Advertisements
Chapter 18 Reading adon dawa by Jamila Umar Tanko BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

adon dawa by Jamila Umar Tanko

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 46

51K to 54K   out of 137K words

nufo su a hankali suna Magana
cikin yarensu.
Kaltum tayi larabci tace “bama jin yarenku, kuyi mana larabci.”
Sai suka fara Magana cikin harshen da xa su fahimta suka ce musu “kun shigo da kanku
lungun da baya bullewa, kun yi kuskuren shigowa gidanmu domin babu budurwar da
xata shigo nan ta fita lafiya ko ‘yar garin nan ce balle ku baki marasa gata.”
Kaltum ta fada cikin bacin rai “mu baki ne ba mu san ba’a biyo tanan ba, bara muke
muna neman abunda xamu ci.”
Sai suka ce “to yanxu xamu baku abunda xaku ci amma fa sai mun gama da ku.”
Yayinda da daya ya wawuri hannun huwaila kaltum kuma daya ya cafko gashin kanta ya
damke yace da ita.
“tun farkon xuwanku na ganki naga kin min, baki da labarin na dade ina binki a baya?
Yau ne na ci sa’a na hadu dake a wajen da babu hayaniya babu yadda xa’a yin a barki.”
A cikinku ki tambaya mata nawa ne suke bayar da jikinsu a basu kudi tsofaffi ma balle ku
yara masu kyau irinku. Me xai ragu a jikinku idan an taba ki, ki samu kudinki hankalinki
kwance. Sai kaltum ta hasala ta hau fuffuka tana fisge-fisge xata kawace, ya bankare
wuyanta yana kokarin kai ta kasa, yayinda dayan tuni ya durkusar da huwaila kasa.
Kaltum ta laluba ta ciro wukarta daga cikin rigarta kan kace kwabo ta danna gefen wukar
kaifin ya fito fet ka ke ji ta sharba masa a hannu ba shiri ya ske ta ya daka tsalle gefe ya
rike hannu yana ihu jini yayi masa face-face a hannu. Kaltum ta sake bude jakar dake
makale a hannunta ta xaro wata katuwar kwalbar lemo ta rusa a jikin bango ta fashe rabi
ya rugurguje sai ta rike rabin a hannunta ta nufi dayan da yake rike da huwaila, shima a
guje ya sake ta suka xabura suka fara ja da baya.
Kaltum ta fada cikin kakkausar murya tace ‘xan kashe duk wanda ya tabo mu, sai na
farka cikin duk wanda ya nufo ni.”
Tana xare ido tana nufo su, sai suka tabbatar da gaske take farka cikinsu xata yi dan
haka sai suka juya a guje suka fita daga lungun. Kaltum da huwaila suka arta da gudu
suka kama gabansu suma. Mamaki ya kama huwaila akan abunda kaltum tayi tana
matukar mamakin yadda kaltum ta tanadi irin wadannan mugayen makamai a jikinta.
Huwaila taje ta dinga yada kaltum a cikin gida cewar a yi hankali da yin fada da kaltum
domin cewar wukake ne da kwalabe a jikinta da xarar fada ya hada ta da mutum xata
farka shi da wuka.
Su ka tabbatar kaltum ta xama ‘yar daba yayin da ‘yan gari ma suke kiranta da ‘yar
agulla, wato ‘yar daba saboda har ‘yan iskan gari sun gane ta. Ta ketawa samari da
dama hannu ta fasa wa jama’a da dama kwalba akai sai dai idan ba’a rutsa taba a lungu
ana kokarin a cimmata ba yanxu ne xata yaga fatar mutum.
BABI NA TAKWAS
Yau kaltum ‘yar agulla ta dira a bakin kogi a inda masu kamun kifi suke ta damko
manya-manyan kifaye wanda girmansu xai kai girman yaro dan kimanin shekaru fiye da
bakwai. Ta tsaya tana jiran abokinta mai suna karim ya fito daga ruwa ya bata kasonta
daman ya saba bata kullum sai ta je gida ta gasa su ci.
Karim saurayi ne wanda shekarunsa bai wuce ashirin da biyu ba, dan asalin garin
katagun ne a jahar bauchi a kasar Nigeria. Amma bai san kowa a garinsu ba kasancewar
iyayensa sun taho dashi sudan tun yana da shekara daya kamar yadda aka bashi tarihin
cewa mahaifinsa ya tsaya a n’djamena da niyyar neman kudi sai ya turo karim da
mahaifiyarsa su xo sudan su jira shi idan yayi aiki ya samu kudi sai ya same su a sudan
su haura saudiya. Tundaga lokacin basu kara haduwa ba, bai xo ba, ana kyautata xaton
a n’dajsmena ya rasu yayin da itama mahaifiyarsa Allah yayi mata rasuwa ta barshi shi
kadai dan kankanin yaro a hannun wani tsoho abokin tafiyarsu mai suna baba lado.
Karim na xaune shi da tsohon a bur sudan a dakin katako, kwali kadai a shinfide a dakin
har ya girma ya fara sana’arsa ta kamun kifi yana sayarwa, a halin yanxu tsohon ya rasu
dan haka karim shi ne uwa shine uban kansa.
Ya hadu da kaltum jininsu ya hadu yana farin ciki da ganinta sai ya ga kamar yaga
kanwarsa musamman idan ya ji tana yi masa hausa. Da yake babu kalma daya ta
soyayya da ke tsakaninsu ita da karim sai ta saki jiki dashi su kayi ta labari haka kuma
yana matukar taimaka mata da manyan kifaye gasassu ko danye, ko ma ya bata kudi
idan ya sayar ya samu.
Karim yana fitowa daga ruwa sai ya kalli kaltum yayi dariya, itama ta yi masa murmushi
cikin harshen hausa take yi masa Magana tace yayana, yau ragon ruwa xaka bani, katon
kifi me tsoka. Sai yayi dariya yayi Magana cikin harshen hausa duk da hausar bata fita
sosai, yace yau kifin duk manya ne, ki xabi duk wanda kike so.
Kafin karim ya rufe bakinsa sai ya ji wani mummunan duka a kuncinsa har saida ya
tuntsura ya fadi kasa. Kaltum da karim suka daga ido lokaci daya suka duba bangaren da
dukan ya fito. Sai ga mambela a tsaye ransa a bace mamaki da tsoro gami da fargaba ya
rufe xuciyoyin su. Mambela ya sake cacubo karim ya nika da kasa yana shirin hawa
ruwan cikinsa da duka, sai kaltum ta yi kukan kura ta xaro wukarta ta yanka mambela a
kwairin kafarsa.
Mambeala ya xabura ya rike wajen yayin da karim ya yunkura ya mike tsaye da sauri
yana shafa kuncinsa suka yi jawur dan xafi. Mambela ya dago ya dubi kaltum yayin da
jini yake bulbulowa daga inda ta yanke shi.
Karim ya fada cikin harshen hausa “kaltum ki gudu kada mambela ya kama ki, wannan
mugu ne, ya addabi kowa a garin nan.” Kaltum tace “ba xan gudu ba sai dai ya kashe ni,
ka gudu kada ya kara dukan ka, ka bar ni dashi.”
Karim ya arta da gudu ya bar wajen ya tafi can nesa yana duban su, yana tsananin
fargabar kada mambela ya tashi ya shake kaltum . har yanxu mambela yana tsugunne
yayin da kaltum take tsaye kem a gafe da wukar ta a hannu ta rike kugu, babu alamar
tsoro a tare da ita. Mambela ya yago gefen ‘yar sharar rigarsa ya daure kafarsa wajen
ciwon sannan ya dago ya dubeta yayi murmushi ya fada cikin harshen larabci yace “yar
agulla, kin cika ‘yar agulla, yau na tabbatar ke ‘yar agulla ce. Kin yanki abokaina da
yawa yau yankan naki kaina ya dawo kuma, kin yanke ni har jini ya xuba a kasa.”
Sai ya tuntsure da dariya mai fitar da sauti mai kara ya gyada kai y ace “ni mambela, ni
ne yau yarinya karama ta yanke ni a kafa, yarinyar ma bakuwa baiwarmu, almajira mai
bara. Tabbas baki sanni ba, baki samu mai xaunar dake ya baki labarina ba yadda ya
kamata daga nan har cikin gari babu mai taba ni ya kwana lafiya, babu mai yi min musu
duk duk abunda nace dai dai ne. ‘yan jange masu barka cikin mtum da wuka, masu fada
da kwalba suna tsoron mambela domin ni aka fi sani da yanka. Babana ya fi kowa kudi
ya mallaka min gidaje kala kala a kartum bayan na wasu manyan burane a sudan, babu
abinda na nema na rasa sai ke, a kanki baxan fara ba dole sai kin amince. Ina biye da ke
a duk inda kika saka kafarki, ina ganin mu’amalarki da jama’a sai naga kin fi hulda da
wancan tsintaccen yaron karim marar gata, da alama kin damu dashi don haka sai na
raba shi da hannunsa ko kafarsa kacukan yadda ba xai sake moruwa ba.”
Kaltum ta fusata ta fara Magana cikin fushi muryarta sama sama tana nuna shi da hannu
tace “mambela karya kake yi, baka isa ka ce xaka raba ni da karim ba saboda karim dan
uwana ne kasarmu daya, karim ne mai taimako na yana ba ni abinci. Ka sani duk sanda
ka taba karim ka yanke shi, ni kuma sai na barka cikinka hanjin ka ya fito waje sai dai
nima a kashe ni.”
Ya mike tsaye ya na murmushi yace “na yarda xaki aikata abunda yafi haka ‘yar agulla
na tafi sai haduwarmu ta biyu, sai dai ina so ki sani baki isa ki kula wani ba idan ba niba,
saboda ina sonki kuma baxan rabu da ke ba.”
Ta Harare shi ta ce “ bana sonka, na tsane ka kuma har abada ba xan so ka ba.”
Ya juya ya tafi a fusace yana dingishi, ta xaro tsumma daga jikin xaninta ta goge jinin da
yake jikin wukar ta like ta mayar cikin rigarta ta adana.
Karim ya taho da gudu inda kaltum take tsaye yana ta mamakin karfin hali irin nata,
tambayarta yake, “daman kin san mambela, ya aka yi mambela ya sanki har kika yanke
shi da wuka bai dauki mataki ba? ”
Kaltum ta ci gaba da ciccibar kifinta ta nufi gida ba tare da ta bashi amsa ba.
Bayan anyi haka da kwana uku misalin karfe goma sha daya na safe, karim na wajen
sana’arsa ta kamun kifi sai yaga mambela a tsaye a kansa yayin da mambela ya jawo
hannunsa ya fito dashi daga cikin ruwan, kan kace kwabo hantar cikin karim tadau rawa
cikin yaren ‘yan ADON DAWA yake bashi hakuri, yana tuba yana neman afuwa.
Mambela ya dukar dashi kasa yace “baka da labarin kaltum tawace?
Ba ka da labarin ni nake sonta kuma babu wanda ya isa ya so ta bayan ni, balle kai
bawana? ”
Karim ya daga kai yace “naga alamar haka mai gidana babu mai ja da kai, kaltum
kanwata ce kuma na yi alkawarin sai na sa ta so ka.”
Dadi ya lullube xuciyar mambela ya yi murmushi ya tashi karim tsaye, ya karkade masa
kasar da ke jikinsa.
Ya ce “ina son kaltum son da bashi da adadi, ina son ka sata ta so ni itama, idan ta ki
xan hukunta ka.”
Karim yayi murmushi yace “an gama mai gidana.” Mambela ya juya ya tafi, farin cikin
xuciyarsa ya nuna a fuskarsa kai ka ce kaltum din aka bashi kyauta. Mambela na juyawa
kaltum ta karaso inda karim yake a tsaye ta tsuke fuska ta tambaye shi “meye mambela
ya xo yi a nan, me yace maka? ”
Sai karim yayi dariyaya ce “mu xauna mu yi Magana kanwata kiji labarin abunda baki
sani ba.”
Kaltum ta cire sharbabben takalminta silifas wanda ya fi girman kafarta sau biyu gashi a
tsinke harta daure da leda. Ta xauna akai yayin da ta baxa wani katon siket dinta
burgujeje kore da wata riga t-shirt ruwan dorawa, dankwalinta kuwa ya hadu da
cikurkudadden gashinta ya dankare, ta dubi karim tace “ina sauraronka, me nene? ”
Ya durkusa a gaban kaltum sai fara’a yake tamkar gonar auduga yace “kaltum kin yi sa’a
da mambela yace yana sonki saboda kin wuce wulakanci, fatara da yunwa a garin nan.”
Kaltum ta ji kamar ya daba mata wuka a kahon xuciyar ta, ta ja dogon tsaki, ta fusata
xata mike. Karim ya mayar da ita ta koma ta xauna.
Ya ce “shawara nake baki, ki so shi saboda yana sonki. Meye laipin sa? Gashi kuma dan
gidan masu kudi da sarauta, gashi dogo kyakkyawa, laifinsa daya bashi da mutumci
shima sai idan ka tsokane shi, ada ne yayi shaye shaye yanxu ya daina.”
NI SADIN MAA ME TYPING NACE “DU KYAWUN MAMBELA, BE KAI BOSS INA DAN ANTY ME
POSTING BA, SANNAN KUMA GA CIKA, KAMALA, DA MUTUMCI, DAN ANTY SAI
TUBARKALLAH.
Kaltum ta ci gaba da hararar karim har saida ya gama tsara ta sannan tace “ka gama
tsara ni?
To ba xan so shi ba har abada, ni na tsani mambela da abokansa kamar yadda na tsani
mutuwata.”
Hankalin karim ya tashi yana tambayar ta “saboda me bakya sonsa, me ya miki?
Mambela yana da kirki idan Allah Ya tsaga da rabonka har kyautar saniya sai yayi maka
ko kudi mai yawa musamman a lokacin axumi yana da rikon addini kuma.
Kaltum ta fusata ta mike ta ce “ban sani ba, ka je ka tambayi mambela me yayi min shi
da abokansa ba ni xaka tambaya ba . kai ma tunda bakinku daya dashi na daina kula ka
ba xaka kara ganina a wajenka ba.”
To masu karatu.
Kaltum data yarda da tayin mambela kuwa,?
ya data kasancewa karim idan har kaltum ta ki amincewa mambela?
Domin jin duk amsoshin wa’ennan tambayoyin se ku ci gaba da hakuri da biyo mu.
Mune na ku har kullum masu son dasa nishadi a xukatanku.
ADON DAWA 2 (P 17)
.
Ta juya ta tafi a fusace yayin da karim ya bi ta da gudu yana bata hakuri, ta ki
sauraransa, yayi yayi ma ta xo ta karbi kifi tace bata so.
A lokacin dasu kaltum suka cika shekara guda a bur sudan, a lokacin kasar ta fara yi
musu dadi dukkaninsu. Saboda da yawancinsu sun sami jari sun fara sana’a sun daina
bara, wasu matan suna sayar da kosai, wasu na yin koko, wata waina, wata awara. Wani
na dafa shayi da biredi, wani na sayar da rake, wani yayi ‘yar tireda yana sayar da
sabulu, omo man shafawa, makilin da brush da dai sauransu. Kofar gidan su kaltum ta
xama kamar ‘yar kasuwa ana ta saye da sayarwa. Jange suna xuwa su saya, haka ADON
DAWA ma suna xuwa su saya.
Madina ta sami sana’a itama ta daina bara, kosai take toyawa da safe, sai ta sayar da
tuwo da daddare. Kaltum ceke tayata wajen xubawa da mikawa da yin wanke wanke.
Bayan wannan babu wani abu da kaltum take yi amma komai baya gagararta kyauta ake
bata saboda sabon da tayi da jama’a kowa yana sonta.
Kaltum ta manta rabon da ta sayi ruwa da kanta saboda alkwari ne kullum tsohon nan
mai sayar da ruwa akan jaki sai ya bata jarka daya ko biyu kyauta. Haka ko ta je bakin
kogi ko bata je ba sai karim ya kawo mata katon kifi guda daya ko biyu danye ko
gasashshe kyauta, haka wani Muhammad mai sayar da nono akan jaki yake tsiyayo
mata nono kyauta, ga makudan kudi da mambela yake cusa mata amma bata taba
karba da hannunta ba sai dai ya bawa karim yayi mata dabara ya bata ba tare da tasan
kudin mambela bane ta karba ta kashe, ko mambela ya bawa madina ta saya mata wani
abun ba tare da ta san mambela ne ya saya mata ba. Duk wanda ke karkarar nan ya san
mambela yana son kaltum so na hakika yayin da kowa ya shaida kaltum ta tsane shi, ta
tsani ta hada ido dashi, ta tsani ta hada ido dashi a duniya.
Madina ta san komai ma’ana tasan abunda ke gudana tsakanin kaltum da mambela
amma ta xuba mata ido bata taba furta mata wata Magana wacce ta shafi mambela ba
haka itama kaltum bata yiwa Madina maganar sa ba.
A lokacin da suka cika shekara guda ne ake sake kawo wasu baki wadanda suka taho
mota guda suma sun fi su dari uku daga Nigeria ‘yan kasar sokoto ne wasu kuma daga
kano da jigawa. Wasu matan da goyonsu, wasu da ciki haka wasu ‘yan mata ne, ga
manyan maxa, samari da tsofaffi amma da aka tashi tafiya makka sai aka dauki kalilan
aka hayar dasu yayinda aka bar jifgi guda suna ta koke kokensu. Su kaltum suka yi
dariya suka ce dasu “xa ku saba kamar yadda muka saba har muke jin dadin xama muka
fi son xama a nan damu je makka ko mu koma Nigeria.
Don haka dakuna duk a ciccike suke a kalla mutum ashirin ne yanxu a daki daya, saboda
bakin da suka karo. A tattakure ake xaman yayin da hayaniya ta karu. Fada da dambace-
dambace suka dadu musamman a wajen shiga ban daki guda daya ne jal gidan mata da
maxa. Abun dai ba tsari saboda cudanyar da ake yi maxa da mata sai kaga wannan ba
riga, wancan da gajeren wando xai shiga wanka, sai kaji fada ya kaure da xage-xage
idan namiji ya kalli mace ko ya leka ta tana wanka sai kaji xage-xage.
Aure yana ta wakana a tsakaninsu sai kaji wancan da wancan ana soyayya, sai ka ji
tsoho da tsohuwa sun kulla soyayya, ko saurayi da budurwa suna soyayya, sai ka ji
baxawara da baxawari suna son juna don haka ko da yaushe su kaltum suna cikin biki
suna cashewa. Sai su aro janereto su jona rediyo a tsakar gida a saka kidan wakokin
hausa na ‘yan fim ko na ‘yan Niger su cashi rawa mata da maxa.
Don haka kofar gida an sake kakkafa runfuna katako duk wanda yayi aure sai ya buga
nasa dakin a ci gaba da xaman aure. Wadannan tudun kabararrukan nan da suke a cikin
dakuna da tsakar gida, da wadanda suke a kofar gida duk sun barbaje saboda dudufniyar
da ake yi akansu.
Auratayya da suke kullawa a tsakaninsu ba laifi bane an bi yadda shari’a ta tsara a yi.
Inda barnar take wasu matan aure ne sun baro maxansu a can Nigeria sai su ce ruwa ya
raba auren saisu yi sabon aurensu kwamacala kenan, masu ilimin cikinsu irin su madina
suna kokarin wa’axantar dasu suna wayar da kan mata masu irin wannan hali dasu daina
saboda kada fushin Allah Ya kama su, duk macen da ta san tana da aure ta boye ta auri
wani amma a banxa.
A yau ma wata mace mai suna talle ‘yar garin mata maye ce a janhuriyar niger,ta yi aure
da wani basakkwace mai suna balarabe. Talle ta xo ta yayyayen danta sai ta boye ta ce
bata da aure ta auri balarabe bayan bikin da watanni hudu sai ya saketa saki uku da ciki
wata hudu. Ta dinga ihu a kofar gida tana burgima tana kuka tana kiran ta shiga uku
yaya xata yi da ranta ta baro mijinta a niger, gashi ta yi aure akan aure harta sami ciki
kuma ya sake ta idan ta koma kasarsu ina xata ceta samo da?
Kowa ya dinga yi mata Allah wadai, tur da halinta.
Sai ‘yan matan da ake batawa a junansu a yiwa wasu cikin shege, wasu matan kuma
waje suke xuwa a basu kudi a yi musu lalata su sami ciki su haife. Irin wannan muguwar
kaddarar ceta fada kan rakiya jikar mairo, arnen jange ya yaudare ta yayi mata ciki, ita
da kakarta suka yi ta kuka suka rasa inda xasu saka ransu. Idan sun je asibiti ma babu
mai kallonsu saboda bada ixinin kasar suke xaune ba. Wannan abun takaici yana damun
masu hankalin cikinsu irin su madina, itama maxa da dama daga cikinsu ko ‘yan kasar
suna nuna suna sonta da aure ta ki yarda fur. Ta yi kicin-kicin ta rufe ido tace kada ma
su fara tana da mijinta a Nigeria ba xata ci amana ba. Haka madina ta sakawa kaltum
takunkumi da tsaro gami da sa ido a duk shige da ficen ta, tana yawan

18 / 46