Author : Binta Umar Category : Complete Novels
Sadauki Omar cmpt[5/24, 12:09 PM] Bintu Novel: 60
"Yaya na meke faruwa ne.''!? tafada tana bin palon da kallo...Hannunta ya rike suka koma cikin dakin ya zaunar da ita gefan gado kana shima ya zauna kusa da ita.
Minti biyu a tsakani yace." Aysha ce ta dawo yanzu haka tana dakinta ina fatan baki mance duk irin maganar da mukayi dake ba."
Jikinta a sanyaye tace"Eh ban mance ba kuma nayi maka alkawari insha Allahu zamu zauna lafiya da juna ta bangarena ba zaka samu matsala ba."
Ajiyar zuciya ya sauke ya mike ya nufi toilet domin watsa ruwa.
Shiru tayi tare da zabga tagumi ji tayu duk jikinta yayi sanyi kalau aysha ta dawo gidan yanzu ko wane irin zama zasuyi da juna oho!
Ita dai zatayi iyakacin kokarinta gurin ganin sun zauna lafiya da juna insha Allahu ta gefanta baza'a samu matsala ba.
Da kallo ta bishi lokacin da ys fito daga toilet din sai taga kamar ransa a bace yake alhalin kuma da zasu kwanta ba haka yake ba asali ma sai da su gama wasanin soyayyarsu sannan sukayi bacci.
Wata zuciyar tace mata to ko bai so dawowar ayshan bane.'!? mikewa tayi jikinta sanyi kalau taje tayi wanka a gurguje ta fito ta shirya jikinta lokacin ma tuni ya fita palo don haka tana futa kai tsaye kicin ta nufa.
To bangaran Aysha kam kuka taci ta koshi tayi lamo kan bed tana tunanin halin d'an adam ta dauka zai shigo ya rarrasheta kamar yanda ya saba sai kuma taji shiru yanzu shigowarta gidan ya kai awa guda ko motsin su bataji ba ballanta ta ta sanya ran zai shigo dakinta.
Yana zauna kan kujera mai cin mutun daya ya dora loptop a cinyarsa yana wani aiki..
"Yayana bari in shiga in tambayi aunty gimbiya abunda take so taci sai in had'a mata kai dai na d'umama maka towon ka."!
Safarau ce ke wannan maganar lokacin da take fitowa daga kicin.
Cike da kulawa gami da tsantsar so yace." Hakan na dakyau Safa Allah yayi miki albarka." ta nufi dakin ayshan tana murmushi kullum tana so taji yana shi mata albarka shiyasa take kokarin yi masa dukanin abunda yake so
Cikin d'ar-d'ar! ta tura kofar dakin ta shiga da sallama.
Fitowarta kenan daga bandaki tana goge fuskarta....Safarau ta saki fuska sosai tace"Aunt gimbiya kin dawo ashe sannu ina kwana ina Abbana."!?
Ba tare da ta kalli inda take ba ta wuce ta zauna kan sofa.
Safa taji zafin abunda tayi mata amma sai ta share tace"Aunty me zan had'a miki na fannin abinci."?
Ta d'ago burkitattun idanunta da suka rine da bacin rai ta watsa mata muguwar harara tace"Ance miki da yunwa nazo ne sarkin iyayi da son iyawa bana ci dallah malama fuce ki bani guri mtsssw!!
Safarau taji gwiwar ta tayi sanyi sai ta juya ta futa daga dakin ranta a mugun bace!
Tana futa ta zabga tsaki tare da daukar wayarta tana dubawa.
Duk yanda taso da ta daure abun ya faskara sai da yanayin fuskarta ya nuna wanda kallo daya yayi mata ya gane aysha tayi mata halin nata dama yasan za'ayi haka kawai ba ya son ya kashe mata gwaiwa ne tayi niyar yin abun arziki.
Kicin ta wuce tana boye damuwarta.
"Safa zo nan."!? muryarsa taji a hankali ta dawo da ta tsuguna kusa dashi.
Yace." Ga yanayin yanda kika fito daga dakin aysha ya nuna min akwai matsala ki fada min me tayi miki."!?
Dariya tasa har sai da duka dadashinta suka bayyana tace"Kaji ka yayana da wani zance wallahi babu abunda tayi min tans toilet ma lokacin dana shiga shine na fito."
Yasan kawai ta fada ne domin ta kare kanta amma yasan ba zata ta'ba shiga dakin aysha ta fito salin alin ba.
Girgiza kansa yayi yace."Kawai ba zaki fada min bane shikken ni na fahimci komai kuma zan dauki mataki mai tsauri a kanta."
Da sauri ta kalleshi murya na rawa tace"Wallahi babu abunda tayi min Yayana kar kaje kayi wani abu mara dadi kawai fa cewa tayi bata so in futa in bata guri kuma ni wannan ban daukeshi a matsayin laifi ba."
Yace."Okey da kuma kika ce babu komai ashe kin iya karya."!?
Rufe fuskarta tayi da hannunta tana dariya.
Murmushi yake yana kallonta ta mike zata gudu da sauri ya riko hannunta yana mata wani shu'umin kallo. murya a ma'koshi yace. "Yaushe zaki samar min da baby girl me kama dake."!?
kunya ta kamata sai ta fara kokorin kwacewa zata gudu shi kuma ya rike ta tamau wai sai ta fada masa ranar.....Fuskarta ta bude ta dunga kyalkyala dariya tana fadin " Ka sakar min hannu to zan fada maka."!
Ya saki hannunta aikuwa da gudu ta wuce kicin tana dariya.
Ya bita da kallo cike da kauna tabbas safa na kokarin ganin ta kawo zaman lafiya a gidansa dole ne shima yayi kokarin kyautata mata da gudun bacin ranta.
Aysha kam tana kwance tana jin maganganun su kasa-kasa sam bata fahintar abunda suke cewa sai dai sautin dariyar Safaraun take ji zuciyarta ta sake tunzura inda a take taji wani irin axababben ciwon kai yayi mata sallama,
Cike da karsashi gami da jarumta ya shigo dakin fuskarsa babu yabo babu fallasa ya karasa bakin gadon ya tsaya kanta.
Dauke kanta tayi sam bata son kallonsa.
Yace."Gimbiyar mata aysha sarauniyar zuciyar Umarulfaruk."!
Ko kallonsa ba tayi ba, ya zauns gefanta tare da d'an jan kafarta guda. Ta janye da sauri ta watsa masa harara
Murmushi yayi ya shafa sajensa kana yace." atlest koda ba zaki gaishe ni ba yana da kyau ki amsa sallamata saboda ni nasan a cikin musulunci a kai haifeki gaba da baya ba dai-dai bane mutum yayi maka sallama da fatan alkairi ka kasa amsawa aysha."
Ta mike zaune tare da d'ora hannunta a goshinta tana matsawa tace"Don girman Allah ka tashi kayi tafiyarka wallahi kana kara min damuwa ne gashi kaina na yi min ciwo."
Yace."Ni babu inda zan tashi naje na shigo ne domun mu fahimci juna dani dake muyi zama na lumana da aminci."
Ta kalleshi har yanzu hannunta na kan goshinta tace"Yanzu awa na nawa da shigowa cikin gidan me ya hanaka zuwa gurina sai da ka gama duk uzirinka sannan zaka zo kanayi min wata magana nifa wallahi a halin yanzu duk irin maganganun da zaka fada min baza su sanya ni naga hasken ka ba mutuncinka ya riga ya zube a gurina." Murmushi yayi yana kallonta ya rasa wace iriyar mata Allah ya bashi.
Hannusa ya dora kan goshinta yana murzawa a hankali yace."Ki bari nayi miki addua insha Allahu xaki samu sassauci."
Tankwabe hannunsa tayi ta mike ta bar masa gurin....kan Sofa ta kwanta zuciyarta cike da damuwa wai shin ya za'ayi ma ta iya zama dashi yana ha'intar ta wallahi namiji munafiki ne.
Ya mike ya isa inda take ta mike da sauri zata bar gurin ya riketa.
Kallon junansu suke ita dashi....Cikin wata irinyar siga ta mayaudaran maza yace."Yace."Aysha don girman Allah ki tsaya ki saurareni ki fahimce ni kan magana why!! ya kike so nayi ne uhhm!! kina so zuciyata ta buga saboda tsananin damuwarki wallahi wannan zaman da muke dake bana sonsa na yarda ko wane irin hukunci zaki dauka ki dauka aikana ki daina in dai zaki huce fushinki."
Ta wani lanjare yana karyar da kai kamar wani yaro sai marairaice fuska yake.
Ko kallonsa ba tayi ballantana tayi masa magana.
ya cigaba da nanikarta yana wasa da jikinta....Ganin yana nema ya tsokano ta ne yasa ta tureshi tana hararasa.
Ya kalleta a galabaice yace."Baki san dauriya kawai nakeyi ba saboda rashin ki aysha bana jin dadin komai duk wani abu da kikaga inayi to cikin dauriya nake aysha na amince nayi laifi amma ki barni na gyara da kaina don Allah ki samar min da farin ciki da zaman lafiya kinji ko."
Jin abunda yake cewa ne yasa ta kalleshi ya d'aga mata girarsa a marairace yace."Da gaske Aysha wallahi sonki na nema ya kassarani ayi hakuri nayi laifi a barni yau na angonce."!
Taji tamkar ta gaura masa mari wai yana sonta amma yake mata iskanci hummm kaji wata magana wai abarshi yau ya angonce lallai namiji kenan.
Hannunta ya rike a hankali yace."Please my wife."!
Ya mutsa fuska tayi ba tace masa komai ba.......Ya dinga sassauta murya yana mata kalamai masu dadi da nuna mata matsayinta a gurinsa jinsa kawai take amma jikinta ya soma sanyi da kalamansa
"Ki yarda dani aysha ba zan iya rayuwa mai dadi ba sai dake wai shin ba kiga yanda na koma bane na rame duk saboda rashinki aysha ki tausayawa d'an uwanki. ki bashi kulawar da kika saba."
Yana yi mata wani shu'umin kallo yake maganar.
Tace"Wai yanzu me kake so nayi."!?
yace."Ina so ki zauna dani lafiya ki kuma zauna da Safarau lafiya."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Zaman lafiya a cikin gidan ka idan kaso za'ayi idan kuma kazo da munafurci to za'ayi ta samun sa'bani don haka ni bani da matsala da matarka kawai dai ka gargadeta ta kiyaye bana son raina zamu iya shekara dari a haka ina rayuwata tana rayuwar ta ban damu ba."
Yace."To ai ba halin Safarau bane haka aysha gaba gami da rashin amsa sallamar dan uka ba kana bace safarau bata iya wannan zaman ba, Dazu ta shigo tayi miki magana kin koreta hakan ba dai-dai bane aysha ki fahimci rayuwa yanda take."
"Okey ta fad'a maka kenan."!? tafada cike da mamaki!
Yace." Eh nine na tambayeta saboda yanayin da naga ta fito.
Murmushi me ciwo tayi lallai yarinyar nan munafuka ce komai sai an fadawa miji Allah ya sawake.
"Yanzu me kike so kici ta girka miki ko kuma kina so in fita in siyo miki." yafada yana rike da hannayeta.
Ba tare da wata kulawa ba tace"Duk wanda kayi dai-dai ne."
Yace."Bari in sanya ta tayi miki girki mai dadi." banza tayi masa ya mike ya futa....Binsa tayi da kallo taja tsaki tare da fad'in munafiki kawai."
Safa na kicin tana aiki ya shiga ta juyo da fara'a a fuskarta tace."Yayana ka gaji da jiran towonka ka biyo sahu ko."?
Fuska a sake yace."Eh mana kin manta dani zaune a palo ina ta had'iyar miyau! shiyasa nazo na kar'ba da kaina kin san fa girkin ki daban yake dana sauran mata idan ina cin abincin ki ina ji tamkar kunnena zai tsinke."
Ta dinga kyakyata dariya tana kallonsa ya karaso ciki sosai yana bude buden tukwane.
Hade fuska yayi irin baya son wasa yace."Ina towon yake."!?
Cikin sigar tsokana tace."Yanzu na bawa Ashiru nace yaje ya cinye.''
Kunnanta ya rike yana murd'ewa a hankali! wata yar 'kara ta saki ta juyo sai ya rungumeta yana sumbutar goshinta yace."Nasan wasa kike ai yanda na himmatu gurin son cin d'umamen towon nan ai idan kinyi haka baki kyauta min ba."!
Tace."Ayya Yayana wace ni a koma ka zauna yanzu zan had'o maka insha Allah."
Ya saketa tare da kallonta cike da farin ciki yace."Allah yayi miki albarka matata."!
Ta amsa da ''ameen Yayana."
Har ya kama hanya zai futa sai ya ja ya tsaya ya juyo a nitse yace."Ina dakin Aysha ki kai min can kinji ko."
Tace."Insha Allah."
Yana futa ta fara tunani itafa bata son shiga dakinta ta dizgata don gaskiya hakurinta ya fara karewa kan irin wulakancin da take mata amma dai tunda umarninsa ne dole ta cika.
Dakin ayshan ya koma ya tadda ita inda take waya suke da Azima amma yana shigowa ta katse kiran ta aje wayar gefe.
Ya nufi bed dinta ya kwanta rigingine kafafunsa a kasa. Hannu ya ware mata wai tazo.
Tayi saurin dauke kanta tana jan tsaki ya wani tale kafafu ko kunya baya ji.
A hankali yace."Aysha ina yarona ne ko kin barwa gwaggo."?
Shiru tayi masa sai da ya sake wata maganar sannan tace"Yana gurin Mama Fulani."
Yayi shiru yana kallonta tare da d'aga mata girarsa.
Ta ruga ta gane abunda yake nufi sai kawai ta dauke kanta tana 'kara cin kunu ji take kamar taje ta sha'keshi, ta huta da takaicinsa.
A hankali ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama....Shi kadai ne ya amsa mata ya mi'ke ta tare ta tare da kar'bar tire din hannunta albarka ya shiga sanya mata ta juya zata futa ba tare da tace komai.....Wani irin fad'uwar gaba ta riski kanta a ciki ganinsu tare a daki daya ya daga mata hankali duk da ba wani abun ta tarar sunayi ba amma taji wani irin azababban kishin ayshan ya sauka a zuciyarta....shikkenan yau babu ita babu kwana a kirjin mijinta shikkenan yau zatayi missing din abubuwa da dama da suke wakana a tsakaninta dashi....Idanunta ne suka ciko da kwalla wanda a maimakon ma ta koma kicin din ta cigaba da aikinta sai ta nufi dakinta ta kwanta gan bed tayi lamo hawaye na zuraro mata a take wani katoton abu yazo ya tare mata a ma'kogwaro.
Tunda ya bude kwanukan abincin taji miyan ta ya tsinke sosai take sha'awar cin d'umaman towo.
Dauke kanta tayi da sauri don kar ta bada kanta amma gaskiyar magana shine towon ya burgeta sosai.
Towon farar shinkafa ne tas da miyar kuka wacce taji daddawa da nama sai kamshin manshanu miyar take abun dau ba'a magana....ga wata ma daidaiciyar roba nan cike da yajin daddawa dama ita gwanar cin yaji.
Yace."Aysha bisimillah ki sauko kici fara da wannan kafin ta gama na rana idan ma ba zaki ci abunda ta girka ba to ki fadi komeye kike so na futa na siyo miki."
Ta kalleshi ranta a bace tace"Wai don Allah me kuka mai dani ne daka kai har matar taka daga zuwana sai wani tura min abinci kuke sai kace wata jaka kasan ni bana cin towo ku cinye abunku."
Yace."Ni wannan yayi min yawa ki sauko ki tayani ci please." ta gane magana yake son janta da ita sai ta shareshi ya mike ya isa in da take....Hannu yasa zai dauketa ta doke hannun sai kawai ya ciccibeta ta dukunkune jikinta cikin kujera haka dai ya dauketa tare da dure ta inda abincin yake.
Ta dinga zabga masa harara shi kuma yana murmushi sam bai nuna mata damuwarsa ba sai ma lallabata da yake ya gutsiro towon ya kai bakinta, tana son ci amma sai ta dauke kanta tana zum'bura baki.....Sosai ya matsa jikinta ya dinga sanyaya murya yana lallaminta sai da taga wulakancinta sannan ta fara kar'bar towon tana ci tana ta'be bakinta tare da kawo suka kan girkin karnin nama gishiri yayi yawa miyar ma kauri take....Shi dai duk yana jinta yana cigaba da gutsiro towon yana bata a baki tana lamushewa amma bata fasa sukar girkin ba.
Sai da ta tabbatar taci ya isheta sannan ta dauke kanta.
Da kanta ta tsiyayi lemo tasha ta dauki ruwa ta sha harda gyatsa ta mike daga gurin.
Ya girgiza kansa yana kallonta, a nutse ya fara cin nasa yana yi yana satar kallonta aysha ta tsaya masa a cikin zuciyarsa wanda duk yanda yaso ya yakice ta daga zuciyarsa ya kasa tabbas ya yarda da cewar idan babu ita rayuwarsa na cike da kalubale,
*****
Sai yamma likis ta tashi domin bacci ne ya dauketa bayan taci kukanta, a kasalance ta tashi tayi wanka hade da dauro alwala azuhur da la'asr tayi ta mamakin irin baccin da tayi gefe guda kuma tana mamakin dalilin da ya sanya Omar din bai tasheta ba zuciyarta tace mata watakila yana tare da matarsa ne ya manta dake.
Kai kishi bala'i ne itafa bata ta'ba tsammanin tana kishin mijinta ba sai yau da Aysha ta dawo gidan domin kin futa palo ma tayi ta takure jikinta kan daddumar da tayi sallah tana tunani,
Omar kam ai yana gama cin d'umamen towonsa ya shirya ya nufi fada don da ya shiga dakinta ya tadda ita ba sai kawai yayi fucewarsa ba tare da ya tasheta ba.
****
Sai bayan sallahr isha'i ya shigo gidan palon tsit!! kai tsaye dakin safaraun ya nufa....Ya tura kofar ya shiga ta amsa ba tare da ta mike zaune ba
Al'amarin sai ya bashi mamaki sosai.
Ya zaune gefanta tare da son ya cire mata hijab din data kudundune a jikinta.
Ta rike hannunsa tana kokarin mikewa zaune taki yarda su hada ido dashi.
Yace"Safa lafiya kike kwance a irin wannan lokacin bayan duk dare kin saba zama a palo cikin kyatacciyar kwalliyarki mai burgewa shin meke damunki ne."!?
Zuciyarta ta karye sai hawaye shaaaaa!!! yayi shiru tare da zuba mata ido yana mamakin sauyin da aka samu ta bangaranta.
Hannu tasa ta goge hawayenta tace"Yayana kaina ne yake min ciwo tun dazu."!
Ya ruke kan da hannunsa kana yace."Kuma sai ki kwanta kina kuka humm! bana so daga yau in kina ciwo kiyi kokarin sanar dani kinji ko."!
Ta daga kanta tana jin karyewar zuciya hawaye kuma bai fasa zubo mata ba.
Ya rike mata kan sosai yayi mata addua ya matse yace."Insha Allahu zaki samu sassauci tashi muje kici abinci sai kisha magani ko."!
Ta mike ya tayata da cire hijab din vest ce a jikinta irin mai matse jiki sai dogon wano na jins sosai Brest dinta suka kara girma....Ya mike tare da daukarta kamar jaririya suka nufi palon suna dariya.
Yana kokarin sauketa kan kujera aysha ta fito palon tana rike da Abdul dake ta faman zabga kuka domin ba'a dade da dawo dashi ba , idanunta suka nuna mata abunda ke faruwa sai kawai ta dauke kanta daga kansu ta nufi kofar futa da yaron.....Ya sauke Safaraun da sauri ya isa tare da tare hanya yana kokarin kar'bar yaron mika masa shi tayi ta juya ta koma d'akin ya bi bayanta tamkar wanu jela.
*Kika futar min da littafi Allah ya isa!/ Kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa!*
Accont numbar
*07084653263_08089965176*
accont numbar
*0542382124......Binta Umar gtbank*
24/4/202
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/25, 10:02 AM] Bintu Novel: 61
Jiki a sanyaye Safa ta mike ta shige dakinta addua take cikin zuciyarta kan Allah ya cire mata kishin aysha dake ranta tabbas a yanzu ta tabbatar da cewar ita da aysha ba daya suke ba a gurinsa dan ganin irin rawar jikin da yake akanta ya sanya gwiwowinta sukayi sanyi kayan bacci ta sanya ta kwanta yunwa ta addabi cikinta....don sai yanzu ma ta tuna da cewar babu abunda ta tsinana a cikin gidan na dangin abinci abunda bai ta'ba faruwa ba tun da tazo gidan rana daya ce bata yi girki ba amma kullum sai ta shirya musu abinci kala-kala masu rai da lafiya.
"Aysha kukan me yake yi ne."!? yafada yana dan bubbuga bayansa.
Tana kokarin shiga toilet tace" Yunwa yake ji."
"Ki bashi nono yasha mana." Yafada tare