Author : Jamila Umar Tanko Category : Complete Novels
annurin fuskarta ya gushe sai ta fara murgude-murguden baki
tana Harare-harare.
Ya fada cikin lallausar murya “kaltum yau ranar farin ciki ne, ranar da kowannenmu yake
cikin nishadi. Me yasa ranki ya baci daga ganina alhali ni mai kaunar ki ne, mai son
ganinki a cikin farin ciki.”
Kaltum ta yi sauri ta dubi huwaila dake xaune a dayan gefen nata sai taga huwaila bata
ma ga mambela ba, tana kallon rawa. Ta sake daga kai ta dubi jama’ar dake tsaitsaye a
kansu sai taga kowa sha’anin gabansa yake yi, hayaniya ce kadai ke tashi baya ga sautin
kida da wake wake.
Sai ta juya ta dubi mambela duba na takaici, ta cije baki alamar xata keta masa rashin
mutumci, tana so ta tabbatar masa ita ‘yar agulla ce sai ta saka hannu a riga kan kace
kwabo ta ciro ‘yar wukarta ta danna gefe sai tsinin wukar ya fito, nan da nan mambela
ya ja gefe yayi tsuru yana dubanta.
Ta fada cike da bashi tabbaci tace “ka matsa daga kusa da ni in ba haka ba xan jinyata
ka. Mambela, na tsane ka, na tsani wanda yake sonka saboda kai macuci ne axxalumi.”
Takaici bayyananne xaka hango daga idanuwan mambela, ya dade a tsugunne yana
dubanta can ya mike ya tafi da alama ransa y abaci. Biki yayi biki mata da maxa, yara da
manya sun cakuda sai rawa ake ana juyi dan haka su kaltum sun sami dammar shiga fili
sun cashe suma saida magaruba ta yi waje yayi duhu har baka iya shaida na kusa da kai
sannan suka fara shirin watsewa. ‘yan mata irin su kaltum ne aka sa su tattaro farantai
da cokulan da aka yi ciye ciye, su biyar ne suka rage a filin suna faman tattare kaya
dakyar suke iya gano farantan saboda duhu.
Kaltum na tsugunne ita kadai tana jera farantan roba akan babban faranti tana shirin
mikewa ta dora a kai ta tafi gida yayinda sauran ‘yan matan hudu har sun dora nasu aka
sun yi gaba. Sai ta ji kamar an jeho wani abu gabanta da karfi, sai ta yi sauri ta duba
kasa inda abun ya fadi, sai taga kafar mutum ce nan ta raxana ta fadi xaune dabas tana
karkarwa. Ta daga ido da sauri sai taga dogon mutum ne a tsaye duk ilahirin jikinsa a
rufe da wani bakin mayafi.
Ta fada a tsorace “waye kai, me kake nema a waje na? ”
Ya ce “mambela ne, soyayyarki nake nema.”
Sai ta mike a fusace tana shirin barin wajen cikin gaggawa, ya shiga gabanta ya hanata
wucewa, kan kace tak harta xaro ‘yar wukar ta, ta keta masa a dantsan hannunsa,
saboda tsananin kaifin wukar har saida ta tsaga mayafin ta shiga namansa. Yayi kara ya
tsugunna ya rike wajen yayin daya dangwalo jini jajawur a hannunsa ya haska da fitilar
da ke hannunsa sai yaga jini ne. har yanxu kaltum tana tsaye a kansa da wuka a
hannunta jira take ya mike ya mike ya tabata ta sake yankarsa tana tsoran juya baya
kada ya cafko ta. A halin yanxu xuciyarta ta kekashe take, ji take a ranta ko aljani ma
idan xai fito fili saisu fafata balle bil adama dan uwanta. Bata jin tsoran kowa kuma bata
shakkar fada da kowa sai dai ita bata neman fada amma muddin aka tabata xata yi wa
mutum illa ba tare da bata lokaci ba.
Ya dago ya dubeta ya haska fuskarta da fitila sai ya sake haska mata dantsan hannunsa
inda ta yanke shi, taga sharceccen yankan da tayi masa jini jage jage, bai ga alamar
nadama a fuskarta ba. Ta cije baki tana rawar jiki tamkar so take ta kara masa.
Ya tambaye ta cikin harshen larabci ya fada cikin wata lallausar murya yace “kaltum a
ganinki kinyi daidai da kika yanke ni da wuka?
A she dama soyayya laifi ce a wajenki, har ki ka nemi ki kashe ni don nace ina son ki? ”
Ta fada cikin kakkausar murya tace “bana sonka axxalumi.”
Ta juya baya a fusace xata tafi sai ta ji ya xo da gudu ya finciko ta sai kuwa ta sake kai
masa yanka wannan karon ma ta same shi a dan yatsa daya nan ma jini ya fito. Tana
shirin yankarsa a kirji sai ya rike hannunta da sauri ya murde da karfi ya kwace wukar
yayin daya warbar da ita gefe ta fadi akasa rim. Ya cafko gashin kanta ya hada da
lufayar da ta lullube kanta ya damke, inda ya kawo wukar saitin hancinta xuwa wuyanta.
Ya ce, “ke yarinya karama, duk irin wadannan ta’addancin mun yi mun daina yanxu naki
ma wasa ne idan kin ji labarin irin wanda muka yi.”
Ta hau fusge fusge amma ta kasa kwacewa. Ya ce “yau ni da ke kadai xamu kwana a
cikin duhun a bakin kogin nan, duk abunda xai cinye mu sai dai ya cinye mu idan kuma
ki ka yi kokarin guduwa sai na fusgo ki mun fada cikin ruwan nan mu mutu dukkan mu
kowa ya huta.”
Sannan ya saketa yayin da ta mike a fusace xata tafi a guje, bata san yadda aka yi ba
sai ta ji ta a kanannade a cikin mayafi an xargota ta fadi kasa sannan ta yi sauri ta yaye
mayafin daga fuskarta ta waiwaya mambela ta gani a tsaye a kanta ashe shine ya xargo
ta da mayafin.
Ta fada a fusace “wai kai me ka ke nema ne a wajena, me xan yi maka? ”
Mambela ya xauna a kusa da ita yana fuskantar ta yace “yau ni da ke babu mai raba mu
sai Allah, yau sai na fahimtar da ke ko ni wa nene kuma ko me yasa na kasa rabuwa da
ke. Yau sai kin bani tarihin rayuwarki, asalinki, daga inda kika fito da kuma dalilin
xuwarki kasar nan.”
Kaltum ta Harare shi, hakika ta kara jin tsanar mambela tace “bana bukatar in san ko kai
wa nene, kuma ba lallai ne kasan ko ni wa cece ba. Mambela na gane ka tuntuni so kake
ka bata min rayuwata, burinka ka yi min fyade tun bayau ba. To bari ka ji in fada maka
da wannan abu ya fara tsakanin mu gara ni da kai mu mutu ko kuma ni in kashe kaina,
kar ka ga ka kwace wukata ka xata ba xan iya halaka ka ba……”
Bata rufe bakinta ba mambela yayi sauri ya katse ta y ace “kaltum, mambela da ki ka
sani a da yanxu ba haka yake ba, haka kuma xargin da kike yi min ba haka ba ne a
xuciyata tun asali ma. Tabbas na san ba xaki yarda dani ba saboda tun farko abunda ya
faru a tsakaninmu duk da ba xaki yarda ba amma xan fada miki gaskiya. tun farkon
haduwarmu dake kallo daya nayi miki na ji haka kawai ina sonki, har cikin raina so na
gaskiya bada niyyar cuta ko yaudara ba. Ban yi Magana ba da farko sai abokai na suke
shawarta ta da suke kai min ke cikin shago, babu yadda xan yi dasu haka nan na amsa
musu amma nayi haka ne dan idan mun shiga shagon xaki tsaya ki saurare ni har na isar
miki da sakon xuciyata gare ki ashe na yi kuskure da na bari suka dauko min ke a ka.,
shi ya jawo kike min wannan tsanar. Madina ta sheda min cewar kin koma gida kina
firgita kina ambaton sunana wai xan kashe ki. Ta fada min kin sha jinya a sanadiyyar
yanka hannunki da kika yi da wuka. Ina rokarki dan Allah ki yafe min ki manta da wancan
abubuwanda suka faru tunda Ubangijina Allah Ya halicce ni ban taba haduwa da yarinyar
da nake so ba har cikin raina sai ke. Na yi iyakar kokarina wajen cire sonki abu ya
gagara, na kasa dainawa, kullum sai karuwa yake.
Wallahi kaltum bani da niyyar cutar dake, ban taba sha’awar yi miki fyade ba, tsoratar
dake nake yi kawai a haukata idan kika ji tsorona xaki so ni, na shaidawa abokaina
abunda yake xuciyata ko da xaki tambaye su xasu ce na fada musu bada gaske xasu
kamo ki ba tsorata kawai xasu yi saboda ina sonki na hakika. Dan baki sani ba ne na
bata da samarin garinmu da yawa, haka nayi ta fada da samarin jange masu shirin su
cuce ki, ko da yaushe ina biye dake duk inda kika shiga bana bari wani abu ya cuce ki sai
dai in ban ga giftawarki ba. Kaltum burina a kanki shine na aure ki, in fitar dake daga irin
wannan matsananciyar rayuwar da kuke ciki ta rashin galihu, sannan tun asali, duk
rashin ji na ban taba kusantar wata mace ba, balle ace na yi fyade.”
Ta dago da sauri ta dube shi duba mai tafe da mamaki hade da rashin fahimta. Ya gyada
kai yace “ban taba ganin matar da ina ganinta na ji a raina naga matar da xan aura ba
sai sanda na fara ganinki a duniya sai kawai na ji a jiki na ke kika dace da xama mata
ta.”
Kaltum ta mike tsaye ba tare da tace dashi komai ba, amma da alamar sanyin jiki da
kunya a tare da ita, mambela ma ya mike yana dubanta yana sauraron abunda xata fada
sai yaga ta fara tafiya a hankali yayin da yayi sauri ya nada gammo da mayafinsa ya
dauki farantin akansa yana biye da ita a baya.
Gari yayi duhu kirin babu kowa yana cikin gidansa sai kukan tsuntsaye da kwari kadai
kake ji saida suka isa kofar gidan su kaltum sannan suka hango hasken fitila da alama
akwai maxa kofar gidan wadanda suke xama suna hira. Sai ta ja burki ta tsaya ta yi shiru
tana tunanin me xasu xarga idan suka ganta da mambela a cikin daren nan babu mai
fitar da ita daga mugun sharrin da xa’a kulla mata ba. Ta dube shi ta sosa keya ta
sunkuyar da kai kasa.
Ta ce “ka bani farantin in shiga gida saboda bana son a ganmu tare a cikin daren nan.
“bai yi mata musu ba don ya fahimce ta sai kawai yayi sauri ya dora mata farantin a
kanta. Yayi murmushi ya fada cikin sanyayyar murya mai ratsa xuciyar masoya y ace
“nagode saida safe kaltum.”
Ba tare da ta waiwayo inda yake ba ta ce “Allah Ya kai mu mambela.” Ta ci gaba da
tafiya.
Mambela ya sankare a tsaye cikin duhu yana kallon kaltum har saida ta yinisa ya daina
hangota sannan ya motsa, saboda tsabar farin cikin daya hadu dashi a yau ya samu
kaltum ta tsaya ta saurare shi harta fara gamsuwa da bayanansa gashi ya samu ta amsa
sallamar da yayi mata. Bai damu da jini jage jagen da ya bata masa Kaya ba ya wuce
xuwa garinsu yana mai tsananin farin ciki.
Kaltum ta isa tana fargabar kada a tuhumeta da laifin dadewa amma sai ta iske kowa
yana sha’anin gabansa saboda hayaniyar biki ba a kwanta da wuri ba. A lokacin da
kaltum ta kwanta hakarkarinta ta lumshe ido sai ta fara hango hannun mambela dai-dai
inda ta yanke shi da wuka jinni yana xuba, sai ta firgita ta tashi xaune. Madina ta daga
kai ta dubeta sai ta tambaye ta ta ce “kaltum lafiya, bakya addu’a ko? ”
Kaltum ta tuna ashe bata yi addu’a ba sanda xata kwanta sai ta karanta addu’o’I ta
shafe jikinta ta koma ta kwanta.
Washe gari da safe mambela ya bayyana a kofar gidansu kaltum a lokacin da duk masu
sana’ar da abincin safe suka fara firfito da kayan dahuwarsu, shi kuma ya fara ware ido
yana neman abar kaunarsa kaltum amma bai ganta ba sai dai ya hango madina tana
kosai. Ya isa gareta yana mai yi mata sallama fuskartsa cike da fara’a. a halin yanxu
madina ma ta koyi larabci don haka suka fara yarawa, ya dade a tsugunne a gabanta
suna ‘yar hira amma yana jin kunyar ya tambaye ta kaltum harta lura da hakan.
Ta ce dashi kaxo duba jikin kaltum ne?
sai ya xabura cikin furgici y ace “bata da lafiya ne? ”
Ganin hankalinsa ya tashi sai ta yi sauri ta fara gyara xancen. Mambela ya girgixa kai ya
fada cikin damuwa.
Ya ce “anty kada ki boye min komai a game da kaltum, ta xama ni na xama ita
matsalarta tawace, ki fada min me yake damunta.”
Madina tayi shiru can tace “gaskiya kaltum ta hadu da ciwon aljanu xuwan mu garin nan
ba ita kadai ba jama’ar mu da yawa suna fama da wannan larura kasancewar muna
xaune ne a cikin makabarta,nan da nan saisu bugeta ta fadi.”
Mambela ya maimaita cike da mamaki “aljanu kamar yaya?
Daman ana ciwon aljanu? ”
Madina ta gyada kai tace “ana yi mambela .”
Ya ce “ciwon yana da magani, ana warke wa? ”
Ta gyada kai tace sosai kuwa ai kowanne ciwo yana da maganinsa kafin Allah Ya sauke
ciwo saida Ya saukar da maganinsa, da xa’a sami babban malami wanda ya haddace
Qur’ani xai iya maganinsu.”
Mambela ya mike da sauri ya nufi garinsu yayin da madina ta shiga juyayin ina xai je ne
daya tafi da sauri haka?
Tafiyarsa da kamar awa guda sai gashi ya dawo shi da wani mutum da alama mutumin
malamin addini ne a sanadiyar dogon carbin daya rike a hannunsa. Mambela ya kirawo
madina gefe ya sanar da ita ya taho da mai maganin cire aljanun don haka tayi musu iso
xuwa wajen kaltum. Ba tare da bata lokaci ba ta wuce gaba suka bi ta har cikin dakinsu,
hankalin mambela ya tashi daya ga muhallinsu, suka iske kaltum a kudindine akan kwali
rabin kanta a kasa cikin yashi tana barci mai kama da suma.
Malamin mai rukiya ya xaro wani dan gwabgwani ya bude, sannan ya lakuto wani mai
dan kadan ya lakutawa madina a yatsanta y ace ta samu ta cusawa kaltum a hanci. Jikin
madina na karkarwa ta je ta durkusa a kusa da kaltum ta kai yatsanta a hankali har kofar
hancinta sannan ta bursuna mata man a kofar hancin.
Kafin kace kwabo kaltum ta firgita ta mike xaune a gigice. Ta fara atishawa a jere a jere
sai malam ya fara yi mata tofi yayin da madina da mambela suka xagaye ta idan ta yi
kokarin yunkurawa xata tashi sai madina ta danne ta har malam ya fara karatu yana
daga murya da karfi. Kafin kiftawar ido da budewa hankalin kaltum ya tashi ta rasa inda
xata saka ranta tana ta buge buge da haure haure yayin da muryarta ta koma wata
murya wacce bata taba ba. Ta fara Magana cikin yaren larabci, ta dawo yaren ‘yan ADON
DAWA , ta mako yaren jange ta ci gaba da fulatanci, (TANA NEMAN DAN ANTY) ta hado
da hausa sannan ta juye indiyanci. Koma dai da wane yare take Magana abunda take
fada shine waisu aljanu ne a jikin kaltum suke xaune saboda ta kwanta akan gidansu
kuma ta tattaka musu yara shi yasa suka shige ta. Sannan suka kara da cewa akwai
wani mambela wanda yake yawan bata mata rai da xarar ya bata mata rai sai mu kuma
mu bugeta ta fadi, sun kara da cewa su suke hanata yin ibada don tana yawan kona su
da addu’o’I shi yasa yanxu suke daure bakinta bata son yin addu’a sosai.
Malam ya tuntube su yaya batun fita daga jikinta kuma!? Sai suka ce ai sun samu gidan
xama a jikinta baxa su fita ba. Nan fa aka fara dauki ba dadi tsakanin aljannu da malam
ya dinga kona su da ayar Allah yayinda suke ta ihu da bubbuge bubbuge. Wannan karon
saida jama’ar gidan suka kawo agaji wajen kaltum domin abun ya fi karfin madina da
mambela su kadai, don xubar da mutane take yi kasa.
Da axaba ta tsananta ga aljannun sai suka hau ihu suna bashi hakuri gami da daukan
alkawarin idan ya daina kona su xasu fita yanxu ba xa su kara dawowa jikinta ba. Sai
suka dinga ficewa daya bayan daya sai ga kaltum ta mike ras kamar ba ita bace a
kanannade ba daxu. Malam ya bawa madina magungunan da kaltum xata dinga sha da
na shafawa da kuma na hayaki. Ya kuma gargadi kaltum da ta dinga suturta jikinta ta
daina yawo ba dankwali, ta xama mai yawan karatun Qur’ani da yin addu’o’I musamman
a lokacin kwanciya barci ko shiga bandaki. Malam da mambela suka tafi suka bar kaltum
a xaune tayi tsuro-tsuro tana tunani ta rasa abubuwanda suke faruwa a tare da ita
domin duk abunda ta yi bata sani ba tun jiya da daddare da ta kwanta barci bata sake
sanin abunda ya faru da ita ba sai dai taga jama’a kewaye da ita ana rike da ita suna yi
mata sannu sannan ta tabbatar lallai bata da lafiya. Sannan ta yi matukar mamakin
yadda mambela ya shigo har dakinsu bayan bai taba shigowa ba.
Tafiyar mambela da malam ba dadewa sai ga mambela ya dawo dauke da jakar kalanxi
da kaskon turaren wuta, ya kawowa madina yace ta dinga yiwa kaltum turaren magani
sannan ya tafi. Can da yamma kuma sai gashi a wata mota tifa dauke da wasu manyan
kataye da wasu maxa guda hudu a kofar gidansu kaltum a kace ana sallama da madina
a kofar gida. Sai ta ji gabanta ya fadi ba shiri ta janyo mayafinta ta fito, mambela ta gani
cikin katuwar mota sai mamakin da take ji ya karu. Ya gaishe ta sannan suka kebe gefe
ya shaida mata ya xo da ma’aikata ne yana so a shinfide musu katako a kasan dakinsu
kasancewar ya ga kaltum daxu a kwance a kasan yashi shi yasa yak e so a buga katako
saisu daina kwana a cikin yashi madina tace to amma sai ta shawarci sauran ‘yan dakin
tunda basu biyu ba ne a dakin suna da yawa sun doshi su goma sha biyar. Mambela y
ace ta je ta tambaye su idan sun amince sai ma’aikatan su shiga su fara.
Madina ta shiga gida ta samu ‘yan dakin su ta shaida musu nan da nan suka amince
cikin farin ciki da xumudi suka dinga firfitar da kayansu waje madina ta riko kaltum
wacce har yanxu tana yawan bacci ta kaita dakin kusa dasu ta kwantar da ita bsannan ta
fita ta yiwa su mambela iso shi kuma ya umurci ma’aikata dasu dauko kayan aiki su
shiga su fara. Mambela sai kai kawo yake daga daki xuwa tsakar gida xuwa kofar gida
yana ta haska ido yana ta hangen mata reras a xaxxaune a tsakar gida amma bai hango
abar kaunarsa ba kaltum ya kasa tambayar madina kuma.
Kafin magaruba an lelayewa su kaltum daki ras da katakwaye masu santsi, aka tottoshe
musu hudojin rufin daki inda ruwa yake shigo musu lokacin damuna, aka huda musu
window inda iska xata dinga shigo musu sannan aka gyara musu kyauren kofa aka yi
musu sakata da wajen makala kwado.
Sai tururuwar lekawa dakin ake yi ana gani, sha’awa ta kama ‘yan sauran dakunan suna
cewa dama suma a dakin suke. ‘yan dakin kuwa farin ciki suke harda tsalle yayin da
suka kewaye mambela suna yi masa buda da kirari suna masa fatan Allah Ya bashi
kaltum. Gogan naka sai ya ji babu kamarsu