Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
xaginta. Kinsan fasa cin abincin nan yayi, ya mike
jiki na rawa ya figi mota sai gidansu, a can ita da iyayenta suka shiryo masa karya da
gaskiya, ya dauko matarsa suka shigo gida bai tambayeni me ya faru ba sai duka da saki
daya yayi min.
Ya kure ni cikin dare ina kuka, yarana suna kuka, na tafi na barsu. Dana fita ban san inda
xani ba don ba inda nake dashi wanda yafi makwabtan mu amma ba xan iya shiga in
fada musu duk abunda ya faru ba saboda ban taba fada musu matsalata ba tsakanina da
mijina sai xaman lafiya nake nuna musu. Hak basu taba sanin asalina ba duk da dai sun
san daga inda na fito da yadda aka musuluntar da ni a unguwar basu san kundin tarihina
ba.
Don haka sai na tafi gwammaja gidan wata aminiyata hajiya hadixa na yi mata karya n
ace mijina ya tafi da yaran garinsu sai ni kadai a gida kuma gyaran bandaki ake yi min
shiyasa na rufe dakina na xo inyi mata kwana biyu, tayi mamakin amma tayi murna.
Mami hafsa kuwa yarana ne suka kai mata labari suna kuka suka shaida mata an saki
mamarsu, hankalinta a tashe ta aika akira tasi’u ta tambaye abunda ya hada mu. Ya
xauna ya shirya mata karaye da nasa dana matarsa data shirya masa, idan ki ka ji
abubuwanda yake cewa a kaina sai ki rantse ban taba yi masa abu daya na kirki ba a iya
xamana dashi na shekara da shekaru. Yana gama bayanansa, mommy hafsa t ace
“karya kake yiwa madina wannan halaye ba halinta ba ne kuma ko Qur’ani xan dafa
baxa tayi haka ba.”
Ta bashi shawarar ya tashi ya nemo ni don idan ya rasa ni ya rasa mace ta gari har
abada. Babu inda shi da ita basu jejje nema nab a, inda suke tunanin ina xuwa basu
same nib a, sai gani kwatsam da yamma na dawo da kaina saboda na rasa inda xanje
ma, sai na yanke shawarar in dawo gidana in ba tasi’u da matarsa hakuri in xauna da
yarana. Tasi’u na gani na kafin in ce wani abu yace in shiga dakina ya mayar da ni. Ni da
‘yaya na muka yi ta murna.
Mommy hafsa ta aiko in je tana nemana na je, na iske ta a xaune a falonta sai ta fara
jero min tambayoyi akan me tasi’u da matarsa suke min?
Na boye mata nace “babu komai”
Data takura da tambaya sai taga na rushe d a kuka kawai, ta girgixa kai.
Ta ce “madina ke ‘yar aljanna ce ki je ki xauna a gidanki, ki cigaba da hakuri Allah xai
jagorance ki.”
Na tashi na tafi gida ba tare dana fada mata komai ba. Haka sumayya ta xo ta dinga
tambaya ta abunda ke faruwa sai dai in yi kuka bana iya fada. Abba kaninta ma har
falona ya shigo yayi iya kokarinsa wajen bugun cikina don ya ji halin da nake ciki a
matsayinsa na lawyer ya bi duk wata hanya da dabaru na jin labari shima daya takura
min sai nayi ta kuka ba shiri ya fice ya kyale ni.
Na dauki tasi’u tamkar rabin jikina na nunawa jama’a tasi’u shine rayuwata ina jin
kunyar ace ya watsa min kasa a ido, kunya nake ji ace baya sona yanxu wata yake so.”
Madina ta shrce hawaye t ace “sai na shiga taka tsan-tsan don kada in batawa sa’ada rai
ta fadawa tasi’u shima ransa y abaci, sai na xama tamkar baiwarta a gidan komai ni
nake yi mata musamman data haihu nake kula da yaron ita tana can a nade a dakin miji
domin ni bani da kwanxa, akwai lokacinda tasi’u yayi wata biyar bai kirani dakinsa ba
balle ya shigo dakina sa’ada ce kadai matarsa a gida. Namiji kenan idan kika kalli sa’ada
kika kale ni sai ki rasa dalilinsa na son sa’ada, shi da yake da mace kamata a matsayinki
na mace ba namiji ba ma sai kice me xai yi da sa’ada baka kirin, xololuwa mai kama da
tabarya ko dan kyawun fuska ma bata dashi amma it ace mace ni kuma bora.”
Madina ta rushe da kuka yayin da kaltum take tayata. Madina ta daga idanuwanta ta
dubi sama.
Ta ce “Allah kana ganin halindana shiga ada da wanda na ke ciki yanxu. Kaltum ba xaki
gane wasu abubuwa da nake fada miki ba saboda baki yi aure ba, baki san rayuwar aure
ba, haka gidanku ba mata biyu ba ne balle kisan ma nene kishi da kishiya.”
Ni da ‘yayana mun xama tamkar bayi, ni ban huta ba suma basu sake a gidan ubansu
ba. Kaltum, bari in takaice miki tasi’u saida ya sake sakina akan yarinyar nan sa’ada, shi
kuma akan abinci ne. ranar girkinta ya bata naira dubu biyu tayi cefanen rana dana dare.
Sai ya tafi kasuwa, ita kuma a ranar xata je gidan suna dan haka ta kwada mana gayan
tuwo na jiya da mai da yaji tace abincin ranarmu ne ni da ‘ya’yana ta shirya tayi tafiyar
ta. Saboda muna jin yunwa haka muka ci nace suyi hakuri xata xo ta dafa mana da dare.
Da ta dawo da daddare sai ta shigo da kwano dauke da alala dauri uku ashe mijinta ta
daukowa abincin darensa mu banda mu kuma ko sisi bani dashi balle in siya mana abinci
ko in yi cefane in dafa mana mu ci ga uwa-uba ina gudun bacin rai dan haka ko farar
shinkafa ban dafa mana ba.
Mijinta ya dawo suka shiga daki suna ci suna hira suna shewa har karfe goma na dare.
Abdul malik yana xaune a daki yana min juye juyen ulcer sa na kokarin tashi saboda
yunwa haka shahida ma kukan yunwa take yi. Na tashi na nufi dakin tasi’u, bayan na yi
musu sallama suka bani ixinin shiga, na shiga sannan na durkusa na gaishe shi. Na ce
dan Allah ya bani naira dari daya in siyawa yara biredi yunwa muke ji. Ya tambaye ni
cike da mamaki y ace ba’ayi abinci bane?
Na ce ai gidan suna sa’ada ta je shiyasa bata yi girki ba.
Sai sa’ada ta hau fada da gatsine gatsine tana min rashin kunya wai ina yawan hada
mata gulma, dan haka in fita daga idonta ta rufe. Ya ce in tashi inje dakina yana xuwa
yanxu. Na tashi na fice xuciyata na tsananin kuna da radadin bacin rai, sai naji jiri ya
dauke ni ina kokarin faduwa a kofar dakin nan da nan na sulale na xauna saboda na san
idan na ci gaba da tafiya faduwa xanyi hawan jinni ne dani ya hadu da yunwa. Sai na ji
yana ce mata “karki damu kishi ne yake damun madina saboda taga na fi son ki shiyasa
take so ta hada mu, kin san rabon da wani abu ya hada ni da ita an doshi wata takwas
bana ma kusantar ta.” Sa’ada tayi shewa ta tafa hannu tayi girgixa taji dadi.
Sai na tuno soyayyarmu da tasi’u a da, na tuna yadda na xama haka a wajensa sai na
rushe da kuka in tashi ma tsaye ya gagare ni saboda jikina ya mutu. Sai gasu sun fito sai
suka yi cikibis da ni a bakin kofa, ya dube ni a sheleke.
Ya ce “kukan me kike yi?
Bana son munafunci ba ni n ace ki je dakinki ki jira niba meye abin xama a nan? ”
Na share hwaye n ace “tasi’u me nayi maka a duniya ka tsanani?
Me nake yi maka yanxu wanda a da bana yi maka yanxu, dan in sani in daina. Tasi’u
yanxu baka tausayina ashe, baka nadamar abinda kake yi min ashe?
Na ji kana fada mata baka sona shi yasa baka kula ni ya dace ka fadawa kishiyata haka
alhalin ina yi mata boye-boye bana bari ta fahimci halin da nake ciki. Ka daina yi min
haka tasi’u nima matarka ce, ni mai sonka ce, har abada ba xan fasa sonka ba kome
xaka yi min. tasi’u na yafe maka, tsakani na da kai sai addu’a ta alkhairi domin bana so
Allah Y tashe ka da shanyayyen bari jiki ranar gobe kiyama saboda rashin adalci a
tsakanin matanka don ana xalunta ta.”
Da alama jikinsa yayi sanyi da farko, saida sa’ada ta kama shi da fada ta inda ta shiga
bata nan take fita ba, t ace wai ya tsaya yana kallona bayan labe nake yi musu kullum
daman ta sha ganina ina yi musu labe ina jiyo duk abunda suke fada. Tasi’u ya kama ni
da fada akan me yasa nake yi musu lae?
Na ce ba labe nake yi musu ba, jiri ne ya dauke ni na ji xan fadi sai na xauna a kofar
daki. Sai ya shiga daki y rubuto min takardar saki daya, kinga ya xama saki biyu kenan
yayi min.
Na karbi takardar na dauki gyalena na fita ban yiwa ‘ya’yana bayani ba. Ina fita nahau
acaba na tafi korau road gidan sumayya kawata na iske tana call a asibiti sai mai gidanta
dr basher da yaransu biyu mami da Khalid sunan mommy hafsa da daddy tukur ne aka
saka musu, sai a wajensa na karbi kudi na biya dan acaban daya kawo ni. Na ce masa
bani da lafiya ne na xo ta duba ni, ina tunanin jinina ne yahau. Ya dauko abun auna jinni
ya auna, yana auna ni kuwa sai ya girgice ya kwashe ni a motarsa ya kai ni asibitin su,
da yake sun bude asibiti nasu na kansu shi da matarsa a lamido cresent.
Allah sarki madina ko me ya sameta oho.
Se a biyo mu dan jin yadda data kasance.
.
Maza wasu da sanin su wasu ba da sanin su ba, abun da mata yasa suka tsani kishia
kenan, inda maza zasu na adalci tsakanin matan su da mata sun so kishia sun dauke ta
abokiyar xama, shi yasa ni dan aunty bana ganin laipin mata akan rashin son kishia,
kuma duk wata matsalar dake kai kawo cikin gida tsakanin mata na miji shine ummul
kaba'isin sa, dan duk na mijin da bai budewa mace kopar iskanci ba a cikin gida bata isa
tayi ba, idan ta para ya dakatar da ita ya nuna mata duk matan sane su ai baza ta sake
ba, amma akwai wanda ake musu pin karpi da asiri basu san su nayi ba.
Nuna banbanci tsakanin su shine babban abun dake haipar da rashin zaman lapia.
.
Allah Ya tsare mu da mata marassa imani, Ya azurta mu da salihai na gari, kuma matan
Allah Ya albarkace ku da maza je na gari Ya kare ku da muguwar kishia Ya hada ku da ta
gari
ADON DAWA2 (P 13)
.
Sumayya tukur ta bani gado na kwanta ta ci gaba da kula da ni, ta fara shawarar neman
number tasi ‘u a waya xata shaida masa halin da nake ciki sai na hana ta, nace ko mami
hafsa bata san na xo ba kuma bana so ta sani. Na dauko takardar saki na nuna mata, ta
yi matukar raxana hadi da gigita tayi ta salati sannan ta ci gaba da bani hakuri tana
gargadina da cire son tasi’ u raina kada ya kashe ni a banxa.
Saida na shafe kwanaki biyar a asibiti, sai da suka tabbatar nayi ras sannan muka koma
gidanta na xauna bana sakewa a giban ina ganin kamar ina takura musu gobia- gobia da
ni na wuce xaman gaban wasu. Sai na yanke shawarar in koma gidana in xauna tunda
ban san kowa ba sai Tasi’ u. sumayya ta hana ni ta ce sai dai ta kira mami Hafsa a sanar
mata halin da nake ciki sai ta xo ta dauke ni ta mayar da ni maimakon ace da kaina na
koma don yin haka xai sake kawo raini da gore-gore a wajen kishiya .
Haka aka yi, mami hafsa da kanta ta dauko ni daga gidan sumayya ta shiga da ni har
falon tasi’ u muka iske shi a xaune shi da matarsa. Ta yi masa fada sosai hade da
gargadi da wa ‘axi mai ratsa jiki akan ya ji tsoron Allah saboda idan bai yi wasa ba
hakkina xai kai shi wuta
Sai sa’da ta hau botsare-botsare tana kokarin yiwa mami hafsa fitsara wai an kori mutum
ba xuciya dan naci an dawo da ita. To ita baxa ta xauna da niba in har xan dawo in
xauna in ci gaba da xama a gidan ni kadai ita xata wuce, a take ta dauki gyalenta ta fice
tabar ‘ya’yanta guda biyu kanana, wannan lokacin tasi’u bai bi bayanta ba washe gari ya
aika mata da takardar ta ya sake ta saki daya. Ai kuwa wannan saki ya girgixa ta, yayi
musu ciwo ita da danginta gaba daya.
Sa’ada ta shiga damuwa dan bata taba xaton xai iya ya mata haka ba saboda yadda
taga yana tattalinta kamar gwal. Tana takama da asiri, asirinta ba xai bari a saketa ba,
dan abinda ta dogara dashi kenan.
Kaltum t ace “wannan rayuwa akwai wahala sai ki kayi xamanki ke kadai a gidan,
hankalinki a kwance ko? ”
Madina tace “na sami sauki dai kadan saboda tasi’u kwata –kwata ya canxa, hankalinsa
baya wajena baya raga min, baya sona, ya xama mutum mai mako ko abincin
wadatacce baya bamu ni da ‘ya’yana ga kananan ‘ya’yan sa’ada da nake rikewa. Daga
nan ma ya sake sabon aure, ni din ce dai ba xa xauna da ni kadai ba.
Ya auro wata baxawara ta girme ni tama gama haife haifenta a wasu gidajen bama a
gida daya ba. Sunanta hajiya talatuwa, ita ma jahila ce ba arabi ba boko, gata katuwar
gaske ce xama da kyar tashi da kyar, fuskarta a cike da tsage suffer mata ‘yan duniya
dai, itama dai na rasa gane mai ya gani a jikinta, har gara sa’ada da yarinta a jikinta.
Itama ta shigo da nata salon iskancin, shima bai isa ba balle ni da ‘ya’yana a haka muka
shekara ana ta tafkawa. Bana kula ta sai dai addu’a ni ke Allah Y daidaita mu amma abu
yaci tura. Sai ma wata masifar ya kara lalubowa wai xai dawo da sa’ada gidan don haka
yasa na kwashe kujeruna na cusa su a daki daya. Ya toshe ya hade mata da falonsa, su
duka suna da daki bibbiyu ni kuwa daya jal amma ban damu ba, ina ta hakuri ina ta
addu’a Allah Ya ganar dashi, duka da haka bana nadamar aurensa da na yi saboda idan
na tuna daga inda na fito da yadda nake a da, na ci riba dana samu na musulunta kuma
ga ‘ya’yana nan hausawa musulmai sun sami ilimin dana boko yadda ya kamata.
Amma duk nacin nan nawa saida dole na fita a sanda yayi min saki uku, tasi’u ya yi min
karya wai dukkanmu ukun mu tafi gidajen mu ya gaji da rigima ya miko min takardar
saki. Ya ce min suma sauran ya basu takardar saki. Suka hau shirye shiryensu a jaka
suka fice ashe dana tafi sun dawo gidan ni din ce dai yake so ya saki shine suka hada
baki aka kore ni.
Tun sakin yana bani tsoro har ya daina, saboda nasan Allah Shi ne gatan bawa. Tasi’u
bai isa yayi min arxiki ba, bai isa ya yaye min maraici da talauci ba, xuciyata ta
kyankyashe tunda yayi min saki biyu ban yi masa komai ba sai na sadakar nasa a raina
xai karasa ukun daman. Sannan na ji bana sonsa saboda yana cusguna min na xabi gara
in xauna lafiya da in cusa takaicin da namiji a raina ya janyo min ciwo a banxa, ba kula ni
xai yi ba hankalinsa na wajen matansa in ji da hawan jinin da na hadu dashi akan sa’ada.
Na shirya kayan sawata tsab a jakuna da akwatina, ‘ya’yana suka taya ni diba na shiga
gidan general tukur domin sune uwata, su ne ubana bani da inda xanje.
Wannan rana itace ranar farko dana xaunar dasu duka na basu labarina naci sa’a kuwa
duk suna gida. Daddy da mami hafsa, sumayya da mjinta sun xo su ma haka abba ya xo
gida daga inda yake bautar kasa. Kannensa na gida. Ga ‘ya’yana nan gaba daya su ukun
suna tare da ni, na fayyace musu tarihin rayuwata tun daga ranar da aka haifeni har
ranar da tasi’u ya sake ni saki uku.
Hankalin dukkanninsu ya tashi matuka babu wanda bai xubar min da hawaye ba
musamman ‘yayana sun gigita da suka ji tarihina koda wasa basu taba sani ba. Don su a
tunaninsu mami hafsat ‘yan uwana ne na jini saboda yadda suka taso suka ga yadda
muke yi dasu.”
Kaltum tace “a lokacin ‘yayanki sun yi wayo kenan har sun san ciwon Magana? !”
madina tace “shekara guda ken an da yin abun ba’a dade ba sosai ba, sun girma mana
har sun girme ki yanxu. Abdul malik, shekarunsa goma sha bakwai yana kokarin shiga
jami’a, Abdul hakim ne yake dab da kammala secondary shekarunsa goma sha shida,
shahida ce take primary ita kuma shekarunta goma a duniya, su dukka sun yi hankali
sun san komai.
Daga karshe nayi musu ban kwana nace xan koma garinmu. Su duka suka hana ni,
shawara daya suka tsayar shine in yi xamana a gidan general tukur ga dakuna nan birjik
in xaba in darje duk inda yayi min, ko in kaura bangaren sumayya tunda tayi aure babu
kowa har yanxu. Falo ne kato da daki mai dauke da bandaki, ga dining area, nace bana
so in xame musu wahala tunda na girma ba xan ji dadin irin wannan xama ba.xan fi son
daddy ya taimaka ya samar min aiki a asibiti in kaura can gara in yi nisa da tasi’u domin
bana so mu dinga haduwa dashi ko da matansa idan ina ganinsu fami ne babba a
xuciyata don xan dinga tuna abubuwan da suka yi min a rayuwata. Sannan idan ina kusa
xasu dinga batawa ‘ya’yana don in ji haushi amma idan bana unguwar koma bana garin
xan fi jin dadi da sakewa, hankalina xai fi kwanciya.
Suka gamsu da bayanina, daddy ya bani goyon baya akan bukatuna sai dai yace bai san
kowa ba a bangaren health a kano amma a jigawa yana da abokai a bangaren health,
nan da nan na amsa masa ina so a jigawar na ma fi son haka, ya karbi takarduna yace in
saurare shi. Tsawon watanni biyu cur ina xaman jiran aiki amma tamkar a daure nake
Allah-Allah nake in samu aiki in bar unguwar. Kinga kuwa abunda nake gudu saida ya
afku, tasi’u ya hana ‘ya’yana xuwa wajena duk san da suka shigo sai an fada masa ya
dake su musammam karamar ba xata iya daurewa ba sai ta shigo sai dai ya kashe ta.
Haka suma kishiyoyi na ina samun sakonnin bakaken maganganunsu musamman daga
sa’ada. Sannan na kan jiyo muryar tasi’u daga dakin da nake shima babban bacin rai ne
domin na tsane shi bana son ganinsa.
Aka kira ni interbiew a dutse na ji nayi, abunka da hanya ba’a dade ba aka bani offer an
dauke ni aiki sai dai kaxaure suka tura ni. Naji dadi nan da nan na hada kayana daddy
yasa direbansa ya kaini kafin in tafi mami hafsa ta