Advertisements
Chapter 27 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 29

78K to 81K   out of 86.8K words

shi kuma a lokacin fitinar sa ta motsa masa sosai gashi gefan aysha ita kuma ta bud'e wuta ta kulle duk wata 'kofa da zata sada shi da ita idan ya shiga sashen Nanne ma sam bata bari su had'u Idan ya fake da cewar 'yayansa yazo dubawa sai ta sanya a dauko masa su ya gansu iyakacinsa Palo sam bata bari ya shiga dakin aysha ta kasa ta tsare a palo ita kuma ayshan na daki ta sanya key.

Idan dare yabi nan ma haka zai gama laluben sa da sand'arsa ya koma inda ya fito domin ta ko wace hanya babu dama Gashi kullum kara rura masa wutar sha'awa akeyi kamar wani matashi dan shekara ashirin.


Dabara ya shirya ya nufi sashen Nanne sai akayi sa'a duk suna palo suna hira harda ayshan ya zauna suka gaisa aysha ta saki jiki sosai suka gaisa kamar ba ita ba ya dauki yaransa yana musu wasa yana satar kallonta suna hira da Jakadiya......Yace."Nanne kuna da labarin zuwan Kawun Safarau gidanan kuwa."?

Nanne tace"A'a bamu da labari Omar yaushe Kawunta yazo ? kai alhamdullahi."


Yace."Ayya ashe baba galadima bai sanar miki kenan Ai yau kwanansa shida a cikin gidanan gobe suke sanya ran komawa gida."

Aysha ta kalleshi cike da mamaki! Kawun Safarau yazo amma bata da labari lallai Safarau bata kyauta mata ba.


Nanne tace"Haba mana shiyasa Safarau ta daina zuwa sashen nan mana amma gaskiya banji dadi ba ai da naje mu gaisa da juna."


"Aikuwa yanzu ma ai zaki iya zuwa gobe da safe da wuri zasu tafi."

Nanne ta kalli Jakadiya tace"Maza dauko min alkyabbata sannan ki shirya kaya sai muje mu gaisa kafin su tafi."


Jakadiya ta mike aysha tace"Bari in shirya muje tare." Itama ta nufi dakinta Omar na ganin Nanne ta shiga dakinta sai ya mike ya bi bayan Aysha.


Tana tsaka da d'aura igiyar alkyabbatar ta ya shigo dakin ta mirror ta hango shi ya nufo inda take ta dauke kanta yana isowa ya rungume bayanta yana sauke ajiyar zuciya.

A hankali ta zare jikinta a murtuke tace"Bana son irin wannan abunda kake min wai shin me kake nema dani ne? kasan fa yanzu duk abunda ka aikata haramun ne."


Marairacewa yayi yace." Aysha ki tausaya min ina cikin wani hali na rashi da takurewar zuciya ina me tabbatar miki da cewa zuciyata daf take data daina aiki a halin yanzu rayuwata tayi kunci damuwa mai tsanani ta dabaibaye ni wallahil azim Aysha ba haramun nake aikatawa dake ba sinna nake yi ke matata ce aysha! ke da su maimartaba kuna so ku kasheni ku cuci 'yayana! karki manta fa wannan al'amari da ya ratsa a tsakaninmu dake ba yin kaina bane umarni ne aka bani ni Omar nasha fad'a miki cewar tsakanina dake babu saki bari yaji Ina sonki cikin ko wane hali zan iya rayuwa dake aysha kada ku sanya zuciyata ta tashi daga aiki a yanzu bani da madafa kuma bani da wata shaida sai ta Allah sai kuma ke!! idan kin amince dani shikkenan idan kuma baki amince da dukanin maganar da na fada miki ba to Wallahi nayi rantsuwar daga yau zan fita daga rayuwarki kamar yanda kika bukata na amince ni in mutu ko in samu tabin hankali ta dalilin wannan lamari."


Jikinta yayi sanyi jin kalamansa tace"Kaje kawai zan zauna nayi tunani kan maganarka." Yace."Shikkenan zanje kamar yanda kika ce amma yaushe ne zaki 'kare tunanin naki." ? Jim!! tayi tana tunani tace"Zan maka magana kai dai kawai tunda nace kaje duk sanda na yanke hukunci zan sanar da kai."


Yayi sakare yana kallonta duk ya koma kalar tausayi ya koma kamar wani maraya tsira mata jajayen idonsa yayi da suke dauke da zallahr sha'awa da fitina a yanzu bai'ki ya kwanta da ita ba.


Koda Nanne ta fito sai ta iske babu kowa a palon Sai baby Safa tana canyara kuka Mimi dama 'yar d'akin gwaggo ce dan wataran ma acan take kwana, kawai sai ta Umarci Jakadiya data dauki yarinyar su wuce tasan iyayen ta a yanzu suna tare da juna kuma sai abunda hali yayi....Fita sukayi suka nufi masaukin baki.


Tace"Ka tsira min ido kana kallo wai me zanyi maka ne? don Allah ni muje in mu gaisa da mutumin nan ai abunda kukayi min kai matarka baku kyauta ba wallahi wannan rayuwa ce ace yau kwanan kawun Safarau shida a cikin gidanan bamu da labari ai babu komai laifin ba na kowa bane sai na ita Safaraun.


Yace."Karki d'ora mata laifi aysha yaushe ne zata shigo ta fad'a miki Kawunta yazo ki saka ta kuka ni ne na hanata zuwa gurinki tunda ke kam baki da tausayi kullum yarinya na gidinki tana rarrashin ki amma ke kuwa kina sata kuka bakya duba larurar da take dauke dashi."


"Ka kyauta ai daka hanata shigowa gurina amma ina mai tabbatar maka da cewar baka isa ka yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu ba."
Ta karashe maganar tare da nufar hanyar futa

Tare mata hanya yayi yana karyar da kai tamkar wani maraya.

'Kungunta ta ri'ke tana kallonsa da mamaki tace"Wai don Allah menene haka? ina fa ganin mutuncinka bana so ka sanya ni na zage ka ko kuma na fad'a maka magana me zafi."!


Yace."Na kasa samun nutsuwa ne aysha yanzu abu guda nake so kiyi min ko zan samu nutsuwar zuciyata."


Cikin 'kosawa tace"Menene shi."!? Ya shafa sumar sa a hankali ya nuna kirjinta da hannunsa.


Tace''Me hakan ke nufi."!?

"So nake ki bari na kwantar da kaina akansu sai na samu sau'kin zuciyata."


Tace"Wallahi baka isa ba idan har sai kasa kanka a kirjina zaka samu nutsuwa to sai dai kar ka samu d'in wannan ai lalacewa ce meye amfanin hakan kaje matarka nada kirji sai ka kwantar da kanka akai amma bana aysha ba."


Yace."E ai nasan tana dashi naki nake so."!!!

Tsaki! taja ta kama hanya zata wuce.....Jawota yayi ta dawo ta tsaya gabansa...Sai gabanta ya fara faduwa ganin yanda yake wani irin nishi yana jawo numfashi da kyar ga idanunsa sun shagid'e sunyi jawur dasu ita ta rasa me yasa yake mata haka, zuciyarta tace ki tsaya ki saurareshi ku rabu lafiya.


Kallon juna suke ita dashi tausayinsa ta fara ji ganin duk ya wani susuce! tace"Ka sakeni ko."!

Girgiza kai yayi yana lumshe ido." Sai ta sake yunkurin kwacewa ya ri'ke 'kugunta da karfi ya dora kansa kan kafad'arta yana goga mata gemunsa a wuyanta.

Tsigar jikinta ta fara mikewa ta dan ture shi tare da jan karamin tsaki gaba tayi ya biyo bayanta suka sake wata tsayuwar palo yace."Aysha bafa zan barki ki fita ba sai kin gamsar dani."!


Ita abun ma sai ya bata dariya wai sai ta gamsar dashi lallai ma mutumin nan "Me zanyi maka to."? tafadi maganar kamar gaske yace." Kawai muje daki sai in fad'a miki."


Sai ta d'an kalli a gogon dake daure a hannunta takwas da rabi na dare tace"Shikkenan ban'ki maganarka ba amma bari muje mu dawo ko."! Ya d'aga kansa kamar wani shashasha!! Dariya ke cinta amma ta guntse ta domin bata so tayi ya raina ta.

Ta tayi aune ba taji ya rungumeta a kirjinsa sai shasshafa bayanta yake mussaman mazaunanta


Sakare tayi kawai tana jinsa sun dauki tsawon minti goma a haka kafin ya saketa yana kallonta tana kallonsa da da tsabar fitinar dake idonsa tana kallo ya ciro wani glass mai duhu a aljuhunsa ya sakaye idonsa dashi kana yayi gaba ta girgiza kai tare da bin bayansa.


Kan hanya suka had'u da Nanne ita da Jakadiyarta sai Omar ya fara washe baki yana kame-kame Nanne kam gaba tayi kwata-kwata bata nuna tasan sunayi ba.



Cikin mutunci Aysha suka gaisa da Kawun Safa da 'yan uwanta Safarau ta gaisheta aysha ta gaisa babu cikakkiyar walwala Safarau bata ji dadin hakan ba Shi kuwa Alhaji Lado sai albarka yake sanya musu da yi musu fatan alkairi gami da zaman lafiya dake Omar ya fada masa cewar aysha itace Uwargidansa.


Aysha ta mike tare da yi musu sallama ta fita to da yake Omar ya dan jima tare da Kawun bai fito ba wannan ya bawa Aysha damar guduwa sashen su dama tana ta tunanin yanda za'ayi ta tseratar da kanta.....Yana fitowa yaga batanan bakin ciki kamar ya kasheshi aysha dama aysha mayaudariya ce bai sani ba hummm! !!! ciki ya koma ya hillaci Safarau da dubara ta bishi sashen su to a tare da ita ya samu kwanciyar hankalin da yake bukata.


*Bari mu waiwayi Azima kuma*


A can asibitin da Azima take kwance tana jinya tana samun kulawa sosai sakamakon irin kudad'en da Omar yake tura musu duk domin ta samu kyakkyawar kulawa to Alhamdullahi Azima dai ta samu lafiya sai da babu kafafu babban abunda yake daga mata hankali kenan duk sanda zata sauke idonta akan kafafunta sai ta zubar da hawaye tana nadama tasan hakkin Aysha ne ya kamata da kuma hakkin aure hakika zuciyarta ta rinjayeta ta aikata babban laifi irin wanda bashi da amfani sannan ta biyewa lalataciyar 'kawa Hasina wacce itace duk ta jefata cikin wannan bala'in gashi duk wani masoyinta yazo ya dubata amma banda ita kwata-kwata yanzu ma an daina samunta a waya Momynta taji takaicin faruwan wannan lamarin sosai da karshe ta dangana tana ganin rashin jin maganar iyayene ya jawo mata shiga wannan matsalar da tana jin maganarta da shawarwarin da take bata to da rayuwarta bazata lalace irin wannan ba......Yanzu Azima sai dai a tura ta a keken guragu kafin ta iya tura kanta.......Omar da ya samu labarin samun lafiyarta yaji dadi sosai yace."A sanyo su a jirgi ita da mahaifiyar tata domin kawo su gida tunda bata da wata matsala....Koda Azima taji abunda Omar yace sai ta dinga murna ta dauka Omar din bai saketa ba tana tunanin wata irin rayuwa zatayi dashi ga wata iriyar kunyar aysha da takeji ai dole taje har inda take ta bata hakuri.
To tun kafin su sauka ne Omar ya aikawa da Kawun Azima takardar sakinta don haka shine ya tura direba har airport aka daukosu Koda Azima taga an nufi gidan Kawunta da ita sai tasha jinin jikinta tun a mota take kuka mamanta na jinta taki rarrashinta wani irin haushinta takeji yarinyar banza da wofi ta cuci kanta ta cuci wasu.


****

Tun ranar da Aysha tayi wasa da hankalinsa yayi zuciya da al'amarinta........amma still tana manne a cikin ransa yanzu ba sosai yake shiga sashen ba domin ya lura kamar Nanne ma tana masa wani irin kallo na tuhuma sai kawai ya kama kansa idan yana bukatar ganin 'yayansa zai sanya a dauko masa su wani lokacin ma idan ikonsa ya tashi idan an dauko yaran baya mayar dasu sai sun kwana biyu babu ruwansa sa kukan dare da kansa yaka dama musu madara ko Costand da sauransu yaran har sun saba dashi da Safarau da cikinta ya girma ya shiga wata na shida ta zama wata katuwa sosai cikin ya bud'ata duk da girman cikinta bai hanata yiwa yaran hidima ba, Abdul kam dama dan bangaran mamane yana tare da ita yaron ya girma sosai sai kuzari da zafin nama tamkar ubansa.

****

Wannan d'auke wutar da yayi sai ya soma damunta tafi so kullum ya dinga mata magiya yana bata hakuri ita kuma tana garashi tamkar gare gare! hanyar da zata karkato da hankalinsa kanta ta fara tunani.


****

Omar ya samu karin girma gurin aiki Alhaji Aliko gwate bashi da babbban amini tamkar Omar kaf abunda ya shafi Aliko gwate Omar babu wanda bai sani ba komai na tafiya ne da sanya hannun Omar dangane da abunda ya shafi Alhaji Ali a cewarsa Omar ba karamar gagarimar nasara gami da cigaba ya kawo masa ba ta bangarori da dama sannan yana da amana da iya aika dukanin abunda ya sanya Omar a ciki sai ya ga nasara a ciki don haka sai ya sanya masa suna wannan shi kad'ai yake kiransa dashi *(Jalabi)* Wannan suna shi kadai yake kiransa dashi yanzu sun sha'ku ta yanda har sai da ya dauki Omar din ya dangana shi ga iyalinsa suka gaisa da juna shima ya nemi da ya hadashi da iyalinsa su gaisa tunda an zama daya to saboda ya san yanda al'amarin yake tafiya ta bangaran iyalinsa ya sanya bai kai shi ba tukkuna yana so Aysha ta koma dakinsa sai ya kaishi su gaisa da juna amma duk ya nuna masa hoton yaransa Abdul da Safarau da Sa'adatu.

Koda Omar yaje wa da iyayensa bukatar son ya bar cikin gidan sarautar da zama dalilin gidan da ya mallaka wanda fadin girman gidan da tsaruwarsa bata lokaci ne wani irin mahaukacin gida ne mai dauke da part hudu da wani irin gini na jan dutse irin na mutanan ingila kusan tsarin ginin gidansa Alhaji Ali ya sanya ma'aikata sukayi wa Omar, abunda dai sai wanda ya gani


Maimartaba ya nuna bujirewar sa kan maganar sa ta barin gidan sarautar, yace."Baya daga cikin tsarin masarautarsa d'ansa ya fita waje ko wancan karon ma da ya bari Ya fita saboda yana so dashi da ayshan su gane rayuwa ne saboda haka bai amince ba."


Omar ya fita daga fada duk ransa a dagule......Yana ganin wannan wane irin mulki ne da tauye hakki shi idan shine kan kujerar mulki wallahi ba zai yanke wannan hukuncin ba zai bawa kowa 'yancin sa.


'Bangaran Sarki kuwa yana sane ya yanke masa wannan hukuncin saboda wani dalili nasa.

Aikuwa washe garin ranar da al'amarin ya faru Sai ya aika aka kira masa Omar din lokacin yana shirye-shiryen tafiya ofis sakon ya iske shi yana zuwa Sarki ya bashi Umarni kan ya shiga fada yau shine zai zauna kan kujera ya gudanar da al'amaran dake faruwa a fadar.....Omar ya cika da mamaki dajin maganar mahaifin nasa shin ina Baba Waziri Ina Baba galadima su meye amfaninsu da baza su kula da fada ba sai shi dake da aikin yi , wai don anga yana aiki a cikin gari shiyasa komai sai ace shi me yasa baya yiwa su Abbas irin abunda yake masa ko don ba a gari suke aiki ba.

Bashi da mai bashi amsa sannan bashi da damar da zai shigar da korafin sa don haka sai ya amsa kai tsaye ya fita sashensa ya nufa Safa ta bishi da kallo ganin ya dawo sai ta bishi dakin tana fad'in "Kayi mantuwa kenan."!? Bai ce mata komai ba ya fara cire suit din jikinsa ransa duk a dagule taga ya bude wardrobe ya ciro manya kaya da wata jar alkyabba mai adon wani kyali kyali a jiki sai ta taya shi sanya kayan ya dora akyabbar akai sannan ya d'ora nad'insa a kansa Safarau taga yayi mata masifar kwarjini sosai tare suka fito ta rakashi har bakin kofar fita sai da ya fita sannan ta koma cikin dakinta.

*****


Wasa-wasa sai da Omar yayi sati biyu yana zama a fada kan kujerar mulki yana gudanar da shari'a da abunda ya shafi harkokin mulki sannan Maimartaba ya bashi umarnin komawa bakin aiki ya tabbatar ko bayan ransa Omar zai iya mulkar mutane saboda yanda ya dinga gudanar da al'amaru har yaso ya zarta shi Galadima da Waziri ta bangaransu suma suna ganin ko yanzu Omar ya kar'bi mulki daga hannun mahaifinsa ba wani abun bane saboda ta kai matsayi sannan shekarunsa sun kai su dai fatansu shine masarautarsu ta cigaba da kafa tarihi mai kyau da ma'ana.


****

To koda ya koma aiki bai samu wata matsala ba saboda dama dukanin abunda ke faruwa Alhaji Ali ya sani shima wani lokacin yakan zo fadar a zauna dashi.


****

Tsakaninsa da Aysha babu sigina balle d'aga hannu babu test babu kiran waya ko wanne harkar gabansa yakeyi ta ciki na ciki dukaninsu zuciyoyinsu a dame suke da junasu mussaman shi ubangayyar wanda da duk wani abu da yake daurewa kawai yake yana so kawai yaga iya gudun ruwanta.



Kwatsam! Ranar wata asabar ta tashi da wani irin ciwon kai da zazzabi kafin kice kwabo ta lafke takasa motsi zuciyarta sai tashi take duk ta rasa ya zatayi hawaye na zubo mata Addua take Allah yasa kada zarginta ya tabbata yau watanta biyu rabon da taga al'adarta.......Wani irin amai ne ya yun'kuro mata a guje ta mike ta nufi toilet wanda yayi dai-dai da shigowar Nanne dakin saboda taji ta shiru shiyasa ta le'ko ta duba lafiyarta kawai ta ganta tana ta she'ka amai a bandaki.[6/13, 8:19 AM] Bintu Novel: 82



Nanne ta tsaya bakin kofar toilet din tana kallonta cike da mamaki gami da zargi.....Aysha kam yunkurin amai takeyi sosai duk ta galabaita sai nishi take da kyar ta mike tsaye Nanne ta taimaka mata sukajw su ka zauna bakin gado.....Suna zama sai hawaye shaaa! ya fara zubowa a fuskarta wani na bin wani.Shikkenan alkadarinta ya karye Omar ya cuceta ya dirka mata ciki shikkenan ta shiga uku! wannan bakin cikin shine ya sanya ta zubar da hawaye wanda ta kasa gogewa.


A nutse tace"Aysha ciki gareki ko."!? Da sauri ta kalli mahaifiyar tata Sai ta hau girgiza kanta wai A'a

"Bana son munafurci Aysha ki fad'a min gaskiya ciki ne dake kike amai da sassafe kome."!?


Murya na rawa tace" Nima ban sani ba Nanne ni dai nasan yau watana uku rabona da Jinin al'ada."


"Dama kina haka ne ina nufin dama kina daukar wata daya ko biyu baki al'ada ba."?


" Ko wane wata inayi." tafada cikin tsanani damuwa zuwa yanzu ta tabbatar da cike ne da ita domin duk ga alamunan sun nuna."


'Bacin rai da takaici bai bar Nanne tace komai ba ta kama hanya ta fita daga dakin kamar ta dora hannu aka don takaici Tabbas jikinta ya bata hakan zata iya faruwa tunda dama tuntuni ta fahimci Halayan Omar sam mutum ne shi mara hakuri da rashin kara da kawaici Sai da burinsa ya cika ya yaudari Ayahan yake kwanciya da ita shin wannan al'amari dame zasu kirashi.

Tana fita aysha ta kwanta nan gefan gadon ta fara kukan bakin ciki wai ciki? ita mamaki ma takeyi har yaushe ta saki jiki dashi da ciki zai shiga yanzu fisabillahi dame zata kira wannan al'amari ji tayi duk duniyar tayi mata zafi tana nadamar rayuwar da takeyi a cikinta.


Zumbur ta mike ta dauko wayarta ta xauna gefan gado tana goge fuskarta numbar sa ta nemo ta fara kira.


Lokacin yana tsaka da aiki yaga kiran bai dauka ba

27 / 29