xai yi jari, sai ta ki amincewa t ace bakin ciki yake yi don ta xuba
nata kiwon a cikin nasa shine yake so ya tona mata asiri a garin ace daman duk
tulin akuyoyin nan ba nata ba ne don tayi karya t ace duk nata ne. muka dade
cikin rashi da fatara da yunwa har Allah Yasa kawu Isiya kanin mahaifin babana ne
yayi masa hanya ya samu aikin gadi a kano,ya tafi kano amma ya bar iyalansa a
xangon daura.”
Madina ta gyara xama ta gyada kai ta ce “lallai yanxu xa’a fara labari. Daga nan
yaya aka yi? ”
Kaltun ta girgixa kai ta ci gaba da Magana cikin marainiya murya ta ce “duk
karshen wata yake xuwa ya kawo mana kudi albashinsa don mu ci abinci amma
yana tafiya xata juya akalar kudin tayi sha’anin gabanta dasu .kuli –kuli guda uku
shine bincin mu na rana, tuwon dawa da miyar kuka lami ko wace babu shine
abincin dare, dumamensa sine abincinmu na safe.Duk muka rame muka lalace ita
kuwa har tsire da kaxa take ci acikin shinkafa muna kallonta.
Da mahaifina yaga alamar mun rame sai ya dinga tambayar mahaifiyata ko lafiya
muke rame wa?
Ta boye masa don itama irin halinta kenan ba xa ta yi Magana ba ko abu xai kashe
ta, sai a makwabta aka fada masa duk abunda yake faruwa damu. Ya samu goggo
fattu yace yana so ya tafi kano da sofi itama ta samu aikin wanke-wanke da shara
duk wata xasu dinga hado mata albashinsu duka suna kawo mana ni da ita. Tuni ta
amince sofi tabi mijinta suka tafi kano suka barni cikin wahala Kaman ta kashe ni
tsunma ma ya fi ni nauyi, ga ciwuka kala-kala kullum.
Mahaifina bai fasa xuwa ba, duk wata xai shiga mota ya xo xango daura ya kawo
kudin albashinsa fiye da rabi. Ina ganinsa sai in hau murna ina kiran “ga baba, ga
baba.” Amma sai ya ture ni gefe in fadi kasa, ya dauke kansa baya kallon in da
nake saboda kada goggo fattu t ace yayi rashen kunya.
Ina shekara uku yunwa da ciwon kyanda suka sa ni a gaba na rame sai kashi da
fata, ido yayi min xuru –xuru kamar mai ciwon kanjamau sai ka kirga kashushuwan
dake kirjina. Sai in suma sau biyar a rana wanar ba xan rayu ba sai ta ji tsoro kar in
mutu a hannunta don haka sai ta nemi kawu isiya ya kawo mu har gidan da
mahaifina yake gadi, suka ci sa’a kuwa a boy’s kuarter gidan suke xaune da
mahaifiyata.
Ta hau fada hard a kumfar baki tana cewa sun gudo kano sun xo sun kwanta sun
bar ta da wahala tana fama da ‘yarsu ko barchi bata yi, don haka ga ‘yar sunan su
rike kayansu. Ta jankwabar dani da kayana ta juya ta tafiyarta, suna binta suna
rokonta ta xo ta huta ta ci abinci, tace ba xata dawo ba dole ta tilastawa kawu
isiya dole ya taso suka hau mota suka koma xangon daura.”
Madina ta girgixa kai t ace “daman haka halin goggo fattu yake! Ni fa na yi
mamakin ace kaka ce take tsangwamar jikarta haka yadda naga tana kyararki a
mota.”
Kaltum ta surnano da hawaye ta cika mata ido ta ci gaba da cewa “mai gidan da
muke gidansa sunanasa Alh Adnan Mahbub, shi da matarsa Salaha sai ‘dan su
daya Mashkur. Mashkur sa’ana ne shima a lokacin shekarunsa uku kamar yadda
shekaruna uku cur a duniya. Alh Adnan yana da arxiki mai yawa duk da matashi ne
a lokacin, aurensa ne na fari kuma haihuwarsa c eta fari bai wuce shekaru talatin
ba aduniya, matarsa kuwa baxata wuce shekaru ashirin da uku ba don da haka
kusan sun girmi iyayena ma. Suna xaune a kataferen gidan, kerarre mai girman
gaske yayin da mu kuma muke xaune a boys quarters in gidan.
Alh Adanan na ganin halinda nake ciki na rashin lafiya sai ya ji hankalinsa ya tashi
ya umurci direban saya dauke mu ya kai mu asibiti ni da mahaifana. Ya ce ayi duk
abinda ya kamata ayi xai biya ko nawa ne. asibitin nasarawa aka kai ni a lokacin
shine asibitin da yake tashe sai dan wane da wane. Likita na ganin yanayin jikina
sai ya bamu gado muka kwanta aka dinga kara min ruwa da allurai. Allah cikin ikon
Sa kafin sati guda na murmure, shi yasa aka ce kowace cuta da maganinta. Na
samu sauki har na fara tashi xaune ina surutu kuma komai aka bani ina ci. Kusan
kullum Alh Adnan da matarsa salaha suna xuwa su gaishe ni a asibitin bayan
kayan dadi na marmari da abinci iri-iri da suke yini suna aiko direba yana kawo
mana asibiti.”
Madina tace “gaskiya wadannan iyayen gidan naku suna da kiriki.”
Kaltum tayi murmushi tace “suna da matukar kirki shi da matarsa dukka. Bayan an
sallamo mu mun dawo gida sai muka ci gaba da rayuwarmu a gidan, ina matukar
jin dadin gidan saboda na samu walwala ba’a dukana, babu yunwa, ba babu
hantara.
Makaranta mai tsadar gaske aka sani.
Madina tace “Allah kenan, haka yake ikonSa.”
Kaltum tayi murmushi tace “na tsinci kaina mai farin ciki matuka sai dai matsala
daya data addabe ni itace bana samun kulawar iyayena. Ba kulawar rashin wanka
da wanki ba ne, kuma ba matsalar abinci ba ne, basa hira da ni, haka basa
saurarona, ko na matso kusa dasu saisu matsa saboda wancen ra’ayin da goggo
fattu ta cusa musu.”
Madina tace “ban fahimci basa sauraronki ba, kamar yaya? ”
Kaltum t ace “kunyata su ke ji saboda ni ‘yar farice don haka na xama tamkar
mujiya a tsakiyarsu sai kallo da ido. Ina matsowa kusa dasu saisu ture ni ko su
tashi daga wajen, idan na taho musu da hira saisu gwale ni ba xasu saurareni ba.
Idan xan yini ina kuka babu wanda xai lallashe ni a cikin su. Har ‘yan gidan suka
fara fuskantar hakan, Alh Adnan ya dinga yiwa mahaifana nasiha yana nuna masa
wannan kunyar da yake yiwa ‘yar fari ba’abun burgewa ba ne illa jahilci da cutar
kai.
Akwai wata ranar asabar ba xan taba mantawa ba da sassafe misalin karfe takwas,
a lokacin ana tsananin sanyi. Ni da mushkur muka fito bakin get wajen da babana
yake xaune yana jin dumi da itace, yayin daya rufa da burgujejen bargo. Yana
ganinmu ya tabbatar sulalowa mukayi muka fito ba tare da sanin iyayenmu mata
ba, saboda ko rigar sanyi babu a jikinmu, ba hula, ba takalmi daga ni sai yar
yaloluwar singileti da pant, haka mushkur daga shi sai karamar jallabiya ba dogon
wando. Ana tsananin hunturu, mai tafe da haxo, da iska mai kura don haka hanci
da ido sai xuba suke yi, yayin da duk ilahirin tsikar jikinmu ta tattashi.
Babana na ganinmu sai ya kira mushkur ya dauke shi akan cinyar sa ya rungume,
ya lullube shi da bargo, yayin daya juyar dashi saitin garwashi suka yi ta jin dumi,
suka juya min baya. Ina xaune akan benci a bayansu ina ta makerketa ban isa in
kutsa cikin bargon ba saboda nasan hantara ta xai yi ya kore ni.
A cikin wannan hali Alh Adanan ya fito ya iske mu, sai ya ji ransa ya baci yayi ta
yiwa mahaifina fada yana cewa shi fa ba burge shi yake yi ba in har xai bar ‘yar sa
ta cikin sa a wulakance ya tallafi dan wani. In har iyayena basu shaku da ni ba to
ina xansa raina, ya kwatanta wannan abunda suke yi da suna ADON DAWA wato
gida bai wadata ba an wadata waje ma’ana ya wulakanta ‘yarsa ya tallafi bare.
Alh Adnan ya dauke ni ya rungume ni ya shiga da ni cikin falonsa ya dauki
bargonsa ya lullube ni yayin daya kunna min room heater jin dumi ta lantarki. Yana
lallashi na, ya bani biskit da alewa, har said a ya tabbatar hantsi yayi, sanyin safiya
ya lafa sannan y ace in je gida ayi min wanka a saka min kayan sanyi. Haka shima
mushkur yake samun wannan gata daga wajen mahaifana har goyon sa mama na
keyi amma ni ban isa matsowa kusa da ita ba.
Dan haka na kasance ako da yaushe ina hanyar bangaren daddyn mushkur. Ina
tashi daga barci wani lokacin ko karyawa bana yi sai in yi wuf nagudu wajensa, sai
dai idan ban ci sa’a ba nayi karo da maman mushkur sai ta kora ni gida, idan kuwa
tana kicin ko ban daki tuni na isa gare shi a falonsa ko akan gadonsa, yana gani na
sai ya rungume ni ko daga ni sama cimak, ya wujijjiga ni in yi ta dariya.
Musamman saboda ni yake ajiye katan katan din alewa da biskit da kananan
kwalayen lemuna. Ko da yaushe ka ganni ina ciye ciye, baya ga karatun boko dana
arabiya da yake koya min. ya na sona saboda ina son karatu, kuma ina son in
koya.
Ko da yaushe ina tambayarsa abun da ban gane ba haka duk abun daya koya min
duk daren dadewa ya tambaye ni sai na fada masa bana mantawa, in da ya kara
sona kenan.
Sabanin dansa wanda ya tsani karatu don haka ma basa shiri da uban. Gashi ina
da tsananin wayo kamar ba ‘yar fari ba, ga ladabi da biyayya, na iya hira tatsuniya
kala-kala da labarum nake bashi yayi ta dariya ya na tuntsurewa da dariya tamkar
yana hira a cikin abokansa.
Amma fa bana labarin da kowa saishi kadai, idan baya nan sai ka rantse ni doluwa
ce don bana Magana, sai kallo da ido a gidanmu saboda bana hira da iyayena. Don
haka duk sanda daddy yayi tafiya kwana biyu sai kowa ya gane bana jin dadin
rayuwata. Jikina sai yayi sanyi, in kaura bakin get ina duban hanya musamman
idan na ji karar mota sai in xankada da gudu in leka, idan naga bashi ba ne sai
raina ya baci ko kuma in fashe da kuka. Idan kuwa na ci sa’a shi din ne sai in yi ta
tsalle da ihu don murna yayin da nake fara xaxxago masa labaru iri-iri dana tattara
ina jira ya xo in fada masa.”
Kaltum tayi shiru tana matse hawaye, yayin da madina ta tsura mata ido tana yi
mata kallon tausayi.
Madina ta nisa tace “ikon Allah idan da ranka babu abunda baxa ka jiba. yaya kuka
kasance? ”
Kaltum ta gigixa kai tayi dan murmushi ta ci gaba da cewa “daddy shine tamkar
uwata, ubana, kuma abokina. Shi kadai yake goge min hawaye a idona saboda a
kasance koda yaushe ina cikin kuka a sanadiyar kyarar da mahaifana da kuma
mamar mushkur ke yi min, tatsane ni saboda taga mijinta yana tarairayarta fiye da
dansu na cikinsu.”
Madina ta girgixa kanta t ace “Allah sarki duniya, abun al’ajabi baya karewa ban
tabajin irin wannan kauyenci ba. Daga kanki ba’a kara haihuwa ba a gidan ku?
Mushkur ma ba’a hqifa masa kanne ba? ”
Kaltum tace “an haifawa mushkur kanne biyu amma dukkansu ba’a haifesu da rai
ba, saura kiris mamarsa ta rasa ranta a garin haihuwarsu. Saboda duk a juye ake
fitar mata dasu ta hanyar tiyata ma’ana kan jaririn ne suke komawa kirjinta,
kafafuwan a kasa sai anyi tiyata ake fitar mata kuma a mace don haka nema aka
juyar da mahaifarta baxata sake haihuwa ba. Ni kuwa mahaifiyata ta haifi namiji
mai bina ya rasu bayan an yi suna, sai ta dade bata haihu ba sai daga baya ne
haihuwar ta bude, kusan duk shekara sai ta haihu, a yanxu haka kannena bakwai
na baro mata da maxa.”
Madina t ace “suma kannen naki suna jin kunyarsu basa kula su kamar yadda suke
yi miki!” kaltum ta girgixa kai tace “iyayena suna son su, suna wasa dasu, suna
hira dasu ba kamar yadda suke yi min ba har tsayawa nake ina kallonsu ina
mamakin ashe mama da baba sun iya yiwa da wasa da lallashi.
Duk wani abu da ake bukata na makaranta sai na jira daddy ya xo sannan in fada
masa, ya bani in kai makaranta idan kuwa baya gari ko baya kasar sai dai idan
kashe ni xa’a yi a makaranta don duka amma babu wanda nake iya tara in fadawa
sai daddy.
Ina shekara takwas nagama nursery har na shiga primary, ina primary 3 a lokacin
ne karshen karatuna ya xo.”
“kamar yaya karshen karatunki ya xo? ”
madina ta tambaya cike da damuwa.
Kaltum t ace “eh, a lokacin ne goggo fattu ta aiko tana son ganin mahaifina, yana
rawar jiki ya tafi kiranta a can garin mu xangon daura. Ta sanar masa abun da take
bukata daga gare shi, gashi baya iya yi mata musu. Nan danan ya amsa mata ba
tare da yayi kokonto ba saboda tsoro.”
Madina ta gyara xama t ace “me take bukata a gare shi!”
Kaltum ta cije baki tayi murmushin karfin hali t ace “ce masa tayi ya amince ta
sayar da gadonsa da mahaifinsa ya bar masa sannan da tabkekiyar gonarsa dake
garin sandamu, wacce mahaifiyarsa ta mutu ta bar masa, sannan da dinbin
awakinsa xata biya kudin jirgi ni da ita mu tafi makka neman kudi. Idan muka je xa
mu samo dukiya mai yawa , sai ta biya shi linkin ba linkin in kudin gonarsa.”
Madina tace “ya yarda a cire ki daga makaranta ku tafi maka? ”
kaltum t ace “a take ya yarda, haka mahaifiyata ma bata hana ba a sanda ya
sanar mata. Ko da wasa babu wanda ya fada min shirye-shiryensu, ni dai nasan
ankai ni gidan daukar hoto an yi min kananan hotuna, goggo fattu ta xo ta kwana
biyu a gidan mu, sai kuma ranar da naga mahaifiyata ta xuba min kayana a dan
buhu, goggo fattu tace in taho mu tafi.”
Madina tace “daddy ya sani bai hana a tafi da ke ba? ”
Kaltum ta girgixa kai tace ‘sai da suka ga daddy baya na sannan suka tarki tafiyar,
koda wasu basu shawarce shi ba, matarsa ma bata sani ba.
Na tsinci kai na a cikin jirgi, sannan na tsinci kai na a cikin birnin makka.
Madina t ace ‘ki ce kin taba xuwa makka ba wannan ne xuwanki na farko ba? ”
Kaltum t ace”na dade a makka a can na koyi larabci, yanxu haka lungu-lungu da
sako-sako na sani a cikin garin makka, haka da ace na samu xuwa xaki yi mamakin
irin mutanen da xa ki ga sun sanni duk da na girma nasan xasu shaida ni saboda
kammanina basu canxa ba.”
Madina tace”yaya xamanku da goggo fattu ya kasance a maka?
Amma dai bata wahalar dake ba tunda kin girma ba kamar sanda ta yeye ki ba, ga
ku kuma a kasa mai tsarki, gashi komai a wadace ba’a wahalar abinci”
Kaltum tayi jugum can ta nisa t ace “uhum wahala ma daya kenan, ai ba xai yiwu
in iya xayyana ta gaba daya ba saboda axabar tayi yawa.
Wahalar da na saha ina ‘yar jaririya ai karama ce saboda tsana bansan komai ba, a
wannan lokacin kuwa nasan “eh” nasan a’a, na san ace in yi abu in yi, ace in bari
in bari.
Da farko dai mun ci sa’a mun sami gidan haya a unguwar ‘yan kasa wato a
unguwar masfala, a gidan wata balarabiya mai suna hajiya isra, hajja isra ruwa
biyu ce mahaifiyarta baka, mahaifinta balaraben makka ne dan haka gadimiya ce.
Hajja isra tana da ‘ya daya mai suna ahlan. Ahlan sa’ata ce, mahaifin ahlan ya rasu
ya bar musu gida sama da kasa. Suna xaune a sama, mu kuma muna haya a kasa
mu kadai ne.
Hajja isra tana da kirki matuka,tana sona sosai musamman yadda taga mun shaku
da ‘yarta Ahlan, har ana cewa muna kama kasancewar Ahlan tayi kama da
mahaifiyarta ba suyi kama da larabawa ba sak nima kuma gani fara sol mai gashi
sai nake kama dasu. Ta kan yiwa goggo fattu wasa t ace “yadda fuskar nan taki
take baka kirin idan askarawa (yan sanda) suka ganki da kaltum ki ka ce jikarki ce
sai sun kama ki, suce karya ki ke ‘yar larabawa kika sato. Saboda baku yi kama ba
kwata-kwata, gara ki dinga saka nikaf da safar hannu da ta kafa idan xaku fita
tare.
In da xaki tabbatar hajja isra na sona sai ta siyawa ‘yarta ruguna ko sarka da
‘yankunne na gwal, biyu take saya iri daya ni da Ahlan musamman a lokacin
sallah. Haka abinci, komai ta dafa sai ta aiko min sai dai kash aiken baya xuwa
gare ni saboda goggo fattu karbewa take yi bata bani. Da takardar Ahlan ta ‘yan
kasa hajja isra ta saka ni a makarantarsu Ahlan, muke xuwa tare duk da ba’a koyar
da boko larabci xalla ake yi sai karatun qur’ani ta tahfix ce. Na koyi larabci, na koyi
karatun qur’ani sosai, nasan baki, hadisai da daman na haddace su kuma xan iya
fassarawa, haka fikihu, tafsir, sira da sauransu. Muna xuwa makaranta da sassafe
misalign karfe takwas xuwa karfe goma sha