Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
goro bayaga lemuka da abinci iri iri a wajen
daurin auren Abba da Madina.
shikuwa agidan Tasi'u a cikin tashin hankali suke saboda Tasi'u nacikin gidansa
hankalinsa inyayi miliyan ya tashi haka ya tashi hankalin iyalansa saboda rike kai yayi
yana ihu yayinda ya dinga faduwa kasa fuk sai an yayyafa masa ruwa sannan ya farfado,
'ya yan madina su dukka uku basu iya halattar wajen daurin auren ba suna ceto ran
mahaifinsu haka ma matansa tun suna ganin shirme yake don suji haushi yakeyi har
suka fara tsorata suka tabbatar ba wasa yakeyi ba da gaskene, suka rugo suka kamasa,
suka dauka a surutunsa baya fasa tsinewa sa'ada wacce itace tayi sanadiyyar rabuwarsa
da Madina, ya dau alwashin Madina na tarewa agidan Abba itakuma zata tare a gidansu
ma'ana zai saketa, rirrikeshi sukeyi hakuri ake bashi shikuma tamkar dalmar wuta ake
dana
masa a kahon zuci musamman dayaji an mika sadaki lakadan dubu hamsin aka shafa
fatiha, jama'a sun shaida Abba ya zama mijin Madina saiyaji tamkar ya cire kayansa ya
danna waje da gudu aka rirrike shi.
Madina dai batasan abunda yake faruwa va tana can agidan sumayyah itada mata yan
uwanta suna ta shagalinsu don kaltum da jakar kayanta tazo sai ta shafe kwanaki uku
cur rakiyar amarya har Abuja za aje da ita,
alh Adnan ya yarje mata, yinin biki tayi kyau walima tayi kyau an ragargaza wa azi da
karatun alkur ani haka ango da abokansa sunyi reception hadadde amarya da ango sun
caba ado sunyi kyau matuka ko makiyansu vaza su kushesu ba, komai ya wadata babu
yunwa babu kishir ruwa an bubbuga abubuwa daban daban aka rarrabawa wadanda
suka halacci bikin da hotunan amarya da ango a kalandu da memo, t shirt hankacib,
barguna, atamfofi , bokitin roba agogo da dai sauran su.
amarya da manyan aminanta a jirgi suka tafi
Abuja sauran jama'arne suka tapi a motoci,
kaltum na makale a kugun amarya itada shahida don haka sun sami tafiya a jirgi
koma dai ame sukaje kowa dai ya isa lafiya kuma kowa ya dire akatafaren gidan amarya
da yake unguwar maitama, gida ne matsanancin girma dauke da falo biyu kicin daya
dining area, dakuna uku kowanne da bandakinsa aciki ga farfajiya mai fadi inda zai ci
motoci uku sai boys quaters daga bayan gidan,
ba girman gidan bane keruwar gidan, tsara shi shine keruwar gida saboda gidan nan ya
tsaru da ga ginin har kayan ciki anzuba kayan
kalarda ya dace komai nagidan ruwan zuma ne brown, yadda kowa yaga gidan nan haka
ita ma Madina saida aka kaita tagani koda wasa Abba bai shawarce taba ko a labari bata
san sanda ya gina ba balle lokacinda zai zuba kayan ciki babu sisinta ya zuba mata
komai sabo,
hawaye kawai take zubarwa na farin ciki saitayita godewa Allah a zuciyarta.
farin cikinda kaltum da shahida suke yi har yafi na kowa saikace su aka mallakawa
gidan,
kowa yana san barka musamman sumayyah tayiwa Madina murna tayi mata fadan zama
lafiya,
kwanaki biyu akayi cur a gidan amarya aka kalkalewa amarya da ango gidansu tas tas
sannan aka tapi aka barsu su kadai,
Abba yace saboda zaman kadaici da kuma girman gidan zai samo mata masu aiki biyu
babbar mace daya da yarinya karama donsu tayata aiki,
Madina tace Allah Ya sauwake ita bata bukatar yan aiki zatayi aikin ta dakanta haka
bazai hanata ta kula da mijinta ba kuma,
dole tasa Abba ya hakura da zancen yan aiki saidai koda yaushe suna rigima idan yazo
tayata aiki, shi yana tausayinta wai aikin gida yayi mata yawa ita tana tausayinsa bataso
yasha wahala tafi so ya koma ya zauna ta dafa ta kawo masa yaci, daga karshe suka
tsayarda shawara guda daya cewar duk sanda zata shiga kicin Abba zai jawo kujerarsa
ya zauna yana tayata hira amma bazai tayata aiki ba, saboda bayaso tayi nisa dashi dole
ce take fita dashi wajen aiki daga ya taso daga aiki baya zarcewa ko ina sai gida wajen
Madina, haka ita ma batajin dadin zuciyarta idan Abba ya fita bata samun nitsuwa har
saiya dawo gareta don haka Abba ya dawo dan lele ko jariri sai haka, tabbas hasashensa
yazama gaskiya ba dukka mace vane zata iya biyayyar da Madina takeyi ba musamman
ma yanzu data kara wayewa a wajen sumayyah ta kara, kozuwa da wahalar rayuwa ta
sake tabbatar wa Abba mai kaunarta ne duk duniya babu mai kaunarta fiye dashi, ta
sake tuna amanarsa da mahaifansa suka bata ta dinga tuna irin hatsari da tuggun da
Tasi'u ya dinga jeho masa don ya tsoratar dashi yafasa aurenta amma baiyi ko gezauba,
uwa uba irin dukiyarsa daya kashe don ya dadadawa rayuwarta yana kan kashe mata
ma don duk abunda ya mallaka baya kyashin bata har sai tace ya isa haka,
bayan aurensu da watanni biyu ranar litinin da misalin karfe goma sha daya na safe
Madina na kishingide akan doguwar kujerar dake tsakiyar falonta tana rike da
tsadaddiyar wayar ta wacce aka yi mata lakabi da Black Berry tana turawa abun
kaunarta Abba sakon soyayya da tsantsar bege sai taga wata lamba ta shigo, ma'ana
ana kiranta saidai tana matukar mamakin ganin sunan mai kiran dai dai wannan lokaci
tayi firgigit ta tashi zaune ta amsa cike da fargaba ta fada cikin girmamawa, alh Adnan
ina kwana?
ya amsa cike da fara a, yace ina mai gidan ki tun dazu ina kiransa vai dauka ba.?
Madina tace yana wajen aiki ko baya tare da wayar akusa dashi nima dai munyi awa
rabonda muyi magana.
alh Adnan yace ba mamaki to, don Allah idan yakira kice masa yayi kokari ya kawo ki
ofis dina ina neman ki.
ta dafe kirji tace alh lafiya?
badai matsala dai aka samu da kaltum ba?
alh Adnan yace karki damu va matsala vane sai alkhairi.
cikin sanyi jiki tace to shikenan zan fada masa zamu zo insha Allah.
yace to daga nan zuwa karfe uku na yamma ina ofis idan ya wuce uku to saidai
kusameni a gida.
suna ajiye wayar sai Abba ya kira tayi caraf ta dauka cikin laulausar murya tace my heart
inaka shigane alh adnan yayita kira va ka amsa ba?
Abba yayi murmushi yace my life Wallahi aikine yayi yawa yanzu na dauko wayar naga
missed calls dayawa hardana alh Adnan din nace sai na kira gimbiya ta tukunna
zankirawo su daya vayan daya, lafiya yake nemana?
Madina ta lumshe ido tace to dai da baisameka ba niyakira yace infada maka ka kai ni
ofishinsa yana nemanmu kaga nan kiran mahimmanci ne kuma da gaggawa.
Abba yace to Allah Ya sa alkhairine bari inkirawo shi inji, ki shirya zanzo yanzu na
daukeki muje.
ba ayi awa ba saiga Abba a gida ya tarar da Madina ta shirya tsaf a zaune a falo tana
jiransa, ya dube ta yayi murmushi yace my love kinyi kyau,
ta lumshe ido tace na gode ai kai daman konayi wanka ko ban yi kwalliya ba sai kace
nayi kyau,
yace tashi mu tafi na kira shi yace mu kwantar da hankalinmu ba matsala bace bazai
wuce dai zancensa da kaltum bane, ya kama hanun ta ya jata suka pita, ya bude mata
murpin mota ta shiga sannan ya xaga Shima ya shiga suka pice.
basu sha wahala ba wajen hawa suna shiga suka iskeshi a luntsumemiyar kujera yana
juyi yayin da yake ta rubuce rubuce akan wasu file yana ganinsu sai yayi dariya yana
nuna musu kujeru,
suka zauna bayan sun gaisa sai ya jawo wayarsa ya kira wata lamba cikin harshen
turanci yake magana yace kazo ofishina gasu sun zo.
Madina ta kalli Abba shima ya dube ta cike da mamaki gaba daya suka kalli alh adnan
sai yayi murmushi yace kada ku damu so nake mutumin yashigo Ya tabbatar min kuyake
nufi sai inyi muku bayani, idan kuma baku bane shi kenan.
Madina ta gyara zama tadafe kirji tace alh lafiya dai ko waye mutumin yasan mune me
muka yi masa?
Abba ya dafa kafadarta ya fada cikin laulausar murya my love ki kwantar da hankalinki
kinsan fa kina da hawan jini banaso ki dinga yawan damuwa meyasa kike firgita alhali
kinsan babu wanda kika yiwa laifi kuma ke kike yiwa jama'a nasiha su yarda da
kaddara....
kafin ya rufe bakinsa aka turo kofa aka shigo, gaba dayansu su dukka suka dago ido
suna duban mai shigowa,
idonsa ya dira akan Madina itama ta dubeshi saitayi wuf ta mike tsaye kamar an
zabureta ta fada cikin yare wanda yayi kama da inyamuranci sai shi ma ya mayar mata
da amsa sai suka ruga da sauri suka rungumi juna suna rusa kuka.
hankalin Abba ya tashi ya fada cike da damuwa Madina lafiya kikaje kika rungumi kato?
Kin san shi ne?
kuka ya hanata bayani shi kuwa daman mutumin ko hausa bayaji balle ya fahince
abunda Abba ke fada,
alh Adnan ne ya hauyiwa Abba bayani yace wannan mutumin da kake gani mun dade
muna harkar karuwar arziki tare daga enugu yake, muna safarar man fetur ne shekara
da shekaru muna abota, mutum ne mai amana har Allah Ya sa ya auri musulma muka
masa nasiha ya musulunta, sunan sa ada innamani yanzu kuwa Abdullahi, dazu yazo
ofishina sai kawai yayi ido hudu da kalandarku ta bikin aurenku gata can sai naga yatafi
da sauri ya fisgo yana kallo har hannayensa yana rawa na tambayeshi lafiya dai ko?
saiyace tayi masa kama da kanwarsa data bata shekara da shekaru yana neman ta
daman ance masa tana kasar hausa ta auri musulmi .to shine na kira wayarku alokacin
babu tantama nasan Madina ce yar uwarsa, tunda na sami labarin tarihin rayuwarta ashe
kuwa itace din, shi ne yasa kagasun rungumi juna suna kukan murna .
Allahu akbar Allah abun godiya kalmar da Abba yake ambato kenan alokacin da alh
Adnan yake bawa Abba labarin abunda yake faruwa ita ma Madina cikin yarensu ta bawa
yayanta tarihin rayuwar ta sannan ta gabatarda mai gidanta Abba,
yayanta ya rumgume Abba yana farin ciki sai godiya yake yi masa nandai suka dunguma
suka tafi gidan Madina don yaga muhallinta shima kuma ashe matansa biyu daya ba
musulma ba ce tana enugu amaryar ce musulma beyarabiyace tana nan cikin Abuja a
maitama, basu da nisa ma,
rayuwa ta dawowa Madina sabo fil mai tafe da tsagwaron farin ciki tana kuka tana bawa
yayanta tarihin yadda Abba ya tarki tafiya enugu nemansa saiya yi hatsari a hanya
saigashi cikin ruwan sanyi Allah Ya hadasu.
Kun ga yadda na yiwa Abba Mutumci na
ADON DAWA 47
.
TRUE LIFE STORY
.
rayuwa ta dawowa Madina sabo fil mai tafe da tsagwaron farin ciki tana kuka tana bawa
yayanta tarihin yadda Abba ya tarki tafiya enugu nemansa saiya yi hatsari a hanya
saigashi cikin ruwan sanyi Allah Ya hadasu,
tun sanda Madina tahadu da dan uwan ta bata ta taba kwana ta yini ba batare data kira
shi awaya taji muryarsa ba, haka shima bai taba kwana 2 baizo ya ganta ba indai yana
gari haka yake ta ambulo mata dukiya domin mutum ne mai dinbun dukiya da
kyaututtuka da ya kamata yayiwa iyayensa da danginsa sai yake jifgewa Madina domin
ita kadai ta rege masa, ita yake gani yaji dadi, yafita shiga damuwa daya rasa ta, ya fita
wahalar neman inda take yafita dauriyar addu ar Allah Ya sa ya ganta.
ta dinga buga waya kano tana shaidawa masoyanta cewar taga yayanta innamani kuma
babban farin cikinta ya musulunta shima,
farin ciki ya rufe kaltum, sumayya, mummy Hafsat, general tukur da 'yayana,
har kano tazo dashi yaga 'yayanta da iyayen Abba,
yayi musu godiya Madina ta nunawa su sumayyah sabuwar motar da ya bata, lalle Allah
mai kyauta duniya da lahira mai yanta bawa Ya azurta talaka a dare daya babu abun da
madina take yi sai sallah da gode wa Allah babu abunda tanema ta rasa a duniya yanzu
sai dai ta nemi lahirarta, ta sami dan uwa da miji masu sonta haka ta sami arziki marar
iyaka, tanaci tana wadata 'yayanta tana kyautatawa masu kudi badan basu dashi ba
sannan tana taimakon mabukata saboda tasan illar talauci da yunwa.
Madina ce ke zaune cikin falonta na kano bangarensu a cikin gidan surukanta aka fitar
musu tana karatun kur ani Abba na gefe yana
sauraronta har lumshe ido yake saboda daddadar kira'arta sai wayarsa ta hau ruri
Madina ta tsaya da karatun ta dube shi ta lumshe ido tace amsa wayar sai inci gaba.
yace alh Adnan ne harta katse ma kafin in amsa,
Madina tace kirashi saboda Kiran wayar alh Adnan alkhairine mutum ne mai hada
khairan baya sharri,
Abba ya kira lambar nan da nan ya sameshi bayan sun gaisa saiyace ina Madina?
inason ganinku.
Abba ya gyara zama yace ga madinar a kusa dani sai Abba ya mikawa Madina kan wayar
cikin fara a da ladabi ta gaishe shi yace da ita kuna gidane anan gida a Abuja?
madina tace a'a muna kano shekaranjiya muka zo sai mun yi sati biyu zamu koma Abba
mai gidanane yake hutu sai.
alh Adnan yace yauwa daman nafiso mu hadu a Kano nima zan shigo kano in anjima dan
haka bayan magruba kuzo ku sameni agidana zamuyi wata magana.
sai madina ta tambaya cike da fargaba alh badai wata matsala bace dai ko?
ka fara fadamin don hankalina ya kwanta.
alh adnan yayi dariya yace alkhairi ne Madina wannan karon dai maganata ce da kaltum.
madina tayi dariya tace AlhamduLillahi haka nakeso inji saboda har na fara damuwa ina
tambayar zuciyata ko lafiya har yanzu bakayi magana ba gashi harta sami admission ta
fara zuwa makarantar BUK.
yace ai maganar ta taso gadan-gadan yau dai komai zai bayyana.
Madina tace Allah Ya tabbatar sai munzo na gode, farin ciki ya rufe madina suka dade
suna tautaunawa da Abba har saida ta daidaici yamma tayi lokacin dora abinci dare yayi
sannan ta tashi ta shiga bangaren mummy hafsat ta durgusa ta gaishe ta ta tambaya
cike da ladabi mezan dafa miki yau mummy?
mummy hafsat tayi dariya tace 'yata Madina ki dafa manan duk abunda da kika ga
yadace da tsofaffi,
su dukka suka tunsure da daria, madina tace to shikenan abinci kala goma zanyi muku
keda daddy duk sai kun cinye.
karfe takwas nadare afalon alh Adnan tayiwa su Madina, ga alh Adnan ga kaltum azaune
akan kafet ga Abba da madinarsa akusa dashi akan kujera daya gefe kuma sofi ce da
abun kaunarta saleh su ma suna sauraron abunda alh Adnan zaice, kowa zuciyarsa cike
da fargabar abunda yasa alh Adnan ya tara su.
can alh Adnan ya daga kai ya dubi kowannen su yayi murmushi yace AlhamduLillah da
Allah Ya bamu ikon haduwa anan kafin muce wani abu Madina ki bude mana taro da
addu'a,
Madina tace suka karanta salati goma ga Annabi (s.a.w) sannan ta dinga koraro addu o i
kala kala daga karshe ta shafa.
alh Adnan yace nakasance ina kaunar yar yarinyarnan kaltum tun tana yar yarinya
karama naga ya dace ta sami mai tattalin ta da nuna mata kauna kamar kowanne yaro
domin ta rasa shakuwa da shagwabarda zata yiwa iyayenta naji inason kaltum tamkar
nina haifeta mun shaku tamkar kawata haka muke labari duk yanda zanyi na gyara
tarbiyarta nayi haka, nayi kokarin turata makaranta don ta samo ilimi kamar kowacce
'ya, duk inda kakai ga iko da dan wani bakayi kamar iyayenda suka haife sa ba, sun fini
iko
da ita saboda bana gari suka cireta daga makaranta suka turata makka wai neman kudi
taje ta wahala aka bautar da ita tamkar baiwa, nayi takaici nayi kuka don takaici na
hakura har saida Allah Ya yanke mata akadawo da ita tazo takoma makaranta sannan
wasu shekaru aka sake daukarta bada shawaraba akasake tafiya da ita sudan, shekaru
biyu da tafiyarta muna tunanin tana
makkah sai ga marigayiya goggo fattu an kamo ta sai a lokacin ma take fada ai basa
tare da kaltum ta barota a sudan, dana bincika sai aka ce ai bara sukeyi a sudan na aika
kudi a daukota aka daukota tabbas kamar yadda saleh da sofi suka fada cewar ni nafi
can-canta in auri yarsu saboda ni nafi kowo sanin darajarta zanfi riketa amana fiye da
kowane da na miji hakane gaskiyane saidai kash!
kaltum ta hadu da wanda takeso fiye dani wanda take ganin zatafi samun nutsuwa
dashi, wannan kuwa shine mambela.
sai kowa ya zazzare ido yana kallon alh Adnan daga nan suka hau kallon kallon a junansu
hawaye ya surnano daga idanuwan kaltum ta girgiza kai tace basai mambela zan aura
ba,
sofi ma ta fashe da kuka tace alh yarinyarnan batada zabi mu bata taba ce mana tana
da wani mambela ba niban ma taba jin sunan ba.
alh Adnan ya girgiza kai yayi murmushi yace sofi ke baza ki san mambela ba kuma na
yarda vaki sanshi ba din saboda bata hira daku yanada nasaba da babban kuskurenda
kuka tafka arayuwa na rashin janta a jiki, tun farko ta tashi tana dar-dar daku bata sakin
jiki daku tamkar dodonni wannan ba daidai bane amma nida take hira dani take fadamin
matsalolinta ta shaida min tana son Mambela, Madina tayi rayuwa dasu acan ta tabbatar
min akwai mambela daga dukkan alamu shima yana kaunarta sosai tsakani da Allah.
Madina tayi ajiyar zuciya tace zancen mambela ai ya wuce alh duk inda aka kai da yabon
kyawawan halayensa baikai kamar ka ba, duk yanda mambela ya kaiga sonta da kula
dakai bai kaiga yadda ka kula da rayuwar kaltum ba itama ta sani kowa anan ya sani ba
kaltum kadaiba koni danazo a baya bayan nan kayimin halacci da ko dangina ba aminba
nida mijina Abba babu irin addu ar da bama maka, saita fashe da kuka.
malam saleh yace alh mudai kai muka sani, kai muka bawa babu kyau mayarda hannun
kyauta baya, yanzu mudai ba mu san da wannan saurayin nata ba, ko baxa ka aureta ba
bazan bashi ba tunda ban san asalinsa ba, ba yarenmu daya ba kuma ba kasarmu daya
ba....
alh Adnan yayi caraf yace amma addininku daya ko?
mambela mutum ne mai nitsuwa wanda yasan ya kamata, mai amana da tsoron Allah na
yaba da halayyarsa kuma na yarda yana son kaltum zai riketa amana ko bayan ranmu.
sai kowa ya zubawa alh Adnan ido suna duban sa duba na rashin fahimta ko basu furta
ba tambayarda suke jerowa azuciyoyinsu bai wuce kai ina kasan mambela da har ka
shaida shi da irin wadannan kyawawan halaye?
alh adnan yayi murmushi ya dubesu daya baya daya yace zaku tambaya ina nasan
mambela da har na shaideshi?
to ba almara bace kuma bana duba amma zan iya rantse muku da Allah duk halayyan
nan dana zayyano muku mambela ya hadasu dukka.
kaltum tayi ajiyar zuci yayinda kwakwalwarta ta kasa tantance abunda alh Adnan yake
nupi ta tambayi zuciyarta shin ko Madina ce ta bashi tarihin mambela?
sai Madina tace alh abunda kake fada akwai daure kai don kaltum ta baka labarin abun
alkhairinda yayi mata shine ka gama tantancewa har ka shaideshi?
ko kuwa alh Sa'adu ne ya fada maka haka?
alh Adnan ya girgizai ya kwashe da dariya yace ga kaltum nan zaune ki tambayeta nida
ita mun taba zama munyi labarin mambela?
tun a waya da ta ambaci sunansa bata sake ambatonsa ba a gaba na ba, haka Sa'adu
babu wanda yaki jini irin mambela sbd har hanci ya fasa masa a garin kwato kaltum suka
yi dambe har yau zaginsa yakeyi yace sanda yaje dauko Madina ma sun hadu ko kallon
juna basu ba don haka zancen ko wani ne yabani