Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
na samu nutsuwa yayi farin ciki
da abunda dansa ya min daga baya.
Xuwa na garinmu da wata biyu muka sake yin shwara da mahaifina xan koma garin
khaltum wajen abokin nan nasa shiek el-mustapha in sake samo ilimi. Na yiwa sarki
bayani ya gamsu ya bani ixini na tafi. Rayuwata a khartum rayuwa ceta ‘yanci, farin ciki
da wayewa. Na yi karatu yadda ya kamata haka na xauna da ‘yan burni na waye, nayi
hankali, na san me yake faruwa a cikin al’umma. Na koyi siya da siyarwa, na kuma sami
ilimin xamani kadan, na iya rubutu da karatu duk da daman mu komai da larabci muke yi
sabanin irin rubutun bokon da naga ‘yan kasarku na yi.
Ganin na nutsu mahaifina ya nunnuna mi gidajenmu da muke dasu a khrtum duka da
akwai ‘yan haya a ciki amma daya bayan daya saida muka xagaya. Akwai wasu abokai
na da muka yi karatu tare a wajen sheik el-mustapha suka ce jami’a xasu wuce akwai
yadda ake su sami certificate daga gwamnati, nima na kutsa muka samu aka dauke mu
a jami’a. saida muka cika shekara uku sannan muka kammala daegree dinmu duk akan
Qu’ani. Komai a saukake yake xo min dan na rika na horu a gidan kangararru, na fito da
sakamako mai kyau daga nan na wuce saudiya inda na shekara biyu a jami’ar madina na
hada masters dina. Sannan na dawo gida, na dawo da wata biyu muka hadu da ke.
Na shiga cikin abokaina da watsatstsu don in shiryar dasu, cikin dubara nake so in cusa
musu ra’ayina su dai na shahsanci, su kintsu su koma makaranta. Na xo da niyyar
wa’axantarwa ga duk marasa ilimi da kafuran garinmu amma sai dai da dabara bada
karfi ba. Shi yasa nake shiga cikinsu mu xauna a kasuwa muna caca a haka nake yi
musu wayo duk sanda lokacin sallah yayi sai in ce to a tashi ayi salla sai aci gaba.
Wancan yayi nan, in taro shi wanca yayi can in kamo shi dole mu musulman mu yi
sallah, kafuran kuwa suna gefe suna kallonmu idan mun idar sai mu sake xama in dinga
wa’axantar dasu cikin wayo ina fadar axaba ga wanda baya sallah, Alhamdulillah na
samu da yawa sun shiga musulunci yayin da wasu sun fara karkatowa da alama xasu
yarda da ni wata rana. Har yanxu wannan tsoran nawa da suke ji da yana nan, haka idan
na fada ba’a kin bi don haka na tsawatar dole an rage shaye shaye da iskance iskance a
garinmu.
Sanin da suka yi min, shiyasa da suka ganki suka ce ga wata mai kyau su kai min ke
shago mana, na biye musu don in samu in yi Magana da ke, in san matsalarki, in taimaka
miki ke kuma baki fahimce niba.”
Kaltum tayi ajiyar xuciya ta gyada kai alamar labarin ya tsuma mata jiki tabbas ta yarda
mambela yasan Qur’ani don baya jimla daya ba tare daya ja ayar Qur’ani ba ya fassara.
Daga karshe ya dubeta yace “kaltum, xaki yarda ki auri mambela, mu koma gidana a
khartum mu xauna in saka ki a jami’a kiyi degree kema daga nan in kai ki saudiyya kiyi
masters? ’
Sai ta yi sauri ta ja mayafinta ta rufe fuskarta da alama dai dariyar jin dadice ta kamata.
Magaruba tayi don haka mambela yayi mata sallalma ya nufi garinsu, ita kuma ta shiga
gida xuciyarta ta kara shaker kaunar mambela.
Kwanci tashi su kaltum sun cika shekaru biyu cur a bur sudan, sun mike kafa sun baxa
kayansu suna jin dadin rayuwarsu basa tunanin komawa gida. Masu aure da haife haife
sai yi suke suna sakewa. Gidan su kaltum sai ci gaba yake yi koda yaushe suna kara
bunkasa yadda xasu sami ci gaba da dadin xama. An kara bandaki haka an lailaye
kowanne daki da katako kamar dai yadda mambela ya bude musu hanya.
Mambela ne ya iske madina a kofar gida tana xaune tana jin hantsi, bayan tagama sayar
da kosanta. Bayan ya gaisheta sai ya tambayi abar kaunarsa kaltum, t ace masa ta aike
ta kasuwa. bayan ya jima suna ta hira sai ya tuntubi madina xancen aurensa da kaltum,
kan kace kwabo hankalin madina yayi mummunan tashi har saida mambela ya gane ta
shiga wani hali shima ya tashi nasa hankalin.
Ya fada a furgice”anty madina lafiya? ”
Ta xubo da hawayen daya cika mata ido ta girgixa kai tace “mambela ba xan boye maka
ba a gaskiya bana son in jefa rayuwar kaltum a irin halin da na jefa rayuwata, saboda ni
babba ce babu abunda ban kammala bana rayuwa tunda na yi aure na hayyayafa, na
girma nayi hankali kaltum kuwa yarinya ce karama wace bata fara sanin rayuwa ba.”
Mambela ya fada cike da damuwa “anty madina, ina son kaltum ba xan cuce taba, xan
riketa amana tamkar ni ne ubanta ni ne danginta.”
Madina ta girgixa kai tace “ba haka ba ne mambela, ba wai don ba xa ka iya rike taba na
fadi haka. Ba na son ace a mtsayin ta na yarinya mai karancin shekaru ace ta rabu da
iyayenta da danginta ta kauro wata kasa ta gina rayuwa ita kadai. Da xarar ta yi aure ta
fara haihuwa ko kudi aka bata ba xata iya tafiya kasarta ba saboda yaranta. Ka ga daga
nan ta xama tsintacciyar mage wacce ba’a san asalinta ba, a iya kiranta shegiya marar
uba, xa’a iya ce mata ma ‘yar iska, ko bata da asali a bola aka tsince ta.
Mambela ya dubi madina ransa ya fara baci ya cije baki ya fada cike da kasaita “me ki ke
son yanxu ki fada min? ”
Madina ta tabe baki ta fada cike da isa tace “ina son sanar maka ba xata yi aure a nan
ba sai dai in ka bi ta kasarsu gaban iyayenta ka nemi aurenta a can; subaka ita da
kansu.”
Ya fada cikin daga murya yace “kaltum ta fada min ba xata koma kasarsu ba a nan xata
dawwama.”
Madina ta girgixa kai tace “rashin hankali ke damunta amma ni na yanke shawarar tura
ta gida. A yanxu haka na kusa tara mata kudin mota, xan hada tada masu tafiya a mayar
da ita gidansu ko tana so ko bata so.”
Mambela ya xubo da hawaye mai xafi daga idanuwansa ya dubi madina duba irin wacce
take kokarin ta raba shi da rayuwar sa yace “me yasa xaki tura kaltum ita kadai ke baxa
ki tafi ba? ”
Madina ta yi shiru can tace “saboda na fi son in ceci rayuwar kaltum akan in ceci
rayuwata. Na fi kaunar in saka kaltum cikin farin ciki da kwanciyar hankali da in nemi
nawa farin cikin.”
Mambela ya mike tsaye a fusace yace “babu inda kaltum xata je, saboda muddin kaltum
ta koma garinsu iyayenta ba xa su bari ta dawo ta yi aure a sudan ba. Ki na nufin in bar
kaltum ta koma kasarsu anan in je in nemi auren ta?
Kema kin san ba xa su yarda ba sai dai idan na aure ta idan ta haihu sannan mu je da ita
a lokacin babu mai raba auren. Ko kina nufin alhaji adnan xai bari wani ya aureta in bashi
ba yadda yake nuna tsananin sonta………..
Kafin yarufe baki sai ga kaltum a tsaye a tsakaninsu yayin da aka hau kallon kallo
tsakanin kaltum da mambela, kaltum da madina. Kaltum ta rushe da kuka, ta dora hannu
aka tana rurawa.
Ta ce “mambela ya isa haka, bana son irin wannan, anty madina ce uwata, ubana a
kasar nan ba dan ita ba da ban kawo yanxu ba, babu wahala da wulakancin da ban gani
ba a baya ita ta kwace ni da tuni an kashe ni. Me yasa xaka dinga yi mata tsawa da ihu
akan tana fadan ra’ayinta tasan abunda take hangowa wanda mu da dukka ni da kai ba
xa mu hango ba. Mambela ba xan iya auren ka ba tunda ka fara yiwa mahaifiyata haka.”
Sai mambela ya sulale kasa ya durkusa yana rokar madina da kaltum afuwa.
Madina ta rushe da kuka ta jawo kaltum jikinta ta rungume ta, su dukka ukun kukan suke
yi, har yin hakan ya jawo hankalin jama’a suka taho suna tambayarsu lafiya. Nan da nan
kowannensu ya share hawaye, ya nuna babu komai.
Sai madina ta mike tace dasu, su biyo ta suka yi tafiya mai nisa xuwa bakin ruwa can
gefen da babu kowa sai yashi turmus da iska mai tafe da feshin ruwa mai sanyi yake
firfita su. Suka samu inuwa suka xauna a kasa yayin da madina ta saka su a tsakiya. Ta
dubi mambela ta juya ta dubi kaltum sai hawaye ya sirnano mata daga idanunta, ta sa
gefen mayafinta ta goge sai ta yi murmushi.
Ta ce “mambela xan baka labarina wanda nake ganin ban ji dadin abunda ya faru da
niba shi yasa bana son irinsa ya faru da rayuwar kaltum.”
Sai ta gyara xama ta bawa mambela tarihin rayuwarta kacokan kamar yadda ta bawa
kaltum a baya, ta bashi labarin haduwarta da tasi’u, xamansu, har xuwa rabuwarsu.
Sannan ta bashi labarin Abba da yadda ajalinsa ya xo.
Ta nuna masa irin halin da ta shiga da irin wulakance wulakancen da ta fuskanta a garin
da ba’a san asalinta ba, ta nuna masa irin gorin da korar Karen da ake yi mata don an
san bata san kowa ba kuma bata da kowa. Ta nuna masa irin tsananin son da tasi’u ya
ya nuna mata amma da xama ya yi xama ya sake ta, ya kore ta alhalin ya fi kowa sanin
bata da kowa a garin shi yasa bata son kaltum ta xama haka itama. Ta kuma nuna masa
cewar ba xa ta so ya fadi halin da Abba ya shiga ba sanadiyar son kaltum, ba xata so ta
dauke masa kaltum ba, ya rasa taba, amma ta amince ya bi kaltum kasarsu wajen
iyayenta ya nemi aurenta idan sun amince su aura masa ita, su biyo su xo aga
muhallinta; yin haka ba wahala ba ne a wajen Ubangiji.
Mambela ya sirnano da hawaye ya girgixa kai yace “abu ne mai wuya iyayen kaltum su
yarda su su bani ita, ko sun amince alhaji adnan ba xai bari ba. Don in bi kaltum Nigeria
nida iyayena ba wahala ba ne amma xai yi wahala su yarda in auri ‘yarsu in taho da ita
alhali suna can suna neman ta ido a rufe hankalinsu xai tashi idan suka ji labarin cewar
tana sudan ba’a saudiyya ba.”
Kaltum tayi shiru tana kallon mambela hawaye kadai yake kwarara tana sake gaskata
abunda mambela yake fadi gaskiya ne cewar tabbas ko iyayenta sun amince ta auri
mambela to alhaji adnan ba xai amince ba ko ba xai aure taba.
Madina taci gaba da lallashin , mambela amma fa tana nan akan bakanta na dole sai dai
yabi kaltum Nigeria ba xai aureta anan ba. Yayin da kaltum a xuciyarta take sake
tabbatarwa cewar ita kuwa sai dai a kai gawarta Nigeria amma ba xata koma ba don tafi
jin dadin xamanta a nan akan a gaban iyayenta. Rugumutsi kenan yaya xa’ayi ken an ,
tunda kowa da nasa ra’asyin a cikin su ukun ?
A hka aka rabu ba tare da kowa ya san a wacce shawara aka tsaya ba.
Tun daga lokacin mambela ya shiga damuwa, walwalarsa ta ragu, fara’arsa ta disashe ya
xama tamkar mutum mutmi gashi dai a xaune amma xuciyarsa tana tunanin yadda xa’a
ayi ya auri kaltum.
Haka ko ya xo hira wajenta hirar bata wuce kaltum karki tafi kasarku ki bar niba, idan
kika tafi ban san yadda xanyi in yi rayuwa ni kadai ba, ba ke. Bata bashi amsa ba, amm
sai dai ta lankwabe kai tayi kamar xata yi kuka saboda itam bata san mafita ba. Kwanaki
uku bata ga mambela ba sai taji labarin ashe bashi da lafiya sosai, ko kofar gida baya iya
fitowa. Hankalinta yayi matukar tashi kana kallonta xaka tabbatar da a cikin damuwa
take. Da yamma kaltum tayi jugum akan katifarta yayin da abincinta na rana na gefe
bata iya ci da yawa ba, sai madina ta xo ta tsaya a kanta ta dubeta tayi dan murmushi
yayin da itama kaltum tayi mata murmushin karfin hali.
Madina t ace “tashi ki shirya, kiyi kwalliya ki sami kawayenki biyu su raka ki garin ‘yan
ADON DAWA gidan sarkinsu ki gaishe da marar lafiya yarima mambela sai hankalinki da
nasa ya kwanta.”
Kaltum ta kwashe da dariya ta kifa kai akan filo, ta rufe fuska alamar kunya. Madina ta
janyo hannuta.
Ta ce “wallahi sai kin je kunyar karya ce kike yi, gashi nan kin kasa cin abinci tun jiya da
aka fada miki bashi da lafiya kika shiga damuwa. So kike ayi majinyata biyu keda shi? ”
Kaltum ta tashi tana farin ciki amma fa tana wayencen har cewa har cewa take yi “ni na
mantama an ce mambela bashi da lafiya.”
Kaltum da kawayenta biyu amina da hansai ne suka ci ado suka nufi garin ADON DAWA .
Tabbas kana hango ‘yan matan nan uku xaka san wacce tayi kama da amrayar yarima
mambela. Amina ta saka riga fara (t-shirt) da siket baki, da shudin gyale. Yayin da hansai
ta saka farar riga (t-shirt) da xanin atamfa, ta ci dammara da gyale kore. Kana ganinsu
kasan wadannan basu taba shiga aji ba, a kasarsu ma ‘yan talla ne. kaltum kuwa baya
ga kyakkyawar halittar da Allah Yayi mata ta iya tsara ado, saboda daman can tana da
wayewa da ajinta ta xo.
Kaltum ta ci kawalliya da wasu riga da siket matsatsu farare, sai ta nada lufaya fara
wacce akayi mata xanen fulawa baki, ta saka wani takalmi mai tsini baki duk mambela
ne yakesaya mata. Kananan kitso ne a kanta yirin yirin wanda ya xubo goshinta yayinda
fuskarta ta dauki hoda, jan baki, da kwalli rangadadai.
Kaltum ce a tsakiyar kawayenta suna tafe suna hira har suka isa garin ‘yan ADON DAWA
fadar sarki suka nufa. Sai suka fara takawa a hankali sakamakon dandaxon samarin da
suka hasko a kofar gidan suna xaxxaune akan wata katuwar tabarma.
Kaltum t ace da kawayenta su juya su koma gida ita ta fasa xuwa dubiyar, yayin dasu
amina suka ce su je kawai dn suna so su shiga gidan sarki daman basu taba shiga ba. Ko
ba’a fada musu ba daya daga cikin samarin ne ya hango su ya wafto sauran ya nuna
musu su saisu kaga gaba daya sun waigo suna kallon su. Harda wasu da suke
kwankwance sai suka mike xaune suna duban su. Suka daure suka ci gaba da tahowa
amma fa suna nonnokewa.
Sai daya daga cikin samarin ya fada cikin yarensu y ace kalli ta tsakiyar ku gani yadda
take da kyau . dama a kauyukan nan akwai hadaddiya haka?
Wannan ai itace ADON DAWA sai suka kwashe da dariya su duka.
Amma dasu kaltum suka kusn isowa karkashin bishuyar sai suka gane su waye yayin da
suma samarin suka gane ashe kaltum ce.
Mambela na daya daga cikin samarin shine wanda yake kwance sai ya tashi ya xauna
nan da nan farin ciki ya kama shi ya hango abar kaunarsa kaltum, yayin da ita ma ta ji
sanyi a ranta da ta ganshi. Suna hada ido sai suka yiwa juna murmushi, mambelan da
ake rikewa idan xai tashi, shine yayi xumbur ya tashi da kansa ya taho da sauri ya tare
su tun kafin su karaso.
Ya fada cikin murna ‘yau sai kun shiga kun gaisa da sarki daman ina bashi labarin ki
yana so ya ganki.”
Kamar kaltum ta nutse a cikin kasa haka taji nauyi da munyar dandaxon matan da suka
dinga diddigowa daga dakunan su suna fitowa kallon amaryar mambela, sai buda ake
ana yabon kyawunta da hankalinta. Don daukaka sai ga kaltum a gaban sarki tana
kwasar gaisuwa. Sarki yasa hannu ya dafa kanta, ya dafa kan mambela yayi musu
addu’ar fatan alkhairi sannan suka tashi suka fito yayin da aka saka bayin gidan suka
rako su da kwaryar dabino daya da kwaryar nono biyu har kofar gidansu.
Mata su ka taru a tsakar gida suka kewaye su kaltum suka dinga bayar da labarin yadda
suka isa gaban sarki. Yayin da sha’awa ta kama ta kama sauran mata kowacce tana
cewa dama itace ta sami dan sarki mambela.
Sallamar wata bakuwa ceta katse hayaniyar da ake yi, suka waiwayo gaba daya suna
duban ta.
Jama’a wace ce wannan matar? ,
daga ina ta xo? ,
wa take nema?
ADON DAWA
LITTAFI NA 2 (PART 20)
.
Matar dai bakuwar fuska ce amma kuma bahaushiya ce, hausar katsina take yi. Bayan ta
karaso tsakar gidan ne aka mika mata karamar kujera ta xauna yayin da ta yi jam’I ta
gaishe da kowa. Sai ta fara gabatar da sunanta da kuma garinsu. Ta ce sunanta Hauwa’u
‘yar asalin garin ‘yan tumaki ne a jahar katsina, sanna ta ambaci sunan wata mata wai
shatutuwa ta xo nema. Sunan matar da ta ambata babu ita a cikin gidan nan don haka
suka tabbatar mata basu san taba. Sannan ta fara dogon kwatance sai can suka gae
shatutuwar da take nufi it ace matar da ta mutu a hanya a wajen haihuwa, sauran ‘yan
uwanta kuwa sun haye makka. Sai suka shaida mata shatutuwa ta mutu tun a hanya a
garin haihuwa.
Sai ta fashe da kuka tana cewa “kanwata ce uwa daya uba daya. Ni ce na aika mata da
kudi nace ta xo mu hadu a khartum mu tara kudi sai mu wuce makka, na ji shiru shiru
bata karaso ba har yanxu kuma bama waya dasu tunda kauyen namu babu waya sai na
xata so take ta haihu sannan xa ta xo. Shekaranjiya na hadu da ‘yar garin mu itama ta
xo kwanan nan shine nake tambayarta shatutuwa sai tace ta dade da tahowa tuntuni.
Aka ce in xo nan bur sudan akwai mutanenmu wadanda basu sami tafiya ba in duba ta
tabbas tana cikin sudan bata da kudin da xata haura makka.”
Ta sake rushewa da kuka mai tsanani, su kuma suna ta lallashin ta.
Can ta tsagaita da kuka sai tasa hannunta a jaka ta xaro wani hoto a ambulan. Ta ce “ga
hoton wata yarinya, ‘yan uwanta sun ce inyi musu cigiyarta a nan.”
Xaibu tasa hannu ta karba ta bude ta xaro hoton, yayin da kowaccensu ta xuro kai suna
kallon hoton, saisu dukka suka bude baki suna mamaki yayin da kallo ya dawo kan
kaltum. Gabanta ya fara kwaranya daga idanuwanta ta fara kiran “inna lillahi wa’inna
ilaihi ra ji’un.”
Hauwa’u tace lafiya, me ya faru da yarinyar, kar dai itama ta mutu?
don an bani tabbacin batahaye ba tana bur sudan shine aka ce lallai lallai a kaita
khartum wajen wata mata mai suna kalah itama ‘yar xangon daura ce, kalah ta dade a
khartum. Kudin jirgin yarinyar da komai yana wajen ta., iyayenta sun turo da isasshen
kudi suka ce lallai a kai musu ita. Shine kalah ta ji ina cewa xan taho tanan sai ta bani
hoton nan in taho dashi in cigiyarta, ga sunan yarinyar nan a bayan hoton.” Madina ta
karbi ta juya bayan ta karanta sai ga kaltum saleh baro baro a rubuce. Madina tace
“Alhamdulillah, Allah Ya yankewa kaltum wahala don haka kaltum shiga daki kiyi
marmaxa ki hado kayanki ku tafi.”
Yayin da