Advertisements
Chapter 23 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 46

66K to 69K   out of 137K words

kowa ya fara taya kaltum murna wasu kuwa suka fara koke koke dama ace
suma nasu ‘yan uwan su kawo musu irin wannan agaji wajen aiko musu da kudin tafiya.
Wasu kuma suka fara kukan rabuwa da kaltum saboda yarinya ce mai dadin xama.
Kaltum ta ja gefe ta cije takiyin gaba ta ki yin baya ta tsaya kawai tana karkarwar jiki
yayin da ta rushe da kuka wanda saida hankalin kowa ya tashi.
Madina ma kukan take yi, ta mike da sauri ta shiga hadawa kaltum kayanta a buhunta
kama daga kayanta na sakawa xuwa takalma, soson wanka, sabulu da sauransu. Ta xo
ta ja hannun kaltum, sai kaltum ta makale hannu alamar ba xata tafi ba. Cikin fushi da
kuka mai tsanani madina tadaka mata tsawa ta ce “ki xo ki wuce ku tafi kafin raina
yabaci. Wa kika ajiye, ko wa kike dashi anan da xa kice baxa ki tafi ba?
Ban da larura ma me xai kawo ki cikin wannan rayuwar ta kangi da wulakanci a
matsayinki na ‘yar boko?
Da tuni yanxu kina jami’a don haka dole ki tafi, fatana ki koma gaban iyayenki ni kuma
in ji da kaina.”
Kaltum ta mika hannu ta karbi Jakarta ta wuce gaba yayin da sauran suka biyo bayanta,
tafiya suke jiki sanyi kalau ana tayi mata fatan Allah kiye hanya. Mata da maxa a kofar
gida suka fito suka tsaya crko carko ana kallon kaltum sai hawayen da yaketa firfitowa
daga idanuwa da yawa daga cikinsu. Iya mairo da jikarta rakiya suka bata sako ta
shaidawa ‘yan uwansu na xangon daura cewar suma su hado kudi su aiko musu su koma
gida.
Hauwa’u ta dubi kaltum ta yi murmushi tace “banda yarinta keda xa’a kai ki gida cikin
gata ina ke ina koke koke kuma?
Mu yi sauri mu tafi kada mu rasa jirgi, da magaruba yake tashi.
Kaltum ta kasa waiwayowa ta dubi jerin mutanen da suke daga mata hannu sai dai ta
dora buhun kayanta aka tayi gaba. Madina da hauwa’u ne suke biye da ita a baya suka
nufi khartum bahari anan ne xasu hau jirgin kasa.
Suna isa suka iske layin yakar tikiti saura mutane kadan saboda jirgin ya kusa cika. Nan
da nan hauwa’u ta shiga layi ta yanko tikiti biyu ita daya, kaltum daya.
Madina ta rushe da kuka yayin da kuka ya ci karfin kaltum itama sai ta ajiye jakar
kayanta a kasa ta rungume madina tana kuka. Ta ce anty, bana so in tafi ni kadai in
barki a nan. Ki xo mu tafi tare xan fadawa iyayena su aiko da kudin jirginki ko mu shiga
mota mu tafi kudin xai ishe mu.”
Madina ta girgixa kai ta sharce hawaye cikin kuka mai tsanani ta ke Magana t ace “ba
xan je Nigeria ba kaltum, ba ni da kowa a Nigeria saboda kowa ya guje ni in yi rayuwata
anan har lokacin da mutuwata xata xo ta dauke ni ki yi min fatan alkahiri kamar yadda
nake yi miki ko bakya tare da ni, ki yafe min duk abunda nayi miki a rayuwa kamar
yadda na yafe miki. Ina addu’a Allah Ya hadamu a gidan aljanna bayan mutuwarmu
domin xai yi wuya mu sake haduwa har karshen rayuwarmu. Daga karshe ina yi miki
nasiha da ki rike addininki, ki tsare kanki daga aikata xina har Allah Ya kawo miki mijin
da xa ki aura na gari, kada ki manta da labarina da na baki ki koyi hakurin xaman aure
da tattalin miji baya da ladabi da biyayya.
Ki yi min alkawari xa ki sakawa ‘yar ki sunana madina don karki manta da ni a rayuwa.”
Kuka mai tsanani ya ruftowa kaltum sai ta yi sauri ta duka ta dauki jakar kayanta suka
nufi kofar shiga jirji saboda axalxalar da hauwa’u take yi mata wai suyi sauri su shiga
jirgi su tafi kada a tafi a bar su.
Madina na tsaye tana kallon su yayin da kuka ya ci karfinta sai ta kwalla kiran sunan
kaltum. Kaltum ta waiwayo da sauri sai ta tsaya cak su duka kuka suke yi. Madina tayi
dan murmushi karfin hali.
Ta ce “kaltum, me xan cewa mambela? ”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai!”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai can tayi ajiyar xuciya yayin da
hawaye xaxxafan hawaye ya xubo sharrrr daga idanuwanta, ta girgixa kai t ace “k ice
masa na tafi gida.”
Sannan ta juya ta juya ta shiga jirgi, suka sami waje suka xauna, sun xauna ba dadewa
sai aka rufe kofar jirgin aka kunna aka fara tafiya yayin da kuka marar kakkautawa ya
ruftowa kaltum da madina. Sai da madina ta tabbatar jirgi ya tafi gida lokacin dare yayi.
‘yan gidan sun dade basu kwanta barci ba suna ta jajen rashin kaltum yayin da madina
ta bude shafin kuka kai kace mutuwa kaltum din tayi. Taji hankalinta ya tashi ko sanda
ta rabu da ‘ya’yanta bata ji irin wannan ciwon rabuwar ba kamar yadda take jin radadin
xafin rabuwa da kaltum a yau. Tunda ta koma gida kalma daya ta kasa furtawa dan
takaici sai aka kewaye ta ana bata baki da nasiha kala kala.
Sai washe gari su kaltum suka isa khartum da sassafe amma kaltum bata daina kuka ba.
Kaltum taga kayatattun birane masu titi da gine ginen dogayen benaye. Ta shiga
mamakin kyawun sudan ashesu a kauye suke ba a sudan ba, don inda suke babu ruwa,
babu wuta, birni kuwa ga lantarki nan tarr, ga ruwa afanfuna bayan motoci tsala tsala da
mata masu kyau a tituna suna wurwucew kamar su suka yi kansu. Duk da irin wannan
kyakkawan gari da kaltum ta gani bai sata daina jin dankararriyar kunar da take ji a
ranta ba. Tana tunanin madina da mambela, sai taji tafi son ta xauna dasu da ta koma
gidansu. Ko sanda ta baro gida bata ji irin wannan kunar ran ba kamr yadda take ji a
halin yanxu.
Sun isa wani gida kato a wata unguwa mai kyau, babban gida ne a lailaye da sumunti
mai dauke da dakuna bijik da katon tsakar gida . hausa ne xalla a gidan kuma mata
xalla, suna xaune a dakuna kasha kasha kowace da sana’arta wacce xata kula da kanta.
A kalla a daki daya akwai mutane takwas xuwa goma da tabarmi a shinshinfide a kowace
daki. Gida ne mai kyau na sumunti xalla sabanin irin nasu na bur sudan.
Tabbas kaltum taga fuskoki da yawa da ta sani sai dai ta manta a inda ta san su, suna
shiga cikin gidan kafin su isa cikin dakin sai ta tambayi hauwa’u.\
Ta ce “nan gidan haya ne? ”
Hauwa’u t ace “gidan Abdul kadir, dan asalin xangon daura ne ya kauro sudan da xama
fiye da shekara talatin anan yake, ya xama dan kasa. Shine yayi arxiki yamaka gidan
nan ya barwa baki nan bangarensa dana iyalinsa kuma suna can baya. Kyauta kowa
yake xama musamman ‘yan xangon daura sun fi xama a nan kowacce ta xo nan garin
sai ta nemi nan gidan ta xauna, har ana kiran gidan da suna gidan xango.”
Sai da suka dade suna jira sannan kalah ta dawo gida, ta tare su da murna gami da yiwa
hauwa’u godiya marar adadi data nemo mata kaltum. Babu tantama duk wanda ya dubi
hoton kaltum yaga fusakarta kuma axahiri ya san itace, ga kamanninta nan rangadadai.
Hauwa’u ta danka kaltum a hannun kalah su kayi sallama ta koma garin da take don ita
ba a khartum take xaune ba.
Kaltum ta sake dukawa ta gaisheda da kalah sannan ta gaisheda ‘yarta budurwa sa’ar
kaltum din ce mai suna lami. Suka amsa mata cikin sakin fuska sannan kalah ta fara yi
mata bayani cewar itama ‘yar xangon daura ce babarta kawar goggo fattu ce.
Kalah ta ci gaba da shaidawa kaltum t ace “an kamo goggo fattu daga makka yanxu
haka tana xaune a xangon daura saida aka kamo ta ne kwanan nan sannan iyayenki
suka san bkya tare da ita a makka, dan haka hankalinsu yayi tsananin tashi suka dinga
tunanin yadda xa’ayi a samo ki. Sai Allah Ya sa musa agent din da yayi muku aikin bisa
yana da lambata shi suka nemo suka tambayi yadda xa’ayi a same ki. Sai yace bashi da
yadda xai yi ya samu wani a bur sudan saboda babu waya kwata kwata a kauyen amma
yana da lambata sai dai ni a khartum nake, don haka suka kira ni a waya. Na ce musu
gaskiya bana xuwa bur sudan amma idan sun tabbata kina bur sudan to su aiko min da
kudin motarki da nawa na xuwa can sannan su aiko da kudin motarki sai in saka ki a
mota har kano.
Akwai wani Alh Adnan dashi muke waya shine yace gara a sako ki a jirgi, to dai yanxu
sun aiko da hotonki da kudin jirgin kasa na xuwa bur sudan, da ban sami lokaci ba, shine
kawata hauwa’u t ace daman tana so ta je ta je ta nemo ‘yar uwarta shine na bata kudin
ta je ta taho dake don haka sai ki xauna ki saurari sanda xasu turo da kudin mota ko
jirgin xuwa kano sai in je har tasha in turaki.”
Kaltum tayi shiru a lungu tana sauraron abinda kalah take fadi mata, jikinta yayi sanyi
kalau ta saddakar ta fawwalawa Allah komai tana fatan Allah Ya xaba mata abinda yafi
alkhairi ba abunda ranta ya fi so ba.
Al’amarin mambela kuwa sai washe gari ya samilabarin an tafi da kaltum Nigeria, har
cikin dakinsa wani abokinsa ya je ya kwatsa masa wannan mummunanlabarin. Duk da
tsananin xaxxabin da ciwon kan da yake yi saida ya taso da kyar ya taho gidansu
kaltum, kai tsaye ya fada tsakar cikin gidan ya kuwa ci sa’a ya iske madina a xaune tayi
gum tayi tagumi itama da alama takaicin rashin kaltum ya dame ta. Yana ganinta sai ya
fara hawaye itama ta fara xubar da wani xaxxafan hawaye mai radadi.
Ya fada cike da fargaba yace “da gaske an tafi da kaltum Nigeria? ”
Madina ta gyada kai tace “haka ne, kaltum ta tafi Nigeria, iyayenta ne suka aiko a tafi da
ita…”
Bata rufe bakinta ba sai suka gay a yi juyi ya daki katakon dakin har saida dakunan su
kayi girgixa.
Ya fada cikin fushi yace “tunda kaltum ta tafi daga garin nan, ko wacce sai ta tafi babu
wacce xata sake xama a kasarmu.
Nan da nan kowa yayi carko carko suna duban mambela a tsorace, hankalinsu duk ya
tashi kan ka ce kobo sai jikinsu ya dau makerketa. Ya dakwa duk wanda yayi kokari
matso kusa dashi xasu bashi hakuri.
BABI NA GOMA
RAYUWAR KALTUM A KHARTUM
Kwanakin kaltum uku a khartum a lokacin ta ji rayuwa ta fara tsananta a gareta saboda
tsananin wulakanci, dabakin halin da kalah da ‘yarta lami suke nuna mata . kalah ma
sana’ar sayar da kosai take yi irin na madina. Kaltum taxage tana taya su aiki, itace mai
wankin wake, itace ixa wuta da wanke wanke ashe ba’a son ransu take yi musu wannan
hidimar ba, suna ciyar da ita ne kawai amma ba’a son ransu ba.
Suna wajen sayar da kosai da safe sai kalah ta dubi kaltum ta tsuke fuska t ace “kaltum
ina fatan dai kin san yadda rayuwar sudan take, kowa ta kansa yake kin ma fi kowa sani
tunda an ce bara ku ke yi a bur sudan. Dan haka ka’idar ciyar da bako kwanaki uku ne
kin cika kwanaki uku yau, don haka ki fita ki nemi naki tunda har yanxu iyayenki basu
bugo waya ba balle su turo da kudin jirgi.”
Hankalin kaltum ya tashi ta rasa abinda yake damunta, ta dubi gabas da yamma, kudu
da arewa babu inda ta sani , bata san inda xata fara neman kudi ba don haka sai ta fara
kuka ta fada cikin tashin hankali.
Ta ce “kalah, ina xan je in nemo abinci bayan ni bakuwa ce?
Ki taimaka min ki kira iyaye na a waya su turo da kudin jirgi ko mota sai in tafi………”
Kalah ta katse ta tun kafin ta rufe baki. Kin bani kudi ne da xaki ce in kira su a wayata,
su baxa su kira niba sai ni, ashe ni na damu suga ‘yar su. Baxan kira ba in daisu ba xasu
kira niba.
Lami ta jakunnen kaltum da karfi tace “ki bude kunnuwanki ki ji, ki sani anan khartum
ba’a bara ba kamar a bur sudan ba, idan ki ka yi bara a nan kama ki xa’ayi a kai ki dajin
mujawara a yarda ke, ke ba a nigeri ba ke ba a sudan ba har sai wahala ta kashe ki.”
Kaltum ta fashe da kuka ta juya ta koma gida ta shiga daki ta xauna akan buhun
kayanta, tayi tagumi tayi kuka har kamar idanuwanta xasu fice. Ta yi takaici akan rabo
tada aka yi da bur sudan aka kawo ta nan inda bata san kowa ba, babu mai taimakonta.
Haka ta yini da yunwa ba abincin safe babu na rana saida daddare tana kallon kalah da
‘yarta suka dafa abincinsu suka juya mata baya suka ci saida suka rage saura suka bata
ta ci ta sude kwano sannan ta iya samun dan barci.
Gari na wayewa bayan kaltum ta yi sallah sai ta shiga wankewa kalah wake, a fusace
lami ta xo ta fuxge kwaryar da waken yake ciki ta sake maimaita mata cewar ba xasu iya
ci gaba da ciyar da ita ba ta je ta nemi sana’arta. Kaltum ta koma gefe ta tsuguna tana
kuka tana ganinsu suka dauki kayan suyar kosansu suka tafi wajen sayarwa.
Hantsi yayi cikinta kuwa ya dau rurin yunwa tana tunanin in da xata nufa gashi bata san
kowa ba a garin sai taji an dafa kafadarta ta baya tana dagowa sai taga wata matashiyar
budurwa ‘yar kusa da dakinsu ce mai suna fatsima.
Ta ce da kaltum”lafiya kike xaune kina kuka ke kadai? ”
Sai kaltum ta fara share hawaye tana murmushin karfin hali tayi sauri ta gyara xancen ta
ce wai ciwon kai ne yake damun ta. Fatsima ta girgixa kai tace “babu wani ciwon kai da
yake damunki mun san komai tun sanda kika xo muke tausaya miki saboda mun san
xaki hadu da wulakanci a wajen kala da ‘yar ta saboda basu da kirki kowa ya san bakin
halinsu ko kadan basu da mutunci gasu da rowa. Ki tashi muje kiyi irin sana’ar da muke
yi.”
Kaltum ta mike jikinta a sanyaye xuciyarta cike da fargaba saboda bata san sana’ar da
suke yi ba, haramtacciya ce ko halattaciya. Tafiya suke yi xugwi xugwi babu wanda yake
Magana a cikinsu har suka isa bakin wata katuwar kasuwa wacce ake kira da suna
makadi. Kasuwar markadi itace kasuwar da ake sauke danyan kaya mota mota irin su
tattasai, tumatur, atarugu, dankali, salad, kabeji da dai sauransu. Sai suka tafi wajen
wata katuwar bola in da ake jibge lalatattun kwanduna da gwalagwajin kayan miya
ma’ana rubabbun kayan miyar da aka tsince aka xubar.
Sai taga fatsima ta samo Kwando ta tsugunna ta fara tsintar masu dan kyau tana Tarawa
a cikin kwandon.
Kaltum ta tambaya cike da mamaki “me xa muyi dashi? ”
Fatsima tace “ke dai kawai ki samo Kwando ki xo ki fara tsintar masu kyau kina Tarawa.”
Kaltum ta aiwatar da abunda fatsima ta umurce ta su yi, suka tottona sosai da hannunsu
ga wari bolar tana yi harda suka tabbatar sun tara da yawa sannan fatsima ta nuna mata
fanfo suka je suka wanke tsaf, suka wanke kwandunan ma sannan tace su dauka aka su
tafi kasuwar adare karamar kasuwa ce. Suna isa adare kuwa Allah Ya kawo wasu mata
suka saya na kowannensu hamsin jine, ya isa su ci abincin yau ko babu nama. Farin ciki
ya kama kaltum ta dinga yiwa fatsima godiya da ta nuna mata hanyar cin abinci badan
ita ba, da batan san yadda xa ta yi ba.
Haka fatsima da kaltum suke yi kullum gari na wayewa saisu nufi markadi a gabansu ake
sauke kwandunan danyan kaya daga mota. Suna tsaye ake ware rubabbun yayin da
suma suke ware masu saukin rubar suna tarawa har sai sun tsince masu dan kyaun wani
lokaci har su sami masu kyau sosai saisu wanke tas su je su sayar a adare.
Xuwan kaltum sai ya xamowa fatsima alkhairi domin a yanxu tafi da samun kudi, mai
makon su siyar hamsin jine har metan jine suke yi saisu hada kudin su je su sayo danyen
kaya su xo su dafa abinci lafiyayya harda kifi ko nama su ci su koshi idan da canji su kora
da lemun kwalba.
Kawance ya kullu tsakanin kaltum da fatsima yayin da haushi da hassada ta kama kalah
da ‘yar ta har suka daina yi mata Magana don bahaka suka soba, sun so kaltum ta rasa
yadda xata yi tayi ta bin su, suna yi mata wulakanci. Ta kai ta kawo ko gaishe su kaltum
tayi basa amsawa idan a taba kayansu ko buta ce sai su kwace su kyareta.
Xuwan kaltum khartum da sati uku da magaruba bayan ta idar da salla a daki sai taji
muryar kalah da lami suna yiwa mutanen gidan sallama a daki daki da alama bulaguro
xasu yi, nan da nan kaltum ta fito daga daki sai ta gansu niki niki da kayansu aka da
alama dai kaura xasu yi. Hankalinta ya tashi ta fito a gigice ta tsaya tana kallonsu tana
sauraron abinda xasu ce mata. Amma sai taga ko kallonta basu yi ba sun kada kai xasu
fice, sai ta fashe da kuka ta bi su har kofar gida.
Ta ce kalah ina xaku je ku bar ni, ni kadai ban san kowa ba a nan sai ku?
Kala ta tabe baki sannan ta kai mata duka kaltum tayi sauri ta kauce.
Ta ce “ina ruwana ki mutu mana iyayenki ne suka ce a kawo ki khartu, ga khartum nan
kiyi xama. Goyonki xanyi ko kuwa nono xan baki? ”
Kaltum ta fada cikin kuka “dan Allah ki kira su awaya, kice gani na xo su aiko da kudin
mota in tafi, ko ki bani number su. Idan kika tafi basu san numer kowa ba sai taki ita
kadai ce suke tunani xasu same ni.”
Kalah tace “ba xan bayar da lambar ba, idan kina da karfi ki xo ki kwata.”
Ta ja hannun ‘yarta lami suka yi tafiyar su, lami tana ta xagin kaltum.
Kaltum ta rushe da kuka ta shiga tsakar gida tana rusawa, kukan kaltum ya sa kowacce
ta fito a gigice suka hau tambayarta me yake faruwa?
Tana kuka tana Magana t ace “kalah ceta tafi ta bar ni alhali ban san kowa ba a nan sai a
bur sudan ni kuma bani da kudin da xan koma bur sudan wajen wadanda na saba.”
Gaje ta yi salati ta salance t ace “af ke ce kaltum wacce iyayenki suka aiko da kudin
jirgin ki suka ce a saka ki a jirgi ki tafi Nigeria? ”
Kaltum tace “kaltum t ace “kala tace basu turo kudin jirgin ba ammam dai sun ce mata
xasu turo.”
Gaje tace a’a sun turo mata kudin jirgin kasa na xuwanta da dawowarku daga bur sudan
sannan suka turo mata kudin jirginki har xuwa kano. Sannan itama

23 / 46